Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya ji motoci na oda alamar sun fara tafiya ya d'ago kanshi, juyawa yayi inda Hamna ke zaune suna had'a ido gabanshi yace wani "Dassss." Ya fad'i ba tare da sanin dalili ba.

Inda ita kuma na ta gaban yace "Dammm." Kallon tsoron da take mishi ne yasa ya had'e fuska yace "Dallah ni bari kallo na sai kace mayya."

Da sauri ta kalli gabanta a ranta tana fad'in "Toh, aifa kuma na shiga uku, gashi yanzu babu ni babu guduwa idan ma na k'ular da shi."

Tashin motar yayi ya fizga da gudu inda ta bi hannunshi da kallo yanda ya murza sitiyarin, k'aramar jakarta ta fito da ita ta d'auki abun sauraro (Γ©couteur) ta danna a kunne saboda tasan zaman shiru ne za ayi, suna shiru haka tana sauraren wak'ok'inta kira ya shigo wayar, d'auka tayi suka fara hira ita da saurayin na ta duk da ba wai son shi take ba, yanda take kashe murya dan kar Ammar yaji yace tayi laifi ashe dai bata tsira ba, dan yanzun ma haushi ne ya kama shi wai akan me zata wani kashe murya haka tana hira da saurayi, cikin hassala ya fizgo wayar hakan yasa abun sauraron ya fita muryar saurayin ta bayyana, yanda shima ya kashe murya ne ya k'ara tunzura Ammar, dan haka saurayin da baisan meke faruwa ba yace "To ai dole ne ko? Yanda kika kashe min jiki haka da muryaki ai sai bacci ya d'auke ni alhalin ina cikin tuk'i."

Tsabar neman fita Ammar sai ce mishi yayi "Insha Allahu kana baccin nan ba zaka bud'e ido a ko ina ba sai cikin k'abari, ku ko kunya baku ji ku tsaya hira da 'ya'yan cikinku haka, yanzu haka matarka na can ranta a b'ace amma baka san ya zakayi ka kwantar mata da hankali ba, k'aryar banza kawai."

Kashe wayar yayi ya cillata k'asan k'afafun shi inda birki yake yana jan wani tsakin, Hamna dake kallonshi ta kasa gane me yake nufi tace "Yaya Ammmm..."

Bai bari ta k'arasa ba ya nuno mata yatsa yace "Kar ki sake ki min magana."

Yanda ta ga fuskarshi yasa taja baki tayi shiru, suna tafiya taji shirun yayi yawa, hannu ta zura ta kunna redion motar dan shi tsabar baya son hayaniya ko redio na mota baya kunnawa, tana kunnawa yayi daidai da tashar ana wak'a, cikin jin haushi ya buge hannunta yace "Kar ki sake tab'a komai dake motar nan."

Tab'e baki tayi suka ci gaba da tafiya, ana haka ta ji masuburbud'ar sanyi (ac) na bata sanyin dayawa ita kuma bata so, sai kawai ta zura hannu zata d'an juyar da shi gefe, ai kuwa sai ji tayi kanta ya bugu da abun sanyin saboda wani wawan birki da Ammar ya taka, kafin ta ankara taji ya fizgo hijabinta dake jikinta wanda dama ta sanya ne saboda zasu zo wajen rasuwa, kamo hannayenta yayi duka biyun ya had'e wuri d'aya yasa hijabin ya d'aure su tamau, kallonta yayi da jajayen idonshi yace "Kinfi kowa sanin bana magana sau uku akan abu d'aya, nayi biyu ba zaki sani bayi uku ba, idan har na ji bakinki yanzu wallahi bolar dake kan hanyar nan zan tattaro na tusa miki su a baki har sai mun kai gida."

Hamna da ido suka cika da hawaye shiru tayi dan babu damar bashi ko da hak'uri ma, bai sake kallonta ba har saida suka isa cikin gari ya kalleta yace "Ke gaki marar kunya, a gabana wani d'an iska zai kira ki har kina kashe mishi murya, shi kuma dayake babban kwarto ne har yana fad'a miki wai zai yi bacci, haba."

Hamna dai ko kallonshi batayi ba har suka isa gida, motoci na tsayawa a farfajiyar gida aka firfito, Hamna babu hannayen bud'ewa saida Ammar ya bud'e mata k'ofar ta zuro k'afafu ta fito, take kallo ya koma kanta inda Junaid da dama yasan abinda zai faru kenan ya riga kowa bushewa da dariya, da sauri Amna ta k'araso ta kunce mata hannuwa tana fad'in "Yaya Ammar ne ya d'aure ki? Ke kuwa me kika masa haka kamar wata dabba?"

Kamar zatayi kuka tace "Me kuwa zan masa, bak'in halin ne ya motsa da mugunta."

Lieutenant ne yace "Yanzu Ammar d'aure yarinyar nan kayi kamar wata dabba, me tayi maka to?"

Yana cikin rufe mota ya nufi b'angaren su yana fad'in "Bata jin magana."

Cikin b'acin rai lieutenant yace "Kai maganar kake ji? D'an iska kawai yarinya bata maka komai ba ka kamata ka d'aure."

Juyowa Ammar yayi ya kalleshi, juyawa yayi ya ci gaba da tafiyarshi haka suma, ana shiga falo Hajia tace "Wai ina shalele na? Ance tare muke amma har yanzu ban ganshi ba."

Umaima ce ta tab'e baki a ranta tace "Mu da ba shalelenki ba ma dai gamu ko ba'a san ganinmu."

Sai lokacin sukayi ido hud'u da Amar, ai kuwa sakin jakarta tayi ta zaburo ta daddafe fuskarshi tana tambayar "Shalele lafiya? Meya sameka a fuska haka? Ba dai hatsari kayi ba kuma shine babu wanda ya fad'a min."

Cikin halin ko in kula yace mata "Eh, ba wani babban abu bane, karki d'aga hankalinki."

Hamna ce tace "Amma yaya Amar na d'auka cewa akayi fad'a kukayi kai da yaya Ammar."

Da sauri kusan kowa ya kalleta inda Amar har saida yaji kamar ya mareta, Hajia ma kafeta tayi da ido tace "Fad'a kuma? Waya fad'a miki?"

Yanda duk taga wasu na kallonta ne yasa tayi shiru, cikin zaro ido Hajia tace "Ba dake nake magana ba kina ji na kinyi shiru."

Cikin duburburcewa tace "A'a Hajia nima ban sani ba, jiya dai naji su aunty suna fad'in ko sunyi fad'a ne lokacin da zasu tafiya, amma bansan meya faru ba, mu bamu ma gidan a lokacin."

Lieutenant ne ya kalli Amar yace "Amma ai jiya ba haka kuka fad'a mana ba, ka ce hatsari kayi da moto."

Hajia ce ta mishi wata tsawa kamar k'aramin yaro tace "Rufe min baki malam, dama ko kun sani wace tsiyar zaku tsinana, duk ba ku kuke d'aure mishi gindin ba."

Amar ta kalla tace "Shalele da gaske ne abinda ta fad'a?"

Ba tare daya had'a ido da ita ba yace "Ba gaskiya bane, ni banyi fad'a da shi ba."

Wani murmushin yak'e Hajia tayi tace "Shalele kasan dai zansan abinda ya faru ko? Ka fad'a min ko kuma na tambayi wanda zai fad'a min komai daya faru."

Cike da k'aguwa yace "Hajia ba komai fa, dan Allah abar maganar."

Juyawa yayi da nufin komawa d'akin shi yace "Ni zan shiga ciki." Da kallo kawai ta bishi har ya fita daga falon, nan kowa ma ya nufi na shi d'aki dan huta gajiya.

Lieutenant na shiga wanka yayi ya sake sabon shiri ya fito, kai tsaye wajen aje motoci ya nufa wanda ke sank'ame da motoci kamar na siyarwa, dan akwai motoci a wurin kusan guda bakwai, a hankan ma dan babu ta colonel sannan Jamil ma moto ne da shi, haka su Hamna ma duk da kuwa akwai halin da zasu hau motar suma, katari akayi Zeituna na share wurin saboda 'ya'yan bishiyoyin dake zuba suna yawon b'ata wurin, duk'e take kusa da motarshi da tsintsiya tana shararta da kuzari kamar yanda ta saba, duk da ba motsin mutum taji ba amma k'amshin turarenshi ya sanar da ita yana tahowa, tana d'agowa ashe ma harya k'araso kusa da ita zai bud'a motarshi, idonsu ne suka had'u wanda hakan ya haifar mata da shiga wani yanayi na shauk'i, shi kuma yana kallonta kai tsaye yayi k'asa da idonshi wanda cikin akasi suka sauka kan k'irjin dake pam-pam a gabanta kamar mai jaririn ciki, gashi dai budurwa har budurwa amma datti ya b'oye hallitunta, yatsina fuska yayi saboda kallon tsaf daya mata, hijabinta kalar ruwan toka ne amma tsabar daud'a har yayi wani duhu, k'afafun nan nata fari k'al da su kamar na mai d'aukar kanwa amma fa daga ciki bak'i k'irin yake, kallon fuskarta ya sakeyi wacce ke fitar da zufa daga goshinta zuwa saman hanci, gashi zufar har cikin kanta zufa yake har tana gangarowa a fuskar, da sauri ya d'auke idonshi ya mayar kan mota ya bud'e zai shiga, cikin ladabi ta sunkuya tace "Abban Ammar a dawo lafiya, Allah ya tsare."

Fuskarshi ba yabo ba fallasa ya amsa da "Allah yasa."

Tayar da motar yayi tana kallonshi ta kasa ci gaba da aikinta har yayi baya baya ya saita motar daidai k'ofar fita, mai gadi ne ya bud'e masa ya fita duk tana kallo kafin ta ci gaba da shararta.

Ashe duk kallon nan da take masa yana hangenta ta madubin motar, saida ya fita yake tunanin wannan kallon duk na miye haka? Ita bata san ba kowa ke son yawon kallo ba? K'aramin tsaki yayi tare da sakin tunanin Zeituna, wayarshi ya d'auka da nufin kiran Ummyn yan biyu saboda ta kira shi yana wanka, kuma yasan ta kira ne taji sun iso lafiya, yana dannawa lambar ta ta ido sai kawai hoton Zeituna da k'irjin ta ya dawo mishi a ido, muryar Ummy ce ta dawo da shi hayyacinshi ya amsa mata sallamar data masa.

*Bayan fitar Zeituna*

Kawu Mamu na zaune k'ofar gida da redionshi yana saurare wannan mutumin ya zo ya paka mota, fitowa yayi cikin wata arniyar shadda wacce tasa kawu Mamu sanin tabbas babban mai kud'i ne, gaisawa sukayi yace mishi "Baba dama wurinka na zo."

Saida ya nuna kanshi yace "Wuri na kuma Alhaji, Allah yasa dai lafiya ko ba wani laifin mukayi ba."

Murmushi yayi yace "Babu laifin daka aikata Baba, alkairi ne ke tafe dani."

Murmushi ya saki ya mishi izini ya zauna kan tabarmar kusa da shi, ya mik'e yace "Bara na kawo maka ruwa Alhaji."

Da sauri ya katse shi da cewa "A'a Baba ka barshi, ai babu k'ishin ruwa a tare dani."

Zaune yayi suka sake gaisawa kafin yace "Baba ni dai sunana *Jano*, kuma ni d'an kasuwa ne, a garin nan nake da zama, daren jiya ina kan hanyata ta zuwa gida a kan motona saina had'u da wata budurwa, sanin ba zata tsaya ta sauraren ni ba yasa bai tsayar da ita ba, amma a hankali na dinga biyo bayanta naga ta shiga gidan nan."

Ya fad'a yana nuna gidan da suke fuskarta ya ci gaba da cewa "To a gaskiya yarinyar ta kwanta min, ina sonta idan har ka amince da hakan."

Kallonshi kawu Mamu yayi yace "Janna ka ke ko?"

Murmushi yayi yace "A'a Jano ne Baba."

Sake kallonshi yayi yace "Amma dai sunan nan bana musulmi bane ko."

Ba fargaba yace "Eh Baba, ni ba musulmi bane, jimawa a cikin musulmi da kuma zama tare da hausawa yasa ba'a iya tantance gaskiyar waye ni, amma ni asalina ma d'an bagwari ne."

Gyara zama yayi yace "Wannan ai ba wani abu bane, gaka 'yarmu ka ce kana so kuma mun baka har abada."

Kallonshi Jano yayi yace "A'a Baba, bana har abada nake buk'atar ta ba, zan fad'a maka gaskiyar abinda nake so daga jikin yarinyar."

πŸ€” _Ba aure ya kawoka ba dama?_

*Mu had'e a pegi (page) na gaba insha Allah.*
29/05/2020 Γ  16:33 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*SANIN MASOYI*
_(sai Allah)_
*BAYA DA K'URA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ’ž _*MASOYA NA*_πŸ’•

_KUNA CIKIN RAINA_

*Raheenat M. Abbakar*
_(My Heenat)_
*Jameela AHK*
_(My Meelat)_
*Ma chΓ©rie Hakeema*
_(Mom Teema)_
*Momyn Dady*
*Maman Labyb*
*My Hawwer*
*Aunty Hawwer*
*Ummi&Ummi*
_(Lil sister's)_
*Nazeefa*
_(My k'awa)_
*Sis Chappa*

πŸ‡³πŸ‡ͺ *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_5_

Bud'ar bakin tsohon sarki cewa yayi "Allah da na shi iko, Imran ai dama ya kamata ka k'ara auren ko dan matsayin da kake da shi, sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba."

Cikin nutsuwa Imran ke kallonshi yana kuma sauraro, d'orawa yayi da "Shekarun baya da suka shud'e nayi magana daga ni sai liman akan ina son ya baka auren 'yarsa *Saratu*, amma lokacin daka kawo wacce kake so kuma za'a maka nad'i sai kawai muka bar maganar, a k'a'idata kai ka sani bana sab'a maganata, dan haka har yanzu nake son cika wannan alk'awarin dana yi tsakani na da liman wanda Allah ne shaida."

Sunkuyar da kai Imran yayi yana jiran umarnin mahaifin na shi, ci gaba yayi da fad'in "Ka cika min burin nan nawa Imarn ta hanyar had'a zuri'a data liman, tun yaya na (mahaifin Sameera) yana mulki suke tare da shi, amintaccenshi ne, ni ma kuma banda amintacce sama da shi, mutum ne mai rik'on sirri da amana, baya duba matsayinka ko kuma muk'aminka, idan har kayi ba daidai ba take zai sanar da kai ba tare da shakku ba, babu tsoro ko shakkar wani mahaluki a tare da shi inba ubangijin daya halliceshi ba, yaranshi sun samu tarbiya wacce nake da yak'inin zakayi alfahari da auren tsatsonsa."

Cike da gamsuwa da bayanin mahaifinshi ya d'ago yace "Mahaifi na wannan hallayar liman ce, dan haka a shirye nake da na bi umarninka."

Cikin jin dad'i yayi murmushi yace "Alhamdulillah, ita Saratu yanzu tana gidan mijinta har da ma yaranta, amma akwai k'anwarta wacce akayi wa saukar hardar Qur'ani mai girma satin daya wuce, a lokacin kana k'asar *Paris* shiyasa ma baka samu halartar taron ba, sunan yarinyar *Safiyya*, na yarda da tarbiyarta saboda nasan mahaifiyarta, idan har ka amince da zab'in nan to zanyi magana da liman, amma ka sani, kai ba k'aramin mutum bane da za'a tsaya b'ata lokaci ba."

Cikin girmamawa yace "Na amince mahaifina, duk abinda ka zab'a min yana zama alkairi a gare ni, zanyi biyayya ga wannan auren na kuma rik'e yarinyar da daraja fiye da yanda zan kula da kai na."

Da haka suka gama tattaunawarsu ya taso ya fito, fadawa biyun ne suka rufa mishi baya izuwa komawa b'angaren shi, yana zuwa ya shiga suka sake tsare bakin k'ofar, d'aya bafaden ne ya kalli d'an uwanshi yace "Zan d'an kewaya, ina zuwa yanzun nan."

Da kai kawai ya masa alamar toh kafin ya wuce ya zagaya ta baya, saida ya tabbatar babu mai ganinshi kafin ya sulale ya nufi b'angaren uwar d'aki, cikin sauk'i ya had'u da wata baiwar ta fito daga falonta da wani abu mai kama da k'warya da kayan marmari a ciki, nan ya fad'a mata yana son ganin uwar d'aki, bata b'ata mishi lokaci ba ta juya ta koma ciki ta fad'awa uwar d'akin sak'on dake tafe da ita, tana kishingid'e jakadiyarta na gefe tana matsala mata k'afafu sai lumshe ido take tace "Ki shigo da shi."

Mik'ewa tayi cikin ladabi ta nufi k'ofa, a hankali ta bud'a ido ta kalli jakadiyar tace "Ki jira mu a waje, karki bari kowa ya shigo har sai *Kullu* ya fita."

Cikin girmamawa da kirari ta mik'e ta fita ta zauna falo shi kuma ya shigo, har saida ya samu wuri ya durk'usa ya gaisheta tare da mata kirarin matar sarki uwar sarki kuma kakar sarki insha Allahu kafin cike da isa da k'asaita tace "Kullu meke tafe da kai a daren nan? Baka san mutanen gidan nan zasu iya saka mana ido ba?"

K'ara sunkuyawa yayi yace "Tuba nake ranki shi dad'e, akwai abinda ke shirin faruwa ne a gidan nan da na ga ya kamata ace kinyi gaggawar saninshi."

A hankali tace "Me yake faruwa?"

"Ranki shi dad'e yanzu haka daga wajen takawa muke tare da mai martaba, sun tattauna sosai, kuma ba akan komai ba sai akan maganar auren mai martaba, takawa yace zaiyi magana da liman kan ya bawa mai martaba auren 'yarsa Safiyya, ya kuma ce ba za'a d'auki lokaci ba."

Da sauri ta tashi zaune ta fito da idonta wanda ada take k'ank'ancesu tace "Kuma mai martabar ya amince?"

Sake sunkuyawa yayi yace "Ranki shi dad'e sanin kanki ne da wuya takawa ya umarci mai martaba abu kuma ya tsallake baiyi shi ba, sai dai in takawa ne ya janye umarninshi."

A harzuk'e tace "Idan kuma bai janye ba fa?"

Cikin ladabi yace " Aure zai tabbata ba fashi, tuba nake ranki shi dad'e, Allah ya ja zamaninki, kinyi taki kinyi ta rago."

Da k'arfi ta katseshi da fad'in "Ya isa, je ka kawai, ka ci gaba da saka min ido akan duk wani motsin mai martaba, kafin nan zanji da wannan al'amarin."

Saida ya mata kirari ya fita daga d'akin ya sake zagayawa ya koma wajen aikinshi, yana fita ta d'auki wayarta ta mik'e tsaye tana dannawa waziri kira, har saida kiran ya tsinke ta sake kira na biyu kafin ya d'auka, cikin hargagi tace "Duk abinda kake gobe ka zo ka same ni zamuyi magana."

Cikin girmamawa yace "Uwar d'aki lafiya? Meya faru ne?"

"Akwai babbar matsala nake fad'a maka, kawai ka zo ka same ni gobe da safe, kuma bana so ka bari wani ya ga lokacin da zaka shigo nan."

"Angama ranki shi dad'e, Allah ya kaimu gobe da safen."

Datse kiran kawai tayi ba tace komai ba, jakadiya da ita ma ko da Kullu ya shigo ta biyo bayanshi ta lab'e tana saurarensu, tsaf ita ma ta kwashe komai da suka fad'a ta shirya fad'awa d'aya daga cikin kishiyoyin uwar d'aki mai sunan *Hannatu*.

Ta k'ofar da babu mai shigowa sai ita kad'ai tasa makulli ta shigo cikin shigar alfarma ta alkyabba, babu kowa falo kai tsaye tukarar ta wuce ta k'wank'wasa k'ofar, sarki Imran da a lokacin yake kwance kan makeken gadonshi na alfarma yana kallon sama, tunani yake akan abinda ke tunkaro shi, yanda zai fara fad'awa sarauniya Ameera yake tunani, k'wank'wasa k'ofar ne yasa ya kalli k'ofar har saida gabanshi ya d'an fad'i, dan yasan ita ce ta zo, umarnin shiga ya bata ta bud'a ta shigo, zaune ya tashi za zuro k'afarshi daya k'asa ya tankwashe d'aya akan gadon yana kallonta harta k'araso kusa da shi, cikin murmushi da girmamawa tace "Barka da warhaka gwarzona, sarkin Basraba sarkin sarakuna, buhun k'aya kake ba'a cikaka a tausa, kwalli mai sa ido shek'i, d'awisu ne kai ko a dawa namanka sai sarki, na Ameera bada kanka a sare kaje gida ka ce ya fad'i, rugum babban motsi, daji ba'a maka k'aure ko da mahaukacin kafinta, d'an sarki, jikan sarki, kuma uba ga sarkin Basraba da yardar Allah, kaga Abban *Ja'afar* da *Safna*, gaba ka bawa mak'iyanka ba baya ba, da baya ka basu da tuni sun cimma ka, na..."

Fizgota yayi ta fad'o kanshi suka fad'a saman gadon suna dariya yana fad'in "Kin gama fasa min kai na yau, ki adana sauran har gobe sarauniyata."

Kwance sukayi ya kalli fuskarta yace "Wai ina kike koyon irin wannan sai kace sarauniyar marok'a ta duniya."

Murmushi tayi tace "Tun ranar dana auri sarki na shiga makarantar koyon wasa mutum, dan ina so na dinga kod'a mijina."

Cikin jin dad'i yace "In kuwa hakane to ya kamata a k'arawa malamin nan albashi, ke kuma miki albishir dana baki kyautar alkyabbata wacce nafi ji da ita."

Dafe k'irji tayi cike da murna tace "Wow my King, godiya nake masoyina, Allah yaja zamaninka, Allah ya k'ara maka nisan kwana da lafiya." Da haka suka gudanar da darensu cikin soyayya da k'aunar juna.

*Abuja*

Rana ta hantse sosai Harira ta zo da yan kayanta, nan Sameera ta gabatar da ita wajen sauran ma'aikatan gidan da kuma Ammie, d'akunan yaran ta nuna mata inda zata dinga kula da shi, fitowa tayi ta barota a d'akin Khalifa da Diya'u tace zata gyara musu duk da Sameera tace ta bari harta huta, tana fita ta juya ta kalli d'akin da kyau, tab'e baki tayi tace "Humm! Sameera kenan, wato yanzu nan ke duk zaman da mukayi tare dake amma ki rasa sakayyar da zaki min sai had'a ni da aikin kula da d'akin yaranki? Ba damuwa, da sannu nima sai nayi iya k'ok'ari na wajen ganin na shigo gidan nan a matsayin kishiyarki, wallahi daga lokacin zata k'are miki."

πŸ™„πŸ€” *Da abinda kika shigo kenan? To takwara aiki ya samemu ashe, su Harira nasan sai dai in wajensu lamma za'a fara durk'usawa.*

Sameera wajen Ammie ta koma ta nemi alfarmar tayi shiru da bakinta kar Abbanta ya sani, dan inhar yasan wacece Harira to akwai matsala, alk'awari Ammie ta mata na ba zai ji ba.

*BASRABA*

Da sassafe Waziri ya shigo b'angaren uwar d'aki bayan ya tabbatar babu wanda ya ga shigarshi, waya na ga ta ya fiddo a aljihu ya danna camera ya saita wayar a jikin k'ofa ya tangaleta a bayan murfin k'ofar, saida ya kalla ya ga tana hasko mishi inda yake da tabbacin nan uwar d'aki zata zauna sannan yayi murmushi ya shigo, jakadiya na mishi iso ta bar part d'in zuwa na Hannatu dan kai mata tsegumi, a falon uwar d'aki ya zauna yana kallonta fuska a had'e, cikin ladabi yace " Hushi bai dace da uwar sarki ba, uwar d'aki ko zan iya sanin meke faruwa?"

Kallonshi tayi tace "Waziri da matsala babba, takawa yana so ya kaini bango har yasa nayi abinda banyi niyya ba."

Yana d'an kallonta yace "Ranki shi dad'e lafiya? Me takawa yayi kuma yanzun?"

Cikin hushi tace "Na samu labarin takawa yana son had'a sarki aure da yar gidan liman, ni kuma ba zan lamunta ba dan ita ma yarinyar bana k'aunar ta kamar yanda bana k'aunar matarshi Ameera, shiyasa na ce ka zo dan musan abinyi tun wuri kafin lokaci ya k'ure mana."

Fuskarshi a had'e shima ya kalleta yace "Yar liman kuma? Amma meyasa takawa zaiyi mana haka?"

Shiru tayi sai kumbura da take hakan yasa yace "To shi mai martabar me yace akan lamarin?"

A d'an fad'a ta kalleshi tace "Me kuwa zai ce? Ai kafi kowa sanin sarki Imran baya tab'a kaucewa umarnin mahaifinshi, ya amince d'ari bisa d'ari zai aureta, kuma ina tabbatar maka inhar liman da takawa suka had'u yau har suka tattauna, to babu shakka auren sarki da yar liman zai zauna daram, dan ba zasu tab'a jan al'amarin da tsayi ba."

Tashin hankali ne k'arara ya bayyana a fuskarshi, shi kad'ai yasan irin k'aunar da yake yiwa mulkin garin basraba, dole sai 'yarshi ta shigo gidan zai cika burinshi, dan haka a shirye yake da yayi komai akan duk wani mai son shiga tsakaninshi da mulkin nan, d'an b'alle botir d'in rigashi yayi da yake jin ya shak'eshi sosai kafin yace "To idan har aurensu ya tabbata ya zamuyi?"

A harzuk'e tace "Ba mai zai tabbata ba, kawai kayi wani abu a kai."

Wani kallo ya mata mai fassara da dama yace "Kamar me kenan uwar d'aki?"

A tsanake ta kalleshi tace "A matsayinka na namiji baka san me zakayi ba da zai hana auren nan? Sai ni ce kake so na samo maka mafita? Bayan kuma 'yarka ce zata shigo gidan, nifa babu wata riba da zan ci, kawai waccen tsinanniyar matar ta shi ce bana son ganinta ita kad'ai a cikin gidan nan."

Ajiyar zuciya ya sauke ya kalleta yace "Zanyi duk abinda ya dace a matsayina na namiji, amma ki ban izinin yin komai."

Ba tare da tunanin komai ba tace "Kawai ka je kayi koma meye banda matsala da hakan, auren ne kawai bana so ya tabbata."

Murmushin gefen labb'a yayi yace "An gama ranki shi dad'e, za ayi

Please Login or Register in order to submit comment