Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dad'in nan, kashe hasken yayi ya lek'o da kanshi ta gilashi yace "Sai na zo na d'auke ki ne dake da moton?"

Da sauri ta sauke hannunta ta kalleshi tana girgiza kai, gabanta ne ya fara fad'uwa inda jikinta na rawa ta kau ce mishi a hanya, da kallo ya bita a hankali ya furta " *Amna* kenan." (Wato ya gane wacece)

Jira take ya wuce ko ta samu ta fita amma taga baida niyyar haka, muryarshi taji yace "Ina zaki?"

Da tsoro fal a fuskarta da kuma muryarta tace "Hajiarsu Jibril ce ta aike ni shagon Ilu?"

Wani kallon babu wasa ya mata yace "Ki aje moton ki zo muje na kaiki."

Bud'e baki tayi cike da bayyanar tashin hankalin zatayi magana sai kuma ta tuna waye gabanta, ruf ta rufe bakinta ta d'an jinjina kai alamar to a zuciya kuma tana fad'in "Kin mutu Amna."

Komawa tayi ta aje moton ta dawo, yana kallon kowace gab'a ta jikinta harta bud'a gidan gaba zata shiga, zata zauna taga wani kallo da yake mata kamar na bansan iskanci, hakan yasa ta rufe k'ofar ta kama murfin baya zata shiga, a tsawace yace "Dan ubanki waye dreban naki? Ni ko uban wa?"

Da sauri ta rufe jiki harya fara rawa ta bud'e gaba ta zauna, yanda ya kafeta da ido yasa yake iya fahimtar yanda take sauke numfashinta kamar wacce tayi gudu, jin bai tayar da motar ba yasa ta d'an d'ago kai ta kalleshi.

Tana kallonshi ya fizgo d'an kwalinta ya jawo kanta ya matse a tsakiyar hammatarshi yasa kallabin ya fara darzar mata fuska yana fad'in "Bak'ar munafuka aiken Hajiar ne zakije sai kinyi kwalliya? Ko yau ma a matsayin kankanar kika fito daga gidan?"

Saida ya gama ya tureta ya jefa mata d'an kwalin, da k'yar ta bud'e idonta saboda tumurmusar da fuskarta tasha, d'aukar kallabin tayi ta d'ora akai a lokacin sun fara tafiya, babu mai magana su dai a haka suka isa shagon Ilu, fitowa tayi ta tunkari shiga shagon, Ammar dake kallonta ganin yanda rigar ta fito mata da surarta ga kuma wani namiji a cikin shagon shima yana siyayya hakanne yasa shi jin wani takaici, tsaki yayi ya daki sitiyarin motar yace "Uban wace ta fito a haka ma? Wato kankana zata koya miki ko?"

K'wafa yayi yana ci gaba da kallon yanda take murmushi suna gaisawa da wannan mutumin, wanda rabon ayi ne kawai yasa Amna gaishe shi ya amsa, ya gama siyayyarshi ya kalleta yace "Hajia sai anjima ko? Gashi zamu rabu bansan ko sunanki ba?"

Murmushi tayi tace "Allah sarki yaya na, suna na Amna."

Cike da zolaya yace "Amna zanyi mata ta biyu dake idan kin amince? Ko zan samu lambar wayarki?"

Jim ta d'anyi tana kallonshi hakan yasa ya mik'o mata wayarshi yace "Da gaske fa nake, ki taimaka ki saka min sai muyi magana a waya ko? Dan bai kamata muyi magana akan titi ba."

Ammar da tunda yaga hirar ta k'i k'arewa gashi dama tun jiya yake neman abokin masifa sai yaji kawai yarinyar ma ta raina shi, a fusace ya fito ya nufi shagon, kafin ta karb'i wayar Ammar yayi wuf da ita sai kuwa yayi cillin tsiya da ita akan titi, mutumin bai gama fahimtar meya faru ko zai faru ba sai kuwa yaji Ammar yayi sama da shi ya dasa a k'asa, kafin dai ya ankara da abinda ke faruwa Ammar ya fara kai mishi naushi a fuska yana fad'in " Kai kwarton ina ne? Daga ganin yarinya kawai sai yi mata magana, kasan wacece ita?"

Ledar dake rik'e a hannun mutumin wanda yanzun akayi fatali da ita Ammar ya jawo, hannu yasa ciki ya rarumo wata leda kamar balam-balam ya buga mishi a fuska, sai kuwa man gyad'ar dake cikin ledar ya tarwatse a jikinsu dukansu, Ilu dake ta k'ok'arin d'aga Ammar daga jikin mutumin da shi yake k'ok'arin ya tashi amma Ammar ya hanashi damar hakan, mutanen dake kusan nan ne suka sukwano da gudu suka zo rabo, da k'yar suka tayar dashi daga jikin mutumin shi ma ya tashi, fad'i yake "Matar tawa zaka wa iskanci? Qur'ani saina kashe ka."

Jin yana fad'in matarshi ce yasa mutanen ganin kamar waccen mutumin ne baya da gaskiya, dan haka suka jawo Ammar da k'yar suka turashi motar shi, Amna dake tsaye cikin shago har ta fara shashek'ar kuka wani ya kalleta yace "Dan Allah madame ki wuce ku tafi, ki samu ki kwantar masa da hankali, kuma ko da kunje gida kada ki biye masa, dan halin da yake ciki zai iya illataki."

A firgice ta sake kallon mutumin tana maimaita kalmar " *Illataki*." Tasan babu abinda zai hana ya illatatan kuwa, dan haka ta girgiza kai tace "A'a, ya tafi kawai zan zo a bayanshi."

Daga cikin mota Ammar yake iya fahimtar me Amna ke nufi, sake dantse leb'en shi na k'asa yayi bala'i kawai yake nema da mai yi, ganin bata da niyyar fitowa yasa shi fitowa daga cikin motar da k'arfin bala'i ya tunkari shagon, wannan mutumin da mutane suka zagayeshi har da Ilu mai shago saida gabanshi ya fad'i dan ya d'auka wurinshi ya koma, kai tsaye cikin shagon ya shiga, Amna na ganin haka ta durk'ushe ta had'e hannayenta tana fad'in "Ka dubi girman Allah y..ahhhhhh." Ta saki k'ara saboda jawo hannunta da yayi da k'arfi, saida ya bud'e motar ya wurgata ciki ya zagayo ya shiga, da wani irin bala'in gudu ya fizga wanda yasa hankalin mutane dayawa komawa kan motar, wasu tuni suka fara jin tausayin yarinyar dansun san wannan ta shiga uku.

Saida sukayi nisa inda babu mutane ya taka birki ya kalleta a matuk'ar zafafe ya daki k'irjin shi yace " Amna ni zaki rainawa wayo? Ni zaki wulak'anta a idon jama'a? A gaban ido na ki tsaya hira da wani har kina neman bashi lambarki, bayan kuma kinsan ke d'in *tawa*, tawa ce mallaki na, ko gani kikeyi waccen banzan zai fini iya hawa ruwa cikinki ne? Gani kike zai fini iya sukuwa a kanki kenan?"

Amna banda girgiza kai babu abinda takeyi, a fusace ya kwad'a mata marin da yasa jinta d'aukewa, ta dafe kunci kenan taji ya shak'o wuyanta da hannu biyu, cikin azaba ta zaro ido ta kama hannayen nashi da nata hannayen taa neman ya saketa ta numfasa, cikin k'aramin lokaci ta fara fafutukar neman numfashi dan ba k'aramar shak'a ya mata ba, shi kuma cikin hargagi ya kawo bakinshi daf da hancinta yace "Saurare ni da kyau Amna, ke da gangar jikin ki nawa ne, duk da akwai inda zuciyata tafi karkata, amma ki sani tunda kakarki tace ta bani ke wallahi kin zama tawan, saina moreki ko da baki son haka."

Wurgata yayi saida kanta ya bugu ga gilashin motar, k'asa tayi da kanta tana sauke numfashin wahala, jan motar yayi suka isa gida, yana paka mota ta fito da sauri ta nufi falon Hajia, ganin yanda kunkuminta ke juyawa ya k'ara tunzurashi, kenan shima waccen mutumin abinda ya gani kenan? Ai da sauri ya fito yana fad'in "Ke ke! Zo nan."

Tsayawa tayi ta kasa motsawa tana kallonshi wasu hawayen na zubowa, yana kawowa daf da ita ya kamo rigarta yace "Uban wa ma yace ki fito haka? Iyee! Wa yace ki fito haka kina tallar kanki?"

Shiru tayi sai sharar hawaye da take, haushi ne yasa shi ciro takalmanshi ya gaura mata a fuska, wata razananniyar k'ara ta saki ta dafe kunci, sake jibga mata shi yayi a baya hakan yasa ta zabura ta zube kwance a wurin, k'afa yasa ya fara harbinta yana fad'in "Wannan rigar data dace ki fita da ita ce? Ke bari kiji daga yau ba zaki sake fita daga gidan nan ba, kinji ni ko."

Jin kururuwar Amna yasa mutanen gidan fitowa suka kawo mata d'auki, ganin abinda ke faruwa yasa Ummy tahowa da gudu ta durk'usa ta rumgumo Amna, babu namiji ko d'aya a gidan sai yaran hakan yasa Ummy kallonshi cikin b'acin rai tace "...

*Addu'arku yan uwa.* 👏
22/06/2020 à 17:26 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*SANIN MASOYI*
_(sai Allah)_
*BAYA DA K'URA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

💞 _*MASOYA NA*_💕


_Bismillahir rahamanir rahim_

🇳🇪 *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_12_


Ma'aruf ne yace "Wai ke yaushe ne zaki fito da kud'in nan a raba kowa ya kama gabansa?"

Ba tare data kalleshi ba tace " Kana gaggawa ne da son samun naka kason?"

A d'an hassale yace "Ban gane? To idan ba'a raba ba uban kud'in zasuyi a account d'in? Kinga ki fito dasu kawai kowa ya d'auki nashi ya san inda dare ya masa."

Aje wayar tayi ta zaburo tace "To idan fa na k'i? Ai dai kasan kud'in a account d'ina aka saka ko? Kuma sai ni ce ke da damar cirewa? Dan haka ka bini a hankali har lokacin da naga dama sannan na fito dasu mu raba."

Shima tasowa yayi yace "Wallahi baki isa ba, ni zaki d'auka d'an iska, wato kinga kud'i kenan shine zaki nemi ki raina min hankali? To baki isa ba wallahi, kinsan ko k'arfi ne zansa na karb'a."

Da k'arfi tace "K'arfi? K'arfi fa kace? Wai kai ka ma san wahalar da nasha kafin a samu kud'in, kana nan zaune nasa kaina a had'ari wanda da sun gano ni me kake tunanin zai faru da ni? Haka na kwashe kwanaki a gidan ina tunanin abunyi har na cimma nasara, kasan ta yanda akayi na shawo kansa ne? Da k'yar ya kwanta dani shima bayan na ci maruka daga gareshi, haka ya shigeni babu imani ya sussuke ni, duk kai kana nan zaune kuma shine yanzu zaka wani bud'e min ido, to bari kaji da kyau tunda abun na ka ya zama iskanci, wallahi kud'in nan ko sisin kwabo ba zan baka a ciki ba, sai dai na maka alk'awarin zan karb'o maka ko million biyar ne ko goma a wurinshi, dan na fahimci baisan zafin neman kud'i ba."

Sai lokacin maganganun Meena suka fara dawo masa da tace ko ita Ma'arufa ta samu yanda zatayi ta cinye kud'in ita kad'ai to zatayi ne, dan haka shi ya mik'e ya karb'i kud'in inba haka ba zai zama d'an kallo, wani iska ya furzar daga bakinshi ya jinjina kai yace "Shikenan, ki samo min million goman, ke saiki rik'e waccen d'in."

A wulak'ance ta kalleshi tace "Ai na d'auka zakayi gardama ne?"

Murmushin mugunta yayi yace "Gardama tame kuma? Abinda ba kai ka tara ba."

Mik'ewa yayi zai fita yace "Yaushe kenan zan saka rai?"

A yamutse tace "Zuwa gobe zan masa magana, yanzun ma dan dare yayi ne."

Baice komai ba ya fita ya barta, daga nan kuma hotel d'in da Meena take ya zarce, tsaf ya fad'a mata komai, tab'e baki tayi tace "Ai dama na fad'a maka, yanzu kawai lambar account d'in nata zaka samo mana, ni inada mutanen arzik'i sosai a garin nan, zamu san yanda za'ayi a maka transfert d'in kud'in zuwa naka account d'in."

Kallonta yayi yace "Amma yaya zamuyi haka alhalin tana raye?"

Zaune tayi kan cinyarshi ta sagala hannunta ta bayan wuyanshi tace "Kalamanka suna so su nuna kamar ka d'au saiti? Ni kuma in hakane ina da maganin matsalarka."

Juyawa tayi bayanta ta d'auko jakarta ta bud'a ta d'auko wani k'wayar magani mai kamar ampicillin ta bashi tace "Kawai ya gyauraya a abun shan ta."

Karb'a yayi ba tare da tunanin komai ba kafin ya had'e bakinshi da na ta, suna lulawa nima na lulo nayi waje .

Abbas da kanshi ya samu magabatan Abdul ya sanar dasu za'a d'aura auren gobe bisa wani dalili mai k'arfi, su kuma cikin farin ciki suka amsa mishi da ba komai ai Abdul d'an shi ne, shi kanshi Abdul d'in farin ciki yayi saboda zai mallaki abar son shi, yayin da zazzab'i kuma ya rufe Raihan baiwar Allah, har likita ya zo ya dubata ya bata magani, tana kwance d'akin Sameera tana bacci, ita kuma Sameera shiryawa tayi cikin kayan baccinta taje bed d'in shi, tana shirin yin kwance yace "Idan ba damuwa ki koma d'akin ki mana?"

Da mamaki ta kalleshi tace "D'aki na kuma? Kana gari me zaisa mu raba shinfid'a?"

A k'ufule yace "Haka nake buk'ata, ina buk'atar kad'aici."

Matsawa tayi kan kujerar da yake zaune ta sunkuya ta kama hannunshi cikin magiya tace "Sir, dan Allah ka fad'a min meke damunka mana? Ni fa matarka ce, Sameera, ko ka manta ne? Idan ni nayi maka laifi dan Allah ka fad'a min saina baka hak'uri, idan kuma kana hushi dani ne kan maganar haihuwar da kake so, na amince ka bar hushin dani, muje sai ka min cikin mana na shirya d'auka, amma bana son hushinka wallahi."

Rintse ido yayi yana jin kamar ya k'ona kanshi yace "Bana jin zan sake haihuwa da ke."

Dam! Taji gabanta ya fad'i yayin da ta kafeshi da ido da alamar tambaya, da tsantsar mamaki tace "Baka son sake haihuwa da ni? Akan me? Me nayi maka da zafi haka? Abban mama na yaran da muka haifa fa? Yanzu har girman zunubin dana aikata ya kai ka fad'a min wai ba zaka sake haihuwa da ni ba?"

Cike da k'osawa yace "Dan Allah ki fitar min daga d'aki."

Had'e kukanta tayi tace "To zamu iya yin magana akan matsalar 'yarmu?"

A tak'aice yace "Ba zamu iya ba."

Kallon fuskarshi tayi tace " 'Yar mu ce fa? Girman laifin data aikata yasa har ka daki yarinyar da ko tsawa mai k'arfi baka tab'a mata ba, sannan ka ce zaka aurar da ita gobe, kana ganin hakan ya dace?"

A gajiye ya kalleta yace"Ya dace Meerah, please ki bar ni nasha iska mana."

Mik'ewa tayi jiki a sanyaye ta kalleshi tace "Sorry."

Juyawa tayi inda ya rintse ido matuk'ar tausayinta ne yaji ya mamaye shi, saida yaji ta rufe k'ofar d'akin ya juya ya kalli k'ofar wasu hawaye suka taho mishi yace "Sameera ba zan yarda na sake had'a jikina da na ki ba, nasan zan cutar dake a hakan, amma k'azamin jikina ba zai sake tab'a tsarkaken jikinki ba, Sam ki yafe min, ba zan iya fad'a miki komai ba, domin kuwa nasan a ranar ko baki kashe ni ba zaki cutar da kanki, ba zan bari ki kashe ni ba dan bana son ki shiga wuta dalilin banza iri na, ba kuma zan yarda ki cutar da kanki ba."

Tana shiga d'aki ta samu wayarta na ta kururuwa sarki Imran ne, d'auka tayi ko gaisawa basuyi ba ya fad'a mata abinda ke faruwa a masarauta.

*Basraba*

Bayan tafiyar Sameera sai kuwa waziri ya taso uwar d'aki gaba akan dole fa ayi auren nan da gaggawa, ya gama tsorata da recoding d'in da yayi tare da mata barazanar zai ce ita ta saka shi ya kashe takawa, nan fa jikinta ya d'auki rawa ta fara neman mafita, amma a k'arshe dai mafitar bata wuce tayi abinda yake so ba, nan ita ma ta tasa Imran gaba sai anyi aure nan kawai nan da kwana biyu, wanda yanzu ya kasance gobe za'a d'aura, Imran ya kira Abban Sameera amma yana hushi akan abinda ya faru yasa ya k'i d'aga kiranshi , dan haka ya kira Sameera dan ta fad'awa Abba akan ya zo ya dakatar da auren nan, shi bai ce ba zaiyi ba amma ba zaiyi aure ba kwana shida da rasuwar mahaifinshi, amma Sameera sai tace mishi kawai ya amince a d'aura dan a zauna lafiya, nan sukayi sallama kowa yaji da abinda ke damunshi.

*WASHE GARI*

Lafiya lau aka d'aura auren sarki Imran Musayyib Ali da matarshi ta farko *Safiyya Ahmad* da kuma mata ta biyu *Jawahir Ya'u* dukansu akan sadaki dubu hamsin hamsin, hankalin waziri ya kwanta kam dan yanzu ne burinshi zai cika, a wautar uwar d'aki ita ma tana ganin hankalinta ya kwanta tunda asirinta ya rufu yanzu, yayin da gimbiya Ameera tayi kuka sosai jin auren mijinta kamar a mafarki, tsawon lokaci ya d'auka yana rarrashinta da bata hak'uri da fad'a mata duk abinda ya faru, yayin da ake toya masa anan acan Abuja kuma ana toya wata masar ne.

*Abuja*

Kamar yanda Fadila ta samu labarin d'aurin auren Raihan a tsakiyar dare haka ita ma ta dokowa Abdul kira a dugun-dugun safiya, bayan ya d'auka ne ta fashe da kuka tana fad'a masa ita fa son shi take ya taimaka mata, cikin ruwan sanyi yake lallab'a ta yana bata hak'uri saboda akwai mutumci tsakaninsu, amma sai baud'ewa take tana fetsarewa, a k'arshe ma zuciya ce ta deb'eta tace "Yanzu kai ka d'auka zasu baka yarsu dan suna sonka ne? To ba gaskiya bane, soyayyar da suke nuna maka ta bogi ce yayin da a ransu babu hakan ko kad'an, sun d'auke ka kamar bawansu ne wanda suka siya da kud'i, Raihan ita ce rayuwarsu, hakan yasa suka tanadar mata kai dan rayuwar gidan aurenta ta mata dad'i kamar yanda suke so, a bayyane yake ai, inhar ka aureta ba zaka yarda ka muzguna mata ba ko ka mata ko da kallon banza, to wannan ne dalilinsu na son had'a ta da kai, amma a bad'ini suna maka kallon wanda ko mai aikin gidan yarsu baka kai."

Murmushi yayi mata yace "Idonki ne suka rufe har kike fad'in haka? To muje ma a hakanne, Fadila na amince zan auri Raihan, ai dama hallacin da iyayenta suka min bai kamata ace na harari ko da k'eyar Raihan ba bare gabanta."

Cikin fitar hayyaci tace "Shikenan ka aure ta mana, ita d'in ka d'auka sonka take? To kaji da kyau zan fad'a maka ko ba zaka yarda ba, basu yarda sun had'a wannan auren ba saida suka saka aka maka gwajin jini a b'oye ba tare da saninka ba kafin suka yarda ma da maganar aurenku, saboda basu so ka lak'awa yarinyarsu cutar da mahaifinka ya d'auko ya kuma gogawa mahaifiyarku, idan kuma baka yarda ba Abdul kaje ka tambayesu, inhar ba k'arya zasu fad'a maka ba to tabbas zasu fad'a maka gaskiyar zancen."

Cikin mamaki ya dafe goshinshi yace "Ke! Wai me kike nufi ne?"

Cikin b'acin rai tace "Ban sani ba, kaje ka tambaya kaji, kai ka mayar da mutanen kamar ababen bautarka, alhalin kuma baka uya fahimtar mai sonka na gaskiya, ni ce ke maka so na hak'ik'a amma Raihan ko a tunaninka bata saka ka, ko da yake ai hausawa sunce *sanin masoyi sai Allah*."

Tana fad'a ta kashe wayar ta cillar ta fashe da kuka, shi kuma zaune yayi bakin gado ya dafe kai ya shiga tunani, shaid'an nata d'awainiya da zuciyarshi sai kuma ga kiran Saleem (masu tambayar waye Saleem da Abbakar, Abbakar shine mijin daya auri Zeenat yar Tahir kawun Abbas), yana d'auka shima ya gama rikita mishi lissafi da nuna mishi Raihan budurwarshi ce ai, suna rayuwar soyayya kuma suna son juna, jiya kuma an kira mahaifinta ne an fad'a mishi an gansu tare a hotel a basraba, dan haka ya umarceta ta dawo, bayan ya nad'a mata na jaki kuma yayi gaggawar d'aukar matakin aurar da ita gare shi shi dake sakarai, nan yace idan bai yarda ba ya duba WhatsApp d'in shi zai gani, ganin wannan hotunan suka saka Abdul fashewa da kuka yana dana sanin yarda da yayi da iyayen Raihan, gashi tun jiya dama da kawunshi ya fad'a mishi halin da ake ciki ya dawo gida nan ya kwana, shiryawa yayi cikin shiga ta ango ya tafi da niyyar nuna musu shima ba kanwar lasa bane.

Misalin *07:30* a masallacin k'ofar gidan aka taru dan d'aurin auren, bai wani samu mutane ba dan ba'a shirya ma hakan ba, dan wani abokin kasuwancin Abbas dake mutumin Niger ne ma masifa ya dinga yi wai ya zai aurar da yarinya haka kamar wata bazawara, shi dai saurarenshi ba har suka shiga masallaci dan gabatar da abinda ya tarasu, Abdul na kallo aka nemi waliyanshi da kuma waliyin Raihan wanda Abbas ya nuna Bashir, saida aka gama d'aura aure akan sadaki dubu d'ari aka shafa fatiha Abdul ya mik'e tsaye yace "Kuyi hak'uri iyayena, auren nan da kuka d'aura yanzun nan zan warware shi, dan ba zan uya zama da fasik'a ba, kamar yanda ba zan iya kiran wad'anda bansan meye nufinsu ba na had'a ni aure da 'yarsu ba a matsayin srukaina ba, dan haka *na saki Raihan saki uku*, idan ta samu miji ko yanzu ma tayi aurenta."

Kallonshi duk mutane cikin masallacin sukayi yayin da kawunshi ya mik'e ya ci kwalar rigarshi yace "Kai Abdul meye haka? Baka da hankali ne? Ya zamu d'aura maka aure yanzu yanzun nan kawai ka saki yarinya? Akan wane dalili?"

Abdul kallon Abbas yayi wanda shi ko d'ago kai baiyi ba saboda yanda yaji abun har tsakar kanshi, yarshi Raihan, ita ce ya d'aurawa aure yanzu kuma aka saketa a gabanshi? Lallai rayuwar nan abar tsoro ce, kallon kawunshi yayi yace "Kawu ina da dalili na, ba haka kawai nayi abin nan ba."

Yayan Safeena mahaifiya Abdul d'in ne yace "Dalilin k'aniyarka, koma menene dalilinka saika saketa daga d'aura muku auren, dama soyayyar k'arya kake mata?"

"A'a kawu, soyayyata gareta ba k'arya bace, sai dai su ne bansan wace irin soyayya suke min ba da har zasu lullub'e min kura da fatar akuya su ban a matsayin mata wacce zata zama uwar 'ya'yana."

Abba ne ya taso daga inda yake zaune yana tattare balaluwarsa, yana zuwa ya kife Abdul da mari yace "Kai butulun ina ne? Wato ka gado a wajen mahaifinka ko? Ni dama da yaron nan yabi ta tawa da bai had'a jininshi da jinin wannan macucin ba, shine yanzu daga d'aura aure a tsakiyar masallaci zaka saki yarinya, kenan nufinka dama ka mayar da ita k'aramar bazawara?"

D'agowa Abbas yayi danya takawa Abba birki kafin allura ta tono garma, suna kallon juna ya mishi alama da dan Allah Abba kayi shiru, Abba daya fahimta fita yayi daga masallacin.

Sunkuyawa yayi kusan Abbas da har yanzu kanshi ke k'asa yace "Na d'auke ka kamar mahaifina, ina girmamaka, duk da nasan mahaifina ya cutar da kai, amma meyasa zaka rama a kaina? Meyasa zaka aura min Raihan bayan kasan wacece ita? Meyasa kayi gaggawar tsayar da ranar auren mu? Bayan kaga wannan ne?" Ya tambayeshi yana nuna mishi hotunan Raihan, a hankali Abbas ya kalli hotunan take ya d'auke kanshi, Bashir dake kusa da shi ne ya fizgo wayar yana fad'in "Meye wannan d'in? Wane sakarci n..."

Bai k'arasa ba shima saboda ganin hoton Raihan tsirara, da sauri ya d'auke kanshi ya jefa mishi wayar, Abdul kuma na karb'ar wayar kawunshi dake tsaye bayanshi ya nuna ma yace "Kawu ganin wannan hotunan ne yasa uncle Abbas saurin aura min yarinyar, bayan haka kuma wai ni har gwajin jini suka min bada sani na ba saboda basu so na aureta ace ina da wata cutar wanda mahaifina ya d'auko ya sakawa mahaifiyata."

Shiru sukayi sai yan maganganu k'asa k'asa yayin da Abbas ya kalleshi yana mamakin inda yaji batun gwajin jinin kuma, suna zaune haka da d'aya d'aya mutanen cikin masallacin suka fece suka bar daga Abbas sai Naseer da Bashir da kuma liman da abokin Abbas d'in nan, abokin kasuwancin Abbas d'in ne mai sunan *Alhaji Khamis Abbas* ya dafa kafad'ar shi da niyyar rarrashinshi, amma zuciya tasa Abbas tashi da k'arfi ya bar masallacin, kai tsaye gida ya nufo kuma ta falonshi ya wuce d'akin Sameera, Sameera na gama shiryawa tana rufe wadrob d'in ta ta juyo ta kalli Raihan dake kwance tana baccin wahala, zata fita kenan Abbas ya shigo d'akin da k'arfi wanda yasa gaban Sameera fad'uwa dan yanayin shi zai nuna maka ba lafiya ba, wajen Raihan ya nufa dake bacci yana zuwa iya k'arfin shi yasa ya mata wani bugun tsiya a baya, da k'arfi ta farka tare da ihu da

Please Login or Register in order to submit comment