Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

kuma gilashin idonsu fari mai kyau, a ciki ba zata iya cewa ga boss ba dan bata gama fahimtar Ammar ne ya saki fuskarshi ko kuma Amar ne ya had'e rai kamar boss, cikin takonsu na zataran maza majiya k'arfi suka k'araso kusan kawunsu, mik'ewa yayi tsaye suka rumgume juna da su cikin farin ciki da k'aunar juna, saida suka raba jikinsu Gambo ya kallesu da kyau yace "Yaran nan raina min hankali zakuyi ko? To a ciki ina Ammar?"

Wani ikon Allah sai kawai Amar ya d'an saci kallon Hamna lokaci d'aya kuma ya d'auke kanshi, ai kuwa Hamna sai cewa tayi "Abba ga boss nan." Ta fad'a har da nuna shi da yatsa.

Tare suka kalleta amma tana had'a ido da Ammar d'in sai taji gabanta ya fad'i da k'arfi, Gambo ne yace "Waya saka dake?"

Turo baki tayi shi kuma ya sake kallonsu sai Ammar daya matso kusanshi yace "Tonton."

Murmushi yayi yace "D'an soja ya aikin na ka?"

Cikin gimtse hak'ora ya amsa da "Pa mal (ba wuya) tonton."

Kafin yace wani abu ya sake cewa "Tonton je dois mon aller (ina so zan tafi), j'ai une visite dan quelque minute ( ina da wanda zan gani nan da 'yan mintuna)."

Kafad'ar shi ya dafa a lokacin Amar yace "Amma dai tonton zamu sameka gida ko?"

Kallonshi yayi yace "Pourquoi tu demande Γ§a (me ya sa ka tambaya)?"

Kallonshi shima yayi yace "Parce que hier j'ai reçu une carte d'invitation en fecebook dans mon counte (saboda jiya na samu wani katin gayyata a fecebook a ma'ajiyata), ce pour cela je demande (shiyasa na tambaya)."

Kallonshi kawai gwamna yayi dan ba zai iya cewa ba haka bane, sai Ammar daya kalli Imminsu wacce ke cikin shirinta yace "Ummi yau ba zaki fita asibitin bane?"

A tak'aice ta amsa da "Ina bayanka."

Kallon gwamna yayi yace "Tonton sai mun dawo."

"Ok yarana, Dieux vous bΓ©nisse (Allah ya muku albarka)."

Saida suka sunkuya suka gaishe da Alhaji da Hajia wacce ta hakimce kai kace wata matar gwamna ce, ta tsufa amma bata jin ta tsufa saboda ta tilasta yara suna yin aikin da take so, kowa ya ji k'ara (alerte) a counte d'in shi ita ma sai taji, ko sutura da take sawa kawai ya ishi gidan wasu cefanai na tsawon wata d'aya, saboda k'arfin hali waya ma cewa tayi sai babba take so wanda ake shafawa da hannu, shiyasa in ka kalleta kallon garaje ba zaka fahimci tsufanta ba, yanda Ammar ya gaisheta ne yasa ta yamutsa fuska ta kalleshi tace "Da ka rik'e gaisuwar taka ai, idan baka sunkuya ka gaisheni ba to ubanka har k'asa zan sashi ya duk'a ya gaishe ni, kuma bai zama lalle na amsa ba, imbΓ©cile kawai."

πŸ˜‚ *(Romo kenan)*

Ammar kuma da dama shi dai yake jin haushin hana shi abinda yake so da tayi shiyasa basa shiri, juyawa yayi zai wuce ya kalli Ummi data mik'e ita ma, daf da ita ya matso zai wuce ya fita murya k'asa k'asa tace "Ban yafe maka ba in har baka gasheta da kyau ba."

Cak ya tsaya tare da cije leb'e da k'arfi, shi dai ya rasa wace irin rayuwa ce wannan, komai k'ank'antar abu sai Ummi tace ban yafe ba, k'wafa yayi cikin zuciyarshi ya sake juyowa yaje gabanta, zai sunkuya ta d'aga mi shi hannu tace "Wallahi ka durk'usa saina tsinkeka da mari a wurin nan, ni zaka rainawa hankali, in tsuguna in haifi ubanka amma kana jin haushin gaisuwar fatar bakin da zaka min wai har sai uwarka ta saka ka, kenan albarkacinta na ci? To bana so ka rik'e tsiyarka, amma ka tambayi ita kanta uwar taka, ta shigo gidan nan ne saboda ni na zab'i ta shigo, sannan tana zaune a gidan nan ne har yanzu saboda ina so, kuran waya d'aya tak ya isa ya jefa uwarka a layin zawarci."

Ammar dake tsaye zuciyarshi sai bugawa take, hannunshi na dama sai rawa yake yana ji kamar ya kai mata haura guda, k'ara damtse leb'en shi yayi sosai ya kalleta da jajayen idonshi, a hankali ya d'auke idonshi ya kalli gefenta sai kawai Ummi, k'wayar idonta ya kalla ya ga sun cika taf da hawaye, da ido ta mishi alamar "Hankalinka ya kwanta yanzu?"

D'auke idonshi yayi yana ji kamar ya k'urma ihu, tafin hannunshi yasa ya dafe goshinshi yana d'an murza idonshi da yatsunshi ta k'asan gilashin shi, saida ya sauke ajiyar zuciya har sau uku kafin ya sake kallon Hajia, zai kuma durk'usawa dan bata hak'uri cikin tsiwa tace "Na fad'a maka wallahi saina mareka idan ka durk'usa gabana."

D'ago kai yayi daga shirin sunkuyawar ya sauke a kanta, a ranshi yace "Wai ni ya zanyi da tsohuwar nan ne?"

Ummi ya kalla danya nuna mata shifa ba zai zauna anan ya b'ata lokacin shi ba, sai yaga har yanzu wannan kallon ne take masa, ya kuma sani ita ma yanzu in suka je asibiti abinda zata mishi kenan, wani k'aramin tsaki yaja wanda bai ma san ya fito fili ba, muryar Alhaji ta dawo dashi yana fad'in "...


*Tsaka mai wuya Ammar (ka sunkuya Hajia ta mareka, ka k'i sunkuyawa Ummi tace bata yafe ba).*

_Ku bashi shawara_πŸ˜‚
18/05/2020 Γ  13:48 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*BADAK'ALA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ _*AHALI NA*_πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦


_Bismillahir rahamanir rahim_

_3_


Alhaji ne yace "Kai Ammaru, wuce dan Allah ku tafi wajen aikinku kaji, sai kun dawo."

Da sauri Hajia ta kalleshi wato ita zai rainawa wayo, Ammar na jin haka ya juya cikin takon k'arfi ya fice daga falon, cikin sanyin jiki Ummi tace "Umma sai mun dawo, Abba mun tafi."

Amma sai dalla mata harara da tayi Alhaji kad'ai ya amsa da "A dawo lafiya Sa'ada."

Wucewa tayi tasa gyalenta tana share yar k'wallar data tarar mata a ido, Amar ma bayanta ya bi ya dafa kafad'ar ta yana rarrashin uwatai, sai Junaid da shima ya musu sallama ya wuce, Jibril ma cewa yayi ya tafi sai Alhaji ne yace "To *B A* (sunan projet da yake aiki kenan, kasancewarshi d'aya daga cikin jigajigen ma'aikatar duk da k'arancin shekarunshi yasa Alhaji dama wasu daga mutanen gari ke kiranshi da haka) yau kuma wani garin zaku kaiwa girgiza?"

Dariya yayi yace "Alhajin Allah kenan, yau tafiyar ba mai nisa bace, wani k'auye ne nan kusa nake so na shiga da kaina tare da sabbin ma'aikatan da muka d'auka, kasan sai ana nuna musu yanda aikin yake kafin su zama yan gari, amma komai dare zan dawo insha Allahu."

"To Allah ya bada sa'a, Allah ya tsare." Cewar Alhaji, da murmushi ya amsa da "Ameen."

Hajia ya kalla yace "Hajia ni na tafi saina dawo."

Dayake shi ba daga tsatsonta yake ba sai kawai ta d'auke kai kamar bata ganshi ba, shi kuma ko a jikinshi dan in da sabo ya saba, wajen kakarshi ya nufa Husseina yace "Yar tsohuwa na tafi saina dawo."

Da murmushi ta amsa da "A dawo lafiya d'an tsoho, Allah ya kiyaye."

Umaima kyakyawar budurwa yar boko mai wayewa wacce ke koyon aiki (stage) a bankin da Amar ke aiki wanda shi dama *DG* (directeur gΓ©nΓ©ral) ne a ma'aikatar, kasancewar gidan duk boko ne yasa ta samu hanya cikin sauk'i a ma'aikatar dan da kanta ta zab'i inda take so, kuma dama mata su kam Hajia tana basu damar yin abinda suke so, maza dai ne take son suyi wanda take so saboda tana son cimma wani burinta a game da hakan, ita ke biwa Junaid sai Jamila dake bi mata, duk da shekarunta har yanzu babu maganar aure a tsarinta, kuma dayake shi aure lokaci ne sai Hajia bata damu da lamarinta ba bare tace zata had'a ta da wani ko a cikin mazan gidan, doguwar rigar ce jikinta data kamata kuma ta fito da jikinta sosai, sai gyalen data d'ora da jaka a hannu kalar takalminta, ita ma gaishesu tayi ta kalli Amar dake rarrashin Ummi tace "Yah Amar ka jira ni mu tafi tare, mota ta na wajen gyara har yanzu."

Juyowa yayi da kai ya mata alamar ta taho, da irin haka gidan yayi shiru ya rage sai iyayen, yara dama ana had'a musu abin kari ne su tafi dashi, in kaga sun zauna cin abincin kari to su suka zab'i abinda za'a dafa musu da safe, manya kuma dama babu wanda ya damu da abincin gidan, ba wai na safe ba har na dare ba wani sai yayi sati bai jefa abincin gidan cikin bakinshi ba, kuma hakan baya rasa nasaba da yawon gidan da kuma kowa na da 'yan canji a aljihunshi.

Yanzu haka masu aiki ne su biyu gogaggu a fannin girki da kuma kula da tsabta wanda Hajia ta yarda dasu rik'a girka mata abinda zata ci ke ta kai kawo a madafa, d'aya budurwa ce sai babbar wacce bazawara ce, kafin ma ta yarda su fara aikin saida sukayi aiki a gidan na sati guda ta gamsu da abincinsu da kuma tsabtarsu kad'ai, sai guda biyu suma d'aya budurwa yar shekara *goma sha tara* da kuma dattijuwa su kuma aikinsu shara da goge goge, yanzu haka ma sune ke goge wajen cin abincin, sai Soueba da Zeinabou da su basu aiki ke jera kwanukan abincin, duk da ba su ke girkin ba amma suna taimakawa masu aikin, wani lokaci kuma suna girkawa da kansu, abin karyawa ana dafawa ne kawai, amma na rana dana dare sai wanda Hajia tace tana so, saida suka gama shiryawa Soueba ta zo cikin fargaba tace "Hajia an gama shirya wajen cin abincin."

Wani kallo ta mata kamar kashi kafin tace "Ina zuwa to."

Dukansu ne suka mik'e suka nufi wajen cin abincin, sai *Alhaji Labaran* mahaifin Jibril dayake shi d'an kasuwa ne yasa bai da k'ayadadden lokacin fita, gyara rigarshi yayi ya kalli Alhaji yace "Ni zan fita Alhaji, sai mun dawo kuma."

"To Allah ya tsare, Allah ya bada abinda aka je nema."

Amsawa yayi da "Ameen." Kallon Hajia yayi wacce tuni ta isa kan teburin Zeinabou da Soueba sun sakata tsaka suna zuba mata abinda ta zab'a, mahaifiyarshi ya juya yawa sallama haka ma Gambo da yake kallon agogon hannunshi saboda gudun wucewar lokaci, Soueba na ganin zai fita tayi saurin aje kwanon miyar zata nufi wajenshi, cikin akasi miyar ta d'an fallatso ga hannun Hajia, sai kuwa ta daka mata wata tsawa "Ke!"

Cikin tsoro ta tsaya tare da kallon Hajiar, d'orawa tayi da "Ke mahaukaciyar ina ce? Me kike kallo da zaki k'ona ni da miya? Ko jarabar ce ta motsa ta miji? Ina ce ai fita ne zaiyi ko, meye kuma na hanzarin biyarshi a baya?"

Cikin rawar murya tace "Yi hakuri Mama, ban..."

"Ba kiyi me ba? Dallah b'ace min da gani."

Labaran da yake jin duk abinda ke faruwa ko juyowa baiyi ba harya fita, Soueba kuma hanyar madafar ta nufa cikin sanyin jiki, tana daf da shiga taji tace "Ki turo min *Zeituna*."

Juyowa tayi da ladabi tace "To Mama."

Saida ta shige Alhaji ya kalleta kamar ya kifeta da mari, baya jin dad'in abinda take a gidan, yana son taka mata birki in tana irin wannan ikon nata, amma idan ya kalli yanda gidan suke girmamata da ganin darajarta mutumcinta ne zai zube yau da gobe idan yace duk sanda tayi ba daidai ba saiya tsawatar mata gaban mutane, dan wata rana iya shegen nata har gaban yara yi take, shiyasa yake bari sai sun keb'e wani lokacin yake mata magana, Husseina dai kallonta kawai take sai Gambo da shi dai yake fatan ma lokacin tafiyarshi ya kusa yayi abinda ya kawoshi ya bar garin kafin ta bijiro da wani abinda take so tace kuma dole yayi, suna haka Zeituna ta fito ta nufo wajen Hajiar, kallo d'aya zakawa budurwar kasan kyakyawa ce wacce Allah ya hore ma albarkatun jiki, amma talauci da rashin gyara yasa datti ya samu gurin zama a jikinta, tana kusa da k'arasowa Hajia ta d'aga mata hannu da fad'in "Dakata malama, koma kawai ma na fasa aiken na ki, jiki duk datti haka."

Juyawa Zeituna tayi zata koma taji tace "Wai ke yaushe rabonki da wanka ma?"

Pik'i-pik'i Zeituna tayi da ido tana kallonta hakan yasa tace "Anya ma kina wankan? Mtsss! Shiga ciki."

Shiga tayi baiwar Allah sai kawai ta fashe da kuka, sai abokiyar aikin nata wacce ita dattijuwa ce da suke kira da *Iya* ta bata hak'uri tace ya kamata ace ta saba da irin haka, Zeituna kuma ciwonta d'aya shine wata jarabawa da Allah ya jarabeta da ita, babar jarabawa ce gareta kam, dan ace ubangiji ya jarabeka da son wanda bai ma son kanayi ba babbar jarabawa ce, gashi ita ba kowa ba kuma ba 'yar kowa ba, sannan matar da zata iya sakata ta shigo gidan ta tsaneta, ita kam dole tayi kuka, gashi tun bata san meye so ba take jin mutumin na birgeta duk wani motsinshi, har ta girma ta fahimci ta kamu da son mutumin da a haife ya haifeta, halayyarshi daban take ko cikin su uku d'in, duk da shine babban amma yafi sauran raha da barkwanci, tun tana tunanin birgeta ne yake har ta yarda *so* ne kawai, *son* wanda ba ma iya kallonta idonta bare ya fahimci ciwonta, *son* wanda yake da mata goggiyar 'yar boko, *son* mutumin daya sha boko ya k'oshi kuma yake da ilimi har na addini ma, *son* mutumin da ko zaratan 'ya'yanshi sun fi k'arfin ta bare kuma shi da kanshi, Iya nata rarrashi ita kuma tana wani tunanin daban, d'aga kanta tayi sama tana zubar da wasu hawayen ta furta a zuciyarta "Allah kai ka jarabeni da wannan ciwon, Allah ka kawo min maganinshi idan har ba ciwon da zaiyi ajalina bane, idan kuma wannan jarabawar ita ce silar ajalina, to Allah na rok'e ka ko sau d'aya ne ka had'a ido na dana *Abbansu Amar* ya fahimci son da nake masa, idan haka ta faru burina ya cika, ko a lokacin wa'adi na ya cika banda takaici ban kuma mutu da buri ba."

Ba dan kar tayi sab'o ba da sai tace meyasa aka jarabceta da wannan k'addara, dan a ganinta bata cancanceta ba ko kad'an, amma kuma idan ta tuna da al'amarin ubangiji, yana da iko da k'arfin da zai juya daidai izuwa ba daidai ba, ya kuma juya ba daidai ba izuwa daidai, dan haka sai tayi shiru tana tunanin ko da Allah yasa soyayyarta batayi nasara ba, to tabbas ta koyi abu guda a wannan karatun, abun kuwa shine ta san ya *so* yake, ta kuma san zafin da ake ji da rad'ad'i lokacin da ka rasa wanda kake so, da wannan ta share hawayenta suka ci gaba da aiyukansu.

*So*
_(Mugun dafi)_

Zeinabou na tsaye ta rasa yanda zatayi, duk da suna zaunawa su ci abinci tare da su amma a takure suke, dan duk wanda ta kalla sai kiga tana yamutsa fuska kamar tana kallon amai, abunda ya faru kuma yanzu yasa ta rasa me zatayi, tana cikin wutsil wutsil da ido Hajia tace "Malama lafiyar tsaya mana a kai? Ki zauna mana."

Da sauri ta koma kusan Husseina ta ja kujera ta zauna, ita bata ma buk'atar cin abincin amma dan kar tayi wani laifin yasa ta zauna, Gambo na ganin k'arfe tara da arba'in da biyar ya kallesu yace "Ina ganin ni zan tafi, dan nan da minti sha-biyar za'a fara taron."

Cike da dattako Alhaji yace "To ba damuwa, Allah ya taimaka, Allah ya maku jagora a cikin al'amuranku, Allah ya kiyaye ya kau da idon mak'iya a kanku."

Shima cike da jin dad'i ya amsa da "Ameen ya Allah Abba, mun gode Allah ya saka da alkairi, Allah ya k'ara lafiya da girma."

Husseina ma addu'ar tabi shi da ita har ya mik'e tsaye, har lokacin kuma Hajia Zeeya ko kallonshi ba tayi ba, saida ya sunkuya yace "Hajia ni zan wuce, sai kuma na sake dawowa, idan da wani abu da kuke buk'ata sai ku fad'a min."

A hankali ta kalleshi tare da nuna mishi wayar dake gefe akan teburin cin abincin tace "Wayar nan ta min tsufa, ina buk'atar sabuwa, kayan d'akina ma na buk'atar a canza su."

Burinshi d'aya shi dai ya samu ya kubce ya tafi karta d'ora mishi abinda ba zai iya ba, dan haka jiki na rawa yace "Hajia wannan ai ba matsala bane, yanzu za'a canza komai kamar yanda kuke buk'ata."

Alhaji ya kalla yace "Abba ku fa ko da wani abunda kuke so?"

Murmushi yayi yace "Babu komai Harouna, Allah yayi albarka, Allah yasa ku gama da duniya lafiya."

"Ameen Abba." Ya fad'a yana kallon Husseina yace "Hajia ku fa ko da abunda kuke so?"

Ita ma kai ta girgiza tace "Ba komai wallahi Gambo, Allah ya tsare mana ku."

Da ameen ya sake amsawa, da haka ya musu sallama ya fito, yana fitowa farfajiyar gidan ya samu masu tsaron lafiyarsa su biyu sai kuma dreba, mota uku ce saita tsakiya wacce yake ciki, dreban dake d'an garin ne ya had'a da neman sak'on Hajia, cikin masu tsaronshi kuma ya tuk'a motar suka nufi wurin taron.

Abunka ga idan kud'i sun kwanta a wuri, sai gashi kayan d'aki da babbar waya sun hallara a gidan ahalin Gaga cikin awa d'aya zuwa biyu, kaya ne na gani na fad'a a ledarsu, aifa nan da nan da dreban da mai gadi tare da su Zeituna da Iya da sauran ma'aikatan aka fito da waccen kayan aka zuba sabbi, Hajia na zaune tana danna sabuwar wayarta, *takaici na d'aya ba'a fad'a min me take yawon dannawa a waya ba*, su Zeinabu da suka tsaya kan gyaran ne suka fito suka tambayeta yanda za ayi da tsofaffin kayan, cikin jiji da kai da isa da tak'ama Hajia tace "Ku har yanzu baku fahimci matsayina bane? Na gama da wannan kayan kuma, su ma waccen idan na shiga naga basu min ba zan kira shi ne kuma a sake min su."

Husseina dake zaune ita ma a falon ce tace "Ai ba wani abu ba suka ce Hajia Zeeya, suna tambayar yanda za ayi da su ne, idan kika ce su zuba shara sufa cika aikinki ne kawai na su."

Juyowa tayi kamar mai ciwon wuya ta kalleta tace "Na d'auka da su nake magana ko? Meye naki na saka min baki kuma? A gidana nake dole nayi iko da komai dake cikin gidan."

Tab'e baki kawai Husseina tayi ta kawar da kanta, kallonsu tayi tace "Kuje duk yanda kuka yi wannan matsalarku ce, idan akwai mai buk'ata ma a cikinku zata iya sakawa a nata d'akin."

Haka suka wuce da tunanin yanda zasuyi dasu, sai dai sun ci alhwashin ba zasu tab'a d'aukar ko da tsinke ne su bawa ko da wani na kusa da su bare su saka a d'akin su, dan wata rana saita goranta musu, dan haka a cikin d'akunan yara aka zuba wasu, wanda basu samu wuri ba kuma aka kai su ma'ajiyar kaya.

*Wasu awanni baya*

Ammar na shiga mota ya tayar ya tsaya bakin k'ofa yana jiran mai gadi ya bud'e masa, Amar ne ya fito tare da Ummi sai Umaima a bayansu, wani matashi ne cikin kayan soja ya matso kusan Umaimai, makulli ta bashi tace "Zan tafi tare da yah Amar, kai kaje ka dubo motar idan an gama gyaran saika d'auko." Tana fad'a ta wuce shi kuma ya bi bayanta ya fita, aikinsa kenan dama tuk'a iyalin colonel Hussein, Ummi na ganin motar Ammar tayi saurin k'arasawa ta bud'e ta zauna, da wutsiyar ido kawai ya kalleta dan yasan ta shigo ne dan ta fad'i abinda ke ranta, mai gadi na gama bud'e masa ya danna hancin motar waje ya harbata zuwa titi, ana d'aukar hanya Ummi ta kalleshi tace "Ammar hankalinka ya kwanta yanzu da aka ci mutumci na? Ka ji dad'i yanzu? To ka zuba ruwa k'asa ka sha dan farin ciki."

Shiru yayi kamar ba dashi take ba, hakan yasa ta ci gaba da cewa "Ammar ku uku na haifa a duniyar nan, amma hatta k'aramin k'aninku da kuka bashi shekaru sha takwas ya fika sanin takamata, Ammar so kake sai bak'in cikinka ya kashe ni sannan ka huta? Gaba d'aya a cikin iyali ka zama wani baud'add'e ba'a gane gabanka, burinka kullum kasa Hajia ta min rashin mutumci akan laifin da ka aikata."

Jingina tayi akan kujera ta ci gaba da cewa "Ka ci gaba dayi, kaga ranar daka tunzurata tasa mahaifinka ya sakeni sai kasa ya auro maka wata uwar, ko kuma idan na had'iye zuciya na mutu shikenan ai saiku huta."

Kallonta yayi lokaci d'aya kuma ya d'auke kan shi ya mayar kan tuk'i, kallonshi ita ma tayi cikin jin zafi saboda yayi kamar ba dashi take ba, haushi ne yasa ta kai hannu da nufin kashe shi da mari ta bayan hannu, shi kuma dama yana kallonta ta wutsiyar ido dan haka yayi saurin gocewa, kallonta yayi yace "Ummi wai meye haka dan Allah, matar nan ya kamata ace ta daina damunku fa, haba."

Da mamaki ta kalleshi tace "Ba zaka canza ba Ammar, idan kuma har akwai ranar bansan ko zan ganta ba."

Ba tare daya kalleta ba yace "Duk da kun barni na tafi aikin da raina yake so da ku da ganina ma sai kun fara addu'a, idan kuma na mutu wajen daga to fa kune zakuyi kukan mutuwa ta."

Da haka suka isa asibiti, suna zuwa Ummi ce baya shi kuma gaba, takaici ne ya rufeta ganin daga ma'aikata masu gadi da shara har zuwa malaman asibitin babu wanda ya kalla bare ya mishi magana, girgiza kai tayi a ranta tana fad'in "Da ace ba kama da mahaifinka kake ba, to ko ni kaina dana fara kokonto anya ni na haifeka."

Faran faran ta gaisa da kowa ita ma ta shiga ciki, yau ma dai kamar kullum majinyata ya fara dubawa, duk wanda ke buk'atar wani agaji na gaggawa kuma saiya rubuta abinda yake buk'ata a kaiwa secrétaire ita kuma ta had'a ka da likitan da zai duba ka, daga cikin wanda Ammar ke bayar da umarni su duba majinyatan har da mahaifiyarshi wacce a gida ita ke iko, a asibiti kuma dole sai abinda yace domin kuwa shi docteur ne ita kuma infirmière ce, dan Ammar saida ya kwashe shekara sha hud'u a *France* yana karantar *Cardiologue* kafin ya zama cikakken likitan zuciya, duk da Sa'ada ita ta so zama *doctorat* amma daya zama sai ta tsallake k'asarta taje wata k'asar yin karatu na shekara takwas sai kawai Hajia tace sam ba da ita ba, idan kuma suka ce zasuyi to ba da yawunta ba, dole ta hak'ura sai shi Ammar ya tafi, da wannan diplôme d'in ne suka samu damar bud'a asibiti ta su ta kansu.

➑️➑️➑️➑️➑️➑️➑️

Misalin *10:00* gwamna Gambo ya sauka babban birnin niamey, nan ma motoci ne suka iso d'aukar shi harda motar sojawa dan tsaron lafiyarsa, tun a hanya ya kira Amar ya fad'a mishi a cire kud'i a counte d'in shi ya bawa su Hamna saboda kusan wata uku bai musu aike ba, kuma gashi yanzu suna ecole ya taho, Amar da a lokacin ke tsaye gaban teburin Umaima yana d'an nuna mata wani abu daya shige mata duhu ya amsa da to, ba b'ata lokaci Hamna da Amna dake cikin aji sak'o ya shigo wayoyinsu na an turo musu da kud'i zasu iya zuwa su cira, farin ciki wurin Hamna ba magana dan dama bikin k'awar ta ake daf da farawa nan da kwana uku, har yanzu ko anko bata siya ba kuma bata damu ba dan tasan zata siya.

➑️➑️➑️➑️➑️➑️➑️

Misalin *12:20* dreba ya d'auko yara da daga ecole, zuwansu yayi daidai da zuwan Ammar dan sha biyu yake saukowa, wani lokaci kuma ya kan koma k'arfe hud'u ya ga wasu, wani likaci kuma
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment