Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ _*AHALI NA*_πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦

πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_76_

*Sati biyu* kenan da rufe shi, colonel da gwamna babu mai labari, lieutenant nan ne ya tsawatar kar wanda ya fad'a musu, amma tsakanin mata da miji sai Allah, yau dai abun ya damu Hamna ta yanda take jin ba zata k'ara kwana ba tare da mijinta ba, kiran Gambo tayi tana kuka, yana jin muryarta cikin kukan nan yasa dreba ya tsayar da mota, yana kan hanyar shi ta zuwa aΓ©roport zai bar k'asa ya dakata, cikin tashin hankali da kulawa yace "Hamna me ya faru? Lafiya kike kuka? Me akayi?"

Cikin matsanancin kuka tace "Abba sun rufe yah Ammar, kuma Abba ya hanaa fad'a maka, dan Allah Abba ka taimaka ka fito dashi, ba fa wani laifi ya aikata ba."

Ajiyar zuciya ya sauke ya rintse ido yace "Me yayi aka rufe shi? Tun yaushe yake rufen ma?"

"Abba satin shi biyu?"

Da k'arfi cikin razani yace "Me? 2 semaine? Me yasa Hamna? Shin yaron nan baya da gata ne ko me?"

Cikin kuka tace "Abba ne ya hana a fad'a maka."

Tsaki yayi tare da kashe wayar, kallon dreban yayi yace"Muje."

Babban mai tsaron lafiyarsa dake kujerar gaba ya kalla yace "Gida zamu je yanzun, kayi magana da dreban jirgin, ni zan kira prΓ©sident muyi magana."

Bai tsaya tambayarshi ba dan in dai kaji yace gida to gidan Hajia yake nufi. A d'an lokacin da bai taka kara ya karya ba suka iso, suna shigowa garin ya kira colonel da a lokacin yake wani k'auye a *mali* ya fad'a mishi tare da neman taimakonshi, wai Allah zo kaji fad'a wajen uban Ammar, yanda kasan Gambo ne mai laifin haka ya dinga kirta masifa ba k'akk'autawa, shi dai bai taya shi ba har ya gama yace yaje gida zai tura mishi da wasu daga cikin sojoji, yo su za'a nunawa kaki, a k'arshe ma cewa yayi kaf jami'an sun ci...har da shi ma bai cire kanshi ba da lieutenant d'in.πŸ˜‚

Da isar shi gidan ko ciki bai shiga ba suma suka k'araso, Hajia kawai ya gaishe da ita yace zai je ya dawo yanzu, daya fito shi kanshi saida gabanshi ya fad'i, to me Hussein ke nufi daya turo wannan motocin, mota har hud'u da sojawa a ciki, duk akan menene? Duk fitowa sukayi suka shiga sara mishi da girmamawa, kafin babban cikinsu ya sanar dashi colonel ne ya turosu su bashi tsaro inda zaije, godiya ya musu kafin suka d'auki hanya, kamar wanda zasu tafi yak'i, shi ga nashi motocin dake ta jiniya wi wi wi, duk inda suka wuce sai an bisu da kallo sai dai zaka san babba ne ya zo.

Sanda suka isa, a lokacin da suka shiga wurin da matsiyacin gudu, kafatanin sojojin dake ciki kowa neman bindigarshi yayi ya sake rik'eta da kyau, kowa ya gama zama a ankare dan tunaninsu gari ne babu lafiya, ko ana wani babban fad'a ko kuma wani garin ne ake yak'i aka zo neman taimakonsu, duk sun tsaya cikin shirin kota kwana na tafiya, suna kallo sojojin ke ta durkowa daga cikin motocin, sai dai motar da gwamna ke ciki suka ga garde cord d'in shi ya bud'e yana hakimce bayanshi, da mamaki suka bishi da kallo suka kam, basu san da zuwanshi dan ana d'aukarsu wani lokacin dan su kare lafiyarshi, sai kawai ganinshi sukayi anan, to me ya kawo shi? Tambayar da kowa ya jefi kanshi da ita kenan, yana gaba garde d'inshi na bayanshi da bindigarshi ya d'ora hannu kanta, sai soja biyu a gaban gwamnan wanda suna cikin masu tsaronshi, sai sauran jami'an a bayansu duk suka k'araso wajensu suka tsaya, suma dai gefe sukayi da bindigoginsu suka shiga sarawa duk wanda ke sama dasu, da hannu kawai ya musu alamar su shiga ciki, jiki duk a sab'ule suka rufa masa baya da tunanin ko lafiya? Kujera suka matso mishi da ita ya zauna, amma saiya tokare ya tsaya ya kalli k'aramin major d'in yace "Je veux voir mon fils, je peux?"

Gabanshi yayi ya yanke ya fad'i a take ya fara salatin annabi, to waye d'anshi anan gidan? Cikin tsoron al'amarin yace "Pardon g..."

Katse shi yayi da cewa "Tout de suite."

Wani d'an matashin jami'i ya kalla kafin ya kalli gouverneur d'in yace "Son ...nom?"

Cikin muryar gargad'i yace "Ammar Hassan Suley Gaga."

Yana kallon k'aramin jami'in yayi sauri ya juya, Gambo ya had'e fuska sosai ya kuma kafe major d'in da ido sai ya d'an jima yake k'yabtawa, shi kuma yayi k'asa da kanshi yasan kallon zaka ci ubanka ne idan aka fito min dashi, jin motsin sun fito yasa shi juyawa dan ya ma k'ara kallon d'an, ko da ya kalleshi a ranshi yace "Wannan sarkin girman kan? To ai shi ya so zama anan."

Ko da suka fito ya hangi Gambo sai kuwa Ammar ya tak'ark'are ya d'ora hannaye saman fuska ya shiga murzar ido wai shi a dole kuka ne yake, da sauri Gambo ya k'arasa ya tarbe shi da niyyar rumgume shi, amma ikon Allah sai Ammar ya fad'i k'asa zaune yana kuka cikin babbar murya yana tumurmusa k'afafu yana fad'in "Ni kawai ka koma babu inda zanje, haka kawai kuka manta dani a wurin nan suna ta dukana."

Rigarshi mai botira a gaba ya shiga kiciniyar bud'ewa yana fad'in "Dubi yanda suka farfasa min jiki, kamar ba d'anku ba ace duk babu mai so na a cikin, kalle ni fa dan Allah."

D'aga kai yayi sama yana wani kukan, kaf wurin babu wanda bai sakar masa ido ba, sai dai Gambo tuni ya harbo jirginshi yasan me yake nufi da abinda yake yi, juyowa yayi ya kalli major kafin yayi magana ya d'an muskuta tsayuwarshi yace "Wallahi yallab'ai babu wanda ya tab'a dukanshi a wurin nan, ko?"

Ya tambayi sauran yaran, dukansu girgiza kai sukayi alamar eh, kallonsu yayi ya tsaya da kukanshi yace "Na muku k'arya kenan?"

Kallon Gambo yayi yace "Abba na, ina k'arya ne ni?"

Juyawa Gambo ya sake yi ya kallesu yayi k'wafa tare da jinjina kai, sunkuyawa yayi ya tallaboshi yana fad'in "Rabu dasu yaro na, ai ba sai ka fad'a ba ma na sani, dubi duk yanda ka lalace."

Ai sai yaji dad'i Gambo ya taya b'era b'ari da sauri ya kamo hannunshi suka dawo kusa dasu, uku daga ciki ya nuna yace "Abba wad'an nan suke cinye min abinci na ina ganinsu, sai su had'a ni da wani banzan abinci bana iya cin shi ma, ni kawai ban yarda ba wallahi sai na shigar da k'ararsu."

A take suka shiga kallon kallo suna tausayawa kansu, su ai basu san girmanshi ya kai haka ba, kallonshi Gambo yayi yace "A'a bana son maganar shigar da k'ara, amma dai ka fad'i wani abinda kake so ni zan maka."

Ai da sauri major d'in yace "Yallab'ai..."

Kallonshi yayi yace "Ferme lΓ ."

Shirun yayi yana kallon Ammar dake kallonsu shima, a hankali yaji yace "Kawai su biyani kud'in abinci na."

Saida ya sauke ajiyar zuciya ta jin dad'i, da sauri cikin yaran wani yace "Nawa kake so yallab'ai."

Saida ya harare shi yace "Dukanku ku bada jaka sha biyar biyar."

D'aya daga ciki ne ya d'an bud'a baki irin yaushe muka ci wannan abincin? Idan siya zamuyi fa jaka goma zata bamu buhun oriba rice, major d'in suka ga yasa hannu aljihu ya ciro kud'in ya mik'a mishi, karb'a yayi tare da tara hannu wa sauran suma, da k'yar suka lalabo kud'in tunda wata yayi nisaπŸ˜‚, kallon major d'in Gambo yayi yace "Ya zamuyi yanzu?"

Girgiza kai yayi yace "Yallab'ai comme tu le veux."

Kallon Ammar yayi yace "Ina so na koma da yaro na, shin akwai tara ko wani abu ne?"

Girgiza kai yayi yace "Tun ranar aka so musu sulhu shine ya k'i."

"Me ye abunyi yanzu?"

Saida ya d'an kalli Ammar daya kafesu da ido yana ta kallo yana tunanin ta yanda zai diro musu kafin yace "Tara ce zai biya, sai kuma dan Allah ya kiyaye gaba, fad'a ba na shi bane yana babban mutum, sannan ya fita harkar yaron dan iyayenshi sun ce zasu d'auki mummunan mataki idan ya k'ara tab'a musu yaro, shine kawai."

Hannu yasa aljihun rigarshi ta ciki ya fito da cash yan jaka goma goma d'auri uku na 300 000 ya ajiye gaban teburin yana fad'in "A biya tarar, insha Allah kuma za'a kiyaye."

Kasa amsa mishi major d'in yayi kud'in nan sun gama haukatashi, yana rik'e da hannun Ammar zasu wuce Ammar yace "To wayata fa ko kuna da gadona ne?"

Da sauri major d'in ya jawo wani coffre ya fito da wayoyi ya aje gaban tebur d'in, dubawa yayi ya d'auki tashi ya juya zasu tafi, Gambo ne yace "Bayan wayar babu kayanka ne?"

Ba tare daya kalleshi ba yace "Me zanyi dasu to? Su d'auka na bar musu."

Suna k'arasa aka bud'e musu motar suka shiga tare, saida suka d'auki hanya Gambo ya kalleshi da kyau, yayi bak'i abinki ga jar fata, ya rame sai gashi da duk yayi baje baje ba kyau, a hankali yace "Ammar."

Ba tare daya kalleshi ba yace "Na sani Abba, zan daina."

Da mamaki ya kalleshi yace "Kasan me?"

Yana kallon titi yace "Nasan cewa za kayi na daina rigima na girma, na daina irin wannan abubuwan ni ba yaro bane, sannan idan ban bari dan komai ba na daina ko dan iyalina."

A d'an tsorace ya kalleshi ya had'e yawu, har ga Allah abinda zai fad'a kenan, dan ko da kalaman sun banbanta maganar dai d'aya ce, da k'yar ya k'ak'aro murmushi yace "Ka min alk'awarin zaka daina to?"

Fuska a had'e yace "Eh Abba."

Rik'o hannunshi yayi yace "Nagode, kuma na ji dad'i sosai, kaga su kanka iyalinka hankalinsu zai kwanta."

Yar k'aramar k'wafa yayi ya matsu ya ganshi gida ya tashi hankalin uban kowa, ba dai shi suka wofantar ba? Zasu gane yau d'in nan zai bar musu gidan ya koma na shi gidan, har ita kankana sai ta ci kakanta yau, inbai manta ba da aka tab'a rik'e shi marigayiya zuwa tayi tace sai dai su kwana, amma ita shine babu ruwanta ko?

Ko da suka zo gida kusan babu wanda ya fita dan safiya ce, a lokacin Hamna tana tare da su Ummy suna shirya teburin cin abinci, suna juyawa dan amsa sallamarsu suka had'a ido, da wani irin farin cikin da ita kanta bata san ta samu kanta a ciki ba ta saki cokalan hannunta ta ruga a guje, ta manta da duk iyayen dake wuri ta fad'a k'irjin mijinta.

Saida ya lumshe ido alamar sak'on ya isa inda aka aikashi, amma da yake jaraba ce ya shigo da ita saiya ture ta a jikinshi ya kalli Gambo yana nuna mishi yace "Ka gani ko Abba, lafiyayyen abun kari ne suke shiryawa zasu ci hankali kwance, nan kaga alamar damuwa tare da wani na rishina a gidan?"

Kallon Ummy yayi da su Hajia da su lieutenant yace "Du barkanku da warhaka, Allah ya k'ara muku lafiya da arzik'i."

Da kanshi kuma ya amsa da "Ameen."

Hamna ya kalla kafin ya ankara ya cakumo hannunta ya fita da ita daga d'akin, k'ok'arin k'wacewa ta shiga yi tana fad'in "Yah Ammar, yah Ammar sake ni mana, dan Allah sake ni."

Saida suka kai k'ofar d'akinsu ya ja ya tsaya ya kalleta yace "Bud'e min k'ofar."

Kamar zata yi kuka tace "Makullin yana can na baro, bara n..."

Bata kai k'arshen maganarta ba taga yasa wa k'ofar k'afa da k'arfin sababi ya turata, ba shiri k'ofar ta wangale ta bud'e, turata yayi da k'arfi har tana neman fad'uwa kafin ya shiga shi ma, da sauri ya shige madafa inda ta mik'e dan binshi ta ga me zaiyi, tana kaiwa k'ofar shi kuma zai fito suka had'e, kwanukan data jera a madafar kamar kwalliya ta ga ya fito dasu a hannu, da mamaki ta kalleshi tace "Yah Amm.."

Bai bari ta gama fad'a ba ya buga kwanukan a k'asa, masu fashewa kam sun fashe mai lotsawa ya lomatsa, baki bud'e irin abun ya firgitata ta kalle shi tace "Wai me ye haka? Lafiyar ka..."

Sam bai bari ta fad'a abinda take son fad'a ba saboda hannun daya d'aga zai gaura mata mari, amma kuma kasawa yayi saiya kafe fuskarta da kallo, tsoro k'arara ne bayyane a fuskarta ta rintse ido ta kawar da kai gefe tana jiran jin saukarshi, jin shirun yasa a hankali ta shiga bud'a ido ta sauke kanshi, suna had'a ido sai kawai ta fashe da kuka dan abinda zata iya yi kenan, tana ganin ya sauke hannunshi k'asa sai kawai ta ruk'umk'umeshi a jiki tana sake fashewa da kukan sosai.

K'amk'ame shi tayi sosai tana fad'in "Kayi hak'uri yah Ammar, kayi hak'uri dan Allah kar kayi hushi dani, wallahi Abba ne ya tilasta ni kar na fad'awa kowa, kayi hak'uri dan Allah, yanzu ma nasan na sab'awa Abba tunda na kira Abba na fad'a mishi."

Wani irin tausayinta ne ya kashe shi, rumgume ta yayi shima ba shiri ya rad'a mata a kunne "Kin gama dani Hamna, ina sonki kinji."

D'ago kai tayi ta kalleshi tace "Muje kayi wanka bawan Allah sai tsami kake."

πŸ˜‚ Bushewa tayi da dariya hakan yasa shi matseta sosai suka shiga d'aki, sosai ta bashi kulawa a wannan lokacin, wanka soso da sabulu haka ta mishi, haka ta b'ata lokaci wajen wanke mishi gasumbarshi da gashin kanshi, hatta aske mafi sirrin wurin dake tara gashi ita ta cire mishi, tun a ban d'aki ta cire mishi akaihu kafin suka fito, da k'yar ya hak'ura ta shafa mishi mai ta caje mishi gashi ta shafa mishi mayukanshi, tana kawo mishi tea mai kauri da zafi ya shanye yaji k'arfi sai fa aiki ya tashi.

Ya nuna mata yayi kewarta na sati biyu, ya nuna mata yana son ta kuma yana son kasancewa da ita, ita ma bata tsaya a baya ba ta nuna mishi tayi kewarshi, suna d'aki hankali kwance suna raya zuk'atansu har azahar tayi. Lokacin da zai fita salla ne yake fad'a mata ta shirya yau zasu bar gidan nan tare da yaransu. Ba tayi musu ba dan tasan yanzu su fara tijara da to kawai ta bishi ta shiga had'a iya abinda zata had'a, sauran kuma tace daga baya sun gama d'auka.

Baya fitarsu kuma colonel ne ya kira Gambo yake tambayarshi yaya? A cewarshi "Mun dawo, gamu ma gida yanzu."

"Ina Hassan yake?" Cewar colonel, ko da Gambo yaji haka yasan babu arzik'i, mik'awa lieutenant wayar yayi yace "Gashi kuyi magana."

Ko da lieutenant ya amsa colonel yace "Hassan ka kyauta, an gode Allah ya saka da alkairi, yau Allah ya rufa maka asiri bana garin nan, da sai na maka k'ullin tsiya a ciki har ka amayo hanjin ka."

Cikin fad'a lieutenant yace "To bismillah, dan kaga bamu kusa shine zaka fad'a min magana, to ka zo kayi abinda za kayi."

Shima cikin fad'a yace "Yo mu ba abun kunyarmu bane wai d'an mu a rufe, kasan irin kunyata mun da kayi?"

"An je an kunyata kun, d'an iska ne ni to da zan tsaya ina lallab'a shi, Labaran fa shaidata ne nan muka je yaron nan ya bayar da hak'uri a gama komai amma ya k'i, to ya zamu mishi?"

A hassale yace "Hak'uri? Ya bawa uban wa hak'uri? Lusari ne shi da zai bayar da hak'uri? To ni daya bayar da hak'urin ma da sai na d'aga mishi nono." πŸ˜‚

Da sauri lieutenant yace "Sakarai ina kaga nonon to? Kenan ka d'aure mishi gindi ya ci gaba da d'aukar rigima."

"Yo sai me? Mu ba rigimar ce ta kawo mu duniya ba? Kaga malam karka k'ara mana irin haka, a irin wannan lamarin ba'a ma yaro haka, yanda yake da laifi shima waccen yaron da laifinshi, tunda waya aike shi kula masa matarshi sannan yasa aka ma d'an uwanshi duka, da kaima ka tsaya a wajen ka kare d'anka ka nuna musu ba bare bane shi ko marar gata, amma saboda Allah saika wulak'antashi a gaban mutane."

Cikin jin haushi yace "To ubana, yanzu yanda za ayi idan zaka dawo ka taho da bulala sai ka zaneni."

"Yo kaine da girmanka zan tsaya sawa bulala? Me ye anfanin bindiga ta to? Ai saidai kaji alburushi tsakiyar zuciyarka."

Zaiyi magana Gambo da yaga abun ya k'i k'arewa ya figi wayarshi ya d'ora a kunne yace "Malam idan fad'an zaka masa ka kira shi da wayarka amma ba da kud'i na ba."

"Au Gambo ni zaka ma iskanci? To kud'in ne bana da ko wayar? Kayi sa'a bana gabanka da na fasa wayar, ba d..."

Bai barshi ya fad'a ba ya kashe wayar yana dariya. Dan yasan yana can yanzu yana mita da jaraba.

*Da yamma* fa tsaf ya shiga ya fad'a musu gidan nan zasu bari, Ummy ce ta kalleshi tace "...


*Alhamdulillah*
04/11/2020 Γ  14:40 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*BADAK'ALA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ _*AHALI NA*_πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦

πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_77_


"Ammar da gaske kake tafiya zakayi? Amma kai tsaye haka?"

Cikin ladabi yace "To Ummy ni kuwa me zan zauna nayi? Ina d'aure fa a gidan nan kuke cin kaji kuna shan faro da exotic, to dan Allah me zan zauna na muku."

Hannunshi ta kama ta jashi zuwa d'akinta, saida ta zaunar dashi kan kujera sannan ta sake shi ta samu wuri ta zauna, kallonshi tayi sosai tace "Ammar ina fata dai rigimar nan ta kwanta ko?"

Da sauri ya kalleta yace "Ta kwanta Ummy? Haba haba haba, wannan magana ai bata taso ba, kamar fa a dake ka ne kuma a hanaka kuka, Ummy ko mutum na kashe a garin nan wallahi na fi k'arfin wulak'ancin da aka min, dan haka da yaron, da jami'an, da dokar, da wanda ya bayar da shawara aka k'irk'iri dokar, da wanda yayi rubutun dokar, da wanda yana nan aka aza dokar kai har da wanda ya aza dokar ma duk sai..."

Da sauri Ummy ta rufe mishi baki tana fad'in "Rufa mana asiri karka k'arasa fad'a, iyayenka ma zasu iya shiga ciki."

Jinjina kai yayi irin haba d'in nan, d'auke hannunta tayi ta mishi kallon fahimta tace "Ammar ka yarda ni mahaifiyarka ce?"

Jinjina kai yayi yace "Na yarda mana Ummy."

Kai tsaye ta d'ora da "Kuma ka yarda ina da girma da matsayin da zan iya sa ka ko hana ka?"

"Tabbas Ummy, kin isa har ma kin wuce."

Jinjina kai tayi alamar gamsuwa tace "In dai hakane to ina so maganar nan ta wuce, wucewa ta har abada Ammar, ka bawa al'amarin nan baya ka fuskanci rayuwarka ta gaba, 'ya'yanka da matarka ka rumgumesu ka watsar da duk wani shirme, idan har ka yarda zaka daina to ina so ka min alk'awarin da zai sani gamsuwa."

Da sauri ya rik'o hannunta yace "Wallahi Ummy na miki alk'awari har abada babu ni babu sake fad'a da wani ko tashin hankali, hasalima Ummy ko zagi ba zaki sake ji daga bakina ba, insha Allahu Ummy na miki wannan alk'awarin."

Da tsantsar farin ciki tace "Nagode sosai d'an albarka, Allah ya saka da alkairi, Allah ya maka albarka ya kareka daga sharrin masharranta."

Shima da jin dad'in addua'r ya amsa da "Ameen Ummy, ni ma nagode."

Mik'ewa tayi tana rik'e da hannunshi tace "Tashi kuje Allah ya tsare, Allah kad'e fitina a tsakaninku."

Haka suka fito suka tattara yaransu suka fita, ana yan koke koke da yan shak'e shak'e haka dai suka bar gidan da yammar nan kamar wanda aka kora.

Yanda Hamna taji ana fad'in gidan ga wanda suka je saida taje ta ga ba haka bane suna k'wauran fassarashi, ba k'arya fa Ammar yayi gini na kece raini na shiga tsara, babu ce kawai babu a cikin gidan amma hatta kayan d'aki saida ya mata sabi ya zuba, har kayan jiki kallonta kawai yake sanda take kwaso kayan jikinsu, bai hanata bane saboda tunanin tana buk'atarsu ne, amma shi babu abinda baiyi ba har yaran ma ya musu sabin kaya.

Savon gida sabuwar rayuwar ga sabon k'aramin ciki da take dashi had'e da sabbin mutane, nan suka fara rayuwarsu ta d'aukar bakin duniya da sababi, babu abinda ya rage na zamansu sai ma sababin salon shiririta da suka fito dasu.

Idan yaran na gidan kad'ai suke d'an d'aga k'afa suna rage wani abu, amma idan suka fita sai su koma yara sai abinda suka ga dama sukeyi babu mai k'wabarsu.

*Wata shida*

Yau ma ya gama shiryawa zai fita yara sun kwana wajen Ummy saboda weekend ne, tana zaune ta d'ora farantin kankana kan tulelen cikinta tana sha, ko kulata baiyi ba ya d'auki hanyar fita, baki bud'e ta kalleshi da mamakin yanda ya shareta zai fita tace "Toh! Su Ammar kuma ko magana babu shine zaka fita?"

Ba tare daya juyowa ba yace "Bani da lokacinki ne."

Ido ta zaro ta shiga kiciyar tashi tsaye rik'e da farantin tana fad'in "Wace yar iskar ce?"

Juyowa yayi ya kalleta, a hankali ya shiga takowa da wani irin kallo mai d'auke da salon mugunta, da sauri ta shiga ja baya ta fara zagaya kujerar tana fad'in "Allah karka matso nan Ammar, ka tsaya nan ka fad'a min wace shegiyar ce ta d'auki hankalinka har tasa kake jin baka da lokaci na."

Cikin dakiya yace "Zan zo ne nan saina fad'a miki yanda zaki fahimta."

Da sauri tace "Daga nan ma idan ka fad'a zan ji, fad'a min wacece ita?"

Da sauri ya d'ago k'afa da niyyar kamota hakan yasa ta juyawa zata zuba a guje d'aki, cikin d'aga murya yace "Hamna in kika tafi a guje da cikina ban yafe miki ba."

Da k'arfi ta juyo tana kallonshi tana ja baya da tsoron kar ya tardata, da k'arfi ya rik'o wuyan hannunta yana matsewa cikin k'eta yana fad'in "Ni na fad'a miki ina da yar iska ne a waje? Wai ke me yasa kishi ya miki yawa ne?"

Cikin zabga ihu kai kace idonta yake cirewa ta shiga fad'in "Ammar zaka karya min hannu, sake ni dan Allah sake ni, hannu na fa zai karye."

Saida ya zaunar da ita kan kujera yayi tsaye k'ik'am a kanta, ko da taga ya fara saita yatsunta tasan me zaiyi, zillewa ta fara yi tana kokawar k'watar hannunta tana fad'in "Na daina na daina, yi hak'uri ba zan sake ba, dan Allah yatsuna fa zasu karye."

Ai kuwa bai kulata ba ya shiga lank'wasa yatsunta yana tausasu suna k'ara da k'arfin tsiya ba tare da sun shirya ba ji kake k'was k'was k'wask'was, saida ya gama ya saketa ya sunkuya ya kama na k'afa, billi ta shiga yi da k'afafunta tana fad'in "Na tuba Ammar na tuna na tuba wallahi."

Saida ya gama tas ya mik'e ya gyara zaman rigarshi ya sunkuya ya sumbaci kumcinta yace "Je t'aime."

Juyawa yayi zai fita ita ma ta mik'e ta nufi d'aki, saida ta kai k'ofar d'akin shima ya kai k'ofar fitar tace "Duk yarinyar daka kalla ko ka bata hannu kuka gaisa ban yafe maka ba Ammar."

Lumshe ido yayi ya juyo kamar mai jin bacci ya kalleta, gwalo ta masa tace "Naje na fad'a ka zo mana."

Gyara tsayuwa yayi yace "Ni kuma yau in na fita sai nayi budurwa, kinsan dai ba zan zauna dake kad'ai ba haka kawai, kamar yanda nake canja abinci na haka ma ina buk'atar canja wurin hutuna, dan haka zan samo yar yarinya yar cakwai da zan iya d'auka ba tare da nayi nishi ba, ke kuma a lokacin zaki san girman da nake da shi."

Hamna da taji kamar ya soketa da mashi da sauri ta manta da wajen b'uya ne ta nufa ta fito ta nufe shi gadan gadan tana shiryin kuka tana fad'in "Ammar Ammar, zo dan Allah muyi magana, zo na baka hak'uri."

Juyawa yayi cike da jin wata isa da izza wai shima akwai wanda yake wahalarwa akan son shi ya nufi
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment