Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma ban iya tuna ranar daka bani ajiyar kud'i ba."

Turo baki yayi irin shagwab'a yace "Abba ba fa ajiya na baka ba, kai ne kawai zaka bani kyauta."

Hanya ya kata zai fita yace "To bana da."

Bin bayanshi yayi yana fad'in "Ni dai ka bani kawai, idan ban tambayeka ba wa zan tambaya? Kai kad'ai ne fa ubana a garin nan, kuma duk hidimar nan da akayi sisinka ban nema ba."

Juyowa yayi yace "Amma uban wa ya biya maka sadaki?"

"To ai kai ka biya na kowa da kowa, kaga kenan ba zanyi lissafi da wannan ba."

Har saida ya kai bakin mota zai shiga ya rik'e murfin mota yace "Allah saika bani, in kuma kace ba zaka bayar ba zan je wajen abokaina nace su bani bashi, kaga ku za ama dariya ace d'a kuma jika ga ahalin Gaga amma ya rasa million biyu."

Ba tare daya ankara ba lieutenant ya kai mishi bugu a k'eya yana fad'in "Dan ubanka yi sauri kaje, daga nan saika biya gidan redio da telebijin duk ka fad'a musu ni Hassan na k'i baka million biyu."

Juyawa yayi yace "Shikenan zaku gani kam."

Kallonshi lieutenant yayi, irin tafiyar nan ce idan yayi hushi, hakan kuma zai iya sawa yayi komai, iska ya furzar ya d'aga murya yace "Me za kayi dasu?"

Juyowa yayi yana dariya har ya k'araso kusanshi yace "...


*Yan nigeria Allah ya saka muku da alkairi.*
09/09/2020 Γ  17:58 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*BADAK'ALA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ _*AHALI NA*_πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦

πŸ‡³πŸ‡ͺ *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_37_


Juyowa yayi har ya k'araso kusanshi yace "Alawa zan siyo?"

Jin abinda ya fad'a yasa lieutenant yi mishi kallon baka da hankali ko me? tsaki yayi yace "Zan tsaya nan sauraren wannan shirmen naka ne?"

Kallonshi yayi tace "To Abba gashi na fad'a maka."

Da k'arfi yace "Uwarka! Alawar uban me zaka siya ta million biyu? Ammar ka kiyaye ni fa."

Kwalar rigarshi ya kama yana wasa dashi sannan yace "Zan fara tarawa jikokinka alawa ne."

Girgiza kai kawai yayi cike da damuwa ya fito da k'aramin makulli a aljihunshi ya mik'a mishi yace "Ka samu mahaifiyarka."

Karb'a yayi ya juya ba tare da yace komai ba, yana shiga falon Hajia ta kalleshi tace "K'aryar banza kawai, kud'in ma da za kayi birgar dasu baka da saika karb'a wajen ubanka."

Murmushi ya mata yace "Magana sahihiya, kinji fa kema ubana kika ce, to idan bai min ba wa zai wa? Nine fa sanyin idanuyarshi na farko."

Kai ta d'aga mishi alamar kai tafi can tare da fad'in "Kai dallah can, shalele shine sanyin idaniyar kowa a gidan nan."

Kallon can ta matse muku ke da shalelen ya mata ya nufi d'akin Ummy, tana shirin fitowa suka had'e a k'ofar d'akin, mik'a mata makullin yayi yace "Inji Abba ki bani million biyu."

Fizgar makullin tayi ta koma d'akin inda ya bi bayanta, juyowa tayi tace "Fice min a d'aki ka jira ni k'ofa."

D'aga kafad'a yayi ya juyo ya tsaya k'ofar d'akin, tana d'auko mishi ta same shi da waya a kunnenshi yana amsawa, abinda taji yace kawai shine "Zan turo a duba ta, ni ina cikin cin amarci ne ba zan fara fita ba gaskiya."

Ta gefen ido ta harareshi ta mik'a mishi kud'in, karb'a yayi yana kashe wayar tare da makullin, kallonta yayi irin ba wasan nan yace "Akwai majiyaciya a asibiti dake buk'atar kulawar d'aya daga cikinmu, Ummy kije ki duba ta."

