Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

fara ita ba zata tafi ba wai, saida ya kalleta yace "In ban ci ubanki a gidan nan Amna ki ce d'an iska ne ni, ke ni zaki mayar sakarai, na barki anan ni kuma me zanyi acan ni kad'ai, tunda mukayi aure dake akwai ranar dana tab'a kwana ba'a malamalanki ba?"

Ummy da Amna tare suka rufe baki sukayi k'asa da kansu cikin jin kunya, lieutenant kam irin basarwa yayi kamar baiji ba, wata tsohuwa a cikin wanda suka zo daga k'auye na gefe ko gani ba tayi da kyau ta kalleshi tace "Halan Ammaru ne?"

Kallonta yayi ya washe baki yace "To dama waye in ba ni ba, Hajja ni ne da kaina?"

Cikin takurarriyar muryarta tace "Miye kuma malamalai? Naji kace a bayansu kake kwana?"

Ko da Lieutenant yaji haka sai yayi gaba ya fita a gidan dan shi dai yasan halin kayanshi saiya fad'a, Ummy kuma kallon waya aikeki tambaya ta mata, saida ya matso kusan Amna ya janye mayafinta yace "Kin gansu nan."

Da sauri Amna ta juya bayanta tana gyara gyalenta, tsohuwar kuma cewa tayi "Ai kasan ba gani nake da kyau ba ko Ammaru."

"To bari kiji." Ya fad'a yana sunkuyawa kusanta, saida ya kamo kanta cikin kunne ya rad'a mata "D'uwawu."

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚ _In dai tambayar k'wak'waf gareki ai shikenan._

D'agowa yayi ita kuma tasa hannaye ta rufe kunnuwa tana fad'in "Sayadina rasulillahi, Ammaru haka ka zama dama?"

Wani kallo ya mata yace "Hajjo daina kira na da Ammaru fa, Ammar zaki ce ko *shugaba*."

Cikin fitar da magana d'aya bayan d'aya tace "Shubagan ina kuma? Ni Ammaru na iya to."

"Ai ko zan miki fatan mutuwa in kika k'ara kirana hakanan."

Tsohuwa najin haka tace "Wai kai baka iya hira mai dad'i bane, to in dai shugaba ne zan fad'a amma bana son hirar mutuwa."

Tsuke baki yayi ya k'are mata kallo sama da k'asa ya kalli Amna yace "Kiji fa wai bata son mutuwa, to ko uwar me zata zauna tayi a duniyar, irinsu basa tafiya taya zamu ji dad'in haifo sabbin yaran mu?"

Turo baki ta k'ara yi gaba ita dai har yanzu bata son tafiya, had'e fuska yayi yace "Ni kike kumburo ma bakin duniyata?"

Sakin bakin tayi tace "A'a." kallon Ummy yayi yace "Mu zamu tafi kuma a yafe mu."

Juyawa sukayi inda take biyarsu a baya tana magana da Amna, saida suka kai mota inda Jamil ke jiransu zai kaisu gidan bus ya bud'a yaran suka shiga, zai shiga Ummy tace "Ammar."

Tsayawa yayi tare da juyowa yana kallonta, kallon data ma Amna yasa ta zagayawa ta bud'a gidan baya ta shiga ita ma ta zauna, saida ta ga shigarta ta kalleshi cikin taushin murya tace "Ka bar min Ameerah nan, saika fad'a min yaushe zaka dawo?"

Kallonta yayi sosai ido cikin ido yace "Ummy Ameera kuma?"

Ckkin murmushi tace "Eh, ina son yarinyar sosai kamar yanda nake son..." Kallonshi tayi sai kuma ta sauke idonta k'asa tace "Kamar yanda nake son mahaifinta."

Baisan yanda akayi murmushi ya sub'uce masa ba, sosai yake murmushi sai kuma ya turo baki alamar shagwab'a yace "Ummy dama kina so na ne?"

Hannu tasa ta mari fuskarshi cikin fad'a tana fad'in "Ubanka Ammar, zan haifeka a cikina ne kuma nace bana sonka? Ina ka tab'a ganin wannan uwar kai? Ubanka ne kai yanzu zaka iya fad'a min adadin son da kake ma yaranka?"

Shiru yayi yana kallon sai Ummy data share yar k'wallarta tace "Yaushe zaka dawo yanzu?"

Cikin ladabi yace "Zan dawo Ummy ranar da kika ce kina son gani na a gidan nan."

Cikin marairaicewa tace "Wai Ammar me yasa kake hakane? Nifa ranar ma magana ce kawai na fad'a maka, amma ba nayi da wata manufa bane."

Langab'e kai yayi yace "To Ummy ai ke ce ke yawan fad'in hakanan, saiki dinga hantarata kina cewa na b'ace miki da gani."

"To naji na daina ko." Tana fad'a ta juya da sauri ta shige falon, da kallo ya bita sai kuma ya bushe da dariya, shiru yayi alamar yana tunani kafin ya tab'e baki yace "Ina ga fa kunyata ce take ji a matsayina na d'an fari."

Kallon k'ofar yayi yace "Zan dawo nan da wata uku Ummy insha Allahu, na miki wannan alk'awarin."

Shiga yayi suka d'aga zuciyarshi fal farin ciki na abinda ya faru, yau ma a Niamey suka tsaya kafin su kwana su wuce, tunda suka zo shi dai bai ganta ba ko yaji motsinta, sai dare ya shirya ya fita cikin gari tare da wani abokinshi dake nan, bai wani jima sosai ba ya dawo, tun a farfajiyar gidan ya fahimci anyi bak'o ko kuma bak'i daga yanda yaga wata mota mai kyau a farfajiyar, har zai nufi b'angarensu yaga mutane biyu sun fito daga b'angaren shak'atawa na gidan, kallonsu yale sosai har suka shigo cikin haske, da sauri ya d'ora hannunshi kan k'irjinshi saboda bugawar da yayi, rintse ido yayi yana girgiza kai, saida yaji takonsu na k'aratoshi ya bud'a ido ya kallesu, cije leb'en k'asa yayi cike da bala'in daya fara gurgurarshi, cikin jin masifa a mutu ko ayi rai yace "Hamna ya zakiyi wannan gangancin? Ya zaki jawa bawan Allah firgitar zuci? Me yasa baki tausayina ne? Akan me zaki min wannan d'anyan aikin?"

Sake kallonta yayi da kyau, yatsunshi ya fara tank'warawa suna k'ara k'as k'as k'as, to wai uban wa ma ya barta ta fito hakane, wannan ai shi take tona ma asiri, wani shegen d'angalellen wando slim wanda ya bi jikinta matuk'a, bak'i ne wulik baya da kwalliya sai zip d'in dake bakin aljihunshi da suka mishi kwalliyar, rigar ma fara ce fat amma hannayenta sun d'an wuce har gwiwoyinta, daga samanta bud'e yake sai k'asan k'ugun daya matse ya zauna kan k'ugunta d'as, wani kallabi ne kanta irin na kanti fari sol dashi shima, amma kitson atach d'inta ya sauka har gadon baya.

A hankali ya fara takowa yana yi kansu har suka game, kallon kallo akuya kallon kura aka shiga yi, kallon.da yake mata babu arzik'i cikinshi, kallon ki fara lissafawa kanki second d'in da suka rage miki a duniya ne, amma kafin nan zan fara kifar da wannan k'aton banzan. Ita kanta gabanta fad'uwa kawai yake, rabon ayi ne da tsautsayi suke bibiyarta yau, dan inba tsautsayi ba bata tab'a yarda ya zo gidan nan ba sai yau daya takurata yana so ya zo ya mata gaisuwa, ta fad'a mishi gidan amma bata d'auka yau zai zo ba sai kawai kiranta yayi yace gashi ya zo, izini ta bayar aka barshi ya shigo ciki, kuma da zuwanshi da yanzun da zai tafi baifi minti goma ba, amma tasan yau sai ta Allah su rabu lafiya, ita abinda ma ke damunta shine babban mutum ne, d'an siyasa ne shima kuma d'an kasuwa, yana da mata da yara uku, bata so ya zubar mata da mutumci kuma shima ua zubar mishi da mutumci, dan shi ba tsoran takife yake yi ba, tana cikin zaro idon nan tana kallonshi taji yace "Malam me ya had'aka da *matata*?"

