Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hajia Ramma ta aurar da yaranta mata, aurensu kamar samun wani kasone daga 'yancin Saratu da 'ya'yanta, dan dama da suna gidan har wankin kayansu su keyi, duk wani abu da zaisa su motsa jiki to saidai susa su musu, dan haka wahalarsu ta ragu da sukayi aure.

Shekaru sun kuma ja dayawa amma su Hassana har yanzu babu ma-nemin aure, hakan ya fara damun Saratu fiye da zato ta yanda har ta kan zubar da hawaye idan ta gansu masha Allah sunata yawo a tsakar gida, sai dai bata san meye matsalar ba kuma, wannan ne yasa wata rana wata mak'wabciyarsu mai sunan *Delu* suna daka a tsakar gidan saboda Ramma bata nan take fad'a mata ta tashi tsaye akan yaranta, dan ko shakka babu akwai sihiri a jikinsu daya hana su aure, bud'ar bakin Saratu cewa tayi "To yanzu Delu meye abunyi? Wallahi lamarin yaran yana damuna sosai, kawai dan banda abokin shawara ne."

Da sauri Delu tace "Haba ke kuwa Saratu, ai mun zama d'aya, damuwarki damuwata ce, akwai abunyi kam in zaki yarda."

Cike da damuwa tace "Zan yarda mana Delu, idan ban samu mafita ba zan saka yaran a gabane na dinga gatsarsu ina ci? Kawai ki fad'a min kedai."

"Yawwa Sarai, kina ji ko." Ta fad'a tana yin k'asa da muryarta ta ci gaba da cewa "Akwai wani malami dana sani can bayan gidan sarki idan kin gangara tudun nan, wallahi yana bada taimako sosai dan aikinshi kamar yankar wuk'a ne, to ina tabbatar miki da zaki same shi da matsalarki wallahi zata zama tarihi."

Jim ta d'anyi kafin tace "Da gaske Delu? To amma ai matsalar ita ce ni ba komai gareni ba kinsani kema, ko abinci mai kyau ba samunshi muke a gidan nan ba, to taya zan samu kud'in da zan bayar a matsayin sadakar aikin da za'a mana?"

Dafa kafad'ar ta tayi tace "Haba Saratu, ni da ke fa yanzu mun zama d'aya, idan da ba zan taimaka miki ba aida ba zan fara fad'a miki maganar malamin nan ba ma, dan haka ki kwantar da hankalinki, insha Allahu zan rakaku idan kun tashi tafiya, kuma ni nan zan sayar da d'aya daga cikin awakina dan ganin yaran nan sun samu mijin aure."

Cikin farin ciki Saratu tace "Da gaske Delu? Kai amma naji dad'i da wannan taimakon da kika mana, Allah ya biyaki da gidan aljanna."

"Ameen." Ta fad'a tana d'aga tab'aryarta sama suka ci gaba da daka, suna haka Ramma ta shigo gidan, saida ta k'are musu kallo kafin tace "Yanzu dan na fita daga gidan shine har da min gayyar tsiya a gidan nan, to yayi kyau bari Alhaji ya dawo gidan sai ki fad'a mi shi abinda matar nan take yi, dan na tabbatar gulma kukeyi tunda ai bata zuwa gidan idan ina nan."

Durk'usawa Sarai tayi har k'asa tana fad'in "Dan Allah Hajia kiyi hak'uri na tuba, wallahi ba zamu sake ba daga yau kiyi hak'uri ki min rai."

Delu ce tace "Kinga Saratu tashi, ni zan tafi kar na ja miki matsala ba da niyyar haka na shigo ba, amma dai ya kamata ki rage tsoron nan tunda miji ba shi ya hallice ki ba."

Da kallo kawai Sarai ta bita a zuciyarta kuma tana fad'in "Dan baki san bala'in shi bane Delu akan matar nan tashi, ke dai Allah ya mana tsari da irinsu Hajia kawai."

