Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

kiyaye hanya yah Ammar, Allah ya baka abinda kaje nema, Allah ya tsare mana gabanka da bayanka, saika dawo."

Tana fad'a ta d'aga masa hannu alamar bye bye ta shige ciki, da kallo ya bita yayin da yake jin wani farin ciki na nuk'urk'usar zuciyarshi, wani murmushi ya saki wanda shi kanshi ya manta rabon da yayi irinshi, ba tare daya daina murmushin ba ya ja mota sai asibiti.

➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️

Maryama da Iklima sun duk'ufa shirye shirye na gyaran jikinta da sauran abubuwan, kulawar da kakarta da kuma mahaifiyarta ke nuna mata kamar yanzu suka haifeta, haka ma Huda soyayya suke nunawa yarinyar sosai, wanda a yanzu Huda bata da aiki sai fad'in Abbanta Jibril wanda ya yanka mata saniya, yau ma asibiti suka shirya suka tafi aka cire mata robar da aka saka mata dan hana d'aukar ciki, a hanyarsu ta dawowa Iklima ke cewa "Yanzu Mari kin shirya haihuwa kenan da zaran kin shiga gidan?"

Murmushi ta mata tace "To me zanyi idan ba haihuwar? Bana da budurcin da zaiga mutumci na da shi, nasan ina shiga gidan soyayyar da yake nuna min zata ragu, kinga kuwa kafin na fara fuskantar tasku k'wara ina shiga na fara dire masa 'ya'ya."

"To amma meyasa ba zaki fad'a masa gaskiyar waye wannan d'an uwan nasa ba? Ina ga hakan zaifi."

Murmushi ta sakeyi tace "Zan fad'a masa, amma bayan naje gidan."

A hankali Iklima tace "To Allah yasa alkairi."

➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️

Kawu Mamu ma tuni yaje rugagensu yayi shelar bikin Zeituna, wacce yanzu a gidan kamar sarauniya, wani lokacin kawu da kanshi ke kawo mata abinci har bukkarsu, wani lokacin ma idan akayi tuwo sai yace ba zata ci tuwo ba, da kanshi zai fita ya siyo mata tsire ko gasassar kaza ya kawo mata, Zeituna saidai tayi wanka ta sake kaya ta koma ta zauna kan katifar Jumare da yanzu kawu yace ta zama ta ta har a d'aura aure, yau dai kam kanta ya sake kullewa da taga yan uwa na zuwa wai gobe aurenta da lieutenant, jira kawai take taga goben tayi saita tabbatarwa da kanta, sai dai kuma ana haka kawu Mamu ya sanar da ita Alhaji yace anjima da dare lieutenant zai zo su gana, hakan yasa ta k'arasa wuninta da muguwar fargabar had'uwarta da lieutenant d'in.

➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️

Yana sauka daga aiki da rana kai tsaye douanes ya wuce, yana fitowa daga mota ya tunkari ofishin, saida wani yaron lieutenant yace masa yana ganawa da bak'i, amma saiya nuna mishi d'an shi ne kuma abune na gaggawa, yana shiga ofishin babu sallama ya same shi zaune tare da wasu manyan alhazzai biyu, tsaye yayi yana kallonshi inda lieutenant ya mik'e da mamakin rashin sallamarshi ko neman izinin shiga bare gaishe da mutanen, cikin jin haushi yace "Wai kai mahaukaci ina ne? Ya zaka shigo wuri babu izini babu gaishe da mutane ka wani yi mana tsaye? To uban wa kake bi bashi anan? Me ma ya kawo ka?"

Kawar da kanshi yayi yana kallon mutanen da suma suke kallonshi, abun mamaki sai lieutenant yaga sun mik'e suna bawa Ammar hannu da fad'in "Likita, kaine anan? Ya kake ya aiki?"

Ba fara'a ya amsa da "Alhamdulillah."

D'ayan ne yace "Yallab'ai ko yaron wajenka ne?"

Cikin ji kunyar amsawa ya d'an jinjina kai alamar eh, murmushi sukayi sai d'ayan da yace "Ko da nace, ashe likita gadon mutumci da kirki yayi tun daga gida, ai likita na ne dake duba ni, yana da son mutane wallahi da jansu a jiki indai aka ce majinyacinshi ne kai."

Kallon lieutenant sukayi suka bashi hannu suka ce "Ba damuwa yallab'ai, zamu jiraku a waje harku gama, nasan abune mai mahimmanci ya kawo shi."

Yana fad'a suka fita suka barsu, cikin jin haushi da halayarshi ya koma ya zauna yace "Meya kawo ka nan?"

Ba tare daya zauna ba yace "Abba ina son sanin wani abu ne, na tambayi Ummy tace na zo na tambayeka, shiyasa na zo."

Fuska a d'aure yace "Menene?"

A tak'aice yace " Wani laifi Ummy tayi daka yarda zaka mata kishiya?"

Da k'arfi ya buga teburin gabanshi ya mik'e yana fad'in "Shirmen banza! Dama abinda ya kawoka kenan? Uwarta ka ce ta turoka ka min wannan tambayar?"

Fuska a murtuke yace "Babu ruwanta, kawai ina son sani ne, idan akwai laifin data maka ka fad'a min?"

Nuna mishi k'ofa yayi yace "Banda lokacin wannan haukan naka, ka b'ace min da gani daga nan."

Jinjina kai yayi yace "Shikenan na tafi." Fita yayi daga ofishin inda lieutenant ya zauna yana dafe kai, daga nan *transa mall* ya wuce dan sunyi magana da abokinshi d'aya daga cikin manyan mall d'in, yana zuwa akwatinan daya siya kawai aka saka mishi a boot ya biya kud'in, daga nan ma wajen masu goro ya nufa ya siyo kafin ya nufo gidan daf da la'asar.

👏👏👏
25/06/2020 à 11:27 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*SANIN MASOYI*
_(sai Allah)_
*BAYA DA K'URA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

💞 _*MASOYA NA*_💕


_Bismillahir rahamanir rahim_

🇳🇪 *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_14_

Wuyan rigarshi ta cakuma tana jijjigawa ba tare data daina wannan kururuwar ba, wayar hannun nata ta kwad'a mishi a kai ta sake cakumar rigarshi ta fara fad'in "Ni! Ni? Ni Abbas?"

Rik'e hannayenta yayi ya fizgesu daga rigarshi ya sunkuya zai d'auki wayar data fad'i, ba zato ba tammani ta turashi kan gadon ya fad'a da k'arfi, ya kalleta da jin haushi zaiyi magana sai kuwa saukar mari katssssss, dafe kunci yayi da wani irin mamaki a fuskarshi na irin yaushe nayi lalacewar da har zaki mare...? Bai gama ma kanshi wannan tambayar ba yaji ta sake shak'ar wuyanshi tare da yin tsalle ta haye ruwan cikinshi ta shak'e mishi wuya sosai, a yanzu kam ya fahimci hankalinta baya tare da ita, hakan ne yasa shi rik'e hannayenta gam ya birkita da ita sai gashi kan ruwan cikinta yana k'are mata kallo ba tare daya saki hannayenta ba cikin d'aga murya yace "Meye haka? Me yake damunki ne? Baki da hankali ne?"

Wani k'arfin tsiya ne ya zo mata wanda yasa ta ture shi daga kanta a dole ya sauka samanta ita ma ta taso da k'arfi tana fad'in "Ni ce ma bana..."

Sai kuma ta kasa magana saboda yau zuciyar ta taso gaba d'aya, hannayenta ta kai zata sake shak'ar shi alamar fa ita ranshi take nema sai yayi saurin rik'e ta ya had'e hannayenta biyu ya matse ya jawo k'ugun ta ya had'a da nashi haka ma ya had'a goshinsu da hancinsu wuri d'aya, lumshe ido yayi yace "Shiiiiiiiiii, Sam, meya faru? Meya sameki ne? Ki nutsu ki fad'a min."

Manyan manyan idonta ta sauke cikin nashi wanda suka mata jawur abun tsoro, bud'a baki tayi tana so tayi magana amma zuciya a wuya take, sai wata shashek'a ta dinga saukewa kamar tana fitar rai wanda hakan ya matuk'ar tsorata shi, k'irjin ta ya kalla wanda keyin sama da k'asa da k'arfi da kuma sauri, idonta sun k'ara fitowa waje sosai kamar dai mala'ikan d'aukar rai ne ke cire nata ran, da sauri ya zaunar da ita kan gadon ya durk'usa gabanta ya tallabo fuskarta ya d'ago kanta ya had'a bakinshi da nata, lumshe ido yayi a hankali ya shiga tsutsar bakinta har yayi nasarar kamo harshenta yana tsotsa, ita ma ruf ta rufe idonta saboda jin numfashinta na daidaituwa, saida taji komai ya fara saisaituwa shi kuma ya fara mata tsutsa dake nuna ya fara d'aukar caji har ya fara matsa na shanunta ya zura d'aya hannun a bayanta zai zare mata zip, bud'e ido tayi ta sauke a lumsassun idonshi, bai ankara ba ta kama leb'enshi na k'asa da iya k'arfinta ta datse hak'oranta ta cije shi, jin cizo a bazata yasa shi tureta da k'arfi ya mik'e yana mata wani kallo, mik'ewa tayi tana kallon idonshi da sukayi jawur saboda rad'ad'in cizon, giftashi tayi zata fita daga d'akin ya rik'o hannunta yace "Wai meye haka? Aljanu ne dake kome?"

Kawar da kanta tayi na wucen gadi kuma ta kalleshi, a k'alla ta d'auki minti ashirin tana kallon k'wayar idonshi ta kasa d'aukewa tsabar mamaki da al'ajabi, shi ma kuma kallonta yake yanayinta na bashi tsoro, da k'yar ta iya nuna kanta tace "Ni Abbas? Ni zaka tozarta? Ni zaka ciwa mutumci? Abbas me nayi maka a rayuwa? Na gaza wajen nuna maka soyayya ne, ko kuma na gaza wajen gamsar da kai ne? Shin baka jin dad'in tarayya dani ne da har zaka kawo min karuwa gida na? A cikin gida na Abbas? A d'akin bak'i na?"

Juyawa tayi zata fita ya rik'o ta tare da shan gabanta, zaiyi magana ta nuna shi da yatsa fuska a had'e a murtuke tace "Zaifi ka rufe bakinka, idan mun had'u a lahira a mana hisabi."

Cikin takon k'arfi ta juya ta fita daga d'akin ya bita da kallo, dafe kai yayi ya zauna bakin gadon yana shafa kanshi, da sauri ya kalli wayar dake k'asa tare da d'aukar ta ya kunna, ganin wannan vidéon yasa ya jefar da wayar yasa hannu yana shafa gemunshi, ya d'auka abin yayi sauk'i amma sai yaji bud'o k'ofar daya sake hargitsa masa lissafi, mik'ewa yayi ya juya yana kallonta, ganin ta nufo kanshi da wuk'a a hannunta yasa shi saurin tunkararta yana neman rik'e hannayenta, da yake masifa take ji da bala'i saita zame tare da wawura mishi wuk'ar sai a damtse, cikin sautin wahala ya dafe wurin tare da juyowa gareta ya furta "Ashhhhhh."

Ido cikin ido suka kalli juna ta masa murmushi tace "Wallahi da haka zan dinga yankan namanka har ka mutu, Abbas ni zaka wulak'anta."

Tayi kanshi ya cabko hannun mai wuk'a ya murd'e sosai yasa d'aya hannun mai ciwo wanda jini ke zuba ya fizge wuk'ar, jefar da ita yayi ita ma ya cillata kan gado ya nuna ta da yatsa yana fad'in "Sameera ki saurare ni mana, ya zaki dinga abu kamar wata marar hankali? Kar kisa na ji miki ciwo a banza mana, shin zina a kaina aka fara? Ko kuma kin saurareni na fad'a miki abinda ya faru ne? Haka kawai zakkk..."

Bai k'arasa ba ta mik'e da k'arfi tana girgiza kanta gashinta duk ya yamutse tasa hannayenta ta tura shi baya, bubbuga k'irjinta tayi cikin disashewar murya tace "Ni ce marar hankalin? Kai ne mahaukaci bani ba, kai da ka zubar da mutumcinka wajen k'aramar yarinya, kai ko kunya baka ji ko kunya ba? A cikin gidanka ka shigo da karuwa, shine harda k'aryar cewa wai ka bigeta ne a hanya shine ka taimake ta, kaji kun..."

Wuyan rigarta daya finciko yasa ta yin shiru, saida ya kai bakinshi saitin nata bakin yace "Kisan me kike fad'a min Sameera, bana son maganar banza, ki zauna ki saurare ni."

Ya k'arashe da sakinta yana nuna mata kan gadon ta zauna, fashewa tayi da dariya ta nufi wajen dressing miror d'in shi ta d'auki kwalbar turare mai kyau da tsadar gaske ta buga a madubin tace "Wai umarni kake bani? To ai yanzu ni bana ganinka da wani mutumci ko kad'an wallahi, kai Abbas ba..."

Marin daya zabga mata a fuska yasa ta dafe kunci tana kallonshi, da yatsa ya sake nunata yace "Wallahi ni banyi lalacewar da har haukanki zai k'are a kaina ba, Sameera kisan ni mijinki ne bai kamata ki d'aga muryarki sama da tawa ba bare har ki dinga fad'a min duk shirmen da ya zo bakinki, tabbas ina sonki, amma son da nake miki ba shi zaisa na miki shiru ki ci mutumci na ba, wallahi tsaf zanyi k'asa k'asa dake a wurin nan, iskancin banza kawai, zuciya kanki farau, ko ke kad'ai ce me zuciya a k'irji? An fad'a miki kowa baya jin zafi ne? Wallahi ba dan tausayinki ba da rashin sabo a gare ni da dukan tsiya zan miki har ki dawo hankalinki, amma duk da haka zan iya hukuntaki ta hanyar data fi dacewa dake."

Hannunta ya kamo da niyyar wurgata kan gadon sai kuwa ta d'auko wata kwalbar turare doguwa, cillata yayi kan gadon ya bi kanta ya haye yasa k'arfi ya b'arka rigarta rantsetsen leshenta wanda yaji kud'i da d'inki mai kyau, shi kanshi yayi mamakin yanda ya iya raba rigar biyu saboda kark'on leshin, zai fizge bras d'in ta yaji saukar kwalbar nan a kanshi wanda take jini ya sake gabce mishi a kai, gefenta ya fad'a ya dafe kai ya rufe ido sosai, mik'ewa tayi cikin k'arajin murya tace "Wallahi ka gama kusanta ta Abbas, indai ina raye ba zaka sake shigar da banzar..."

Jin an shigo d'akin ne yasa ta shiru ta kalli k'ofar, Khalifa ne ya shigo wanda hayaniyar iyayen nashi da jin lallai ba lafiya ba yasa shi shigowa, a hankali ya tako har ya tsaya gabanta yana kallonta, a tsawace tace "Lafiya? Meya kawoka?"

Juyawa yayi ya kalli Abbas daya d'ago ido d'aya ya kalli Khalifa, matsawa yayi kusanshi yace "Dady ciwo kaji?"

D'auke hannunshi yayi wanda yasa jini sake gangarowa har yana neman rufe mishi ido ya mishi murmushi ya girgiza kai alamar a'a, juyawa yayi ya kalli Sameera dake k'ok'arin cire rigarta yace "Ammie meya samu Dady?"

Tsayawa tayi daga shirin gyara rigar ta nuna mishi k'ofa tace "Dan ubanka fice min a d'akin nan kafi na ji maka ciwo."

Wani kallo Abbas ya mata na mamaki, shi kanshi zai so Khalifa ya fita danya nuna mata shi ba sa'anta bane har yanzu, cikin sanyin jiki Khalifa ya juyo ya kalli Abbas yace "Dady dan Allah ku daina fad'a, duk gidan nan fa ana jin muryoyinku, mun saba ganin kuna rigima da fad'a, amma waccen fad'an naku yana saka mu nishad'i wani lokacin ya kuma bamu dariya, amma wannan ba kamar kullum ba, dan Allah Dady karka biyewa Ammie."

Kanshi ya dafa zaiyi magana Sameera tace "Iyee! Khalifa ni zaka wa iskanci? Wato halin ubanka ne zaka d'auka ko? Shine ma zaka ba hak'uri ba ni ba? Kasan me yayi kuwa? Bara ka gani to."

Jujjuyawa ta fara kamar mahaukaciya tana neman wayar nan, can ta hangeta kusa da k'ofar toilet inda Abbas ya cillata, da sauri ta d'auko ta bud'a vidéon nan zata tunkaro Khalifa tana fad'in "Dubi tsiyar da mahaifinkkk."

Marin da Abbas ya wanka mata lafiyaye a kumatu yasa ta sakin wayar ta fad'i ta kaiwa k'ofar toilet d'in karo, a fusace yasa k'afa ya take mata k'afafu biyu ya juyo ya kalli Khalifa ya nuna mishi k'ofa yace "Fita anan, ka umarci k'annan ka ku je gidan Naseer."

Jiki a sanyaye Khalifa ya nufi k'ofa yana kallon mahaifiyarshi dake yashe k'asa, saida ya kai k'ofa zai rufe yace "Dan Allah Dady k..."

A tsawace Abbas yace "Ka fita nace."

Da sauri ya rufe k'ofar sai hawaye, da gudu ya fita neman taimako gashi kuma Ammie bata nan, a k'ofar gida ya samu Abba ya sanar dashi babu lafiya a ciki fa, a sukwane suka taho tare...

Yana ganin fitar Khalifa ya cakumi gashinta ta baya ya buga kanta da bangon wurin, hakan ya haddasa mata sakin k'ara mai k'arfi da sauri kuma ya sunkuya ya sa hannunshi ya rufe mata baki, da k'afa ya tura k'ofar ban d'akin ya sake cakumar gashinta ya jata cikin ban d'akin, yana zuwa k'aton bahon wankan dake cike da ruwa ya kinkimeta sai kuwa ji kake tamjam ya sakata ciki, da k'arfi ta yunk'uro tana neman tsira ya tausa kanta ciki, hannayenshi ta shiga k'ok'arin b'anb'arewa daya taushe mata kai, amma dayake Abbas yana son ya koya mata hankali ta gane shine gaba ba ita ba, a kullum tana tunk'aho da jiji da kanta da zuciyarta da jarumtarta, rufe ido yayi ya k'i sakinta yana kallon yanda take son ta fito ta numfasa, amma ya kawar da kai daga kallonta yana fad'in "Wai ba kasheni zakiyi ba? To ni zan fara kashe ki in ya so mu had'u a lahira a mana hisabin,."

Kallonta yayi yace "Wai ni kam ba kece Sameera mai zuciya ba da d'aukar fansa? To ina zuciyar ta ki? Shin ba kece ba kya yafiya ba duk abinda aka miki sai kin rama? To gani ki rama mana, ki fito ki rama nace."

Saida yaga ta galabaita sosai ya saketa ya juya zai fita daga toilet d'in, da k'arfi ta yunk'uro ta zuro kanta waje tana tarin wahala da kakarin amai, juyowa yayi yana kallonta wani tausayinta ya baibayeshi da tuna cewa fa shine mai laifin, dawowa yayi ya tallabota ya d'auko ta ya fito da ita har kan gado ya direta, kallon fuskarta yake yana gyara mata gashinta daya had'e wuri d'aya yana zubar da ruwa, tallabo fuskarta yayi yana kallon cikin idonta cike da rarrashi yace "Dan Allah Meerah ki kwantar da hankalinki muyi magana, ni da ke yan uwan juna ne kuma miji da mata, ki bani had'in kai mana mu fahimci junanmu, shin kina ganin wannan abinda kike har kina so ki kashe shine mafita? Sam, zaki iya rayuwa ba tare da ni ba?"

Yanda ya kafeta da ido ya nuna amsa yake jira, da wani wahalallen kallo ta kalleshi da manyan idonta wanda suka canza gaba d'aya sai lumshewa suke, cikin hard'ewar hak'ora ta bud'a baki tace "Kashe ka yanzu shine kawai mafita, dan inba gawarka na gani ba hankali na ba zai kwanta ba, idan ba gani nayi ka daina numfashi ba ba zan tab'a farin ciki ba, Abbas dole ka mutu, dan ba zan iya ci gaba da zama da kai ba, to akan me ma zan zauna da kai? Ni b'ata shekaru ina killace maka kaina, sai kawai na wayi gari naga hoton iskancinka kai da wata, watan ma kuma har cikin gidan da yake mallakina, Abbas ni zaka rainawa hankali da wata banzar k'aryarka ka shigo min da karuwarka har gida, gaban iyayenka da yaranka da kuma ni, ni Abbas? To me kake so nayi idan ba kashe ka ba?"

Girgiza kai yayi yace "Yanzu kenan ba zaki saurare ni ba, shin kinsan ma wacece wannan yarinyar? Meerah daga had'uwar mu da ita har abinda ya faru tsakaninmu duk shiri ne, shine da suka shirya dan ruguza mana rayuwa, shiri ne dan tarwatsa rayuwata da kuma taki data yaranmu, idan kin tuna fa washe garin ranar da abun nan ya faru aka nemeta aka rasa, shin kinsan nawa ta nema a hannu na tana blackmailn d'ina? Ki farka daga bacci Sam, idan ba haka ba sunyi nasara a kanmu a karo na biyu."

Mik'ewa tayi tace "Ban damu nasan wacece ita ba, abinda na sani kawai shine ita ce wacce ta kwanta da mijin da nake ganin kamar nawa ne ni kad'ai, Abbas a tunani na na d'auka ko aure kayi matarka ta sunna zakaji kunyar kwanciya da ita a gidan nan, saboda ina tunanin kana so na kuma na gama maka komai ta yanda zakaji kunyar kusantar wata mace, ashe ba haka bane, da karuwa ma zaka iya wulak'anta ni, ashe kasan abinda kake aikatawa kenan shiyasa ka d'aga hankalinka daga ganin hoton Raihan wanda ita nata mai sauk'i ne ma akan naka, haka ka dinga shirgar min 'ya kamar ka samu jakarka duk dan kana tsoron kar tayi abinda kayi, kasa mun aurar da ita a gaggauce ko mak'wabtanmu ba duka suka san da aurenta ba kamar wata marar gata, ka had'a ta da wanda baka san halinshi ba kuma tayi nesa damu, duk dan kana so ka b'oye laifinka."

Juyowa yayi zaiyi magana a lokacin su Abba suka shigo a hargitse, tsayawa sukayi suna kallonsu da mamaki, Abba ne ya iya cewa "Abbas lafiya? Me yake faruwa ne haka?"

Murmushi Abbas yayi ya d'an dafe ciwonka da duk taji mishi yace "Ba komai Abba, kawai dai..."

Shiru yayi hakan yasa Sameera mik'ewa ta kalli Abba tace "Abba ba gaskiya bane, baya so ya fad'a ne saboda abun kunyar daya aikata ba k'arami bane, amma ni zan fad'a maka."

Matsowa ta sake yi inda Abba da Khalifa suke kallonta da ido, Abbas kuma matsowa yayi kusanta yana so ta bud'a bakin zatayi magana ya dakatar, dan ba zai lamunci ta fad'i abin nan ba a gaban d'an shi na cikin shi, sam ba zai jura ba ko da hakan na nufin ya mata dukan da zai sumar da ita ne, kallon idon Abba tayi ta kalli Abbas tace "...


👏👏👏
25/06/2020 à 11:27 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*SANIN MASOYI*
_(sai Allah)_
*BAYA DA K'URA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

💞 _*MASOYA NA*_💕


_Bismillahir rahamanir rahim_

🇳🇪 *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_13_


Yana isa ya sameta a ciki tsaye bakin wata bishiya da lemu a hannunta tana sha, inda Harira ke binshi cikin iya takonka ba tare daya sani ba, yana zuwa ya tattare babbar rigarshi kamar zaiyi dambe da ita cikin fad'a yace " Meye kuma yanzu? Meyasa kika ce na zo nan? Ko kin manta da na biyaki kud'in da kika nema?"

Kallonshi tayi tana murmushi tace "Dady..."

Yanda ya nunata da yatsa yasa tayi shiru, ido ya zaro mata yace "Karki sake bakinki ya sake kirana da ubanki, ni ba ubanki bane."

Ita dai murmushi take kafin ta fito da wayarta ta rik'e a hannu tana jujjuyata tace "Ok, dama nace ka zo mu had'u ne saboda wani tunani da nayi, na fahimci waccen farashin nayi maka sauk'i sosai, shiyasa yanzu na zo dan na fad'a maka ina buk'atar wasu kud'in."

Cikin b'acin rai da hassala ya shak'i wuyanta da duka hannayenshi biyu ya had'a ta da jikin bishiyar cikin d'aga murya yace "Me kike nufi? Me kike so ki mayar da ni? D'an iska ko me? To ba zan bayar ba, kije kiyi duk abinda zakiyi, abun kunya ba'a kaina aka fara ba."

Ma'arufa da tunda ya shak'eta ta saki waya da jaka da lemun hannunta ta fara kakarin numfashi, sai dai a wannan d'an tsakanin kuma sai wani ciwon ciki daya taso mata na ajali, dafe cikinta tayi tana matsawa tana so ma tayi kuka da ihu amma Abbas ya shak'eta sosai, shi kuma duk a ganinshi wahalar shak'ar daya mata ce, ganin jini ya fito ta hancinta ne yasa shi sakinta sai kuma ta fad'i gabanshi, juya mata baya yayi yana huci da son saisaita nutsuwarsa suyi magana, juyowa yayi da k'arfi zaiyi magana sai kuma ya ga har yanzu bata tashi ba, baya ya ja yace "Ki mik'e, we need to talk."

Shiru ko motsi ba tayi ba hakan yasa ya d'an sunkuya ya daddab'a kafad'arta yace "Dake nake magana."

Shiru babu amsa daga Ma'arufa, turata ya d'an yi hakan yasa fuskarta ta fito tayi rairai tana kallon sama, ganin idonta a kakkafe bakinta bud'e daga yanda take neman numfashi ga kuma jini a hanci, tsoratar da yayi yasa shi wajen yayi baya da k'arfi harya fad'i zaune a wurin, tabbas gawa ce wannan, na kasheta ko me? Da sauri ya rarrafo ya fara jijjigata yana fad'in "Dan Allah Ma'arufa, karki mutua wannan halin kuma a hanu na, kar zunubin ya min yawa mana, please ki tashi Ma'arufa."

A tak'aice ya d'auki minti talatin a wannan halin yana tausa k'irjin ta da nufin numfashinta ya dawo, amma shiru babu labari, haka kawai ya fara hawaye da sambatu barkatai yana ji kamar ya kashe kanshi, tunani ya shiga yi na mafita kafin daga bisani zuciyarshi ta yanke miki kawai ya jefar da gawarta, yana gamsuwa da haka ya mik'e ya cire balaluwarsa ya jefata cikin mota, sam ya manta da wayarta da kuma lemun da
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment