Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*SADAUKARWA GA*

πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ _*AHALI NA*_πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦

πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_68_


"Wai Ummy Abbana mijinki na shekaru barkatai, yau dan kin masa wani d'an laifi shine yana kallonki kika fice a gidan nan bai tsayar dake ba, Ummy ba wannan yafi damuna ba kamar yanda wai saida Hajia ta lallab'a sa tace ya dawo dake, wai Ummy kinga kuwa yanda take rok'onshi, humm ai ni abun ya mugun b'ata min rai wallahi, ji nake ina ma ace nine wallahi...hmmm shikenan dai Ummy sai anjima, zuciyata ma zafi take zan je nasha magani."

Ko da ya gama fad'a ya kashe kiran, Ummy da tunda ya fara magana take dariya ta riga data hango manufarshi, murmushi tayi tana kallon wayar tace "Ja'irin yaro nasan me kake nufi, zanyi yanda kake so dan nima raina ya b'ace."

Shima ko da suka gama wayar wanka ya shiga ya fito ya shirya cikin farar shadda, fita yayi hankali kwance yana istigfari da hailala a bakinshi har ya isa mak'abarta, a gaban k'abarin yake durk'ushe, kallon k'abarin yake inda abubuwa da dama ne ke zuwa mishi a kanshi, na farko akwai wa'azantarwa a game da lamarin mutuwa, sannan rayuwarshi da ita tarihi ya kafu wanda babu abinda zai iya goge shi, addu'a ya shiga kwaranya mata kamar saukar ruwan sama, ya d'auki tsawon lokaci kafin ya shiga gabatar da addu'a ta duka musulmin dake kwance, tare da addua'r Allah ya kyautata nasu k'arshen yasa mu cika da imani, awa d'aya da rabi ya d'auka a mak'abartar kafin ya juya ya tafi cike da kewar ma'abociya aminci da salamarshi. Gida ya koma ya cire kayan nan ya saka wando iya gwiwa ya kwanta abinshi a falo.

Da safe d'aya daga cikin wanda suke zama tare yaje har gida ganinshi daya fad'a masa abinda ya faru dashi jiya, a k'ofar gida suke tsaye yana jajanta masa, shi dai kunya da takaici basu barshi ya fad'i abinda ya faru ba, saida abokin yayi shirin tafiyarshi sai yace "In tambayeka mana abokina?"

"Uhum! Ina ji." Cewar abokin yana kallonshi, gyara tsayuwa yayi yace "Dan Allah kasan yayan yarinyar nan Hamna?"

Kallonshi yayi yace "Hamna? Wacece hakanan?"

D'an tsaki yayi yace "Yarinyar nan mai salon mana ta kusan fada."

"Oho, na gane, wane daga cikin yayanta? Kasan fa yar gidansu Jibril ce."

"Yayanta ne shi?"

Cikin rashin tabbas yace "Eh to ban sani ba gaskiya, kasan yawa ne da mutanen."

"To kasan Ammar?" Shi ma ya fad'i hakane saboda yaji sunan daga bakin Hamna sanda tace ka k'aleshi Ammar, cikin rashin kulawa yace "Ina jin sunanshi dai a gari."

"To baka san wani wanda ya san shi ba?"

Cikin kallon rashin fahimta yace "Akwai Jibril, d'an uwansa ne, amma me yasa kake nemanshi?"

"Ba ruwanka, kayi k'ok'ari ka samo min da hoton shi kawai."

Yanda yayi maganar zaka san ba lafiya ba dan haka yace "Ka fad'amin mana me ke faruwa?"

"Ba komai, in zaka samo min ka samo min, in kuma ba zaka iya ba ka bani lambar Jibril d'in."

Cikin damuwa yace "Haka kawai shi ba mace ba na zauna ina neman hoton fuskarshi, ba zan iya ba gaskiya, d'auki lambar Jibril d'in kai saika kirashi da kanka."