Dan kuwa tasan inhar ta fad'a mishi to fa ya mata k'aramin hukunci shine ya mata dukan tsiya bayan idon 'ya'yansu, shine ya mata gata kenan, masifa Ramma ta ci gaba da yi ai kawai munafurci ne ya kawo Delu tunda bata cika zuwa gidan ba musamman ma idan tana gidan, Husseina da Husseina suna d'akin Ramma d'aya na gyaran d'akin d'aya na shara, suma tana shiga ta balbalesu akan basu gama gyaran ba tun lokacin data bar gidan, nan fa ta had'e su ta zage son ranta, da magrib Sarai da 'yan biyu suna zaune a d'akin su sai fitar k'wai (aci balbal) dake bayar da haske, Sarari ce ta lek'o a hankali tsakar gidan taga babu kowa, dawowa tayi ta kalli Hassana tace "Husseina, kinga yi sauri kafin Babanku ya shigo ki tambayo min Delu ki ce nace yaushe ne tafiyar nan, idan ta fad'a miki sai ki ce nace ni ba zanje ba amma ku zaku tafi tare da ita."

"To." Kawai Husseina ta fad'a ta tashi ta fita tana waiwayen d'akin Ramma, tana fita Alhaji Hassan kuma ya danno kai cikin gidan, kamar kullum kai tsaye d'akin Ramma ya nufa, tana jin motsinshi ta fashe da kukan makurci, nan fa hankalinshi ya gama watsewa Ramma na kuka, bai samu nutsuwa ba har saida yaga tayi shiru ta fara zayyana masa abinda ya faru kamar haka "Gaskiya Alhaji na gaji, na gaji da irin cin mutumcin da Sarai ke min a gidan nan, wai daga nasa k'afa na fita shikenan saina tarar da Sarai da Delu a gidan nan sunata cin nama na, a k'arshe ma dana musu magana kar ka so kaga rashin mutumcin da suka min ba, da nace kuma idan ka zo zan fad'a maka dan ka shiga tsakani na da ita, amma wai sai Sarai ta bud'a baki tace ai kai miji ne kawai ba ubangiji ba, dan haka baka da wuta ko aljannar da zaka sakata, dan haka ni kawai ka rama min cin mutumcin da ta min gaban k'awar ta."

Wani huci yayi yace "Yanzu dama akan Saratu ne kike kuka haka? Me ya sa zaki tsaya ki bawa kanki wahala? Naga ai kina da damar dake kanki zaki hukunta ta ko bana nan, amma ba komai zata gae kurenta, wallahi zata san ta tab'a ki a gidan nan, yau zanga waya d'aure mata gindi a garin nan."

Fitowa yayi daga d'akin ta biyo bayanshi tana ci gaba da rera kukan iskanci, shi kam d'akin shi ya shiga ya d'auko bulalar fata ya nufi d'akin Saratu da ita, suna zaune ita da Husseina saiko ya fad'o d'akin kamar an turo shi yana fad'in "Ina kike marar mutumci, har ni zaki wa fitsara a gida."

Bai tsaya komai ba ya rufeta da duka da wannan bulalar, kamar yanda ta fad'awa yaran cewa babu ruwansu duk abinda suka ga mahaifinsu na mata, wannan dalilin ne ya tilastawa Hassana mik'ewa ta fito daga d'akin tana zubarda hawaye, karo ta ci da Ramma dake shirin shiga d'akin wanda yasa kafad'ar su ta had'u, kashe Hassana tayi da mari tana fad'in "Dan ubanki ni zaki bige? Ai bani nake dukan uwar taki ba, ubanki ne gashi nan idan zaki rama mata ne."

D'auke hannunta tayi daga kunci ta rab'ata zata wuce Ramma ta sake cewa "Koda yake ma ai ba 'yan halak ta haifa ba shiyasa babu mai jin zafin abinda ake mata duk cikinku."

Daf da k'ofar shigowa gidan ta tsaya tana kuka, cikin sand'a Husseina ta shigo dan kar kowa ya ji shigowarta, amma tana dosowa taji ihun mahaifiyar ta da gudu ta banko kai tana shirin zarcewa d'akin, da k'arfi Hassana ta rik'e ta gam tana fad'in "A'a Husseina, kinsan fa abinda Iyya ta fad'a mana, dan Allah ki barsu."

Fizgewa tayi cikin zafin rai tana fad'in "Dallah malama ni sake ni, haka kawai muna ji muna gani saiya kashe mana uwa bayan ba wata tsiya yake tsinana mana ba."

Sosai ta sake rik'e ta tace "To me zamuyi? Idan kin shiga zaki rama mata ne? Ko kuma zaki masa magana ne yaji? Kawai ki barshi idan ya gaji da dukanta ai zai dakata."

Cikin b'acin rai da tafasar zuciya ta zauna k'asa dab'as ta fashe da kuka ita ma, kuma har lokacin Hassan bai daina dukanta ba har ta kai tayi shiru, suna haka cirko cirko suka ga ya fito daga d'akin yana ta bambami, Husseina kam da harara ta bishi ta mik'e suka shiga d'akin da gudu, zaune suka sameta rakub'e da bango sai shashek'a da take yi, kamar yanda suka saba Hassana ce ta rulgumota tana jijjigata tana fad'in "Kiyi hak'uri Iyya, kiyi hak'uri dan Allah komai zai zama tarihi wata rana."

Suna haka kuma Suley ya shigo da sallama d'akin jiki a matuk'ar sanyaye sai ledar dake hannunshi, Hassana kad'ai ta amsa mishi kafin ya zauna gefensu ya mik'awa Husseina ledar hannunshi, sai lokacin Hassana tace "Suley kana lafiya? Na ganka kamar baka lafiya?"

Ajiyar zuciya ya sauke ya kalleta yace "Lafiya ta lau Hassana, na zo zan shigo ciki na ji hayaniya da sautin Iyya, shiyasa ban shigo ba tunda banga abinda zan iya yi ba."

Husseina ce ta kalle shi tace "Wai har kaima dake namiji baka tab'a ji a zuciyarka ba kana so ka d'auki tsohon nan ka nunawa sama shi sannan ka sauke k'eyar shi k'asa? Gaskiya ni na fara gajiya."

Kallonta yayi zaiyi magana Saratu ta mik'e saboda tuna abinda ya fad'a mata da zai fita cewa ta kai mi shi abincin shi yanzun nan, ganin ta fita ta bar musu d'akin yasa sukayi shiru kawai.

Sai bayan kwana biyu Delu ta shirya tare da su Hassana suka tafi wajen malamin nan, shima kuma aradu Saratu ta tara da kai domin ba barinsu ake suna fita ba, haka Delu ta tafi dasu wajen malam Rabi'u, sam a ranta babu mummunan nufi sai na son taimaka musu, amma sai gashi tunda malamin ya d'ora idonshi akan Husseina sai yawunshi ya tsinke, ta wani fannin ya fad'a musu gaskiya kam da yace asiri ne aka musu dan kar suyi aure, ta wani b'angare kuma b'atar da su yayi da yace akwai maganin da zai bayar suyi aiki da shi amma dole Husseina ce zata dawo gobe ta karb'a, ba musu suka juyo suka dawo gidan, yau ma Hassana da Husseina shegen duka suka sha wajen Babansu saboda fitar da sukayi, amma hakan bai hanata komawa ba washe gari da magriba kamar yanda sukayi da malam, wannan zuwan kuma shine ya wargaza duk wani tanadi da tattali data jima tanawa kanta, duk yanda ta so bijere masa bai bata dama ba saboda ya nuna mata k'arfi, kuma tun farko ya riga daya ci galaba a kanta, a wannan zuwan ne malam rabi'u ya rabata da mutumcinta ta hanyar yin kaca-kaca da shi.

Da k'yar ta kawo kanta gida tana kuka, amma kuma sai ta k'i yarda Saratu tasan abinda ya faru sai yar uwarta kad'ai abokiyar shawararta ta fad'a ma, Hassana ma ta shiga damuwa har ta kusa ta fita tashin hankali, amma haka suka dinga b'oyewa har lokaci ya dinga gangarawa, cikin hukuncin ubangiji kuma sai Allah ya fito musu da maza, d'aya d'an abokin Babansu ne yace yana son Hassana, sai wani mai mata biyu dake nan unguwarsu yace a bashi auren Husseina, dama mahaifinsu ya gaji dasu kamar yanda yake fad'a, dan haka ba'a d'auki lokaci ba aka d'aura musu aure kowace ta shiga d'akin aurenta.

_K'alubalen har yanzu bai fara ba, yayin da *BADAK'ALAR* yanzu ne zata soma._



๐Ÿ˜ *See u guy's*๐Ÿ˜
05/06/2020 ร  20:36 - Ummulkhairi: ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
*BADAK'ALA*
๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ

*Labarin gaske*


*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*


๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ _*AHALI NA*_๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_12_


Zaha ta d'an shawarci mai gidan nata cewa ya za ayi aure haka kawai basu san waye shi ba, sannan ka d'auki 'ya ka bashi a sadaka, sanin dama sai anyi wannan cecekucen yasa yace shi zai yi wa 'yarshi duk wani abu da akewa kowace yar gata, haka lokacin ya ya fara tafiya dama kuma ba wani lokaci bane mai tsayi, har lokacin Zeeya da suley basu had'u ba dan k'iyayyarshi ce zalla a zuciyarta, shi kuma bai ma san ainihin me yake ji a game da ita ba, ana haka juma'a ta zo kuma aka d'aura aure, inda Alghabit ya wa suley wakilci liman kuma ya wa Zeeya, sadaki mafi girma da daraja ya biya wanda sai wane da wane, duk wata al'ada saida akayi ba'a bar komai ba, kafin nan amarya ta tare ita da halinta.

Zaman *doya* da *manja* suka fara, Zeeya dai banda gori da rashin kunya babu abinda take wa Suley, kullum ita ce fad'in bashi da kowa bashi da komai, da dukiyar ubanta yake duk wani abu na rayuwa, tunda sukayi aure basu kwana d'aki d'aya ba, dan lokacin shigowarshi nayi zata rufe na ta d'akin, abunci kam dama iya bakinta take dafawa, Suley yasha wahalar Zeeya fiye da tunanin mai karatu.

Ni kaina da ana bani labari na yaba da hak'urin shi, dan kad'an daga iskancin Zeeya yana iya d'iban ruwan wanka ta zubar da gangan ko kuma ta zuba wasu ruwan masu datti a ciki, ko kuma ta d'ibi k'asa ta zuba, ya kan shiga wanka ya rataya kayanshi a katanga da gangan ta d'auke kayan ta musu shark'af da ruwa, ankai matakin da saida Zeeya ta d'auki kayan Suley masu kyau wanda yake fita da shi tasa sabuwar wuk'a ta yagasu, Zeeya na iya ganin Suley zaune yana alwala ta d'auki sharar iskanci ta dinga bad'a mishi k'ura a jiki, wallahi wallahi yanda mai bani labarin ta fad'a min tace duk wannan iskancin idan tayi sai dai ya kalleta ya girgiza kai yace "Allah ya kyauta, ya ganar da ke gaskiya."

*Bayan wata d'aya* ya shirya tafiya gida dan ganin me ake ciki tunda yanzu Allah ya hore mishi kud'in mota harda ma na guzuri da tsaraba, haka ya sa kai ya tafi Zeeya bata damu ba dan dama nesa take so suyi da juna, bayan yaje ne ya samu labarin rasuwar mahaifiyarshi da ita kad'ai ta rage mi shi, hakan yasa shi dasa nashi kukan harya gode Allah, abin duniya ne ya taru ya mishi yawa, ga rashin uwa ga rashin sanin inda Husseina take, dan har yanzu babu wanda yace ya ganta da idon shi, haka Hassana ta bashi labarin rabon gadon da akayi tare da nuna masa yan dabbobin da aka basu, hakan ya b'ata mi shi rai sosai ta yanda har ya fara ikrarin cewa sai an sake wannan rabon gadon, dan son zuciya yayi yawa cikin wanda akayi, kuka sosai Hassana ta dinga yi tace yayi hak'uri kawai ya share ya barwa Allah, tunda gashi a cikin watannin da basu kai shekara ba har sun had'a garke, haka ya hak'ura badan ya so ba ita kuma tasan ko yanzu sai wani abun ya faru idan yayi maganar, haka ya shirya sake komawa wajen iyalinshi cike da burin son zama a mahaifarshi, sai dai abu d'aya ba zai yiwu lokaci d'aya haka yace zai dawo da Zeeya garin nan ba a yanda take, dan haka ya shirya ya shirya ya tafi ya kuma ce Hassana ta ci gaba da saka ido wajen neman yer uwarsu, idan an samu labari to taje kasuwa ta samu fatake dake yawon fatauci har zuwa Agadez ta bayar da sak'o za'a sanar da shi, sannan ta ci gaba da kula da duka gadon na su, haka ya koma ya samu Zeeya suka d'ora daga inda aka tsaya.

*Wata shida* suka d'auka a haka kafin ta fara kunno masa wutar saiya saketa, ita a dole ta gaji da zama da shi saiya saketa, shi kuma ya fad'a mata abinda ba zai iya ba kenan saboda darajar mahaifinta a wurinshi, duk dan tasa ya saketa saita fara fita barkatai ba tare da saninshi ba, idan ta fita har ta kan iya kai dare bata dawo ba, idan ya tambaye ta daga ina kike sai dai tace "Daga wajen wanda zuciya ta ke so, idan kuma kana da zuciya ka sakeni tun kafin na kawo maka cikin da baka da iko a kan shi."

Girgiza kai kawai yake yace "Allah ya kyauta, ya ganar dake gaskiya."

"Ya dai ganar da kai, dan kaine ke k'in gaskiya kake rufe ido ma idan ka ganta, na fad'a maka ya fi yawan gashin rak'umi cewa vana sonka, amma ka k'i rabuwa da ni na huta kaima ka huta."

Haka abubuwa ke tafiya ba dad'in yau bare na gobe, kuma duk fitar da take babu inda take zuwa, daga gidan 'yan uwa sai abokai, duk da bata da ilimin addini da kuma sanin yakamata, amma tasan zina da aure babban bala'i ne, shiyasa bata sake zina ba tunda sukayi aure, ana hakane har ranar dai ta ji tana buk'atar kusanci da namiji, tun safiyar ranar Suley ya ga banbanci, daga yanda take lumshe ido tana kallonshi, murya k'asa k'asa cikin wani irin yanayi, rigar dake jikinta ta matseta sosai ta fito mata da komai, haka shi dai ya fice ya barta dan baisan me hakan ke nufi ba baima fahimci meye damuwar ba, yana fita taji haushi sosai inda tasa hannunta tana ta shafar k'irjin ta da take jin yana mata k'yaik'ayi, haka ta wuni ba kuzari har lokacin dawowar Suley, dole ta yanke shawarar tunkararshi da kanta, ya dawo kamar yanda ya saba ya shiga wanka bayan ya aje kayanshi inda ba zata iya gani ba bare ta d'auka, tsaf ya gama ya saka kayanshi, saida ya fara lek'owa dan tunanin kar azo ta fara sharar nan ta rashin gaba, jin shiru yasa ya k'arasa fitowa gaba d'aya, mamakin rashin ganinta yake a tsakar gidan har yayi gaggawar shigewa d'akin shi ya maida k'ofa ya rufe, juyawar da zaiyi sai ko Zeeya zaune bakin gadonshi na k'arfe, gabanshi ne ya shiga fad'uwa ta ko ina yana kallon hannayenta kar azo da makami take, tasowa tayi ta nufo shi ta fara shafashi, ido ya zaro yana kallonta yace "Zeeya'atu kasheni zakiyi?"

Cike da salo na yan duniya tace "Kai ne dai zaka kasheni idan baka kulani ba."

Hannunshi ta kamo ta d'ora tafin hannunshi akan nononta na b'angaren dama, tana jin haka ta wani lumshe ido tare da zage rigar tayi k'asa, shi kam yana jin babu rigar da tayi shamaki saiya rufe ido yace "Sallalahu sanyi k'alau."

๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚ *Maganar fa babbace domin kuwa harkace wannan ta kakanninmu*

Sai wannan rana ce Suley yasan da wannan duniyar dake b'oye jikin kowace mace, a wannan rana ce yayi dana sanin k'in zuwa tun da wuri, musamman da Zeeya ta zage ta nuna mishi ita fa 'yar barikin gida ce, sam mantawa yayi a wannan lokacin saida ya samu nutsuwa ya tuna da hakan, ita kanta Zeeya ta yaba da namijin k'ok'arin shi, dan inhar zata fad'i gaskiya to ya zo mata yanda take burin azo mata, buk'atar ta na biya ta koma Zeeyar ta ta asali, ta sake fito da salon rashin mutumci iri iri, *sati* uku babu wani abinda ya sake shiga tsakaninsu saida Suley yaji ya kai mak'ura ba zai iya hak'ura ba ya sameta har d'akin ta ya labb'eta, amma sai cewa tayi idan har yana so ta yarda saiya siyo mata gasashen nama na bakin kasuwa, tasan tafiya ce mai nisa amma haka ya daure ya je ya kawo, duk da haka saida ta gama wainashi taga kamar zai mata kuka kafin tayi wanka ta fito ta kwanta kan gado ta wani kalleshi tace "To taho."

_Sai kace zaki bawa yaro nono._

Jiki na rawa ya haura kan gado, tashi tayi zaune cikin tsawa tace "To ni ce zan cire maka kayan?"

Saukowa ya sakeyi daga kan gado ya cire kayan zai sake haurawa tace "Kaga muje ma d'akin ka, na fasa anan d'in."

Haka yabi bayanta bawan Allah shi dai ya samu nutsuwa kawai, a d'akin nashi ma saida taji yana daf da shiga ta zabura ta tashi zaune tace "Kaga ruwa nake so nasha, duk naman nan ya tsaya min a k'irji."

"To, to bara na kawo miki." Ya fad'a yana barin d'akin bai ko da nutsuwar da zaisan babu kaya a jikinshi, da irin wannan iskancin ta dinga ja masa rai, har saida ya shiga ya fara kenan ta sake yakice shi daga jikinta tace ya isa haka ta gaji, da sauri ya durko k'asa ya rik'e k'afar ta yace "Ki wa Allah Zeeya kiyi hak'uri, wallahi ba zan iya ba, ki fad'i duk abinda kike so ni kuma zan miki shi."

Ba tausayi ta mik'e ta d'auki zaninta tayi d'aurin k'irji ta nufi k'ofar fita, wani takaici ne ya rufe shi dan tunaninshi d'aya ne akwai abinda ta mishi tun waccen ranar shiyasa yake jin haka, hannunta ya fincikota ta fad'a kan gadon ya bita ya haye, zata tureshi ya rik'e hannayen nata ya matseta d'aya hannunshi kuma ya rufe mata baki sosai yace "Wallahi duk abinda kika min sai dai ya k'are kanki, ina zamana lafiya kika tsokano ni."

Haka ya janye zanin nata ya bud'e k'afafun ta ya danna kanshi ciki, lilis ya mata dan bai tausaya mata ba ko kad'an saboda takaicinta da yake da shi, ita kanta tasan ta shiga uku a ranar, dan bata tab'a tsalmanin irin haka ba, tunda wannan abu ya faru Zeeya ta sake tsanarshi, zagin yau daban na gobe daban, duk wata mummunar kalma bata jin nauyi ko kunyar fad'a mishi ita, kullum saita mishi gorin daga ta lasa mishi zuma shine zai zama jarababbe, mugu azzalumi, macuci, wannan kalmomin kam tamkar sawar albarka ne a wurinta, tun ranshina b'aci yana tunanin ya fad'a mata shi fa yasan komai har ya kai ma baya son tona mata asirin, haka rayuwar ta ci gaba da gungura musu har lokacin da Allah ta mishi baiwar gane Zeeya na da ciki tun ita bata fahimta ba, kuma ya gane ne daga yanda kwana biyu ko kallonshi ba tayi bare tayi masifa da bala'in data saba, sai yawon tsargin yawu da take ga kuma kyawu data k'ara, duk da ta tab'a d'aukar ciki amma saita kasa ganewa da wuri cewa ciki ne da ita, yau ma kamar kwana biyu da suka gabata tana zaune k'ofar d'akinta tunda safe ya fito zai fita, kallonta yake sosai ganin kwanon d'umame a gaban ta amma ta kasa ci sai yamutsar fuska take tana tofar da yawu, karo na farko a zamanshi da ita da ya ji wani abu ya bugi zuciyarshi a game da ita tare da jin wani mugun tausayinta ya kama shi, dan a iya fahimtar da yayi mata ya fahimci tana son cin d'umamen tuwo musamman ma miyar kuka, dakewa yayi yana murmushi yace "Ni zan fita, me kike so na taho miki da shi ne? Tunda na ga baki son cin tuwon."

A zatonshi zata taso mishi ne kamar yanda ta saba cikin wannan muryarta ta data zama zazzak'a a kunnenshi, amma sai tace cikin ruwan sanyi "Ina ruwanka da matsalata to, kaje kayi abinda ke gabanka malam."

Cikin wani yanayi yace "Taya zan iya kallonki a haka baki ci komai ba, bayan kuma bake kad'ai bace."

"Ban gane bani kad'ai bace? Mu nawa ka gani anan? Kaga malam dan Allah ka fita ka bani wuri ko, wallahi na tsaneka ban son ganinka kusa da ni."

Murmushi ya mata yace "Ashe da ido na zanga ranar da Zeeya'atu take gajiya da surfa tijara, to shikenan idan na fita na siyo miki tsire sai na zo na kawo miki, dan bana barki da yunwa ba alhalin kina da juna biyu."

Yana fad'a ya sa kai ya fita, sosai ta girgiza da jin wai ciki ne da ita, ai sai ta kasa zaune ta kasa tsaye, sam tana ji ba zata iya yarda ta haihu da Suley ba, dan haka ta canza kayanta ta nufi gidansu, da shigarta mahaifinta ta fara cin karo da shi zai fita shima, da mamaki ya tambayeta "Zeeya'atu lafiya na ganki da safiya haka?"

Cike da girmamawa tace " Lafiya k'alau Baa, na zo ganinku ne dama."

"Amma a safiyar nan? Ina mijin naki yake?"

"Baa ai tare muke da shi ma ya wuce kasuwa, yace na zauna zuwa yamma saina koma."

Fita yayi ita kuma ta shiga ciki, nan a mahaifiyarta ta samu sai dai bata fad'a ata meya kawota

Please Login or Register in order to submit comment