Da k'arfi ta k'ara zaro ido ta kalleshi, shi ma alhajin kallonta yayi da mamaki ya kuma kalleshi yace "Matarka kuma? Ta ina?"

Rik'e k'ugu yayi yace "Au! Tambaya ta ma kake? To matata ce ko bata fad'a maka ba?"

Hamna ya kalla da mamaki ya ma kasa cewa komai, kallonshi tayi tace "Karka kula shi dan Allah muje na rakaka kawai, baya da lafiya ne."

Kallonta yayi yace "Kafin na gama sabautashi ki daure ki min shiru da bakinki, meye na ki na gaggawar son tafiya ke da yau acan zaki kwana."

"Ina?" Ta fad'a da k'arfi, saida ya kalli mutumin yace "Lahira mana."

Baya taja da sauri tana fad'in "Ammar bana son iskanci wallahi, ka fita a harkata mana."

Kallon kumatunta yayi, jinjina kai yayi tare da addua'r Allah ya bashi k'arfin zuciyar da zai uya dalla mata mari, mayar da hankalinshi yayi kan mutumin yace "Bawon Allah kai nake saurare, meya had'aka da matata nace?"

Cikin nutsuwa mutumin yace "Kaga, ni ba..."

Da sauri ya katseshi da cewa "Ina zuwa, bara ka gani."

Wayarshi ya fiddo ya d'an daddana kafin ya nuna masa yace "Idan ba matata bace to ta uban wacece?"

K'uri mutumin yayi yana kallon hoton Amna da Ammar suna tare da Ameer Ameera, amma da yake a zaune take kuma ga kama sosai da kwalliya a fuskarta sai kawai ya d'auka tabbas Hamna ce, kallonta yayi yace "Hamna, taya..."

Ammar ne ya katseshi da fizge wayarshi yace "Malam saida izini na zakayi magana da ita."

Kallon Ammar yayi yace "Kayi hak'uri bawan Allah, ka tabbatar matarka ce ko kuma dai tsohuwar matarka?"

Wani kallo ya mishi yace "A ganinka haukana zai iya sa na mallaki wannan kayan kuma na rabu da ita? Kai ba kayan bane ka biyo?"

Matse baki kawai yayi yace "In kuwa har matarka ce yanzu to akwai buk'atar ka sake saka ido akanta, kayi hak'uri."

Kallonta yayi yace "To kai baka ganta bane? Mahaukaciya ce fa ta sakawa a gidan gaba, yanzu haka magani take d'auka."

Girgiza kai kawai mutumin yayi ya wuce abinshi, kallonshi tayi sai kawai ta fashe da kuka ta juyawa da sauri zata koma ciki, da k'arfi yasa hannu ya jawo gashinta yayo baya da ita, sam bata tsammanin haka ba sai kawai ta fad'o a jikinshi gaba d'aya, cit wurin yayi kafin ta fara k'ok'arin tashi da k'afarta, sakinta yayi ta mik'e daga jikinshi inda suka sake kallon juna, cikin masifa da neman sababi tace "Wallahi Ammar ka fita a hanyata, ya zaka korar min saurayi na wanda nake tunanin shi zan aura? Kana da matsala dani ne?"

Sunkuyar da kansa yayi ya d'ago idonshi kamar wani zaki yana kallonta, tambaya yake wa kansa me yasa bata nesanta kanta da wasu ne? Ya jima yana kallonta haka ita ma tana kallonshi kafin ya gyara tsayuwa yace "...


*Alhamdulillah*
14/10/2020 Γ  00:58 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*BADAK'ALA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ _*AHALI NA*_πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦

πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_58_


"Hamna ame kika d'aukeni?"

Sauda ta d'aga masa gira sama ta kalleshi tsaf sannan tace "A babban mah...mana."

Wani kallo ya mata jin rainin hankalin data masa, mahaukaci take so tace amma shine bata k'arasa ba, kenan mahaukaci take kallonshi? Ai kuwa zai nuna mata a aikace, matsawa yayi kusanta zaiyi magana sai ta k'ara ja baya tace "Malam tsaya daga can mana."

Jiniyar motocin da suka ji ne yasa su juyawa duka suka kalli k'ofar, mahaifinta ne ya dawo cikin rakiyar masu bashi tsaro kamar kullum, suna kallo akayi pakin motocin aka bud'e mishi ya fito, sauran motocin duk wajen ajiyesu aka nufa dasu inda wasu jami'ai biyu ke biye a bayanshi, kallonshi tayi ta harareshi sama da k'asa ta juya baki tare da jan dogon tsaki tace "Malam ka shirya saina sa ka bawa saurayi na hak'uri, sannan da kanka zaka bashi aure na a matsayinka na babban yayana."

Shigewa tayi a lokacin kuma mahaifinta ya k'araso, saida ya d'an rumguma Ammar a jikinshi suka gaisa, tare suka shiga babban falon, suna shiga Aissata ta tarbe shi sai ma'aikata da suke ci gaba da gyara wajen cin abinci, Ammar kuma kallon kawun nashi yayi yace "Ina zuwa tonton."

Bayan Hamna ya bi data haye sama d'akinta, ko zaune ba tayi ba taga ya fad'o mata d'aki yana cire mata cazar waya a jikin bango data saka, da mamaki tace "Malam lafiya? Me ya shigo da kai d'akina?"

Rintse ido yayi ya sake bud'esu akan ta tarau, da k'arfi ya d'aga cazar ya zuba mata a baya, wata uwar ihu ta sake tare da juyawa ta fara taka rawar da babu shiri tana matse k'afafunta da taji fitsari na barazanar danno mata kai, kuka take da iya k'arfinta ta rasa me ke mata dad'i, bata gama jin azabar ba taji ya shak'o wuyan gashinta a daidai infa ta d'aureshi da ribom ya jawota, hannu tasa ta rik'e hannun nashi d'aya kuma ta rik'e rigarshi daidai mab'allan rigarshi tana sakin wani kukan tana fad'in "Kayi hak'uri yah Ammar, kayi hak'uri dan Allah ba zan sake ba, karka dake ni dan Allah na tuba."

Tunda suka ji ihunta suka d'aga kai sama suna kallo, suna ganinsu ya sauko da ita k'asa har gabansu ya gurfanar da ita, tonton ya kalla fuskarshi babu alamar ya tab'a dariya a rayuuwarshi yace "Ku zama shaidata, wallahi saina karya yarinyar nan idan ta sake tara mana yan iska a gida, sannan..."

Ya fad'a yana sake kallonta yace "Ki tattara kayanki gobe zaki koma gida, nan dan kinga babu mai saka miki ido yasa kike abinda kika ga dama, to zaki koma can gaban Hajia da Ummy."

Cazar hannunshi ya jefa mata a jiki ya sunkuya ya nuna ta kamar zai tsone mata ido yace "Ki tuna da cewa indai akwai rai da rabo, sannan akwai lokaci to wata rana zanyi iko akan ki."

Kamar zai taka ta haka ya wuce ko kallonsu tonton bai sake yi ba, da kallo ya bishi baki sake, shi fa ba mamakin abinda yayi bane yake bashi, kalamanshi na k'arshe da kuma yanda abun ya b'ata mishi rai, to duk me yayi zafi haka? Dawo da kallonshi yayi kanta yace "Koma ciki, sannan ki had'a kayanki gobe zaki koma, ba zan iya jarabar yaron nan ba."

Cikin kuka ta mik'e tace "Wallahi Abba babu inda zanje, haka kawai sai kace wani uba na."

Nunata yayi da yatsa yace "Ke ki bar bala'i yayi kwana, ina ce yanzu a gaban uban naki ya miki wannan k'wak'waran kashedin? To dan haka ki d'auka ma yafi ubanki."

Tumurmusa k'afafu ta shiga yi tana fad'in "Allah Abba ba zan koma ba, ni nafi son zama anan, kawai dan ya fad'a shikena ba zaka ce masa komai ba."

Matsawa yayi kusanta ya dafa kafad'arta cikin taushin murya yace "Yar albarka, kiyi hak'uri ki tafi kinji, shi da gobe ne zasu tafiyarsu, daya tafi saiki dawo idan haka kike so, pour les moment dai ki tafi kinji ko."

Jinjina kai tayi tace "Ok Abba, amma ka fad'a masa ya daina takura min ya fita a harkata, inba haka ba zan masa rashin mutumci."

Jinjina kai sha yayi ya shafa kanta yana kallo harta haye sama, kallon Aissata yayi wacce ita hausar ma bata gama ji da kyau ba yayi murmushi, ciki ya wuce da jinjina al'amarin yaron nashi mai kama da d'an uwanshi colonel a zafi.

Saida ta gama shiri tsaf yace ai tafiyarsu ba yau ba saiya koma gida, bata nuna bata ji dad'i ba saboda gudun tashin k'wank'wamanshi dan su rabu lafiya, da addu'a ta rakashi sam bata san tare da wa zai tafi ba, har d'akinta yaje ya tisota gaba suka fito, a motarshi daya bari suka d'auki hanya inda Hamna take addua'r sauka lafiya, gudu yake na ganganci da kauce k'a'ida, ita har ga Allah tasan a d'ane yake jaraba yake neman, a yanda yake tasan ko jami'an kan hanya yau saita Allah su rabu lafiya, ita kuma ba zata so ya ja mata kwana a magark'ama ba, a hankali ta kalleshi cikin rawar murya tace "Yah Ammar ka tafi a hankali dan Allah, kana taka doka fa."

Ashar d'in daya malmalawa masu dokar da wanda ma aka d'orata yana wajen yasa ta ja baki tayi shiru tana girgiza kai, shirun da tayi kuma wata masifar ce sai ya fara fad'a wai ta maida shi mahaukaci tayi banza dashi, cikin salon rashin kunya tace "To Allah ya huci zuciyarka, bana so nayi laifi ne."

Damtsen hannunta mai tarin tsoka ya mara yana fad'in "Ba dan kin raina mutane ba, wai ke har ki fito da wandon daya kamata ace mijinki ne kawai zai gani a gaban namiji, to me kile son nuna masa kenan? Ya gani yayi sha'awa ko me?"

Ta wutsiyar ido kawai tale kallonshi ba zata yarda tayi magana ba ya sata a boot ya rufe, cikin masifa ya sake cewa "Ke ko can na kaiki kika k'ara kula wani Hamna saina babbaka d'an iska sai dai uwarsa ta haifi wani."

Baki bud'e ta kalleshi tace "Saboda me? Akan wane dalili? Kar nayi aure kenan kake nufi?"

Shiru ya mata baice komai ba dan haka tace "So kake na zauna haka har k'arshen rayuwata?"

Ba tare daya kalleta ba yace "Zakiyi amma ba yanzu ba, zan samo miki wanda ya dace."

A ranta tace "Bigagge kamar ko?"

A zahiri kuma tab'e baki tayi ta kalli titi, suna cikin gudu sosai wata mota ta giftasu da gudu tana zabga oda ita ma ta wuce, zuro kai yayi tsabar neman fitina yace "Idan kunje ku d'auke hanyar kusa aljihu kar mu wuce."

Dawo da kanshi yayi yana fad'in "Yan iska kawai mashaya."

Ajiyar zuciya ta sauke ta rumgume hannaye, kallonta yayi ya taka birki da k'arfi yace "Meye? Na dameki? To koma baya."

Zage ceinture d'inta tayi ta bud'a zata fita dan tafi son haka ma sai kuma ya jawota da k'arfi ya zaunar da ita yace "Ba zaki koma d'in ba tunda ba drebanki bane ni, kenan ma da gaske na dameki ko? Ba komai Hamna Allah yana gani."

