Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ba, ko da taga haka ta mik'e ta shige gida da gudu da niyyar yau saita kawo k'arshen wannan bura'ubar da yake mata a gidan nan. Shima yana ganin shigewarta ya fashe da kuka na gasken gaske yana birkid'awa yana rik'e hannunshi da yake jin kamar zai cire ya barshi, gashi ba zai iya tuk'a motar ba bare ya kai kanshi wajen magani, baida nutsuwar da zai iya kiran wani ya zo ya d'aukeshi, mai gadin gidan ne yaji kukan babban mutum a waje ya fito da gudu, da taimakonshi ko da ya duba hannun yace karaya ce, tsaf ya mishi magani yasa mishi magani yanata addua'r Allah ya sawak'e, saida aka gama yace mi shi "Amma ba kaine bak'on da ka zo wajen Hajia Hanne (Inji shi)?"

"A'a." Ya fad'a yana tashi tsaye, shima tsaye ya mik'e yace "Amma garin yaya ka karya hannu haka? Gashi kuma banga alamar hatsari ba."

Huyowa yayi ya kalleshi, hatsari? Hatsari ma yake cewa baiga alama ba, bayan abinda ya faru yafi karon babbar mota muni, juyawa yayi ya ci gaba da tafiya a hankali yana d'an sosa bayanshi inda ya daka mishi gwiwa, motar ya bud'a ya shiga ya tayar ya fara janta a hankali yana tuk'i da hannu d'aya, sai dai ya ci alhwashin ko ma uban waye wannan yayan nata wallahi saiya tara masa yaran nan na unguwarsu yan zaman kashe wando sun ciro masa jijiyar dake sadar da ji da ganinshi.

*Allah yaba mai rabo sa'a.*

*Ko da* ta shiga da masifa a falon ta same shi yana wa Shureim bala'i yana fad'in "Akan banzar waya zaka zauna ana zagin ubanka a gaban k'aton banza, me yasa baka buga wayar a k'asa ba ta b'are? Duk duniya idan ka cire ni ubanka da uwarka da kuma yan uwanka ban yarda ka d'auki raini a hannun kowa ba, kaji na fad'a maka."

Girgiza kai Shureim ya shiga yi yana sako da hawaye, tana bayanshi a hassale tace "Wannan har d'ab'ia ce kake jin kana koya masa to?"

Juyowa yayi ya kalleta, kallon jin haushi da zan iya miki komai, ganin bai tanka mata ba yasa tace "...


*Alhamdulillah*
04/11/2020 ร  14:38 - Ummulkhairi: ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
*BADAK'ALA*
๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ _*AHALI NA*_๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ

๐Ÿ’ซโœจ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*๐ŸŒŸ
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_๐Ÿค

โ˜† *[ T.M.N.A]* โ˜† ๐Ÿ“–๐Ÿ–Š๏ธ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_67_


Ammar me ye matsalarka da samari na? Akan wane dalili ne kullum ka ganni da saurayi saika wulak'anta ni a gabanshi ko kuma ka muzantashi? Me yasa? Ka fad'a min idan ba haka ba yau ni da kai a gidan nan wallahi sai dai duk mu babbake."

Da fari da kallonta yake yana tunanin hannun da idan ya bigeta dashi zata fi jin zafi, amma data ce wai duk su babbake sai ta bashi dariya, dariya ya shiga yi hankali kwance wanda hakan ya sake hassalata cikin d'aga murya ta kalli Hajia dake zaune tana kallonsu kamar tv tace "Hajia ki mana tsakani da bawan Allahn nan ya daina shiga tsakani na da samari na, tunda dai ba zamansa nake ba kuma ba aurenshi ne akai na da zai addabe ni ba."

A hankali Hajia ta d'an dafe kanta dan ciwon kai taji suna neman sanya mata, lallai da taso a had'a aurensu, amma yanzu tunaninta shine yanda wannan yara zasu zauna in aka aurar dasu, lallai gaskiyar Junaid ne gidan nan zai iya kamawa da wuta, ganin Hajia ma ta k'yalesu saita k'ara jin haushi tace "To Allah idan na sake tsayawa da saurayi ka min iskanci Ammar saina soke ka da wuk'a."

Hajia ta kalla tace "A matsayinki na kakarshi Hajia ki fara nema masa magani, dan wallahi ya gama kwancewa."

Sama da k'asa ta bishi da harara ta giftashi zata wuce d'akinta, cikin salon da ka rantse bashi yayi maganar ba yace "Nan gaba ma wuyansu zan fara takawa, kin k'waci kanki da rumgumar da kika min, amma kika sake gigin zagar min yaro sai jini ya fita a bakinki, dan abu d'aya dana lura dashi shine baki k'aunarshi, to ni ina son kayana ehee."

Tab'e baki tayi tace "Akan me zan k'aunace? Wannan d'in?"

Ta fad'a tana nuna Shureim, gyara tsayuwarsa yayi yace "Me yasa baka son shi? Shi ba d'a bane?"

Kawai dan ta b'ata masa rai tace "Saboda bai min ba."

Gabanta fad'uwa yake saboda kallon da yake mata, murya k'asa k'asa yace "Me yasa bai miki ba?"

Da sauri Hajia dan ta tsayar da maganar tace "Hamna wuce d'akinki bana son tashin hankali."

Har ta fara takawa sai kuma ta tsaya ta kalleshi, cikin gadara da isa da rashin tsoron abinda zai biyo baya tace "Saboda da kai na same shi."

Wucewa tayi ta barshi tsaye, had'e labb'anshi yayi yana lasarsu, har ga Allah baisan ta yanda zai fara fad'awa yarinyar baya son ya ga ana nuna masa k'iyayya ba, musamman ma daga mutane masu mahimmanci a gare shi, saboda bata son shine yasa ma bata k'aunar d'an data haifa dashi, to wace irin k'iyayya ce take masa?Wani shu'umin murmushi yayi dan har ya tsara abinda zai rama shi ma, juyawa yayi ya nufi d'akin Ummy sai Hajia da tace masa "Bata nan."

Tsayawa yayi ya juyo yana kallon agogon hannunshi, shi dai duk yau banga Ummy a asibiti ba, to kuma in bata gida tana ina kenan? Saida ya zo kusan Hajiar yace "Ina taje a wannan daren?"

Tsakiyar idonshi ta kalla yanda ba kowa da falon zaiji ba tace "Tana arlit yanzu, amma gobe Abbanka zai je ya taho da ita."

"Arlit kuma?"

Bata bashi amsa ba sai kallonshi da tayi kawai, sunkuyawa yayi kamar zai fad'a kanta shima cikin rad'a yace "Hajia lafiya? Yaushe ta tafi ? Me yasa kuma ban sani ba?"

Kafeshi tayi da ido kawai hakan yasa yace "Dama ta fad'a min Abba na mata wasu abubuwada ni kaina fa bana jin dad'insu? Ko dai korarta yayi?"

Saida ta d'aga kafad'a tace "Kusan haka."

"Kusan haka." Ya fad'a yana jinjina kai, fita yayi daga falon yana tunanin abunyi.

Kamar kullum yaran sun tafi b'angarenshi suna ta wasarsu, Ameera yaja a jikinsa ya kwantar da ita saman k'irjinta yana lallab'a yana shafata, da wani abun ya d'auki hankalinta ta mik'e zata tashi saiya mayar da ita kwance, tun suna haka har ta gaji bacci ya d'auketa, ko da ya lek'a fuskarta yayi dariya yana d'an cike leb'enshi yace "Da kanki zaki zo na hukuntaki kan tsiwar da kika min."

Ci gaba yayi da kallon yaran saida suka gaji suka ga dare yayi sannan Ameer ya kama hannun Imam yace "Abba gida zamu tafi, Imam bacci zaiyi."

Aje Ameera yayi kan kujera yace "Muje na raka ku to."

"Ameera fa?" Ya fad'a yana kallon Ameera dake bacci, saida ya kama hannunsu suka nufi k'ofar fita yace "Tayi bacci mana."

Ameer ne yace "Abba Ummy fa ba zatayi bacci ba idan bata nan, tare suke kwana akan gadonta."

Murmushi yayi yace "Sai ka ce ta zo ta d'auke ta to."

"To." Ya fad'a suna shiga b'angarensu, saida ya ga shigarsu falon kad'ai ya dawo, d'aukar Ameera yayi ya kaita d'akinshi ya shinfid'e ya dawo ya kashe wuta da tv ya kwanta kan kujera yana jiran zuwanta, ya sani ne dole ta zo dan zata iya hak'ura in cikin mazan ne amma banda Ameera, yarinyar data tab'a yanke hannu da reza wajen k'in ji, ita kuka yarinyar ma kuka aka rasa wa ya yanke d'in.

Ko da suka shiga ta k'are musu kallo tace "Ina Ameera?"

Ameee ne yace "Abba yace kije ki d'aukota tayi bacci."

Sak'e tayi tana kallonshi, Abba kuma? Lallai ma ai ita d'in ba sakarya bace, bayan ihu da rashin kunyar data masa zata yarda taje su had'u, ai sai dai in a cikin mutane suka had'e, kallonsu tayi tace "Ku je ku kwanta to."

Wucewa sukayi kowa ya kwanta a inda yake kwantawa, hannayensu duk suka d'aga tare da ita sukayi addu'a kafin suka shafa a jikinsu, tana hangensu har bacci ya d'aukesu cikin nutsuwa, tashi tayi ta k'ara gyara musu kwanciyar ta sumbaci kowane, dawowa tayi kan gadonta ta d'auki wayarta, lambarshi ta kira lambar data kasa gogeta a wayar kuma ko sak'on gaisuwa babu mai aika ma wani. Sanda kiran ya shigo wayarshi saida ya ji tsinkewar gaba dan abu ne da baya faruwa ko ya jima bai faru ba, saida ya k'ara gyara kwanciyarshi ya lumshe ido sannan ya d'auka, cikin muryar da ko a bacci ya tashi takan zama kamar ruwan d'umin dake wartsakar da gajiyarsa, muryar da ko hayaniya take masa yana iya tsayawa ya saurare ta, murya ce da ko halin rashin lafiya yake yasan zata iya zama wani muhimmin maganin da zai taimaka masa wajen warkewa, lumshe ido yayi sanda tace masa "Hello."

Ba tare daya bud'a ido ba yace "Ya akayi?"

Saida ta sake tausasa murya tace "Ameera, tayi bacci ne?"

"Umm." Ya fad'a k'asan mak'oshi, marairaicewa tayi tace "Dan Allah ka taimaka ka kawo min ita, ba zan iya bacci nesa da ita ba."

Wani murmushi yayi yace "Wai ke mahaukaciyar ina ce?"

Cikin zazzak'ar murya kamar mai rera masa wak'a tace "Ta gidanku mana."

D'orawa yayi da "Inba haukanki ba wa ke son 'ya'ya kuma ya k'i ubansu?"

Jujjuya idonta tayi dan ta fahimci zai ja maganar da tsayi ne ita kuma bata da wannan lokacin, a hankali tace "Malam ni dai taimaka ka kawo min yarinta, yarana ina son su saboda suna da nutsuwa hankali da sanin ya kamata."

Jim yayi yana fassara kowace kalma data fad'a, iska ya furzar yace "Ba damuwa, kankana, idan akwai abun rubutu kusa dake ki d'auka ki rubuta, wallahi akwai ranar da zata zo ba wai ki min rashin kunya ba, sautin muryata ma idan kika ji sai kin nemi wurin b'uya."

Bushewa tayi da dariya tace "Ammar, amma zazzab'i na damunka ko?"

Shi kanshi murmushi yayi mai ciwo irin yanda wai Hamna ce ke soka masa iskanci irin na yaran zamani, cikin sigar gargad'i yace "Amman dai kinsan waye Ammar ko? Sannan kinsan kalar na wa iskancin, muje zuwa tunda haka kike so."

Gyara kwanciyarshi yayi yace "Abu d'aya nake so dake shine, ki janye wannan kalmar da kika fad'a a kaina da kuma yaro na."

Cikin k'aguwa tace "Zaka kawo min 'yata ko sai na zo da kaina?"

Murmushi kawai yayi kamar yana gabanta bai tanka mata ba, hakan yasa ta kashe wayar ta aje kan gado, wayar ya bi da kallo kafin ya aje ta gefe, har ya shiga tunanin duniya kuma Hamna da taji ba zata iya hak'ura ba ta sake kiranshi, ko da ya ga kiran kashe wa yayi amma saida ta k'ara maidowa, sake kashewa yayi ta k'ara kira a karo na uku, a k'ufule ya d'auka yana fad'in "In mayya ce ke ki ci kanki kankana, wannan wace irin masifa ce ba zaki barni nayi bacci ba, ke dai da gani zakiyi jarabar tsiya."

Ido ta zaro tace "Wace irin jaraba kuma malam? Daga kira ta waya."

Cikin masifa yace "To uwar me zan miki? Me yasa ba zaki kira saurayin nan naki ba mai zubi da figaggar tantabara kiyi hira dashi ba."

Cikin sanyin murya tace "Ammar me yasa ka daki d'an mutane? Wallahi ko sunanshi ban sani ba daga had'uwar farko ka same shi ka narka kamar kai ka haife shi, kasan dai baka kyauta ba kuma wallahi Allah zai saka masa."

Tintserewa yayi da dariya yace "Ni ma Allah zai saka min na shiga hurumina da yayi, kuma ina so na nuna miki irin mazan da kike soyayya dasu duk babu wanda zai iya rik'e ki."

Cike da gatsali tace "Sai kai kenan ko me?"

Murmushi yayi yace "Ni ai na fad'a miki goma kamar ki ma zan rik'e su, bare ke dana yi wa wanka na saka miki d'an wando da hannu na."

Kamar sub'utar baki sai cewa tayi "Haba ko da nace, ashe tun ina yarinya ka gama lalata ni."

Dariya yayi kamar yana gabanta yace "Da yanzu shekararki nawa da mutuwa to?"

Cikin rashin fahimta tace "Ban gane ba?"

Saida ya d'aga sauti yanda zata ji da kyau yace "Ina nufin a yanzun ma ba zaki iya d'aukata ba, ina ga tun a waccen lokacin ne? Hamna waccen ma maleji nayi kinji."

Kamar zata fashe da kuka tace "Ammar Allahya isa, kuma karka manta ka ma yarinyata addu'a ka shafa mata, mugu kawai."

Wata sanyayyar dariya ya bushe da ita yana kallon wayar data kashe, tashi yayi ya shiga d'aki ya samu Ameera, addu'a ya mata kamar yanda ya nema kuma yake wa yaran, shafa mata yayi tare da komawa d'akin marigayiya wanda har yanzu kayanta kenan ya kwanta, zanin rufar yaja ya rufe duka har kanshi. Abune daya zamar masa jiki yanzu duk zafin da ake saiya rufe kanshi da zanin saboda k'amshin turaren Amna da yake jikin zanin, da iskan turaren ya fara barin zanin saiya sake d'auka ya zazzaga, hakan na samar masa da nutsuwa sosai.

K'arfe *03:47* na dare Ameera ta farka, madarar da take sha babu ita kusanta kuma babu kowa a tare da ita, tasowa tayi ta fito falon ma babu kowa, a cikin fridge yana aje madarar saboda ya san suna buk'ata yaran, amma sai ba tayi tunanin bud'awa ba ta d'auka, haka kuma bata tsaya nemansa ba saita tunkari k'ofa, uwarta kawai take son gani taji dad'i, dama bai rufe k'ofar ba saboda tunanin Hamna zata zo, ko da taji ta bud'e saita fita ta nufi b'angaren, amma matsalar shine k'ofar shiga falon Hajia a rufe take, jijjigawa ta shiga yi amma shiru ga kukan tsintsaye dake tsoratar da ita, sulalewa tayi ta zauna manne a jikin k'ofar, a hankali ta saki fitsarin da take ji a wurin.

Ganin dai babu motsin kowa kuma babu mai shirin zuwa saita fara rera kuka,Tsawon wannan lokaci Haka tayi shi zaune ita kad'ai tana kuka tana son yin bacci, kiraye kirayen sallah yasa mai gadi ya fito dan yin alwala, amma duk kai da kawon da yayi Allah bai nuna masa ita ba saboda akwao duhu ma.

Firgigit ta farka kamar wacce tayi mummunan mafarki, ko da ta bud'a ido juyawa tayi inda yarinyar ke kwanciya bata ganta ba, ganin lokacin sallah ma ya kusa saita ta tashi ta shiga ban d'aki tayi alwala ta dawo, har ta bud'a wajen kayanta da niyyar sake na jikinta na bacci, a hankali a hankali sai take jin kamar sautin kuka k'asa k'asa, shiru tayi tana saurarawa har dai ta fito daga d'akin, a lokacin da Ameera ta farka ta k'ara fashewa da kuka mai gadi ya ganta, matsowa yayi yana dubawa da kyau, cikin tsoron ko dai ba yarinyar bace yace "Wacece nan?"

D'aga kanta tayi ta kalleshi fuskarta duk tayi jina jina da hawaye da bacci a idonta, cike da mamaki ya sake cewa "Hajia k'arama ce? Me kike yi anan?"

Cikin kuka da maganarta bata ko fita tace tace "Wajen Ummy zani."

Sai lokacin ya saki jikinshi ya matso sosai ya fara buga k'ofar, daidai lokacin Hamna ta fito taji ana buga k'ofar, take a wurin ta sawa ranta Ammar ya dawo da Ameera ta tashi a bacci kenan, sam mantawa tayi da riga da wandon dake jikinta, wando iya gwiwa yake na sojawa ne sai rigarshi bak'a mai k'ananan hannu amma ba sirara ba, da sauri ta shiga saukowa zata nufi k'ofar sai ga Labaran shima ya fito tare da yaranshi maza ya iza k'eyarsu gaba zuwa masallaci, karo suka ci sai Kamal da shima ya fito daga nashi d'akin daga sama, rage saurinta tayi ta kalli Labaran da yace "Ina zaki tafi kike sauri haka?"

Cikin girmamawa tace "Naji ana buga k'ofa ne."

"Nan?" Ya fad'a yana nuna k'ofar, da "Eh." Ta bashi amsa tana kallo ya hanzarta zuwa ya bud'e, mai gadi ya gani tare da Ameera a hannunshi, Hamna na tsinkayarsu bata bari wani cikinsu yayi magana ba ta daka a guje ta finciko Ameera ta rumgume a jikinta, kallon fuskarta take tana share mata hawayen da har sun fara bushewa, kallon mai gadi tayi tace "Ina Abbanta yake? Daga ina ka d'aukota?"

"Wallahi nima anan na ganta ita kad'ai tana kuka, tace wajenki zata tafi."

Cike da tausayi ta kalleta tace "Abbanki ne ya kawo ki?"

Girgiza mata kai tayi hakan yasa tace "To yana ina?"

Cikin shahsek'ar kuka tace "Ban ganshi ba."

"To ya akayi kika taho nan Ameera?" Ta fad'a cikin yanayin tashin hankali, murya k'asa k'asa tace "Ban ga Abba na ba kuma ban ganki ba, shine na taho wurinki kuma k'ofar ta k'i bud'ewa."

Cikin d'aga murya kamar za tayi kuka tace "Tun yaushe Ameera? Kin jima anan d'in?"

Yarinya da babu hankali sai tace "Tun da daddare."

Zaro ido tayi da matuk'ar tsoro ta sako da hawayen tausayi tace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, yanzu Ammar nan ya bar min ke kikayi kwana."

Labaran ne yace "To shiga da ita ci..." Bai gama fad'a ba ya ga Hamna ta aje Ameera ta wuce da sauri ta nufi b'angaren Ammar, Kamal ne ya kalli Labaran yace "Tonton muje muyi sallah, gobarar nan ubangiji ne kawai zai iya kashe ta."

Wucewa sukayi sallah har da mai gadi, tana zuwa da k'arfi ta bud'a k'ofar falon ta shiga, ba tsayawa komai ta tunkari k'ofar d'akin baccinshi, tana daf da kaiwa shi kuma ya bud'a ya fito zai tafi masallaci shima da doguwar riga, kamar wata zakanyar da aka cinyewa ya'yanta suna had'a ido taga shine kawai tasa k'arfinta da hannayenta ta tura shi baya da k'arfi, k'ofar d'akin ya kaiwa karo yana kallonta da mahaukacin mamakin lafiyarta.

Cikin kuka kamar an ce mata Ameera rasuwa tayi da d'aga tace "Ammar me yasa zaka min haka? Me yasa zaka bar min yarinya ta kwana a tsakar gida ita kad'ai kamar wata marar gata, me yasa baka kira ni na zo na d'auketa ba in kai ba zaka iya kai min ita ba? Haka kawai ka maidata kamar wata *marainiya*."

Cikin rashin fahimtar inda kalamanta suka dosa ya matso kusanta yace "Wace yarinyar wai? Ameera kike nufi? Amm..."

"Amma me?" Ta fad'a da k'arfi, d'orawa tayi da "Saida na kiraka nace ka kawo min ita, ko ban kira ka ba? Kasan ba zaka iya kula da ita ba shine ka k'i kawo min ita tsabar mugunta, kuma ai kasan ba wajenka suke kwana ba, amma tsabar fitina da nema na da magana ka rik'eta wajenka."

Sake matsowa yayi kusanta yace "Ke yi k'asa da muryarki, d'anki ne ni da zaki zauna kina min fad'a, dan fa yana asuba ne bana masifa a irin wannan lokacin."

"To kayi mana, na ce kayi, ni ita nake nema da kai." Duk tayi maganar ne tana turashi baya da k'arfinta, saida ta ga ya dangane da bango ta nuna shi da yatsanta mai d'auke da doguwar afaifa da bak'in lalle tace "Ya zama na k'arshe kenan da zaka k'ara k'ok'arin rabani da yarana, wannan ba samari bane da zanyi shiru idan ka shiga tsakani na dasu, akan 'ya'yana saina dafaka da ranka kuma na shanye romon."

Ido ya zaro tare da bud'e baki irin firgicin nan cike da shak'iyanci yace "Mayya ce ke dama? Yaushe kika fara cin naman mutane?"

Sama da k'asa ta daddala masa harara tace "Tun ranar da bak'in bakinka ya rairaye min k'iba ta."

Juyawa tayi zata fita yace "Ki nemi abinda ya ramar dake kankana, amma ba bakina ba, kuma nasan kema kinsan ko a ina matsalar take."

Tsayawa tayi ta juyo tace "Babban matsalata a rayuwa kai ne Ammar."

Sake juyawa tayi zata fita abinda zata iya cewa bai tab'a faruwa ba, indai kaga jikinshi a hannunta to mugunta ce zai mata, amma sai gashi ya rik'e hannunta kuma ba da k'arfi ba, hasalima yatsunta ne ya rik'e yana mammatsa su a hankali a hankali, matsowa yayi kusanta saida ya tsaya gabanta yana kallon fuskarta, tayi shiru alamar abun ya ratsata, babu wani yanayi a tare da fuskarta na bak'in ciki ko b'acin rai, fuskarta dai kamar tana bacci yanayin nutsuwa sosai.

Yana kallon fuskarta cikin yanayin fahimta shima yace "Hamna kina son yaran nan sosai, rabaki dasu abune da ba zaki ji dad'inshi ba, amma me yasa kika k'i amince da maganar iyayenmu na son had'a aurenmu?"

Da sauri ta kafe tsakiyar idonshi da kallo, kasa d'aukewa tayi kuma ba tace komai ba, shima ba tare daya rusunar da idonsa ba duk da hakan kuwa na galabaitar dashi yace "Hamna kina da girma da mahimmanci a zuciyata fiye da tunaninki, ni mai iya mallaka miki yarana ne har abada sun zama naki, amma matsalar d'aya ita ce idan kika auri wani, ba fa lallai ya barki tare da su ba kamar yanda kike so, kuma na tabbata iyayenmu ma abinda sukayi la'akari dashi kenan suka so had'a aurenmu, amma da yake mahaukaciya ce ke lamba d'aya sai kika kawo wani mai suffar yan tsaki wai shi kike so."

Har yanzu idonta na kanshi cikin taushin murya tace "Nice mahaukaciyar?"

Saida ya kawar da kansa yace "Eh mana."

A hankali ta zame hannunta daga na shi tana fad'in "Ni da kai bamu dace ba Ammar, ba zamu iya zama a inuwa d'aya ba."

Murmushi yayi yace "Tsakaninki da Allah idan na baki umarni ba zaki bi ba?"

Saida ta dafa girarta sama tace "Me zai hana ni bi, zan bi mana idan bai sab'awa Allah ba."

K'wayar idonta ya kalla yace "Tsakaninki da Allah baki jin komai a kaina?"

K'asa tayi da nata idon tace "Kamar me fa?"

D'an ja baya yayi yace "Ranar dana samu hatsari sai gashi naga tsoro fargaba da tausayi a idonki, ranar da zamu bar garin nan tare da margayiya kin d'aga murya akanta, sannan duk da abinda na miki baki iya d'aga muryarki kowa yaji ba, hasala dake ake ta rufa rufa, an fasa aurenki sau uku amma babu wanda kika damu dan an fasa shi, wannan duk menene *kan..ka...na*."

Yanda yaja sunan kankanar yau sai taji sunan ya mata dad'i a kunne, amma dan karta saduda a gabansa sai kawai ta yamutsa fuska tace "Kai kuma a yanda ka fahimci abun kenan? Gaskiya kana buk'atar ganin likita."

Rab'ashi tayi zata wuce ya bi bayanta da kallo, rintse idonshi yayi dan ba zai yarda alwalarsa ta karye ba yace "Kina mantawa da ni likitan zuciya ne ko?"

Tsayawa tayi ta juyo ta kalleshi, murmushi tayi ba tace komai ba dan haka yace "Shekaru na b'ata ina wannan karatun, matakan kare kai daga kamuwa da cuta har zuwa yanda zaka mu'amulanci marar lafiyarka duk a karance nayi shi, karki d'auka haka kawai na zama tantiri a gidan nan Hamna, komai da nake yi ina sane nake yinshi, duk abinda zanyi ina yi ne dan ya tsayawa kowa a rai yayi nishad'i da zulumi, lokuta dayawa kuma har ayi dariya, taya kike ganin ba zan karanci kowa da halin da yake ciki ba."

Takawa yayi ido rufe saida ya tabbatar ya kai gareta kafin ya bud'a ido ya wuce ta bai tsaya ba, fita yayi ya wuce masallaci ya barta tsaye, da kallo ta bishi tana takawa a hankali ta koma wajen Ameera, ya daki zuciyarta sosai amma taji haushinta kanta data yarda ya ganota, ko da yake ma ai k'arya yake yi bata jin komai a game dashi, abinda ya fad'a tayi kawai yayi dogaro da su ne dan ya kunyata ta, dan haka kawai ta share al'amarinshi.

*Ko da* ya dawo daga masallaci ya kira wayar Ummy, batan ta d'auka sun gaisa yake ce mata "Ummy Abbanmu na nan tafe zai zo d'aukarki, amma kinsan me?"

Daga b'angarenta ta amsa da "A'a saika fad'a."

Gyara tsayuwa yayi yace "...


*Allah yasa ba zugaki zaiyi ba uwarmu.*


*Alhamdulillah*
04/11/2020 ร  14:38 - Ummulkhairi: ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
*BADAK'ALA*
๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._


DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment