Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amma tuni har ya shige, yana shiga kuma Hamna ta fito da hijabi sai turo baki take, ko kallonta baiyi ba saboda fad'uwa da yaji gabanshi yayi, kamar yanda ya saba babu sallama babu fara'a ya k'arasa yana kallon kujerar Alhaji amma kuma baya nan, tun kafin ya isa kusan Hajia ya wani d'aga mata hannu irin na inka had'u da mutum a kan hanya kuna kan ababen hawa wato yar hannu, kai tsaye ya sauke hannunshi yace mata "Barka da zama."

Ummy da tunda ya shigo dama take takaicin wannan d'abi'a tashi ta rashin sallama hararanshi tayi, wato dai baya jin magana? Yanzun ma so yake saiya ja mata bala'i sannan ya bar gidan, lieutenant ma kallonshi yake wato ita Hajiar ta ma samu barka da zaman? Su kuma ko oho ko? Juyawa yayi ya kalli Ummy yace "Na jiraki ne ko zaki taho a motarki?"

Rarraba ido tayi tana tsoron bashi amsa Hajia ta juye kanta, lura da yayi da hakan ne yasa shi juyawa ya kalli Hajia, ganin tana hararenshi tana so taga gudun ruwanshi yasa ya kalleta da kyau yace "Shi kuma wannan hararen me sunanshi?"

A hassale Hajia tace "Ubanka, nace ubanka."

Mayar da fuskarshi alamun ko in kula yayi yace "To ba gaki ga shi ba." Ya fad'a da nuna mata lieutenant da yake mamakin yanda Hajia ke biyewa lamarin Ammar, nuna shi tayi da yatsa tace "Kai bari kaji magana ta k'arshe, wallahi tallahi in ka sake zuwa gabana da wannan gaisuwar rashin mutumcin taka sai na ci ubanka nan gidan, Ammar ni zaka d'auka mahaukaciya? To wallahi ka kiyaye ni, idan ma k'wank'wanmai ne a kanka ka sani nawa sun dame naka sun shanye, kuma aure ne babu fashi ko zaku mutu sai an d'aura shi."

Gyara tsayuwa yayi da kyau yace "To banda abinki Hajia na nuna miki bana son auren ne? Ba dai aure ne ba? To a d'aura, shawara kawai zan baki ki gogar da jikarki dubarun zama da ni, dan inba haka ba wallahi zata sake dawowa gabanki ta tare, aure kam ai ni shirye nake da a d'aura shi ko yau ne, lafiya ta k'alau wallahi ina da ingancin da zan iya tafiyar da mace hud'u ma a dare d'aya, ci da sha da sutura bata da matsalarsu saboda duk iyayenta masu kud'i ne, wannan hakk'in ne kawai ba zanyi wasa dashi ba wajen saukewa."

Tsayawa yayi kamar an taka masa birki ya d'an juya ya kalli su Amar dake zaune suna kallon ikon Allah, d'orawa yayi da "Hajia kin manta da wani abu, tun ranar da aka haifeni k'wank'wanmanki suka dawo kaina."

Ciro gilashin shi yayi gaban aljihun rigarshi ya manna a idonshi ya juya, lieutenant ne ya mik'e ya fizgo rigarshi, hannu ya d'aga da niyyar marinshi sai Hajia ta dakatar da shi ta hanyar fad'in "Barshi."

Kallon Hajia yayi ya saki rigar Ammar shi kuma saida ya gyara rigar ya wuce yana fad'in "Babu abinda dukanku zaiyi min da baiyi min shi ba a baya."

Hajia kuma kallon Sa'ada tayi wacce ita fa take ganin duk rashin mutumcin da Ammar keyi ita ke d'aure mishi gindi, k'wafa tayi ta harareta ta wuce d'akin ta da tunanin koyawa uwar tashi hankali sai taga ta tsiyarshi ai.

Alhaji na d'an tattaki a gaba d'aya gidan harya isa bayan gidan, tsayawa yayi ganin Zeituna wacce abun duniya ya isheta tana kuka, girgiza kai yayi dan yasan matsalar ba zata wuce Hajiar shi ce ta mata wulak'ancin data saba, takawa ya fara yi da niyyar zuwa ya bata hak'uri, sai kuma ga Iya ta fito daga d'aya hanyar dake sadaka da bayan gidan da mamakin ganin Zeituna tana fad'in "Subhanallahi! Zeituna dama nan kika zo kika zauna? Ina can ina nemanki ki ka ma min d'auke kujerun wurin nan mu share wurin, amma kuma..."

Shiru tayi ganin Zeituna na kuka, da sauri ta k'araso Alhaji kuma ya tsaya, kusanta ta zauna ta dafata tace "Zeituna lafiya? Me akai miki kike kuka?"

D'agowa Zeituna tayi ta kalleta cikin goge hawaye tace "Iya, kamar mahaifiya na d'auke ki, bayan iyaye na babu wanda ke nuna min kulawa kamar ke, Iya wani abu yana damuwa na sosai a zuciyata, na b'oye nayi addua'r Allah ya cire min amma har yanzu babu sauk'i, yanzu gashi wata masifar na neman kunno min kai, Iya zan fad'a miki matsala ta watak'ila na samu sauk'in abinda ke damuna, amma Iya dan Allah ya zama sirri tsakani na dake, kuma bana so kiga wautata ko shirme na da haukana, shawara kawai nake so ki bani Iya."

Ajiyar zuciya Iya ta sauke cike da dattako ta dafa kafad'ar ta tace "Nima kamar 'ya na d'auke ki Zeituna, ki fad'a min matsalarki insha Allah zamu samu mafita, kuma zan fahimce ki da yardar Allah, sannan babu wanda zaiji maganar nan."

Gyara zama Zeituna tayi ta fuskanci Iya da kyau ta kalleta da idon basira tace "...


_Duk wanda yasan zaiyi comment zai iya kasancewa grp d'ina ta hanyar neman wannan lambar *88-35-50-01*, ko kuma wannan *+213-65-81-91-316*, ko kuma wannan *99-32-99-10*, kuji da kyau wanda yasan zaiyi comment kawai._πŸ‘
16/06/2020 Γ  13:21 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*BADAK'ALA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ _*AHALI NA*_πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦

πŸ‡³πŸ‡ͺ *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_17_


Tunda Junaid ya samu labarin gobe za'a je neman auren Maryama hankalinshi ya tashi , sam bai d'auka abin zai zo da wuri haka ba, duk da shi ba matse yake da yayi aure ba, amma tunda wacce zata aurar dashi d'in ta amince dole ya gaggauta, kiran Iklima yayi yace ta dubi Allah ta dubi annabi ta had'a shi da Maryama yana so suyi magana mai mahimmanci, magiyar da yayi mata tasa tace ba damuwa ya zo gida suna nan, saida ya d'auki wanka cikin k'ananan kaya yayi kyau sosai sannan ya fito, har zai shiga motar shi saiga Jibril ya shigo, takowa yayi wajenshi yana fad'in "Yawwa d'an uwa, gwara da Allah ya kawo ka, wani taimako zaka min dan Allah."

Cikin sakin fuska Jibril yace "To wane irin taimako kuma malam?"

Tsaye yayi ya bashi hannu suka gaisa yace "Yanzu haka wajen Maryma na nufa, Iklima ta min alk'awarin ganinta idan naje, sai dai Maryama tana da taurin kai sosai, ina so ne muje ka rakani dan Allah wala'allah ko in ta ganka zata saurare ni, dan ya kamata ace yau ta koma gida saboda gobe su Abba zasu je garinsu nema min aurenta."

Ido Jibril ya fiddo yace "Toh, da wuri haka? Amma ni..."

Katse shi yayi da cewa "Amma kai me? Dan Allah d'an uwa karka ce a'a, ka taimaka min muje, in kuma ba zaka je ba saina je na d'auko Ammar duk inda yake."

K'ara zaro ido yayi yace "Ammar fa kace? Kai yanzu zaka yarda kaje wurin matar da kake son aura da Ammar? Lallai."

Dariya Junaid yayi yace "To miye a ciki? Shi ba mutum bane?"

"Mutum ne, amma kasan danya d'udd'ura mata ashar k'aramin aikishi ne ko."

Kafin Junaid yace wani abu Jibril yace "Jirani kawai na zo mu tafi, amma sai nayi wanka nima."

Cikin gidan ya nufa Junaid na fad'in "Sai ka ce wanda zaije neman kasuwa, ko ka manta kai kana da matarka?"

Bai wani jima sosai ba ya shirya ya fito ya shiga b'angaren iyayen ya gaishe su sannan ya fito, ya fito kenan a farfajiyar suka had'e da Jamila zata shiga falon, k'asa tayi da kanta tace "Ina wuni."

Cikin dakakkiyar murya ya amsa da "Lafiya lau, me kike a waje?"

Sororo ta kalleshi a ranta tace "Tofa! Wai kowa daya samu dama saiya dama tsiyarshi."

Saida ta kalli k'wayar idonshi tace "Ba daga waje nake ba, daga bayan gida nake."

Baice komai ba yasa kai ya wuce saida ta juyo ta kalleshi, yana samun Junaid suka fita daga gidan suka d'auki hanya sai gidansu Maryama, suna zuwa Iklima ya kira yace gashi waje, sosai Iklima tasha daga da Maryama kafin ta fito daga d'akin suna fad'a, a k'ofar gidan ta samu Huda tare da yara suna wasa, hannunta ta kama da tunanin idan sunje ya ga Huda ba zai mata wannan maganganun nashi ba da ba zasu anfaneta ba, daga cikin kwana inda suka paka mota ta shigo, tana zuwa taja ta tsaya ta jingina a motar a b'angaren da take tunanin babu kowa dan bai tab'a zuwa mata da kowa ba, ta k'ofar da yake tuk'i ya fito ya zagayo wurinta yana doka murmushi da fad'in "Gimbiya sarautar mata, Maryama kina lokaci fa, gani na ma sai kin so."

Cike da jan aji tace "Hakan yafi ko? Asha wuya kafin a ganka."

Murmushi yayi ya dafa kan Huda yana kallonta yace "Huda ya kike? Ya karatu kuma?"

Da murmushi yarinyar ta amsa da "Lafiya lau, ina wuni."

"Lafiya lau Huda, ke ba kya baccin rana kenan?" Ya fad'a yana kallon Maryama, shiru Huda tayi dan kallon da Maryama ta mata bata fahimci me yake nufi ba, kallon Maryama yayi yace "Mari magana na zo muyi dake mai mahimmanci, amma kafin nan zan so ku fara gaisawa da d'an uwa na Jibril."

K'ofar daya nuna mata yasa tayi saurin tasowa daga jinginar da tayi ta juyo tana kallon k'ofar, bud'e k'ofar Junaid yayi yace "Malam saika fito ko."

Zuro k'afa yayi ya fito sannan ya fito da d'aya k'afar yana murmushi da kallon Junaid yace "Ai na d'auka ka manta da ni zakin soyayya."

Kai tsaye kuma ya kalli Huda dake kallonshi ita ma tana murmushi, murmushi ya mata yace "Sannu bebbbbbbbbb."

Cak ya rasa maganarshi saboda kallonshi da ya kai kan fuskar da duk da akwai canji amma ba zai tab'a mantawa da ita ba har abada, dakan uku uku k'irjin shi ya shiga yi a lokaci d'aya kuma ya ji komai na jikinshi ya tsaya daga gudanar ruwa da jini har zuwa numfashinshi ma neman gagararshi yake so yayi, ba zaka ce yana da rai ba inba dan zufar dake tsatsafowa daga kowace k'ofa ta jikinshi ba.

Irin dai yanayin d'aya ne da Maryama ita ma ta shiga, k'uri ta mishi da ido tana kallo ba ko k'yabtawa, zufa da hawaye kam har tsere suke wajen fito mata, mutumin da kullum saita zage shi kafin bacci ya d'auke ta? Mutumin data rabu da iyayenta a dalilinshi? Mutumin da mahaifinta ya rasu ba akan idonta ba a sanadiyarshi? Mutumin da yake da babban kaso na duk zunubin da take aikatawa? Uban 'yarta da kullum take son gani? Wai yau shine a gabanta? Wannan wace irin rana ce? *Fara ko bak'a a gurinta*? Tasan dai a wurin Huda fara ce kam, wannan yanayin da Junaid ya gani a tare da su yasa shi dafa Jibril yace "Ya dai malam? Ko ka santa ne?"

Sakaka ya kalli Junaid ya rasa me ma zai fad'a masa, wannan wane irin tashin hankali ne? Maryama ce tayi k'arfin halin kallon Junaid tana shafe zufa tare da hawayen dan kar ya gani tace "Kamar ya ko ya sanni?"

Murmushi Junaid yayi yace "A'a ranki shi dad'e ayi hak'uri, ni ba wani abu nake nufi ba, kawai dai naga yayi wani iri ne." Ya k'arashe yana kallon Jibril dake satar kallon Maryama, yana ganin sun kalleshi yayi saurin kallon Huda yana cewa "D'an uwa wannan ce matar ta mu kenan?"

Wani kallon mamaki Junaid ya masa dan yanda muryarsa ta fita zaka iya fahimta tashin hankalin dake cikin sautin, ganin Maryama da Junaid duk kallonshi suke kallon daya kasa fahimta gashi duk ya tsargu, dan haka ya sake kallon Huda ya mata murmushi ya zura mata hannu alamar ta taho yana fad'in "Beby ya sunanki?"

Zuro mishi hannun tayi tana fad'in "Nurul Huda."

Kusa da shi ya tsayar da ita yana kallon kyakyawar fuskarta mai kama data uwarta, gabanshi har yanzu bai daina fad'uwa, ga wani sabon tashin hankali daya ziyarce shi yanzun, *Nurul Huda*, idan fa ta kasance 'yata ce? Wannan tunanin ne ya sashi jin kamar zai k'urma ihu, jin zuciyarshi na barazanar tarwatsewa yasa shi kallon Junaid yace "D'an uwa ban makullin motarka zanje nan na dawo, kafin lokacin ka ida kai ma."

Junaid ne yace "Amma ai ba haka mukayi da kai ba, meyasa zaka tafi ka barni nan?"

Abubuwan da yake ji a kanshi yasa yaji ba ma zai iya mishi magana ba, rufe k'ofar daya fito yayi ya zagaya b'angaren matuk'i, ganin haka ba zai gyarata ba yasa Maryama cikin shak'iyanci tace "Amma d'an uwa ko gaisawa bamuyi ba sai tafiya?"

Tsayawa yayi ya kalleta, wannan idon nata har yanzu dai basu sauyawa ba cewar Jibril, kai tsaye ya mayar da kallonshi ga Huda yace "Ba damuwa ai ba jimawa zanyi ba, wani abu na tuna da shi yanzun nan."

Murmushi ya ma Huda yace "Nurul Huda ko? Zan dawo yanzu sai muyi hira dake."

Cike da gatsali Maryama tace "Huda, zanyi magana da tonton d'in ki mijin da zan aura, ki tafi tare da waccen *Abban nanki* kafin mu gama kinji ko."

Huda da har cikin zuciyarta taji dad'i da yau har mahaifiyarta ta iya nuna mata wani namiji ta kuma kirashi da abbanta, da farin ciki ta zagaya kusan Jibril daya kafe yarinyar da ido, *Abbanta*, ta tabbata dai kenan? Na shiga uku ni Jibril, yanzu wannan 'yata ce? To ya zanyi da ita? Haka kawai saina nunata a gida gida a matsayin 'yar wacce nayi wa fyad'e ko me? Junaid ma mamaki Maryama a bashi sosai jin yau tana alak'anta Huda da d'an uwanshi, to me hakan ke nufi? Gamon jini ne ko me? Da k'yar Jibril yayi murmushi ya shiga motar ya zauna, zuro hannayenshi yayi ya d'auki Huda ya ajeta mazaunin mai zaman banza sannan ya rufe, suna kallonsu har sukayi nisa kafin Junaid ya kalleta yace "Abun mamaki."

Kallonshi tayi da fara'a tace "Me fa?"

Ba tare daya daina kallonta ba yace "Wace irin sa'a Jibril ya zo da ita haka da har kika yarje masa ya tafi da Huda haka? Wace irin sa'a ce haka ke tattare da shi da har kika iya kiranshi da Abban Huda kuma a gabanta? Maryama ko dai da wani abu ne?"

Jin yana neman harbo jirginsu ita kuma ba haka take so ba yasa tace "Ba sa'ar shi bace, taka ce, domin nayi niyyar saurarenka, sannan na shirya fad'a maka abinda ke raina a game da kai, ko da baka zo ba yau ni zan neme ka, ina so ne na fad'a maka na amince zan aure ka, shiyasa ma na so sai Huda tayi nisa da ni sannan na fad'a."

Tunda ta fara magana yake kallonta cike da jin dad'in abinda take fad'a, da farin ciki yace "Mari, kina nufin kin amince zaki aure ni?"

Gyad'a mishi kyai tayi alamar eh, tafukan hannayenshi yasa ya rufe fuska da su, saida yayi godiya ga Allah kafin ya bud'e ya kalleta yace "Nima maganar dake tafe dani mai girma ce, domin kuwa jiya warhaka muna cikin filin gidanku tare da kakarki muna cin abinci muna hira da ita."

Waro ido tayi tace "Kakata? A ina kuka ganta? Gidanmu kuma?"

Murmushi ya mata kafin ya kwashe komai ya fad'a mata tun daga labarin da Iklima ta bashi har zuwansu garinsu da kuma abinda ya faru gidansu, kuka ta dinga yi tana ji a ranta lallai son ta yake sosai, sai dai kuma ita har k'asan zuciyarta babu wani son aurenshi a ranta, son da take masa ma ba wani so bane na azo a gani, yanzun haka ta amince ni zata aure shi saboda uban yarta data gani, ko ba komai zata gasa masa aya a hannu, saita rama zalincin daya mata, saita d'and'ana mishi irin *uk'ubar* daya sata ciki shima, abun mamaki saiga Junaid sunyi hira ta fahimtar juna da Maryama, kuma duk abinda yace saita amince ta nuna ta yarda, harda cewa yau zai had'ata da dreban da zai mayar dasu gida ita da Huda, gobe kuma za aje nema mishi aurenta, bata mishi musu ba sai cewa da tayi bari taje tayi sauri su had'a kayansu.

Tunda Jibril ya d'auki hanya ya rasa meke masa dad'i, shi fa daya shigo motar ya so ya samu damar da zaiyi k'wararan ihu ne da zaisa yaji sakayau , amma kuma an had'a shi da Huda, tsayawa kawai yayi bakin titi yana kallonta tana ta waige waige a cikin motar da tab'a abubuwa alamar dai kamar shigarta ta farko kenan, a zuciyarshi yake ayyana data hanyar data dace aka sameki da wannan motar zata iya zama taki wacce dreba ma na musamman gareki da zai dinga tuk'a ki, ganin kallon da yake mata yasa ta zauna tsaf ta daina tab'a komai tsoro ya bayyana tare da ita, fuskarshi ba yabo ba fallasa yace "Kina karatu?"

A hankali ta kalleshi tace "Eh Abba ina yi."

Wani kallon ban gane *Abba* ba? Ya mata kafin yace "Maryama mamanki ce?"

"Eh Abba." Ta sake fad'a d'orawa yayi da "Ina Abbanki yake? Mamanki ta tab'a nuna miki shi?"

Cikin sanyi jiki Huda ta girgiza kai tace "A'a, nima ban sani ba, amma dai yaran unguwarmu suna ce min shegiya ce ni 'yar karuwa, kuma Mamana kullum sai tayi fad'a da mutanen gidanmu idan suka ce min shegiya ce ni ko ragon suna ba'a yanka min ba, kuma idan na tambayi Mamana waye Abbana saita dinga hushi tana min tsawa da fad'a tace na tashi na bata wuri."

Rintse ido Jibril yayi saboda jin hawaye sun cika idonshi har suna neman zubo mishi, *ragon suna*? Shine abinda yafi tsaya mishi, 'yar dana haifa a cikina ko bata hanyar aure bane ace ba'a yanka mata rago ba, ya ilahi, shine abinda ya fad'a k'asa k'asa, d'an bud'a idonshi yayi ya juya inda Huda take, sai gani yayi tana ta goge hawaye da bayan hannayenta wasu na biyar wasu kam, gyara zamanshi yayi ya kamo hannunta ta mik'e tsaye ya d'auke ta ya zaunar da ita kan cinyoyinshi ya fara share mata hawayen yana fad'in "Yi hak'uri kinji 'yata, ba dai yana suna tsokanarki ba? To daga yau ba zasu sake ba saboda Abbanki ya dawo, kuma maganar rago ma ki fad'a min me kike so a yanka miki, kama daga rak'umi, saniya, da kuma raguna, ke da ana yanka zaki da su gwiwa ma ni zan yanka miki."

Kallonshi tayi tana dariyar jin dad'i tace "Ka zama *Abbana* daga yau?"

Gyad'a mata kai yayi yana murmushi, d'orawa tayi da "Kuma duk kana da kud'in siyan wannan abubuwan?"

Cike da tabbatarwa yace mata "Sosai ma, kuma ko da bana da saboda kiyi farin ciki ki wuce gori a idon jama'a ai ko bashi ne zan ci dan na siya miki."

Cike da yarinta tace "Abba saniya nake so babba, kuma nafi son kalar ja tafi kyau mai manyan k'aho."

Cikin dariya yace "Angama gimbiyar Abbanta."

Wani dad'i ne ya kashe Huda daya sata fad'awa k'irjin shi ta kwanta luf tana k'ara goge hawaye, wata ajiyar zuciya ya sauke mai k'arfi, a hankali ya lumshe idonshi ya fata shafa kanta wanda yasha sabon kitso ya fito tsaf da shi sai walk'iyar mai yake, hakan daya faru kuma saiya zama kamar antsaga zuciyarshi an dasa mishi soyayyar yarinyar, take yaji k'aunarta na gauraya da jinin jikinshi, ba tare daya bud'a ido ba ya sumbaci kanta, cikin tausashiyar murya taji yace "Huda ki yafe min, nayi gaggawa a waccen ranar, duk laifi na na komai daya faru, mahaifiyarki ba da laifi ko d'aya."

Ita dai da yau take jinta a k'irjin Abbanta yana shafata bacci ne ma ke sonyi gaba da ita, hakan ne yasa bata damu da me ya fad'a ba kawai ta sake yin shiru, ci gaba yayi da shafar kanta har yaji shirunta yayi yawa, yana lek'a fuskarta yaga ashe bacci harya d'auke ta, hak'ik'a mahaifiyarta ce tayi, daga kallon fuskarta kuma abubuwa dayawa ne suka ziyarci tunaninshi, ya zakayi da *Junaid, iyayenka ma, da ita kanta Maryama, sannan iyayenta ma da suka ganka*? Amma kallon fuskar Huda da yake sai yaji ya bashi k'arfin gwiwar tunkarar kowane irin bala'i da masifa, 'yace dai gata ta zo zo duniya, tasha wahala kafin bayyanarshi ya kuma dan da ita, amma daga yanzu daya sani har zuwa lokacin da kowa zai fahimce shi ba zai bari tayi kuka ba, shafa kanta yayi ya sake sumbatarta yace "Wannan *alk'awari* na ne gareki."

Ba tare daya d'auke ta daga kan cinyarshi ba ya tayar da motar a haka ya tuk'a suka isa wata alimentation, tsayawa yayi ba tare daya fito ba kawai ya sauke gilashin motar yace babbar leda yake so a had'a mishi ta kayan da suka san zasu birge yaro, saida ya siyo suka juyo dawowa inda suka bar Junaid, shi kad'ai ya samu zaune bakin dakali Maryama ta shiga dan kimtsawa, Junaid ne ya kirata a waya ta sake fitowa, fitowa Jibril yayi da Huda a hannu ya matsa daf da Maryama zai bata ita, murya k'asa k'asa tace "Baccin farin ciki ne take na ganin mahaifinta? Ko kuma baccin wahala ne?"

Da sauri ya sauke idonshi cikin nata idon da alamar tambayar me take nufi? A lokacin da zata amsheta ne tace "To ai naga kai idan har aka shiga mota d'aya da kai sai kayi b'arin ingantacciyar madarar da tana shiga mahaifa dole a tashi mutum da ita."

Kallon wannan wace irin magana ce haka? Ya mata kafin shima yace "Huda, 'Yata ce?"

Murmushi ta masa tace " 'Yar ka ce mana, a waccen ranar aka sameta, dalilin haka kuma na shiga karuwanci."

K'asa ya kalla tare da saisaita murya yace "Ya fad'a min kuna shirin tafiya, amma dan Allah kafin ku tafi ki jira naje na dawo."

Cikin makirci ta amsa mishi da "Karka damu zan jiraka, domin kuwa akwai matsalolin daya kamata mu warwaresu."

Gabanshi ne ya fad'i ita kuma ta kalli Junaid dake waya da wanda yake so ya had'a shi da dreba tace "Zan shiga ciki na k'arasa shiryawa."

Da kai kawai ya mata alama ta wuce ciki suma suka shiga mota suka d'auki hanya, gida Jibril yace ya aje shi, yana sauke shi kam d'akin shi ya shiga ya fito ya shiga motarshi shima, bai zame ko ina ba sai *Soura* mayanka.

➑️➑️➑️➑️➑️➑️➑️


Yana zuwa cikin takon rashin mutumci ya shiga hotel d'in, zuwanshi yayi daidai da Hamna na sakawa wani saurayi a cikin abokan ango lambarta a wayarshi, k'are mata kallo yayi, har zuciyarshi fa shi ya zo ne da niyyar ci mata uwar raina musu hankalin da tayi a gida, amma yana ganinta cikin ankon shagalin duka yan matan riga da siket ne jikinsu na less, amma yanda suka fitowa da da Hamna komai na jikinta saida yaji zuciyarshi ta buga, abinka ga mai yar k'iba k'irjin nan an fito dashi ya tsaya tsam-tsam, ga faffad'an k'ugun nan ya fito da kyau, d'aurin d'an kwalin dake kanta iya rabin kan kawai ya tsaya, inda manyan kitsonta na gashin doki (atach) ya kwanta a bayanta har yana kusan kaiwa a k'ugun, wani tafarfasa yaji zuciyarshi nayi, gani yake kaf mazan wurin surarta kawai suke kallo suna yabawa, jinjina kai yayi irin yana nufin zaki ci ubankin nan kafin yace " Wato ni zata rainawa wayo?"

Daidai Hamna ta mik'awa saurayin wayarshi cike da jan aji zai karb'a idonta ya sauka kan boss, fad'uwar da gabanta yayi da d'aukar rawar da jikinta shima yayi yasa ta mantawa harta saki wayar bada gangan ba, saida taji fad'uwar wayar kuma tayi sauri ta kalli wayar ta rufe baki da hannu, zata sunkuya ta d'auka kuma Ammar na daf da kawowa, d'an girgiza kanta tayi a ranta tace "Wallahi wannan kallon rashin mutumci ne yake min, ba zan zauna ya kunyata ni ba cikin mutane."

Ai saita mik'e ta kalli saurayin tace "Kayi hak'uri dan Allah."

Fittt, ta kutsa cikin taron tana neman mafaka duk da saurayin na fad'in "Ba komai."

Tsaye yayi gaban saurayin daya sunkuya ya d'auki wayarshi, kasancewar sun san juna yasa ya figzi wayar ta shi, ganin lambarta rau akan Γ©cran d'in daya fara tsagewa yasa shi goge lambar ya

Please Login or Register in order to submit comment