Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi ta juyo ta kalleshi tace "Ya dai kake biyata malam?"

Wani kallo ya mata yace "Ke kike bina ko ni ke binki?"

Girgiza kai kawai tayi ta wuce, ko da suka shiga suka same su kwance kan gado d'aya Huda har ta fara bacci, wucewa yayi ya kwanta kan gadon Hamna, kallonshi tayi da mamaki cikin rad'a tace "Meye haka malam? Baka ga yara ne?"

Rintse ido yayi yace "Ban gansu ba."

Juyawa tayi ta kallesu sai taga Nazifa ta mik'e zata fita, da sauri tace "Ke dawo kwanta wajenki, ina zakije ke da nan ne wajen baccinki, bak'on daya mana haure shine zai fita."

Ko da ta fad'a ta shige ban d'aki da kayan baccinta a hannu, da murmushi ya bita ya kalli Nazifada ta dawo ko ta koma ta kwanta, bata jima ba ta fito ta aje kayan data canza kan kujera, kan gadon da suke kwance taje ta shige tsakiyarsu tana fad'in "Ku matsa min nima."

Bud'a ido Huda tayi ta kalleta ta hangi gadonta, saida gabanta ya fad'i ganin tonton d'in ta kan gadon a dakinsu, juya baya tayi ta yanda take kallon k'ofar shigowa ta matsa mata, wajen k'afafunsu ta maido kanta ta d'ora matashi ta kwanta, ta lik'e ido taji muryarshi tsaye a kanta yace "Ku matsa min nima."

A tsorace suka tashi zaune tare ban da Hamna data san halin kayanta, kallonshi sukayi ya kuwa tsaya kusan kanta rik'e da pillow shi ma, Nazifa ce tayi saurin wuntsilawa ta sauka daga gadon ta nufi hanyar fita, da sauri Huda ta tashi ita ma ta bi bayanta suka fice Nazifa na fad'in "Yau mun shiga uku, to su kna d'akinsu wai?"

Cikin turo baki Huda tace "Muje d'akin Hajia kawai mu kwanta."

Ko da taga sun fita ta mik'e ita ma da niyyar bin bayansu, da k'arfi yayi tsalle ya fad'a kanta hakan ya tilasta mata fad'awa kan gadon da k'arfi, da k'arfi tace "Aouch."

Kafin ta bud'a ido taji yayi kwance kanta gaba d'ayanshi ya kuma sakar mata nauyinshi, yanda ya tausheta yasa ta kasa yin numfashi mai kyau, bud'a ido tayi ta kalleshi tace "D'aga ni."

Girgiza kai yayi yace "Zaki koma d'akinmu?"

Girgiza kai ita ma tayi tace "A'a, har sai na yarda babu komai tsakaninka da Amie."

Da k'arfi yace "Babu komai kankana, taya kike tsammanin zanyi iskanci a waje bayan ina da ke? Sannan na rasa da wanda zanyi iskancin ma sai k'awar ki? Na yarda ni mahaukaci ne kuma ba mutumin kirki ba, amma bana neman mata Hamna kuma bana shan ko da sigari bare k'waya."

K'afeshi tayi da ido tana kallo, kallon tausayi da jin k'ai da rahama, wa yace shi mahaukaci ne? Dan tana fad'a masa haka ai kawai tana fad'a ne, me yasa zai yarda shi mahaukaci ne kuma ba mutumin kirki ba? Bata ji dad'in abinda ya fad'a ba, a hankali cikin fitar da wahalallen numfashi tace "Wa yace kai ba mutumin kirki bane?"

Saida ya k'ank'ance idonshi yace "Ke mana, haka kike kallona ai."

A hankali ta d'aga hannunta ta shiga shafa fuskarshi a hankali tana kallonshi, cikin taushin murya sosai tace "Kai mutumin kirki ne Abban yarana, duk gidan nan muna alfahari da kai, dalilinka ne abubuwa dayawa suka canza, ka daina wa kanka wannan kallon, kaji? Ka daina bana so."

Yanda ta k'arashe maganar da matuk'ar shagwab'a da kashe murya yasa shi jin zuciyarshi ta k'ara narkewa, murmushi ya saki yace "Amma duk da haka ai baku sona."

Idonshi ta kalla tace "Waya fad'a maka, muna sonka yah Ammar, muna k'aunarka dukanmu."

D'aya hannun tasa ta tallabo fuskarshi suna kallon juna sosai tace "Ammar *ina sonka*, d'azu nayi niyyar fad'a maka haka, amma wannan Amien..."

Ture shi tayi daga jikinta ta tashi zaune tana kallonshi, shi ma kallonta yake yana jin kamar ya fasa ihu yau Hamna ce tace tana son shi? Yana kallonta ta tashi tsaye tana fad'in "Saina fara cin uwar yarinyar nan kafin hankali na zai kwanta, sai naji abinda ya had'ata da mijina."

Tasowa yayi yana k'arewa fuskarta kallo yana fad'in "Hamna ni kike kira mijinki? Wuuuuu duniya dad'i, Hamna yau nine kike so? Kishi na kike?"

Da sauri ya d'auki wayarta dake kan kujera ya bud'e ya shiga danne danne, tana kallonshi ita dai sai ji tayi ya saka wak'ar *Umar m Shareed* mai taken *soyayya akwai dad'i*, aje wayar yayi sai kuwa ya shiga kwasar rawa ba kunya ba tsoron Allah, da fari da mamaki ta fara kallon yanda yake rawar, amma sai abun ya fara bata dariya, zaune tayi bakin gadon tana kallonshi, tsakaninshi da Allah yake rawar kamar ya ga *Adam A. zango* a gari, bata ankara ba taji ya jawota yana juyata a dole ita ma tayi rawar.

Tun tana tirjewa tana so ya rabu da ita har wata wak'ar ta shigo wacce ta iya taka rawarta fiye da zaton mai karatu, (in baku manta ba tun a farkon littafin ita d'in gwanar rawa ce da iya shokiπŸ˜‚), biye masa tayi suka shiga rawa har da dariya kamar mahaukata.

Ummy da tasan sai sun tsula tsiya tunda taga ya shiga d'akin, kuma a gaban idonta su Nazifa suka fito, ta jima tana k'wank'wasa k'ofar amma basu ji ba, kuma gashi tana jin dariyarsu da sautin kid'a, dan haka kawai ta tura k'ofar ta shiga idonta rufe dan kaucewa mummunan gani, a hankali ta bud'a ido ta hange su sun cake sai kwasar rawa, rik'e baki tayi tace "Inna lilliahi wa'inna ilaihi raju'un."

Da sauri suka tsaya suna kallonta, ko da ya ga Ummy ce ya matso yana fad'in "Ummy albishirinki?"

Ta d'auka zai ce Hamna ce ke da ciki, sai kawai ta kalleta tace "Hamna wace lalacewar ce kuma wannan? Rawa a daren nan?"

Laushi tayi kamar ba ita ba tana k'yabta ido, jinjina kai Ummy tayi tace "To maza d'auki kayanku ku koma b'angarenku kafin ku tara mana aljanu, tunda abun ya zama iskanci, nan kike ta kumbura ke hushi kike ashe d'aurin duniya ne."

Langab'e kai tayi tace "Allah Ummy da gaske ne, yanzu ma da zan ga Amie saina tattaka ta."

Kallonta Ammar yayi yace "Wai ke ba zaki fita harkar yarinyar nan bane?"

Zaburo mishi tayi tace "Eh d'in ba zan fita ba, sai naji dalilin da yasa ta kula ka."

Kallon fahimta ya mata yace "Ki tabbatar zaki b'arar min da ita?"

Cike da tabbaci tace "Allah kuwa zan iya."

Kallonta yayi da kyau yace "Gobe da safe ki shirya idan zan fita na kaiki gidansu, zan so ganin yanda zaki d'auketa ki nunawa sama ta bakwai kafin ki dirota k'asa, dan ni abun farin cikina ne ace matata na fad'a akai na, kinji ko?"

Cikin murna tace "Da gaske?"

Ba alamar wasa yace "Ina fad'an abinda ba zan iya bane?"

Da farin ciki tace "A'a."


"Dan haka ki shirya zan kaiki." Ko da ya fad'a ya juya zai fita, ita har ga Allah ta ma manta wai yaji tayi, kallon Ummy tayi tace "Saida safe Ummy."

Rik'o hannunta tayi ta dawo da ita baya tana fad'in "Zo nan."

Kallon juna suka shiga yi Ummy tace "Hamna ina yace zai kaini? Gidansu Amie fa naji yace."

A hankali tace "Eh Ummy."

Da mamaki Ummy tace "Anya kuwa Hamna kina so mu zauna lafiya dake? Ke fad'a min me kike so ku zama yanzu?"

Shagwab'e fuska tayi tace "To naji Ummy ba zamu je ba."

Tab'e baki tayi tace "To yanzu binshi ne zakiyi?"

Da sauri ta juya ta nufi kan gadon tana fad'in "A'a Ummy, bacci zanyi."

Nufa kanta Ummy tayi tana neman abun bugu tana fad'in "Hamna zan ci ubanki a gidan nan, tashi wuce ki bi mijinki, na gaji da masufarku wallahi karku kashe ni da raina."

Da gudu ta arta ta fito daga d'akin, ko sauka bai gama ba daga matakala tayi tsalle da niyyar haye bayanshi, shi kuma da baisan da zuwanta ji kawai yayi yayi sungululu ya tafi ta kai suuuu.πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚


*Tsakaninku ne*

Bashi daya rigata ba har ita san da kai tayi duk suka wuntsile a wurin, saida suka gama durkuwa k'asa suka fara kallon kansu dan ganin salon fad'uwar, AmmarπŸ˜‚ da yaji kamar wuyanshi ya karye kallonta yayi, tana zaune kan matakalar ta rik'e k'afa da hannu tana kukan shagwab'a, wani huci ya shiga saukewa da tunanin me ma zai mata ne shi kam, shin ya d'auke ya jujjuyata sannan ya dasata a k'asa, ko kuma ya sake hawan benen da ita sai ya sakota ta fad'o, ko kuma...

*Uwar Lalla ranar da aka kawoni gidana haka na kusa tahowa ta kai na karya wuyaπŸ˜‚ amma tuni angona ya cab'oni aradu ta baya, kai bene baiyi ba.*

Ummy dake tsinkayensu ta sama tana jiran taga me zai faru, tashi yayi a hassale yana fad'in "Ke dan ubanki ni kika wuntsilo? Hamna ni kikawa wannan wurgowar? Ashe k'arfin tsiya ne dake kamar bagwariya, ai kuwa yau zaki c..."

Da sauri Hamna data kasa tashi saboda k'afarta ta bud'e hannayenta ta jawoshi da k'arfi har yana neman fad'awa kanta, bai gusar da fuskarshi daga kanta ba yana mata kallon mamaki yaga ta k'amk'ame shi tana fad'in "K'afata! Wayyo Allah k'afata, yah Ammar ka taimaka min dan Allah."

Kallon fuskarta yayi kawai yaji a ranshi ta gama dashi, kallon k'afar yayi wacce ke rufe da dogon wando, sake kallonta yayi yace "Ciwo take miki?"

"Eh." Ta fad'a tana rushewa da kukan shak'iyanci, d'aga kai yayi ya kalli Ummy sannan ya kalleta yace "Bari Ummy ta taho saita kaiki d'akinki, ni dai ba zan d'auke ki ba."

Da sauri ta k'ara jawo rigarshi tace "A'a d'auke ni, d'aukeni muje b'angarenmu kafin Ummy ta taho, ita ta koro ni fa daga can."

Murmushi yayi yace "Allah?"

"Eh." Ta fad'a da sauri tana d'aga mishi hannu saiya d'auketa, gyara tsayuwarshi yayi ya d'auketa gaba d'ayanta ya k'arasa sauka da ita, ba tare daya juyo ba yace "Ummy saida safe, yar yajinki ta koma."

Rufe fuska tayi cikin k'irjinshi har suka fice, har saida suka b'acewa ganinta sannan ta girgiza kai ta shiga saukowa a hankali tana fad'in "Allah kaine Allah, Allah ka shirya min yaran nan shirin addinin musulinci, Allah ka kawar da idon mak'iya da bakin mutane akan su."


*Ameen Ummy.*


*Alhamdulillah*
04/11/2020 Γ  14:39 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*BADAK'ALA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ _*AHALI NA*_πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦

πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_75_


Ko da suka shiga ya sauketa kan gado, zaune yayi ya fuskanceta da kyau yace "Hamna, yanzu nan duk cutar nan da kika min shikenan kin cuci banza kenan?"

Saida tayi da gaske ta samu ta rik'e dariyarta tace "Rama to."

Zaro ido yayi yace "Ni! Ni d'in banza da zan rama, a'a na yafe."

Cikin bushewa da dariya tace "To bacci zanyi."

"Kwanta." Ya fad'a yana kallon idonta, zanin rufa taja ta rufa tana dariya k'asa k'asa, sai yanzu take hango sanda ta bankad'o shi yayo k'asan nan daram, sai kawai ta juyo tana k'ara barkewa da dariya, ganin tana dariyar ba tsayawa har da rik'e ciki yasa yace "In ban miki Allah ya isa ba ki ce ba sunana Ammar ba."

D'aga mishi hannu tayi alamar ta daina tare da rufe bakinta tana wata dariyar, shi dai har bacci ya d'aukeshi bai tanka mata ba tana dariya.

*Ko da* suka gama kari zai fita yace su tafi ya kaita, kallonshi tayi tace "Wai da gaske kake dama?"

Ba alamar wasa a tare dashi yace "Ina wasa dake ne?"

"A'a." Ta girgiza kai a hankali, d'orawa yayi da "Zaki tafi ko na tafiya ta?"

Cikin turo baki tace "Gaskiya ka tafi, Ummy tace zanga b'acin ranta."

Wani kallo ya mata na tsanake, shi fa akwai abinda yake nufi daya fad'i haka, in bata amince ba kuma akwai matsala, amma cikin ruwan sanyi zai bita sai kawai ya juya yana fita yace "Shikenan, saina dawo, amma kar kiyi mana abinci yau zamu fita waje." K'ala ba tace ba har ya fice.

*An shirya* dan fita kamar yanda yace, amma sanda ta fito cikin shirin riga da siket d'inta da mayafi saiya shiga zagayata, tsaye tayi tana binshi da kallon kafin ya tsaya gabanta yace "Yanzu Hamna dan zamu fita shine sai kin fad'a ma kowa cewa gaki nan kin fito."

Da mamaki tace "Kamar ya fa?"

Saida ya nuna kamar yana ganinshi yace "Shi wannan turaren da kika fesa fa?"

Yar ajiyar zuciya ta sauke tace "Ohh, yana da dad'i ko?"

Wata harara ya wurga mata yace "Dad'in banza dad'in wofi, ni ba dad'inshi nake tambaya ba."

Kamar wacce ta tuna da wani abu sai kuma tace "Au, sunanshi? Sunan shi *Oud zarkah*, ka gane."

Rik'e k'ugu yayi dan ya fahimci zata raina masa hankali ne yace "To je ki cire kayan nan ban son jin k'amshinshi jikinki."

A kasalance ta amsa da "Ba fa a kayana bane, a wuya da baya kunne kawai nasa."

Cike da raini yace "To je kiyi wanka."

A kasalance ta sake amsa shi da "Ko nayi ba zai fita ba, kamu ne dashi."

Da hannu ya mata alama yace "Can naga lalle iyakar kamu, je ki wanke min shi Hamna kafin ranki ya b'ace, ko da ruwan gidan nan da garin nan zasu k'are to zan d'ebo miki ruwan maliya dan ki wanke shi."

Galala ta kalleshi tace "To da wannan nayi zamana mana, fitar ta zama dole ne?"

Saida ya sake rik'e k'ugu gam yace "Qur'ani sai kin tafi."

Saida ta waina idonta alamar gajiya da zancen sannan ta juya ta koma ciki, canza kayan tayi ta sake wasu kafin ta fito suka fita.

Saida aka d'auki hanya yace ai fa an ma fasa cin abincin, kawai wasu almajirai zasu tsaya wani cin abinci a waje, ji tayi rainin hankalin ma ya wuce misali, k'ufula tayi ta had'e girar sama da k'asa ta rumgume hannaye, saida ya samu wurin da babu hayaniya ya caka birki ya tsaya, a hankali ya kamo hannunta yana kallon fuskarta yace "Baby, kalle ni nan."

Kallonshi tayi amma asali harara ce take masa, kashe murya yayi yace "In tambaye ki mana?"

Kafeshi tayi da ido alamar ina saurarenka, saida ya d'an muskuta zamanshi yace "Kina so na da gaske?"

Turo baki tayi tace "Me kuma ya kawo wannan maganar yanzu?"

"Ki bani amsa." Ya fad'a yana ci gaba da kallonta, juya kanta tayi tace "Eh."

Sakin hannunta yayi yana tayar da motar yace "Muje to na siya miki ice cream."

Kallonshi kawai tayi ita dai har suka fara tafiya, ta kusan salon d'inta suka bi wanda har ta kalli wajen ta ga a rufe alamar *Lina* har ta rufe, dama ba wata tsiya suke yi ba tunda ta bar zuwa sai jifa jifa, a hankali yake tuk'in zasu wuce ta wata majalisar samari, Hamna da idonta ke kallon hanya da sauri ta rik'o hannunshi da yake tuk'i tace "Lah! yah Ammar dubi mutumin nan da yasa aka daki yah Amar."

Saida ta gama fad'a sai kuma ta gane katob'arar da tayi, a hankali ta shiga sakin hannunshi tana jujjuya ido da matse bakinta, cak ya tsayar da motar yana kallonta yace "Yana ina?"

Ko kallonshi ba tayi tace "Wanene?"

Da k'arfi yace "Ban sani ba? Yana ina na ce?"

A tsorace ta kalleshi inda ta ga ranshi ya fara b'acewa zai iya cin ubanta ma, cikin i'ina tace "B..a komai fa, na d'auka shine."

Bayan wuyanta ya cakumo da k'arfi ya matso da fuskarta kusanshi cikin daka tsawa yace "Hamna karki b'ata min rai, ki nuna min shi ko na had'a duka wanda ke wurin na taka su da mota."

Yanda ya rik'e wuyan nata yasa ta cewa "Zan fad'a maka to, sake ni dan Allah."

Sakinta yayi inda ta sake kallon matasan, a hankali ta kalleshi tace "Waccen ne mai jan riga."

Kallonshi yayi da kyau, murmushi ya saki ya kalleta tare da jawo kanta ya sumbaci bakinta yace "Ni ma ina sonki."

Ture shi tayi tana fad'in "Ni bana son ka."

Dariya yayi yace "Baki isa ba yarinya, ko kina so ko baki so dole ki soni, inba haka ba duk zamu mutu tare."

Saida suka siyi ice cream d'in ya mayar da ita gida ya aje, sanda ta sauka kallonshi tayi tace "Kai ba zaka shigi bane?"

"Kije akwai inda zanje." Ya fad'a yana wucewa a hankali, da kallo ta bishi kafin ta shiga sam bata tunanin me zaiyi.

Inda suka bari ya koma ya tsaya, cikin sa'a yana zuwa kuma saurayin ya hau moto zai bar wurin shi da wani, bin bayansu ya shiga yi hankali kwance har ya aje wanda ya d'auko a wani shago yayi gaba, ya shiga layin gidansu kenan yayi gaggawar shiga gabanshi, tsaya yayi da sauri yana kallon motar, bud'ewa yayi ya fito da k'arfi cikin tako mai ban tsoro ya nufi kanshi, shi kam gabanshi ne ya shiga fad'uwa dan yasan akwai matsala, wanda yasa aka daka ne ya dawo d'aukar fansa, gashi shi kad'ai a wurin kuma ko ihu yayi ba za'a iya jinshi a gidansu ba, jiki na rawa ya shiga k'ok'arin sauka daga kan moton.

Bai bari ya gama sauka ba, bai bashi damar sauka ba ko da kare kanshi ne yayi, da iya k'arfin da yake da shi ya gabza mishi wani k'ulli a baki, rikicaaaa sukayi shi da moton duk suka fad'i b'angaren hagu, moton ne ya taushe k'afarshi hakan yasa shi kiciniyar jawo k'afar, k'afa yasa ya take moton yasa hannu ya jawo madubin moton da k'arfi, yana cire shi ya gaud'a mishi a fuska a take jini ya sake gabce mishi, shak'o wuyanshi yayi ya kalli idonshi yace "Wai kai ga sakarai, a madadin ka fuskance ni ka rama dukanka, sai ka zagaya ka turawa d'an uwana yara suka dake shi."

Sauda ya gaura masa mari yace "Shine har da sawa suka karya mishi hannu."

Hannu ya d'aga zai sake marinshi yayi saurin tara hannu yana fad'in "Yi hak'uri, yi hak'uri dan Allah, bansan d'an uwanka bane."

A hankali yace "To ka sani daga yau, ni dashi tare muka fito duniya, sannan ina jiranka ka sake aiko min yara yanzu."

Dungurar dashi yayi ya juya ya koma mota, saida ya bad'a mishi k'ura ya bar wurin hankali kwance, yanzu kad'ai yaji sakayau daya ramawa d'an uwanshi, shi fa bai son abinda zai tab'a mishi Amar, waccen lokacin ma yayi shiru ne dan baisan mutumin ba.

Shi ma saida aka d'aukeshi daga nan akayi asibiti, sai dai al'amarin yayi k'amari sosai, mahaifinshi ranshi ya b'ace sosai ya kuma ce ba zai yarda ba, sai sunyi k'arar shi tunda dai akwai mahukunta a gari, da yake shima d'an dangi ne kuma akwai masu abun hannu sai fa kowa ya goyi da bayan haka, dan haka suka jiran gari ya waye yaji sammaci.

*Washe gari* ya shirya ya fita cikin farin ciki, amma fitar da bai dawo gidan ba kenan, motar police ce ta zo har gidan nemansa, mai gadi ya gane wa ake nema da suka fad'a masa yan biyu, domin kuwa yanda sukayi rΓ©clamΓ©n abun ba da wasa bane, sun d'auka zafi sosai su ma, nan ya fad'a musu yana asibiti suka pantsama can, ganin motar ma da yanda take tafiya saiya kayar da gaban mai tsoro (iri na ba, ai bana son had'uwa dasu ko da croisement ne). A tak'aice dai kunsan halin kayanku ai, bai musu magana da ladabi ko girmamawa ba, su kuma hakan ma sab'a dokarsu ne, dan haka laifinshi ya k'ara girma suka ram da shiπŸ˜‚ (yau maza an shiga hannu aradu, uwar Lalla a shirya kai mishi abinci).

Ko a jikinshi ko nace a kwalar rigarshi, binsu yayi babu gardama ko musu ko nadama a tare dashi, sai dai abun ya wuce yanda yayi tunaninshi, dan kai tsaye babban gidan kaso suka wuce dashi, kuma ba'a b'ata lokaci tsayawa tambayarshi wani abu ba, jefashi kawai sukayi ciki suka rufe bayan sun raba shi da wayarshi.

Babu wanda hankalinsa bai tashin ba sanda labarin ya riski kowa, Hamna da Hajia ma kuka suka shiga yi, a tsaye lieutenant yaje dan jin abinda ke faruwa? Fad'a, ya daki wani har ya ji masa ciwo yana kwance, sannan ya zagi tenu (ma'aikanta masu kaki) shine abinda aka fad'a mishi, al'amarin bai mishi dad'i ba, ranshi ya b'ace ta yanda ya juya ya tafiyarshi ba tare da yace komai ba, tunaninshi shine akan me Ammar ba zai yarda ya girma ba? Da yaranka har shida amma kana abu kamar yau aka haifeka.

Gidan ma daya fad'a musu basu ji dad'i ba, amma su Hajia suka ce ya zasuyi daya wuce hak'uri su fito da shi, Hamna kuma da taji sai ta aza sabon kuka tana fad'in laifinta ne ai, da bata kula saurayin ba duk da haka bata faru ba, sannan da bata nuna mishi shi ba jiya da yanzu yana gida. Nan dai lieutenant da Labaran suka shiga k'ok'arin fito dashi tun kafin ma kowa yasan da al'amarin, amma abun ya wuce yanda suka tunaninshi, dan abu d'aya da aka fad'a musu shine sai an musu sulhu sun ce sun yafe, kafin nan saida suka d'auki nauyin maganin yaron.

*A gurguje*

*Abu* fa ya ci tura yaja daga, duk abinda aka ce suyi yi sukeyi amma shiru, saida aka kwana *shida* kad'ai aka zauna dan ayi sulhu, mahaifin yaron mai sunan *Ak'il* da yayanshi duk suna tare dashi, sai lieutenant da Labaran da kuma Ammar d'in. Nan aka ce ya bashi hak'uri sannan babu shi babu shiga harkarshi har abada, nan fa ya rantse ya maimaita cewa ba zai bashi hak'uri ba, in ma suna da abunyi suje suyi kar su b'ata lokacinsu, Labaran ya lallab'a ya bashi hak'uri a wuce wurin, durk'usawa wada ba gajiyawa bane, amma yace wannan wanda dai sai dai ya ida takeshi ya shige cikin k'asa.

Hakan yasa lieutenant ranshi b'acewa yace su barshi kawai, fita yayi ya bar Labaran yana ta tausarshi, amma abun haushi yaron nan da shegiyar kafiya yace ba fa zai bayar ba, babu yanda za ayi an dakar masa d'an uwa kuma ace ya bayar da hak'uri dan an raina shi, shi ma Labaran haka ya baro wurin rai babu dad'i, su kuma suka ce zasu nuna mishi taurin kai da iskanci, tuni kuga gane shi suka kafa mishi kahon zuk'a.

*Daga* lokacin nan kam abubuwa suka canza mishi, ya jigata ya kuma yarda daya fara wahala, amma dai bai yarda ya nuna uban kowa ya gane baπŸ˜‚ (wuya makarantar kare), abinci da aka kawo masa kullum na safe daban na rana daban na dare daban, amma suma ana kawo shi zasu juye a nasu kwanon su cinye, wanda ake girkawa anan wanda maza ne ke surfa masarar ayi tuwon suke bashi, sai randa sukayi niyya ne suke rage mishi su zuba a leda su jefa mishi, bai tab'a nuna musu komai ba yana kallonsu dai duk ya gane fuskokinsu zaiyi wanka ya canza kayan da aka kawo mishi, amma fa sauro da rashin lafiyayyar shinfid'a da kuma rashin kankana ma kad'ai sun addabe shi, suna tsangwamarsa a wurin da jefa mishi magana, wankin ban d'aki da shara duk babu abinda basa saka shi a wurin, amma duk sanda yake aikin cikin izza da jin kai yake yin shi, ko wayarshi basa bashi kamar yanda suke ba wasu dan suyi kira su maido, sun hana shi ganin kowa kai kace ya saci kud'in gwamnati ko kisan kai, shi kuma ya riga daya san laifinshi bai kai hukuncin da suke mishi ba, shiyasa ma ya zuba musu ido yana k'arewa duk wanda ya masa da kallo, jira yake su gama nasu kafin ya darza musu salon tashi didimar.


*Comment...*

*Alhamdulillah*
04/11/2020 Γ  14:40 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*BADAK'ALA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*



Please Login or Register in order to submit comment