"Saboda me?" Ta fad'a a hassale, kallonta yayi yace "Saboda ni jiya aka d'aura min aure, ina hutu."

Ganin tayi shiru bata da abun fad'a yasa shi wucewa yana fad'in "Duk kwanakin da kikayi ma ba kya zuwa da izinin wa?"

Da kallo ta bishi a ranta tana fad'in "Ya zanyi ma wannan yasan ina da cikin? Zai iya sakani gaba yana min dariya, a k'arshe ma yace na tsufa da haihuwa."

Iska ta furzar tace "Allah gamu gareka."

Yana daf da isa wajen Hajia Hamna ta shigo falon da alama daga waje take, riga da wando ne jikinta irin kayan nan na indiya, sai dai tsagar dake da rigar gefe da gefe har saman k'ugun ta, kallabin dake kalar wandon k'arami ne wanda ke saman rabin kanta, k'ura mata ido yayi yana kallo, har ta fice bata kula da tsiyarshi ba, juyawa yayi ya bita da kallo, shi kam ya fara gajiya da wannan yanayin da yake tsintar kanshi a ciki a duk sanda ya ganta, al'amarin girmama yake ba raguwa ba, har zuciyarshi canza salon bugawa take idan suka had'u. Hankalinshi yafi tafiya ga shigar data fita da ita, akan me Hamna bata jin magana? Me yasa ba zata taimaka mishi ba ta dinga rufe jikinta? Me yasa bata son kwanciyar hankalinshi ne? Hasalima bata damu da damuwarshi ba? *Ba zan lamunta ba gaskiya*, yana fad'in haka ya daka mata tsawa yace "Ke."

Hamna data fara taka makala ko juyowa ba tayi ba, da k'arfi ya sake cewa "Kankana ke."

Hajia dake zaune tana kallonshi ne tace "Wai kai ba zaka daina kiranta kankanar nan ba?"

Kallonta yayi fuskarshi a had'e rai b'ace yace "Akan me zan daina? A baya ma na kirata haka bare yanzu dana tabbatar."

"Ka tabbatar dame?" Ta fad'a tana kallon idonshi, Ummy dake tsaye k'ofar d'aki tana nata jimamin tana jin haka ta zaburo tana dariya tace "Ya riga daya saba ne Hajia, zai daina ai."

Kallon Ummy yayi wacce baiga komai ba a idonta sai tsoro, wato ta d'auka zai fad'a ne? Shi data barshi ma ya fad'a mata yanda zata fahimta, kai shi fa yanzu zai iya fad'a in ya so ayi duk wacce za ayi, sai lokacin ya kalli Hamna data juyo tana hararenshi, yana ganin haka ya bi ta bayan kujerar Hajia ya taka wurinta, da yatsa yake nuna kanshi yana fad'in "Ni dai kika harara ko? Bari kiga iskanci."

Ai da gudu ta fara haurawa sama dan tasan tsaf zai mata iskancin kamar yanda ya fad'a, tana kaiwa ta mayar da k'ofar ta rufe, Ummy dake binshi da kallo kar ya ja mata magana yasa take fad'in "Dawo, kar tab'a min yarinya wallahi."

Tab'e baki Hajia tayi dan ita dramarsu bata dameta ba dama, yana zuwa k'afa yasa ya tura k'ofar sai kawai ta bud'e, baya tayi da sauri tana nuna shi tana fad'in "Allah ka fita a d'akin nan, Ummy, Abba zai kashe ni."

Murmushin gefen labb'a yayi yace "Kinga kuwa banyi tunanin haka ba."

Da mamakin me yake nufi ta kalle shi, fahimtar da ita yayi ta hanyar fad'in "Eh mana, sai yanzu ne kika fad'a min cewa kasheki ne kad'ai zai zama maganin matsalata."

Da k'arfi ya shak'o wuyanta da hannu d'aya, fitowa yayi da ita a haka yana fad'in "Ban fad'a miki ki dinga saka hijabi ba? Ban fad'a miki ki daina saka wannan d'an banzan gashin ba? Raina ni ne kikayi kenan da ban isa na fad'a miki kiji ba."

Ummy da su Zeinabu da Zeituna suna ganin ya fito da ita a haka suka rik'e baki, Ummy ce ta tunkare shi ta fara k'ok'arin b'anb'are hannunshi tana fad'in "Wallahi saketa, Ammar kar ka kashe min yarinya, bana son iskanci fa."

Saida ya kawota gaban Hajia ya watsota daf da k'afafunta ta fad'i k'asa, rik'e wuyanta tayi tana wahalallen tari da hawaye tsabar wahala, Hajia ya kalla yace "Madame Suley, ki zama shaidata, Allah kar na karya yarinyar nan wani yace zai tambayeni dalili, ki fad'a mata kar ta sake fita babu hijabi jikinta, sannan wannan gashin."

Ya fad'a yana kamo gashin da hannunshi yaja da k'arfi wanda yasa ta saki k'ara da k'arfi tana rik'e hannunshi, d'orawa yayi da "Idan na sake ganinta dashi reza zan saka na yake shi har da asalin gashinta."

Sakinta yayi hakan yasa ta tashi da sauri tayi baya tana hararenshi, Hajia ce ta wurga mata harara tace "Sa'anki ne shi da kike hararenshi?"

Sunkuyar da kai tayi tana k'ara jan d'an kwalinta saman kanta, a tsawace Hajia tace "B'ace min da gani malama."

Rai a b'ace Hamna ta taka da sauri tana d'an bubbuga k'afafu tana gunguni kamar za tayi kuka, da kallo ya bita har ta haye sama sannan yayi k'wafa ya kalli Hajia, wannan kud'in ya mik'a mata yana murmushin shegantaka yace "Ga wannan ko, ni a wurina tafi k'arfin rak'umi d'aya sai biyu."

Juyawa yayi zai fita ya kalli Ummy dake tunanin abinda ke tsakaninshi da Hajia, rak'umi biyu? Tab'e baki tayi irin Allah ya shiryakan nan kafin ta juya ta nufi d'akin ta, murmushin gefen labb'a yayi ya bar d'akin.

Wannan al'amari ne da ba zata d'auka ba, a gidanta? A ahalinta har za'a samu wacce za tayi iko da 'ya'yanta? Wannan ba abu bane mai yiwuwa! Waya ta d'auka ta danna mishi kira, a daidai lokacin da uwar gida ta tsare gaba ta tsare baya. Ya sani a gidanshi Aissata ce ke mulkarshi, a gidansu kuma Hajia ke juyashi, a waje kuma shi yake nasa mulkin, tunda Aissata ta ga sunan wanda ya kira ta hana shi d'aukar wayar cike da kwarkwasa, sai dai hankalinsa na wajen bala'in da zai jawa kanshi, saida ya gama da duk buk'atunta kad'ai ta barshi ya fito daga d'akin da aka saukesu, mugun fad'uwa gabansa keyi da tunanin abinda zai tarar, hatta salon tafiyarsa saida ya canza zuwa kamar wanda aka cirewa lakka, da sallama ya shigo falon murya k'asa k'asa yana d'an tattare jalabiyarsa har bak'in wandonsa na fitowa, yana hango fuskarta kwarjininta yasa shi yin k'asa da kanshi, har saida ya ji kamar zaiyi fitsari tsabar razana, dan yasa ba zata duba mutanen dake kai da kawo ba suna shirin barin garin ba tsaf zata wankesa wankin babban bargo, duk wanda suka gaishe shi kasa amsawa yayi sai yak'e daya musu dan kar suce bai amsa ba, yana zuwa gabanta ya durk'usa da fad'in "In..."

Bata bari ya gama fad'a ba ta mik'e tsaye tace "Bana son gaisuwarka, Haruna ku tattara naku ya-naku ku bar min gida tunda an gama abinda ya kawoku, idan ba haka ba wallahi zan tsinkawa matarka rashin mutuncin da kare ma ba zai ci ba."

Hanya ta kama da sauri ta nufi kusurwar da zata sadata da d'akin ta, shafa gashin kanshi yayi yace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un."

Mik'ewa yayi jiki a sanyaye ya bita d'akin, yayi sa'ar bata rufe ba dan haka ya shiga ya sake durk'usawa ba tare da sun had'a ido ba, cikin sigar rarrashi yace "Hajia dan Allah kiyi hak'uri ki gafarce mu, duk da dai bansan laifin da mukayi ba, amma Aissata bata..."

"Bata da me? Me kake so kace?" Ta fad'a wa k'arfi, nuna kanta tayi tana fad'in "Har ni zaka nuna banda mahimmanci a gurinka, sanin kanka ne Gambo na juya jikokina ma bare ku dana haifa, har ka kwana cikin gidan nan ka bari rana ta fito ba tare da ka zo inda nake ba, wai sai yanzu ne k'arfe *01:00* rana zaka shigo min falo, kuma a hakan ma bayan na kira ka baka d'auka ba, shine har zaka ce baka san laifin daka min ba, to yayi kyau nagode, ka tashi ka bar min d'aki."

Marairaice yayi yace "Dan Allah Hajia kiyi hak'uri, gajiya ce tasa dukanmu mukayi bacci mai nauyi, kiranki ma ban gani ba sai yanzu ina farkawa, kiyi hak'uri dan Allah ki yafe min, insha Allahu zuwa gobe zamu koma dama."

Da yatsa ta nuna shi tace "Wallahi ba zaku sake kwana anan ba, ku had'a kayanku ku koma kaji na fad'a maka, in ba haka ranka zai b'ace fiye da tunaninka, kaje can ka k'arata tunda ka zama lusari shashashan da mace ke juyawa."

Sululu ya mik'e yana fad'in "Allah ya huci zuciyarki Hajia, kiyi hak'uri dan Allah zamu tafi."

Da kallo ta bishi tana tunanin idan tayi haka ai ba tayi nasara akan Aissata ba, kenan zata hak'ura da d'anta ne ta bar ma wata cen? Ai tak'amarta yana nesa dasu daga ita sai danginta ke morarshi, dan haka za tayi abinda zata k'untata mata ta nuna ita ma ta isa da shi, murmushin mugunta tayi ta zauna bakin gado tana jiran su tashi tafiya.

Cikin tsananin damuwa Jibril yace "Abba ku fad'a min abinda ke faruwa mana, tun jiya gaba d'ayanku kun canza, Hajia har kuka na ga tana yi, kai ma kuma Abba ka shiga damuwa waccen ta kasa b'oyuwa, sannan Alhaji ma na fahimci haka daga gare shi, gaba d'aya kun sani rud'ani, dan Allah ka fad'a min abinda ke damunku."

Shiru yayi, tunani yake ya fad'a mishi ko kuma yayi shiru, to idan ma yayi shiru wata rana fa shima zai zo ya sani kamar yanda shima ya sani bayan wannan shekarun, sannan yana da hakk'in ya sani shima dan ya shafe shi. Ajiyar zuciya ya sauke ya kalleshi cikin nutsuwa yace "Jibril, daga ni har kai mun kasance muna son sani iyalenmu na d'aya b'angaren, ni da kai duka mun yarda da k'addarar da ubangiji ya d'ora mana, wannan iyalen namu da muke son sani ne muka san su jiya, shiyasa kaga duk kowa ya shiga damuwa, domin kuwa wanda ya na gani a matsayin mahaifia sam babu wanda yayi tsammanin haka."

Me Jibril zaiyi inba dariya ba yaji labarin kakanshi, da tsantsar fara'a yace "Abba da gaske? Wai kakana yana raye? Alhamdulillah, Abba waye shi? Fad'a min naji dan Allah na k'agu."

Kallonshi yayi babu kuzari a tare da shi yace "Kasan wannan tsohon malam Rabi'u? Kakan Maryama matar Junaid? To shine."

Saida yaji kanshi ya sara, malam Rabi'u kuma? Maryama kenan yar uwarsa ce ta jini? Kaga wani ikon Allah, kallon mahaifinshi yayi yace "Abba Maryama yar uwarta ce?"

Cikin tab'e baki yace "Hakan alamu nuna."

Dariya Junaid yayi yace "Abba alamu kuma? Ai abune a zahiri, Abba kawai kayi farin ciki kaima."

Kallon Junaid yayi da mamaki, sai dai bai ce mishi komai ba, Junaid kam murmushi yake inda yake son wata rana Maryama ta nemi gaya mishi maganar banza, saiya zauna ya bud'e mata littafin rashin mutumci, dan saiya yagata ya nuna mata ba'a kanshi aka fara ba.

*BADAK'ALA*

*BADAK'ALA*

*BADAK'ALOLI*

Ko da Ammar ya koma kai tsaye madafa ya nufa inda yake jin motsin mutum, da shigarshi ya tunkareta cikin fad'a yana fizge karotte da wuk'ar hannunta yana fad'in "Dallah bani nan malama, ubanwa yace ki shigo nan? Daga zuwanmu jiya sai wani d'ora girki, to kiji da kyau daga yanzu har kwana shida ba zakiyi girki ba."

Za tayi magana sai ji tayi ya kimkimeta ya fito da ita ya nufi d'aki, wutsil wutsil ta fara da k'afafu ta rufe ido gam ta sunne kanta a k'irjin shi, kallonta yayi yace "Ina fatan dai a k'oshe kike?"

Shiru tayi, ba zata iya magana ba dan numfashinta ma taji ya sauya mata, bai sake magana saida suka shiga ciki ya sauketa kan gado ya kalleta, saida ya had'e alamar ba wasa ya nuna ta yace "Karki gusa daga inda kike."

Girgiza kai tayi cike da tsoronshi a idonta, dan daga jiya zuwa yau ya gundureta matuk'ar gundura, yana da shan kai da takurar tsiya, safiyar yau ma wanka ya dage saiya mata saida tayi kuka ta rok'eshi ya k'yale ta, yanzu kuma bata san me yake nufi da kawota kan gadon ba da rana tsaka haka. Tana kallo ya fita daga d'akin, ba jimawa ya shigo da faranti a hannunshi, yana zuwa ya aje farantin ya juya yasa makulli a k'ofa ya dawo, matsakaitan idonta ta zuba mishi tana had'e yawu masu d'aci d'aci, hannunta ya kamo ya shiga ban d'aki da ita, zip d'in rigarta ya zuge yana neman zage rigar daga jikinta, da sauri tasa hannayenta a k'irjinta tana kallonshi tana shirin fashewa da kuka, kallonta yayi ranshi a b'ace ya saketa, juyawa yayi ya d'auko soson wankanta, yana juyowa ya had'e hannayenta biyu, had'a ta yayi da bango ya matseta ya d'aure mata hannayenta ta baya, kafeta yayi da ido yana zare rigar daga jikinta, girgiza kai ta shiga yi kamar zata cire shi, lab'e baki tayi irin yaro zaiyi kuka hakan yasa shi cewa "Inban zubar miki da hak'ora ba Amna ki ce d'an iska ne ni, wallahi kiyi hankali dani kar kiga ina d'aga miki k'afa, dan kina amarya ne shiyasa."

Duk yanda ta so rufe jikinta kasawa tayi saida ya mata zigidir kamar yanda ta fad'o duniya, ba zato ba tsammani taji bakinshi a kan kan...


*Ma'assalm*


*Alhamdulillah*
09/09/2020 Γ  17:58 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*BADAK'ALA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_ (sai Allah)
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura...)_
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ *AHALI NA*πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦

©🌠

*πŸ‡³πŸ‡ͺTAURARIN NIGER..*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

βœͺ{T . N}βœͺπŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurarin-Niger-100155928500614/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_38_


Da k'yar ya rabu da ita ya d'ago kai ya kalleta, hawaye sharkaf a fuskarta, kuka taka sosai kamar dukan tsiya ya mata, wurga idonshi yayi irin ya damu d'in nan tare da ja baya, juyowa yayi ya fito daga ban d'akin yana fad'in "Zo nan."

Bata kula shi ba saida ya fita, rigarta ta mayar sannan ta wanke fuskarta ta fito, k'ura mata ido yayi harta zo ta zauna kusa da inda ya nuna mata, k'asa tayi da kanta bata da niyyar kallonshi, dan haka ya jawo farantin nan gabanshi ya d'auki wuk'a ya fara yanka lemun yana sha yana kallonta, lokaci lokaci yakan saci kallonta amma ta k'i d'agowa, aje lemun hannunshi yayi ya kamo nata hannun ya taso wa ida, zaunar da ita yayi akan cinyar shi hakan yasa ta rintse ido sosai, wuk'ar nan ya d'ora mata a wuya yace "Kalle ni."

Tana bud'a ido taga wuk'a ce ya aza mata bata san lokacin data kwamtsa k'ara ba tasa hannayenta ta rufe fuska, lumshe ido yayi sanda siririyar muryarta ta daki kunnuwanshi, gaba d'aya jikinshi saida ya amsa, bud'e ido yayi ya aje wuk'ar ya d'auki lemu, janye hannayenta yayi yasa mata lemun a baki, amsa tayi tana sake sunne kanta, cikin taushin murya yace "Amna, kafin a d'aura aurenmu na d'auka ni dake zamu zama kamar abokan juna ne, amma gashi daga jiya zuwa yau naga sai k'ara tsorata dani kike, ba haka nake so mu zama ba Amna, ina so naga kin zama komai tawa wacce zan iya samun farin ciki a wurinki, ina so ki zama sirrin farin cikina, zan so ki zama maganin damuwata, Amna burina shine ki zama mai share hawaye na a duk sanda suka kwaranyo, Amna ki zama aminiyata kuma abokiyar shawarata, Amna *banda kowa*, sannan *banda komai*, babu wanda yake *kusanta ta*, ina so ki zama tare dani a kowane hali kuma a kowane yanayi, na sani Amna gidan nan ko kuma nace duk ahalinmu suna min kallon wani mahaukaci kuma marar kunya fitsararre marar tarbiyya, amma...amma..."

Sunkuyar da kai yayi yana furzar da wata zazzafar iska daga bakinshi, rawa muryarshi keyi kamar zaiyi kuka, zuciyarshi bugawa ta fara yi da sauri sauri, ya jima kanshi na kallon k'asa kafin ya d'ago yana kallonta sai dai basu had'a ido ba, bud'a baki yayi a hankali yace "Amna ni ba mahaukaci bane, ni ba marar tarbiyya bane, sannan ina da kunya da nutsuwa, duk abinda nake yi ina sane nake yin shi, da gangan nake yi da fatan samun kusanci a wurin iyayena, amma..."

Da sauri yasa bayan hannunshi ya goge yar k'wallar data taho mishi, da sauri ya turata gefenshi ta fad'a kan gado shi kuma ya mik'e tsaye, juya mata baya yayi yace "Har yanzu ban yi nasara, na d'auka zasu iya zama dani suji dalilin da yasa na zama haka, sun kasa fahimta har yanzu, babu mai iya gane ina jin yunwa ko na k'oshi, to tayaya ne zasu iya fahimtar abinda ke zuciyata, na zab'i na fara fito dashi ne dan kar ciwon zuciya ya kama ni a k'arshe na mutu, bansan ya zanyi da su ba."

Juyowa yayi ya kalleta wacce ita ma ta k'ura mishi ido yace "Na gaza Amna."

Ban d'aki ya shige ya barta zaune, k'urawa k'ofar ido tayi tana tunani da nanata abinda ya fad'a, ta d'an jima a haka kafin ta d'aga kafad'u tare da tab'e baki ta mik'e ta koma madafa, girkin data jima da d'orawa ta ci gaba daga inda ta tsaya, sai dai jikinta a matuk'ar sanyaye yake tana tunanin halin da mijinta ke ciki, meye damuwarsa? Meye tsakaninshi dasu Ummy? Meye ainihin abinda ke faruwa? Hak'ik'a ko ita kafin yanzu tana jin yana matsa mata ne sosai, tana ji babu kunya a al'amuransa, yana da k'arancin nutsuwa wani lokacin, kenan duk yana sane yake yi? To me yasa? Me yasa namiji kamar Ammar ke saurin zubar da hawaye? Bayan ita shaida ce akan jarumtarsa wacce ke tattare da masifa da bala'i, a sanin data mishi ko baka nemi jaraba da shi ba shi zai nemeka da ita, a sanin data mishi baya da saurin kasawa haka, mutumin ne dake tsaye tsayin daka wajen ganin ya ci galaba akan abokin karawarshi, to amma meya raunata zuciyarshi har haka? Wannan amsa ce daya kamata tasan amsarta, domin yanzu alhakin farin cikinshi na wuyanta ne, da haka ta k'arasa girkinta ta fito ta gyara wurin cin abincin, ta nufi hanyar da zata sadata da d'akinta taga ya fito daga d'aya d'akin cikin k'ananan kaya, amma abun mamaki bai yarda ya had'a ido da ita ba.

Ya nufi hanyar fita tayi saurin cewa "Yah Ammar."

Tsayawa yayi ya juyo ya kalleta amma baice komai ba, shagwab'ar da fuskarta tayi kamar ta jarirai tace "Abincinka fa."

Har ga Allah da ya so irin d'aurawer nan, amma yanayin da tayi da fuskarta saiya sashi sakin murmushi, domin kuwa abinda ya zo masa a rai ita ce Hamna, wato Hamna tafi k'warewa wajen shagwab'ar bubbuga k'afafu, ita kuma wannan gaba d'aya take canza fuskarta da yanayinta idan zatayi ta ta shagwab'ar, d'aga gira yayi yace "Kenan saida kika dafa abincin?"

Nufowa kanta yayi yana k'ok'arin cire belt d'in shi yana fad'in "Idan na rugurguza miki jiki gobe ba zaki sake bijirewa abinda na fad'a ba."

Tana ganin ta durk'ushe ta had'e hannaye biyu tasa kusa tana fad'in "Dan Allah yah Ammar kayi hak'uri ba zan k'ara ba wallahi, idan kana so ma yanzu sai nake na zubar da wanda na dafa, dan Allah karka dake ni wallahi bana son duka a jiki na."

Ganin ya kawo daf da ita amma bai cire belt d'in ba yasa ta rintse ido, yana zuwa yasa hannayenshi ya tallabota yana dariya yana kallon fuskarta, ganin bata bud'a idon ba tsabar tsorata da tayi yasa shi rumgumeta jikinshi yana fad'in "Amna yanzu fa na gama fad'a miki, shin idan ban zolayeki wa zan zolaya?"

Shiru tayi daga kukan da take rerawa ta bud'a ido ta d'ago kai ta kalleshi, yanda idonsu suka had'u ne yasa kowannensu jin wata wutar tsartsatsi ta bulbulo daga zuciyarsu, murmushi ya dalla mata ya tallabe fuskarta yace "Irin rayuwar da nake so muyi dake kenan Amna, mai cike da mutuntawa, farin ciki, annashuwa, k'aunar juna, tsokana da zolaya."

Sunkuyar da kanta tayi a cikin k'irjinshi, shi ma kuma yana jin haka saiya k'ara kwantar da ita yana shafa kanta yana sauke mata numfashi a kai, sanyanyen turarenshi mai tayar da tsikar jiki da kuma kwantar da hankali take shak'ar k'amshinsa, luf tayi kamar mai son yin bacci tare da zura hannayenta ta baya ita ma ta d'an rik'e shi amma ba sosai ba, tunanin duniya take a daidai wannan lokacin.

Ammar dai, yayansu dake matuk'ar firgita lissafinsu, wanda basa fatan a kai mishi k'ararsu idan sunyi laifi, wanda

Please Login or Register in order to submit comment