"Bani." Ya fad'a yana bud'a sΓ©curitΓ© na wayarshi dan d'aukar lambar, yana juyawa ya tafi shi kuma yayi kiran Jibril, faran faran suka gaisa cikin sakin fuska, saida Jibril yace ban gane ba sannan yace "Eh ba zaka gani ne ba, abokin Ammar ne ni, dan Allah inba damuwa fotonshi nake so ka turo min, shi ya k'i turo min ne dana tambaye shi."

Ko alama Jibril baiyi mamaki ba ko tunanin wani abu daban, abinda ya sani kawai shine watak'ila Ammar zai raina masa hankali da fuskokinsu biyu shi da Amar, dan haka sai yace "Ba damuwa, yana son yi maka iskanci kenan ka rasa gane shi."

Da farin ciki yace "Yawwa nagode sosai."

"Ba komai." Ya fad'a shima sukayi sallama, lambarsa ya shigar a wayarsa kafin ya tura masa hoton Ammar d'in na ranar d'aurin aurensu, ko da yaga hoton ya k'are masa kallo yace "Duk yanda akayi wannan soja ne, dan dukanshi ma bana wasa bane, amma zan rama an dad'e ba'a yi sama aka durmiyo k'asa ba."

*Da yamma* Abba suka shiga garin kai tsaye gidan k'anwar mahaifiyarta *Ardayi* suka wuce dan yasan can zata nufa, matar akwai karamci da sanin takamata, dan kamar yanda a gida suke ganin laifin lieutenant ita kuma laifin Ummy take gani, dan Ummy bata b'oye mata komai ba, yanzu ma da suka zo cewa tayi bata ji dad'i ba daya k'yaleta ta zauna gidan har ta gasu, faran faran suka gaisa ta kuma jadadda mishi hak'uri da kanta tare da cewa yarinta ceπŸ˜‚, lieutenant kanshi saida yayi dariya, ciki ta shiga ta kira Ummy ita kuma ta shiga had'a mata kayanta dan su wuce duk sanda suke so.

Tun kafin ta k'araso inda yake zaune kan kujera ta basar ta had'e fuska irin ba wasan nan, tana zuwa ko zaune ba tayi ba ta tara masa hannu, πŸ˜‚ (Allah gamu gare ka) d'aga kai yayi ya kalleta da mamaki, mayar da kanshi yayi k'asa bai tanka mata ba, cikin jujjuya baki tace "Kai nake jira."

D'aga kai ya sake yi ya kalleta, ba alamar wasa shi ma yace "Baki iya sallama bane?"

Saida ta turo baki tace "Ina wuni."

"Ba wannan na tambayeki ba ai."

Kallonshi tayi sai kuma ta juya baya ta rik'e k'ugu ta sake mik'a hannunta tace "Ka bani na juya na koma ina da abun yi a ciki."

Kallon nutsuwa ya mata yace "Me zan baki wai? Kin bani ajiya ne?"

Juyowa tayi da mamaki tace "Ban gane me zaka bani ba? Takarda ta mana."

Da sauri ya kalli idonta yace "Kinga Sa'ada ba wasa na zo muyi ba, ki d'auko kayanki ki wuce mu tafi, komai dare ina so mu bar garin nan."

Wani yamutsa fuska tayi tana kallonshi tace "Ai ba haka mukayi da kai ba, ko ka manta?"

Kallonta yayi sai kawai ta ma bashi dariya ganin har wani girgiza take wai ita rashin mutumci take so ayi, mik'ewa yayi ya tsaya gabanta yana k'are mata kallo yace "Jaraba kike so muyi Sa'ada?"

Saida ta rage girman idonta tace "Eh, ai gidanmu ne nan ina da masu tsaya min."

Ba alamar annuri yace "To ni kuma kinga a gidan naku zan kakkarya ki kuma a gode min akan haka, amma bana so a k'ara miki wani dukan bayan wanda zan miki, dan haka in bala'in kike ji muje gida sai ayi."

Matsawa tayi baya tana fad'in "A'a me zai kaini gidanku, ni na zo gidanmu kenan ai da kake gani na nan, da kaga na fita to..."

Shiru tayi tana k'yabta ido dan bakinta yake kallo kamar jiran yaji me zata fad'a yake, saida ya kawar da kanshi yace "Ki d'auko jakarki mu tafi, in kuma ba zaki tafi ba ki gaya min."

Saida ta juya d'an k'aramin bakinta mai d'an tsayi kafin tace "Eh."

Da kyau ya kalleta yace "Eh me?"

Saida taja baya sosai ta saita k'afafunta k'ofar shiga cikin d'akin Ardayi sannan tace "Ba zan tafi ba."

Da sauri ta k'arasa shigewa ciki tana ma kanta dariya, da kallo ya bita yace "Eh lallai yarinta ce kamar yanda Hajia suka fad'a."

Fita yayi ya samu dreba suka k'arasa wani masauki mai kyau a garin suka yada zango anan, dan ya lura wannan bikon mai tsada ne na gaske, watak'ila saiya salwantar da wasu zinariya kafin ta yarda su koma, tunda dai ba zai yarda yayi tafiyar banza ba, uwa uba kuma umarnin gwamnatinshi ce dole a cika ko ba'a so.

Saida akayi sallah magrib yayi wanka yana kwance ya d'auki wayarshi ya tura mata gajeran sak'o kamar haka "Uwar Ammar ce quoi t'on problème? Qu'est ce que tu veux?"

Sanda ta samu sak'on murmushi ta saki ta mayar masa da harufa hud'u tace "Rien."

Shi ma maido mata yayi da "In dai hakane to ki yarda mu koma gobe."

Maido masa tayi da "Indai hakane saika yarda zaka hau rak'umi a garinmu."

Zaro ido yayi yana k'ara nanata karantawa, maida mata yayi da "Amma ai na hau lokacin aurenmu, me zaisa yanzu na hau da girma na haka kawai."

Cikin basarwa tace "Shikenan sai ka koma inda ka fito kai kad'ai."

Ba alamar wasa a amon muryarshi yace "Kinsan Allah, wallahi tare dake zan koma, bari ganin fa ina lallab'a ki sa'a ce kika ci."

Wata dariya tayi kafin ta maido da " *Sa'ada, Sa'adatu sa'ar mata, ko bakiyi kyau ba kinyi sa'a*, ka daina fad'in sa'a a gabana sunanta gare ni."

Iko sai Rabba, da mamakin wannan sabon canjin dan shi dai bai santa da shi ba yace "Nima fa har yanzu ban huce kan abinda kikayi ba, dan kin samu na zo shine sai kin waina ni."

Kafin ta maido ya kirata a wayar dan ya tabbatar mata ta shirya gobe zasu koma, ko da ta d'auka tace "An zo wurin, ai dama an fad'a min ba da son ranka ka zo ba saboda ba so na kake ba dama, shiyasa nake so kawai ka bani takardata tunda banda mahimmanci a wurinka."

Cike da mamaki yace "Sa'ada ni? Ni ne kike fad'awa haka?"

"To ai gaskiya ce." Ta fad'a tana juya baki kamar a gabansa, cike da kokonto yace "Anya kuwa Sa'a baki yi waya da babban d'anki ba? Dan naga irin fitinarsa ke kike min yau d'in nan."

Kai tsaye tace "D'ana ba fitananne bane gaskiya kawai yake fad'a."

"Shikenan." Ya fad'a yana d'orawa da "Yanzu fad'a min abu d'aya, zaki shirya ko kuma ba zaki shirya ba, dan ba zan zauna ina lallab'aki ba sai kace wasu yara masu shirin aure."

Cikin muryar shagwab'a da kuka tace "Eh mana kace haka, idan kana tare dani sai ka nuna min mun girma mun tsufa muna da yara da jikoki, amma idan ka shiga d'aya d'akin saika d'anyance ka zama yaro kana kinibibi..."

Duk da ta kai k'arshen kalmar amma saida ta rufe baki, rarraba ido ta shiga yi tana saurarenshi yana fad'in "Ade nine kinibabben? Ba damuwa karki je d'in ki ci gaba da zama anan."

Kashe wayar yayi ya aje gefe, shi kad'ai kamar wanda aka tab'a saiya fashe da dariya kuma, wai kinibibi? Shi ne yau ake ma rigima, ko Zeituna dake yarinya ai yanzu ta daina tunda ta haifi nata yaran, in kaga rigimarta yanzu ita ma tana son wani abu shi kuma yaga yanzu ya wuce wannan ajin, to fa haka zasu kwana tana botsare masa yana tarota tana baud'ewa.

A gida kuma rabon ayi zamu ce Amar na kan hanyarshi ta dawowa gida saida ya shigo cikin kwanar gidan wasu samari biyu suka sha gabansa, tsayawa yayi ya bud'e mota ya fito, tunda dai suka ga fuskar wanda suka gani a waya aka kuma biyasu kan su jigata shi sai kawai suka mame shi da duka, su bakwai ne dan haka babu yanda ya iya dasu, dan bak'in ciki kuwa shi ma saida suka masa tsinanniyar karaya a hannu, abunka ga unguwar masu hali babu hayaniya mota ko moto ma sai jefi jefi suke wucewa, saida suka ga ya daina motsi suka barshi nan ba tare da sun raba shi da komai na sa ba sai su da suka d'ora masa takarda a kan jikinshi.

A k'alla mota uku ta wuce amma babu wanda ya kula dashi, Junaid ne kad'ai da yaga motarshi ce anan ya tsaya da niyyar tuntub'arshi yaji lafiya, ya shiga tashin hankali sosai ganinshi a kwance kamar ba ma kama bace babu rai kam, gigicewa yayi ya rasa ta ina zai fara, sai yayi bakin titi da gudu kuma ya dawo yayi hanyar gidan kamar ya k'arasa, yayi haka har sau hud'u kafin daga bisani ya fara kiciniyar janshi zuwa mota, a lokacin kad'ai takardar data fad'i ma ya kula da ita, da sauri ya d'auka tunaninshi abune mai mahimmanci, saida ya bud'a ya karanta rubutu kamar haka " _Duk wanda ya min kankara sai nayi masa na itace, baka dake ni ka karya min hannu akan banzar k'anwarka ba, to ka dafata ka cinye kai kafin nan muyi jinya tare, banza dak'ik'i mai k'walwar kifi."_

Da sauri ya zura takardarshi ya ci gaba da janshi har ya sa shi motarshi ya fizga ya bar erea, da suka tafi ganin yan uwa ne da yallab'ansu suka karb'eshi da gaggawa, dan su duk da sun san Amar amma tashin farko ma sun d'auka Ammar d'in ne, cikin ikon Allah suka samo shi dan dama k'ananun raunika ne sai karyar hannu da suman da yayi, saida aka bawa Junaid kyakyawan labari kad'ai ya samu nutsuwar kiran d'an biyun Amar d'in.

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

Wallahi yana gida kwance yana kallo ana lallasa d'an uwanshi sakamakon masifarshi, da Junaid ya fad'a masa cikin tsananin damuwa da d'an uwanshi yace yana zuwa, bai d'auki lokaci mai tsayi ba ya isa ya same su, har ga Allah Junaid bai nuna masa takardar nan ba dalilinshi kuwa shine, in dai ya gani to baisan ina rigimar zata tsaya ba, a sanin daya ma Amar ba mutum ne mai rigima ba, shi fa da Ammar d'in ne to ko shakka ba zaiyi ba, amma Amar har yanzu abun na bashi mamaki, duk tambayar daya masa sai dai yace ba komai ko ban sani ba ko uhum, haka ya d'auki Amar yace ai sai dai su koma gida, ya zaiyi inba zuba ido ba, yana kallo ya labta Amar a bayanshi ya fito dashi har waje kuma yana k'orafi wai zai karya masa baya k'aton wofi.

Da suka dawo gida ma zasu kaishi b'angarenshi ce ma Junaid yayi "D'ora min shi a baya."

Saida yayi dariya yace "Kamar wani yaron goye, dan Allah ka barshi zai tafi da k'afarshi."

Amar ma cikin yanayin jigata yace "Zan iya tafiya, nagode."

Kallon fuskarsa yayi ya masa gwalo yace "Ka daku fa, wai waya dake ka haka kana tsaye kana kallo kuma?"

Saida suka fara takawa suna rik'e dashi yace "To ni ina na sani, rufeni kawai sukayi kamar Allah ne ya aikosu."

Ammar ne yace "To me ka musu? Fad'a kake yi dama a waje?"

Murmushin k'arfin hali yayi yace "Fad'a dai Ammar? Haba dama dai kaine ai ba za ayi mamaki ba, na sani yanzu ma wani ja tsokana shine ya sauke akai na da tunanin ni ne kai, ai kasan ba yau aka saba haka ba, kankana ma nasha cutuwa a hannunta idan ta tashi zuwa d'aukar fansa."

Shiru Ammar yayi, tunanin kalaman Amar yake yi, tabbas fa maganarsa gaskiya ce, to idan fa hakane? Amma waye ya zo dukanshi ya daki d'an uwanshi? Wane mai k'arar kwana ne wannan? Har suka kai b'angarenshi bai iya tunawa ba, to ai abun dayawaπŸ˜‚ ba zai iya cewa gashi ba, shi ya sani a dangi ma ana jin haushinsa bare kuma waje, duk da dai wanda fad'a ya tab'a had'asu dashi na akai ga jiki ba yawa ne dasu ba, shi ma kuma shi ne ke saurin kai hannu maimakon cacar baki, wanda kuma ya dank'arawa magana da zagi da yan k'ananun abubuwa basu da adadi, Jano kuma da yayi sanadiyar shigarshi gidan maza shi bai ma san a ina ake ba yanzu, dan tunda aka kama shi ya rufe babinshi ya shiga wata sabgar, sai wanda ya daka suna tare da marigayiya Amna, sa kuma wannan na jiya shima, to cikinsu kuwa akwai wanda ya daki d'an uwansa.

Saida suka shiga suka zaunar dashi Farisa da Umaimah hankali tashe suke tsaya kansu suna tambayar me ya faru dashi? Babu wanda ya basu amsa sai Ammar daya kalli Farisa yace "Ku samo mishi abinci ya ci yasha magani.

"To." Ta fad'a tana nufa madafa, Junaid ma fita yayi yaje ya sanar da iyayensu, dukansu suka rukuto suka taho da mamakin abinda ya fad'a musu da kuma jimami.

Ko da Junaid ya fita ya kalli Amar yace "Dan ubanka fad'a min wa kayi fad'a dashi?"

"Allah babu kowa, to wai me zai kaini fad'a kamar marar aikin yi ko yaro k'arami."

Ko da su Hajia suka shigo sun samu yana fad'in "To inba wani abu kayi ba wa zai maka wannan dukan har da karya maka hannu."

Cikin tashin hankali suka jajata masa suna tambayar ba'asi, maganar dai d'aya ce bai san komai ba kawai an rufe shi da duka ne, sai lokacin Junaid ya fara lalaba aljijunshi yana fad'in "Bari kuga abinda na gani kusa da inda na same shi kwance, abun yafi kama da d'aukar fansa."

Firo da takardar yayi ya mik'a ma Ammar, daki daki ya shiga kallon kowace kalma yana hardaceta a kanshi, kowa ya zuba masa ido suji me zai ce sai ji sukayi ya gunduma wata ashar yana fad'in "Kuturun uban cen, ni? Yanzu nine wannan yaron ya ma tarko dan ya dake ni? Shine har da wata tsinanniyar wasik'a yana kirana da dak'ik'i, kankana kuma ita ce banzar? Banza fa, bayan yace min mai k'walwar kifi, ah lallai."

Mik'ewa yayi yana jefar da takardar zai fita Junaid ya rik'oshi yana fad'in "Ina zaka je Ammar? Ka wa Allah da manzonsa abun ya tsaya iya haka?"

Kallonshi yayi yana murmushi yace "Haba dai kaima fad'a kawai kake, k'anan na wa su masa wannan dukan sannan ya kira kankana da banza, ni kuma dak'ik'i mai k'walwar kifi kuma ka ce na k'yale, to miye anfani na kenan inhar zan iya yin shiru kan wannan cin zarafin."

Zai wuce ya sake rik'eshi sai Hajia da tace "Ammar dan Allah dan uwarka Sa'ada ka k'yaleshi koma wanene, kaga dai abinda ya faru yanzu bala'in ya fad'a kan d'an uwanka, ita fa fitina kwance take mu ne ke tashinta."

Hajia ya kalla yace "Dan Allah Hajia ki cire bakinki a maganar nan, abu d'aya da nake so dake shine ki kira tonton colonel ki fad'a masa yau zanyi kisan kai ya tanadar min wuri a gidan maza, mazan ma k'arti manyan yan ta'adda."

Husseina ce tace "Subhanallah, mun shiga uku mu kam, Ammar kisan kai?"

Ko kallonta baiyi ba ya fincike a hannun Junaid ya tunkari fita, karo suka ci da kankana da yara suka fad'a mata iyayen na b'angaren tonton Amar, bata san hawa ba bata san sauka ba kawai yace "Yar banza mai shegen farin jini, to yau dai gashi banzan lusarin saurayin naki da kika kunyata iyayenki akan shi shine ya turo miki sak'o yake kiranki da banza, wai banzar k'anwata na dafa ki na cinye."

Ita dai da bata fahimci komai ba wucewa tayi ta gaishe da Amar tana masa ya jiki, dawowa yayi yana kallonta ya ci gaba da zazzaga masifa wai duk ita taja, ko kallonshi ma ba tayi bare ta kula shi haka kowa ma yaja baki yayi shiru, saida ya kalli kowa yace "Eh mana ga d'an iska mahaukaci na magana, dole kowa ma yayi shiru, to ni na tafi sai kunje gani na a gidan yari."

Kamar zai tashi sama ya nufi k'ofar fita cikin rashin kunya Umaimah tace "...


*Insha Allah zanyi k'ok'ari nayi wata page d'in anjima amma fa idan kunyi comment, ku shirya kowa ya kawo goron d'aurin auren fitinannu na.*



*Alhamdulillah*
04/11/2020 Γ  14:38 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*BADAK'ALA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ _*AHALI NA*_πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦

πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_69_


"Yanzu dama akan ka ne aka dakar min mijina? Dan Allah yah Ammar wace irin rayuwa ce wannan kai da jan masifa shi da shan duka? Ya kamata fa ace kasan ka girma amma irin haka bai kamata ba, yanzu gashi baisan hawa ba bare sauka kawai an sauke mishi kwandon rashin mutumci, gaskiya dai akwai alhaki wallahi Allah ma ba zai barka haka ba, haba mutum sai jaraba kawai k..."

Kamar saukar aradu kowa yaji Hamna ta daka mata tsaw da cewa "Ke."

Juyawa tayi ta kalleta suka shiga kallon kallo kafin ta nuna mata shi tace "Umaimah tsaranki ne shi da kike fad'a masa haka? Saboda an daki d'an uwansa wanda na tabbata baki fi shi jin zafin a zuciyarshi ba, ki tambayi shi yah Amar d'in kiji kafin ki ci masa albasa, shin yana jin haushin d'an uwansa kan abinda ya faru yanzun?"

Cikin rashin mutumci tace "To ke kuma a wa? Dake nake bare ki sa min bakinki? Ki bari shi da nayi dashi ya tanka min mana amma bake ba."

Murmushi ta mata tace "To ai naga ba shi ne daidai ke ba, ni nan ni ce daidai da ke wallahi."

Ammar dake kallon ikon Allah saiya bushe da dariya ya nemi kujera ya zauna yace "Buga min ita a k'asa kankana, yau saina cika miki gidan nan da kankana Allah kuwa."

Kallonshi tayi ta dalla masa harara ta mayar da hankalinta kan Umaimah da tace "Kin tare masa saboda ke ce daidai dani? Ko kuma kin tare masa saboda shine uban d'anki?"

Hajia da Husseina ne suke musu magana amma bata saurare su ba saida tace "Ki d'auka a yanda kika ga zai fi miki sauk'in d'auka akan ki, amma idan zan zab'ar miki sai nace barshi dan yana uban d'ana, ai kinsan saduwa ba k'arya bace, haka ma haihuwa ba wasa bace, ai ke wannan abubuwan biyu ne yasa kike tayar mana da jijiyar wuya saboda an tab'a mijinki, ke ga mai miji maji dad'in miji."

Cikin shewa da tapa hannaye tace "Wuuuu! Alhamdulillah Ina da mijin da zan iya nunawa, kuma nagode Allah daya bani mijin da nake jin dad'in dashi, ke fa? Har yanzu gantali kike a titi har kin tsofe a gari babu mai so, sannan kaf yarana na haife su a k'ark'arshin inuwar aure, har nayi zamani na ban aje d'an dak..."

Dan bai da kuzarin da zai tashi ne amma yayi niyyar marin fuskarta, dan haka kawai ya daka mata tsawa da cewa "Umaimah."

Shiru tayi tana hararan Hamna wacce ita ma ke kallonta tana murmushi, cikin b'acin rai ya gyara zamanshi yana kallonta yace "Umaimah me yasa baki da hankali? Ta tsawarta miki ne saboda kina d'aga murya kan babba kuma d'an uwana da take da tabbacin ba zan ji dad'in abinda kika masa ba, yaushe zakiyi hankali ne wai?"

Wani harare ta sake dalla ma Hamna tana turo baki gaba tana gunguni, ba tare daya daina kallon fuskarta ba yace "Ba tace ki tambaye ni ba? Me yasa baki tambaye ni ba? To bari ni na fad'a miki kiji da babban murya, wannan dukan da d'an uwana aka wa shi wallahi ba zan sake cin abincin gidan nan ba har sai ranar da idona suka ga cikakkiyar lafiyarsa, Umaimah ina farin ciki sosai da godiya ga Allah da dukan nan ya tsaya kaina, yanzu haka na yafewa wanda yasa aka dake nin, amma da d'an uwana ya daka har abada babu yafiya tsakani na da shi, dan haka wuce d'akinki bana son ganinki a wurin nan."

A hassale ta kalleshi tace "Ni ce ma mai laifi kenan? Ba damuwa."

Ta fad'a tana wucewa d'akinta, da harara ya bita cike da takaicin hallayarta yana fad'in "Inma da damuwar fa sai me."

"Hahahahahahahahahahha, wuuuuuuuuuu, wayyo Allah na, Hajia kin gani ko?" Cewar Ammar kenan dake nufa kusan Hajia, nuna mata Hamna yayi yace "Allah Hajia yarinyar nan so na take, kiji fa yanda take fad'a dan an tab'a mata ni, wuuu! Gaskiya zamuyi kyau da aure."

D'ora kanshi yayi kan kafad'ar Hajia cikin jin kunya yace "Dan Allah Hajia ki daure ki aura mata ni, kinji?"

Me Hamna za tayi ba dariya ba, har ga Allah shirmenshi ko rashin kunyarshi suna bata haushi da takaici, amma na yau saiya bata dariya da yace wai ta daure ta aura mata shi, kallonta yayi ya kalli Hajia yace "Kin gani ko, na fad'a miki ai."

Junaid ne yace "Yanzu ya maganar d'aukar fansar to? Ka hak'ura kenan?"

Kallonshi Husseina tayi kallon ya kuma zaka tuno

Please Login or Register in order to submit comment