Gyara zamanta tayi ita dai ba tace komai ba har ya sake d'aukar hanya, kallonshi tayi kallo na nutsuwa da basira, yayi shiru abinshi, shigar yan gayu ce jikinshi bleue d'in jeans da bak'ar riga mai dogayen hannu amma ya lank'washe su har zuwa gwiwar hannunshi, takalminshi k'afa ciki bak'i masu kyau, gemun nan yayi luf dashi sai walk'iya yale idan suka gifta ta cikin rana, zara zaran gashin idonshi wanda ke rufe girman idonshi duk sanda ya rufe su, kakkaurar girar mai yalwargashi da tsayi, dogon hancinshi daya tafi daidai da tsayin fuskarsa abun gwanin sha'awa, amma kuma kyawun d'an maciji ne, nan idan yayi wani abun saika rantse a gidan mahaukata ne yake.

D'an kawar da kanta tayi ta kuma kallonshi har yanzu dai hankalinshi na ga tuk'i, cikin sanyayyan murya tace "Kai likitan zuciya ne, amma me yasa baka tsoron saka mutane a damuwa?"

Saida ya fara d'aga idonshi sama sannan ya d'an kalleta, da alama nutsuwa ta zo mishi dan cikin sanyin murya shima yace "Ba damuwa nake saka mutane ba, ina musu magani ne."

A hankali tace "Comment?"

Kallonta yayi sosai sai kawai yayi murmushi mai sauti yace "Tu ne comprends rien, rien Hamna."

Kallonshi tayi tace "Me yasa kace haka?"

Ba tare faya kalleta ba yace "Peut Γͺtre wata rana."

Cikin odonshi ta kalla tace "Ammar je te connais bien, (na sanka sosai), mai jusqu'Γ  prΓ©sent je ne comprends rien (amma har yanzu bana fahimtar komai a game da kai)."

Dariya yayi wacce ta fito da hak'oranshi yana girgiza kai yace "Idiote."

Kallonta yayi yace "Dana bari kin fahimce ni da kin k'ara tagayyara ni kankana."

Da mamaki ta kalleshi tace "Kamar ya?"

"Comme je le dit (kamar yanda na fad'a)." Ya fad'a yana kashe mata ido d'aya, girarta ta d'aga sama ta kalli titi tace "Moi aussi."

Kallonta yayi yace "Ke ma me?"

kallonshi tayi tace "Dana tagayyari daka gane."

Bushewa yayi da dariya yace "Ni na sani dama."

Da sauri ta kalleshi tace "Vraiment?"

Sake kanne maya ido yayi yace "T'inquiète pas ma puce, chaque chose a son temps, petit à petit les oiseaux..."

Sai kuma ya bushe da wata dariyar yana k'yalk'yalewa da ita, ita ma da bata fahimce shi ba sai kawai taji ta bushe da dariya, kallonshi take tana tayashi dariyar kamar zararru, sun jima suna dariyarsu kafin suka tsagaita kuma akayi shiru, kallonta yayi yace "Me kika ma dariya?"

"Abinda kake ma." Ta fad'a tana hararenshi, da wannan ne sai tafiyar tasu ta d'anyi dad'i, dan har tsayawa yayi a station d'in Alhaji suka sha mai suka wuce, haka ma saida ya siya mata kayan k'walama suka ci, tafiya tayi nisa sosai kawai ya tsayar da mota a gefe ya kalleta yace "Fita kiyi fitsari yarinya karki min shi a mota."

Da zata ce masa bata ji, sai kuma taga ya raina mata hankali ma sai kawai tayi banza dashi, cike da zolaya yace "Ko na siya miki 4 (kun dai gane kalmar da english ai) ne kiyi?"

Fuska a had'e ta kalleshi tace "Eh, ko kuma penpers ba."

Wani kallon shak'iyanci ya mata yace "Wannan ki bari sai zaki fara bulbuli."

Yamutsa fuska tayi tace "Bulbuli kuma? Yara fa ke bulbuli."

Kallon baki da hankali ya mata yace "Waccen bulbulin nake nufi wanda ku kukeyi duk wata."

Murmushin baka da hankali ita ma ta masa tace "Da har na fara tunanin ko an canza ka ne da naji baka saka kaina yayi nauyi ba, amma yanzu na ji na gamsu da kai nake tare."

Wayarshi ya d'auka yana dannawa inda Hamna ta gyara zamanta ta jingina sosai, Amna ya kira suka gaisa tare da shiga hirarsu ta soyayya, tana kallonshi har bacci ya d'auketa a haka, yana idawa ya kalleta, murmushi kawai ya saki ya ci gaba da tuk'i cikin aminci.

Ganinsu tare ya ba kowa mamaki, har d'akin Hajia ya kaita ya gindaya sharud'anshi wai ko fita karta sake yi ba tare da dalili ba, saida ya gama tsaf Hajia ita dai ta kalleshi tace "To za'a kiyaye."

Ummy kuma kallon al'ajabi take da ikonshi, inda Hassana da wasu daga cikin dangin Hajia suka bishi da kallo suma, har zai fita Hamna ta fara gunguni k'asa k'asa tana fad'in "Wallahi babu wanda ya isa ya hana ni fita tunda ba yar zaman banza bace ni, kaji mutum kamar wani uba na ehee."

Juyowa yayi ya kalleta yace "Ki jaraba ki gani to."

Fita yayi duk suka raka shi da ido, a ranar dai kamar wasa Hamna ta rantse cewa ba zai hanata abinda tayi niyya ba kamar wanda ya haifeta, kai ita ko dan ta nuna mishi bai isa ba ma saita fita a yanda ta ga dama d'in. *Washe gari* tsaf ta shirya dan zuwa salon d'inta, doguwar riga ce ta saka ta kanti kuma ta mata kyau sosai, kallabin rigar ta yane kanta dashi ta fito, a falon suka had'e yana sallama da su Hajia zai wuce, gaisu tayi tasa kai zata fita tsohuwa mai tambayaπŸ˜‚ tace "Amina (yanda take kiransu kenan) banji kin gaishe da shugaba ba?"

Juyowa tayi ta kalleshi sama da k'asa tace "Tsohuwa wane shugaba kuma?"

"Ammaru mana, ba yayanki bane da zaki fice baki gaishe shi ba?" Cewar tsohuwar, tab'e baki tayi tace "Sauri nake Hajjo."

Cikin rarumar gani tace "Ina Sa'ada take?"

Ummy dake rik'e da kular abinci ce ta tsaya tace "Hajjo gani, wani abu kike so?"

Cikin dattako tsohuwar tace "Yanzu Sa'ada kina ji Amina bata gaishe da yayanta ba kuma baki mata magana ba?"

Kallon Hamna tayi da ita ma take kallonta, rasa abin fad'a tayi sai Ammar daya kalleta yace "Ki rik'e gaisuwarki ma, kije ki saka hijab kawai saman jayan nan naki."

Cike da raini tace "Doguwar riga ba'a saka mata hijab, ko baka san haka bane?"

D'auke kanshi yayi daga kanta yace "Ki canza wasu kayan da zaki iya saka hijab."

Cike da gatsali tace "Malam wai me ya maka zafi ne da shigata? Ina ce haka kuke son gani?"

Hajia ya kalla yace "Hajia dan Allah ban son tashin hankali, ki fad'a mata ta dinga rufe jikinta kafin ta fita, nan fa babban gida ne da ake ganin mutumcinmu, ita kad'ai bai kamata ta zubar mana da daraja ba, ni ina ga ko dan rasuwar da akayi zata iya kama kanta ai."

Dariya tayi tace "Kama kai? To wane irin kama kai kuma bayan ko ka kama shi akwai masu warware maka, kaga malam ka fita a hanyata idan kana da zuciya dan Allah, kuma fita haka zan fita na ga wanda zai hana ni, zaka zauna kawai kana sa min doka kamar kai ka haifeni, bayan kuma duk wani mugun abun kaine ka fara shi, saika nuna kai na Allah ne amma kuma ba haka bane, to idan tayar maka da hankali nake ka fad'a min inda zamu had'u, a shirye nake yanzu tunda na ga abinda kake so na zama kenan."

Saida ta dasa aya, ta
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment