Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'aki, had'e fuska yayi kamar ba shine ke dariyar nan ba ya juyo ya d'auki sallaya yana shinfid'awa yana fad'in "Kaji min yarinya, ku mata kun d'auka ku kad'ai kuka iya kwarkwasa ko, to ni ma da nayi niyya dana zama karawi."

Duk da ta gama alwalar amma saita kasa fitowa tana tunanin abinda zata tarar, ganin shiru yasa shi sanyo kai cikin ban d'akin, had'a ido sukayi tana tsaye gaban madubi ta jinjina a bango, ba tare daya shiga ba ya zura hannunshi ya kamota suka fito, suna zuwa ta samu hijabi ta saka suka kabbara sallah, suna kammalawa daga nan ya juyo ya fuskanceta, hannunshi ya zura ya d'an janye hijabinta daga kanta ya dafa kan nata ya karanta mata addu'a "Allahumma ini as'alukha khairuha wa khairu ba jabaltaha alaihi, wa a'uzu bika min sharriha wa sharri ma jabaltaha alaihi."

D'auke hannun yayi ya k'ara gyara zama ya k'ura mata ido yace "Amna, yau gani ni dake a d'aki d'aya a matsayin mata da miji, wannan wani al'amari ne daga ubangiji, domin kuwa a rayuwata ban tab'a tunanin zaki zama matata ba, sai dai ina farin ciki da kasancewarki matata d'in, dan zan iya cewa ko Ummy data raineku bata kaini saninku ba, yarinyar kirki ce ke, dan haka ina fatan Allah ya bamu zaman lafiya."

Cikin sanyanyar murya tace "Ameen."

K'arawa yayi da cewa "Amna, nasan kuna zuwa islamiyya, zan iya sanin zurfin karatunki?"

Ba tare da sun had'a ido ba ta fara mishi bayanin matakin karatunta, kallonta yayi yace "Amma me yasa baki fara karanta arba'una hadisi ba har ki fahimce shi sannan ki fara bulugul maram? Duk littafin hadisin da zaki karanta idan baki karantashi ba ba zaki fahimci abubuwa dayawa ba, domin kuwa wasu malaman sunce gaba d'aya kafatanin musuluncin yana dunk'ule ne a cikin hadisai k'waya talatin, kuma wad'annan hadisan guda talatin suna cikin littafin arba'una hadisi, yayin da wani malamin shi kuma yace ai gaba d'aya addinin ma yana cikin hadisi guda d'aya ne tak, kuma wannan hadisin shima yana cikin littafin, kinga kenan indai har kina so ki fahimta zaifi miki ki fara dashi, idan kikayi nasarar kammalashi saiki fara da muwadd'a, kin gane?"

A hankali ta jinjina kai alamar eh, mik'ewa yayi tsaye yace "Ki d'auko ledar ce ki juye abin ciki a faranti."

Mik'ewa tayi ita ma ta d'auko ledar shi kuma taga ya fita, ita ma fitowa tayi inda ta tabbatar nan ne madafa ta shiga, d'auko faranti tayi da cup biyu ta dawo, har ta juye ta zuba komai shiru bai dawo ba, bakin gado ta zauna tana jiran ya shigo taji yanda zasu k'are dashi, ai kuwa yana shigowa ta kalleshi lokaci d'aya ta sauke idonta k'asa, farin dogon wando ne jikinshi na zallar kad'a da farar singlet, saida ya aje wayarshi a hannu ya k'araso yana fad'in "Wai ke me kike nufi? Kunya ce kike ji? Ina ce dai tare muka rayu gidan nan, kin sanni tun lokacin ina yawo da gajeran wando, haka nima na sanki tun ina saka miki wando da kaina, to kuma miye na wannan nok'ewar, dallah tashi ki canza kaya ki zo ki ci abinci cikinki yayi nauyi, idan ba so kike ki b'ata min rai ba yanzu na karya miki k'afafu."

