Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba, dan tasan ba lallai ta yarda da abinda ya kawotan ba, duk da tana goya mata baya amma wannan karan tasan zasu iya samun matsala, dan haka taja baki tayi shiru amma ta saka ido kowane lungu da sak'o na gidan da tasan mahaifiyarta na ajiya, kusan wuni tayi a gidan kafin tayi nasarar ganin k'ullin maganin da suka je suka amso wajen wani mai maganin gargajiya na zubar da ciki, d'auka tayi ba jimawa kuma tace ta tafi gida, tana zuwa bata tsaya komai ba ta jik'a maganin kamar yanda sukayi waccen lokacin tasha, baifi awa d'aya ba cikinta ya fara matsanancin ciwo, lokaci d'aya ta fita hayyacinta kamar ba ita ba, ana haka kuma jini ya biyo baya ya fara mata zuba, Suley ne ya shigo da sallama amma jin ihunta yasa ya hanzarta lek'awa d'akin nata, k'arasawa yayi yana tambayarta lafiya, amma ta kasa magana sai matsar ciki take, tunawa da yayi yanayin daya ganta waccen ranar da kuma tunawa da yayi tana da ciki, ranar farko da ranshi ya b'ace fiye da kima a kan Zeeya wanda har yasa shi zabgeta da mari duk da halin da take ciki, kamar zaiyi kuka yace "Yanzu Zeeya'atu cikin nawa ne zaki zubar? Cikin da muka samu ta hanyar sunna?"

Shiru yayi yana tattara nutsuwarshi kafin ya juyo ya kalleta yace "Insha Allahu indai wannan cikin na halak ne wallahi babu abinda zai same shi, ba zai zube ba Zeeya'atu saiya fito duniyako ba kya so."

Hak'ik'a a duniya akwai bayin da Allah ke musu baiwa ta hanyoyi daban daban, Zeeya'atu kam tasha wahala a banza dan kuwa cikin nan bai zube ba, zan iya kiran haka da dama Allah ya rubuta cikin nan zai rayu kuma zai fito ya taka k'asa, ko kuma na ce Suley bawan Allah ne wanda Allah ya kub'utar da rantsuwarshi saboda kar kaffara ta hau kanshi, (duk hakan mai yiwa ne a wajen ubangiji), saida akayi tafiya mai nisa aka kaita babban asibiti, jini aka k'ara mata tare da cewa a kiyaye gaba, daga haka kuma ta fara rainon cikin, sai kuma sabbin rashin mutumcin data fito da su kala kala, amma sai Suley ya sake banza da ita yana shanyewa kamar yanda ya shanye na baya.

Yau ma kamar kullum daga d'akin shi ya fito cikin shirin fita, ya rufe k'ofa ya juyo kenan kamar saukar ruwan sama sai ko yaji ruwa a jikinshi, saida numfashinshi ya sauke na wucen gadi dan sosai ruwan suka dira a fuskarshi, kusan minti biyu yayi a haka kafin ya bud'e ido ya sauke akan Zeeya dake gabanshi da robar wanke-wanke ita ma tana kallonshi, a hankali ya fara kallon jikinshi ba wai jik'ewa kad'ai kayanshi sukayi ba harda datti na abinci duka, sake kallonta yayi wata zuciya na fad'a mishi yi mata shegen duka gobe ba zata sake ba, amma yana kai kallonshi kan tulelen cikinta da yanzu yake wata na bakwai sai kawai yaji ya k'ak'aro wani murmushin da ganin kasan na bak'in ciki ne, girgiza kai yayi yace " Ke ba shed'an bace Zeeya, dan haka baki fi k'arfin addu'a ba, duk da nasan komai a kanki wanda ba kya tunanin na sani, amma ina miki fatan shiriya saboda ina so na zauna dake cikin aminci ko dan hallacin da mahaifinki ya min a rayuwa, dan haka kije Allah ya shiryeki shirin addinin musulunci, Allah ya ganar dake gaskiya."

Cikin sanyin jiki ya cire rigarshi ya shanyata a zanar data shiga tsakanin filin gidan da k'ofar shigowa, d'aki ya koma ya sake kaya ya fito ita kuma ta ci gaba da kai da kawonta , saida taga harya kusa kaiwa k'ofa tace "Ni idan ka fita ka siyo min masara ina so zan dafa."

Juyowa yayi ya kalleta yace "To, zan siyo miki."

To fa da irin wannan wulak'ancin suke zaune, duk da dai an samu canji ta b'angaren zuciyar Zeeya, amma a halinta kam babu abinda ya sauya, *kwana tashi* a haka har Allah ya sauki Zeeya lafiya, ta haihu kuma haihuwa ta ban mamaki a waccen lokacin, domin kuwa *'yan uku* haka ta haifesu kuma duka maza, ba mutane a kad'ai har gwamnati saida ta shiga lamarin yaran nan ta hanyar basu kyauta da kuma iyayensu, yara sun zo da arzik'i dayawa, dan bayan kyautar da gwamnati ta musu har sarkin garin agadez mai zamani a wannan lokacin saida ya musu goma ta arzik'i, masha Allahu yaea sun ci sunan *Hassan*, *Hussein*, da kuma *Harouna* (wanda suke kiranshi da *Gambo*), duk abubuwan da Zeeya tayi a baya Suley ya manta da su ya kuma mata uzuri, gashi tunda ta haihu abubuwa sunyi sauk'i saboda kakarta da kuma k'anwar ta *Fatime* suke zaune a gidan tare da ita, Fatime yarinya ce mai nutsuwa da kunya, dan ko ido bata had'awa da Suley bare wasa ya shiga tsakaninsu, har tayi arba'in suna tare da ita saboda rainon yaya uku da wahala sosai, ganin idon mutane yasa Zeeya ziyartar d'akin Suley idan dare yayi, yanzu kam sai ladabi da take mishi idan gaban mutane ne amma bayan idonsu kuma halin take siyarwa, a haka wata rana ta shiga d'akin na shi ya nemi hakk'in shi wurinta amma ta zazzaga masa bala'i son ranta, har da cewa ba zata yarda wani abu ya sake shiga tsakaninsu ba bare harta sake haihuwa dashi, murmushi ya mata yace "Kuma gashi kam an fad'a mana a tarihin gidanmu muna da baiwar haihuwar 'yan bibbiyu, sai gashi ke kin fara da uku abun birgewa, mahaifina ma yana da Husseini, sannan k'annai na ma yan biyu ne."

Rana ta farko data fara sanin yana da yan uwa, amma bata nuna wani damuwa ba, zaune yayi a lokacin sosai yana kallonta yace "Zeeya'atu, a k'alla yanzu muna da shekara d'aya da rabi da aure, a wannan lokacin zan iya cewa ni dake bamuyi farin ciki ba, Zeeya kinyi min abubuwa da dama a gidan nan daya kamata ace na d'auki mataki akan haka, amma ban d'auka ba saboda mahaifinki ya min komai a rayuwa, amma daga ranar da kika haifo min yaran nan, na kallesu da idona na kuma tuna wahalar da kika sha wajen haihuwarsu, sai naji kin samu wani girma da matsayi a zuciyata, Zeeya'atu duk da kin k'untata min a rayuwa amma sai naji a duk duniyar nan babu mai so na da k'aunata sama dake, zee'ayatu matsololin rayuwa da muka shiga ne harya jefoni garinku, banda kowa sai yan uwa na mata biyu, wanda har yanzu d'aya daga ciki bansan ina take ba, amma sai gashi lokaci d'aya kin haifo min magada yara maza har uku..."

Rawarda muryarshi takeyi ne yasa yayi shiru ya duk'ar da kanshi, hawaye ne suka dinga zarya a fuskarshi, hakan ne yasa Zeeya jin wani abu a zuciyarta da bata tab'a ji a game dashi ba sai yau, ji take kamar ta tashi ta rarrasheshi amma kuma tana jin ba girmanta bane, saida ya gaji dan kanshi ya share hawayenshiya d'ago ya ci gaba da cewa "Tabbas kyautar daga Allah take, amma kema kinyi k'ok'ari Zeeya, ina godiya sosai ga Allah daya bani su, sannan kema ina gode miki, Allah ya saka miki da alkairinsa, Allah ya baki lafiyar da zaki shayar dasu cikin k'oshin lafiya."

Hak'ik'a maganganunshi Sun huda zuciyarta sosai ta yanda ta kasa ko motsin kirki harya fita daga d'akin, haka aka ci gaba da tafiya duk da Zeeya na jin soyayyar mijin nata amma babu abinda ta rage a game da rashin mutumci, a haka yara sukayi wata uku da haihuwa, zuwa lokacin kuma kakarta ta koma sai Fatime ke tayata kula da yaran, ana haka Suley ya shirya sake komawa ganin iyalinshi, ya so tafiya tare da Zeeya dan taga mahaifarshi ko ya tsira daga gorin da take masa, amma sai Zeeya tace ai babu inda zataje tunda babu wanda ta sani, haka yayi ban kwana dasu ya kuma bar musu duk abin buk'ata sannan ya kama hanya.


*Allah ka mana kyakyawan k'arshe.*

😍
06/06/2020 Γ  12:38 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*BADAK'ALA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*Labarin gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ _*AHALI NA*_πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦

πŸ‡³πŸ‡ͺ *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_11_


Husseina dai dama ba nisa akayi da ita ba daga gidan iyayen ta, dan daga gidan ana hangen gidan nata iyayenta, sai dai kuma a wannan rana taga tashin hankalin da bata tab'a gani ba a tsawon rayuwarta, dan wannan daren nata na farko daren tonon asiri da tashin hankali ya zamar mata, sam *Salisou* bai mata da kyau ba a wannan rana ko nace dare, domin kuwa dukan mutuwa ya mata tare da yi mata saki har uku, daga shi har ita da sauran matanshi babu wanda yayi bacci, kumfar baki kawai yake yana fad'in shi taimakonsu ne yayi ya aureta saboda ganin ta jima babu aure, ashe dai da dalili shiyasa basu samu miji ba, tunda gudun-gudun safiya ya shiga gidan mahaifiyarshi dake had'e da nashi gidan, kaf ya kwashe ya fad'a mata abinda ke faruwa, nan fa ita ma ta d'ora ta ta kalar tijarar tana sababi, abinka ga sanyin safiya da sannan duk wanda yasan unguwar d'an gulbi yasan unguwa ce da babu sarari sosai, hakan yasa kowa kamar har gidanshi akaje aka fad'a mishi saboda yanda mutane dayawa suka fito kallon k'wam, kamar a tatsuniya haka Salisou da uwarshi suka dinga watso yan kayan da aka kaiwa Husseina wacce ita kanta suka turo k'eyar ta waje, banda kuka babu abinda take kamar zata had'e zuciya ta mutu, ga shegen dukan daya mata wanda yasa jikinta yin tsami.

Labari ne ya samu mutanen gidansu suma suka fito dan jin ance da Husseina abin ke faruwa, a lokacin tana tafiya a hankali zata zo gidansu, tana zuwa k'ofar gidan Hassan ya tare k'ofa yace "Gidan nan kike nufin shiga? Ai in kinga haka ta faru to babu raina ne, dan haka tun wuri ma kisan inda dare ya miki, dan ni ba'a zina aka haife bi ba kuma duk zuri'ar mu babu mazinaci, dan haka wallahi ba zan haifi karuwa a gidana ba."

Ramma dake daga cikin soro ce tace "Alhaji haihuwar karuwa na nawa kuma, ai sai dai kar a k'ara, amma kam ka riga daka haifeta."

"Ai kuwa ba dai a gidan nan ba wallahi." Ya fad'a lokaci d'aya ya kalli Husseina da banda kuka babu abinda take yace "Zaki b'ace min da gani ko sai ci uwarki a wurin nan, k'ur'ani ba zaki shiga gidan nan ba, idan kuma uwarki ce ke saki duk iskancin to ki fad'a min saina turo miki ita ku tafi tare."

Zubewa tayi kan gwiwoyinta cikin tsananin kuka ta had'e hannayenta tace "Dan Allah Baba, dan annabi, ka dubi girman Allah ka barni na shiga ciki, Baba bana da inda zanje idan na bar nan."

"To ni ina ruwa na, wannan matsalarki ce ba tawa ba, da da kike iskancin baki tuna da irin wannan ranar ba."

Saratu na k'ofar d'akin ta tana hango duk abinda ke faruwa daga nan, kuka take tana addu'a tare da tunanin yanda akayi haka ta faru, tana cikin wannan tunani ne ta sake jin ihun Husseina wacce Ramma ta sake mik'owa Hassan wani ice daga nan soron wanda ake ajewa saboda lokacin damuna ya fara jibgarta a filin Allah yana fad'in "Kije ki yi karuwanci mana, wannan keta shafa bani ba, dama karuwar gida ce bamu sani bane."

Lokacin ne Saratu ta fito tana kuka tana bashi hak'uri, amma a k'arshe sai yace ta zab'a ko zama dashi ko da 'yarta, bud'ar bakin Saratu cewa tayi "Ita fa 'yata ce data fito daga jikina, ko ka manta da karin maganar nan da ake cewa *namiji goma ba uba goma bane*? Zanyi farin cikin k'arar da rayuwata a tare da 'ya'yana, dan haka na zab'i na tafi tare da ita duk inda zata saka k'afa."

Kama Husseina tayi amma saita sake sulalewa tana kuka tace "A'a Inna, ban cancanci ki ruguza rayuwar aurenki ba a kaina, shekararku talatin da hud'u tare, ba zan yarda yau na zama silar wargajewarshi ba, komai daya faru laifina ne."

"Nima kuma ba zan tab'a bari taki rayuwar ta lalace ba, dan ni tawa rayuwar dama ta jima da gurb'acewa tunda na shigo gidan mahaifinku, dan haka ba zan tab'a barinki ke kad'ai ba bayan bansan ina zaki je ba."

Hannayenta ta rik'e sosai tace "Inna kiyi hak'uri ki barni na tafi, na miki alk'awarin kare mutumci na, sannan zan dawo nan bada jimawa ba, Inna yanzu ran Baba a b'ace yake, zuwa lokacin da zai huce zan dawo nasan zai karb'e ni."

Sun jima suna wannan musayar yawun kafin Husseina ta saki hannunta ta fara tafiya, za tabi bayanta Hassan yace idan har ta tafi bada yawunshi ba Allah ya isa, juyowa Husseina tayi taga tabbas mahaifiyarta fa idonta sun rufe, hakan yasa ta kalli gabanta ta ari na kare da gudu ta ratsa mutanen dake kallonsu ta bar wurin, saboda a lokacin akwai kula da hakk'in mak'wabtaka yasa wani mak'wabcinsu ne ya bi bayanta ya tafi da ita gidanshi.

Kwanan Husseina *takwas* a gidan nan babu wata matsala, babu wani abu da mutanen gidan ke nuna mata na k'yama ko banbanci, duk da Saratu bata zo ta ganta ba saboda tun ranar da abun nan ya faru doka mai tsanani Hassan ya kafa mata, wanda yanzu ko abincin gidan baya bata sai Suley ne idan yayi fafutuka yake kawo mata, sai Suley ne ke ziyartar Husseina yaga halin da take ciki, haka ma yar uwarta Hassana ta zo ta ganta, ana haka kuma sai wata matsalar ta kunno kai, domin kuwa ciki ne ya bayyana jikin Husseina, bayan ta tabbatarwa da kanta tana da ciki shigar wasu watanni da suka gabata sai kawai ta yanke hukunci a kai, da asuba ta bar gidan *malam Yacub* ta shiga gari, dan a tunaninta bata da ciki ma aka wulak'anta ta bare yanzu asan tana da cikin banzan malamin nan.

Yawo take babu wurin zuwa, wanda a lokacin kud'in mota kawai take nema da zai kaita Diffa wajen dangin mahaifiyarta komai rashin dad'in can d'in zaifi mata, amma sai gashi har magriba ta mata bata ma samu abinda zata saka a bakinta ba, dan duk wanda ta nema taimako sai an mata kallon tsaf, ganinta zaune da kyau tsaye da kyau amma tana neman taimako dan mutuwar zuciya, dan haka babu wanda yayi yunk'urin taimaka mata, tana cikin yawo ta had'u da wani babban mutum ta nemi taimakonshi, amma saiya nuna mata idan ita ma zata taimaka masa saiya taimaka har da wurin kwana ma, mik'ewa tayi daga durk'ushin da tayi ta juya baya zata tafi, hawaye ne suka fara mata zarya a ido inda kalmar mahaifinta ke dawo mata a k'wak'walwa ta cewa " *Kije kiyi karuwanci mana*, wannan ke ta shafa bani ba, dama karuwar gida ce ke bamu sani bane."

Wannan maganar ita ta tsaya mata a rai sosai inda shed'an kuma ya rad'a mata tashi hud'ubar a kunne, juyowa tayi da sauri wajen mutumin ta same shi yana shirin tashin motonshi, tana zuwa yace "Ke ya dai, me kika dawo yi?"

"Na yarda." Abinda ta fad'a kenan, kuma wannan kalmar ita ce duk wani makulli na ruguza rayuwarta, shi dai dama d'an tasha ne na gaske, yana d'aukarta daga nan wata unguwa ya nufa da ita inda matattara yan bariki ne, *kara*, wani fili ne da duk wata karuwa ko karuwiπŸ˜‚ ke zama anan, suna zuwa ya abka da ita wata bukka dan dama ba d'akunan basa wuce na kara, saida ya fara cika mata cikinta da gasasshen nama tasha ruwan rada sannan sukayi abinda ya kawo, farkon al'amarin Husseina taji wani iri da ita ga matuk'ar kunya data hanata katab'us, amma bayan komai ya kammala ta kalleshi take shed'an ya cire mata duk wata kunyar da take da ita.

Malam Yacub da suley ne suka shiga nemanta amma shiru, bai ma yarda Saratu tasan bata nan ba har saida aka kwashe kwana biyar, tunda ya sanar da ita ta tashi hankalinta, a lokacin ne fa duk wasu tsofaffin ciwuna da take fama da su wanda basu bayyana sai suka fara bayyana, sosai take jin jiki Suley kuma na fama da k'ok'ari wajen samar mata magani na gargajiya, *ba'a rabu da Bukar ba an haifi Abu*, Alhaji Hassan shima saiya samu had'ari a hanyarshi ta zuwa kasuwa, gawarshi kawai aka dawo da ita gidan, tashin hankalin da suka gani a ranar bai misaltuwa, duk k'ok'arin Suley na ganin mahaifiyarshi bata san halin da ake ciki ba abun ya ci tura, dan koke-koken Ramma da yayanta Barira da Rahmatu shiyasa tasan meke faruwa, nan ita ma jiki ya yamutse aka gaza gane kanta.

Tsawon kwana sha hud'u d'in da akayi na rasuwar Alhaji Hassan Saratu bata san me ake yi ba, saida mak'wabtan su suka taimaka aka kaita asibiti, jinya take sosai inda ake kula da ita a asibiti, wasa wasa sai gashi ta kwashe sati biyu a asibitin, bayan an sallamota kuma sun dawo gida da kwana shida akayi wa Hassan sadakar arba'in.

A ranar kuma a gaban mutane Ramma ta nemi yan uwan Hassan da maganar a raba gado tunda anyi arba'in, duk da abun bai ma kowa dad'i ba amma dayake ta riga data dasa musu shakkunta a zuciyarsu yasa suka amince da maganar, bayan kwana biyu da faruwar hakan Ramma ta yiwa Suley kurciya ya bar gida gaba d'aya, wayar gari akayi babu shi babu dalilinshi, abun bai tashi hankalin saratu ba saida aka kwashe kwana uku, a haka kuma Ramma ta tilasta aka raba gado duk da a lokacin akwai k'arancin ilimin addini, an raba gado yayanta sun samu rabonsu inda saratu aka bata abinda ko kashi d'aya na mace d'aya bai kai ba, wannan bak'in cikin da k'uncin yasa Saratu ita ma cewa ga garinku nan, haka ita ma akayi na ta makokin inda abinda aka basu ya zama k'ark'ashin kulawar Hassana.

*Duk* abin nan dake faruwa Husseina na cikin garin, inda gaba d'aya ta lalace ta zama karuwa mai lasisi, duk da ba kowane lokaci take zaune garin maradi ba, dan wasu lokuta mawak'a suna d'aukarsu su tafi dasu wani gari dake nigeria da ake kira *hirji*, cikin jikinta kuma magajiya uwar karuwai ta so a zubar dashi amma tace a'a, da haka ta dinga rainon cikin kusan a wannan lokacin ita ce karuwar da wasu suka fi nema suna bayar da kud'i masu yawa dan su kwanta da ita saboda tana da ciki, saida cikinta ya tsufa ta aje harkar na d'an lokaci har saida ta haihu, namiji ta haifa wanda mata masu zaman kansu sukayi babban bidiri, mawak'a suka baje nasu kolin daga ciki harda irinsu margayi *Sa'adou bori*, ranar suna an kwana ana cashewa daga k'arshe dai yaro ya ci sunan *Labaran* a cewar Husseina shi yafi kowa bawa gidan karuwan tallafi, dan haka ya cancanci a mishi takwara, (duk wannan fa abun ya faru),duk da a lokacin ta samu labarin mutuwar mahaifinta amma sai tace "Allah raka taki gona."

Rasuwar mahaifiyarta kad'ai ta girgiza ta data samu labari, amma duk da haka bata je gidan ba saboda tace bata son sake ganin unguwar ma, haka ma wajen Suley tafiya kawai yake yi, yunwa na ci k'ishin ruwa na ci, domin duk abinda yake samu yasa a cikinshi ba isarshi yake ba, hasalima ba komai ne yake samu mai kyau ya ci ba, haka yake tafiya ba um ba um um, ya galabaita sosai ya jikkata ta yanda ya fita hayyacinshi, haka Suley ya d'auki tsawon lokaci yana tafiya ba tare da yasan inda yake saka k'afar sa ba har tsawon *wata biyu*, a cikin tafiyarshi ne Allah ya had'a shi da wani mutum mai kirki d'an kasuwa mai sunan *Alghabit*, mutumin *Agadez* ne kuma hamshak'in mai kud'i, yana kan rak'uminshi ya ga Suley na tafiya kamar gunki, kallo d'aya ya masa ya tabbatar yana tare da k'ishin ruwa da kuma yunwa dama gajiya, dan kuwa har k'afafun shi sun kumbura kamar na mai tsohon ciki saboda tafiya, tsayar da rak'umin yayi dan a wannan lokacin shine abun hawan kuma mai daraja garesu, duk da akwai mota a lokacin amma dai bata damesu ba kamar rak'umi ko kuma moto, saida rak'umin ya durk'usa har k'asa ya sauka ya tunkari Suley, tare gabanshi yayi yana mishi magana da gurb'atacciyar hausarshi daya d'an kama wajen yawon kasuwancinshi a bakin hausawan, ganin kallonshi kawai yake ya tabbatar ba lafiya yake ba, hannunshi ya kamo ya zo kusa da rak'uminshi ya d'auki aglami (buzun sallah) da gorar ruwa da kuma wani d'aurin abu a cikin fata, gefe suka koma k'ark'ashin wata bishiya ya shinfid'a aglamin ya zaunar da Suley, ruwan ya fara bashi ai ko da sauri ya fizga daga hannunshi ya kifa baki bai sauke ba saida ya shanye, da mamaki da kuma tausayinshi ya zauna kusa da shi ya bud'e wannan d'aurin ashe akushi ne a ciki da abinci, nan ma abincin nan ya ci sosai kafin ya sake bulbulo mishi ruwa a yar babbar jarkar da ke d'aure da rak'umin. Tare ya tafi da shi a d'ora shi akan rak'umin, idan dare yayi su yada zango da safe su ci gaba, kwana goma sha bakwai suka d'auka kafin suka isa garin agadez.

*A garguje*

Haka ya sauke Suley gidanshi da taimakon iyalinshi, inda ya samu limamin unguwarsu ya zo da shi har gidan ya nuna mishi Suley, daga lokacin aka d'ora shi akan magani da rok'on Allah, Allah maji rok'on bayinsa sai gashi cikin *wata biyu* Suley ya samu lafiya ya dawo kamar yanda yake, Alghabit dama 'ya'yanshi mata ne suka fi yawa, dan haka saiya rik'e Suley kamar d'an daya haifa, tunda jiki yayi kyau sai Suley ya d'aura d'amarar neman kud'i dan yaje ga ahlinshi ya tallafesu, hakan yasa duk safe ta Allah ya kan shirya ya fita kasuwa, lokuta da dama dakon kayan mutane yake ana biyanshi kud'i kad'an, wani lokacin kuma idan kayan manyan yan kasuwa sun zo sai su sauke kayan a biyasu, da irin wannan k'ok'arin na shi ya fara tara kud'in komawa gida, duk lokacin da zai fita idan Alghabit ya tambayeshi sai yace zaije zaga gari ne kawai, a haka wata rana Alghabit ya sake komawa fatauci, a lokacin ne Suley ya fahimci wani ha'inci da ake mishi idan baya nan kuma a cikin gidanshi, babbar 'yarsa *Zeeya'atu* wacce gaba d'aya shekarunta basu haura sha shida ba tana ganin ya bar garin ita ma zata fara na ta yawon dan jin dad'in rayuwarta, kuma mahaifiyarta *Zaha* iya ke d'aure mata gindi tana bata umarni, babban tashin hankalin shine wani lokaci har ta kan iya kwana ba gida ba, nan yayi niyyar sanar da mai gidan idan ya dawo, domin kuwa babu mai zarginta, dan idan ta tashi fitar ta kanyi shiga ta kammala sannan tayi nesa da gida.

Bayan Alghabit ya dawo tuni sauran yaran dake tayashi kasuwanci suka rigashi isowa tare da sauran rak'uman dake d'auke da kaya, dan haka kai tsaye ya wuce kasuwar garin dan a sauke wannan kayan a rabawa k'ananan yan kasuwa, a nan fa yayi kicib'us da Suley a cikin masu sauke kayan, wannan abu shi ya birgeshi a tare da yaron ya kuma ji ya yarda dashi ba ko kokonto, hakanne yasa ko da suka iso gida bai bawa Suley damar fad'in abinda yayi niyyar fad'a ba yace ya d'ora shi akan harkokinshi, yanzu ya zama kamar magajinshi zai dinga tafiyar da komai, wannan karamcin da wa suley ya sa bai iya fad'an komai ba saboda kunya, ba b'ata lokaci Suley ya durmiya cikin kasuwanci ya fara

Please Login or Register in order to submit comment