Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'auko kwalin wata allura da abin k'arin numfashi (oxygène) haka ya rumgumoshi a jikinshi ya sake fitowa da gudu.

Yana shigowa ya sameta yanda ya barta sai jan numfashi take, cikin gaggawa ya samu wuri ya aje bunburutun oxygène d'in ya jona ya saka mata, wasu allurai ya had'a yasa a ciki take wani iska ya dinga taimakawa Hajia wajen numfashi inda daga k'asa kuma wasu ruwa ke ta tafasa, k'ura mata ido yayi yana kallo sannu sannu numfashinta ya fara saisaituwa, ajiyar zuciya ya sauke tare da jawo kujerar gaban madubinta ya zauna yana kallonta, Zeituna ce ta shigo da sallama ya amsa, kallonta yayi yace "Uwa antashi lafiya?"

Tana kallon Hajia tace "Antashi lafiya? Ya kuma naga an sa ma Hajia wannan?"

Kallonta yayi shima sai kawai ya bushe da dariya yace "Kin ganta nan fa sai alamun margaya take nunawa."

Duk da tana lumshe ido bacci na son d'aukarta saida ta kalleshi, hannun dake kusa dashi ta d'aga mishi tana son kama nashi hannun, da sauri ya had'a hannunshi da na ta, da alama magana take so tayi sai kuma ta fara lumshe ido, a haka kuma bacci ya d'auke ta ya saki sannunta, haka kawai yaji ba zai iya yin nisa da ita ba a halin da take ciki, dan haka ya kira asibiti ya fad'a musu yana da wani marar lafiyar da yake dubawa, duk wanda zai gani yau a basu rendez vous da yamma.

Sosai Labaran ya mishi fad'a da nuna baiji dad'in abinda ya faru ba, Soueiba dai abinda ta fad'a mishi shine, tunda hakan ya faru da farko dai ayi hak'uri tunda ba jiya ko yau bane haka ta faru ba, sannan su rik'e yarinyar su kula da ita tunda dai dama duk yan uwa ne, a banza ma zasu iya rik'eta bare kuma jikanyarsu ce, na biyu kuma Jamila dake ikrarin ya rabu da ita suyi k'ok'ari su ga auren bai mutu saboda wannan matsalar, da haka ta kwantar masa da hankali suka fuskanci gaba.

Bai fita ko ina ba sai wayarsa da yake dannawa yana gudanar da harkokin daga nan zaune, agogon hannunshi ya kalla sannan ya kalli Hajia, tabbatarwa da yayi daga yanzu zuwa kowane lokaci zata farka yasa shi fita daga d'akin ya fito, a falo ya gansu zaune suna ta hira abinsu cikin raha, fuska a had'e ya kalleta yace "Ke had'a ma Hajia abinda zata ci, amma kada kisa arΓ΄me (d'and'ano) tare da abinsha naturel."

Kamar bata ji ba dan haka ya sake kallonta yace "Dake nake fa."

Saida ta harari gefenta ta mik'e tana fad'in "Sai kace banda suna wani wai ke, menene ma'anar ke?"

Kallonta yayi ya cije leb'en k'asa, zai matso kusanta ta rufa da sauri ta shige madafar, dariya Amna tayi ta girgiza kai tace "Naga ranar da zaku girma."

Kallonta yayi yace "Amna nine ban girma ba? Ni kike had'awa da waccen yarinyar? Ni Amna?"

Kanta yayi kamar zai mazgeta hakan yasa ta rufe fuska da hannaye cikin muryar kuka tace "Kayi hak'uri to ba kai ba, ni ita nake nufi."

Dariya yayi ya sunkuya ya sumbaceta ya juya ya koma d'akin Hajia, minti arba'in ta d'auka kafin ta shigo d'akin da sallama, d'agowa yayi yana kallonta har ta shigo ta aje farantin hannunta, juyawa tayi zata fita yace "...


*Alhamdulillah*
14/10/2020 Γ  00:58 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*BADAK'ALA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ _*AHALI NA*_πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦

πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_50_


"Uban waye zai zuba miki?"

Juyowa tayi ta murgud'a baki tace "Kai musaki ne?"

