Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

In haifeka a ciki na amma kullum burinka shine kaga ina zubar da hawaye, akan me Ammar? Meya kaika d'aki na a daren nan? Me tayi maka da sai kayi mata fyad'e ne kad'ai zaka huce? Ammar akan wane dalili ne kake son raba zumuncin dake tsakanin iyayenku? Kasan abinda hakan zai iya haifarwa kuwa? Baka sani ba? Kawai kenan iskancinka ne ya motsa ka kuma rasa inda zaka sauke shi sai akan yer uwarka, yarinyar daka rainesu a hannayenka, yarinyar da kake nuna baka k'aunar ta, babu abinda ka saba mata dashi sai muguntarka, yanzu shikenan ka ida zama dodo a wurinta, kasan irin b'arnar da kayi? Ka lalata mata komai, ka k'wace abu mai daraja a gurinta, tirr da hali irin naka, wai kai kana da zuciya ma a k'irjin ka? Meyasa da bak'ar jarabar taka ta taso baka fita ka nemi matan banzan daka saba bi ba, dan ba zan tab'a yarda da kai ba idan kace min baka tab'a yi ba sai yau, dan ta'asar da kayi tafi k'arfi ta d'an koyo, alamu ne na wanda ya saba kuma a dole yake neman sauk'in jarabarshi."

K'ura masa ido tayi tana kallo hakan yasa shi kama k'afafun shi cikin kukan jin zafin kalamanta yace "Ummy ki yarda dani, wallahi ni ba d'an iska bane, ban tab'a zina ba, dan Allah Ummy kiyi hakkk..."

Bai k'arasa ba ta fizge k'afafun ta ta juya zata bar d'akin, tsayawa tayi bakin k'ofar ta juyo ta kalleshi tace "Ammar ka tabbatar min kai tantagaryar d'an iska ne na gidan gaba, nagode maka."

Da sauri ya d'aga kai ya kalleta da tsantsar mamakin jin furucin daya fito daga bakinta tare da jin zafi a zuciyarshi, jinjina kai tayi tace "Eh, saboda kai iskancin naka daya tashi ma a cikin gidanku kayi, a cikin gidanku ma akan k'anwarka, da k'anwar taka ma kuma Ammar cikin d'akina, d'akin mahaifiyarka, akan gadon iyayenka, Ammar wace irin lalacewa ce wannan? Ka kwanta da yarinya akan gadon da iyayenka ke kwanciya, Ammar abinda ya faru ya isa yasa na tsine maka albarka ka shiga duniya, amma ba zanyi haka ba saboda in nayi haka to nasan wata rana ni zaka farmaka."

Zaro ido yayi da matuk'ar alamun tashin hankali da yanda maganar ta sokeshi, mahaifiyata? Take tunanin na...?

D'orawa tayi da "Dan Allah daga yau karka sake shiga d'akin, bana buk'atar gaisuwa ko samun girmamawa daga gareka, sannan ka fita harkar Hamna, karka nunawa kowa wani abu ya shiga tsakaninku, inba haka ba kuma har ni za'a tsine ma a gidan nan, dan Allah ka min wannan alfarmar."

Rintse ido yayi sosai hawaye wasu na bin wasu, yana kallo ta fita ta bar d'akin yana kuka kamar yaro na goye, ranar dai kamar yanda masu hidima basuyi bacci ba haka ma Hamna da tasha d'inki tana ta wani sabon kukan Ummy na rarrashi, Ammar ma kwana yayi yana kuka yana ji kamar ya kashe kanshi, amma tunani biyu ya hanashi aikata hakan, na farko ba shi ba rahamar ubangiji, na biyu kuma mahaifiyarshi yana da yak'inin ba zai samu addua'r ta ba ko bayan ba ranshi, dan haka ya bawa kanshi hak'uri sai dai kalamanta sun matuk'ar tsaya masa a rai fiye da kima.

*Washe gari* yan makaranta sun so su zauna wai tunda ana biki gidansu, amma aka ce su tafi har su dawo, Jamila da Umaimah ma drebansu ne ya aje kowace wajen sagbarta, tun a d'aki Amna ke faman yi wa Hamna magana amma tayi shiru, yanzun fa suna fitowa tace mata "Hamna yau fa a motonki zamu tafi dan ni nawa baida isashen lafiya."

Shiru ta mata ta wuce kawai tana sauka daga matakala, Amna da zuciya sai tayi hushi ta taho da sauri ta wuce ta tana fad'in "Kada Allah yasa ki min magana kiga idan ban rayu ba, ni zaki d'auka yar iska tun daren jiya da kike shigo nake miki magana kin min shiru, aikin banza kawai."

Da kallo kawai Hamna ta bita wacce take tafiya da k'yar, dan ko yanzu ma saida tasha gashin jikinta tare da magungunan da Ummy ta bata, duk da auren babban mutum ne kuma a k'urarren lokaci, amma hakan bai hana gidan fara d'aukar hayaniyar jama'a ba tunda harka ce ta masu kud'i, hakan yasa yau Hajia bata falon zaune kowa ya tafiyarshi ba tare daya gaisheta ba, Amna na fita b'angaren samari ta nufa da fad'a mishi zata tafi, Hamna ma na fitowa a farfajiya suka had'u da Ummy suna ta kai da kawowa, tayi bala'in kyau cikin tsadadden leshenta daya dace da kalar jikinta, tarbenta Ummy tayi ta shafa fuskarta wacce zaka fahimci yanayin damuwa da kuka a tare da ita, cikin sanyin jiki Ummy tace "Hamna har yanzu kina jin ciwo ne?"

Idan tace a'a k'arya tayi, idan tace eh ma k'arya ta fad'a, dan haka kawai tayi shiru tana kallon k'asa, wasu hawaye ne sukayi barazanar taho mata ta dafata tace "Kiyi hak'uri kinji Hamna, insha Allahu zai bari, yanzu ki saki fuskarki dan Allah ki d'anyi fara'a, duk da nasan dai an rabaki da farin cikinki kenan har abada, amma...Hamna kiyi hak'uri dan Allah dan annabi, ki yafe mana."

Haka Ummy ta k'arasa maganar da fashewa da kuka, jin ba dad'i yasa Hamna kallonta ita ma idonta jawur tace "Dan Allah Ummy ki daina kuka kema, Ummy ba kiyi min komai ba wallahi, ba komai zanyi murmushi, kin gani?"

Kallonta tayi ita ma tayi murmushin kamar dai yanda tayi sannan tace "Ki kula da kanki kinji, ku je Allah ya bada sa'a."

Wucewa tayi ta nufi wajen motonta, sai dai ina tana hawa taji wani bala'i daga k'asanta kamar ana sukarta saboda d'inkin da aka mata, sauka tayi kawai ta fita daga gidan ta samu adaidaita ta hau.

Amna ma na shiga sallama tayi amma shiru, Jamil dake shirin fita ne ya amsa mata suka gaisa kafin tace "Yah Ammar yana ciki ne?"

Cikin rashin sani yace "Eh to, gaskiya ban sani ba, amma bari na duba miki."

K'wank'wasa k'ofar yayi tare da "Yah Ammar, kana ciki kuwa?"

Ammar daya ji buga k'ofar ya taso ya bud'e dan k'ok'arin kawar da damuwarshi, Amna dake tsaye a bayansu kawar da kanta tayi dan tun towel d'in nan na jiya ne a jikinshi, juyowa Jamil yayi yace "Ga mai son ganinka can."

Kallon Amna yayi wacce kanta ke kallon wani wurin, ficewa Jamil yayi shi kuma ya kafeta da ido, jin shiru yasa ta d'an sunkuya tace "Ina kwana yah Ammar."

Cikin wata irin murya yace "Amna da wata matsala ne? Ko makaranta zaki tafi?"

Ba tare data kalleshi ba tace "Eh yah Ammar, dama na zo ne na fad'a maka."

Cikin matuk'ar sanyin jiki yace "Ok kije kawai, Allah ya bada sa'a, ba zan fita ba yau dana sauke ki da kaina."

Saida ta d'ago ta kalleshi saboda mamakin yanda yake mata magana cikin taushi kamar ba shi ba, jinjina kai tayi tace "Ba komai yah Ammar, sai anjima."

Juyawa tayi ta fita ita ma akan motonta ta tafi duk da yana da yar matsala, yayin da shima ya koma ciki ya sake kwantawa ya duk'ufa tunani, yana haka kiran Hajia ya shigo wayarshi, bugawar zuciyarshi ne ya tsananta yayin da gabanshi ya fara dukan tara tara, me zaisa Hajia ta kirashi bayan rabon daya ga kiranta a wayarshi tun yana France, shima idan tana son ya aiko mata da wani abu ne, mik'ewa yayi jiki a sanyaye ya zauna yana ci gaba da kallon lambar, saida kiran yayi daf da tsinkewa kafin ya d'auka ya d'ora a kunne yayi shiru, cikin yanayin rashin mutumci tace "Sai kaga dama zaka d'aga wayar ko?"

Shiru ya sake mata kafin tace "...


*Insha Allah page 25 sai nan da wani lokacin idan Allah ya bud'i ido lafiya, ina buk'atar addua'r ku.*๐Ÿ‘
09/09/2020 ร  17:58 - Ummulkhairi: ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
*BADAK'ALA*
๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ _*AHALI NA*_๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_25_


"Tv ta nake buk'ata ka kawo min yanzu yanzun nan, idan kuma ba haka ba wallahi sai nasa ubanka ya siyo min tv guda goma ya zube min su gabana."

Tana gama fad'a ta kashe wayar, lumshe ido yayi tare da sauke ajiyar zuciya, aje wayar yayi gefe ya mik'e a kasalance ta fad'a bayi dan yin wanka, bai wani d'auki lokaci ba ya fito ya shirya cikin shadda kalar chocolat da tasha d'inki da chocolat zare had'e da kalar ruwan madara, ba hula a kanshi sai takalman kalar ruwan madara da agogo duk da dai tafi takalmin haske, turarenshi ya d'auka *Dolby* ya fesa kafin ya d'auki wayarshi da makullin d'aki dana mota ya fito, kai tsaye wajen aje motoci ya nufa ya kuma bar gidan, saida ya fara siyan sabuwar tv a wajen wani daya sani ya bayar a kai gidan kafin ya wuce asibiti.

Sunyi mamakin ganinshi da safe a asibiti dan duk ranar juma'a sai k'arfe *02:00* yake shiga ofishinshi, yana zuwa ya shiga ciki ya rufe da makulli ya zauna, take abubuwan da suka faru jiya suka shiga dawo masa a kai, cikin zuciyarshi ya tambayi kanshi da "Ko a wane hali take yanzu? Ta tafi makarantar ne? Shin zata iya jarabawar ma?"

Ta wani b'angaren kuma tunanin tattunawarshi da mahaifiyarsu yake, ya aunty Hadiza zatayi idan tasan abinda ya faru? Da wane ido zai kalleta ya mata bayani? Wace irin d'auka zata mishi? Wannan tunanin shine suka tayashi hira har tsawon wani lokaci, yana cikin wannan tunanin agogon dake jikin bangon ta sanar dashi k'arfe *12:00* daidai na rana, sosai ya jima yana mamakin yanda lokacin yayi sauri haka, a hankali ya mik'e ya d'auki makullan ya fito, ba tare da kula kowa ba ya fice duk da likitocin na gaisheshi da girmamawa, yana shiga motar gida ya koma da niyyar kwantawa, amma yana shiga a wajen aje motocin ya samu mata zaune harda Ummy ma a cikinsu, fitowa yayi a raunane yana kallonta amma tana d'aga kai suka kalli juna ta wurga masa harara tare da had'e rai, takowa ya farayi da niyyar yau dai zai gaisheta harda ma k'awayen ta, amma Ummy na ganin ya nufesu ta mik'e kamar wacce aka tsikara ta nufi hanyar falon Hajia, cak ya tsaya yana kallonta da matuk'ar rauni a tare dashi, tahowa yayi da niyyar shiga b'angaren su saiya hangi Amar ya fito daga falon Hajia, baiyi mamakin ganinshi ba dan duk samarin suna zuwa gida dan shirin zuwa masallaci, abun daya sosa zuciyarshi shine ganin Ummy tare dashi tana ta faman b'alla masa botiran rigarshi ta shadda wacce ke nuna yayi shirin zuwa masallaci da d'aurin auren babansu, da kanta ta karb'i machette d'in shi ta saka mishi tare da gyara masa zaman hula, cikin gaggawa Amar ya wuce yana fad'in "Ummy sai mun dawo."

Hannu ta d'aga masa tana fad'in "A dawo lafiya shalelen Hajia."

Wani murmushi Ammar yayi da shi kanshi baisan manufa ko fassararshi ba tare da juyawa ya koma motarshi, zai tayar Amar ya k'araso ya buga gilashin motar, saukewa yayi ba tare daya kalleshi ba shi kuma yace "Wai har ka shirya ne?"

D'ago ido yayi ya kalleshi take kuma ya d'auke idonshi, a haka Amar ya sake cewa "Ammar Abba fa yace muje da wuri masallacin, kuma kai na ga yanzu ga shigo."

Tayar da motar yayi yana cikin d'aga gilashin shi yace "Tunda dai kaje ai ba sai naje ba." Yana fad'a yayi baya baya ya daidaita hancin motar kan k'ofar fita ya fice, girgiza kai Amar yayi shima ya shiga tashi motar ya fice.

Tun a hanya ya saka a ransa zai ci gaba da zama a yanda yake, Ammar d'in sa, ba zai bari wannan damuwar ta canza shi ba, tunda dai ba zasu fahimci nadamarshi ba bare su bashi damar neman gafararsu, to kawai zai nuna kamar babu wani abu daya faru, sannan ya murje idonshi ya kalli kowa kamar yanda yake kallonsu a baya, da wannan ya isa makarantar su Hamna wanda ya samu d'alibai nata fitowa daga cikin makarantar, ta cikin gilashi ya k'urawa k'ofar ido yana jiran fitowarsu.

Amna ce ta fara fitowa akan motonta tana shirin hawa titi, oda yayi da k'arfi wacce tasa ba ita ba har wasu saida suka juya suka kalli wajen, tana ganin motar k'irar Honda bak'a wulik ta tsaya, sake juyowa tayi ta dawo kusa da motar ta kashe moton ta sauko ta zo daf dashi, sauke gilashi yayi ya k'ura mata dara dara idonshi ta cikin farin gilashinshi wanda ke zagaye da maroon d'in kala, saida ya shafa gemunshi kafin yace "Ina kankana?"

Nuna masa k'ofa tayi cikin taushin murya tace "Tana kan hanyar fitowa."

Mayar da idonshi yayi kan k'ofar yace "A motonta ta zo ita ma?"

A hankali ta girgiza mishi kai alamar a'a amma ba tace komai ba, dan ta tuna in sunyi fad'a da Hamna shi ke musu dukan tsiya ya musu sulhu, tana kuma tsoron ya tozartasu cikin mutane akan hanya shiyasa tayi shiru, shirun yayi kamar yanda tayi ba tare daya daina kallon k'ofar ba, ita ma kafe k'ofar tayi da ido har suga fitowar Hamna tare da k'awarta Farida, ba tare daya kalli Amna ba yace "Kirata."

Da sauri ta wuce dan cika umarninshi, gabanta tasha fuska a d'an had'e tace "Wai ki zo inji yah Ammar."

*Ammar*, wannan sunan da taji ne yasa gabanta zubewa ya fad'i, yayin da zuciyarta ta shiga harbawa da sauri kamar zata fasa k'irjinta ta fito, yake kiranta? Akan wane dalili kenan? Me zai mata kuma bayan duk abinda ya faru? Rashin sanin amsar yasa ta kalli Amna ita ma rai a b'ace tace "Ki ce masa ba zan zo ba."

Ita ma cikin hassala tace "Ba zaki zo ba fa kika ce? Yah Ammar fa nace miki yake kiranki."

A harzuk'e tace "Eh shi d'in, ubana ne da ba zan fad'a masa haka ba? Ke dai da kika ji zaki iya sai kije amma banda ni."

"Me kike nufi? Hamna karki fad'a min maganar banza mana daga yar k'aramar magana, ni d'in naji zan iya kuma zan tabbatar miki da haka, zan kuma juya na fad'a masa kince ba zaki zo ba, watak'ila shi ya zo da kanshi kinga sai ranki ya b'ace a banza."

Cikin rashin damuwa tace "Eh kije ki fad'a masa d'in, ya jima bai zo ya yanka ni ba."

Amna ta juyo da niyyar tafiya ta ga ya bud'e k'ofar ya zuro k'afa d'aya, cike da wani tako na isa da k'asaita kamar sarki ya fara takawa zuwa gabansu, tsayawa Amna tayi tana kallonshi gabanta na fad'uwa na abinda zai faru, haka ita kanta Hamna gabanta fad'uwa yake dan tasan k'aramin aikinshi ne ya mata akuyanci, yana k'arasowa fuskar nan kamar baisan sunan wani abu dariya ba, Amna ya kalla ya tara mata hannu yace "Makullin motonki?"

Hannu na rawa ta mik'a masa makullin a zuciyarta tana fad'in "Yau kuma wak'i'ar harda moton zata shafa."

Wannan k'awar ta Hamna ya bawa makullin moton ba tare daya kalli k'wayar idonta ba yace "Kije dashi, zata je ta d'auko."

Ita kanta Farida jiki na d'an rawa ta karb'a yayin da ta kasa kallon fuskarshi saboda kwarjinin daya mata da kuma tsoron al'amarin shi, Amna ya kuma kallo yace "Wuce mota mu tafi."

Kallonshi tayi ta kalli motar ta kuma kalli Hamna kafin ta wuce tana waiwayen bayanta, sai lokacin kad'ai ya sauke idonshi a fuskar Hamna, gani yayi ta mishi wani haske sai idonta da zaka gane tayi kuka, motsa labb'anshi yayi a hankali ta hanyar fad'in "Shiga mota kema."

Saida ta kalli idonshi cike da tsanarshi ta d'aga murya tace "Ba zan je ba nace, kai mugu ne, nasan me zaka min yanzu ma idan na bika."

Take ya lumshe idonshi tare da bud'e su akanta cikin wani irin yanayi da saida ta d'an tsorata, kallon Farida yayi wacce har yanzu ke tsaye bata tafi ba, yana kallonta taji gabanta ya fad'i da sauri ta kalli Hamna tace "Sai anjima besty."

Da kallo ya bita har ta hau moton ta tuk'a ta wuce, Hamna na ganin haka ta fara takawa da nufin tarar adaidaita, bata shirya ba taji ya finciko hannunta ta cikin hijabinta ya rik'e gam, janta ya fara yi ya nufi motar da ita da k'arfi, d'aya hannunta tasa tana son ta k'wak'ule hannunta amma ina, wata zuciyar ce tace mata "Da zaki iya k'watar kanki aida kin k'wata jiya, rik'on da yayi miki jiya shine yasa fa kila kasa katab'us harya cika k'udirinshi a kanki."

Yana zuwa ya wurgata cikin motar mazaunin baya sai Amna dake gaba, mayar da k'ofar yayi da k'arfi ya rufe kafin ya zauna mazauninshi yaja motar, rufe duka k'ofofin yayi ya fara sharara gudu, kamar mahaukaciya ta fara bubbuga k'ofar tana jijjigawa tana fad'in "Malam ka bud'e min ko, bana son tafiya tare da kai d'in, ko ana dole ne? Wallahi dana had'a hanya da kai gwara na had'a da shaid'an, nace ka bud'e min na fita can kuje duk inda zaku kai da ita bai dameni ba."

Ganin ko sauraronta baiyi ga Amna dake jin zafin kalaman da yer uwarta ke jifanshi dasu ita ma ta k'i kulata, sai ta fara saka k'afarta saitin kujerar da yake tana ta turoshi da k'arfin tsiya, duk da a zaune yake amma jijjigar da take masa tasa har saida sitiyari yayi k'ok'arin sub'uce masa, banza ya mata saida ya har dab'e kan titin filin jirgi wurin kamar jeji ya taka wani mahaukacin birki, har Amna dake zaune daidai saida tayo gaba kad'an ya rage kanta ya bugu a motar, da k'arfi ya bud'e murfinshi ya bud'e k'ofar da Hamna ke zaune tana ta hargagi ya bud'e mata, amma tana ganin ya tsaya ya fito tayi shiru ta kama bakinta, yana bud'ewa ya cakumota da hannu d'aya ya figota ta fito kamar kaza, mannata yayi a jikin motar ya matseta sosai cikin b'acin rai da d'aga murya yace "Ke mahaukaciyar ina ce? Ni ne zaki raina? Ni tsaranki ne? Saboda kawai abinda ya faru zaki nemi ki raina ni? To baki isa ba kinji na fad'a miki."

Wurgata ya sakeyi cikin motar yana fad'in "Banza kawai."

Yanda ya hankad'ata cikin motar taji zafi sosai daga k'asanta wanda har yanzu ke mata zugi, wata k'aramar k'ara ta saki amma bai kulata ba sai Amna data juya tana kallonta, kafin ta mata magana taji ya figi motar da wani sabon gudu ya d'auki hanya, Hamna kam da ke jin azaba sosai dan ko adaidaita data shigo cikin dubara tayi zaman, kasa zaune tayi da kyau sai d'ogala k'ugunta da take, tana d'an cije leb'e tana dafe cikinta.

Babu wanda ya sake magana a motar har suka ga ya d'auki doguwar hanyar madarounfa, sabo kuma dogon titin nan ya samu yana ta raraka ba ji ba gani da kuma gudun tsiya, Amna dai na son tayi magana amma tana jin tsoro, Hamna da abun duniya ya dameta ne cikin zubo da k'walla ba tare data kalleshi ba tace "Dan Allah ni ka sauke ni anan na koma gida ko a k'afa ne, bana jin dad'in zaman nan fa gaba d'aya."

Amna ce ta juyo ta kalleta tace "Baki da lafiya ne?"

Cike da tausayin kanta tana zubo da k'wallan tace "Bana da lafiya, kuma shima ya sani."

Wani irin fad'uwa gabanshi yayi da sauri ya kalleta ta madubi, amma sam bata kalleshi ba sai cije baki da yaga tana yi, k'ala baice ba ya ci gaba da tuk'inshi, suna haka Hamna tace "Nifa bawali nake ji."

Da k'arfi ya juyo ya kalleta lokaci d'aya kuma ya kalli gabanshi, ba alamar wasa ta sake cewa "Wallahi fitsari nake ji."

Saida tayi tafiyar minti biyu kafin ya samu wuri ya paka motar, aje jakarta tayi ta fito ta duba da kyau ta samu wuri, matsawa tayi nesa dasu zata tsugunna taji ya bud'e murfin motar ya fito, da sauri ta mik'e tana kallonshi cike da raini, gurin yaje yana dube dube kamar yana neman wani abu mai daraja daya rasa, fuska a had'e ya kalleta yace "Ki hak'ura da fitsarin nan ki koma mota."

Shek'ek'e ta kalleshi tace "Ban gane ba? A matse nake fa."

Tsawa ya daka mata yace "Nace ki koma ko? Ba zakiyi fitsarin a nan ba, ke ba dan ma baki san ciwon kanki ba har nan kinga gurin da zaki iya tsugunawa da abinda yafi komai mahimmanci a tare dake, baki tunanin abinda zai faru dake?"

Saida ta harareshi sama da k'asa taja tsaki ta wuce tana fad'in "To meya rage min yanzun? Ko ka manta jiya ka fatatakashi."

Ba wai abinda ta fad'a bane ya tsaya mishi a rai kamar tsakin data masa da harara, sai yaji ya gamsu da mace na iya raina namiji inhar ta ganshi tsirara, wata zuciyar tace mishi "Amma ai kai bata ganka ba, wacce idonta ke rufe tana kokawa da kai tana kuka, amma kuma duk da haka lokacin da taji baka da niyyar barinta ai ta bud'a ido ta kalli k'wayar idonka tace " *Dan Allah yah Ammar ya isa haka, na tuba ba zan sake maka rashin kunya ba, dan Allah ka k'yale ni haka na gaji, wallahi kamar zan mutu.*"

A hankali ya lumshe idonshi saboda a daidai lokacin ita ma ido ta rufe ruf hawaye na mata zarya a fuska, wata irin shashek'a ce take saukewa mai barazanar tafiya da numfashinta, gaba d'aya jikinta ya saki kamar wacce babu lakka a tare da ita, bud'e ido yayi ya ga dukansu shi suke kallo, cikin mutuwar jiki ya zo ya shiga suka ci gaba da tafiya. Izuwa yanzu kam dukansu sun fahimci wajen mahaifiyarsu ne zai kaisu, sai dai me zasuje yi haka zuwan bazata shine basu sani ba, cikin mintin da bai gaza talatin ba suka isa garin har k'ofar gidan, Amna ce ta fara fitowa ta nufi cikin gidan, Hamna ma fitowa tayi cikin tako da k'yar ta nufi cikin gidan inda ya bita da kallo, saida ya ga shigarsu kad'ai ya tuk'a motar zuwa masallacin juma'a dake garin.

Da gudu Amna ta k'arasa shiga da kiran sunan "Mama, Maman mu."

Tana zaune kan kujerar k'arfe tana girki a k'aramin gas d'in ta taji muryarta, mik'ewa tayi da murna ita ma ta d'an fito daga cikin runfar zanar da tayi shamaki a wurin, suna ganin juna Amna ta rumgumeta sosai tana farin ciki, ita ma rumgumeta tayi tana fad'in "Auta ta, ke ce haka bazata? Ke da wa?"

D'agowa tayi ta juya bayanta da tsantsar farin ciki tace "Tare da Hamna da yah Ammar, shine ya kawo mu."

Murmushi tayi ta kama hancinta tace "Kice dake da angon naki ko? Ja'ira kawai ai nasan komai, Ummynku ta fad'a min a waya."

Sake fad'awa tayi jikinta tace "Kai Mama, da saura fa."

Da d'an mamaki tace "Amma ya akayi kika riga Hamna shigowa? Kullum ita ke fara shigowa da ihun murna, ko dai dan kuna tare da d'an albarka ne yasa ya daidaita mata zama?"

Tab'e baki Amna tayi tace "Tace bata da lafiya ne, tun jiya nima na kasa gane kanta."

K'arasowar Hamna yasa Hadiza kallonta, yanayin fuskarta ne ya canja lokaci d'aya saboda ganin wani sabon yanayi a tare da Hamnar, hatta tafiya ma da k'yar take yinta alamar tana mata wahala, Amna ce tayi bayan mahaifiyarta su tana bud'a fridge d'in dake kusa dasu ta d'auko ruwan sanyi, Hamna ma na zuwa fad'awa tayi jikin mamansu ta fashe da kuka, wannan abu shi ya d'aga hankalin Hadiza harda Amna dake shirin shan ruwa amma ta dakata tana kallonta da mamaki, cikin rud'u Hadiza ta d'agota tace "Hamna, lafiya? Meye na kuka kuma? Wani abu ne ya faru?"

Amna ce tayi saurin cewa "Mama kawai ki rabu da ita iskanci ne, na fad'a miki tun jiya fa take wani basarwa tana share mutane, ba wani abinda ke damunta."

Juyawa Hadiza tayi ta kalleta tace "Yi min shiru Amna, akan me zaki ce a rabu da

Please Login or Register in order to submit comment