Tashi tayi da sauri ta nufi wajen kaya ta kuma nufa ban d'aki, ganin duk ta diririce yasa ya kama hannunta har ban d'aki, gashi dai sun shigo kuma babu alamar zai fita, cire mata hijabin jikinta yayi da d'an kwali ya jefosu kan gado dan bai rufe k'ofar ba, juyata yayi ya kama zip d'in rigarta ya cire, sake juyota yayi ya kama rigar zai zageta ta k'asa, da sauri ta d'an rik'e rigar tana kallonshi a tsorace, kallonta yayi gira a had'e yace "Meye? Amna kina so na ci uwaki ne a daren nan?"

A hankali ta girgiza masa kai idonta har sun cika da k'walla, ko a jikinshi sai ma kama rigar da yayi ya zuge mata ita ta k'asa, sunkuyawa yayi ya fitar da rigar daga k'afafun ta ya d'ago, Amna da tuni tasa hannayenta ta rufe jikinta ta rintse ido, kamar daga sama taji yace "Wow, 'yar k'anwata ce ta zama haka? Lallai kun girma, gobe dole naje na yiwa kakarku godiya, domin kuwa ta min zab'in daya dace dani, kamar tasan irin yanda nake son matata ta kasance."

Sunkuyar da kanta ta sake yi shi kuma bai kula ma da tsiyar da take ba, rumgume hannayen shi yayi a k'irji yana k'are mata kallo, duk da ta rufe abubuwa dayawa amma bai hana shi gane wasu abubuwan ba shima, fad'in k'ugunta da cikinta yasa mazaunanta suka zama masu d'aukar hankali, fuskarta ya koma kallo d'an k'aramin bakinta da kurmin idonta, wata tausassan dariya yayi a daidai lokacin Amna ta gaji da yin shiru ta bud'a ido a hankali, suna had'a ido ta sake rufe ido ta juya baya, hakanne ya bashi damar kallon kayan da suke d'aukar hankalinshi, jefo rigar yayi bata ko sauka akan gadon ba, rumgume ta yayi ta baya yasa hannun dama yana shafa mazaunanta, har ga Allah inhar zai fad'i gaskiya a lokacin daya ruk'unk'umeta saida yaji yanda jikinta ke rawa, amma kuma tsikar jikinta duk ta tashi, dan kar ya saba mata da tsoronshi yasa ya taushe abinda yake ji a lokacin, sakinta yayi yace "Maza kiyi wankan ki fito ina jiranki."

Bata iya cewa komai ba saida taji ya rufo mata k'ofar, ajiyar zuciya ta sauke idonta na zubo da hawayen da suka mak'ale, da k'yar ta iya wanka ta fito, nan ma ta sameshi kwance akan gadon kamar jiranta yake, saukowa yayi ya bud'a wajen kayanta ya shiga bincika, wata riga ya samu iya gwiwa tsayinta fara k'al tare da wandonta a jikin rigar, d'aukowa yayi ya juyo gareta tana zaune tana shafa mai ya rufe robar man yace "Kina shafawa ne saboda jikinyi kiyi tsantsi na kasa kama ki da kyau, muguwa."

Ita dai k'ala ba tace ba sai turare daya d'auka yana ta fesa mata har saman kai da bayanta saida ya feshe, mik'ar da ita yayi tsaye ya cire wandon daga rigar ya durk'usa k'asa irin dai yanda ake wa yara in za'a saka musu wando, k'in d'aga k'afar tayi hakan yasa shi d'agowa ya kalleta, cikin razananiyyar muryarta tace "Dan Allah yah Ammar."

"Dan Allah me?" Ya fad'a ba tare daya daina kallonta ba, sake marairaicewa tayi tace "Zan saka da kaina, kayi hak'uri."

Tsaki yayi yace "Malama d'aga min k'afar ki kafin na tsagaki gida biy..." Tun bai k'arasa fad'a ba ta d'an d'aga k'afa a hankali ta zura, kasa d'aga d'aya k'afar tayi ta fashe da kukan shagwab'a tace "Dan Allah yah Ammar ka barni zan saka, wallahi ni..."

Tsaye ya mik'e yace "Ke me?"

Bayan hannu tasa tana murza ido tace "Kunya nake ji wallahi."

"Kunya?" Ya fad'a da k'arfi, ta hudar yatsunta taga yana k'ok'arin kwance d'aurin zariyar wandonshi yana fad'in "To bari na tub'e nima ki ganni sai ki daina jin kunyar, kinga kenan anyi 1-1."

Da saurin bala'i ta sunkuya ta rik'e hannayenshi tana fad'in "Yi hak'uri yah Ammar dan Allah, ba sai ka cire ba."

Kallonta yayi ya tab'e baki inda ta k'urawa fuskarshi ido, tunani take wai haka kowane ango keyi a daren farkonsa? Ko kuma ita ce amaryar da tayi wannan rashin sa'ar? Ita kam da zai barta ta kwanta ta huta da taji dad'i, amma bata ga alamar hakan ba a tare dashi, yana cikin d'aurawa yaga irin kallon da take masa, ba tare da sanin abinda take tunani ba yace "Tunani kike wannan wane irin daren farko ne?"

Girgiza kai tayi ta sunkuya cike da dubara ta saka wandon nan dan dama tana sanye da rigar wanka, tana tunanin yanda zata saka rigar cikin sa'a shima saiya zauna gaban farantin data zuba naman nan, da sauri ta saka rigar ta cire waccen ta d'auki hijab ta saka, juyowa yayi zai mata magana yaga ta saka hijab, kallon da yake mata ne ya fahimtar da ita me yake nufi, "Ki cire shi ko na ci uwaki." Tasan ko magana zaiyi abinda zai fad'a kenan, dan haka ta rufawa kanta asiri ta cire ta aje ta zauna, kamota yayi ya zaunar da ita kan k'afafun shi ya d'ebo naman ya saka mata a baki, tun tana jin kunya tana sunkuyar da kai har ta daina tana karb'a, tace ta k'oshi tayi magiya ya barta haka amma yace ta k'oshi sosai ko ta iya...(al'amarinka ya fara damuna), haka suka kammala suka sake tsabtace kansu kafin suka kwanta, duk da tayi nesa dashi saida ya mirgino ya rumgumeta ta baya ya d'ora hab'arshi a wuyanta ya zagaya hannayenshi ta bayanta, kamar wanda za'a rabashi da ita haka ya rik'eta sosai, Amna dake jiran taji abinda zai faru sai kawai ji tayi numfashinshi ya sauya alamar bacci ya d'auke shi, saida ta k'ara d'aukar wani lokacin kafin ta iya samu ita ma bacci ya d'auke ta.

*Safiya*...


*Alhamdulillah*

*Masoyan k'warai ina godiya, 'yan k'asata ba zan manta da hallacinku gare ni ba.*
09/09/2020 ร  17:58 - Ummulkhairi: ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
*BADAK'ALA*
๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ _*AHALI NA*_๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_36_


Gaba d'aya baya jin dad'i tunda ya tashi, tunda ya ganta kusa dashi yaji baya tare da wannan zumud'in na son ya kasance da ita, tunanin abinda ya faru jiya ya tsaya masa a rai, duk da shine farko a wurinshi daya tab'a aure, amma yanda ita ce taja hankalinshi sai yanzu ne yake b'ata masa rai, ta nuna masa ita yar bariki ce, tabbas ya samu gamsuwa da ita, amma tunanin irin mazan da tayi mu'amula dasu, har yanzu yana ganin fuskar yaron nan da suka tab'a had'uwa lokacin da yaje wurinta. Har ga Allah, yau d'in nan duk yaji ta fice masa a rai, yana ji kamar ba zai iya rayuwa da wannan tunanin ba, dan zuciyarshi ba zata d'auka ba, zai kuwa iya jurar wannan matsin? Sukuku ya k'arasa shirinsa suka kammala karin kumallo wanda aka aiko musu daga cikin gida, duk da ta lura da yanayinshi ya canza amma da zai fita sai tace "Junaid ina so zan shiga cikin gidanku na gaisa da mutane, ina so nasan kowa kuma kowa ya sanni mu fahimci juna."

Kallonta yayi a gatse, *Junaid*? Sunanshi ta kira gatsau haka? D'auke idonshi yayi daga kallonta yace "Ba damuwa, kije."

Ficewa yayi wanda hakan ya matuk'ar b'ata mata rai, kutumar uba, ita zai cewa kije kuma ya tafiyarshi, me yasa bai ce su tafi tare ba tunda yasan ba ko ina ta sani ba? Lallai ma yaron nan a cewar ta, mik'ewa tayi ta shiga d'aki ta sake gyara shirinta ta yafa mayafi ta fito, tabbas ta ga k'ofar da taji ana cewa har da k'ofa da zata sadaka da cikin gidan, dan haka bata tsaya komai ba ta bud'a ta shigo, k'arewa gidan kallo take tana tunkarar babban falo, tsari da kyawun gidan ya birgeta sosai, ta kuma saka a ranta dole sai tayi gatsau gatsau ta hakane kawai zata iya tsallake rashin mutumcin da zata iya fuskanta, dan in tayi laushi zasu samu abun gori a kanta, shiga tayi falon da sallama tana sake kallon falon, Hajia da lokacin ta gama karyawa tana zaune, tana ganinta ta saki wata shegiyar dariya tace "Sanin wa Junaid ya auro min ya kawo cikin gida yasa ba zanyi mamakin ganinki a yanzu ba kuma anan."

Murmushi Maryama tayi ta k'araso ciki tace "Kamar yanda nima banyi tunanin ganin mamaki a fuskar kowa ba saboda ganina."

Cike da k'asaita Hajia tace "Wannan na d'aya daga cikin dalilan da suka na gujewa Junaid aurenki, bana son rashin kunya da fitsara a rayuwata."

Ba tare data daina murmushi ba tace "Gashi kuma hakan har ya zama d'ab'iata ta yanda ba zan iya dainawa cikin sauk'i ba."

Saida ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya tace "Ina fatan dai ya fad'a miki akwai doka da oda a gidan nan, kuma nice nan mai bayar da wannan doka da odar, dan haka ki iya bakinki kisan me zaki dinga fad'a min, da ban so ba da yanzu haka baka cikin gidan nan, kina can bakin titi kina neman wanda zai kwantaki ya baki na abinci."

Kalaman sun mata zafi sosai, kuma wannan ne dama take gudu a auren Junaid, amma sai bata nuna ba tace "Bai fad'a min akwai mai bayar da doka da oda ba, watak'ila kuma bai fad'a min bane saboda yasan a inda ya d'auko ni, ina rayuwa ne cikin 'yanci babu mai hanani bare sakani, yana da tabbacin ba zanji maganar kowa ba anan shiyasa."

Sake had'e fuska tayi tace "Ki fad'a min meya shigo dake nan kika baro b'angaren ku? Dan ban son kai da kawowa haka kawai."

Murmushi ta mata sosai tace "Na zo gaishe da surukata ne."

Da yatsa ta nuna mata d'akin Zeinabu tace "Ki wuce to ki gaggauta fitowa ki koma d'akin mijinki, dan ba zan lamunci rashin hankali ba."

Zata wuce d'akin data nuna mata ta ji tace "Su sauran amaren ko suna ina?"

Juyowa Maryama tayi zatayi magana sai kuma Hajia tace "Kai na manta fa, ashe su d'in tarbiyata ce, ba zasu tab'a yin wannan fitsarar ba."

D'aga gira tayi tace "Har mu gani dai." Zata sake wucewa Hajia tace "Gashi kuwa muna gani a halin yanzu, da budurwa ya aura da watak'ila yanzu sai an taimaka miki, amma kash, da yake baiji magana ta ba gashi da k'afafunki kika shigo nan cike da k'aryar rashin kunya."

Fitowar Ummy tare da Zeituna daga madafa sun gama gyara komai yasa Maryama yin shiru, ganin kamala a fuskar Ummy kuma dama tasan ita ce uwarsu Ammar saita gaisheta da ladabi, da fara'a Ummy ta amsa da "Lafiya lau amarya, ya kwanan bak'unta kuma?"

Hajia ce ta katse da cewa "Kinga alamar bak'unta a tare da ita ne? Matar data shigo da kanta nan ba tare da ko rakiyar mijin ba, mtssss."

Sunkuyar da kai sukayi hakan yasa Maryama kallonsu a ranta tace "Eh lallai, da alama wannan ita ce hawan jinin gidan nan, to wallahi idan ba tayi wasa ba ni zan k'asara ta kowa ma ya huta, ni ba zan d'auki wannan iskancin ba."

Juyawa kawai tayi ta nufi d'akin Zeinabu, zata k'wank'wasa k'ofar wacce ke bud'e sai labulen d'akin da akayi ruf dashi sai kuma ta tsaya, kasa kunne tayi sosai jin muryar Inna na fad'in "Ya kamata dai ku sani duk son ku na kuga kun rufe sirrin nan wallahi ba zai rufu ba, dole wata rana gaskiya tayi halinta, munyi kuskure baya bai kamata mu ci gaba da zama cikin wannan kuskuren ba, babban laifi muka aikata da muka bari aka d'aura miki aure da ciki a jikinki, idan har baku fito kun fad'a ba kowa yasan halin da ake ciki, to fa ku sani matsalar zata farane daga lokacin da ta Allah ta kasance da colonel Hussein."

Cike da damuwa Zeinabu tace "Inna nima sai yanzu na fara fahimtar hakan, na sani da ace a waccen lokacin muna da ilimi na addini da bamu yarda munyi aure da ciki ba, yanzu gashi shekaru sunja babu wanda yasan da al'amarin nan, ina jin kunya da tausayin Junaid idan yaji cewa an haifeshi kafin aure ne, hakan na nufin baya da gadon mahaifinshi, sannan waccen jarababbar matar bansan me zata iya yi ba idan ta sani."

Inna ce tace "To sai me? Hajia tunda bata da wutar da zata saka ku duk hargaginta ai na banza ne, kuma karki damu da Junaid akan gadon ubanshi, tunda dai yana da aikinshi mai kyau da yake yi duk da ma bashi ya so ba, dan haka wannan ba damuwa bane."

Shiru kawai Zeinabu tayi tana tunanin mafita, Inna ce tace "Kawai ki fad'awa colonel d'in dan kusan ta yanda zaku fad'awa wanda suka dace su sani, amma dai kuyi da hanzari dan rayuwa yanzu ba tabbas."

Kallonta Zeinabu tayi tace "Kenan yanzu Inna kin yafe kud'in fa muke baki duk wata?"

Dariya Inna tayi tace "Na yafe kam, amma ai dole kinsan dai nauyi na yana wuyanki."

Dogon tsaki Zeinabu tayi a zuciyarta tace "Aikin banza, kamar ba ke kika bamu shawarar yin shiru ba a waccen lokacin."

Maryama dake tsaye bakin k'ofa tana jin haka ta juya da k'arfi ta bar wajen, bata tsaya komai ba ta koma b'angaren ta, tana shiga d'aki ta cire mayafinta ta shiga safa da marwa a tsakiyar falon, lallai ita ma ta samu makamin yak'ar mutanen gidan nan, kenan mijin data aura kafin aure aka haifeshi? To ai gwara ma ni da banyi aure da ciki ba, da wannan tunanin ta kira Iklima tace ta kawo mata Huda tare da kayanta yarinya zata dawo gidan ubanta kawai, Iklima ta so ta bari har tayi sati d'aya amma tace ta kawota kawai, ba yanda ta iya ta shirya Huda wacce da za'a koma da ita Goure ta kawo mata ita.

*Jumare* ce yau ta kawowa Zeituna ziyara, tunda suka shiga d'akin ta dama ta fad'a mata kawu Mamu ne ya turota yace ta zo ta karb'ar mishi kud'i zai siyi magani bashi da lafiya, hankalin Zeituna ya tashi jin ance bashi da lafiya, can bayan gidan b'angaren ajiyar bak'i taje ta samu lieutenant ta fad'a mishi, kud'i ya bata masu yawa yace ta bata kuma zasu zo duba shi anjima da dare, ko da ta kawo mata kud'in ta bata zata tafi saida ta tsaya gaban kayan shafe shafenta ta d'auki wanda take so kafin ta fito, tare suka fito ta rakota tana fad'a mata cewa "Jumare dan Allah ki rik'e kud'in nan da kyau karki jefar a hanya, dan na sanki da shiririta da son wasa."

Daidai suna kawowa farfajiya daidai tana fad'in "Dallah ni ki rabu dani ko, me kika d'auke ni to da zan kasa rik'e wannan kud'in? Kawai gani kike kin haifeni saboda kin auri mai kud'i kin ci kin sha kinyi taib'a."

Zeituna bata ji dad'in abinda ta fad'a ba, musamman da farfajiyar akwai mutane cikin bak'in da suke shirye shiryen komawa garuruwansu. Duk abinda ta fad'a kan kunnuwan *Ammar*, jar bala'i, wannan wace yarinya ce? Uban waye ubanta a duk area nan? Har cikin gidanta kuma take fad'a mata haka? Tana cikin tafiya ya taho cikin takon isa yana fad'in "'Yan mata ji mana."

Cak Jumare ta tsaya tana kallonshi har ya zo kusanta, Zeituna da tasan yau yar uwarta ta had'u da daidai ita matsowa tayi ita ma tana kallonsu, saida ya kalleta sama da k'asa ya rik'e hab'a yace "Ke bafulatana ce?"

Fuskar mutumin dake tattare da haiba da kwarjini ta bala'in firgitata, da k'yar ta iya cewa "Eh."

Ta fad'a a hankali, jinjina kai yayi yace "Kina jin hausa sosai?"

Zeituna ce tace "Tana ji ita ma."

Ba tare daya kalli Zeituna ba yace "Kina iya gane kowane yare?"

Jumare ce ta d'aga kai alamar eh, dan haka ya gyara tsayuwa yace "Alhamdulillah." Nuna Zeituna yayi yace "Wannan ya kike da ita?"

Kallon Zeituna tayi tace "Adda Zeitu? aunty na ce."

Cikin kafeta da ido yace "Kina nufin dai ita ke gaba da ke?"

Da sauri ta kalleshi tace "Eh."

*Gauuuu* ya d'auketa da wani bahagon mari, k'ara ta saki tare da sakin kayan hannunta ta durk'ushe, da sauri Zeituna ma ta durk'usa ta dafata, d'ago kai tayi ta kalleshi da nufin fad'a mishi wannan fa ita ba komai bane a wurinta, amma sai taji ya d'ora da "In kika bari na sake ganin wannan guntulallar k'afar taki a gidan nan wallahi sai kin gane kurenki, na kuma mareki kije ki turo ubanki kowaye shi, a shirye nake dana tsaya da kowa a gaban alk'ali indai akan uwata ne."

Saida ya zuba hannun dama a aljihu ya fara takawa ya nufi falon Hajia, kamar an kirashi sai kuma ya tsaya ya sake dawowa ya sunkuya kusan fuskokinsu yace "Ke kalleni nan."

D'agowa Jumare tayi ta kalleshi da jajayen idonta, saida ya mata alama yace "Kin fara hak'oran hankali ne?"

Duk da tana jin hausa amma yanzu saiya gindayar da ita, kallon Zeituna tayi da alamar tambayar me yake nufi? A harshen fulatanci Zeituna ta mata magana, hakan yasa ta kalleshi cikin muryar kuka tace "Eh sun fito min."

Murmushi ya mata yace "To nan gaba idan kika sake mata rashin kunya Allah su zan zubar miki, kin gane."

Tsaye yayi yana kallonta yace "Ya sunanki?"

Cikin kumburo baki da tsantsar fulatanci a bakinta tace "Jumare."

Yatsina fuska yayi yace "Jumare kuma? Juma'a aka haife ki? To me yasa ba'a saka miki Jumma ba?"

D'an zaro ido tayi ta kalleshi, Jumma? Uwa ta fa kenan? A tunaninta yasan sunan mahaifiyarta ne shiyasa ya mata wannan shagub'en, ganin kallon da take masa yasa shi kallon Zeituna yace "Uwa ya gajiyarku?"

Bai kuma jira me za tace ba ya sa kai falon Hajia d'aukar magana, Zeituna kuma lallab'a Jumare tayi ta tafi gida, saida ta tafi ne tayi murmushi tana fatan hakan da yayi ya zama silar daidaita tsakaninta da Jumare.

Inda Maryama ta bar Hajia nan ya sameta shima, sai dai akwai mutane a falon wanda wasu ke shirin tafiya wasu kuma sai anjima, daga ciki akwai dangin Ummy, gaba d'aya yayi jam'i yace "Ina gajiyarku?"

Duka d'akin da lafiya lau suka amsa tare da d'orawa da "Ya taku gajiyar?"

K'ala babu wanda yace ma sai zaunawa da yayi kusa da Hajia yana kallonta tana kallonshi ita ma, ganin kallon da suke ma juna yasa Hajia k'ara had'e fuska tace "Da wane rashin mutumcin ka shigo kuma yau? Dan wannan murmushin na ka ya bayyana shegantaka ta kawoka."

Hannunta ya kamo ya sumbata sannan ya kalli idonta yace "Hajia ina godiya, Allah ya saka miki da alkairinsa, Allah ya zundumaki aljanna bayan kinsha ruwan khausara, Allah ya dawwamar da farin ciki a rayuwarki kamar yanda kika saka rayuwata farin ciki."

Cike da shewa 'yan cikin d'akin suka saka tare da amsa mishi da "Ameen."

Bai kulasu ba sai d'orawa da yayi da" Hajia ni kam babu abinda zan saka miki da shi a gidan duniyar nan, amma duk da haka zan sakawa 'yata ta farko sunanki."

Kallonshi kawai take bata tanka masa ba, matsowa yayi sosai kusa da ita cikin tattausa murya yanda babu mai jinsu yace "Hajia maganar al'adar nan ce na zo k'arasawa, ance a rana irin ta yau namiji yana bayar da rak'umi ne ko kuma wata kyauta mai tsoka, to gaskiya ni na zauna nayi tunani na kasa tunano abinda zaiyi daidai da dank'waleliyar jikar nan taki, shiyasa nace bara na kawo kaina saiki fad'i abinda kike so nayi."

Dai lokacin tayi murmushin zaka raina kanka tace "Komai idan na fad'a za kayi?"

Cike da tabbatarwa yace "A shirye nake Hajiata."

Ita ma saida ta sassauta murya tace "Jan rak'umi zaka kawo lafiyayye, saika had'o da kud'i million d'aya, sannan ka siya mata sark'a da d'an kunnai na zinariya, idan kayi haka ma ya wadatar."

Tana fad'a ta d'an kawar da kanta alamar zaka gane kurenka, shi kuma murmushi ya mata yana shafa sumar kanshi, kafin yayi magana Allah ya kawo lieutenant d'akin, mik'ewa yayi da sauri ya tarbeshi yana fad'in "Yawwa Abba barka, kud'i nake so ka bani."

๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚

Saida ya harareshi kafin ya mayar da hankalinshi kan mutanen d'akin suka gaisa sosai, daf da Hajia ya zo ya duk'a ya gaisheta, yana mik'ewa ya juya ashe Ammar na daf dashi a baya sai kuwa suka had'e, tsabar k'arfi yasa lieutenant yin baya yana neman fad'uwa, da azama Ammar ya tallaboshi baya, kallon jua sukayi ya sakar masa murmushi, d'aga shi yayi lieutenant kuma cikin fad'a yace "Meye haka wai? Yanzu dana fad'i kaji dad'i kenan?"

"Amma ai baka fad'i ba, Abba ina tare da kai fa, haka ba zai faru ba sai in k'asa ce tarufe min idona."

Cikin fad'a yace "To yanzu uban me kake so da kake biyata a baya kamar wutsiya?"

Saida yasa hannaye aljihu kamar wani k'aramin yaro yace "Kud'i zaka bani?"

Da mamaki yace "Kud'i kuma? Gashi

Please Login or Register in order to submit comment