Tattare rigarta tayi ta tafi a guje, takon da baifi uku ba ya rik'o wuyan rigarta da k'arfi yayi baya da ita, k'ara tayi wacce tasa Hajia k'arasa bud'e idonta ta kallesu, hannu ya d'aga da niyyar kasheta da mari, amma me sai yaji ba zai iya tab'a lafiyar jikinta har haka ba, tsaki ya ma kansa kafin yasa k'arfinsa ya damk'i gashinta yana fad'in "Sa'anki ne ni?"

K'ara tayi tare da rintse ido tana k'ok'arin cire hannunshi a kanta, hannu ya d'aga kamar zai mareta, da sauri ta rik'e k'afarshi cikin kuka tace "Yi hak'uri to zanyi, zan zuba, zan zuba wallahi, dan Allah yi hak'uri."

Da k'arfi yace "Tashi to."

Tashi tayi ta dawo inda ta aje kwanukan ta fara zubawa, saida ta gama ta mik'a mishi tace "Gashi."

D'aga idonshi yayi ya mata wani kallo yace "Aje a kaina."

Saida ta turo mishi baki kafin ta aje gefen gadon, juyawa tayi saida ta bud'a k'ofar tayi shirin rufeta sannan ta zuro kai tace "Allah ya saka min cutar daka min."

Tana fad'a ta ari na kare, cikin nutsuwa ya bita da kallon rashin fahimta, cutar daya mata? Wace cutar kenan? Abinda ya faru baya ko kuma yanzu? Tab'e baki yayi ya mik'e ya kama Hajia ta tashi, saukowa tayi daga kan gadon yana rik'e da hannayenta, ta mik'e tsaye Zeituna ta shigo da sallama, da sauri ta k'araso tana kwance goyon Fatima ta aje kan gadon tace "Yah Ammar bari na kaita."

Sakinta yayi suka shiga ban d'aki shi kuma ya d'auki Fatima yana mata wasa, baki kawai ta wanko ta fitota koma ta zauna, ita ta zuba abinci ya bata da kanta ta ci tasha lemu, maganin ya bata ta bata sannan yace ta d'an zauna, amsar Fatima tayi suka fita dan aikin gabanta, kallonta yayi shima yace "Hajia nima zan tafi asibiti yanzu, dan Allah kada kiyi wasa da magunan nan."

Ya fad'a yana nuna mata su, juyawa yayi zai fita tace "Ammar zo."

Juyowa yayi ya tsaya ta nuna masa kusa da uta tace "Zauna mana."

Zaunawa yayi yana kallonta, saida ta sunkuyar da kanta tace "Ammar tun yaushe kasan da haka kuma baka fad'a ba kowa ya ji?"

Da mamaki ya kalleta yace "Subhanallah! Hajia na fad'a? Na fad'a ma wa to?"

Kallonshi tayi tace "A gani na k'iyayya na nuna maka, shiyasa nake tunanin ko zaka iya fad'a dan ka kunyata ni."

B'ata fuska yayi yace "Haba Hajia, ke fa kakata ce wacce ta haifi abun tutiyata, taya zan miki haka? Hajia duk abinda kike min gaskiya ne ina jin zafi a zuciyata, amma kuma bana rik'e ki ta yanda har zanyi tunanin d'aukar fansa a kanki ko kunyata ki, Hajia duk da kina fad'a min gaba da gaba cewa baki sona ni ban tab'a yarda ba, abu d'aya da nayi imani dashi shine babu wanda zai k'i nasa sai dai ya k'i wani halinsa."

Jinjina kai tayi alamar gamsuwa kafin tace "Tun yaushe kasan da maganar nan Ammar kuma kayi shiru?"

Murmushi yayi yace "A k'alla wata goma yanzu, wani dare ne naji yana fad'a tsakaninshi da mahalincinsa, dare ne da ni kaina ya shiga cikin tarihin rayuwata, domin abinda ya faru a daren bayan naji abinda ya fad'a ne ya tabbatar min da lallai duk abinda magabatanmu suka aikata yana iya dawowa kanmu, sannan na tabbatar da abinda ya fad'a miki yanzu cewa dole sai kin tuba Hajia, inba haka ba akwai wasu abubuwan da zaki k'ara ji nan gaba wanda a gaskiya zasu iya k'arasaki ga kushewarki."

Abun mamaki da al'ajabi, abunda ko a mafarki baiyi tsammani ba shine ya faru, Hajia Zeeya'atu, Hajia dai sarauniyar izza ji da kai tak'ama da alfahari, ita ce wai ke kuka da idonta tana rik'e hannunshi tana fad'in "Ammar ka fad'a min dan Allah me yake faruwa a cikin iyalina? Ammar na fara jin tsoro, sai nake ganin kamar shashashar uwa ce ni."

Da sauri yace "A'a Hajia, ke uwa ce tsayayya kan iyalinta, Hajia akwai wuya samun uwa kamarki, ba kowace uwa bace ke tsayawa har kan tarbiyar jikokinta ma bayan ta tarbiyaccin 'ya'yanta, kawai dai yar matsala ce aka samu daga wani wurin."

Ba tare data saki hannunshi ba tace "Ka fad'a min Ammar idan kasan wani abu dake faruwa, dan Allah ka fad'a min kaji."

Girgiza kai yayi yace "Hajia bana so hankalinki ya sake tashi, k'azantar da baki ganta ba kuma baki jita ba tsabtace a gareki."

Cikin kuka mai matuk'ar nuna nadama tace "A'a Ammar ka fad'a min zan d'auka, zunubi na ne bai kamata ya shafeku ba, nayi alk'awarin tuba ga Allah abisa cin amanar mahaifina da nayi da kuma zina, zan rok'i Allah ya yafe min zubar da cikin dana tab'a yi, dan Allah ka fad'a min Ammar ko zan samu na nemi iyalina gafara."

Da k'yar ya iya b'oye tashin hankalinshi da tsoron al'amarinta, shi bai ma san ta zubar da ciki ba sai yanzu, lallai abun azimun ne, shirun da yayi yana kallonta yasa ta kalleshi tace "Ammar yanzu ne na fahimta banda masoyi a duniyar nan sama da kakanka, ashe duk yasan da abun nan kuma bai tab'a nuna min ko ya fad'a min ba, duk irin rashin mutumci da wulak'anci dana masa..."

Kuka ne ya k'wace mata ta sunkuyar da kai tana kuka, saida ta nutsu ta d'ago tace "Da wane ido ne zan dinga kallonshi yanzu, Ammar babu irin k'ask'ancin da ban mishi ba a rayuwa, a rayuwar aurenmu nasan akwai lokacin da yayi farin ciki, amma bak'in cikin da yayi ya ninka farin cikin sau ninkin ba-ninkin, duk da yasan lagona yasan makullin ruguza duk wani gidan rashin mutumcina amma bai bud'e ba, Allah sarki bawan Allah, wannan dalilin ne yasa nake k'ara son shi kullum, *hak'uri*, yana da matuk'ar hak'uri."

Murmushi yayi yace "Hakane Hajia, amma ki gode Allah da yasan kika fahimci haka tun dukanku kuna raye, kinga kenan akwai damar neman yafiya da gyara kuren gaba."

Kallonshi tayi tace "Hakane Ammar zanyi, amma dan Allah ka fad'a min idan kasan akwai wani abu daya kamata na sanshi?"

Shafa gemunshi yayi yana nazari, sake matsowa yayi kusanta ya rik'o hannunta yana kallon idonta cikin bin kowace kalma daki-daki yace "Hajia, bansan komai a game da kowa ba sai wanda ke fitowa yanzu, kaina kawai na sani."

Bakinshi ta k'urawa ido tana kallo kamar mai son fahimtar yarenshi tace "Ka aikata wani abu ne kai ma daya kamata na sani?"

A hankali ya jinjina mata kai alamar eh ba tare daya rusuna idonshi daga kan fuskarta ba, cikin zak'uwa tace "Meye? Me ka aikata Ammar? Kenan pentina ya shafeka?"

Kai ya fara jinjina mata tare da cewa "Eh, Hajia nawa yafi na kowa muni, kowa abun bai faru dashi da wani na shi ba, amma ni da yer uwata haka ya faru, wacce muka tashi tare uwa d'aya ta rainemu, da ita d'in ma hakan ya faru ne a d'akin uwata mahaifiya."

Yanda suke kallon juna kai kace basa gane yaren junansu, cikin mamakin dake son kasheta tace "Wa kenen? Ka fad'a min kaina ya kulla na gaza tuna komai."

Marairaicewa yayi yace "Wallahi Hajia tsautsayi ne da kuma k'addara, ban shirya yin hakan ba, banyi niyyar yin hakan ba kawai aikatawa nayi."

Fahimta da tayi yasa ta kafeshi da ido tace "Hamna ko Amna?"

Saida yayi k'asa da idonshi yace *"Hamna."*


"Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Hasbunallahu wa ni'imal wakil."

Wani irin kallo ta masa taja baya sosai tace "Wallahi Ammar ba dan kana d'aya d'aga cikin wanda suka min sanin shanu ba da yau saika raina kanka."

Sunkuyar da kai yayi baice komai ba, d'auke kanta tayi daga gareshi tace "Jikana da jikanyata? A cikin gidana suka aikata zina? La'ilaha illallah."

Jujjuya kai ta dinga yi tana ta fafutakar saita nutsuwarta, kallonshi tayi ta mik'e tsaye da duka sauran k'arfin daya rage mata ta gaura masa mari a kumatun dama tace "Kasan kayi wannan ta'asar akan me ka yarda aka aura maka yer uwarta? Kai wane irin shaid'ani ne Ammar, kayi tarayya da babba kuma kayi da gaba d'aya tazarar lokacin dake tsakaninsu bata wuce minti biyu zuwa uku ba."

Komawa tayi ta zauna kan gadon ta kalleshi cike da jin haushi tace "Fitar min a d'aki."

Mik'ewa yayi ya kalleta yace "Kuyi hakuri Hajia, wannan shine dalilin da yasa duk wanda yayi katob'ararsa yake rufe abarsa, kowa yafi so kiji daga baya yanda zuciyarki zata buga ki mutu kowa ma ya huta."

Da kallo ta bishi, shima hushi ne yayi shiyasa ya fad'i haka, gajeran tunani tayi sai gata babu buk'atar yin zafi a wannan lokacin, kuma abinda ya fad'a gaskiya ne kawai, cikin taushin murya tace "Dawo nan Ammar."

Tsayawa yayi daga shirin bud'a d'akin ya dawo ya zauna inda ta nuna masa. Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi ta rik'e hab'a tace "Duk laifina ne da bana iya fahimtar komai, kamata yayi ace na gane yarinyar dake gabana, amma ban gane hakan ba."

Kallonshi tayi tace "Amma me yasa baka fad'a min har ka bari ka auri yer uwarta kuma? Ai da sai ka auri ita Hamna."

Kallonta yayi shima yace "Ummy ce matsalar, bata so kowa ya sani sannan ta daina kulani."

Cikin raha tace "Rabu da ita kawai, yanzu ma karka fad'a mata na sani nasan dai duk nice take jin tsoron kar na sani."

Rik'o hannayenta yayi yace "Dan Allah Hajia ku gafarce ni ku yafe min, Allah nima ina jin kunyar kaina dan nasan ban aikata daidai ba, ku yanke min duk hukuncin daya dace dani zan d'auka, ba zan ji kunya ko tsoro ba, kuma zan nemi kowa yafiya daga iyayenmu dana zubarwa da mutumci har ita Hamna da kuma Amna."

Da sauri ta girgiza masa kai tace "A'a Ammar, muyi shiru d'in shi yafi, ka sani a rayuwa akwai abubuwan da ba'a buk'atar su fito fili, yin shirun shine maslaha a yanzu duk da dai nasan akwai ranar da zasu fito, domin kuwa daga yanda yanzu naji sirrin k'uruciyata a wajenka ya tabbatar min babu wani abu fa da za'a b'oye bai fito fili ba, sai dai kafin mu fitar dashi mu fara duba maslahar dake cikin rashin fad'an da kuma fad'an."

Cikin nutsuwa tace masa "Misali yanzu idan Hazida taji me kake tunanin zatayi?"

Saida ya d'an rarraba ido yace "Ba zata ji dad'i ba Hajia."

Da hannu ta masa alamar tace "Ba iya rashin jin dad'i kawai ba, hatta zumuncin dake tsakaninta da mahaifiyarku zai lalace, 'yarta ce fa data haifa kuma su kad'ai gareta, sannan ni kaina zata min alawadai da salon rainon nawa tace shiyasa ban barta da yaranta ba, shin zakaji dad'i idan haka ta faru?"

Girgiza kai yayi a hankali yana d'an shigar da leb'enshi na k'asa cikin baki, d'orawa tayi da " Sannan ka duba al'amarin ta b'angaren yer uwarta da kake aure, Ammar ya zakayi ka fahimtar da ita sanda taji? Wane irin gamsashen bayani zaka mata?"

Shiru yayi yana d'an girgiza kai, shi fa bai tab'a tunanin yanda Amna zatayi ba idan taji, kawai a yanda ya tsara ko da abin ya fito kowa yaji zai murje ido ne ya tsula tsiyarshi dole kowa ya shafa mishi lafiya, Amna kuma daya bubburma mata ashar tare da mahaukacin mari dole ko mafarkin yi mishi iskanci tayi sai tayi addu'ar tsari ta juya kwancinta, kamar Hajia tasan me yake tunani sai kuwa tace "Kasan adadin kishin matarka? Ammar kasan suffar da mace ke zama yayin data rikid'e sakamakon kishi? To ko da wasa ne ka jaraba ka gani, wannan mai tsoron na ka kamar mutuwarta zata kalleka ido cikin ido, rawar muryar da take sanda take magana da kai zata rera maka b'acin ranta kamar tana rera k'ira'a, shiru da takeyi sanda ka daketa to ba fa lallai ta iya yin shirun ba, Ammar, a wannan fannin ba lallai ka samu girmamawa daga wajen Amna ba, dan haka shirun nan shi yafi kamar yanda mahaifiyarka tayi."

Cikin marairaicewa yace "Hajia to dan Allah ki yafe min, idan kika yafe min nasan komai zai zo min da sauk'i insha Allahu."

Murmushi ta masa tace "Ba komai Ammar na yafe maka, nima ku yafe min kaji."

"Baki mana komai ba Hajiata." Ya fad'a da murmushi, kallon agogo yayi da sauri ya mik'e tsaye yace "Hajia zan tafi asibiti yanzu, saina dawo."

Kai ta jinjina alamar to, tana binshi da kallo har ya fita, yana rufe k'ofar d'akin ya sauke wata ajiyar zuciya mai k'arfin gaske yayin da yaji wani sanyi ya ratsa shi, ita kanta yana fita wani sakayau taji kamar ta rage nauyin wasu kaya data jima tana dakonsu a kanta.

A falon dai ya same su dukansu, saida yaje kusanta ya kalli fuskarta, murmushi kawai yayi yana mamakin taya wannan innocent face d'in zata tabka rashin mutumcin da Hajia ta zayyana masa idan idonta suka rufe akan kishi, yo shi kwarjininshi ma zai barta tayi? Ganin ya tsaya kanta yana murmushi yasa tace "Yah Ammar ya dai?"

Kallonta yayi sai kawai ya had'e girar sama da k'asa ya zama boss ya sunkuya yace "Kalli ido na."

Bud'a matsakaitan idonta tayi ta kalli k'wayar idonshi, Hamna ma dake gefe tana jin ya fad'i haka ta kalle shi duk da ba ita yake kallo ba, tab'e baki tayi ganin sun k'urawa juna ido. Tana kallon idon nashi tayi saurin sunkuyar da na ta tana dariya tace "Ba zan iya ba yah Ammar, mutuwa zanyi da tsoron abinda nake gani."

Wani shak'iyin murmushi ya mata ya shafa kumatunta yace "Ki ci gaba da kasancewa haka to ko da ranki ya b'ace a kaina."

Sumbatar bakinta yayi yace "Ina sonki aljannata."

"Nima haka." Ta fad'a tana mayar masa da martani, ta gefen ido ta harareshi ko da taji ya fad'i kalmar, tsaki tayi wanda yasa ya kalleta yace "Yarinya kiyi aure ki rage zafin zuciyar nan, kin ganni nan ba zan fasa abinda nayi niyyar yi ba da duniyata, wannan kayan halak d'ina ne kuma malak, naga wanda ya isa ya hanani yin abinda naga dama."

A hassale ta kalleshi tace "To ina ruwana, dama na fad'a maka zan hanaka wani abu ne? Su dake halak d'in naka dai kaji da su, wasu ai sun maka nisa."

Cike da rainin wayo yace "To ina ruwana dana wasu dama? Na ga dai duk abinda ke akwai can shine anan, to miye na k'aryar kuma?"

Ita ma murmushi tayi tace "Banyi musu ba cewa akwai hallitu dayawa da suke iri d'aya da na ta ba, amma bai zama lallai komai ya zama d'aya ba, kamar yanda tasirin ma ba d'aya bane."

Kallonta yayi da wata fassara a fuskarshi kafin ya kalli Amna yace "Duniyata na tambayeki mana? Yanzu dan Allah sai muka je shago tare muka siyo alawa iri d'aya a ledarta, yanzu zaki yarda na ce tawa tafi taki kyau da dad'i ko kuma ni na yarda idan kika fad'a min haka?"

A tare Hamna da Amna suka ce "Ya danganta."

"Ya danganta." Kallon kowace yayi sai Hamna data d'ora da cewa "Ya danganta idan ya zamana ita ta fika jin dad'in abu a bakinta, ko kuma ya zamana dama ta fika son alawar ko kuma ta fika sanin dad'inta, sannan zai iya yiwuwa a lokacin bakinta na da d'and'ano kai kuma naka baya da, ko kuma ya zama wunya take ji wanda hakan zaisa duk abinda ya shiga bakinta ta fika jin armashinshi, dole ko iri d'aya ce wani sai yafi wani jin dad'insa a baki, sann..."

"Ke dallah can ya isa." Ya daka mata tsawa, hararanta yayi yace "Sai wani maganar jin dad'i da d'and'ano kike, amma dai kin yarda alawar d'aya ce ko? To Alhamdulillah daya zamana komai iri d'aya ne babu wata burga da za'a mana."

Kallon Amna yayi "Yar banza shine kika shigar mata dan tana yer uwarki ko? Ke baki san bayan miji ake shiga ba."

Lab'e fuska tayi dan haka ya kalli Hamna yace "Ke rumbud'ed'iya biyo ni na baki sak'o ki kawo ma masoyiyata."

Kallon juna sukayi a tare, dan haka ya kalli Amna yace "Sak'on soyayya ne zan bata ta kawo miki."

Da sauri cikin jin dad'i Amna ta kalleta tace "Dan Allah yer uwa tashi kije."

Juyawa yayi zai fita Hamna tace "An k'i a je d'in, Allah Amna ki fita idona, kai kuma wallahi ka da ka sake tanka min k'ibata, idon sha'awarta kake kasa matarka tayi maka can ka cinyeta idan kana so, maye kawai."

Yanda ta k'arashe da murgud'a baki da harara yasa shi kallonta yace "Ai aljannata idan tayi k'iba saita hanani fita gaba d'aya, a yanzun ya muka k'are tana neman kasheni bare ta k'ara auki."

Wani haushi ne taji na neman kasheta, to wai akan me yake mata wannan rashin mutumcin? Ina ruwanta dashi ma da zai rik'a b'ata mata rai?
Cikin shagwab'a Amna ta kalleshi tace "Duniyata, ya isa haka mana ka tafiyarka saika dawo."

Kallon Hamna yayi yace "Kin ci albarkacinta, yanzu tashi muje na fad'a miki abinda nayi niyyar fad'awa masoyiyata."

Cike da tsiwa tace "Ba zanje malam ka d'aukeni in ana dole."

Bushewa yayi da dariya yace "Na d'aukeki? A gaskiya yanzu ban shirya ganin likitan k'ashi ba, gashi kuma yanzu rob ya k'ara tsada a kowane shago, dan haka ba zan iya ba amma wallahi sai kin je."

"To na gani idan akai zaka d'auke ni."

Nufowa yayi wajenta da sauri ta mik'e tsaye tana ja baya tace "Ammar bana son iskanci fa, Allah ka addabeni, wai kai baka da abunyi ne daya wuce ka bini a guje?"

Kallonta Amna tayi ta kalleshi tace "Dan Allah yah Ammar ku fita farfajiya, ni dai kaga ba iya tashi zanyi ba bana so ku fad'o min ku k'arasani."

Kallon Hamna yayi yace "Ni ne Ammar kai tsaye ko kankana? Kuma ni ne baki san iskanci? To ki rubuta wannan kalaman ki aje saboda ki iya tuna dalilin da yasa na hukuntaki yayin da na miki rugu-rugu."

Hanya ya kama zai fita ya kalleta yace "Ke dai kinfi kowa sanin kalar nawa horon, tarihi nake kafawa mutum idan har na tashi zuwar masa."

Gabanta taji ya shiga fad'uwa dakan uku uku da sauri, ai kuwa ta sani dan ya kafa mata wannan tarihin, to miye abunyi? Hak'uri! Na bashi hak'uri kawai tunda na ga jarababbe ne na k'arshe kuma kaifi d'aya, bugu da k'ari kuma bugu d'aya yake yi sak'onsa ya isa inda ya aika shi, kallon Amna tayi tace "Ina zuwa."

Da gudu ta fita ta nufi wajen ajiya motoci, tana hangoshi ta tsaya tafiya d'aya bayan d'aya, har ya shiga ya tayar ya hangeta saiya bud'e ya zuro k'afa d'aya yana kallonta har ta k'araso, murmushin gefen labb'a yayi yace "Kin zo bayar da hak'uri ne? Munafuka kinji tsoro kenan?"

Had'e fuska tayi ta harareshi tace "Allah ya sawak'e na baka hak'uri, kawai na zo fad'a maka..."

Shiru tayi ta rasa abinda zata fad'a sai shi yace "Me kika zo fad'a min?"

"Na zo karb'an sak'on ne." Ta fad'a da sauri, wani murmushin ya sake yi ya kalleta da kyau yace "Kankana, wannan kayan da kika ce sun min nisa ki sani daga yau su ma *mallakina ne*, ka da ki kuskura ki jawa wani tsautsayi ko k'arar kwana ta hanyar k'ok'arin mallaka masa mallaki na, in kuma ba haka ba to ki sani har ke sai nayi kasonki (prison)."

Yana gama fad'a ya rufe murfin motar da k'arfi yayi baya baya ya daidaita ya fita a gidan, fitsari ne ko kuma ruwan haihuwa? Bata san ainihin meye ke son zubo mata ba tsabar kad'awar da cikinta yayi, to me yake nufi? Zai ajiyeta ne a haka yayi ta kallonta yana tsokanarta yana binta da gudu? Ko kuma karuwarsa yake da niyyar mayar da ita? Wannan al'amari yafi k'arfin tunaninta, amma zata k'aryatashi ta nuna masa ita ke da kanta bashi ba, zata nuna masa abinda ya faru ma ya k'wata ne da k'arfi ba da son ran ta ba ya karb'a, yanzu kuma zata bawa wanda ya dace ne, amma ba zata zauna ba kamar yanda yake mata wannan fatan, dan kuwa fatan zama ne yake mata.

*Da dare* yana kan hanyarshi ta dawowa gida tsautsayi da ba'a saka masa rana ya afka mishi, mai mashin da wata mota ne suka kwatse sai kawai suka bigi tashi motar daga k'ofar da yake zaune, Allah ya kiyayeshi bai ji wani ciwo ba sai buguwa da k'afarta tayi, bayan jami'ai sun zo sunyi dube dubensu da aune aune aka tafi asibiti, ya so tafiyarshi gida amma lura da

Please Login or Register in order to submit comment