Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

cikin neman lambar Iklima yace "Ai ko bai ci ba kai kasan zaiyi b'anna."

Danna ok yayi ya d'ora a kunne, ba jimawa sosai ta d'auka suka gaisa kamar yanda suka saba, tambayarta yayi sunan unguwar tace gaskiya bata sani ba, amma ya bari ta kira Mari ta tambayeta, har zai kashe wayar tayi saurin cewa "Dakata."

D'orawa tayi da "Da jima wata rana mun tab'a had'uwa da wani mutum a kasuwa babba, sun gaisa dashi sosai har take tambayarshi ya mamanta take, sai naji yace mata jikinta da sauk'i sosai, tabbas koma meye sunan unguwarsu babu nisa tsakaninsu da gidan bus d'in *Sonef*, dan tace min a unguwarsu yake aiki a gidan bus d'in."

Godiya ya mata sosai kafin suyi sallama ya fad'awa yan uwan nashi yanda sukayi, shiru motar ta d'auka kowa da waya yana aikin latsawa, inda Jibril ya shiga tunanin inda zaiga yarinyar nan, gashi ko wani ba zai iya tambaya ita ba tunda babu wanda ya ganshi tare da ita, gashi tun jiya da akayi maganar garinsu yaji ya k'agu ya zo garin, yana matuk'ar son ganinta da idonshi, tayi aure? Ko kuma dai ta kasa samun jarumin namijin da zai iya zama da ita? Ko kuma dai... rasa ma abun tunanin yayi sai kawai yayi d'an k'aramin tsaki ya ci gaba da latsa wayarshi, haka suka dinga rarakar hanya ba ji ba gani ba tsayawa komai, dama bus ce idan ta zo *zinder* take tsayawa, amma su basu da dalilin tsayawa dan haka sukayi tazarce, daga zinder zuwa nan sai gasu a awa d'aya wanda yayi daidai da agogonsu k'arfe *11:20*, hakan na nufin sun ci awa hud'u a hanya, Jibril ne ya nuna musu inda gidan motar yake a sanin daya ma wurin, cikin sa'a suka iso sai Junaid dake tambayar gidan malam Muhammad wanda ya rasu shekara bakwai zuwa shida da suka wuce, mutum na farko ne yace bai sani ba, amma mace ta biyu koda ya tambaya tace "Eh na sani, ko ba Baban Maryama ba wacce tayi ciki? Ai yanzu basa waccen gidan mamanta na tare da kakarta ne."

Daga cikin mota Ammar yace "Eh ita, ni ne nai mata cikin, na zo karb'an abinda ta haifa ne, ko zaki nuna mana gidan."

๐Ÿ™„ K'uri ta masa da ido tana kallo, wannan wane marar kunya ne? Ganin kallon ya k'i k'arewa yasa shi bud'e murfin mota ya fito tare da d'ora duka gwiwoyin hannayeshi saman motar yace "Ya dai? Ko na tsaya da kyau ne ta yanda zaki ga ko na isa nayi wa mace ciki? Dube ni fa."

Ya fad'a yana zagayowa inda suke tsaye tare da Junaid dake ta dariya, _(yan uwa haka fa jarumin yake, yana da sako zance ta yanda dangi ke ganinshi kamar faranci ne ke damunshi na d'an fari ko kuma rashin wayo, ni kuma nace a'a, haka wasu mutanen suke da sako zance ko wane iri ne)_, da sauri matar nan ta matsa tace "Da kun shiga kwanar nan kuka tambaya za'a nuna muku."

Da sauri ta wuce ta bar wurin tana mamakin kalaman mutumin, tana gusawa kuma ta fara fad'a ai wanda yayi wa Maryama ciki ne ya zo amsar 'yarshi, a k'aramin gari kuma da baya da maraba da k'auye sai gashi mata wasu har fitowa suke suna lek'e.

Suna shiga kwanar suka tambaya aka nuna musu, yaron daya nuna musu suka ce ya shiga ciki ya fad'a anyi bak'i, jim kad'an yaron ya fito tare da wata tsohuwa a bayanshi, masha Allah ta tsufa sai dai k'aramin jiki dake gareta amma doguwa ce sosai, Junaid dake kallonta ji yake kamar Mari yake kallo dan akwai kama a fuskarsu, d'aya bayan d'aya ta kallesu tana k'ara yafa gyalenta a kafad'a tana rufe rigarta munafata, cikin dattako tace "Ina kwananku yan samari."

Junaid har k'asa ya duk'a yana fad'in "Ina kwana Hajia."

Su Amar kuma daga tsaye suka gaisheta da girmamawa, amsawa tayi kafin ta kalli Ammar da hankalinshi ke kan waya tace "Gashi kuma ban shaida ku ba yara, daga ina haka? Naga kamar ba 'yan garin nan ba."

Junaid ne ya d'an kalli Amar hakan yasa Amar cewa "Hakane Hajia, ba garin nan muke ba, yanzu haka daga maradi muke, mun zo wajenku ne da muhimmiyar magana."

Da mamaki a fuskarta tace "To! To ba damuwa, Allah yasa alkairi ke tafe da ku."

Junaid ne yayi murmushi yace "Insha Allahu alkairi ne."

"Shikenan, ina zuwa ko." Ta fad'a tana juyawa ciki jiki a sanyaye, mamakinta me zai kawo zaratan samari haka har su hud'u gidan nan, iya tunaninta ta kasa gane me suka zo nema ko yi a wajensu, da haka ta samu d'iyar Baba zaune kan kujerar k'arfe tana tsiga musu yakuwa da zasuyi miyar taushe da ita wacce tun ranar data yanki jiki ta fad'i har yanzu tafiyarta sai jan k'afa d'aya take, maganarta ma ba duka kake fahimta ba, tsaye tayi gabanta cikin harshen barbarci tace " Bak'i ne a wajen suka zo nan, sunce daga maradi suke, ni dai bana da kowa a can, dama daga Diffa suka ce, sai dai ko wajenki suka zo yan uwan mijinki ne, amma kuma basuyi kama da dangin Muhammad ba, dan gaskiya dukansu kyakyawa da su, wasu ma biyu a ciki kamar buzaye dan gashin kansu ma a murd'e yake, ko shakka babu kuma wannan 'yan biyu ne, amma dai bari na shigo dasu sai muji meke tafe dasu ko?"

Saida ta gyad'a kai tare da d'aga harshenta sama ya manne a hak'oran ta na sama kamar yanda maganarta take yanzun tace "Tttoh."

D'aki ta shiga ta fito da tabarma babba ta shinfid'a a bakin bishiyar magwaron dake akwai wanda baya 'ya'ya, lek'awa tayi cikin dattako tace "Bismillah ku shigo."

Shigowa sukayi suna doka uwar sallama, d'iyar baba ce ta amsa tana kallonsu ita ma d'aya bayan d'aya, izinin zama ta musu suka cire takalmi suka zauna, kaka ce ta wuce ta d'auko k'atuwar mazubin (tarmus) ruwa masu sanyi ta kawo musu, su uku ne suka sha amma Ammar yatsina fuska yayi alamar bai sha, kujera yar tsugunno kaka ta d'auko ta zauna kusa da d'iyar baba ta kallesu a tsanake tace "Yaran nan ina jinku, har yanzu na kasa tsayar da hankali na wuri d'aya saboda tunanin abinda kuke tafe da shi."

Kallon kallo suka shiga da tunanin waye zaiyi magana, Amar ne ya fara nuna kanshi yace "Hajia ni sunana Amar, wannan dukansu 'yan uwa na ne, wannan d'an biyu na ne sunanshi Ammar, wannan kuma Jibril, sai wannan Junaid, dukanmu gida d'aya muke, kuma muna zaune ne tare da iyayenmu dukansu, 'yan uwane mu da muke k'aunar junanmu, sannan muna yin komai na mu tare, wannan yasa ma yanzu muka rako d'an uwan mu ya zo gabatar muku da kanshi a matsayinshi na mai son 'yarku."

Kallon juna kaka da d'iyar baba sukayi kafin su sake kallesu, d'iyar baba ce cikin salon maganarta tace " 'Yyar mu kuuuma? Wace 'yaa?"

Junaid ne ya kalleta da murmushi a fuskarshi yace "Maryama."

Yana fad'in Maryama saiji sukayi tace "Ashhh." Suna dubanta suka ga ashe wuk'ar da take yankan yakuwa da ita ce ta yanketa, kaka ce ta karb'e wuk'ar da kwanon tace "Shiyasa tun farko nace ki bari zan gyara da kaina."

Cikin yanayin hushi ta kalli Junaid tace "Dama wannan maganar ce ta kawo ku? Maganar Maryama kuka zo yi mana? To kunga ni da idonku anbaton sunanta kad'ai abinda ya jawo, idan kuka k'ara anbaton sunanta nan gaba tafasashin ruwan can zata zubawa kanta."

Ta fad'a tana nuna musu tukunyar dake kan wuta gaban d'iyar baba, cikin b'acin rai ta fara yanka yakuwar tana fad'in "Kalleta ka gani, tana zaune akan kujera ne dalilin wannan yarinyar, ita ta mayar min da 'ya haka, ta riga data fad'a ai babu ita babu Mari, nima kuma haka ban san wata Mari a rayuwata ba."

Ammar da kai ka rantse kace baisan tsiyar da suke ba ne ya aje wayarshi gabanshi ya kalli kaka yace "Ke dai baki santa ba, amma ita har yanzu tana so da kuma k'aunar 'yarta, shin kinsan meyasa ta yanki kanta da wuk'a daga jin an anbaci sunan 'yarta? Tsoro, fargaba duk sun ziyarceta a lokacin da taji sunan, ba kuma komai ya haddasa mata su ba sai tunanin wane irin labari muka kawo mata a game da 'yarta Maryama, tana jin tsoron kar ace wani mummunan abu ne ya samu 'yarta tilo, kaka, kina zaune da ita ne amma kin kasa fahimtar damuwarta, kin kasa kallon cikin idonta ki karanci rubutun dake cikin zuciyarta, baki zama mai adalci a gareta ba, da kuwa kin zama mai adalci a wurinta, to da kina kwatanta abinda take ji da a zuciyarta da abinda ke kike ji a duk sanda kika kalleta a wannan halin, nasan babu wanda yafi ki sonta a duniyar nan, kamar yanda babu wanda ya kaiki son ganin ta samu lafiya, ki daure ki kalli idonta zaki fahimci ciwo da rad'ad'in data jima tana d'awainiya dasu a zuciyarta."

Mik'ewa yayi ya kalli su Junaid yace "Ina daga waje."

Da kallo suka bishi dukansu banda d'iyar baba data duk'e kai tana zubar da hawaye, hak'ik'a yaron nan ya birgeta dan ya fad'i abinda shekaru ta kasa fad'a, tabbas ta gane kuskuren da tayi a waccen ranar na yi wa Mari baki, amma ba'a je ko ina ba ta gane kuskurenta, sai dai ina mahaifiyarta ta d'auki zafi sosai dole taja baki tayi shiru, shiyasa ma har idan aka d'auko maganar mari take nuna kamar ita ma ranta a b'ace yake da ita, amma kullum addu'ar ta bata wuce Allah ya dawo mata da ita gida ba, kaka da ita ma sai lokacin ne taji jikinta yayi wani bala'in sanyi har hannayenta sunyi nauyi, tunanin abinda ya fad'a take, a hankali ta juya ta kalli d'iyar baba dake kuka, cikin harshensu tace "Ki kalleni d'iyar baba."

Saida ta gama shan majina da share hawaye kafin ta d'ago ta kalleta lokaci d'aya kuma tayi k'asa da kanta, juyawa kaka tayi ta kallesu tace "Dan Allah ina Mari take yanzu?"

Junaid ne yace "Tana Maradi."

"Kenan can ta tafi bayan munyi watsi da ita? To me take yi acan, wurin kakanta take malam Rabi'u ko kuma Khadi?"

Da mamaki Junaid ya kalleta, idan zai iya tunawa Iklima ta anbaci sunan nan, amma kuma a yanda tace ba mazauni ne shi ba, da wannan mamakin yace "Dama kakan nata acan yake?"

Cikin sanyin murya tace "Ba can yake da zama ba, amma yana da iyali acan saboda yana yawan zuwa can wajen harkokinshi."

D'orawa tayi da "Dan Allah in da gaske kana sonta ka ce mata ta dawo gida, wallahi a yau d'in nan na gane duk kuskuren nawa ne, bai kamata mu mata haka ba, amma ku fad'a min me take yi acan? Wajen wa take zaune?"

Junaid ne ya kalli Amar da Jibril kafin ya kalleta yace "Insha Allahu Hajia zan zan dawo miki da ita gida, na jima ina son Mari ta amince da soyayya ta, amma ta k'i yarda dani saboda waccen abun ma daya faru sam babu laifinta , tayi ne dan ceto rayuwar mahaifinta, da kuma ceton mahaifiyarta daga shiga takaba, yanzu haka ma bata san zamu zo nan ba, wata k'awar ta ce ta taimaka mana har muka zo nan, ina so na koma mata da tabbacin kun bar hushi da ita, idan har ta amince ta dawo to zan zo nan na nemi aurenta, dan nan d'in shi ya fi dacewa dana nemi aurenta."

Kamar daga sama d'iyar baba ta kalleshi tace "Ya cikin data tafi dashi? Ta haife shi?"

Cikin sanyin jiki yace "Ta haife shi Mama, 'yarta tana nan mai wayo sannan mai kama da mahaifiyarta, yarinya ce mai shiga rai."

Sake fashewa tayi da kuka harda rufe baki cikin kukan tace "Dan Allah ku ce ta dawo, ina son ganinta ita da abinda ta haifa, ku bata hak'uri dan Allah, nasan bamu mata adalci ba da muka koreta, bamuyi tunanin halin da zata shiga ba idan ta var gida, watak'ila ma taje ta fad'a karuwanci."

Shirun da sukayi yasa tayi shiru ta kallesu, ganin babu wanda yace mata komai yasa tace "Zaman kanta ta shiga?"

A hankali Amar yace "Mama karki damu, insha Allahu zata dawo gareki, dama mu abinda ya kawo mu kenan."

Kaka ce tace "Abinda kukayi ya nuna mana ku 'ya'yan manyan mutane ne masu dattako, da ace ni na haifi uban Mari wallahi da yanzun nan zan baka Mari halak malak, amma bana da wannan ikon tunda tana da dangin mahaifi, duk da suma sun k'i karb'arta a lokacin da mummunar k'addara ta sameta, amma dole hakk'in su ne mu sanar dasu abinda ke faruwa, anyi sa'a malam rabi'u yana garin nan, dan haka yau ba sai gobe ba zanje da kaina na sanar dashi duk abinda ke faruwa, idan zai yiwu ma sai muje tare daku wurinshi."

D'an kallon juna sukayi kafin Jibril yace "Ba damuwa Hajia, zamu iya tafiya dan ba anan zamu kwana ba, muna so ne mu sake komawa gida."

Da mamaki tace "Amma yaran nan kamar ana korarku, wannan doguwar tafiyar kawai dan wuni d'aya."

Nan dai suka nuna mata eh fa komawa zasuyi, dan haka tace bari ta shirya saita fito su tafi, d'aki ta shiga ta sauya kaya da mayafi ta shafo turare na barebari mai dad'i ta fito, nan suka mik'e suka wa Mama sai sun dawo, suna fitowa Ammar na cikin mota zaune da waya a kunne, Amar dai a zuciyar shi cewa yayi "Mai abun tsiya dana kirki, da kana da budurwa da sai nace da ita kake waya."

Junaid ne ya bud'e ata gida gaba ta shiga ya rufe, baya suka shiga su uku Ammar yaja motar ba tare da sanin inda zai nufa ba, mutanen da suka fito ganin k'wam ne suka koma tsegumi an tafi da *Magaram*, su kuma suna hanya ta dinga nuna musu wurin da hausarta da basu cika ganewa ba har suka isa dan babu nisa sosai ma tsakaninsu, sunyi sa'a samun malam rabi'u a d'akin shi na soro yana rubutu da allo, nan ma gaisawa sukayi za'a kawo musu ruwa suka ce a'a sun gode, cikin harshen barbarci kaka ta dinga mishi bayani, sun d'an jima suna hira wacce tasa suka fara tsarguwa musamman yanda suka ga malamin yana d'an d'aga murya yana magana cikin fad'a-fad'a, Ammar da ranshi ya gama b'acewa ne yace "Dan Allah ko zaku iya yin yaren da zamu fahimceku? Ko kuma idan maganar bata shafe mu ba ku fad'a mana sai musan inda dare zai mana, amma mu ba k'ananan yara ba, ba kuma jahilai ba mu zauna kuna yi damu."

Kallonshi kaka tayi, ita dai duk da ta lura yaron yana da yan matsaloli amma kan daya wayar mata yasa yake birgeta, malam rabi'u kallonshi yayi, (kunsan barebari da fad'a da zuciya) sai kawai ya ga ai tsagwaron marar kunya ne wannan, dan haka ya kalleshi da kyau yace "Magana nake a kan ku, shin ku su waye? Su waye iyayenku a duk garin maradi? Ina kuka san Mari?kuma kuna nufin kun zo neman auren Mari ne ko me? Ina iyayenku suke da ba zaku turo su ba? Ina son sanin amsar wannan tambayoyin yanzu daga bakinku."

Duka gira Ammar ya d'aga sama alamar mamaki ido bud'e sosai, gyara zamanshi yayi yanda zaiji dad'in magana, lura da hakan da Amar yayi yasa shi kallonshi yana mishi kallon "Karka siyar mana da halinka dan Allah ko dan Junaid."

Cike da jin masifa yace "Kai jira zan bashi amsa ne kawai, to ko tsohuwar gidanmu dake da k'wank'wamai ai ina ji da ita bare wannan malamin."

_Yan uwa a yanda labarin gasken ya kasance saboda Ammar yasa aka sha daga sosai kafin rabi'uya ya amince da auren Junaid da Mari, dan yace yaron k'arshen marar kunya ne bashi ba wannan zuri'ar, amma saboda yanayi yasa zan tak'aita masifar dan akwai abubuwa dayawa anan gaba da zasu faru._

Kallonshi Ammar yayi harda alama yake mishi da hannu danya gane yana fad'in "Ni, da wannan da kake gani, uwar mu d'aya ubanmu d'aya, ince dai a garin maradi kasan lieutenant Hassan Gaga? To in ma baka sanshi ba ka tambaya zaka sani, duk wani mai shige da ficen kaya zaisan waye lieutenant Hassan, dan shine babban douanee a garin nan, idan bai yarda ba sai kayanka su shekara dubu a ajiye kuma a wulak'ance."

Nuna Junaid yayi yace "Shi kuma wannan d'ane ga colonel Hussein Gaga, shi ma d'in idan baka sanshi ba ka fara kallon tv zaka san waye shi, ko kuma ka zama d'an tada k'ayar baya a cikin al'uma zaka fahimci waye shi."

Nuna Jibril yayi yace "In dai har garin maradi kake tabbas zaka san d'an kasuwa Labaran Gaga, wanda yan kasuwa suka bashi matsayin chairman d'in su, dan haka tsoho karka d'auka wata bishiya ce aka girgiza muka fad'o, da kuma nayi niyya wallahi ba zan zo nan da niyyar neman aurenta ba kawai, sai dai na zo da sadakinta a d'aura auren mu tafi da matarmu."

Malam rabi'u da al'amarin ya gama zund'umeshi shima kallonshi yayi zaiyi magana sai kuma Ammar yace "Kuma ka tambaye mu wai ina muka had'u da ita? Ai ina ga kamar kunfi kowa sanin inda zamu had'u da ita tunda kun koreta daga gareku, kenan ina kuke son tayi rayuwa?"

A hassale malam rabi'u yace "Ka ce idan da kayi niyya da zaka zo da sadakinta? To jini da kyau marar kunya fitsararre, ni kuma bawai ina raye ba, wallahi ko bayan ba raina auren Mari ya haramta gareku, dan ga dukkan alama baku samu tarbiyya a gidanku ba, na ga kuma shafaffe da man daya isa a kaf dangin nan nawa daya isa ya d'aura auren Mari ba da amincewa ta ba."

Wata dariya Ammar ya shek'a wacce ko hak'oran shi basu fito ba sai sautin kawai kafin ya tsagaita yace "Ni kuma Ammar in dai har d'an uwana Junaid bai janye k'udirinshi na son auren Mari ba, na rantse da Allah ko saceta ne sai nayi na kuma d'aura musu aure."

"A matsayinka nawa? Kai bari dai in mik'e kaga tsawona" Cewar malam rabi'u yana mik'ewa tsaye, Ammar na kallon idonshi yace "A matsayina na yayanshi, zan uya wakiltar iyayenmu akan al'amarin daya shafi dukansu nan, saboda babu wanda ban bawa watanni da haihuwa ba."

Jibril da shi dai tun shigowarsu yaji gabanshi sai fad'uwa yake, yana kallon tsohon kuma sai yake ganin wani yanayin mahaifinshi a tare da mutumin, baisan dalili ba amma yaji tsohon ya shiga zuciyarshi daga *kallo d'aya*, tunda suka fara musayar yawun nan yake jin baya jin dad'in abinda Ammar d'in keyi, yanzun ma mik'ewa yayiya kama hannun Ammar ya matse sosai ya kalli tsohon yace " Dan Allah kaka kayi hak'uri, yana da zuciya ne."

Malam rabi'u shima sai yanzu ne ya kalli Jibril d'in kallo na tsanake, shi kanshi gabanshi ne ya fad'i, Jibril dake rik'e da hannun Ammar fita yayi da shi waje inda malam ya bi Jibril da kallo, wata zufa ce yaji tana tsatsafo mishi ba gaira babu dalili, take ya fara tuna abubuwan da yayi zamanin k'uruciya wanda har yanzu wannan banzar d'abi'ar bai wani barta ba sai dai in bai samu dama ba, sai dai ya kasa tuna wace uwar ce ta haifa mishi wannan yaron? (Ko kuma ta haifa maka wannan jikan ba, wato shi aiki ko na alkairi ko na sharri dama kana iya mantawa idan kayi, amma wanda kayi wa baya mantawa), Amar da Junaid da kaka ne suka dinga bawa malam hak'uri suna tausarshi, da k'yarsuka shawo kanshi bayan Junaid ya nuna mishi yana so su taimaki rayuwar Mari wacce ke tallar kanta ga kowane namiji yana biyanta, sosai ya jima yana mishi nasiha cikin girmamawa, gamsuwa malam yayi hakan yasa yace ya amince da buk'atarsu, amma indai da gaske yake to dole ya turo iyayenshi dan suyi magana ta manya, alk'awari suka mishi kan zata turo manyansu kafin daga bisani suka mishi sallama suka taso suma.

Jibril dake rik'e da hannun Ammar suna fitowa ya fizge hannunshi, bud'e mota yayi ya fito da gorar (bidon) ruwa ya bud'e ya sunkuya yana dararawa a kanshi, saida suka k'are yayi cilli dashi yasa hannu aljihu da niyyar fito da abinda zai goge fuskarshi, lalitarshi ce ta fara fitowa dan haka ya rik'e a d'aya hannun ya sake mayar da hannun aljihu zai fito da shi, kai mai tsautsayi da Allah ya aiko ka kana ganin bak'i ne a garin sai kuwa wani matashin saurayi yayi wup da lalitar ya sura a guje, da sauri da kuma mamaki suka kalli juna shi da Jibril, haba ai saiya mik'awa Jibril mouchoir d'in ya fito da wayarshi a gaban aljihu ya damk'a mishi, da mamaki Jibril ya ke kallonshi yace "Me zakayi Ammar?"

"K'ure mishi gudu zanyi." Cewar Ammar dake hangen yaron nata gudu.

*Kai jama'a*๐Ÿ˜‚

*Sai A shafi na gaba muji wai da gaske artawa zaiyi ko kuwa zai rabu da wannan daya tari aradu da kai.*

_Rashin comment, hummm, saura kad'an ku daina jina._
05/06/2020 ร  20:21 - Ummulkhairi: ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
*BADAK'ALA*
๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ _*AHALI NA*_๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_9_


Kamar a almara Jibril ya hangi Ammar ya zage k'arfi ya palla a guje ya bi bayan yaron, tuni hankalin jama'a ya koma kansu ana kallo, yanda yake gudun kamar wanda aka ce idan ya fad'i ya rasa gasar shiga soja kenan, shi kanshi gudun da akeyi saiya birgeka, dama kuma haka Allah yake hallitarsa, idan ya maka kyau sai kaga komai kayi saiya maka kyau ko kuma wani yaga kyanka, duk gudun yaron nan saiga Ammar ya cimmasa har yana neman take shi, k'afa yasa ta baya ya harbi nashi k'afafun hakan yayi sanadiyar fad'uwar yaron warwas a k'asa, kafin ya ankara yasan fad'uwa yayi Ammar ya shak'o wuyan rigarshi tare da bank'are hannunshi ta bayan wuyanshi ya murd'e ya amshi lalitar, ba tare daya sakeshi ba kuma ya izo k'eyar shi gaba izuwa inda suka bari, mutane dake kallon k'aramin kafce wasu na tunanin su bayar da hak'uri su raba, sai dai tunanin su yafi basu cewa soja ne duk da cikin wani yadi yake kalar ruwan madara shara-shara, dan haka meya kaisu shi ma yaron tsautsayi ne da kuma k'arar kwana, yaron da yaga Ammar na dawowa dashi fashewa yayi da kuka yana so ya durk'ushe ya bashi hak'uri amma ya k'i barinshi ma ya kai k'asan, cikin kuka dake nuna tashin hankali yake fad'in "Dan Allah baba na kayi hak'uri, wallahi yunwa ce tasa nayi maka k'wace, ka rufa min asiri kayi min rai."

Ko saurarenshi baiyi ba har suka zo inda Jibril ke tsaye mamaki ya gama kashe shi, suna zuwa Amma ya jingina ga koma ya saki yaron ya kalli Jibril yace "Ban hankici (handkiciep) na."

Mik'a masa yayi yana kallon yaron da tsoro ya gama bayyana a tare da shi kamar ya ga mala'ikan d'aukan rai, yana cikin goge zufar dake tararowa kanshi zuwa fuska da wuyanshi ya kalli yaron yace "Durk'usa."

Kamar marar k'ashi a jiki haka ya lauye ya durk'ushe yana sake fad'in "Dan Allah kayi hak'uri baba na, wallahi ni ba b'arawo bane tsautsayi ne da yunwa, dan Allah magajina ka bashi hak'uri kar ya kaini prison (magark'ama)."

Ya k'arashe maganar da duban Jibril, idon nan sun kad'a sunyi jawur ya kalli yaron da kyau yace "Kai, kasan ko wanene ni?"

Da sauri ya girgiza kai yace "A'a."

"To meyasa duk garin nan ka rasa wa zaka figi kayanshi sai ni?"

K'uri ya masa da ido yana kallo jikinshi banda rawa babu abinda yake, hannu ya d'aga kamar zai mareshi yace "Da kai nake kana jina ka min shiru."

Cikin kukan firgici yace "Wallahi yunwa ce tasa, kwana biyu ban ci komai ba, kuma nayi bara ban samu abinda zan ci ba shiyasa, dan
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment