Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sarrafa dukiyar yanda ya kamata, sai Allah yayi wa Suley baiwa ta nasibi ta yanda duk abinda ya tab'a yakan hauhawa, cikin wata *uku* sai gashi shi kanshi alghabit na mamakin yanda dukiyar take bunk'asa, sai kawai ya sake yarda da shi ta yanda wata ranar *alhamis* ya shirya yace wa mutanen gidan zaiyi wata yar gajeriyar tafiya ya dawo, fatan alkairi suka mishi amma babu wanda tunaninshi ya bashi wani abu.

Sam Suley baya dawowa idan ya fita sai yamma, amma a ranar mantuwar da yayi tasa shi dawowa gidan lokacin da bai kamata, bai samu kowa a tsakar gidan ba dan haka ya shiga d'akin shi dake farkon shiga gidan, ya d'auko sak'on ya fito ya rufe d'aki zai juya kenan yaji sauti kamar kukan Zeeya'atu, A hankali ya dawo ya d'an daga k'afafun shi ya lek'o ta katangar data mishi shamaki da nasu d'akunan, ashe ciki ne da ita mahaifiyarta kuma ta amso mata maganin gargajiya dan cikin ya zube, ganin jini duk ya b'ata mata jiki ga bala'in kukan da take uwar na k'ok'arin shigar da ita d'aki yasa shi sukwanowa da nufin taimaka musu, yana daf da isa wurin su basu san da shi ba mahaifiyarta tace a harshen buzanci "Dangana mana Zeeya, ke da kin samu ma cikin zai zube."

Duk da bai iya komai a hausarsu ba amma yana jin d'aid'ai, a cikin hakane ma ya gane ta ambaci sunan ciki, da kuma zubewa amma sauran kam baiji komai ba sai dai kasancewar shi matashi mai matuk'ar basira da d'aukar duk abinda yaji yasa ya hardace kalaman data fad'a a buzancin, juyowa yayi ya fita ya barsu nan, yaje kasuwa ya kai sak'on yana cin abincinshi na rana tare da wani shi ma yaron Alghabit ne, da k'yar yaron ya fahimci abinda suley ya fad'a mishi yace yana son sanin fassarar , haka dai ya had'a haussar da k'yar ya fad'a mishi abinda ake nufi, sosai wannan al'amari ya girgiza shi ya kuma yi niyyar fad'awa mai gidanshi.

*K'addara ta riga fata*

Ko da ya samu alghabit dan sanar dashi sai ya katseshi tare da cewa ya kira mishi liman, bayan sun dawo tare da liman ya kira Zaha da Zeeya, bud'ar bakin Alghabit shine ya baiwa Suley 'yarshi Zeeya'atu wacce yafi so da k'auna, kuma baya buk'atar komai daga gare shi sadaki ma shine zai biya a matsayinshi na uban Suley, da sauri Suley ya kalleshi gabanshi na tsananta bugawa, juyawa yayi a hankali ya kalli Zeeya wacce take jin kamar ta mutu tsabar bak'in ciki, amma son nuna ita saliha ce yasa ko d'agowa ba tayi ba, zaha kuma kuma ba tace bata ji dad'i ba ba tace taji dad'i ba, kowa da abinda yake tunanin a zuciyarshi har Alghabit ya katsesu da cewa zai basu gidan da zasu zauna kuma gidan ya mallakawa Suley halak malak, sannan ya k'ara da cewa ya ware mishi jari mai yawa da zai tsaya da k'afar shi shima, wannan abun ne yasa Suley yin shiru ya karb'i auren Zeeya, gashi kuma Alghabit yace za'a d'aura auren juma'a ne ba b'ata lokaci.

*Allah ka gafarta mana.*
10/06/2020 Γ  12:07 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*BADAK'ALA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ _*AHALI NA*_πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦

πŸ‡³πŸ‡ͺ *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_13_


Lafiya lau Suley ya zo maradi kuma wannan karan tafiyar tashi tayi goshi, domin kuwa da idonshi yaga k'anwar shi da irin mummunar rayuwar da take, wacce a lokacin take d'auke da yaronta Labaran daya ke da shekara d'aya da haihuwa, wani ikon ubangiji cikin sauk'i Suley ya shawo kanta suka dawo gida tare, amma bata yarda ta biyo shi gidan mahaifinsu ba saida ya tabbatar mata da yana da kud'i zai siye musu gida su zauna tare saiya kawo iyalinshi, kasancewar lokacin akwai albarkar rayuwa yasa ya siye lafiyayyen gida kuma a farashi mai sauk'i, gyara yasa aka ma gidan sosai tare da ware d'akuna uku, nashi, na Zeeya, na Husseina, saida aka gama gyaran gidan Husseina ta tare a ciki sannan ya juya ya koma agadez dan sanar da mutanen can halin da ake ciki tunda ba waya ke akwai ba a lokacin, nan Husseina ta ci gaba da zama a gidan tana jiran dawowarshi, babu wani abu da bai bar mata ba duk dan tsoron karta sake sub'uce musu, wanda wannan zaman da tayi kuma mutane aka sake d'ora mata ido, dan dama gidan daya siye ba nesa ne sosai da gidan nasu ba wanda yanzu daga Ramma sai Innusa a gidan da matanshi biyu, haka yaje gida lfy kuma tun a zuwanshi iyalinshi Zeeya ya fara yi wa magana akan komai, kuskuren da yayi shine sanar da ita da yayi halin da Husseina ke ciki tunda farkon abinda ya faru har k'arshe, sannan yace a matsayinshi n'a mijinta dole ta shirya su koma mahaifarshi tare.

Kamar dai yanda yasan zai faru hakane kuwa, domin direwa tayi tace Allah ya tsareta da komawa garinshi ta bar na ta garin, kwana hud'u ya d'auka yana lallab'ata kan ta shirya su tafi amma tana botsarewa, dan haka k'arshe ya samu iyayenta ya fad'a musu komai da ake ciki, Allah sarki dattijon arziki Alghabit, nan ya rufe ido duk da son da yake mata ya mata tatas tare da bata umarnin ta had'a kayanta su tafi, sannan yace Suley zai iya siyar da gidan daya bashi saiya k'ara ya ci gaba da kasuwancinshi, haka kuwa akayi sai dai hakan ya d'auke shi kusan wata d'aya kafin suka d'auko hanya kuma suka zo da izinin ubangiji.

Duk da a lokacin ana ganin yara 'yan biyu, amma ganin 'yan uku kam ba'a cika samu ba, dan haka wannan yara na Suley sai suka samu farin jini a cikin unguwarsu fiye da kima, gasu kuma dama sak mahaifiyarsu suka d'auka buzuwa jawur da su kuma tub'ur tub'ur, hakan yasa mutanen sintiri cikin gidan ana duba yaran wasu ma har uwar kallonta suke suna son tayi magana suji harshenta da hausarta ke da ban sha'awa da dariya, sai dai ba anan gizo yake sak'ar ba, tunda suka zo ta ga d'akin daya fitar ma da Husseina ma had'e yake da nata saita mayar da ita kamar kishiyarta, wani haushinta take ji tare da k'yamarta, ita ma Husseina a lokacin da sauran d'anyan kai na rayuwar da tayi saiya zama babu ruwanta da harkar matar yayan nata, dan haka babu mai shiga shirgin kowa, hatta yaranta Zeeya bata bari ko da rarrafe suje d'akin ta, suna dosa zata taro su tana habaici da bak'ak'en maganganu a harshenta na buzanci, Husseina kuma tunda ta fahimci yayanta ma zaman hak'uri yake da ita kuma kullum yana cewa tayi hak'uri da halin Zeeya'atu sai kawai take ba banza ajiyarta, duk da zamansu gida d'aya baisa ta d'aga mishi k'afa ba na salon rashin mutumci, zai kawo abinci mai rai da lafiya ta sarrafa amma idan ta gama sai tace bata dafa da shi ba sai ita sai 'ya'yanta, shi kuma sai yace yaji dad'i tunda ma an dafa da 'ya'yan nashi, maganar saduwa kam shi har ma ya manta rabon daya kusanceta, dan tun kafin su fahimci tana da ciki, yanzu kuma daya nuna mata buk'atar shi sai tace ai ina, bata sake shirya haihuwar wasu yaran ba, idan ya isheta da magiya saita dinga cewa wai ai da karuwa a gidan yaje ya biya kud'in shi mana ya samu nutsuwa, hakan yana k'ona masa rai sosai, da wannan rayuwa har ya saba da shan jar kanwa da lemun tsami, Husseina kuma ta fad'awa yer uwarta Hassana wacce ke gidan aurenta ita ma halin da d'an uwansu ke ciki, shawartarshi sukayi yayi aure, kuma bai watsa musu k'asa a ido ba, sai dai Allah ya hukunta Zeeya ita ce matarshi ta har abada a duniya, watak'ila tanadin da ubangiji ya mishi ne mai girma a lahira, shiyasa duk yarinyar daya nema maganar bata zuwa ko ina sai a barta, harya gaji yace ya hak'ura ba zai zama kamar mane-min mata ba kullum a hanyar zuwa gidan yan mata, mutane kuma da 'yan uwa sun alak'anta hakan da Zeeya wacce take kallonsu tace eh tabbas ita ce, ba zai tab'a had'a ta da wata mata a duniya ba, kuma har ga Allah babu boka babu malam a lamarinta, kawai tana tauna tsakuwa ne dan aya taji tsoro, k'iyayyar Husseina ta sake hudawa ta shiga zuciyar Zeeya a sanda duk in ta k'i bashi abinci ita take bashi, ya zamana ma harda rana ita ke dafawa tana zuwa kasuwa da kanta tana kai mishi, hakan yasa take ganin ba tada maraba da kishiyarta, saidai duk masifar da take daga Suley har Husseina babu mai tanka mata.

Shekaru na ja duniya ana sake ci gaba zamani na k'ara shigowa, kai ya waye ta yanda kowane yaro akan saka shi makaranta dan yak'ar jahilci, sai dai ga wanda kan nasa bai waye ba kawai, a lokacin ana shiga ajin farko da shekara bakwai, haka Suley ya had'a duka yaran harda Labaran ma daya d'an fisu da watanni aka kaisu makaranta aka saka, takaici kamar zai kasheta dan bata so hakan ba, shiyasa har yaran saida suka shiga uku, dan dukansu take sosai tana cewa babu su babu d'an karuwar nan, amma abinka ga yaro yanzu yanzu ne zata sake ganin sun had'e wuri d'aya, musamman ma Hussein da yafi sauran zuciya, tana dukanshi zai koma bakin k'ofa yace anje anyi, shi kuma Labaran yaran sun shiga ranshi sosai, suna matuk'ar birgeshi sosai sosai, yana mamakin ganinsu su uku duk iri d'aya, haka zai saka su gaba ya tab'a hancin wannan ya duba yatsunsu ya ga kala d'aya, yace suyi dariya ya ga iri d'aya wannan yasa yake k'aunarsu sosai, haka suke zuwa makarantarsu tare suna dawowa, wani hukunci na Allah kuma sai Labaran ya zab'i zama kamar Suley ma'ana d'an kasuwa, cewa yake shi zai dinga binshi kasuwa ya daina zuwa makaranta, amma Suley yace yaje yayi karatu da hakane zai zama d'an kasuwa mai ilimi ba jahili ba, Hassan shima da abinda yake son zama, domin yaro ne mai son k'irk'irar abu da kanshi, haka ma Hussein yana son ya ga ya zama matuk'in jirgin sama wanda a lokacin idan ya wuce zakaga har babba ma ya d'aga kai sama ya kalla, Gambo kuma tunda ya samu Suley wata rana yana shan lemun tsami ya tambaya shi dalili yace cikinshi kawai ke ciwo, sai ya d'auri niyyar zama babban likita danya warkar da mahaifinshi, amma sakamakon wani abu daya shigo ya gifta ya musu shamaki da cikar burinsu wanda zasu iya kiranshi da k'addararsu sai kowa ya zama abinda bashi yake so ya zama ba, hakan kuma ya faru ne sanadiyar jiji da kan uwarsu da kuma son cika nata burin.

Innusa yayan Suley ne ya kwanta rashin lafiya mai tsanani, Suley na shiga gidan ya ganshi sai dai baya samun wani sakin fuska daga kan Ramma har shi Innusa, domin kuwa suna matuk'ar jin zafin ci gaban da yake samu a harkokinshi, dan Suley mutum ne mai k'wazo, duk abinda yasan zai samu riba a kai to ya kan siyoshi ya siyar, ya zama d'an kasuwa da ake ji da shi a wannan lokacin, sannan matarshi da suke gani buzuwa ce wanda a lokacin sun san auren buzuwa *jidali* ne kamar yanda wani mawak'i ya fad'a, har yan uku yaje dasu sun ga baffan nasu har Gambo yana cewa idan ya zama likita zai bashi magani ya warke, Zeeya ce bata je ba dan haka Suley yace taje ta dubashi, kunsan dai halin kayan gidan Suley sai kuwa tace babu inda zata je, wannan karan bud'e mata ido yayi yace wallahi ko a kai ne saiya d'auketa, hakan ne yasa ta shiryawa suka tafi tare da dare, wata atamfa ce a jikinta wacce a wannan zamani sai wane da wane mai sunan *ABC* a jikinta, hak'ik'a tasan mijinta namiji ne na gaske, dan duk abinda zai shigo dashi garin nan komai tsadarshi saiya fara kawo mata shi kafin ya fara siyarwa a gari, d'inkin riga da zane ne aka mata wacce rigar aka mata tattara da robo take ja sosai, kallabin daya kamata ta d'aura shi ta d'aura a k'ugu (wanda kowa yasan a zamanin iyayenmu da kakaninmu wannan ba wani abu bane dan mace ta fita kai sake, musamman idan aka ce ma anyiwa kan gyara), dama kuma ba kasafai aka cika saka gyale ba, sai dai a yafa zanin atamfar a mazaunin gyalen, maimakon ta d'ora zanin ta rufe kanta sai kawai ta ninkeshi gida biyu ta d'ora saman kafad'a, takalminta ta saka bak'ak'e k'afa ciki masu tudu sosai, inda kuma kanta ya ci uban gyara (coiffure) sai k'amshi yake da walk'iya, a haka fa suka jero suka zo har gidan duk da babu nisa, tunda suka shigo matan gidan da yara ke kallonta, hak'ik'a fa ta had'u sosai, sai dai bak'in ciki kawai da hassada ya hanaka fad'an hakan, Suley kawai ke gaisawa da su suna amsawa sama sama yana tambayar mai jiki, saida ya gama tsaf kafin Zeeya ta kalli Ramma cikin ido tace "Ya mai jikin?"

Ita ma kamar yanda ta tambaya haka ta mayar mata da "Mai jiki da sauk'i."

K'ala ba tace ba dan ita ma ba k'aunar su take ba kamar yanda basa k'aunar ta da kuma mijinta da yaranta, tun a labarin daya bata da kuma yanda yanzu suke zaune anan shekara kusan tara kenan ta fahimci haka, ita kuma duk wanda baya k'aunar mijinta da zuri'arta ita ce baya so, dan ita fa tana mugun bala'in son Suley, kawai dai tuna yanda aurensu ya kasance ne da irin zaman da sukayi yasa take jin ba zata iya neman sulhu ba ko ta kyautata mishi, mik'ewa sukayi zasu tafi tana gaba Suley ya ciro kud'i masu yawa ya aje gaban shinfid'ar Innusa yace a siya mishi magani, kullum idan ya zo ya bayar suna karb'a, amma yau Innusa daya kalli matar Suley ya ga ta take nashi matan har biyu, ga uban shirin da tayi sai ranshi ya b'ace, d'aukar kud'in yayi ya watso mishi yana fad'in "D'auki tsiyarka bana so, da can kai kake siya min maganin, ni zaka wa birgar mata, to bana son alfarmarka, dan wannan kud'in ganinsu nake kamar alfarma ce daga gareka, ni kuma duk wata alfarma da zata fito daga wajenka bana buk'atar ta a gidan duniyar nan, Suley babu ni babu kai wallahi na tsaneka."

Zeeya da tunda ya fara magana ta dawo ta tsaya take kallonshi , kallon Suley tayi taga sai doka murmushi take yana girgiza kai, a hankali yace "Allah ya baka lafiya kai dai, nasan zafin ciwo ne."

Haushi ne yasa taji kamar ta mare shi, dan haka ita ta kalli Innusa tace "Ka ce baka son alfarma kowace iri ce indai daga *Suleyy* ta fito?"

Kallonta Suley yayi saboda wani bala'in dad'i da yaji sunanshi yayi a bakinta, bai tab'a jin sunan cikin nutsuwa ba kamar yau, Innusa ne yace "Eh haka nace, ke ba tashi ma kaf zuri'ar shi da zuri'ata ba ma buk'ata, kuma ko bayan raina ban lamunce wani daga cikin tsatsona ya nemi alfarma ko taimakon zuri'ar Suley ba."

Murmushi tayi tace "Ni kuma Zeeya'atu muddin ina numfashi a doran k'asa sai na saka neman alfarmar Suley, idan haka bata faru ba to ka sani zuri'ar ka zata nemi taimakon zuri'ar Suley da ikon Allah, ka rubuta wannan ka aje ka kuma d'auka yanzu fad'an tsakani na da kai ne ba da mijina ba, dan shi yafi k'arfin ajinka yanzu."

Tana fad'a ta juya ta kama hannun Suley kamar yaro suka fita, kallonta kawai yake yana mamakinta, shin abinda aka mishi ne ya b'ata mata rai? To meyasa? Saboda tana sona? To meyasa bata nuna min soyayyar? Da haka suka k'arasa gida har ciki d'aki kafin ta saki hannunshi, ganin kallon da yake mata yasa ta fara cire shirin jikinta dan ta rage ma kanta nauyi, Suley na ganin haka saiya durmiya da ita duniyar maji dad'i daya jima har ya manta rabon da yaje can d'in, ita kanta fa ta gane tayi kewarshi sosai, *wannan rana*, *wannan dare*, shine ya shiga cikin tarihin rayuwar aurensu da ba zasu tab'a mantawa ba, kwana sukayi suna fad'awa juna kalamai masu taushi, kwana sukayi suna gajiyar da junansu da nuna yanda sukayi kewar juna, yan uku ma sai d'akin Husseina suka kwana da sukaji iyayen na su sun k'i bud'e musu k'ofa.

*Abu* kamar ya canza ashe ba haka bane, dan tunda gari ya waye Suley ya fahimci hakan, har yanzu dai ba wata girmamawa tsakaninsu, sai dai duk wannan billin rashin mutumcin da d'aga mishi murya ta daina, abinci ma yanzu har na safiya kawo mishi take ko ta aika cikin yaran wani ya kai mishi, idan an kwana biyu kuma ta kan ziyarce shi har d'akin shi ya d'an samu nutsuwa, kuma duk da haka tana nan tana tunanin hanyar da zata saka Innusa neman alfarma ko taimako wata rana, tana ji a jikinta zamani zai zo da komai zai zama ko dai d'an kud'i ko kuma alfarma, da wannan harta samu tsayayyar magana ta kuma tsaya a kanta.

A cikin shekaru *goma sha biyu* Zeeya bata sake haihuwa ba sai b'ari data dinga yi har sau biyar, hakan yasa tace ma Suley ta hak'ura da haihuwar kawai Allah ya raya mata ukun ma, tuni kuma lokacin ta juya akalar burin kowa izuwa nata burin, tun farko data nuna ga aikin da take su suyi basuyi mata musu ba, dan dama ita ce mala'ikan gidan mai horo, dan Abbansu babu ruwanshi tsakaninsu dashi wasa da dariya ne, amma ita babu wannan sai had'e fuska kamar sojiya,πŸ˜‚ Hassan ya duk'ufa nashi karatun inda yana kammalawa kafin ya samu aiki tace ai dole yayi aure, har Suley yace mata da son samu ne a aurar dasu baki d'aya, amma gudun kar ya kawo mata zab'inshi wacce zata zo ta sauya mata ra'ayin yara daga yanda suke mata biyayya yasa ta k'i yarda, haka yaran suka nunawa mahaifinshi ya rabu da ita kawai zasu mata biyayya, kuma kullum dama idan ya so mata magana akan tsaurin da take musu su ke nuna babu komai, saiya zab'i yayi shiru dan kar yaran su fahimci akwai rashin jituwa tsakaninsu da har zai saka su dinga saka bakinsu a al'amarinsu, *Sa'ada* yar aminiyarta ce wacce ke Agadez ita ma, sanin babu ruwanta ita da yarinyar tana musu kallon kidahumai yasa ta nema mishi aurenta, duk ba'a b'ata lokaci ba akayi komai aka gama, kasancewar tana karatu yasa bayan auren aka nema mata gurbin karatu anan ta ci gaba, duk da babu soyayya tsakaninsu suna mutumta junansu da girmamawa, baifi wata d'aya da aurensu ba Allah ya bata cikin ' yan biyu, lokacin kuma Hussein ya dawo gida hutu shima aka fara maganar aure, sai dai tace bata ga yarinyar data dace da Hussein ba, tana buk'atar yarinya wacce bata da wayewa da zurfin ilimi ta yanda ba zata damu ko saka ma rayuwar d'an ta ido ba, sannan wacce bata da wani gata ta yanda ko ya daketa zai daki banza (πŸ˜‚) dan ta sanshi da zuciya, yana da kwana biyar da zuwa ya tuk'a Hajia da kanshi ya kaita bikin 'yar k'awarta a Zinder, to fa anan ta had'u da *Zeinabu* a cikin k'awayen amarya take, duk yanda ta so ta kasance haka take, bugu da k'ari iyayenta sun rasu tana hannun kakarta ne *Inna* wacce ta haifi Babanta, su ma dai ba'a d'auki lokaci ba aka fara shirye shirye, su suna ganin zasu shiga babban gida ne, dan wannan lokacin *Alhaji Suleymane Hassan Gaga* ya zama d'an kasuwa lamba d'aya wanda ya zama komai da ruwanka, kampanin buga ledoji, kampanin sarrafa pliwa da sukari, kampanin sarrafa duk wani abu daya shafi roba irinsu robobi, bokiti tabarma da takalma na roba, gidajen mai wanda lokacin basuyi yawa sosai ba, baya ga shaguna ba adadi, da kuma kampaninshi na buga atamfofin dake garin *Niamey* , ya dai zama kicima shima, dan haka suke cewa kakarsu ya yanke sak'a, *(kuna musu kallon biri suna muku kallon bishiyar hawa)*, lokacin da aka saka ne ya bawa Hussein damar yin tafiya kafin lokacin, duka wata biyu yayi sai suka zo Zinder za ayi *18 DΓ©cembre* anan, bayan an kammala ana ta shirye shiryen komawa Hajia tace dole ya kira Zeinabu yaje ya sameta su gaisa karya yarda ya bar garin nan basu ga juna ba, Hussein ya kira Zeinabu da yar wayarta yace ta zo su gaisa kafin ya wuce dan shi ko gidansu bai sani ba saita waya dama suke gaisawa, Inna da rawar k'afa ita ta tayata shiryawa aka fesa mata turaruka sannan ta tafi a taxi, haka taje compagnie wajenshi babu mai tunanin faruwar wani abu a cikinsu, turarukan data fesa yasa hankalin Hussein tashi, hakan ya ingizashi har yayi abinda bai tab'a yi ba, duk da yaga Zeinabu kuma bata wani birgeshi ba, amma hakan ya kawar da budurcinta a wannan ranar, duk da ta so bijire masa amma daya tuna mata shine zai aureta sai tayi shiru ita ma, a wannan tarraya ne aka samu cikin *Junaid*.

Ana gobe d'aurin aure Inna taga laulayin Zeinabu yayi yawa, tana dubata ta gane ciki ne da ita, ko da ta tambayeta wane shegen ne? Ta fad'a mata wanda zata aura saida ta sauke ajiyar zuciya, nan tasa ta kirashi a waya wai yazo, ba tare da shakku ba yace idan ya zo me zai mata? Inna dai da taga yaron fitananne ne ba zai zo ba sai kawai ta amshi wayar ta fad'a mishi komai tare da cewa ita zata sanar ma da iyayenshi, nan fa hankalinshi ya tashi dan ba zai ce k'arya bane, sulhu ya nema anan ne fa Inna tace zata rufa asiri amma dole ya biyata, nan tace tunda dama ba mataimaki gareta ba to ya d'auke mata abinci da sutura, ba musu ya amince da hakan inda washe gari aka d'aura aure sukayi gum da bakinsu.

Bayan aurensu da wata uku Sa'ada ta haihu kuma 'yan biyu, *Ammar* da *Amar*, Hajia na d'ora ido a kansu Amar ne yafi shiga ranta, tana kallonshi kawai taji kamar yaranta ne take kallo lokacin data haihu, Ammar kuma daya cika asibitin da kuka sai take ta mishi sharri wanda mutane ke dariya ana ganin na kaka da jika ne, to fa da irin wannan hantarar ta gina rashin jituwa tsakaninta da Ammar, iyayensu ma da suka gane tafi k'aunar Amar sai suka fi mayar da hankalinsu kanshi, indai suna gabanta duk abinda Ammar zaiyi sai sun hantareshi da zaginshi dan jin dad'in ta, Amar kuma baya laifi a wajensu dan ko bata gidan babu mai dukanshi, dan tsaf zata gurza maka rashin mutumci ko uban daya haife shi ne, a wannan lokacin cikin Zeinabu na wata hud'u, Husseina ma sai tace Labaran yayi aure dan tunda yasan ta hanyar da aka haifeshi ya mayar da hankalinshi kan kasuwanci harya tsaya da kafarshi, da k'yar ya samu yarinya mai nutsuwa da hankali wato *Soueiba*, amma data amince tana son shi tsaf ya fad'a mata tarihinshi bayan ta mishi alk'awarin ba zata gujeshi ba, haka tace taji ta gani kuma daga shi har mahaifiyarshi babu mai laifi, girma da mutumcin Suley da ake gani a gari yasa iyayenta basu wani zurfafa bincike ba suka bashi aurenta, dan dayawa d'auka suke Husseina matar Suley ce saboda har wannan lokacin miji bai samu ba, suma anyi aure lafiya lau lokacin kuma aka haifi Junaid, kuma suna da wata tara da aure ta haihu, bayan watanni ma Soueiba ta haifi Jibril.

*Bayan shekaru biyar* Gambo

Please Login or Register in order to submit comment