Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai takwas na dare, yana fitowa daga mota yaran suka dinga gaishe shi, da ido ya bi kowane yana kallo har suka shige ciki, juyawa yayi yana kalkad'a makullinshi ya nufi na su b'angaren.

*12:50* motoci uku suka tsaya k'ofar gidan, biyu daga cikin motocin na sojoji ne sai wacce ke tsakiya ita ce babba k'irar *Prado*, da sauri sojan dake tuk'a motar ya fito tare da zuro hannu ya bud'e mazaunin baya, colonel Hussein ne ya fito da k'arfin shi, yana fitowa sojojin suka k'ame suna sara mishi, saida ya kallesu ya sara musu sai suka saki na su hannu shi kuma ya wuce ciki tare da rakiyar soji biyu, saida ya kai k'ofar shiga falo suka tsaya shi kuma ya juyo ya kallesu yace "Dukanku zaku iya tafiya, amma *sajan* (sergent) Idris zai iya tsayawa." Yana fad'a ya wuce suka bishi da "Ok chef."

Duk wanda ya shiga wanka yake farawa da shi, ga mai buk'ata kuma ya nemi abinci ya ci sannan ya kwanta ya huta, amma colonel bayan sun dawo daga masallacin juma'a tare da Ammar bayan gidan suka nufa inda ke da fili da tarin shukoki da kuma kayan motsa jiki barkatai suka fara abinda suka saba indai suna tare, haka ya zage ya dinga koya mishi horon soja wai saboda kare kai kuma tunda yana son abun, a k'alla sun d'auki awa d'aya kafin suka had'a gumi kowa ya shiga dan yin wani wankan, bayan colonel ya shiga yayi wanka ya fito ya canza kaya, zai fita Hajia Zeinabu tace "Yallab'ai ina son magana da kai fa."

Dawowa yayi ya zauna bakin gadon yana kallonta yace "Uhum."

Duk da bata had'a ido da shi ba amma gabanta fad'uwa yake, haka ta daure tace "Dama ina so na ji ko yaushe ne hutunka zai k'are?"

Fuskar nan ba fara'a yace "Tun yaushe nake garin nan? Ba kya lissafi ne?"

Cikin rarraba ido tace "Ba haka bane, dan naga yanayin aikin naku ana iya kiranku ma ko wa'adin bai cika ba."

Tsura mata ido yayi yace "Me kike so ki fad'a?"

"Kawai zaman gidan nan ne ya gundure ni, ina buk'atar wani abu da zai rik'a deb'e min kewa, tunda na ga ita Sa'ada tana zuwa aiki, kuma ba finmu tayi ba karatu ne kawai bamuyi ba."

Wani kallo ya sake mata kamar zai had'e ta kafin ya mik'e yace "Alhamdulillah da Allah yasa da mai hankali nake magana ba mahaukaciya, ashe kinsan sai wanda yayi karatu ne zai iya shiryawa yace zai tafi wajen aiki?"

A tak'aice tace "Kai ma ci mana mutumci zakayi?"

"Kinga Zeinabu, matsalata dake tsegumi, kuma rashin wayewarki ne ya haddasa miki haka, shiyasa na so tun farko ki shiga ko da makarantar yak'ida jahilci ce amma ki ka k'i, ga Jibril nan kina ganin aikinsu kenan kullum, idan kinso ko shi zai iya yi miki hanyar samun hasken k'wak'walwa."


Kallonshi tayi da takaicin abinda yake fad'a mata tace "Dan bana da ilimi shiyasa dama ba ka iya zuwa ko ina dani, to ai sai ka d'auki karuwan naka ka dinga yawo da su tunda sun fini."

D'an cije leb'en shi yayi yana kallonta yace "Ni kike fad'awa ina da karuwai Zeinabu?"

A yanda yake kallonta tasan tsaf zai mareta dan ba bak'on abu bane a wurinsu, duk da baka shaidar mutum amma a zahirance zata iya cewa mijinta baya shan giya ko neman mata duk da kasancewarshi soji, dan duk inda yake ya ji shaid'an na neman kaishi ga aikata zina haka zai biyo jirgi ya zo wajenta, dan har doguwar tafiya ya tab'a yi ya zo kuma ko awa baiyi ba ya koma, matsalarshi d'aya saurin hushi da marin fuska ko harbi da k'afa idan ta mishi nisa, shi ma kuma ya fad'a mata ta dinga kiyayewa tana sanin me zata fad'a mishi saboda yana da zuciya tun fil'azal daman ba wai dan yana soja ba, amma inda aka samu matsalar Zeinabu irin matan nan ne masu tsegumi da ganin an musu ba daidai ba, dama dama Hajia na gyara musu zama, amma in zaiyi shekara baya gari ya samu hutun wata uku ya zo sai tace ga abinda akayi, kuma idan ka duba sai kaga k'orafi ne kawai na banza da wofi, gashi matsayin wasu yana tsone mata ido musamman Sa'ada, ta mayar da ita kamar kishiyarta duk wani motsinta akan idonta, sanin halinshi yasa ta kawar da kai gefe tana gunguni tana fad'in "To k'arya na fad'a? Matan ne baka kul...?"

Bata gama fad'a ba taji saukar yatsu biyar a fuskarta, d'ago fuskarta yayi cikin d'aga murya yace "Kalleni nan ki fad'i duk abinda ke ranki, ke har ni zaki mayar d'an iska, dan kinga na zauna tare da ku har na wata biyu shine zaki d'auke ni wani mahaukaci, to yau zan bar miki garin sai ki d'auki tsiyar da kike d'auka idan bana nan, aikin banza." Ya fad'a yana barin d'akin, tana ganin fitarshi ta d'ago tace "To ka tafin mana sai me? Idan baka nan b'acin raina yana raguwa ne da kaso arba'in cikin d'ari, kai ka k'unsa min bak'in ciki mahaifiyarka ta tusa min, mun zama kamar bayi a gida duk saboda bamuyi karatu ba."

Ko da su Hamna suka dawo aka fad'a musu Abbansu ya tafi basuyi mamaki ba, dan haka basu damu ba saima shirya fita da sukayi da yamma dan su siyo ankonsu suma, baccin rana sukayi ko da suka tashi la'asar tayi sai suka shirya cikin dogayen riguna bak'ak'e iri d'aya, komai na jikinsu kala d'aya suka saka ta yanda ba zaka iya tantacewa cikin sauri ina Hamna ba ko Amna, tun a d'aki suka fara rigima moton wa za'a hau? Nan Hamna tace ai da nata aka tafi Γ©cole, Amna kuma tace jiya da nata ai aka tafi, k'arshe dai dana Amna aka tafi dan dukansu basu damu da matsayinsu ba ko na mahaifinsu, shiyasa ko dreba basu damu a d'aukar musu ba bare a siya musu mota.

Tun a falo suke jiyo hayaniya a farfajiyar gidan, can suka samu yara da iyayen ana ta hira sai dai babu Hajia babba, saida suka dawo d'akin ta da sallama amma ba'a amsa ba, wata sallamar suka sake yi Hajia dake zaune tace "Ku shigo mana."

Shiga sukayi duk jikinsu yayi sanyi dan kar ta hana su fitar, Hamna ce tace "Hajia barka da yamma."

Kallonsu kawai tayi bata amsa ba dan haka Hamna tace "Hajia dama..."

"Dama me?" Ta katseta, d'orawa tayi da "Fita zakuyi ko? To ku tashi ku tafi, amma ke Hamna ki sani na barki ne saboda na ganku tare da Amna, dan na lura duk shegen bak'in halin uwarki ne kika d'auko na rashin son zama wuri d'aya."

Shiru sukayi har saida tace "Ni ku tashi ku bani wuri, saura kuma idan kun tafi karku dawo sai an aika nemanku."

Mik'ewa sukayi sai Amna da tace "Mun gode Hajia, insha Allahu ma ba zamu jima ba zamu dawo."

Suna fitowa Hamna ta yaye kallabinta ta zubo da manyan kitsonta na gashin doki har gadon baya tare da fad'in "Shikenan dan uwarmu bata gidan saiki d'auki karan tsana ki d'ora mana, dad'in ta dai bamu muka kashe musu auren ba."

Suna fitowa farfajiyar suka kalli matan suka ce "Su tanti (aunty) sai mun dawo."

Hamna ce ta tuk'a mai gadi ya bud'e musu k'ofa suka fita, a k'ofar gidan suka samu colonel da Ammar zaune kan kujeru, hira ce suke amma babu mai annuri a fuskarshi, dama kana ganin Ammar na hira ne da mutum biyu a duk fad'in gidan, ko dai colonel ko kuma Gambo, da kaga dariya ko murmushinshi to Gambo ne, tsayawa tayi tace "Kawu ana hutawa?"

"Ina zakuje kuma da yammar nan?" Ya jefo musu tambayar, cikin turo baki tace "Kawu zamu je yar kasuwa ne, amma yanzu zamu dawo."

Kunna moton tayi yace "To dan Allah ku kula da kyau, sannan karku yarda magriba ta muku a waje."

"To kawu." Ta fad'a tana murd'a moton, kallon Ammar tayi tace "Boss ba ko magana."

Sai lokacin ya d'ago idonshi ya sauke a kanta amma tuni harta ja moton da k'arfi tana mishi dariya, dariya colonel yayi yace "Saika nuna mata kai boss d'in ne ko zaku kwashe lafiya da ita."

K'ala bai ce ba shi dai dan yana so ne ya lissafa duk iskancin data masa ta yanda idan ya damk'eta zata gane shayi ruwa ne, inda shi kuma colonel yake mamakin yanda Gambo ya bar yaranshi sakaka a gari haka ba zaka tab'a cewa wasu 'ya'yan manya bane, sa'a d'aya ma yaran su kansu basu damu ba harkar gabansu suke.

Tashi colonel yayi ya shiga cikin gida yana jin shi sakayau, dan dama sai mutum ya zo hutu ne yake samun 'yanci da sakewa, ya shiga ne da niyyar yin wanka ya kuma had'a kayanshi, dan yayi niyya saiya bar garin ko zeinabu ta ji dad'i, ya shiga d'aki kenan ya aje wayar zai shiga ban d'aki sai wayar ta fara ruri, dawowa yayi yana kallon mai kiran, d'an uwanshi ne wanda yake da tabbacin yana garin nan wato Abban su Amar, to meyasa yake kiranshi? Tabbas ba lafiya zuciyarshi ta gaya mishi, d'auka yayi ya d'ora a kunne, daga b'angaren lieutenant yace "...


*Me kuka ya faru ko zai faru?, sai mun had'e a shafi na gaba insha Allah.*
18/05/2020 Γ  13:51 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*BADAK'ALA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ _*AHALI NA*_πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦


_Bismillahir rahamanir rahim_

_4_

Lieutenant ne yace "D'an uwa kaga na kiraka ko? Dama yanzu na samu wayar *Aisata* (babbar d'iyar Fatime kanwar Hajia) take fad'a min Allah yayi wa Hajia (mahaifiyarsu) rasuwa."

Takawa colonel yayi gaba yana fad'in "Subhanallah, Hajia kuma? Yaushe? Dama bata da lafiya ne?"

Wani d'an murmushi lieutenant yayi yace "Haba d'an uwa, mutuwa ai ba sai ba'a lafiya ba take zuwa, dan nima dana tambaya Aisata ta fad'a min yau da safe ma har unguwa Hajiar ta fita, kawai dai lokaci ne yayi."

"Ikon Allah, kaga wata mutuwa bagatatan, yanzu to ya zamu sanar ma da Hajia?"

"Shiyasa na kiraka d'an uwa, dan kaine soja watak'ila ka fini sanin dubarun kwantar da hankali."

Yanda ya k'arashe maganar cikin zolaya yasa colonel cewa "Ba fa nasan iskanci, ka d'auka a sojan rarrashin mata da soyayya ake koya mana ne, ai wannan aikin ko Ammar ba zan sa shi ya fad'a mata ba."

Dariya lieutenant yayi ya mik'e daga kan teburinshi wanda ke cike da tarin takardu da tarkace yace "To ni dai na fad'a maka kasan yanda zakayi karka d'aga mana hankalin uwa, yanzu haka gani nan tafe zuwa gidan zan canza kaya, dan ina so na samu bisar Hajia dan sunce k'arfe hudu da rabi za'a rufe ta."

Da sauri colonel ya kalli agogon dake d'akin yace "Eh to, kuma kaga fa da sauran minti talatin da wani abu, kana ganin zamu iya isa *Gidan roumji* nan da wannan lokacin?"

"Sosai ma, kai dai kawai kuyi harama, duk wanda yasan zaije ya kimtsa da wuri mu d'auki hanya, zan kira Labaran na fad'a mishi shi ma nasan zaije."

"Shikenan." Yana fad'a ya kashe wayar ya shiga neman wata lambar, ana d'auka ya bayar da umarnin motocin d'azu su dawo zai fita shi da iyalinshi, yana gamawa ya shiga wanka cikin k'ank'anin lokaci ya fito ya shirya cikin bla (bleue) d'in shadda amma kanshi ba hula, wayarshi ya figa ya fito ya nufi d'akin Alhaji, ba wani b'ata lokaci ya fad'a mishi abinda ke faruwa tare da cewa su fito yanzu zasu d'auki hanya, lieutenant ma na shigowa wanka ya zarce kai tsaye ya shirya da gaggawa, Alhaji da kanshi ne ya samu Hajia a d'aki yace ta saka gyalenta zasu fita, tayi tambayar ina? Amma bai bata amsa ba, da haka ta fara gunguni tana saka tsadadden gyalenta ta d'auki takalmi masu shegen kyau da jakarsu ta saka, waya a d'aya hannu sai mouchoir (handkiciep) a hannu na goge k'ura da datti, haka ta fito cikin takon izza da k'asaita suka nufi k'ofa, a farfajiyar gidan suka samu mata da yara, lieutenant ne ya kalli matan yace "Mu zafi tafi gidan roumji sai Allah ya mana dawowa, akwai yiwuwar mu kwana acan, dan haka ku kula da gidan da yaran."

Zeinabu ce ta kalli mijinta tace "Wani abun ne ya faru yallab'ai?"

D'an juyawa yayi ya kalli Hajia da sai wani yamutsar fuska take ya kuma kalleta yace "Ba komai, zamu kiraku idan mun isa can, kuma gobe zan turo a d'auke ku."

Muryar Hajia ce ta katse shi tace "Wai meye ya faru a gidan roumjin? Ko dai wani abu ya samu Fatime ne?"

Lieutenant ne yace "Ba komai Hajia, idan munje sai muji meke faruwa."

Cikin had'e fuska tace "Ku tabbatar ba wahalar banza zaku sani nayi ba, dan na tsani na kwashi jiki na je k'azamin wuri kuma ba da wani dalili ba."

Kafin wani yace wani abu Labaran ya shigo a hargitse da sallama, kamar wanda yayi gudu yace "Wai har kun shirya? To zamu iya tafiya kenan?"

Cikin tafiya kamar ta saurayin doki Ammar ya shigo saboda kawu Labaran ya fad'a mishi komai, lieutenant ne ya kalli Ammar fuska ba walwala yace "Ka kira sauran yan uwanka ku same mu acan, ba wai kowa yayi tafiyarshi ba nake nufi, ku tabbatar kanku a had'e kuka tafi, kai kuma ka wuce ka canza wannan kayan na jikinka, kar wanda ya kuskura ya zo mana da shigar turawa a wurin jama'a."

Kamar wanda ciwon kai ya dameshi haka ya juya ya nufi b'angaren su ko magana babu, su kuma suna jin tsayawar motoci suka fito, colonel da kanshi ya bud'ewa su Alhaji suka shiga motarshi mazaunin baya, shi kuma wani soja ya bud'e mishi ya zauna gaba, motar soji ce gaba saita colonel sai kuma wata motar ta soji a baya, sai motar Labaran wacce lieutenant ke ciki suka d'auki hanya, tunda suka samu titi suka bud'e wuta ake gudu sosai saboda suna so su isa da wuri, a lokacin ne Alhaji ya kalli Hajia ya fara da bata hak'uri da kuma tausarta kan haka Allah ya so, nan ya fad'a mata k'anwar ta ce ta rasu, dafe k'irji tayi tace "Fatime, ta rasu?"

Kallon titi tayi tace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, Fatime lokaci yayi, shikenan yer uwata ta tafi ta barni."

Jimami ta dinga yi amma dai babu kuka ko alamun razana a tare da ita, da haka kuma cikin ikon Allah sai gasu gidan roumji cikin minti ashirin da bakwai, ko da suka iso anata shirya shiryen kawar da ita, nan Hajia ta shiga cikin ciki mazan kuma suka shigar da mitocisu cikin layin masu rakiyarta gidanta na gaskiya.

Ko da Hajia ta shiga gidan bata gaisa da kowa dake waje ba tayi cikin d'aki cikin jagorar autar margayiya duk da kana ganinta zaka san tasha kuka, tana shiga d'akin ganin mutane ga zahi yasa ta wani had'e fuska tasa jelar gyalenta ta fara firfita, autar Fatimen ce tace "Hajia ku shigo nan ciki."

Bayanta ta bi har suka shiga d'akin margayiya, kan gado ta zauna inda autar ta juyo mata da pankar dake aiki, juyawa tayi zata fita Hajia tace " *Sayyada*."

Juyowa tayi ta amsa da "Na'am Hajia."

Cikin gatsina fuska tace "Ki bud'e min tagar nan." Ta fad'a tana nuna mata tagar dake gefe da yatsa, da sauri ta bud'e mata sannan ta juya ta fita, kafin ta shigo kuma mutanen da suka shigo gaishe da Hajia da yi mata ta'aziya basu da adadi, duk da ita bata kula su ba amma dayake a dangin kaf babu wanda Allah ya hore ma abun duniya da matsayi da iko kamar ita, shiyasa suke girmamata suma a dolensu, har yaran margayiya su ne da kansu suka shigo akayi wa juna jaje, suma mazan suna dawowa daga bisa suka shigo aka k'ara jajantawa da bawa juna hak'uri, saida mutanen suka tsagaita Sayyada ta shigo da karap (jug) mai kyau da kofi ta zubawa Hajia gumbar da aka had'a mai sanyi, tana mik'a mata ta girgiza kai tace "Um um bana sha."

Duk da ba gari d'aya suke ba amma Sayyada tasan ta farin sani, dan haka bata damu ba ta juya zata fita da shi sai kuma tace "Kinga, idan kin fita..." Sai kuma ta kalli wayarta tace "Jeki ma ya isa."

Fita tayi inda ita kuma ta d'auki wayarta ta dannawa colonel waya dake zaune k'ofar gida, yana ganin lambar Hajia saida gabanshi ya fad'i saboda tunanin abinda za tace masa yayi, cikin sauri ya d'auka ya aza saman kunne tare da fad'in "Assalama alaikum Hajia."

Cike da iko da nuna ita ce gaba dashi tace "Ruwa mai sanyi da lemun da kasan ina sha nake so, ba kuma wani nake buk'atar ka aika ba, kai da kanka zaka je ka samo sannan ka kawo min, ina d'akin Fatime."

Tana gama fad'a ta datse kiran, d'auke wayar yayi a kunne ya kalli lieutenant dake kusanshi mutane na ta kallonsu abun birgewa saboda ganinsu iri d'aya sak, yunkurawa yayi zai tashi lieutenant yace "Ina zuwa kuma? Lafiya dai ko?"

Cikin rad'a yace mishi "Zanje aiken Hajia, yanzu zan dawo."

Kallonshi yayi da kyau yace "Amma ga yaranka nan ka basu mana."

Had'e fuska ya sakeyi ya wuce bai kula shi ba, yaranshi dake gefe suna ganin haka suka matso suna sara mishi, ko kulasu baiyi ba ya saka takalmi zai fara tafiya ya ji suna take masa baya, juyowa yayi rai b'ace yace "Meye kuma na bi na, ku jira ni na dawo to, wannan ba aikin gΓ©nΓ©ral bane ko aikin k'asa zanje yi, uwata ce ta aike ni, ko dole sai kunga me zanje yi."

Yana fad'a ya wuce kamar zai tashi sama musamman abinka ga tafiyar mai k'arfi, su kam da bayar da hak'uri suka bi bayanshi suna jinjina girma girma ne, duk girmanka da tsiyarka uwa ko uba ko mata sai su juyaka, kai idan ma ka zama lusari har 'ya'yan daka haifa sai su juyaka yanda suke so, da k'yar ya isa shagon daya samu duk abinda take so, da kuma yasan cewa tana son yaour sosai sai kawai ya siyo ita ma, dan k'aramin aikinta ne saiya kawo tace kuma tana son ta, haka colonel ya kinkimo bak'ar ledarshi a hannu ya taho da ita, sabo da kuma sanin kan aiki yasa d'aya daga cikin yaranshi suna ganinshi yayi saurin mik'ewa zai nufi wajenshi, wasu jajayen idanu colonel ya zaro mishi hakan yasa ya k'ame wuri d'aya, cikin gidan ya haura ya shiga ya wuce d'akin, yana zuwa ya sameta zaune ita kad'ai a d'aki kamar mayya, ita ba zata iya shiga mutane ba saboda k'yank'yamin su take tana ganin ta wuce ajinsu, durk'usawa yayi akan tafukan k'afafun shi ya fara bud'e ledar yace "Hajia ruwan zan baku?"

Ba tare data kalleshi ba tace "Umm."

Bud'awa yayi ya bud'e murfin robar ya mik'a mata, karb'a tayi tasa abin goge gogen nan na hannunta ta goge bakin robar sannan tasha, gefe ya aje mata sauran yace "Ga sauran nan Hajia ko zaku buk'ata."

Wani kallo ta masa tace "Hussein yanzu dayawa ka siyo saboda kar anjima nace ina so ka sake wahala? Tafiyar ce ka ke jin wahalarta ko me?"

K'asa yayi da kanshi yace "Ba ko d'aya Hajia, na dai siyo ne ko zaku iya buk'atar su a kowane lokaci."

Cikin b'acin rai tace "To bana so Hussein, ka d'auka ka fitar min da su yanzun nan, idan buk'atar ta tashi zan sake nemanka."

D'aukar ledar yayi yace "Shikenan Hajia, Allah ya huci zuciyarki."

Har ya kusa kaiwa k'ofa tace "Ka ban lemu d'aya."

A hankali ya bud'a ledar ya fito da kwalin lemu ya sunkuya ya aje mata k'asa gefenta, yana d'agowa suka had'a ido ta mishi wani kallo tace "Cewa nayi fa ka bani, shine zaka aje k'asa."

"Yi hak'uri." Ya fad'a yana sake d'auka ya bata ga hannun, amma sai cewa tayi "Aje kawai zan d'auka." Ajewa yayi ya juya ya fita yana addu'a a ranshi Allah ya k'ara musu hak'urin zama da mahaifiyarta su, dan iyaye irin mahaifiyarsu wuyar sha'ani ne da su ba kad'an ba.

Lieutenant ne ya kira Gambo ya sanar da shi, nan fa aka bi duk 'ya'yan margayiya ana bashi yana musu ta'aziya, kafin daga bisani ya sake cewa a mik'a ta'aziyarshi ga kowa dake wuri dan ba lallai ya samu lokaci ya zo ba tunda ya riga da ya bar garin.

*Bayan tafiyarsu*

Ammar n ma shiga d'aki ya fara tunanin wanda ma zai fara kira a cikin su ukun, tunda Jibril shi baya garin watak'ila zuwa gobe yaje idan ya dawo, ba komai yake dubawa ba sai doguwar maganar da zaiyi da su, kuma ya tabbatar duk wanda ya kira saiya tambaye shi ya akayi? Ya ake ciki? Me ya faru, me zai faru? Dan haka ya yanke shawara ya kuma rubuta sak'o ya had'e duka lambobin nasu ya aika musu, kowa na inda yake wannan sak'o ya shigo na su zo gida yanzun nan zasu wuce gidan roumji Hajia Fatime ta rasu, duk basuyi mamakin ganin sak'on ba saboda ganin wanda ya turo shi, cike da jimami kowa ya antayo motarshi ya nufo gidan.

Kamar had'in baki saiya zamana babu wata tazara tsakanin zuwan nasu, kuma kowa b'angaren su yake nufa dan ya shirya babu mai tunanin aiki gobe tunda dama asabar ce, sa'a akayi Junaid zai shiga d'akin shi Amar kuma ya shigo falon, nan Amar ke tambayarshi "To wai yanzu hanya zamu d'auka kenan?"

Junaid ne yace "Yanzu ba wannan ba, mu fara saurin kimtsawa dai, daga nan sai mu san abinyi, dan kasan gidan nan akwai yan gaggawa dayawa, babu wanda zai jiramu idan..."

Fitowar Ammar cikin bak'in yadi shara-shara har ana ganin farar rigarshi yasa sukayi shiru suka kalle shi, kamar dai kullum fuska a tamke ya kalli Junaid yace "Su waye yan gaggawa a gidan nan?"

Juyawa Amar yayi ya nufi d'akin shi yana fad'in "Na gode Allah da yasa tambayar nan taka ce d'an uwa, fatan alkairi."

Junaid kuma murmushi yayi yace "Ah haba dai soja, cewa nayi dayake gidan nan akwai..."

Da gudu ya shige d'akin shi ya rufo k'ofar daga ciki yake fad'in "Yan gaggawa na ce, kuma kaine farko, sai wannan kawun naka (mahaifinshi kenan) colonel yake ko me ma."

K'anan Jibril ne ya shigo da sauri wanda yake da tare da mahaifinshi Labaran a kasuwa suna kasuwanci shi ma ya shigo dan shine na uku da Ammar ya turawa sak'on duk da suna gaba dashi nesa ba kusa ba, kallonshi Ammar yayi yace "Ka fad'a ma yaran nan ina jiranku waje nan da minti biyar, idan lokacin nan ya cika baku fito ba, to zan tafiya ta ne tunda kowa da motarshi ai, amma ka fad'a musu umarnin Abba ne yace mu tafi tare."

Yana gama fad'a ya fice daga d'akin inda *Jamil* ya bi dak'unan daya nuna mishi da kallo, k'wank'wasa musu k'ofar yayi ya sanar da sak'on Ammar kafin shima ya shiga dan shiryawa.

*Minti hud'u* Amma ya fara doka wata uwar oda data firgita duk wanda ke cikin gidan, wad'anda suka san da su ake tuni suka gigice suka rasa ma abunyi, ba tare daya daina odar ba sai kuwa gasu da gudu suna rige rige, Jamil bawan Allah ko d'akin shi bai rufe ba ya taho da gudu da takalmi a hannu da k'yale alamar gogewa zaiyi ko yake cikin yi, bud'e k'ofofin motar sukayi suka zauna Junaid yace "Dan girman Allah odar ta isa haka, gamu nan fa mun shigo ko."

Amar ne ya doka wani uban tsaki saboda sai lokacin ya kula da abin goge bakin (brush) daya taho dashi a aljihu, juyawa sukayi suka kalle shi ai sai Junaid ya kwashe da dariya, cikin jin haushi Amar dan ko turare bai fesa ba yace "Kai ban son k'ananan iskanci fa."

Mayar da kallonshi yayi ga Ammar yace "Allah Ammar ba ka kyautawa, yanzu shirin ma ka barmu mu tafi a tsanake amma ba zaka iya ba, wane wace

Please Login or Register in order to submit comment