Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwantar da kanta saman k'afafun Ammie tayi shiru, cire mata d'an kwalin tayi ta fara shafar kanta data ji shi a jik'e, take ta fahimci komai, dama ba kunya ce tsakaninsu ba dan haka Ammie tace "Auta halan hukuntaki yayi saboda baki taho tare da mu ba?"

D'agowa tayi ido taf da hawaye kamar zata fashe da kuka tace "Ammie hukuncin ma mai tsanani, wallahi bai tab'a min irin shi ba sai yau, bansan a ina ya koyi wannan muguntar ba, ni gaskiya Ammie daga yanzu d'akin ki zan kwana har saiya bani hak'uri."

Kwantar da kanta tayi tana daddab'ata b'angare d'aya tana toshe baki tana dariya, labari ta fara bawa Ammie yanda sukayi da matar waziri, dariya kawai Ammie take tana godewa Allah da abun ya tsaya iya mari kawai, suna haka sai ga Abbas ya shigo tak'im tak'im kamar wanda aka bawa sarauta, Ammie na ganinshi ta had'e rai tace "Kai kuma malam lafiya? Meya kawoka wajenta?"

Saida ya harari Sameera yace " Ni ba wurinta na zo ba."

Zaune yayi kan kujerar dake fuskantarsu ya kalli Sameera dake wurga masa harara yace "Ke tashi ki bamu wuri zamuyi magana da uwa ta."

Sake mak'alk'ale Ammie tayi tace "Ba zan je ko ina ba, ka fad'i duk abinda zaka fad'a ina gaban uwata."

Murtuke fuska ya sake yi, matsalarshi da ita daman kai tsaye zai bata umarni tace ita ba haka ba, kafeta yayi da ido kawai hakan yasa Ammie kallonta tace "Yarinyata, shiga d'aki na ki kwanta abinki gani nan zuwa yanzu, idan kin shiga ki duba a drower akwai kayan dad'i ki d'auka kinji."

Mik'ewa tayi a kasalance ta wuce ko d'an kwalin nata bata d'auka ba, da kallo ya bita kafin ya kalli Ammie wacce tace "To ina jinka, lafiya da zaka wani katsewa yata jin dad'in ta?"

Mik'ewa yayi yace "Ba komai, dama zan d'an fita."

Kafin tayi magana taga ya sa kai ya nufi d'akin nata kuma, girgiza kai tayi tace "Kaji da munafurcinka, da nace wurinta ka zo ai cewa kayi a'a."

Sameera na sunkuye zata d'auki chocolat taji saukar mari a mazaunanta, da sauri ta d'ago ta dafe kayanta tana fad'in "Washhhh."

Tana ganin yanayin shi sai kuma tayi shiru, cikin muryar shagwab'a tace "Dan Allah Abban Ameer ka daina wahalar dani haka, ya kamata fa ace yanzu na wuce ajin shan wahalarka, wacce na sha ma a baya lokacin da nake maka bauta ta isa haka."

Yana kallon k'aramin bakin har saida ta dasa aya sai kawai ya had'ata da bango ya had'e bakinsu, wani bala'in kiss ne yake mata mai matuk'ar zafi kamar zai cire mata labb'a, tuni idonta suka kawo ruwa ta rufe ido wasu hawaye masu zafi sirara suka shiga fitowa suna bin kumcinta, a gefen fuskarshi ne ya ji alamar lema hakan yasa ya tsaya yana kallonta, cikin wata irin murya ba tare daya matsa daga cikin jikinta ba tace "Sam ki dinga jin magana ta mana, bana so muna irin haka dake dan mun girma yanzu, ki ce zaki dinga ji duk abinda na fad'a miki, ni kuma ba zan sake bari ki zubar da hawaye ta dalili na ba."

Bud'a ido tayi cikin shashek'a tace "Zan dinga jin maganarka indai kayi alk'awarin ba zaka sake min irin muguntar nan ba ta yau?"

Yanda tayi maganar saiya k'ayatarda shi, bud'e mata hannayenshi yayi alamar ta taho, sake fashewa tayi da kukan da bata san dalilinshi ba ta fad'a cikin lafiyayyen k'irjin shi, matseta yayi sosai yace "Na miki alk'awarin ba zan sake ba indai nima zaki dinga jin duk abinda zan fad'a miki."

Cikin shashek'ar kuka tace "I promise u, please forgive me."

Cikin shafar tattausan bayanta yace "I forgive u my Meerata, i really love u."

Sake k'amk'ame shi tayi a haka suka fito falon tare, Ammie na ganinsu rumgume da juna sai ita taji kunya, dama kuma ba sabon abu bane a wurinta, kullum suka samu matsala saita tsaya bayan Sameera ko tasan ita ce bata da gaskiya, ba jimawa kuma sai ka gansu a had'e a jone.

➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️

Abbakar ne ya samu Saleem a d'akin shi yana waya da Fadila kamar sun jima da fahimtar junansu, yana ganin shigowarshi ya datse kiran yana fad'in "Yah Abbakar, kaine yanzu?"

A hankali ya k'araso cikin jan k'afar shi ya tsaya kusa da shi yana kallonshi yace "Saleem baka kwanta ba har yanzu?"

Murmushi yayi yace "Ban kwanta ba yah, amma kai ma ya akayi baka kwanta ba har yanzu?"

Shima murmushi yayi yace "Ina ta tunaninka ne Saleem."

Da mamaki yace "Tunani na kuma yah? Akan me? Ko dai tunanin Zeenat?"

Girgiza kai yayi yace "Tunaninka nake Saleem, tsoro kake bani, ina gudun kar kaje kayi abinda zai saka mu cikin matsala, shiyasa na gagara bacci har na zo na sameka, kwanan nan kana wayon fita kuma baka zama sosai a shago, sannan kashe kud'in ka ya k'aruda kaso goma, me kake yi da kud'i Saleem? Ina kake zuwa idan ka bar shago?"

Cike da nuna alamun rashin gaskiya ya fara shafar kai yana fad'in "Yah ba komai fa, ka yarda dani mana, ni fa yanzu ba k'aramin yaro bane, nasan abindake daidai da wanda ba daidai ba, so calm down bros."

Ajiyar zuciya ya sauke yace "Saleem kai ba yaro bane, amma dai kasan ina gaba da kai ko? Please Saleem ka fad'a min idan akwai wani abinda ke damunka, na maka alk'awari insha Allah zan taimaka wajen solven matsalarka, amma bana so kaje kayi abinda ya sab'awa shari'a da ma al'ada da mutuntaka ta d'an adam."

Shiru Saleem yayi baice komai ba, jin ba zaiyi magana ba yasa Abbakar cewa "Saleem idan kana da matsalar sha'awa ne ka fad'a min sai mu maka aure, amma karka jefa kanka a harkar neman mata, mummunan zane ne da zaka yiwa kanka na har abada."

Cike da k'aguwa ya kalleshi yace "Yah ba komai fa, dan Allah kaje ka kwanta, ba zan tab'a neman mata ba kai ka sani."

Cikin sanyin jiki ya juya ya bar d'akin inda Saleem yace "Har na fara jin k'amshin yanda zan kuntatawa rayuwarsu zaka zo min da wata magana, yanzu kana komawa d'akin ka hoton matsiyaciyar yarinyar nan zaka d'auka ka fara kallo har gari ya waye maka."

➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️

Gari na wayewa yau yan matan suka shirya driver ya kaisu school dubo result d'in, suna zuwa kuma basu sha wahala ba suka samu sakamokonsu mai kyau suka juyo cike da murna, kai tsaye gida suka sake dawowa, suna zuwa da farin ciki kowace ta nuna nata, gaskiya ne Raihan tafi k'ok'ari sai Fadila sai kuma Ma'awa, hakan yasa Bashir da Naseer suka dinga yabawa Raihan har kowane yayi alk'awarin kawo mata kyauta, Abbas kuma su Fadila ya dinga yabawa wanda yasa Fadila jin kawai yana yaba musu ne saboda iyayensu basu yaba musu ba, shima cewa yayi zai bawa kowace kyauta, suna tsaka da raharsu Harira ta fito cikin kwalliyarta kamar yanda ta saba yanzu ta kawowa Ameer takalminshi, saida ta durk'usa har k'asa ta saka mishi takalmin kafin ta mik'e ta juya tana jijjiga, duk da Sameera ta ga hakan amma saita barshi a matsayin zawarci tana neman mijin aure ne, kuma tasan babu abinda mijinta zaiyi da Harira, dan haka bata damu ba, nan Abbas yace yaran su shirya sai su fara tafiya basraba, nan da sati biyu idan aka gama bikin Husna sai a tafi tare da su kan amarya daga nan zasu iya yin hutun su a can, sunyi farin ciki sosai saboda zasu fita wata k'asar da ba tasu ba.

Da dare kam su Bashir sun cika alk'awari ta hanyar kawo musu kyaututtukansu, sai dai Abbas ne ya gwangwajesu da manyan wayoyi yan zamani duk iri d'aya, sunyi godiya sosai tare da binshi da addu'a kafin daga bisani kowa ya nemi gado ya kwanta, Sameera da Abbas ma har sun kwanta ya tuna sam rabon da yaga bak'uwar nan tunda rana, dan duk hayaniyar nan da aka dinga yi tana d'akin ta, dan haka ya fito dan dubata, yau ma k'wank'wasa k'ofar yayi ta bud'e, sai dai yau doguwar riga ce a jikinta ta bacci, tambayarta kawai yayi ya k'afar ta ta amsa da sauk'i ya mata saida safe ya koma, Sameera kuma yana zuwa ta fara mishi mita akan yarinyar nan ita fa bata son ganinta, ya fad'a mata yana so ta samu sauk'i ne saita fad'a musu gidansu ya kaita, amma tace me zai hana ya tambayeta tun yanzu saiya kaita can tayi jinyar? Da dai yaga yana tarota tana zillewa sai kawai yace ina alk'awarin data d'aukar masa jiya jiya? Hak'uri ta bashi tace to yayi hak'uri ta daina kuma zata zuba mishi ido har lokacin daya sallameta.

*Bayan kwana biyu*...
12/06/2020 à 15:19 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*BADAK'ALA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

👨‍👩‍👧‍👦 _*AHALI NA*_👨‍👩‍👧‍👦

🇳🇪 *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_15_


Kai tsaye dama yake shiga d'akin Hajia, sallama kawai yayi ya tura k'ofar ya shiga, zaune ya same ta kan gado cikin doguwar yellown riga ta bacci, saida ya ja kujera ta gaban madubinta ya zauna ya kalleta, ita ma shi take kallo tana murmushi kafin tace "Shalele na ka ci abincin?"

A dak'ile ya amsa da "Na ci."

Cike da kulawa tace "Ina fatan dai baka tare da gajiya ko?"

Saida ya sake b'ata rai yace "A'a."

Murmushi tayi saboda yanda ya turo baki saita tuna lokacin yana k'arami, mik'a mishi hannunta tayi alamar ya taso, bata hannun yayi ya taso ya zauna kusa da ita ta fara shafar sumar kanshi, a ranta tana ayyana ai dole ma ta so shi, dan kaf cikin yaran babu wanda suka d'auko kalarta kamar shi da d'an uwanshi, hatta gashin kansu ya murd'e yake, dogayen hanci har baka da k'aramin baki jawur da shi, kurmin ido kuma manyan ido masha Allah, sannan gasu zabga zabga wajen tsayi wanda nan kuma kakansu ne sukayi Suley, tana kallonshi tace "Shalele ina fatan dai zab'in dana maka yayi maka ko?"

Kallonta yayi da mamaki, wato ta kira shi ne dan taji idan zab'in ya birgeshi, idan har yace bai mishi ba yasan dole zata canza mishi kuma cikin dubara, ganin kallon da yake mata yasa tayi murmushi tace "Kasan wani abu shalele? Ina matuk'ar k'aunar ka a zuciyata, kaine jin dad'i na da rayuwata, na zab'ar maka Umaima ne saboda kaga tafi sauran yan matan wayewa da ilimi, bata da kwaramniya da shiga abinda bai shafeta ba, sannan kaga tana koyon aiki a inda kaima kake aiki, shiyasa na maka wannan zab'in."

Shi dama baida matsala da zab'in data mishi, matsalar shi kawai yan uwanshi dake cikin damuwa saboda zab'in nata, dan haka yace "Hajia, ni banda matsala da zab'in da kika min, kin sani nima ina sonki kuma ina son farin cikinki, saidai Hajia 'yan uwa na ba duka ne suka gamsu da zab'in nan ba, idan zai yiwu dan Allah ki bar kowa ya zab'i wacce yake so."

Wata hamshak'iyar dariya tayi tace "To meya shafeka da su? Ai ka barsu kawai babu abinda zai faru, duk wanda aka kaiwa macen d'akin shi ba zai fasa kulata ba."

Cikin butsuwa yace "Hajiata, aure fa rayuwa ta din-din-din, ya kuke tunanin zasuyi farin ciki idan basa son junansu? Wallahi dukansu zasuji basu da maraba da marasa 'yanci, Hajia dubeki mana ke da Alhaji, a shekarun nan da kuka d'auka tare kina ganin da babu soyayyar junanku a zuk'atanku da zaku iya zama da juna ne? Ko da kun zauna Hajia dole d'aya daga ciki yana jin an takura shi, wannan rayuwar ce bana so yan uwana suyi, Hajia Junaid yana da wacce yake so, wacce yasa mukayi doguwar tafiya dominta, haka ita ma Hamna tana da burin da take so ta cimma, lokacin auren da kika saka yayi daidai da lokacin daya kamata ta fara zuwa koyon darasin zanen ta, yanzu haka kuka na barota tanayi saboda tana ganin kamar an ruguza mata burinta ne, shi kanshi Junaid d'in yana can kukan ne kawai baiyi ba saboda shi namiji ne ya fita dauriya da juriya, dan Allah Hajia ki taimaka ki musu wannan alfarma."

A hankalce ta kalleshi tace "To yanzu shalele sun turoka ne ka samar musu abinda suke so?"

Murmushi yayi yace "Hajia ban isa su turo ni ba? Na d'auka yanzu kika gama fad'in nine rayuwarki, hakan da suka bai isa yasa su turo ni ba? Sannan ni babu wanda ya turo ni, na fahimci damuwar kowane ne kuma nake rok'a musu alfarma a wurinki, idan kuma ba zan samu ba saina hak'ura, amma dai abun zai tsaya min a zuciyata ace na kasa samun wannan yar alfarmar a gurin kakata da nake da yak'inin babu mafi soyuwa a zuciyarta sama da ni."

Shiru tayi ta zurfafa tunani akan buk'atar shalelen ta, ya zatayi Allah ya d'ora mata k'aunar shi, shi kuma jin shirun yasa ya mik'e yace "Saida safe Hajia."

Tana kallo yake tafiya harya kusa kaiwa bakin k'ofa, da sauri tace "Shalele na."

Cak ya tsaya tare da juyowa ya kalleta, da murmushi a fuskarta tace "Na amince da buk'atar ka saboda jin dad'in ka, ka fad'awa Junaid zanyi magana da iyayenshi suje su nemo mishi auren yarinyar, amma karku d'auka zata samu karb'uwa a zuciya ta dan karuwa ce ita, sai kuma Hamna, ita ma ka fad'a mata zata iya tafiya duk inda take so indai ba zai kai ga fita k'asar waje ba, amma kuma ya zama dole ta zauna ta halarci bikin nan, dan yer uwarta ma na buk'atar ta a kusa da ita, idan sun amince da hakan to shikenan."

Dariya yayi sosai ta nuna tsantsar farin cikinshi, da sauri ya zo gabanta ya durk'usa ya kamo hannunta ya sumbata yace "Allah ya bar min ke Hajia ta, nagode sosai da wannan alfarmar."

Shafa kanshi tayi da hannu d'aya ta tallabo hab'arshi ta kalli farin cikin dake kan fuskarshi tace " *Amar*."

K'ura mata ido yayi dan bai cika jin sunanshi a bakinta ba, d'orawa tayi da "Ka ci gaba da farin ciki irin haka ko da bayan raina ne, wannan shine burina a kan ka, kuma ina fatan Umaima ta zamo macen da zata dinga saka ka farin ciki irin wannan, in tayi haka zata zama suruka ta farko data fara shiga zuciyata saboda kyautatawa, zan so ta, zan k'aunace, zan faranta mata rai, duniya zata mata dad'i, zan so duk abinda ya fito daga cikinta, suma 'ya'yanku zan so duk abinda zai fito daga garesu, kaji ko?"

Murmushi ya mata sosai hakan yasa ta kama dogon hancinshi taja tana fad'in "Ka tashi kaje ka kwanta dare yayi, saida safe."

Da haka ya baro mata d'akin, bai bi takan d'akin su Ummy ba dan yasan mahaifinsu na nan, a inda ya bar Hamna ya same ta tayi shiru, yana mata albishir taji dad'i, amma daya fad'a mata dole zata kasance a duk wata sabga sai kuma ta marairaice tace "Amma yah Amar ai kamar ba'a rabu da bukar bane aka haifi Abu."

Dariya yayi yace "To yanda zamuyi shine, bara na samu Hajia na fad'a mata kin amince da auren ma kawai."

Da gudu ta nufi falon tana fad'in "A'a yah Amar ba sai munyi haka da kai ba."

A gurin Junaid ma farin ciki ba'a magana, Jibril ya tayashi murna sosai inda Ammar yayi gum yana kallonsu, da wannan kawai suka samu suka kwanta da huta gajiya.

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

Ko da Zeituna ta shiga gidan yau ma babu wannan hantarar da kyara, abun mamaki ne shine wanka da Jumma tace tayi saita kwanta dan taji dad'i, haka ta shiga wanka amma bata jima ba ta fito, ta zo aje bokitin hannunta ne ta bukkar kawu Mamu taji suna hira a harshen fulatanci, kawu Mamu taji yace "Ki dinga matsa mata fa tana wanka akai akai, dan ni dai ba zan iya fitar da wasu kud'i ba dan gyaran jikinta, shi kuma Alhajin yace baya son k'azanta da tsami."

Jumma ce tace "To yanzu ma ba a gabanka ba nace taje tayi wankan ba? Ni wallahi gar yanzu ina d'an d'ard'ar da lamarin ne, bana son mu shiga bakin duniya, ina gudun azo mutumin nan kashe ta ma zaiyi."

Cikin fad'a kawu Mamu yace "Ke wai wace irin jahila ce? Na fad'a miki ba kasheta zaiyi ba, buk'atar shi kawai yace zai biya ta duburarta fa saboda akwai aikin da yake so ya cimma, kullum ina gaya miki amma kina wane baud'ewa kamar ke ce za ayi abin da ita."

Shiru dai Jumma tayi dan bata iya masifar, wannan batu da Zeituna taji shine yasa taji k'afafun ta na rawa jiri na fizgarta, cikin wani mawuyacin hali ta kai kanta bukkarsu, zaune tayi a k'asa inda ta shinfid'a tsohon hijabinta a kai, kasa fahimtar halin da take ciki tayi tsabar rud'un data shiga, tunda ta d'ora idonta wuri d'aya ta kasa d'aukewa, hakan yasa hawaye bin fuskarta wani bayan wani, tambayoyi ne jere reras take wa kanta kuma ta kasa samun amsarsu, kawunta karuwa yake son mayar da ita? Karuwar ma wacce za'a dinga mu'amula da ita ta bayanta? Nawa ya karb'a domin wannan lalatattar harkar? Wanene mutumin? Meyasa sai ni da ban tab'a iskanci ba zai zab'a? Me nayi kawu Mamu har haka da k'iyayyarshi tayi tsamari a kaina? Ya Allah gani gareka! Allah ka dubi halin da nake ciki ka kawo min d'auki? Domin kuwa da nayi wannan rayuwar da yake son jefa ni har gwara na mutu ace bana raye, tana gama wannan tunanin kuma saita fashe da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, yanda taga safe haka taga wannan dare bata rintsa ba tana sak'ada warwara, ta rasa mafita akan yanda zatayi, da wannan har ta wayi gari tayi abinda ya sawak'ata nufi wajen aikinta.

*Gaga's family*

Kamar kullum dai Hajia na zaune kan kujerar data saba zama, inda yara da ma wasu daga cikin iyayen ke zaune gefe sai maganganu k'asa k'asa, ko karyawa ba ayi ba bare kowa ya kama gabansa, Hamna da Amna da Jamila ce suka fito tare cikin shirinsu na uniforme (tenue) d'in makaranta, dukansu da Hijabi amma banda Hamna da siririn d'an kwali ne kawai ta d'ora, kayan nasu komai ido d'aya ne ita da Amna hijabi kawai ya banbanta su, yanda suka saba haka suka gaishe da Hajia da kuma Sa'ada da lieutenant dake kusa, ganin Amna da Hamna zasu fita yasa Sa'ada cewa "Yan biyu na tafiya zakuyi ko karyawa bakuyi ba?"

Cikin taushin murya Amna tace "Ummy kinsan yanzu ana kusan jarabawa ne, wallahi ana yawan yi mana jarabawar bazata a classe."

Lieutenant ne yace "To akwai kud'i aljihunku ko?"

Hamna ta amsa da "Akwai Abba, sai mun dawo."

Har sun juya zasu fita suka ji muryar Hajia tace "Ke ai kinji sak'o na ko?"

Juyowa sukayi sai Hamna da tace "Eh Hajia, na ji."

Cike da gadara tace "Da kyau, tunda kin zab'i zama yar fashion amadadin zama matar aure sai kije kiyi, nasan dai duk tsiyar ba zata wuce uwarki ce ke zugaki ba, kuma ni nafi k'arfin ta wallahi, dan haka babu inda zaki ji har sai an gama bikin nan."

Shiru Hamna tayi tana kallon k'asa tana gunguni inda maganar kuma ta kashe Amna, ita kullum Hajia saita zagar mana uwa ta d'ora mata laifin da bata ji ba bata gani ba, a wulak'ance tace "Ku b'ace min da gani."

Juyawa sukayi suka fita a hanyarsu ta fita kuma suka had'u dasu Amar zasu shigo falon, gaisawa sukayi cikin mutumci kafin Hamna ta kalli Junaid sai taji kunyarshi ta kamata kar yayi tunanin ta k'i shine, shi kuma murmushi ya mata na suna cikin farin ciki kawai, fita sukayi Hamna na mamakin ko ina boss d'in yau, suna nufa inda zasu d'auki motonsu suka hangeshi yana waya.

Gabansu ne duka ya fad'i wanda a wajen Amna sabon al'amari ne daya fara zuwar mata yau, masha Allah cewar ta a zuciyarta, hak'ik'a k'ananan kaya na bala'in mishi kyau, kamar kullum kuma takalminshi k'afa ciki ne inda ya d'aure wuyanshi da cravete (nikctie) kai ka rantse *jan kunne* ne idan ba magana yayi ba, cikin tsoro Amna ke tafiya ta sanda kanta k'asa dan bata so su had'a ido, inda Hamna dake rik'e da makullin motanta take gaba sai kace idan sunje za tayi wata tsiyar, kasancewar ba tsaye yake wuri d'aya ba yana d'an kai da kawowa yasa shi d'an zaunawa kan motan nasu, suna isa suka tsaya inda Hamna ta d'an rik'e kan mota tana nesa da shi tace "Bossss..."

Da sauri ta kama bakinta dan tasan ko da gudu ya bita zai tarar da ita, shi kuma yana d'ago idonshi akan Amna ya sauke wacce ta tsaya daga gabanshi nesa da shi, ganin ta k'i yarda su had'a ido yasa shi k'arewa fuskarta kallo, saida ya gama kallonta tas ya d'an karkata idonta ya kalli Hamna dake bayanshi tsaye ta madubin moton, kowace shigar da tayi ta dace da ita, Amna kuma duk da tana jikin hijabi amma kasan ita ma yar duma-duma ce kamar 'yar uwarta, hak'ik'a Hamna tafi haske, amma baisan dalilin da yasa yau kuma yanzu daya kalli Amna ba sai yaga duhun nata ma mai kyau ne, sannan sai yaga tafi mishi kyau akan ita Hamna, a hankali ya mik'e daga kan moton ya juyo da dubansa kan ta, babu alamar wasa bare raha, kallon da yake yamutsa mata lissafi ya mata cikin muryarshi dake tayar mata da hankali yace "Baki iya gaisuwa?"

Saida ta turo baki gaba tana zuntoshi tace "Ina kwana."

Sake kallon surarta yayi sai yaji haka kawai ranshi bai mishi dad'i ba ganin kayan sun kama jikinta, duk da ba sosai bane suka matseta amma dayake anfitar da gurbin komai yasa komai d'in fitowa, masha Allah faffad'an k'ugunta ya kalla ta k'asan ido, da sauri ya d'ago cikin tsawa yace "Dan ubanki maza koma ki sanyo hijabi, kuma wallahi kika k'ara bari na ganki babu hijabi sai ci uwaki gidan nan."

Juyawa tayi ta sa kukan shagwab'a harda bubbuga k'afafu take tana tafiya kamar zatayi gudu, "Shegiya!" Ya fad'a a ranshi a zahiri kuma yanda k'ugunta ke kad'awa yasa yace "Kankana."

Dole ta tsaya ta juyo dan kiran sunan da yayi cikin wani yanayi ne dake nuna kifa kiyayeni, k'ara d'aure fuska yayi yace "Ba zaki iya tafiya a hankali bane har sai kin tashi hankalin wad'anda ke kwance k'asa?"

*Maganar nan da biyu, sai dai bangane manufarta ba*

Daina bubbuga k'afafun tayi amma bata daina saurin ba da kukan, saida ya ga shigarta ya d'an juyo a hankali, Amna na ganin zai juyo kanta tayi saurin cewa "Yah Ammar ina kwana."

A hankali ya taka kusanta yana kallonta da mayatattun idonshi da lokaci d'aya ba zaka iya fahimtar manufar kallonshi, saida yaga ya k'ureta kad'ai ya tsaya kamar zai ci tuwo a saman kanta, Amna da ke jin kamar ta sako fitsari jira take taji yace dan ubanki bakiyi abu kaza ba, amma taji shiru gashi babu niyyar ya d'an bata wuri tasha iska, shi kuma baiwar da Allah ya mishi yasa yake iya hango yanayin da take ciki a goshinta, ji tayi yace "Kalle ni."

Gudun laifi yasa ta d'ago da sauri ta kalleshi, kamar saukar aradu a kanta taji yace "Tun yaushe kika fara al'adarki?"

Wani bazawarin tari ne ya taho mata bata san da zuwanshi, da sauri ta rik'e tarin ta hanyar rufe bakinta gam tana kallonshi, gashi kuma yayi alamar kamar na shi yayi maganar ba, k'asa tayi da idonta ta kasa cewa komai, ji tayi ya sake cewa "Ki tabbatar kafin aurenmu kin shirya fad'a min lokacin da kike farawa, da lokacin da kike gamawa, sannan yaushe kike wankan tsarki?"

Yana gama fad'a ta hange shi cikin wannan takon nashi na in sojojin sun motsa a kanshi, baki sake ta maimaita kalmar " *Kafin aurenmu*, kenan ma yana son auren? Anya kuwa zan iya?"

Firgigit tayi ta sake kai dubanta hanyar falon Hajia

Please Login or Register in order to submit comment