Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rufewa tayi ta taka da hanzari ta tunkarin gidan, saida ya ga shigarta kad'ai ya ja d'an k'aramin tsaki ya tayar da motar ya bar unguwar.

*11: 49* na dare Ammar ya mik'e zaune tsakiyar gadonshi, tsaki yayi tare da kama hantsar wandonshi yace "Shikenan mutum idan baida aure baya da nutsuwa har abada."

Sakin wandon yayi ya sauko daga kan gadon, ban d'aki ya shiga ba wani jimawa ya fito, rigar wandon baccinshi ya d'auka fara ya saka ya fito, duk wani kwanon abinci daya gani a falon nasu saida ya duba amma babu abinci, fridge ya duba nan ma sai lemu kawai da ruwa, wani tsakin ya kuma ja tare da nufa k'ofar fita, acan bayan gida yake jin hayaniyar matan suna aiki, kai tsaye falon Hajia ya shiga wanda ke bud'e har yanzu saboda matan basu shiga ba bare a rufe, madafa ya wuce da niyyar shiga sai yaji k'ofar a rufe, baiyi mamaki ba dan dama idan dare yayi ana rufe k'ofofin ko ina, dawowa yayi da niyyar fita kawai dan ba zai iya jura jin bak'ar magana daga bakin kowa ba, ta kusurwar d'akin Alhaji yabi zai wuce sai yaji motsi, d'an murmushi yayi ya matso ya kama k'ofar zai bud'e sai yaji muryar Alhaji na magana da alama addu'a yake yana fad'in " *Allah kaine Allah, Allah kai kace mu rok'eka zaka amsa mana, gashi ina rok'onka kaina k'asa, Allah ka kare min zuri'ata da ahalina, Allah ka karesu daga aikata alfasha, Allah ka kare min 'ya'ya da jikokina daga sharrin zina, Allah ka kub'utar dasu da ikonka, Allah kai shaidane ban tab'a aikata zina ba, ban tab'a k'etara iyakar wani ba ta hanyar cin zarafin iyalinshi, amma ya zama dole na rok'awa iyalina kariya saboda sharrin zamani, sannan iyali suna kimtsuwa ne idan ka zab'ar musu uwa ta gari, nayi kuskure tun farko dana amince da auren Zeeya'atu, duk da a waccen lokacin ina da k'arancin ilimin addini ban kuma farga ba saida muka hayayyafa, Allah ina rok'onka ka kare min zuri'ata kada zunubin zina da mahaifiya ko kakarsu ta aikata a lokacin k'uruciyarta ya shafesu, Allah ka nesanta su da laifin zubar da cikin da mahaifiya kuma kakarsu tayi kar ma ya shafesu daidai da k'wayar zarra, Allah ka sani baiwar nan taka har yanzu bata neman shiriya daga waccen laifin, kullum tsanar mazinata take k'arawa a zuciyarta saboda tasan muninta, Allah ka shiryeta dan tsarkin mulkinka, Allah ka farkar da ita ta gane kurenta na baya ta buba gareshi, astagfirullah, astagfirullah, astagfirullah ya Allah.*"

Jin wannan addua'r yasa Ammar sakin k'ofar yayi jim, Hajia? Hajia dai, wannan shine dalilinta na tsaurara sa idonta akan zuri'ar ta kenan? Wannan shine dalilin da yasa take k'in yayan da aka haifa bata hanyar aure ba? Ashe ita ma tayi rayuwarta a baya ta holewa? Kukan da cikinshi yayi ne na yunwa ya farkar da shi daga tunaninshi, dafe cikin yayi ya juya ya kalli d'akin Ummy, murtuke fuska yayi kafin ya tukari d'akin da niyyar tambayarta makullin madafa, dan ba zai tambayeta abinci ba yasan zata fad'i bak'a ne, yana isa ya zura hannu zai bud'a sai yaga k'ofar ba rufe take ruf ba, turawa yayi ya ga ta bud'e sai kawai ya shiga cikin takon isa da k'asaita.

Mahaukacin turarenshi ne ( *Respond*)ya ganar da ita shine, da sauri ta d'ago ta sauke ido a kanshi saida gabanta ya fad'i, mamaki take meya shigo dashi a wannan lokacin d'akin Ummy? Dare fa yayi, shi kanshi mamaki yake ganinta a tsakiyar gadon Ummy zaune da littafinta na makaranta da kuma farantin kankana a gabanta, cikin kallon tuhuma ya tsaya gaban gadon fuska a had'e yace "Me kike anan d'akin?"

D'auke idonta tayi daga kanshi ta harareshi ta wutsiyar ido a zuciyarta tace "Kai baka ga abinda nake bane?"

A zahiri kuma cewa tayi "Karatu nake."

Cike da kallon raini yace "Yawon biki ya hanaki d'aukar darasinki ko? Da alama kuma jarabawa zakuyi gobe, to Allah yasa ki fad'i watak'ila ki shiga hankalinki."

Baki bud'e ta kalleshi da mamaki irin wace irin magana ce wannan? Fahimtar kallon yasa shi cewa "Eh naje na fad'a, ko zaki ci min uwa ne?"

Wani murmushin baka da hankali ta masa tace "Ah haba dai ranka shi dad'e, ni na isa, Allah dai ya k'ara girma."

"Zaki iya mana, ba kece sarauniyar ce min Allah ya isa ba."

Yanda yayi maganar yasa ta zabura ta durka daga kan gadon da nufin shigewa ban d'aki, da sauri yasha gabanta ya tsaya k'ik'am, sai lokacin ya k'are mata kallo ya fahimci ashe wando ne iya gwiwa a jikinta da rigarshi saidai basu kamata ba, sai wata hula data saka bak'a mai duwatsu masu k'yali a gabanta, kasancewar yafi ta tsayi sosai yasa yayi k'asa da kanshi yana kallon k'irjin ta wanda da gani kasan rigarce kawai babu bras, kawar da kanshi yayi ya d'an cije leb'e, ba tare daya kalleta ba yace "Koma ki zauna, ai idan na tashi hukuntaki duk inda zaki shiga zan biki."

Turo baki tayi gaba ta kalleshi kamar zatayi kuka, yana kallonta yayi saurin d'auke kanshi ya furta "Ya Allah." Lumshe ido yayi ya d'aga kai sama, wannan yanayin da tayi ba k'aramin tashin hankalinshi tayi ba, "Meyasa take birgeshi wani lokacin?"

Kafin ya samu amsa ya sake kallonta rai a b'ace saboda halin da take k'ok'arin jefashi yace "Ki koma ki zauna na ce."

Kamar sakara haka ta saki baki da tunanin to meyasa kai ba zaka tafiyarka ba? Juyawar da tayi ita tafi sa shi yin nadama, gaskiya Allah ya musu hallita ta wannan fanni kam sai godiyar Allah, juyawa yayi ya zagaya inda ya fara tsayawa ita ma ta koma ta zauna, kankanar da take sha ya d'auki yanka d'aya yasa a baki ya guntsira, wani matashin murmushi yayi yace "Kankana."

Kallonshi tayi sai kuma ta mayar da kallonta ga littafinta, sauran daya rage hannunshi ya mik'o mata da fad'in "Sha."

Wani yamutsa fuska tayi alamar k'yama k'arara, sake zuro mata yayi kamar zai saka mata a baki hakan yasa tayi saurin kawar da kanta, cikin tsawa yace "Karb'i nace."

Juyowa tayi tasa hannu ta karb'a zata aje yace "Cewa nayi kisha."

Kallon fuskarshi tayi tana d'an nuna mishi da hannu cike da k'yama tace "To ai yah Ammar ni...wallahi bana son wannan..abun ne."

Kafeta yayi da ido yace "Meye ba kya so?"

Saida ta matsa baya kafin tace "Ka gane yah Ammar, gaskiya ba zan iya sha ba saboda wannan dogon gashin na fuskarka."

Na farko daya kalleta da mamaki, wai dogon gashin fuskarshi, tana nufin gemunshi fa? Gashin da man da yake shafa mishi ma wata rana saiya zagaye garin nan bai samu ba sai yasa abokanshi da sukayi karatu a France sun aiko mishi, shine za tace wai tana k'yama, shi kam ya zaiyi da kankana ne? Kama gemun yayi yana shafawa tare da kallonta, can ya saki wani murmushi na mugunta, ba tare daya daina murmushin ba yace "Wato kina k'yamarshi ko?"

D'agowa tayi ta kalleshi, ganin kallon da yake mata yasa ta sauka daga kan gadon da gudu ta nufi ban d'aki, harta kama hannun k'ofar taji yayi ram da k'ugunta ya dawo da ita baya, mannata yayi jikin bango ya mata runfa da gaba d'aya jikinshi.

Tunda yake ritsata bai tab'a mata irin haka ba, hakan yasa ta tsorata sosai jikinta ya fara b'ari ta fara inda inda, cikin rawar murya tace "Dan Allah yah Ammar ka matsa, hakan fa bai dace ba."

Sunkuyo da kanshi yayi yasa dogon gashin da bata so yana mata yawo dashi a wuya har zuwa fuskarta yana shafa mata shi, tattausan k'amshin turarenta ne ( *Feminism*) yayi tasiri sosai wajen sa shi ya sake fita hayyacinshi, rufe ido tayi tana kawar da kanta tana jin tsikar jikinta na tashi wani bak'on yanayi na shigarta, yatsanshi yasa ya tallabo hab'arta, k'urawa fuskarta ido yayi yanda ta rintse ido tana kakkaucewa, cikin wata irin murya yace "Wato wannan ne baki so ko?"

Jin yana ci gaba da shafar fuskarta da gashin yasa tasa k'arfi ta tura shi baya tana fad'in "Dallah ni ka matsa min, wannan wane irin iskanci ne? Bana son irin wannan wasar fa."

Ko motsi baiyi ba bare tasa ran zai gusa daga kanta, matse damatsanta yayi sosai ya jijjigata yana fad'in "Ke kina iya tunanin matsawa daga nan ne? Ai tunda kika nuna kina k'yamar gashi na ta yanda ba zan iya shan abu kisha ba, to kuwa dole yawu na da naki su gauraya."

Wuyanta ya cabko ta baya ya d'ago kanta ya daidaita bakinta ya kai nashi bakin, tana jin bakinshi a nata tasa k'arfi ta fara tureshi, amma gam ya sake lik'e mata saboda jin dad'in abinda yake yi da mantawa a ina yake me kuma yake yi.

_Dan Allah duk wanda zai karanta page d'in nan ya fad'i alkairi ko yayi shiru, karku manta da cewa abune daya faru a zahiri, addu'a da fatan shiriya ita wasu mutanen ke buk'ata, kar mu manta da Hajia wace irin mace ce da kuma mummunar kalmar da kullum iyayenshi ke binshi da ita, musamman kalmar *d'an iska* da *shege*, so mi bishi da addu'a kawai dan dole wata rana dama addua'r tayi tasiri a kanshi, tunda shi ba zai iya zama shege ba sun mishi gatan samar dashi ta hanyar aure, to fa dole suyi hak'uri dan zasu goyi jikan shege, Allah kasa mu dace._

Sosai yake tsotsar bakinta ya manta da ba halak d'in shi bace, ita kuma kokawa take dashi sosai duk da ya rik'e mata hannayenta sosai, zura hannayenshi yayi cikin rigarta sai kawai yayi karo da tula tulan...

Jinsu a tafin hannunshi yasa ya saki bakinta ya zuro d'aya daga cikin na shanunta ta saman rigar ya kai bakinshi yayin da d'aya hannun ya rufe mata baki dashi, a lokaci d'aya kuma yake tahowa da ita har yayi nasarar kwantar da ita ka gadon, kuwa take iya k'arfin da tunanin a kawo mata d'auki tare da kokawa iya k'arfin ta tana dukanshi tana cizon tafin hannunshi daya rufe mata baki...


๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ‘
19/07/2020 ร  19:25 - Ummulkhairi: ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
*BADAK'ALA*
๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ _*AHALI NA*_๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_24_


Aikin gama kam ya gama, rana ta farko daya fara sanin 'ya mace a duniya kamar yanda ita ma shine na farko gareta, zaune yake bakin gadon yana bubbuga kanshi da hannayenshi yana so ya farka daga mummunan baccin da yake, amma ganin ya k'i tashi yasa ya mik'e da k'arfi tare da kaiwa bango naushi yana fad'in "Meyasa? Meya sameka Ammar? Me ka aikata? Tirr da kai."

Fuskantar gadon yayi idonshi rintse baya son ganin Hamna a wannan halin, saida ya sauke numfashi mai k'arfi kafin ya bud'e ido a hankali da addua'r Allah yasa yagababu kowa kawai gizo ne ko mafarki, tarau ya sauke ido kanta tana jan numfashinta da k'yar sai matsawa take har tana neman fad'uwa daga kan gadon tana kuka, kallonshi ya kai kan ta'asar da yayi hakan yasa shi cabko wuyanshi ta baya da k'arfi ya sake rintse ido yace "Shiiit, Ammar alawadaranka, ashe dama d'an iska ne kai kamar yanda suke fad'a, meya kaika aikata wannan b'arnar?"

Hamna data sauka daga kan gadon ne ta rakub'e ta had'a kai da gwiwa tana ta k'ara dunk'ulewa cikin zanin gadon data janyo ta rufe jikinta sai k'ara sautin kukanta take, lallai yau ta koyi wasu darusa da dama na rayuwa, na farko ta fara jin *tsoronshi* ta yanda take jin ba zata sake shiga harkarshi ba, na biyu kuma ta *ji wata tsanarshi ta gauraya jini da tsokarta*, na uku kuma duk *abinda Allah ya hukunta* shine zai sameka ko baka so, domin kuwa saida Ummy tace mata ta rufe d'akin saboda ko bacci ya d'auketa tunda su suna aiki basu ga ranar gamawa ba, sannan har yer uwarta Amna saida tace me zaisa taje d'akin Ummy karatu bayan ga nasu d'akin, bata tunanin Abba ya dawo ya kuma buk'aci d'akin? Amma haka ta shareta ta taho, ashe wannan mummunar k'addarar ce ke bibiyarta, bak'ar ranar da d'an uwanta na jini zai mata fyad'e, ita kam tsakaninta dashi sai Allah isar mata, dan kuwa ba zata yafe masa ba har abada.

Kallonta yayi duk yanayin tashin hankali da rashin jin dad'i ya bayyana a tare dashi, kallon littafinta yayi na karatun wanda ya turmushe da kuma kankanar data zube, girgiza kanshi yayi yana tunanin ta ina ma zai fara rarrashinta? Da wane ido zai kalleta yace zai bata hak'uri? Me zai fad'a mata ta yarda dashi? Wane kallo mutanen gidan nan zasu mishi? Ya ma akayi ya zarce daga ya d'an mata horon da bai wuce sumbata ba? Sai kawai ya tsinci kanshi yana sukuwa akan 'yar mutane yana hak'arta kamar rijiya, bayan kuma babu aure tsakaninsu, kai Ammar ya ma zakayi da yer uwarta ne wacce kayi niyyar aura? Me zata ji? Yer uwarta da suka fito ciki d'aya? Rashin samun madafa ya sashi sake kaiwa bango dukan tsiya wanda yasa har saida jini ya shake gabce mishi sanadiyar ciwon da yaji ranar, da saurin bala'i ya bud'e k'ofar d'akin ya fita dan hakan shine ma daidai a wurinshi, saida ya zo zai wuce ya kalli k'ofar Alhaji, ji yayi wasu hawaye na neman taho mishi na tausayin tsohon, mintuna nawa ne daya saurari addua'r shi, amma ace haka ta faru dashi, lallai wannan k'addara ce, dan ba dan Allah ya rubuta hakan zai faru ba da babu abinda zai fito dashi neman abincin ci, duba da yasha kwana da yunwa kuma baya damuwa, sannan ko da *11:00* na dare Hajia tasa an rufe mata k'ofar falon nan, amma yau sakamakon sabga yasa ba'a rufe ba har ya iya shigowa, sannan da farko yayi niyyar barin d'akin, amma addua'r Alhaji data tsayar dashi har tasa yaje d'akin Ummy, gashi yanzu ya aikata abinda baisan ina tashin hankalin zai tsaya ba, da sassarfa ya taka zai fita ba tare daya lura ba yayi karo da mutum, da sauri ya kalli wanda suka had'u ashe Ummy ce rik'e da jug na ruwa, wani kallo ta masa kamar zata cinyeshi tace "Kai kuma meye haka? Me kake yi anan a wannan lokacin?"

Kafeta yayi da ido kawai dan rashin gaskiya yasa yana tunanin kamar zata karanta a goshinshi abinda ya faru, shirun daya mata yasa taja dogon tsaki ta wuce ta barshi nan, da sauri shima ya fita ya koma b'angaren su ko k'ofar bai rufe ba ya wuce d'akin shi, yana shiga wanka ya shiga yayi na tsarki kafin ya tsaya gaban panpo yana sako mishi ruwa, ido rufe ruwan ke sauka yana hasko duk abinda ya wakana, "Tabbas nine na fara bud'e kankana, ni ta fara sani, ashe duk wayewar nan tata bata sa ta zubar da mutumcinta ba, ina ma ta hanyar aure hakan ta faru?"


*Ummy* na shiga d'akin ta tsaya turus saboda ganin bak'in abubuwa, babu zanin gado shinfid'e sai ma alamun jini-jini, farantin kankana tarwatse tare da kankanar, littafin karatu ya turmushe sai kuma pilow dake kan gadon suma duk a k'asa, tana cikin duba wannan abubuwan ne taji sautin kukan Hamna, saida ta sake kallon wurin da kyau tare da matsowa kad'ai ta ganta, ganin dunk'ule cikin zanin yasa Ummy sakin jug d'in ta k'arasa da gudu ta durk'ushe ta rik'ota tana fad'in "Subhanallahi, Hamna lafiya? Meya sameki haka? Meya faru dake? Lafiya k'alau na barki, meya faru?"

Hamna sake fad'awa tayi jikin Ummy ta sake fashewa da kuka sosai, gaban Ummy ne ya ninka fad'uwa tare da k'arfin halin cewa "Hamna dan Allah ki fad'a min, meya faru na ganki?"

Kuka kawai take ta kasa cewa komai tana tunanin ta fad'a ko tayi shiru, Ummy kuma data gama fahimtar meya faru hawaye ne suka taho mata ta k'ara k'amk'ame Hamna a k'irjinta tana fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, Hamna Ammar ne?"

Kukan data sake fashewa da shi ne yasa Ummy ma fashewa da kukan da k'arfi, d'ora bakinta tayi kan gashin Hamna har hawayenta na zuba saman kan tana fad'in "Hamna kiyi hak'uri, laifi na ne, laifina ne Hamna, kiyi hak'uri dan Allah, Ammar ya zamar min kamar dodo, bansan me nayi masa ba da yake son ganin ya d'ora min hawan jini, ba zan tsine masa bane kawai dan kar ya k'arasa zamar min tashin hankali."

Kuka suka ci gaba da rerawa kafin daga bisani Ummy ta d'agota ta kalleta ta dafa kumatunta tace "Hamna kiyi hak'uri kiyi shiru kinji, bara na taimaka miki."

Mik'ewa tayi ta shiga ban d'aki, heater ta kunna mata ruwa masu yawa kafin ta fito ta fara gyara d'akin, duk tana aikin nan tana zubar da hawaye na takaicin abinda Ammar yayi, tana tunanin abinda zai faru idan mutan gidan nan suka samu labari, da wane ido zata kalli mahaifinshi? Me zata fad'awa mahaifiyar Hamna da mahaifinta ma? Wane irin kallo zasu mata? Me zasu ce? Hajia fa? Babban tashin hankalin kenan Hajia? Da wannan tunanin ta gama kimtsa d'akin taje tasa ma k'ofar d'akin makulli ta rufe sannan ta kamata suka shiga ban d'aki, saida ta nuna mata ta shiga cikin bahon wankan suka lura da jinin dake bin k'afafun ta, a marairaice Ummy ta kalleta tace "Ki shiga kiyi wankan, idan kika fito saina dubaki watak'ila kinyi k'ari ne."

Shiga tayi ita kuma ta fito ta d'auke zanin gadon da tattare kayan jikinta, duk da basu yage ba amma sunji matsa, ta jima tana jiran fitowarta kafin ta fito ta zaunar da ita, wani zama tayi kamar akan wuta saboda zafin da take ji zaman ma tayi ne dan Ummy ce ta zaunar da ita, kallon kumburarrin idonta Ummy tayi ta dafa kafad'ar ta tace "Hamna zan iya rok'onki wata alfarma? Dan Allah? "

Cikin lumshe ido ta kalleta tana cije leb'en k'asa ta jinjina mata kai kawai alamar eh, nisawa tayi tare da kallonta a tsanake tace "Hamna, bansan taya zan fara baki hak'uri akan abinda ya faru ba? Haka bansan meya had'a ku ba har haka ta faru? Amma dai Hamna aikin gama ya riga daya gama, muyi tunanin abinda zai biyo baya Hamna idan abu nan ya fito fili, Hamna, shin kina son zumuncin dake tsakanin mahaifinki da mahaifinshi ya wargaje? Ko kuma zaki so mutumcin dake tsakani na da mahaifiyarku ya tarwatse? Ko kuma zaki so ganin Hajia cikin wani mawuyacin hali sakamakon abinda ya faru dake?"

Hamna da duk ta fahimci inda kalaman Ummy zasu dosa ne cikin muryarta data disashe tace "Ummy na fahimci me kike nufi, ba sai kin rok'e ni kan nayi shiru ba, nima abinda nake tunanin rok'onki kenan, Ummy ba zan so kowa yasan abinda ya faru dani ba, ba lallai zumuncin iyayenmu ya tab'u ba saboda duka iyayena suna k'aunar shi, amma ni zan ji kunyarsu, sannan bana so Hajia ta sani dan zata tsine min tare da shi, sannan Ummy..."

Fashewa tayi da kukan hakan yasa Ummy k'ura mata ido tana kallo, da k'yar ta tsagaita ta ci gaba da cewa "Ummy yer uwata Amna, ita ce fa wacce zai aura, kuma kinsan Hajia ba canza maganarta take ba, Ummy da wane ido zan kalleta idan tasan...idan tasan mijin da zata aure ne ya min..."

Hannunta Ummy ta kamo tace " 'Yata hakan yana nufin wannan ya zama sirri a tsakaninmu kenan?"

Jinjina kai tayi cikin kuka alamar eh, rumgumeta Ummy tayi tana fad'in "Nagode Hamna da kika fahimce ni, nagode da kika yarda zaki rufa masa asiri, tabbas ni uwa ce, amma karki d'auki hakan a matsayin tauye miki hakk'i, nasan an zalinceki sosai ta yanda ba zamu iya dawo miki da abinda ya fizge miki ba, amma lokaci zai zo da zaki gane hakan da nayi shine gatan daya dace na miki."

D'agota tayi tace "Ki kwanta na dubaki na gani."

Kunya ce tasa tace "Ba komai Ummy ki barshi kawai."

Kwantar da ita tayi tace "A'a ba zan yarda ba Hamna, tun yanzu ne ta kamata na dubaki dan nasan waccen d'an banzan ba hankali ne dashi ba, kaca-kaca ya miki da gani ma."

Sunkuyar da kai tayi wasu hawaye suka zuba kan k'afafun ta, tana ji tana gani Ummy ta bud'eta ta dubata, kuma tabbas akwai k'ari wanda inba d'inki aka mata ba zai iya haifar mata da matsala a gaba, cike da tausayi Ummy ta kalleta tace "Hamna kin k'aru fa sosai, gashi dare yayi yanzun nasan duk inda kawunku yake yana kan hanyar shigowa gidan, dan nasan wannan hidimar ce ta hanashi shigowa da wuri, ya kamata na miki d'inki, bansan ko zaki iya jurewa ba yanzun?"

Cikin zubo da wasu hawayen taysayin kanta tace "Ummy tsoro nake ji gaskiya, kawai ki barshi ma ba komai."

Cike da gargad'i tace "Hamna akwai komai, ba zaki fahimci haka ba sai kinyi aure ko kuma kin haihu, gaskiya ba zan iya kallonki haka ba."

Wani kallo ta ma Ummy, sai tayi aure? Kai amma boss ya cuceta, yanzu shikenan fa ya rabata da mutumcinta ta k'arfi? Kuma ya auri yer uwarta ita ma ya moreta, riba biyu kenan, ya jini ya ji yer uwata, k'wank'wasa d'akin Ummy akayi tayi sauri ta dauk'owa Hamna littafinta ta bata a hannu tace "Ki saki fuskarki dan Allah kar wani ya fahimta."

Mayar da kanta tayi ga littafin ta yanda ma mai shigowa ba zai iya ganin fuskarta ba saita juya ko kuma shi ya shigo har inda take, Ummy na bud'ewa Jamila da ake aiki tare dasu ne tace "Aunty wai ki zo inji Mama."

Murmushi tayi mata tace "Shikenan kice ina zuwa."

Murmushi tayi ita ma tana kallon bayan Hamna tace "Yan biyun Ummy wacece a cikin? Ku ba zaku fito muyi aiki ba?"

Murmushin yak'e Ummy tayi ta juya ta kalli Hamna da ko juyowa ba tayi ba tace "Hamna ce, karatu take saboda jarabawarsu gobe."

Juyawa tayi ta fita Ummy kuma ta juyo ta kalleta tace "Hamna zan tafi naji, dan Allah ki saki ranki kinji, komai dare idan na dawo zan miki d'inkin nan."

Da kallo kawai ta bita harta fita, juyowa ta sake yi a hankali ta zubawa littafin ido, Ammar ne ya sake dawo mata a tunaninta tun daga shigowarshi har abinda ya faru, fita yayi ma ko bata hak'uri bare ya rarrasheta, a hankali ta furta "Allah ya isa, mugu kawai azzalumi mai bak'ar zuciya, wallahi sai mun tsaya gaban Allah ya mana hisabi."

Ummy na zuwa naman da aka soya ne Zeinabu ta tambaye ta yanda zasuyi dashi a matsayinta na babba garesu, tana fad'a musu yanda zasuyi tace tana zuwa ta bar wurin, b'angaren su Ammar ta nufa a harzuk'e tayi sa'ar shiga saboda k'ofar a sake, tana zuwa k'ofar d'akin shi ta bud'a da k'arfi ta shiga, zunbur ya tashi tsaye dama zaune yake bakin gadon da towel ya fito daga wanka ya kasa katab'us, yana ganin Ummy ce kuma yanayin fuskarta ya nuna mishi abinda zai faru, shi kuma yau ya yarda yayi laifi kuma zai bayar da hak'uri, dan haka kafin ta k'araso ya durk'usar da gwiwoyinshi k'asa ya sanda kanshi yana jiran hukunci, Ummy na zuwa gabanshi ta d'auke shi da mari har saida ya tangad'a, yana dawowa daidai ta sauke kai mishi wani marin a d'aya kumatun tasa k'afa ta hankad'ashi ya fad'i warwas k'asa, tashi ya sakeyi ya koma yanda yake a farko yana kallonta yace "Ummy ki min duk hukuncin daya dace dani, wallahi zan d'auka, amma dan Allah karki tsine min Ummy, ba zan iya jurar tsinuwarki ba, Ummy kada ki zageni dan Allah, dan bansan inda hakan zai sake kaini ba."

Cikin zafin rai ta sake kashe shi da mari duk da rad'ad'in da hannayenta keyi, sunkuyawa tayi kamar zata fad'a kanshi ta nuna kanta tace "Ammar me nayi maka? Me na aikata maka da wannan hukuncin ne kad'ai ya dace dani?

Please Login or Register in order to submit comment