Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

"Amna baki da hankali ne? D'an iska kika mayar dani ko me? A wannan lokacin kika fito daga gida kika zo nan kuma da wannan shigar?"

Kallon kanta tayi, riga da siket d'in na leshe wanda suka amshi jikinta sune matsalar? Ko kuma d'aurin data b'ata lokaci ta kashe wajen d'aura shi? Kwalliyar fuskarta ko kuma mayafin data yafa? Kallonshi tayi tana turo baki gaba duk tayi kalar wallahi kuka zan ma ka tab'ani, a hassale yace "Billahil azim kifar dake zanyi wurin nan kika min kuka, ke ni d'an iska ne?"

Girgiza kai tayi da sauri tana fad'in "A'a." Rik'e k'ugu yayi yace "To uban wa yace ki fito haka? Kuma waya kawo ki nan?"

Saida ta k'ara yin kalar tausayi sannan tace "Aunty Zeituna ce."

"To waya kawo ki?" Ya sake jifarta da tambayar, saida ta d'anyi baya kad'an tana kallonshi sannan tace "Adaidaita...Ahhhhh." Ta fad'a da k'arfi saboda d'aga hannu da yayi kamar zai kifeta da mari, a hankali ta bud'e idonta jin bai sauke mata yatsunshi ba a kumci, kallonshi tayi sai taga ya k'ura mata ido yana kallo, da kankana ce da yanzu ta zuba a guje, amma ita
saita tsaya ko kasheta zaiyi, abun ne ya bashi dariya sai kawai ya figo hannunta ta fad'a jikinshi ya rumgumeta yana dariya yace "Mahaukaciya, ke baki iya guduwa ba idan za'a dake ki."

Cikin shagwab'a tace "To yah Ammar taya zan iya tsere maka? Mai guduwarma (Hamna) naga in kayi niyya kana ritsata duk inda take."

Lumshe ido yayi yana sakin murmushi kafin ya d'agota yace "Yanzu to ki koma gida, amma k'asa zaki tafi in ba kya son ki jazawa masu adaidaita bala'i, kinji ko." Ya fad'a ba alamar wasa a tare dashi.

Shagwab'e fuska tayi tace "To ai ni ban zo dan na koma ba, nan zan kwana tare da kai."

K'ura mata ido yayi yana kallo, ya jima yana tausar kansa kafin yayi nasarar kwantar da hankalinshi yace "Amna kuka kike so kiyi ne?"

Da sauri ta rik'e hannayenshi tana fad'in "Bana so, amma kuma ina nan tare da kai yah Ammar."

"Me yasa?" Ya fad'a yana son k'watar hannayenshi, saida ta langab'e kai tace "Aunty Zeituna tace idan na zo nan dole Abba ma zai zo yayi belinka da kanshi."

Kallonta yayi sosai yayi murmushi yace "Uwa ta shiga al'amarin?"

Kai ta jinjina masa alamar eh, sai kawai ya zauna kan bencin ya sashi tsakiya yace "Zuba min abinci na ci kinji yarinya, tunda uwata ta shiga lamarin nasan ma dole zai zo."

Murmushi tayi ta fito da kwanukan ta soma zuba mishi abincin, har ta d'auki cokali zata fara bashi saiya girgiza mata kai, aje cokalin tayi ta wanke hannunta ta fara bashi da hannunta, yana ci yake ce mata wai tayi hak'uri na rashin zamanshi gida a tare da ita, uffan ba tace ba sai yanka mishi loma da take tana aika masa.

Tana komawa b'angaresu ta samu lieutenant a inda ta barshi, shiga tayi ta tsaya gabanshi tana kallonshi, ta jima tsaye amma bai motsa ba alamun baisan da zuwanta ba, ajiyar zuciya ya sauke tare da d'an juyo da kanshi hakane yasa ya ganta, cikin basarwa ya d'an had'e fuska yace "Ya dai?"

Murmushi ta masa tace "Ba komai."

Bai ce komai ba sai juyar da kansa da yayi, ita ma ba yanayin wasa a tare da ita tace "Yallab'ai akwai matsala fa."

Kallonta yayi yace "Matsalar me kuma?"

Saida ta gyara tsayuwa ta mayar da hannayenta bayanta sannan tace "Yanzu daga b'angaren Amna nake, na sameta tana ta kuka saboda rashin sanin halin da mijinta ke ciki, dana fad'a mata tayi hak'uri dan ba zaka je ka fito dashi saita d'auki mayafinta ta fita, da k'yar ma ta fad'a min tace zata je wajen mijinta ne tunda babu mai k'aunarshi."

Kamar an tsikare shi haka ya tashi tsaye yana mata wani mugun kallo cikin d'aga murya yace "Babu mai k'aunarshi? Wai wace irin magana ce kikeyi haka? Taya kike tunanin zamu haifi d'an a cikinmu amma mu ce ba ma k'aunarshi, akan me zaki fad'a mata haka kuma har ki bari ta fita a wannan lokacin, ke a ina kika tab'a ganin haka?"

Ba tare data nuna tsoron yanayinshi ba tace "Akan ku mana, kanku na fara gani."

Jinjina kai yayi yace "Ok, to ni kuma yau zan nuna miki k'arya kike, ina son d'ana kuma ina k'aunarshi fiye da komai dana mallaka a duniya."

Fuuu ya rab'ata zai wuce cike da shak'iyanci sai cewa tayi "Taya zan tabbatar ina daga nan bansan me ya faru a can ba?"

Tsayawa yayi ya juyoya kalleta da mamaki, raina shi ne tayi kome? Shi kananta ne da zata mayar dashi abokin wasanta? Saida ya jinkina mata kai yace "K'arfin shaukin da zan nuna masa zai riskeki har gidan nan."

Juyawa yayi ya fita ta bishi da murmushi Allah ya bada sa'a, tun a hanya yake k'ulla kalar k'aunar da zai nuna masa, to wai a kan me zata fad'a masa baya k'aunar d'an shi, ko bata san shine sanyin idaniyarshi na farko bane? Bata san duk suna mishi abinda suke mishi ne ba dan suna son ya gyaru ya zama na k'warai? Ta manta da duk fafutukar da yake saboda 'ya'yanshi yake yinta sannan Ammar shine magajinshi na farko? Me yasa bata tambaye shi me yaji ba a sanda aka fad'a mishi an rufe mishi? Amma ba komai zai nuna mata ba haka bane abinda take cewa ta ganin, da wannan tunanin ya isa ya baka tsandareriyar motar data sanar da jami'an babban mutum ya shigo, sanin sosai suka masa ba sanin shanu ba, dan haka suka sara masa cikin girmamawa ya shiga ciki, ikon Allah sai kallo, ganinshi hankali kwance matarshi na ciyar dashi cikin nishad'i, abinda ya aikata ya cancanta ya bibbige shi amma ba hali, k'wafa kawai yayi ya shiga inda zai samu belinshi. Cikin mutuntawa aka fad'a mishi ai Amar ya biya tarar kawai zasu iya tafiya, amma gobe da safe saiya dawo a musu sulhu saboda gaba, duk da haka saida ta d'ebo kud'in da baisan ko nawa bane ya zube kan teburin kafin suka fito, sai lokacin ne suka ga lieutenant, hannu ya d'aga masa yace "Abbana barka da dare, har ka iso?"

Tasowa yayi daga bencin kamar k'aramin yaro sai kawai ya rumgume shi yana wani k'amk'ame shi da kwantawa kan k'irjinshi yana fad'in "Nasan kana min son da baka ma kowa Abba, dama nasan zaka zo, ba zaka iya bacci a gidan can ba idan bana gidan nan, ko ba haka ba?"

Abun yafi k'arfin tunanin lieutenant, sai kawai ya tsinci kansa ya rumgume shi shima har da shafa kansa yana murmushin da baisan ko na miye ba yace "Gaskiya ne, ai indai har zaka kwana a nan to sai dai in gaba d'aya ahalin Gaga ne suka tare a wurin nan."

D'ago kai yayi ya kalleshi ba tare daya d'aga daga k'irjinshi ba, turo baki yayi gaba irin tunda na samu ka biye min to bari na yi abinda na jima ina kewarshi daga gareku, sai k'ara narkewa yake jikinshi kamar zai shige cikinshi, Amna dake kallon ikon Allah tashi tayi ta wanke hannunta ta had'a kayan, kallonta lieutenant yayi yace "Shikenan 'yata sai ki taho wurin mijinki baki sanar da kowa ba."

Murmushi kawai tayi kafin lieutenant ya d'agoshi daga jikinshi yace "To mu tafi ko?"

Kafad'a ya d'aga alamar a'a kamar yaron goye, kallon zan ci ubanka a wurin nan lieutenant ya mishi tare da cewa "Meye kuma?"

Cike da shagwab'a yace "Sai kace muje shalele."

Anya yaron nan banda aljanu kuwa? Tambayar da lieutenant ya ma kanshi kenan, wato dan ya ga ya zo shine saiya mishi iskanci yasa ranshi ya b'ace har ya kasa yin abinda ya fad'a, daga Ammar d'in har Amna kallonshi suke suna jiran suji me zaice, rarraba ido yake ganin jami'in dake tare dasu ne kawai yasa yayi murmushi yace "To muje shalele."

Dariya yayi ya rik'e hannun lieutenant da kuma hannun Amna suka rankaya yana fad'in "Daga yanzu ni ma na zama shalelenka, kaga Amar shalelen Hajia ne ni kuma na ka ko Abba?"

"Umm." Kawai ya fad'a ba tare da yace komai ba, kallonshi lieutenant yayi yace "Motarka fa?"

Saida ya bud'a ta lieutenant ya shiga ya hakimce sannan yace "Tare da Abbana zan tafi, gobe na dawo na d'auka daga nan nima saina shigar da k'arar wannan banzan."

Shiga sukayi duka Amna na baya yace "K'arar me kuma?" Saida ya kalleshi yace "Abba k'azafi ya min wai ina saka kayan soja, har da cewa wai ina da bindiga."

Kallonshi lieutenant yayi irin kallon nan na anya Ammar ba gaskiya bane kuwa, saida ya tayar da motar suka d'auki hanya kafin yace "Ka daina shiga rigima Ammar, bana jin dad'in haka fa, wai kai baka san ka girma bane?"

"Zan daina Abba, dana gama da wannan yaron shikenan." Ya fad'a yana kallon titi, *meye nufinshi akan Jano ne? Ni dai nasan da abinda yake so dashi*, suna zuwa gida suka fito a mota suka nufi hanyar da zata sadasu da b'angarensu, dole ta inda lieutenant ya paka mota indai zasu wuce sai sun bi ta k'ofar shiga falon Hajia, hakanne yasa Ammar hangota zaune kan kujerar mulki, murmushi yayi ya tunkari shiga ciki, rik'oshi lieutenant yayi yace "Ina zaka kuma? Wuce ka bi matarka."

Langab'e kai yayi yace "Abba Hajia zai gaida duk yau bamu had'u ba duk bana jin dad'i."

Wani kallo ya masa yace "Ammar uwata ce fa, karka ja min zagi yanzu a daren nan mana."

"Allah Abba ba zan sa ba, nayi alk'awari." Yana fad'a ya shiga ciki da sallama, Amna kam da take jin haushin tura mata yer uwarta wani wuri bata shiga ba sai na su b'angaren data nufa. Yana zuwa kamar an tura shi ya durfafeta ya rumgume tare da sumbatar goshinta yana fad'in "Hajiata ikon Allah, wallahi duk nayi kewarki wunin nan kawai da ban ganki ba."

Tareshi tayi daga jikinta tana goge goshinta da fad'in "Kai rabu dani dallah, wai kai baka da lafiya ne?"

Kallonta yayi ya dafa saitin zuciyarshi yace " Yanzu ne kawai na fara jin na samu lafiya da nayi tozali dake."

Da k'arfi ya sake fizgo fuskarta ya sumbaceta a kumatu yana fad'in "Ina sonki, saida safe, karki bari kishina ya hanaki bacci."

Saida ta marmad'a ido saboda yanda ya fincikota, da kallo ta bishi tana mamakin halin wannan k'waya d'aya tak dake saka mata hawan jini, yanda ta kafe k'ofar da ido har ya b'ace ma ganinta sai kawai taji tana murmushi, kamar an tsikareta sai kuma taja tsaki tana fad'in "Mahaukaci."

*Capital*

Baccin marar dad'i har ya fara d'aukarta d'aya daga cikin ma'aikatan gidan ta shigo ta kirata, fitowa tayi jiki a sanyaye ta zo ta tsaya gabanta kamar yanda ita ma take tsaye, kasa d'aga kai tayi ta kalleta saboda tun tana tahowa taga kayan bacci ne jikinta masu shegen kyau da d'aukar ido, kamar saukar aradu ta kashe ta da mari tare da mata tsawa tace "Idiot, ina tsaye shine ke ma zaki tsaya min a kai haka."

Dafe kumci tayi ta bud'e baki ta kalleta tace "Kika mare ni?"

D'aga hannu ta sakeyi zata sake marinta tayi baya da k'arfi tana fad'in "A'a wallahi, ko uwata ban rayu da ita ba ta yanda zan iya fad'a miki ranar data d'aga hannunta a kaina, dan haka ya tsaya nan gaskiya."

Cike da iko tace "Ni kike fad'awa haka? To bari kiga abinda zanyi, ubanki zan fad'a ma ya sanar dake k'arfin ikona, idan ya fad'a miki da kanshi zaki fi ji da kyau."

Juyawa ta shiga ta wata k'ofa da zata sadata da d'akin baccinshi, tab'e baki Hamna tayi ta juya ta koma ni'imtaccen d'akinta ta kwanta, amma abun takaici sai ga mahaifinta cikin jallabiya tare da matarshi sai wani rirrik'eshi take tana kukan munafurci, bata san me ta fad'a mishi ba? Bata san meya faru ba kawai saiya rufe ta da fad'a kamar saukar ruwan sama, saida ya gama sannan ya jaddada mata duk abinda Aissata ta sakata tayi ko bata so dan ita ce mai gidan nan, sannan idan ta mata musu Allah ya isa bai yafe mata ba, juyawa yayi suka fita sai kawai ta fashe da kuka, duk rashin kirkin Hajia suna sakata su wala, babu takura babu matsi sai in ka taka mata doka, amma nan, lallai ma.

To fa hakan data faru ne yasa washe gari da safe ta kirata, tana zuwa tace "D'aki na zaki gyara min ki min shinfid'a, idan kin gama ki wanke ban d'aki da kyau sannan kiyi turare, idan kin gama sai ki zo na fad'a miki aiki na gaba da zaki min."

Hararanta ta farayi sama da k'asa kafin daga bisani ta tuna kalmar Allah ya isa da mahaifinta ya fad'a mata, cikin ladabi tace "To." Ta juya ta shiga d'akin, duk ni'imar duniya ta taru a d'akin nan, kud'i ko nace kayan kud'i kamar zasuyi magana da baki tsabar yanda aka tarwatsa su, komai na kud'i ne d'aruruwa ko milyoyi, gyarawa tayi ta share ta wanke har ban d'akin ta goge komai sannan tayi turare, kama daga na ruwa na tsintsiya har na wuta, hakan yasa d'akin k'ara sanyaya da sanyin k'amshi, tana idarwa ta fito ta fad'a mata, ki shiga madafa ki samu *Betrice* ta baki jadawalin duk abinda nake ci da kuma lokacin da nake cin shi, daga yanzu ke ce mai wannan alhakin."

Yawu ta had'e ba tace komai ba kawai ta wuce madafar, tana zuwa ta fara fad'a mata "07:30 zaki kai mata lipton a d'akinta, 08:00 zaki kai mata ruwa da matsatsun kayan itatuwa a d'akin motsa jiki, k'arfe 09:00 daidai zaki shirya mata petit dΓ©jeuner (karin kumallo) a kan table, da k'arfe..."

Hannu ta d'aga mata tana yatsina fuska tace "Dakata dan Allah, ki samu takarda ki rubata min zan duba daga baya, bana da lokacin wannan shashancin."

Yana fad'a ta barta nan tsaye tana kallonta, kamar yanda ta buk'ata haka ta ruba ta mata komai ta kai mata, daga wannan lokacin ta fara aiki dan matar muguwar yar tamne-tamne ce bata gajiya da had'id'iya, bata awa d'aya bata buk'aci wani abu ba, ko ba komai taji dad'i daya zama ita ce a gidan ba Amna ba, dan da ita ce to tana iya yin zuciya ta bar gidan sai kawai an ganta ta koma Maradi, sai dai Allah ya isar ta bita kam amma ba zata d'auka ba, da wannan yau ta kwanta baccin gajiya saboda bata huta ba ko kad'an sai kai da kawowa, abunka ga gidan gwamnati ga girma daga wani wurin zuwa wani tafiya ce mai tsayi.

*Gaga's house*


*Ko da* aka wayi gari Jibril ya kaiwa Hajia santalelen rak'umi a matsayin yaba kyautar samun Jamila a budurwa, har ya mik'e zai fita boss ya shigo tare da Amna dan ta gaishe da iyayensu, Hajia na ganinshi ta dafe fuskarta da nufin kar ya mata sumbatar nan, yana ganin haka ya zo kusanta ya ruk'umk'umeta ya sumbaci bayan hannunta dan ta rufe fuskarta da hannuwan, yana sakinta ta kalleshi tace "Jarababbe, wai kai ba zaka iya rayuwa ba tare daka shiga harkata bane?"

Daf da ita ya zauna yace "Ko kad'an ai, idan kinga haka sai in babu ke ne a duniya."

Hararenshi tayi tace "Fatan mutuwa kake min?"

Kallonta yayi yace "Kar dai kice min ba kya son mutuwa ke ma?"

Wata hararar ta sake mishi tace "Uwarka ce zata mutu ba ni ba."

Murmushin rainin hankali ya mata yace "Toda uwata ta mutu me zai hana a d'auke Alhajinki? Tunda naga shine tsoho a gidan nan."

Wani uban dundu ta sakar masa a baya tace "Ammar bana son iskanci, ina son shi har yanzu bana so ya barni."

Murmushi kawai yayi ya kalli Jibril yace "Halan kai ka siyo waccen rak'umin?"

Gira kawai ya d'aga mishi alamar eh, kallon Amna yayi ya mik'a mata hannunshi yace "Zo ki gaishe ta mana."

Matsowa tayi ta d'an sunkuya tace "Ina kwana Hajia."

Ba annuri a fuska tace "Lafiya lau." Mik'ewa yayi yace "Kewace irin gaisuwa ce haka? Dallah malama haka zaki mata, rumgumeta zakiyi, ina so kema ki zama mafi soyuwa a zuciyarta kamar yanda tafi so na sama da kowa."

Da k'arfi ya jawo Amna ya tallabo Hajia ya mannesu wuri d'aya yace "To rumgumeta ki sumbaci kumatunta."

πŸ˜‚ *Covid19 inji aunty*

Amna dake jin abun wani iri kasawa tayi, Hajia kuma sai k'ok'arin tureta take kamar kashi tana fad'in "Kai kana da hankali kuwa?"

Bata ankara a sunkuyawar nan da tayi sai kuwa ya sauke mata k'ulli a baya yana fad'in "Ke dan ubanki rumgumeta."

Bata shirya ba sai kuwa ta fad'a kan Hajia da k'arfi tana sakin tarin da bata shirya zuwanshi ba, da sauri ta rumgumeta ta raba jikinta da nata tana dafe bayanta tana kallonshi, yanda duk ta shagwab'e fuska kuma saita kashe shi a wurin, take ya jawota ya rumgume kuma yana shafa mata bayan yace "Yi hak'uri kinji chouchouta (shoushouta), kin yafe min ko."

D'aga kai Amna tayi ta raba jikinta da nashi saboda fitowar iyayensu, kafin su gaisa kuma Marya suka shigo ita da Junaid.

*Alhamdulillah*

*Yawan sharhi yawan rubutu.*
14/10/2020 Γ  00:58 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*BADAK'ALA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ _*AHALI NA*_πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦

_44_


Ko da ta gaishe da kowa ya amsa da sakin fuska amma banda Zeinabu da Hajia, Amar ne suka shigo shima tare da Umaimah, gaisawa akayi sosai inda Hajia ta zaunar dashi kusa da ita tana ta mishi tambayoyi kamar yaro, shi kuma duk a takure yake jin kanshi a kusa da ita, kallon Umaimah tayi tace "Zo."

Kusanta taje ta zauna kanta k'asa, saida ta kalleta ta nuna shi da yatsa tace "Kinga wannan? Shine farin ciki na, kiyi iya k'ok'arinki wajen faranta masa rai, ni kuma na miki alk'awarin duk abinda kika nema a wajena zaki samu, kinji ko?"

Kai kawai ta d'an d'aga alamar to, Alhaji ne ya shigo da sallama da farin ciki a fuskarshi na ganin ahalinshi, nan ma wata gaisuwar ce ta b'arke tsakaninsu kafin ya kalli kowa yace "Masha Allah, tunda kusan duk mun taru muje mu ci abinci tare mana."

Duk da akwai wanda basu buk'atar cin abinci amma basu mishi musu ba sun nufi kan babban teburin, Amar da Hajia ke rik'e da hannunshi yana son ya sub'uce amma ta rik'e, ta bayanshi Ammar ya mazge mishi k'eya yana fad'in "Jiya kaine ka hareri ni ko?"

Dafe kai yayi yana kallonshi, a hassale Hajia tace "Ammar meye haka? Zan ci uwarka fa."

Ganin ko kulata baiyi ba yasa tace "Yaje ya hararekan to mugu mak'etaci."

Duk uwayen kowa ya samu ya zauna sai kuma matasan maza, su Amna kuma su suka zuzzuba abinci, ana fara cin abinci Ammar ya kalli Amna ya mik'e tsaye da farantinshi a hannu ya zagaya har inda take, kama hannunta yayi suka nufi hanyar d'akin Ummy yana fad'in "Aljannata zo muje d'akin Ummy na ciyar dake."

Rufe baki Amar da Jibril sukayi suna dariya, sai Junaid daya bishi da kallo yace "Bak'auye anyi agogo."

Saida ya wani sassako wandonshi yayi k'asa kamar yanda gayun nan keyi kafin su waye yace "Dole mana, mata wasa ce, ita ce mahutata dole na kula da ita."

Jibril zaiyi magana yana dariya Ummy ta kalleshi tace "Dan Allah ku rabu dashi, kada kusa muji abinda kanmu ba zai iya d'auka ba."

Ba tare daya daina tafiyar shak'iyancin nan ba har suka shiga d'akin Ummy su dai suna binsu da kallo, suna kammala cin abincin suka fito, kusa da Amar ya tsaya yace "Yaro tashi muje ka sauke ni, banda mota a hannu."

Kallonshi Ummy tayi kamar tayi magana sai kuma tayi shiru, Hajia ce tace "Halan ka siyar da motar?"

Kallonta yayi yace "To Hajia idan rashin kud'in ne zaisa na siyar da uwar gidata ai ina ga kina da kadarori ajiye, ko sark'ok'in da kike sakawa ma kad'ai sun isheni rayuwa idan na siyar."

Wani kallon sai dai haushi ta masa tace "Dad'inta dai gadar arzik'in nayi tun daga gida, a sanda mahaifina yayi zamaninsa babu wanda bai san shi ba."

Murmushin gefen labb'a ya mata yace "Yanzu? Ai har yanzu mu yana zamaninshi a wurinmu, tunda Alhaji ya fad'a mana duk shine silar arzik'in nan da muke ciki, da taimakon Allah da taimakonshi da yyanzu watak'ila muna can anata fama."

Wani murmushin jin dad'i tayi ance arzik'i daga mahaifinta ya fito tayi, yana kallonta saiya bushe da dariya yana fad'in "Kinsan wani abu Hajiata, Allah sai naga k'aramin bakinki nan na ki zaiyi mugun kyau idan kina yanko lomar tuwon dawa kina shinfid'ata kan miyar daddawa kina jefawa baki."

Wata irin tattausar dariya Alhaji yayi yana kallonta yace "Ai kuwa saima ka gani da idonka, abun sha'awa ne sosai, gata kuma gwanar iya tuk'a tuwo yayi taushi laushi da santsi."

Wannan karan kusan babu wanda baiyi dariyar ba sai Hajia da ranta ya b'ace ta kalli Alhaji, sama da k'asa ta harare shi sannan ta ci gaba da cin abinci ta, Ammar dake dariya har da rik'e ciki ne ya kalli Amar yace "Kai nake jira."

Lieutenant ne ya d'auki makullin motarshi ya jefo mishi yana fad'in "Je da wannan."

Cab'ewa yayi yace "Abba kai fa?" Kallon Amar yayi yace "Shi saiya kaini."

Bai ce komai ba ya zagaya wajen da Hajia ke zaune ba tare data kula ba taji ya sumbaceta a kumci yana fad'in "Uwar gidana saina dawo."

Kusan Husseina yaje ita ma ta samu nata rabon tare da cewa " 'Yar tsakiya kenan mai ban haushi."

Saida yaje har inda take tsaye ita ma ya sumbaci kumcinta yace "Wannan ce amaryata."

Kusan lieutenant ya tsaya ya sunkuya ya mik'o mishi kumatunshi alamar ya sulbace shi, saida ya kalli Ummy da Hajia da sauran mutanen wurin wanda suma duk idonsu akansu suke, yana kallon Zeituna ya fahimci ma'anar kallonta sai kawai ya danna mishi wata k'aramar sumba a kumci, mik'ewa yayi daga sunkuyawar yace "Abba baka ce komai ba."

Kallonshi yayi to shi me zai ce? Saiya tuna da jiya sai kawai yace "A dawo lafiya."

Murmushi yayi sosai yace "Nagode Abba na, kai bai ma ka dawo lafiya."

Zeituna ya kalla yace "Uwata saina dawo."

Da murmushi a fuskarta tace "A dawo lafiya, Allah ya bada abinda aka je nema."

Murmushi ya mata yace "Nagode."

Ummy ya kalla, ido cikin ido, kallo mai ma'anoni da dama mai wuyar fassara, ba tare daya daina kallonta ba ya wuce yana dank'ara gilashinshi a fuska wanda ya fito mishi da manyan fararen idonshi. Haka kawai ta samu kanta cikin yanayin rashin jin dad'i, ta kasa d'auke ido daga gare shi har ya fita, kowa ya ma magana banda ita, har gaisawa da akayi tun a falo bakinshi bai had'u da nata ba, tana kallo sai wata ya kira da sunan uwa ba ita ba, sai taji kamar tayi ihu ko wani ya tambayeta lafiya har ta fad'a mishi abinda ke ranta, a hankali ta dawo da kallonta kan farantin abincinta, amma sai taji ya fita a ranta sai kawai ta mik'e zata bar wajen, idonta ne suka sauka kan Zeituna da ita ma a lokacin ta kalleta ganin ta tashi, had'e mata fuska tayi tare da jan dogon tsaki wanda bata san ma ya fito fili ba ta bar wajen.

Da kallo kawai aka bita inda lieutenant ke tunanin larurar ciki ce kawai, Hajia kuma take ganin kishi ne ba komai ba, haka suka gama cin abincin sai dai babu wani nishad'i tunda Ammar ya tafi bare ayi raha, haka kowa ya tashi ya kama gabanshi sai kuma randa ta juyo aka sake irin wannan zaman, dan abune mai wuya ka gansu zaune hakanen wuri d'aya dukansu.

Ko da yaje ya samu Jano a can, insp. ya basu hak'uri yace su ba juna hak'uri kuma a kiyaye gaba, rumi-rumi suka fito daga ciki kowa ya shiga motarshi, saida Ammar ya kira wani matashin saurayi dan ya zo ya
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment