Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

allurar da zaren."

D'ago kanshi tayi tace "A kaina ne dama kake kukan?"

Turo baki yayi yace "Ina sonki sosai Hamna, duk abinda zan miki da zai cutar dake ba nayi shi dagangan bane, b'acin rai ne ke saka ni, ki yafe min kinji."

Jawo kanshi tayi ta manna a tsakiyar mamanta tana shafa kanshi tana fad'in "Kayi hak'uri ai nice mai laifi ni ce bana jin maganarka, kuma duk horon da kake min ina jin dad'i dan hakan yana nuna min ka isa dani ne, sannan ina d'aukarshi a matsayin horo na yaya da k'anwarsa, dan haka ka daina zubar min da hawayenka na cancanci wannan hukuncin, ko ba komai kaga gobe zan kiyaye fito da b'acin rai a fili yayin da ka saka ni aiki."

D'ago ido yayi ya kalleta cike da k'aunarta yace "Yunwa nake ji fa."

Hannu tasa a rigarta tana fito da nononta tana fad'in "To dama me ye anfanin nonon da har yanzu yake min zuba? Saboda kai dama nake ta ajiyarshi."

*Iko sai Rabba*, k'ato ya daddage a k'afafun yarinyar sai tsotsar nono yake, rayuwa kenan ta musu dad'i, komawar da bata yi ba kenan wajen bikin nan sai dare, a lokacin da suka je har an zo d'aukar amarya, ko da ya sauketa yace "Ki kula min da kanki Hamna."

Kallonshi tayi tace "Kaima ka kula da kanka, amma ana zaka jirani har mu dawo sai mu koma gida ko?"

Saida ya kalli gabanshi yace "A'a, daga nan majalisa zan tafi, akwai wad'anda na gayyata d'aurin aure kuma ban gansu ba, to zan je ne na shukawa kowa rashin mutumci, sannan su biyani katin d'aurin aurena dana basu, tunda 'ya'yan k'ananan mutane ne su."

Kafin tayi magana ya ja mota ya wuce, da kallo ta bi motar tana mamakin abinda zaije yayi, bata ankara taji an daketa a baya da sauri ta juyo ta ga Sayyada, hararanta tayi tana fad'in "To dad'i miji sai yanzu kika dawo?"

Murmushi ta mata tace "Kin fad'i daidai, mijina miji ne da zan iya kiranshi namiji gaban zaratan maza."

Dariya tayi tace "Ba sai kin fad'a ba ai, kowa ya ganshi zai gane hakan, shi yasa ma nake nan har yanzu banyi aure ba shi nake jira yayi ta biyu dani."

Wata harara ta galla mata tace "Sayyada rufawa kanki asiri wallahi, mijin nawa? Ai kuwa sai dai ki mutu babu aure."

Dariya tayi tace "Au ba'a aure ke ya aure ki?"

Kallonta tayi sosai tace "K'addararsa ce ni babu yanda zaiyi, ke baki ga yer uwata ba ma aka raba shi da ita saboda ni."

Yanda Sayyada taga duk tayi ne yasa ta daddab'a kafad'arta tana fad'in "Sai hak'uri Hamna, ki ci gaba da mata addu'a."

Saida ta goge k'walla tace "Allah ya jik'anta da rahama."

"Ameen ya Allah." Ta fad'a kafin ta d'ora da "Haka naji mutane na fad'a, ashe kema kin fahimci haka."

A nutse ta kalleta tace "Sayyada kullum na kalli Ameera sai na ga fuskar yar uwata a fuskarta, kuma kullum na ga haka saina tuna rayuwata da ita, haka zalika ina tuna cewa tsananin rabon haihuwar dake tsakani na da yah Ammar ne ya amshi rayuwarta."

Jinjina kai tayi tace "Hakane, kinsan shi rabo ba'a rantsewa akan shi, da wani yayi k'ok'arin shiga tsakaninku to sai dai ya mutu."

Kama hannunta tayi tana fad'in "Muje ciki na samu zagina a wurin Ummy tun yanzu, yau nasan har uwata sai Ummy ta ci."

Cike da raha tace "Ai ko ni zan kama mata, kina matar uban d'aurin aure ace anyi biki babu ke."

Bushewa sukayi da dariya inda Hamna tace "Kinsan kuwa mutumin naki ya tafi majalisarsu wai zaiwa duk wanda bai zo d'aurin auren ba rashin mutunci, sannan su biyashi katin d'aurin auren daya raba musu."

Girgiza tayi tana dariya tace "Yer uwa wannan mijin naki ki dinga tofa masa lahaula kowace safiya, sannan ki dinga binshi da ayatul kursiyu dan bai rasa shafar mutanen b'oye."

Hararanta tayi tace "Sayyada bana son iskanci fa, mijin nawa?"

Cikin dariya tace "Ai ni labarinku ma zaki ban wallahi ina da marubuciyar da zata rubuta min shi."

Dafe k'irji tayi tace "Ni? Rufa min asiri, idan ya gani babbaka ni zaiyi da raina."

"Ba wani nan, ni zanje har gidan na same shi sai ya yarda ko baya so."

Dariya tayi tace "Gaki gashi ne ai kar tasan kar."

*Ammar* na zuwa duk ya tashi hankalin bayin Allah, kububuwa ya dinga musu ai duk sai ya ci ubansu tunda basu je d'aurin auren fari daya fara ba, sannan su tattara mishi katinshi su bashi inba haka ba zasu ga tsiya, su uku ne a wurin da basu je ba su dai hak'uri suke bashi amma da yake sauran da suka je suna zuga shi saiya dinga botsarewa, fad'i yake ai basu da mutumci ne shiyasa suka mishi haka, kenan ko auren Amreerarsa ya tashi haka zasu mishi? K'arshe dai yace a bashi katinshi kad'ai zai hak'ura, biyu daga ciki har motarsu suka duba basu ga katin ba suka ce bari suje gida su d'auko.

Rigarsu ya rik'e yace "Yo ni saida naje gida na d'auko muku? Anan na baku nima anan zaku ban kayana."

D'aya ne yace "To ai shine zamu d'auko maka a gidan ko."

"Ban yarda ba, a bani yanzu kawai hankali ya kwanta, ko a biyani da kud'i."

Wani daga zaune dake ta musu dariya ne yace "Eh su biyaka da kud'i, kati fa yanzu tsada yake, kuma irin wanda kayi ma na manyan mutane ne mai tsadar gaske, ya kai jaka goma fa wannan."

Kallonsu yayi yace "To kunji dai da kunnenku, dan haka a fiddo a bani kud'i na yanzu."

D'aya da abun ya dame ni ya fiddo jaka gomar ya mik'a mishi yana fad'in "Allah ya rabaka da wannan jaraba Ammar, wallahi ni daga matata ta farko har ta biyu babu wacce ta tab'a titseni irin haka akan abu, yo ni naga jaraba da zafi zafinta."

Saida ya soka jaka gomar aljihu yace "Yo suma sakarkaru ne matan basu san yanda zasu amshi kud'i a hannunka bane."

Haka dukansu suka biyashi kud'in katinsu kafin ya rabu dasu, mik'ewa yayi yana fad'in "Sai anjimanku to."

D'aya daga ciki ne yace "Allah raka taki gona."

Saida ya kwaso shoki ya yarfa mishi yace "Na dai ji, sai dai haushi wallahi."

Suna kallo ya tayar da mota yayi gaba, wajen wani mai soya doya da kw'wai da kaji ya tsaya, ya mik'a mishi abu amma kuma bai amshi komai ba ya wuce, saida suka ga ya bar wajen inda wani ya tintsire da dariya yace "Ammar jaraba, Ammar bala'i, Hamna na hak'uri da bawan Allahn nan."

Cikin wanda suka bashi kud'in ne yace "Ni yanzu kud'in nan daya raba ni dasu daya bar min kayana wallahi dana bawa amarya data nemi kud'in anko."

Wani ne yace "Saika bata wasu mana."

Babban aminin Ammar ne yace "Kar ma kace zaka mishi Allah ya isa, kud'inku bashi zai cisu ba, in kuma kayi gardama je ka tambayi Buharin kaji."

Tashi yayi kuwa da sauri yaje waben mai doyar Buhari, ko da ya ganshi yace "Mutumin yane?"

"Lafiya lau, wai Ammar da naga ya tsaya nan me yace maka?"

Cikin murmushi yace "Kud'i ne ya bayar yace duk magidancin da ya zo siyan abu a bashi kaza d'aya."

Cikin kafe shi da ido yace "Nawa ya baka?"

A tak'aice yace "Jaka talatin."

Juyowa yayi yana fad'in "Ta tabbata gaskiya ya fad'a, kud'inmu ne yayi sadaka dasu, to Allah ya bashi ladar da mu baki d'aya."


*Ameeeeeeeeen*.


*Alhamdulillah*
04/11/2020 ร  14:40 - Ummulkhairi: ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
*BADAK'ALA*
๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ _*AHALI NA*_๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ

*ALHAMDULILLAH Allah abin godiya, kamar jiya ne na fara BADAK'ALA yau gashi na kawo k'arshenshi cikin hukuncin mai duka, Allah ya gafarta kuraraina da zunubina, Allah yasa muyi tarayya daku a cikin ladar baki d'aya.*


๐Ÿ’ซโœจ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*๐ŸŒŸ
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_๐Ÿค

โ˜† *[ T.M.N.A]* โ˜† ๐Ÿ“–๐Ÿ–Š๏ธ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*FIN*

_80_


*Laraba* ce yau amma ko da ya fito zai tafi masallaci ya mik'ar da ita tsaye yace "D'auko hijabinki."

Kallonshi tayi tace "Hijabina kuma? Ina zamu je?"

Fuskar nan a had'e yace "Hijabinki nace ki d'auko, ko gani kike zan siyar dake ne?"

Girgiza kai tayi ta juya ta d'auko hijabin ta dawo, hannunta ya kama har sun kai k'ofa taga ba mota zasu shiga ba, gabanta ne ya shiga fad'uwa ta tsaya tace "Yallab'ai lafiya? Dan Allah ka fad'a min me ke faruwa? Ina zamu je yanzu da rana haka?"

Ba tare daya kalleta ba yace "Masallaci."

Da k'arfi tace "Masallaci? Yin me?"

Juyowa yayi ya kalleta yace "Me akeyi acan?"

Cikin tsoron kar ya zabga mata mari tace "Sallah."

"To ita zamu je muyi, yan uku nake so na haifa, ko jiya saida Hajia ta min gori wai mijinta kad'ai ke da wannan bajintar, ni kuma ina so na kafa mata tarihi."

Karantar yanayinshi ta shiga yi, indai bata amince ba zai ci ubanta, in kuma ta amince zata jawa kanta yan kallo, a k'arshe shi da kanshi zai iya mata hukunci yace ai ta shiga cikin maza, a hankali ta d'an girgiza kai a ranta tana fad'in "Ba fa yau na fara saninka ba Ammar, ka daina wahalar dani."

Saida ta dafa kafad'arshi cikin rarrashi da taushin murya tace "Duniyata, kayi hak'uri mana kai ka tafi yanzu, nima zanje nayi sallah nayi mana addu'a, insha Allahu ranar juma'a tare zamu tafi masallaci, amma yanzu kaga ni ba nik'ab gareni ba, kuma maganar gaskiya ina maka kishin kaina bana so kowa ya kalleni."

Yanda ta k'are maganar da shagwab'a saiya kalleta yana murmushi yace "Ja'ira kuma fa gaskiyarki, amma gaskiya Allah ya taimake ki dan da ace kin bini kuma naga ana kallonki...hummm da uwar mutum ta haifi wani yau."

Wani kallon ba ga irinta ba ta mishi kafin tace "Gaskiya kam, shiyasa nake kiyaye duk abinda zai tayar min da kishinka, ai bana so ka k'ara karya 'ya'yan mutane ba."

Dariya yayi yana kallonta yace "Yar banza kice dai ba kya son jaruminki ya sake kwana a gidan maza."

Dariya tayi tana fad'in "Ina zan so haka kai ma, Allah yanza ka sake tsokano rigima aka kamaka sai na zubar da cikin nan na jikina."

Da k'arfi ya juyo yana kallonta yace "Ciki Hamna? Yaushe ki kayi cikin ban sani ba?"

Har ta juya da niyyar guduwa ya rik'o hannunta, da k'arfi ya matseta ya d'aga rigarta yana d'an tausa cikinta, ko da ya kai ga mararta ya danna tayi wata yar k'ara mai d'an k'arfi tare da ja baya, sake rik'ota yayi yana kallon idonta yace "Yanzu kankana dan kar na samu yan ukun shine kika samu ciki da wuri?"

Cikin kallon kayi hak'uri tace "Allah ba haka bane, nima ina so ka samu."

Sakinta yayi yana fad'in "Uhm, zan dage n ci gaba da addu'a idan ma d'aya ne za'a mayar dashi uku insha Allah."

Da kallo ta bishi har ya fice, komawa tayi ita ma tana dariya yau wai za'a kaita masallaci.

Da yamm lafiya lau ya fita daga gidan, amma bai jima ba sai gashi ya dawo tunda ta hange shi ya fito daga mota yana kumfar baki ta kama jikinta, ko da ya shigo ciki taji yana ta masifa, zaune yayi k'asan carpet sai fad'a yake, kuma ba komai ya jawo masifar ba si ganin Jano da yayi a gari aka, shine ya tambaya yaushe aka fito dashi aka ce masa ai ya kusa shekara biyu da fitowa, shine fa ransa ya b'ace ya dawo gida ya saukewa mi tsotsai, tana gyaran akaifu sai dai ta saci kllonshi da taga zai kalleta tayi saurin d'auke kanta.

Yara ne suka shigo da gudu da ball d'insu suna bugawa, da gudu ta taresu a k'ofar d'akin, Shureim ta kama kunnenshi ta murd'e tace "Saurare ni, kaga ubanku nan ya dawo kuma ranshi a b'ace yake, wallahi ku koma can sam kuyi wasarku hankali kwance, in kuma kuna so jikinku yayi tsami to Bismillah."

Saida ya d'an lek'a y hangeshi zaune sai k'wafa yake yana cije leb'en k'asa sannan ya kalleta yace "Ummy wai me yasa Abba ya fiya rigima ne? Sai a b'ata masa rai a waje sai ya shigo nan mu ya balbalemu da masifa."

Da sauri ta rufe masa baki tace "Shiii, maza ku wuce."

Kallon Ahmad tayi da yanzu shim yake tare dasu tace "Ku wuce kaji yarona."

Da gudu duk suka nufi komawa sama, Ameera ta kalla tace "Ki wuce d'akinki bana son wasan nan da maza ayita tsalle tsalle."

Jinjina kai tayi ta kama hanya zata shiga Ammr ya fito yana fad'in "Ke dai baki san gaskiya ba a rayuwarki, yanzu waccen da kika koresu su ba yara bane?"

Kallonshi tayi a hankali tace "Amma ita macece ai."

"To sai akayi yaya?" Ya fad'a da alamar tijara kad'an yake jira, girgiza kai tayi tace "Komai, kawai dai ba zan bar yarinyata bane a cikinsu kowane lokaci."

Cikin d'aga murya yace "Kinfi so ku zauna kullum kina koya mata kinibibi ko?"

Wani kallo ta masa tace "Yan uwa fa shida gareta kuma duk maza, idan ban jata a jikina ba ya kake so na mata to? Zata zauna tana fad'a musu damuwarta ne su?"

Juyawa tayi ta kama hannunta suka shige ciki ta tura ta d'akinta. Kallon juna sukayi shi da Shureim da ko da yaga ya fito ya tsaya, ido ciki ido yake kallonshi babu rusunawa, shi ko a abokanshi yana wuya yag wanda suke kallon juna haka bare uwarsu, amma ga babban d'anshi na kallon idonshi kamar yanda shima yake kallon kowa a haka, hararanshi yayi yace "Kai kuma lafiyar kallona?"

Me zaiyi sai kawai ya jawo hannunshi suna gaisawa a dole yana dariya yana fad'in "Haba Abba rabu da su dan Allah, wallahi in kana masifa ba kya kyau, yi dariya mana."

Kallon yaron yayi sosai, in yana *masifa* baya kyau? Shine d'ansa ke fad'a masa haka? Lallai *Ammar* d'in da Hajia ke addua'r kar a samu gashi za'a samu.

K'ok'arin k'watar hannunshi ya shiga yi yana fad'in "Kai d'an uwarka sake ni, tsaranka ne ni."

Rik'e hannun yayi gam yana fad'in "Abba ni fa abokinka ne, fad'a min meye damuwar dan Allah."

Fizgo hannunshi yayi yana fad'in "Je ka tambayi uwarka mana."

Kallonshi yayi yace "Abba wai me yasa ita Ummy sai tace abbanku? Amma kai sai ka dinga cewa uwarmu uwarmu?"

Shima kallonshi yayi yace "Bari to zan ma uwar taku kishiya, kaga sain dinga cewa auntynku."

Da sauri yayi tsalle ya mak'ale a wuyanshi yana fad'in "A'a wallahi Abba bari wannan magana ma, karna saukewa yarinya kafad'a."

Dariya Ammar ya shiga yi dan yasan a bakinshi yaji kalmar sauke kafad'ar nan, lallai iko sai Allah, yana mak'ale a wuyanshi ya shiga falon dashi yana fad'in "Ke zo ki min tsakani da yaron nan naki, kinga dai kin lalata shi nema yake y zama wani iri."

Wani kallo ta masa tace "Kai da kan irin hka way rabak da Abba? Dubarun zama dashi kawai zaka koya kaima, dan ba lallai kayi hak'uri kamar yanda su Abba sukayi ba."

Zaune yayi dashi suna hira da k'yak'yata dariya, duk abinda Ammar ya fad'a Shureim na da amsa ko abin cewa akai shima, baya waske mishi saiya taroshi, basira fikira da zalak'a da kuma wayo, rashin kunyar jarabar da kwatirar duk babu abinda ya rago daga ubanshi, ita kam fatanta bai wuce su jashi a jikinsu ba su raka shi da addu'a, dan ranar mai zuwa tana musu wankin kaya duk sati ya kalla ido cikin ido yace "Habbi ki dinga wanka dan Allah ko kya samu bazawari kema."

Ce mishi tayi "To wani bazawari nake nema bayan gaka anan?"

Wata dariya ya mata yace "Haba Hajia Habbi, yo ni matar da zan aura ma ai yanzu ne ubanta ke k'uruciyarsa."

Sallah magriba kad'ai ta fitar dasu daga gidan basu dawo ba kuma har akayi isha'i, suna kan teburin cin abinci Sayyada ta shigo fa sallama, kai tsaye can ta nufa tana fad'in "Yara ku ce na zo a sa'a?"

Hamna ce ta kalleta tace "Su waye yaran?"

Kallonta tayi tace "Ku mana, ko ba yarana bane da jikokina anan?"

Duka yaran ne suka gaisheta ta amsa da sakin fuska, kallonta Ammar yayi yace "K'aramar uwa daga ina haka a daren nan? Kinsan fa bana son yawon nan saboda ina kishinki."

Saida ta kalli Hamna ta bashi hannu tana fad'in "Bamu gaisa ba ma d'an albarka."

Da sauri Hamna ta taso ta rik'e hannunshi tace "Aunty bana son iskanci fa, mijin nawa kuma a gabana?"

Rik'eta yayi gam a jikinshi ya mik'a mata hannun yana fad'in "Allah sai mun gaisa sai dai ki mutu."

Suna gaisawa Hamna ta kalleta sanda take jan kujera ta zauna tace "Allah Aunty idan kika ci amanata saina kasheki a garin nan."

Dariya tayi sanda take d'aukar plate zata zuba abinci tana fad'in "Kya kasheni bayan na haifa masa yan uku, ko d'ana?"

Ta fad'a tana kallonshi, gyara zama yayi yace "Ai ko da sai na baki kyautar kankana idan kika haifa min yan uku."

Hararanshi tayi tace "Ni ko kuma kankanar ta gasken?"

Dariya yayi yace "Yo ai kece ta gasken waccen yanzu bogi ce, ke yaushe rabonki da kiga ina shanta?"

Shiru tayi dan kar ya b'aro musu kunya a gaban yara, Shureim ne ya kalleta yace "Kakanmu amma dai da yunwa kika shigo gidan nan ko?"

Kasancewarshi babban d'a yasa Ammar yace ya dinga zama kujerar tsakiya dake fuskantar tashi kujerar, kuma ko bayana nan babu mai zamanta sai shi, dak'uwa ya masa yana fad'in "Kai uwar tawa zaka ma buru-uba? To da d'anta bai nemo ba ku kanku zaku ci ne."

Kallonshi tayi tana murmushi tace "Fad'a masa dai d'ana, ni ai bana da lokacinshi."

Murmushi Shureim yayi yace "Gashi kuwa Abba maman nan taka ta iya aika loma baki."

Kallonshi Hamna tayi kallon ka shiga taitaiyinka fa, saida ya sunkuyar da kai yace "Yi hak'uri Ummy na daina."

Ammar na kallonsu saiya ga wannan sak rayuwarsa ta baya ce zata sake maimaituwa kanshi da kuma d'ansa, dan haka dole ya takawa abun birki tun yanzu, duk da yana so 'ya'yanshi su biyoshi amma fa ba'a komai ba, dan ba zai so suyi wasu halaye nashi ba.

Saida suka gama cin abincin yaran suka hau sama inda Hamna tace zata same su suyi karatu, kallon Sayyada yayi yace "Amma dai k'aramar uwa gani na kika zo ko?"

Cikin murmushi tace "Eh mana kai da kasan komai d'an albarka."

Wani kallo ya mata yace "Samari babu kyauta yan mata babu kud'i, hakane ko?"

Da sauri ta kalleshi tace "Wallahi kamar ka sani kuwa, nifa al'amarin mazan nan na bani mamaki."

Kallon Hamna yayi yace "Kinga kakana nan ta mayar dani kamar katinta na kud'i, sai dai tace kawo, kawo, kawo kullum a haka."

Ba tare data kalleshi ba tace "To idan bance kawo ba wa zan ce wa, ka hanani fita inda zan samu kud'in dole ka zama katina ai."

Gwalo ya mata yana fad'in "Hanjin doguwa ce kike ci ta cikin ruwa."

Ita ma gwalon ta masa tace "In ma dai ta cikin k'asa ce na ci, mu ai haram d'in ita ke girman da k'assan jikinmu."

Kallon Sayyada yayi yace "Kina ji ko uwa, yarinyar nan fa yanzu yar daba ta zama."

Tab'e baki Sayyada tayi tace "Karka damu zata daina idan taga ka mata kishiya."

Haka dai sukayi hirarsu cikin raha kafin ta mik'e zata koma, jaka sha biyar ya bata yace ta shiga taxi canji saita ci goro, godiya ta masa ta fita ya rakata har k'ofar gidan tare da Hamna, har zai bi bayanta Hamna ta rik'o rigarshi tana fad'in "Ina kuma zaka tafi? Malam muje ciki."

Kallon Sayyada yayi yace "Uwa zan kiraki a waya muyi sirri, yanzu d'iyar nan tafi k'arfina."


*Bayan sati biyu*

Tun jiya dai taga kai da kawonshi ya k'aru sai kaya kaya yake, yau kuma bata san me ya faru ba tun a waya dai taji yana ta fad'anshi, zaune yake kan teburin cin abinci yana daddana wayarshi yana ta sababi kuma, ita dai jera mishi abincin ta shiga yi da duk abinda yake buk'ata k'ala ba tace mishi ba, zuba mishi tayi ta aje mishi gabanshi ta zauna kusa dashi dan ta saba tana kallon tv daga nan.

Kallonta yayi ya ga kenan ma babu ruwanta da damuwarsa ko? Cikin masifa yace "Nagode Hamna, dan ki nuna ni mahaukaci ne shine kika aje min abinci wato ina ci ina fad'a ko? Ki ma tambaye ni lafiya abun ya gagara sai ki zuba min ido kina kallo? To nagode."

A hankali ta juyo ta kalleshi, yanzu da tace yi hak'uri yace kuma ta ci uwarta ita da hak'urin, sake juya kanta tayi bata ce mishi uffan ba, a hassale ya sake kallonta yace "Ah yayi daidai, yanzu kuma baki da lokaci na ko? Yayi kyau Hamna ki ci gaba da wulak'anta ni son ranki."

Mik'ewa tayi ta kalleshi tace "Na d'auke abincin ne har ka gama saboda kar ya huce?"

Wani kallo ya mata irin yana so yayi magana amma baisan me zai ce ba, d'auke kanshi kawai yayi daga gareta yana datse leb'enshi dake rawa rawa tsabar fitina bai kuma samu abokin yi ba, juyawa tayi zata shiga d'akinta yace "Ke."

Juyowa tayi ta dawo ta tsaya, kallonta yayi yace "Bani ruwa nasha mak'oshi na ya bushe."

Cikin kwanciyar hankali ta tsiyaya masa ruwa ta mik'a masa, karb'a yayi yasha ya aje kofin ya kalleta yace "Mak'ogwaro ya fara ciwo wallahi."

Cikin nutsuwa tace "Idan baka kiyayi saurin hawan nan ba zaka jawa kanka matsala."

Yana ci gaba da kallonta yace "Wai yanzu nan fad'a gareni sosai? To ni ina na samo wannan bak'ar zuciya?"

Murmushi kawai tayi tace "Ina ma zakayi koyi da Alhaji, da ka zama mafi dacen rayuwa wallahi."

A k'ufule yace "Ke fito fili ki ce Ammar kai masifaffe ne kai mafad'aci kai jarababbe ne, anje anyi d'in to inba tab'aka akayi ba ai haka kawai ba kayi fad'a ba."

Juyawa tayi ta bar masa wurin dan ta lura da tsiya ne take so ya jata ta biye masa k'arshe ya turmusheta kuma ya d'inketa da kanshi, sauk'inta d'aya ma yanzu ciki dake gareta bai cika mata wannan hawan k'awarar ba.

Ko da ya ga zata shige d'aki ya d'auki cokalin abinci yana bubbuga teburin yana fad'in "Yeeee, ku dubi matar dake kallon mijinta masifaffe, an daiji kunya wallahi, kuma sai nayi mata uku a lokaci d'aya naga wanda ya isa ya hana ni."

Ko juyowa ba tayi ba har ta shige tana jin shi yana ta sambatunshi, saida ya gama yayi wanka ya shirya zai fita ya same ta a d'akin, bai kai ga mata magana ba kuma wayarshi tayi k'ara, yana dubawa ya ga Sayyada ce, tun ranar data zo ya kirata sukayi magana kan ranar haihuwar Hamna da zata zagayo yace yana so ya shirya mata party a gida, shi kuma yana so ya mata bazata shiyasa ko da ya ga kiran saiya d'auka yace "Oui zan sake kira idan na fita."

*Mata muke fa, kowane yare na maza ganeshi muke cikin sauk'i*

Daga jin yace zan kira bai ce zan kiraka ba kenan ba namiji bane, sai kuwa Hamna ta sauko daga kan gadon tayi kafar da wayar ta d'ora a kunne tana fad'in "Hello! Hello."

Fizge wayar yayi yana fad'in "Ke me yake damunki ne?"

Cikin d'aga murya tace "Abinda yake damunka, Ammar amana ta kake ci? Wace yar iska ce ke kiranka har cikin gida?"

A hassale shima yace "Wai ke kullum sai ki ce yar iska, to duk matan duniya yan iska ne? Ke ma fa macece saiki dinga kiransu da yan iska?"

Cikin b'acin rai tace "Saboda yar iska ce kawai zata kula min miji."

Kallonta yayi yace "Fito kai tsaye ki ce nine d'an iskan mana, idan ban kulasu zasu kulani ne? Kinga kenan nine kike so ki zaga dama."

Wayarshi tasa hannu zata fizgo tana fad'in "Na ga wayar to."

Hannu ya d'aga kamar zai mareta yana fad'in "Idan ban mareki ba Hamna kice Allah ya tsine min, ke bari gani ina k'yale ki fa."

"To ka da ka k'yale ni d'in ka kashe ni."

Zaune tayi kan gadon ta fashe da kuka tana dafe cikinta tana fad'in "Daga

Please Login or Register in order to submit comment