Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

had'ari akan moton wani abokina, shine da na zo gida sai aka ce su Junaid su taho saboda Ammar shi ya duba min ciwon, bayan Ummy ta zo gida kuma sai shima suka ce ya taho, ni kuma ganin duk sun taho yasa na kasa hak'ura na taho."

Colonel ne ya kalli Junaid yace "To kai kuma uban wa ya ci uwaka a bakin na ka?"

Bawan Allah Junaid sai lokacin ya d'auke hannu daga kuncinshi yace "To ni kuma waye zai dake ni a baki ina d'an soja guda."

Jinjina kai yayi yace "Da kyau to tunda kana tuna hakan."

Mayar da kallonshi yayi kan boss da ke harkar gabanshi kamar baisan sunayi ba ya kamo hannunshi yace "Soja d'an soja muje ko."

Wucewa sukayi inda suma suka bi bayansu lieutenant na jin haushin colonel saboda sam baya ganin laifin Ammar, zaka iya cewa ma yafi nuna mishi k'auna fiye da Junaid da kuma Umaima da Jamila.

Bayan sunyi sallah isha'i aka fito da abinci aka ci, lokacin ne suka fara haramar komawa gida dan sun fahimci kwana anan ba zai musu ba, har cikin gida suka samu Hajia suka fad'a mata, sam Amar bai yarda ya had'u da ita ba dan saita tambayeshi meya same shi, ita kuma k'aramin aikinta ne ta musu bala'i a gidan rasuwa, da k'yar ta yarda zata kwana dan cewa tayi zafi kasheta zaiyi kafin safiya, saida Alhaji yasa baki yace shima zai kwana anan dan bai dace ta bar wurin ba daga yanzu har zuwa kwana uku, haka dai ta hak'ura amma tace ba tayi alk'awarin zama har sadakar uku ba, nan suka juyo dukansu sai Hajia da Alhaji acan, ba tare da wata matsala ba Allah ya kawosu gida lafiya, kowa wajen na shi iyali ya nufa ya samu yayi wanka, k'arfe *10:00* na dare lieutenant Hassan da colonel Hussein da Labaran suka hallara kan babban teburin cin abinci, in dai har suna gari dama sukan had'u ko dan su tattauna matsalar data shafesu, Soueba ce yau take zuba musu duk abinda zasu ci, tana cikin zuba musu ruwa da lemu ta kalli mijinta Labaran tace "...


*Mu had'u a shafi na gaba insha Allah.*✋

*Allah ka mana kyakyawan k'arshe*👏
27/05/2020 à 14:46 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*SANIN MASOYI*
_(sai Allah)_
*BAYA DA K'URA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*


💞 _*MASOYA NA*_💕



*😂 Nasan za ku sha mamaki sosai ganin na dawo da ci gaban sanin masoyi, to ku kwantar da hankulanku kusha kallo kawai, duba da akwai wasu abubuwa daya kamatain ace an warwaresu tun a na farko, amma Allah bai nufa ba sai yanzu idan ya ara mana rai da lafiya, insha Allahu abun zai k'ayatar da ku fiye ma da na farko, kuma wannan shi zai zama na k'arshe da yardar Allah.*

_Bismillahir rahamanir rahim_

_1_


_Idan masu karatu basu manta ba mun tsaya a waccen labarin *Sameera* na da ciki na wata biyar, sannan Abbas na shirin had'a *Raihan* aure da *Abdul* d'an wajen Abbas mai biwa *Husnah* da zaran ta kammala secondary d'in ta, to zamu d'auki labarin daga bayan haihuwar Sameera muyi gaba insha Allah._

*Abbas* ne zaune tare da Abba (mahaifin Sameera Mus'ab) da kuma Umma (mahaifiyar Abbas Falmata) a gefensu, cikin hushi Abba yace "Ina! Wannan ma maganar banza ce, wallahi ba zan tab'a bari ku had'a *Raihan* da tsatson wannan mutumin ba, *Abba*? Ina! Ba dai d'an Abba ba wallahi, mutumin daya cutar da kai ya cuce mu gaba d'aya."

Cikin taushin murya da nutsuwa Umma tace "A gaskiya nima abin bai kwanta min a rai ba, kuma naga ma du-du-du yaron shekararshi nawa? Bai ko gama mallakar hankalin kanshi ba, sannan ita kanta Raihan d'in nawa take da har zaku fara maganar aurar da ita? Shekara goma fa, ba kwa tunanin ku zo ku tsayar da magana akan ga wanda za'a bata, a k'arshe zuciyarta ta kamu da son wani kuma ba shi ba, tunda zata ci gaba da zuwa makarantarta ai."

Abba ne yace "Wannan ma abun dubawa ne, irin wannan had'in tun da k'uruciya yana da matsala gaskiya, bansan me kuka gani ba da har kuke tunani had'a su."

Cike da kulawa *Sameera* ta kalleta tace "Hakane Umma, amma ai ba yanzu za'a musu auren ba, sai nan da shekara hud'u, kunga a lokacin ya samu cikakkiyar shekara ashirin da uku, ita kuma ta koba komai dai ta zama balagaggiya, sannan ba zamu had'a su bane haka kawai, zamu fara tambayar ra'ayin du akan lamarin."

"Yanzu in banda abinki *takwarata* ina Raihan ina wani sanin so? Ko ta amsa miki da eh wallahi idan ta mallaki hankalin kanta zata iya canza magana, 'yar shekara goma fa ake miki magana ba 'yar sha shida ba ko sama da haka."

Cikin tafasar zuci Abba yace "Kunga, ni ba k'arancin shekarun yaron bane damuwa ta, tunda ko yanzu aka mishu aure za'a samu kyakyawan sakamako daga gareshi ta hanyar zuri'a, kuma idan da shak'uwa da fahimta duk wannan ba matsala bace a tsakaninsu, kawai dai yaron ne bai min ba saboda kasancewarshi d'an mak'iyina."

A hankali *Abbas* ya d'ago ya kallesu cikin nutsuwa da girmamawa yace "Abba, Umma, sam banyi tunanin wannan maganar zata iya rasa muhalli a zuk'atanku, Abba, ko fa ubangijin daya hallicemu baya kamamu da laifin da waninmu ya aikata, ina ganin kamar rashin adalci ne da kuma dacewa ace zamu hukunta *Abdul Malik* akan laifin da mahaifinshi ne ya aikata, duba da lokacin da abun ya faru ko kanshi bai sani ba, namiji ne shi ba kuma lallai yayi halayyar mahaifinshi ba, zamu iya cewa mu shaidane akan hallayarshi, bai kamata mu hanashi auren Raihan ba in har suna son junansu, ko 'yar uwarshi *Husna* ta samu miji tayi aure a dalilin rabin rayuwarta da tayi a gidan nan, ni da hannu na na bayar da aurenta Abba, shin kuna ganin ya kamata ace mu mun hana auren d'an su da 'yar mu saboda tunanin abinda mahaifinshi yayi? Bai dace ba hakan iyayena, kuyi hak'uri ku sawa yaran nan albarka, hak'ik'a idan kuka ce baku yarda ba za'a fasa dole, amma hakan ba zai mana dad'i ba."

A hankali Sameera tace "Gaskiya ne Abba, kuma na ga ko shi kansa Abban ai mun yafe masa laifin daya mana, kuma kuyi hak'uri ku yafe masa sannan ku manta da baya, duba da mutumin nan yanzu baya raye a doron duniya."

Kallon juna Abba da Umma sukayi kafin Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Shikenan, mun amince, amma abisa wani sharad'i guda d'aya."

Sameera ma da Abbas kallon juna sukayi kafin Abbas yace "Wane irin sharad'ine wannan Abba?"

Ba alamar wasa yace "Sai in kun amince za'a yi wa yaron gwajin cuta mai karya gwarkuwar jiki da ma sauran cututtuka masu had'ari wanda akan iya d'auka ta hanyar mu'amula."

Dafe kai Abbas yayi yana tunani, yasan halin gogon nasu in har basu amice ba to za'a fasa ne, dan haka ya d'an kalli Sameera wacce ita ma take kallonshi kafin ya kallesu yace "Shikenan Abba, mu ma mun amince."

"Shikenan, Allah ya tabbatar da alkairi." Cewar Abban, da "Ameen." Suka amsa da shi.

Sai Abba daya mik'e zai fita daga falon yana fad'in "A dole wai sai an raba mutum da matarsa, ni ina son amaryata amma kuke son saita min kishiya."

Dariya sukayi sai Umma da tace "Shi ya sa zanfi kowa farin ciki idan haka ta kasance, dan ko ba komai na rabu da kishiya d'aya."

Suma mik'ewa duka sukayi suka nufi b'angaren nasu Abbas, masha Allah falon ya had'u iya had'uwa, gashi duk yaran dake d'akin kowa harkar gabanshi yake amma cikin nutsuwa, sai Raihan dake zaune kan kujera da littafi tana karatu, sai kuma Abdul dake gefe tare da k'aninshi *Jabir* suna danna wayoyinsu, duka zaune sukayi kafin Sameera tace "Ku tashi kuje ku kwanta dare yayi."

Kusan duka yaran suka amsa da "Ok Ammie." Mik'ewa sukayi inda kowa ya nufi nashi d'akin, Raihan ma tashi tayi sai Sameera ce tace " *Mamana* zo nan."

Cikin sanyi jiki da nutsuwa wanda ya zama halitar yarinyar ta taho ko kallon idon mahaifiyarta ba tayi ba harta zaune kusa da ita, Abdul ma da Ameer zasu mik'e Abba yace "Kai Jabir kaje, Abdul ka zauna zamuyi magana."

Cikin tsananin fad'uwar gaba da fargaba ya zame ya zauna k'asa duk da Abbas yace ya zauna inda yake, shiru falon ya d'auka kafin Abba yace "Abdul, abinda yasa nace ka zauna dama ba wani abu bane, ni da iyaye da kuma mai sunan Mamana (Sameera) munyi wata shawara akan ku kai da Raihan, kunsan ance abinda babba ya hango yaro ko ya hau dutse ba zai hango ba, to duba da hakane yasa muka fahimci kamar da wani abu tsakaninka da Raihan, shi ya sa na ce bara mu tambayeku muji ko kuna son junanku?"

Tsaro ne matuk'a ya bayyana a fuskar Raihan duk ta zaro ido, yayin da Abdul zufa ta fara tsatsafo masa saboda jin abun banbarak'wai, wasu kirce-kirce ya fara ya rasa amsar da zai bayar, hakan yasa Abba cewa "Ka yi magana mana Abdul, ba za'a tauyeka ba ai."

Shiru ya sakeyi gabanshi na fad'uwa, Abbas ne yace "Abdul."

A hankali ya d'ago yace "Fad'a min gaskiya, kana son Raihan?"

Raihan da taji abun wani iri tashi tayi da gudu ta haura sama ta shige d'akin ta suna kallo, murmushi Sameera tayi kafin tace "Ita ta amince, saura kai."

Shima yunk'urawa yayi cike da kunya da murmushi ya nufi d'akinsu da suke sauka idan sun zo nan, Abbas ne yace "Bamu fahimci komai ba Abdul, hakan na nufin ka amince kenan?"

Juyowa yayi cike da kunya ya d'an jinjina kai alamar eh, da sauri ya k'arasa sama shima ya bi kusurwar da zata sadasu da na shi d'akin, Abba ne ya kalli Abbas yace "Amma ya kuka barshi ya tafi baku fad'a mi shi sharad'in ba?"

Abbas ne yace "Abba karku damu da wannan, na muku alk'awarin kawo muku sakamakon gwajin Abdul nan da kwana biyu insha Allahu."

"Shikenan Allah ya yarda." Suka amsa da "Ameen."

Umma da Abba b'angarensu suka koma inda Abbas ya wata kusurwar wacce ka d'auka wani sabon gida ne a ciki, sai Sameera da ta haura sama ta shiga d'akin Raihan, tsaye ta sameta ta saka kayan baccinta tana caje gashinta, zaune tayi bakin gado harta juyo ta kalleta tace "Ammie ke ce?"

Murmushi kawai ta mata, takowa tayi ta zo ta zauna tana turo baki gaba cikin shagwab'a ta rik'o hannun Sameera tace "Ammie, wai akan me Dady yake magana ne?"

Murmushi sosai Sameera tayi tace "Wai baki fahimci me yake magana akai ba? Kee 'yan matana fad'a min gaskiya kedai."

K'ara had'e rai tayi tace"Ammie, da gaske na ke fa." Shafa kanta Sameera tayi tace."To in tambayeki mana? Tsakani da Allah Abdul baya birgeki?"

Saida ta juya idonta kafin tace "Ammie, yana birgeni mana, kamar yaya na d'auke shi fa."

Tana ci gaba da shafa kanta tace "To ba kya jin wani abu a game da shi a zuciyarki? Misali idan kin ganshi, ko kuma yayi nesa da ke?"

B1 tare da sanin mahimmancin abinda take tambayarta ba tace "Ammie ba na jin komai, kawai dai ina sonshi a matsayin yayana."

Kallon fahimta ta mata sosai tace "To kina ganin zaki iya aurenshi? Ma'ana zaki iya yin rayuwar aure da shi ta har abada?"

Ido ta d'an zaro tace "Ammie, irin rayuwar da kuke da ke da Dady? Da kuma Mammy da Papy?"

Saida ta kama kumatunta tace "Good girl, haka na ke nufi."

Dariya ta bushe da ita ta fad'a k'irjin Sameera ta rumgumeta tana fad'in "Ammie ni kunya nake ji, bana so na yi aure na barku, ina so na ci gaba da zama da ku a gidan nan."

Sosai ta rumgumeta tace "Hakan na nufin Mamana ta amince kenan?" K'ara tusa kanta tayi a k'irjin ta ba tace komai ba, dan haka ta d'ora da "To karki damu, indai kina son zama tare damu ai abune mai sauk'i, Dadynki zai iya ware muku part na musamman."

Kunya ce tasa Raihan tashi ta shiga toilet da gudu, binta tayi da kallo kafin ta mik'e tace "Ni na tafi saida safe, ki fito ki kwanta ke ma."

Daga toilet d'in ta amsa da "Good night Ammie." Saida ta shiga d'akin sauran yaran duk ta samesu sukayi saida safe kafin ta wuce nasu sashin, saida sukayi rigima da Abbas kafin ta yarda ta kai Ameer wajensu Ammie ya kwana, dan cewa yayi wani cikin zai mata dan yana so tayita haihuwa, haka fa rayuwar gidan nasu take tafiya ba tare da tunanin wata rana bak'in ciki zai iya ziyartarsu ba, ta b'angare d'aya kuma maganar Abdul da Raihan na nan daram, sai dai har yanzu Abbas bai iya maganar gwajin da za'a wa Abdul ba saboda yana ganin rashin dacewar hakan, su Ammie kuma basu sake mishi maganar ba tunda ba abu bane na gaggawa, sai dai kuma Raihan kunyarta tayi yawa sosai ta yanda har yanzu ba wata shak'uwa bace tsakaninsu, dan ko tana zaune a wuri ya zo tashi take da kunya da nutsuwa ta bar wajen, Fadila da Ma'awa kad'ai suke sakewa dashi suna hira amma ita tana jinsu, duk da dai a zuciyarta tana jin yana birgeta, amma bata iya nuna mishi, idan ya koma gidansu ne kad'ai tafi sakewa da walwala, ta b'angare d'aya kuma suna karatunsu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, yan watanni kad'an Abdul ya kammala secondary d'in shi Abbas ya turashi jami'ar madina, bayan wani lokaci kuma Jabir kuma shima ya kammala nasa inda ya zab'i yin karatunshi a jami'ar Ahmadu Bello, shima babu wata matsala da yake fuskanta saboda yana tare da magajiyar mahaifiyarsu *Safeena*, kwana tashi babu wuya a wurin Allah sai kuwa su Raihan suma suka samu shiga secondary.

*Bayan shekara hud'u* sai gashi Raihan Fadila da Ma'awa sun fara jarabawa ta zangon k'arshe a ajinsu, lokacin fa masha Allah yan mata an girma sosai kowace hallitarta ta fara bayyana ta zama budurwa yar shekara sha-biyar, musamman Raihan wacce tayi k'aramin jiki kamar na Sameera sai tsayi wanda ya dace da ita, ga farar fatarta ta gama bayyana kyau da shek'i, haka ma dogon gashinta wanda yafi ma na uwarta, domin kuwa ita tun tana yarinya ana gyara mata shi sab'anin Sameera data girma a k'auye, sam bata da wadatar k'irji dan kusan Raudat dake k'anwarta ta biyu ma kuma ko balaga batayi ba har nonuwanta sun kusa na Raihan d'in, lik'e suke a k'irjin ta sosai ba su da wani girma na azo a gani, dama idan Allah ya hanaka wani abun saiya baka wani abun, kamar yanda take da shafaffen ciki mai fad'i haka k'ugun ta yake a bud'e, kuma masha Allah tana da mazaunai daidai gwargwado, k'irarta abar birgewa ce da d'aukar hankalin maza, kamar yanda mahaifiyarta take haka ita ma take, gashi dama Sameera har yanzu ba wata k'iba bace tayi shiyasa ma idan kaga fuskokinsu sai kace wata yaya da k'anwa ne, yanzu haka sun kammala jarabawar sakamako kawai suke jira sai islamiyya da suke zuwa, ba jimawa kuma Abdul shima ya dawo daga madina hutu dan *doctor* yake sha'awar zama na musulunci, a yanzu ne kuma Abbas ya fara tunanin yi mishi gwajin jinin, amma rasa hanyar da zaibi yasa ya shirya shawartar su Bashir da Naseer.


*K'auyen Gwagwa*


*Harira* ce ta fito cikin shirin tafiya birni ita da yayanta, *Baaba mai wake* (k'anwar mahaifiyarsu) ce ta k'are musu kallo kafin ta tab'e baki tace "Tafiyar ce zakuyi?"

Harira ce ta amsa da "Eh Baaba, zamu tafi sai mun dawo."

Sake tab'e baki tayi tace "Humm." Juyawa sukayi sai yayanta daya fito da naira d'ari a aljihu ya bata yace "Baaba ga wannan, idan su *Karime* sun taso daga islamiyya saiki basu wake dashi."

Nan ma dai sake tab'e bakin tayi tace "Yanzu d'ari ce zata isa su ci abinci su k'oshi? Kasan su da shegen cin tsiya fa."

Cikin taushin murya yace "Kiyi hak'uri Baaba, kud'in mota kad'ai suka rage mana anan, suma wallahi aro su nayi wajen *Halidu* mai tebur, ko na abinci ba zamu samu ba."

Cikin jin haushi tace "Naji dan Allah, ca-ca-ca-ca kamar carbi ta tsinke, kuje sai kun dawo."

Mik'ewa tayi ta nufi wajen bisashen da take kiyo tana fad'in "Ba gaira ba dalili na d'auko wa kaina jaraba, shegen jaraabben son kud'in iyayenku ne ya ja muku ai, yanzu gashi a banza a wofi suna d'aure a magark'ama suna neman k'are rayuwarsu can, jaraba kawai."

Duk abinda ta fad'a akan kunnuwansu, dan haka suka juya jiki a sanyaye suka fita daga gidan, cikin nutsuwa suke tafiya inda *Adamu* yace "Harira kina ganin idan muka je zasu sauraremu har su taimaka mana kuwa? Dan ni har yanzu a tsorace nake."

Saida Harira ta share hawayen dake zubowa a idonta tace"Ban sani yah Adamu, iyayenmu sun cutar dasu sosai ta yanda ko basu yafe musu ba basu da laifi, matar yallab'ai Abbas kuma Sameera bana tunanin zata iya kallon fuskata ma, domin kuwa a lokacin da muke aiki a gidan na lak'a mata sharrin sata, kaga kuwa banda tabbacin zasu sauraremu."

Rik'e k'ugu Adamu yayi suna tafiya a hankali yace "Wannan fanti da iyayenmu sukayi mana Allah kad'ai zai iya wanke mana shi, nifa yanzu duk da ina namiji har kunyar fita waje nake, har bana iya fad'in cewa ni d'an *Bukar* ne saboda abinda suka aikata."

Da ire-iren wannan maganganun suka k'arasa tashar shiga mota, cikin sa'a suka sauka lafiya suka samu adaidaita suka lula unguwar zone 2, fadar Sameera aka ajesu inda mai gadi ya tambaye su "Wa ku ke nema?"

Harira ce tace "Munzo ganin Sameera ne."

"Me? Hajia kike kira haka gatsau?" Cewar mai gadin, Adamu ne yace "Kayi hak'uri yallab'ai, munzo ganin Hajia Sameera ne."

K'asa da sama ya kallesu yace " Tasan da zuwanku ne?"

Adamu ne yace "Gaskiya bata sani ba, amma ka taimaka mana mu ganta dan Allah, wallahi daga nesa muke."

Saida ya sake kallonsu kafin yace "Ku bari na sanar mata tukun." Yana fad'a ya juya ya fito da wayarshi ya danna kira, a tabkekiyar kitchin d'in *Razeena* mai aiki ta ji kyakyawar wayar mai kama da masarrafin telebijin tayi k'ara, d'auka tayi tare da fad'in "Razeena ce akan layi."

Mai gadin ne ya fad'a mata zuwansu Harirar tare da wanda suke son ganin, a cewarta "Zan fad'a ma Hajia yanzu."

Aje wayar tayi kafin ta nufo falon Sameera, zaune ta sameta da *Ameer* (Mus'ab sunan mahaifinta) d'an shekara hud'u yana wasa saboda yau yan rigimar ne akanshi shiyasa ban je islamiyyar ba, sunkuyawa tayi tace "Hajia kinyi bak'i a waje, sunce ke suke son gani, su biyu ne mace da namiji, macen sunanta Harira sai namijin Adamu, sunce sun zo ne daga k'auyen gwagwa."

Cike da jin dad'in yanda Razeena ta gama fahimtar halayyarta ta kalleta da mamaki, ta jima tana kallon fuskarta kamar tana son gano wani abu kafin ta zaro ido tace "Harira, k'auyen gwagwa?"

Cikin ladabi tace "Eh madame."

Tsaye ta mik'e ta kama hannun Ameer tace "Ki musu iso Razeena, na gane wace Harira."

"Ok." Ta fad'a tana nufa k'ofar fita, ita ta bud'e musu k'aramar k'ofar suka shigo ta shigo da su, tana gaba suna biyarta suna k'arewa gidan kallo, Harira na tsananin mamaki wai Sameera ce a wannan gidan, wacce a lokacin da sukayi aiki ake mata kallo tsintacciya marar gata, saida ta shigo da su har falon anan Sameera dake tsaye har yanzu ta kalli Ameer tace " Ameer Kaje wajensu Ammie kuyi hira."

Harari ta kalla tace "Ki kawo musu abun tab'awa."

"To." Ta fad'a ta fice da shi, kallon Harira tayi wacce ta kafeta da ido tana kallo, sosai ta saki fuskarta d'auke da murmushi tace "Harira ku k'araso mana, ku shigo ku zauna."

Saida taje ta kama hannunta ta zaunar da ita akan kujera inda shima Adamu ya zauna kamar akan wuta, kallon falon yake sai kace falon shugaban k'asa, a ranshi yace "Wasu na fafutukar neman abinda zasu ci, wasu kuma sun wadatu sunyi birgima a cikin kud'i, burinsu shine su tara dukiyar da har jikokinsu zasu mallaka."

Muryar Sameera ce ta dawo dashi tana fad'in "Sannu ko, ya hanya?"

Da "Lafiya lau." Suka amsa ta d'ora da "Harira dama kina nan? Ina kika shige haka ko labarinki babu?"

Cikin sanyinjiki tace "Ina nan mana Hajia, ina k'auyen mu."

Zaune Sameera tayi a kujerar data tashi tana fad'in "Amma shine kika b'uya kuma?"

Murmushi kawai Harira tayi saboda fitowar wata mai aikin d'auke da faranti da kayan tab'awa da masu sanyi ta aje gabansu, saida ta zuba musu ta bawa kowa kafin ta juya zata tafi Sameera tace "Ku shirya mana wajen cin abinci saboda bak'i."

Saida ta sunkuya tace "To Hajia." Ta fice, kallonsu Sameera tayi tace "Harira wannan mijinki ne?"

Kallon Adamu tayi tace "A'a, yayana ne, uwar mu d'aya ubanmu d'aya."

"Ayyah, Allah sarki, sannu ko." Ta sake fad'a tana kallonshi, da d'an murmushi ya amsa da "Barka Hajia, ya yara?"

"Lafiya k'alau." Ta fad'a da murmushi sosai, maida kallonta tayi ga *Wassila* dake shirya kayan abinci a dinning duk da ba lokacin cin abinci bane, mik'ewa tayi ta kallesu tace "Bismillah Harira, ku zo ku ci abinci."

Daga ita har Adamu babu wanda yace a'a saboda dama basuyi karin kumallo ba suka fito, k'arasawa sukayi suka zauna akan kujerun suna jinsu kamar akan wuta, suna kallo Wassila ta gama shirya komai ta zubawa kowa ta aje masa gabanshi kafin tace "Aci lafiya."

Tana tafiya suka fara tsakurar abinci cikin kunya, Sameera kuma da dama ba ci za ta yi ba saboda ta ci abinci lemu kawai take sha, ganin suna kallon farantin dake gabanta yasa ta d'an fara kaiwa bakinta ita ma, ganin sun kasa sakewa yasa ta mik'e tace "Ina zuwa ko, ku ci dan Allah sosai, ku saki jikinku kamar gida kuke."

Kicthen ta nufa inda suka bud'e sosai suka dinga cin abinci suna had'awa da naman ciki da lemu, saida sukaji cikinsu yayi k'at alamar ya cika kafin suka sarara suna kallon shi kanshi wajen cin abinci, sai lokacin Sameera ta fito tace su dawo falo, nan suka samu wuri suka zauna kafin Sameera tace "Harira, kince kun zo gani na ne, Allah yasa dai lafiya?"

Saida Harira ta nisa sosai kafin tace "...


*Kuna son ci gaban labarin ne ko kuwa???*

*Barkanmu da sallah, Allah ya maimaita mana ya karb'i ibadunmu.*
27/05/2020 à 14:46 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*SANIN MASOYI*
_(sai Allah)_
*BAYA DA K'URA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

💕 _*MASOYA NA*_💞



_Bismillahir rahamanir rahim_

_2_


"Sameera mun zo neman taimakonki ne, dan Allah ki taimaka mana kamar yanda Allah ya taimake ki, ki wa yallab'ai Abbas magana akan iyayenmu da ya sa baki a fito da su, wallahi muna cikin wani hali saboda rashinsu a kusa da mu."

Shiru tayi tana goge hawaye kafin ta ci gaba da cewa "Sameera a dalilin abinda iyayenmu suka aikata yasa duk k'auyenmu an tsanemu, k'annan mu basa iya shiga cikin yara suyi karatu ko wasa ba tare da an tsagwamesu ba, haka muma dake manya a cikin hantararmu ake, ana fad'a mana an gadar mana bak'in hali, son kud'in iyayenmu yasa suke d'aure, Sameera in tak'aice miki wallahi aurena ya mutu saboda maganar iyayenmu nan, shi ya sa muka ce bara mu zo mu rok'i alfarma ko zaku iya taimaka su fito, izuwa yanzu nasan sunyi nadama tare da tuba akan zunubinsu."

Cike
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment