Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

zai fara bata hak'uri yana cewa dan ta barshi yayi bacci ne ya fad'a mata hakanan, da haka ita ma bacci ya d'auke ta.

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

Tunda Harira ta koma gida ta samu Baaba mai wake ta fad'a mata ta samu aiki a gidan tsohon mai gidanta, bud'ar bakin Baaba cewa tayi "Karki raina min hankali mana Harira, wane irin aiki ne mutanen nan zasu baki bayan abinda ya faru? Kawai ki fad'i gaskiya idan karuwanci zaki fara, koda yake ma ba wannan ne karo na farko da zaki fara ba, amma ki sani wallahi ni babu ruwana duk abinda kika je kikayi can ke kika jiyo da matsalarki."

Bata damu da abinda ta fad'a ba haka ta ci gaba da shirye shiryen tafiya, da dare kuma ta tara k'annan ta a d'akin su ta fad'a musu zatayi tafiya, Karime ce mai wayon cikinsu dan haka tafisu shiga damuwa, sosai Harira ta rarrasheta tare da nuna mata zata je yin aiki ne dan su dinga samun abinci suna ci suna k'oshi, sannan ta dinga biya musu kud'in makaranta akan lokaci, sannan ta cire dubu uku ta basu a kud'in da Sameera ta bata tace ta b'oye karta yarda Baaba ta gani, haka kuwa akayi haka suka kwana da tunanin wayewar garin gobe.


*Mu had'e a shafi na gaba insha Allah.*
29/05/2020 à 11:10 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*SANIN MASOYI*
_(sai Allah)_
*BAYA DA K'URA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

💞 _*MASOYA NA*_💕


*Wannan kyautar taku ce*

_My Heenat_
_My BK_
_Aunty Aishan Umma_
_Mamienmu_
_Maman Annur (ma chérie)_
_Momyn Dady_
_My Hawwa_
_Sweet Hawwer_
_Sis Chappa_
_Mamar Hassan_
_Yar Baba (yar tsohuwa😜)_
_Rahila_
_Voisine Ruky_


_Auntynmu *Madame Dakoro*, jinjinar ban girma tare da fatan alkairi zuwa gareki, hak'ik'a samun masoyiya kamarki abun alfahari ne ga kowane mutum mai zuciya, alkairi yana da dad'i komai k'ank'antarshi, farin cikin da kika saka *habibiyata* yasa naga ya dace nima na mik'o godiyata zuwa gareki , domin kuwa duk wanda zai farantawa wani na kusa da kai, to hak'ik'a kai ya farantawa, da wannan nake miki addu'a Allah ya sama rayuwarki albarka, Allah ya jik'an mahaifa, Allah ya albarkaci rayuwar 'ya'yanki, Allah ya k'ara yalwata miki, Allah ya k'ara dank'on soyayya tsakaninki da mijinki, Allah ya saka miki da gidan aljanna, wannan k'ok'ari da kike Allah ne kad'ai zai iya biyanki, fatan farin ciki *mdm Dakoro*._👍


🇳🇪 *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_4_



*Tunda safe* Abbas ya shirya saboda tafiyar data kama shi dolenshi zuwa k'asar *Belgium*, a wannan lokacin yasan Sameera na kitchen dan in har yana gari da kanta take had'a mishi abin break, dan haka ya kira da téléphone d'in dake kitchen d'in, tafi kusa da wayar dan haka Razeena na matsowa zata d'auka ta kalleta tace "Bari na duba."

Tana d'orawa a kunne tace "Hello."

Murmushi ya saki kamar tana gabanshi yace "Uwar gida sarautar mata, daga kanki an gama mulki na kowane fanni, matar Abbas kuma k'anwar Abbas sannan garkuwar Abbas, uwar 'ya'yan Abbas kuma wacce ke mulki a zuciyar Abbas, farin cikin gidana, na ce ko zan iya ganinki a part d'ina yanzun nan?"

Duk da kalamanshi sun bala'in fasa kanta kuma taji dad'i sosai har zuciyarta, amma dayake daren jiya ya b'ata mata rai sai ta dake tace " Why not? I'm coming."

Saida ya sake kashe murya yace "Takawarki lafiya 'yar sarki jikar sarki k'anwa ga sarki mai mulkin garin *Basraba*."

Aje wayar kawai tayi kafin ta kalli Razeena tace "Ki kula da sauran aikin, ina zuwa yanzun."

K'ofar falon tasa makullinta ta bud'e ta shiga, wani katafaren falo ne daya gaji da kyau da tsaruwa, duk da tayi mamakin ganinshi zaune akan kujera yana d'aura takalminshi k'afa ciki bak'ak'e sai shek'i suke da d'aukar ido amma saita sake had'e rai ta rumgume hannaye tana kallonshi, d'ago kai yayi ya kalleta har dariya na kusan kubce mishi, amma dariyar da zaiyi itama rigima ce zai b'allowa kanshi dan haka yayi shiru, har ya gama d'aure takalmin ya mik'e tsaye yana ci gaba da kallonta ya kuma d'auki jakarshi bak'a ya d'ora a kafad'a, tabbas yayi kyau ya kuma birgeta, dan gaba d'aya bak'ak'en suit d'in daya saka sun zabge mishi shekarunshi, gabanta ya tako ya tsaya yana kallonta yace "Are you stil angry with me?"

Kai ta d'aga mishi alamar Eh, dan haka ya kamo hannunta ya marairaice yace "Sorry mai sunan mama na, tafiya zanyi yanzu bana so na tafi kina hushi dani, please kiyi hak'uri ki manta kinji."

Wani kallo ta masa ta zage hannayenta tace "Abban Raihan wai me ya sa yanzu kake min haka? Sam yanzu baka da lokaci na, jiya fa magana na ce zanyi da kai amma ka k'i ban dama, amma yanzu ka tsaya gabana kana fad'a min wai zakayi tafiya."

K'asa yayi da kanshi yayi shiru saboda baida hujjar kare kanshi, ya sani shi kanshi yanzu ya zama buzy sosai, ba kuma komai ya janyo hakan ba sai gabatowar zab'e, duk da baya siyasa amma yana da ruwa da tsaki a harkar sosai ta yanda ya kan zama haka, kallonta yayi yace "Amma ai nace kiyi hak'uri ko."

Cikin hassala tace "Amma ai hak'urin jiya ne ka bani, kuma ban hak'ura ba har sai ka fad'a min me ka so fad'a a k'arshen zancen ka."

"Na fa riga da na sha maganin zama dake Meera, kin daina wahalar dani yanzu." Shine abinda ya fad'a cikin ranshi, amma a fili saiya shagwab'e yace "Dan Allah ki yafe min, tafiya zanyi fa na fad'a miki, kinsan kuma ance tafiyar hali, ba lallai na dawo garekkkk..." Bata bari ya k'arasa ba ta rufe mishi baki da tafin hannu tace "Shiiii, please don't say that, you know i love u, huh?"

K'asa tayi da kanta sharrr sai hawaye saboda duk lokacin da yayi maganar rabuwa ko mutuwa to ta kan tuna had'arin daya shiga a baya ne, rumgumeta yayi yana shafa bayanta yace "I love u too my Falmata."

Sun jima haka yana rarrashinta kafin yace "Yanzu fad'a min me kike son fad'a min tun jiya?"

Kallonshi tayi tace "Na so fad'a maka tun jiya a lokacin da kake cikin nutsuwa, yanzu kuma gashi zakayi tafiya bana so mu samu mis-understand ka tafi kuma kana hushi dani."

Shafa kumatunta yayi yace "I promise u ba zan fahimceki ba daidai ba, so teld me what's going on?"

Saida ta d'an ja baya ta zauna kan kujera kafin ta nuna mishi kusa da ita tace "Please have a sit."

Zaunawa yayi yana kallonta yana fahimtar yanda maganar ke mata nauyin fad'a, sai dai baisan kome take son fad'a ba haka, dan shi dai abune mai wuya ganinta irin wannan yanayi, babu wani abu da take jin tsoro ko shayin fad'a masa sai dai in bai zo bakinta ba ko tunaninta, da k'yar ta had'a ido da shi kamar marar gaskiya tace "Dama jiya ne, Harira ta zo...nan.tare da yayanta, sun zo neman taimakonka akan iyayensu da ke rufe a cell , n...na...na fad'a musu hakan ba zai yiwu ba., shine sai ta nemi wani taimakon nawa..., kuma nayi mata."

Wani kallo ya mata kamar mai son gano wani abu kafin yace "Idan na fahimceki daidai kamar Harira tsohuwar mai aiki kike magana a kai ko?"

A hankali ta d'aga mishi kai alamar Eh, d'auke kallonshi yayi aga kanta yana kallon gefe, ya jima haka kafin ya kalleta yace "Wane irin taimako kika mata?"

Ganin yanda yake kallon ta yasa gabanta fad'uwa tare da jin tsoron fad'a mishi, shirun da tayi yasa yace "Na ce wane irin taimako kika mata?"

Nan ma shiru tayi sai k'yabta ido da take, wani kallo ya sake watso mata yace "Are you a deep?"

Girgiza kai tayi da sauri alamar a'a, dan haka yace "To fad'a min."

Cikin sark'ewar murya tace "À...a..aiki Na...bata..., a gi...ggg.idan.nan."

Da k'arfi ya mik'e harda buga kujerar yace "What nonsence? What traying to teld me? Harira? A gidana? Harira again."

Mik'ewa tayi ta kalleshi tace "You promise me."

Juya baya yayi ya rik'e k'ugu yana sauke numfashi, ya riga daya mata alk'awari, sannan akwai alk'awura da dama daya mata wanda burinshi kullum ganin ya cika mata su, daga ciki kuwa harda mallaka mata gidan nan da duk abinda ke cikinshi, dan haka ya daidaita nutsuwarshi ya juyo gareta yace "Kina ganin hakan ba matsala?"

"Insha Allahu ba za'a samu matsala ba."

Kallonta ya sakeyi yace "Are you sure?"

Cike da tabbatarwa tace "I'm very sure."

"Kin yarda tayi aiki a gidanki?"

Nan ma cewa tayi "Na amince da hakan, ina ganin kamar mun taimaka mata dan suna buk'atar taimako, kuma kaga yanzu bazawara ce ita ba budurwa ba, ta k'ara hankali da rayuwa da kuma nutsuwa."

Ya so nuna mata illar yin hakan, amma yanzu yana kan hanya ne dan haka ya rik'o hannaunta d'aya yana murzawa yace "Falmata." K'ura mishi ido tayi dan inhar taji ya kirata da sunan Falmata to tabbas abinda zai fad'a yana da mahimmanci kuma iya gaskiyarshi ne zai fad'a, d'orawa yayi da "Sanin kanki ne na miki alk'awari da dama wanda a kullum nake son ganin na cikasu, sannan gidan nan na jima da mallaka miki shi ya zama naki har abada, dan haka banda ikon hanaki yin abinda kike so, ki kawo Harira gidan nan amma da sharad'i d'aya."

Zaro ido tayi tace "What, sharad'i kuma?"

Murmushi yayi yace "Yeah, da me kike tunani?"

"To ina ji fad'a min."

Ba alamar wasa yace "Sharad'in shine ko da wasa bana son ganinta a part d'ina bare naga k'afar ta a falon nan, ko da kuwa me ake ko kuma me ke faruwa ko zai faru, kin amince?"

Murmushin jin dad'i tayi tace "Sauk'i kamar shan ruwa, dama ba wannan aikin zatayi ba, dan haka i agreed."

D'aga kafad'a yayi yace "Then, all the best wifey."

Rumgumeshi tayi sosai harda kukan shagwab'a tace "Zanyi kewarka mijina."

Shima saida ya sauke ajiyar zuciya yace "Ba zaki tausaya min ba ni halin da zan shiga babu rigimarki a kusa da ni."

Ba tare data d'ago ba tace "Oho, kenan ma ni d'in rigimammiya ce ko?"

Matseta yayi yace "Number one ma kuwa in this world."

Da k'yar suka rabu baya ya mata alk'awarin zai dawo nan da kwana uku da ikon ubangiji kad'ai ta barshi ya tafi, saida suka fito falo sun samu yara na zaune suna jiran break, sai Raihan da ita ma ake had'a break d'in da ita, gaisheda mahaifin nasu sukayi kafin ya fad'a musu zaiyi tafiya, addu'a suka bishi da ita kafin kowa ya fad'i abinda yake so a siyo mishi musamman ma Ameer da Abdul raheem, daga nan kuma part d'in su Ammie suka wuce dan basu riga sun shigo ba, nan ma addu'a yasha kafin ya wuce cikin rakiyar Sameera har zuwa bakin motarshi, drivenshi ne ya bud'e mishi amma saida suka k'ara rumgume juna kamar karsu rabu kafin ya shiga mota driver ya jasu, cikin minti talatin suka isa filin jirgi inda suka samu *captain Ali* ya gama shirya komai shi kawai yake jira, nan ma driver ya bud'e mishi ya fito yabi bayanshi da jakarshi, wata budurwa ce tsaye a k'ofar matakalar jirgin cikin uniforme d'in ta tana ganinshi ta d'an sunkuyar da kanta ta gaishe shi, ko kallon fuskarta baiyi ba ya amsa da "Fine."

Yana fara takawa ita ma ta karb'i jakarshi a hannun driver ta bi bayanshi, suna shiga ciki matakalar ta d'ago ta rufe a hankali, jirgin dai gashi babba amma cikin inda yake zaune duka kujerun guda hud'u ne, biyu b'angaren dama biyu na hagu suna kallon juna, captain Ali ne ya fara sanar dasu jirgi zai tashi su kimtsa tare da daidaitawa, ba b'ata lokaci jirgin ya haura sama suka fara tafiya, wannan budurwar ce ta fito ta tambayeshi ko da wani abu da yake buk'ata, a tak'aice kawai ya fad'a mata da favorite d'in shi yake so, ba jimawa ta kawo mishi wata fresh milk kalar kad'ai abar kallo ce, haka suka dinga tafiya inda wannan matar duk minti talatin takan zo ta tambayeshi da abinda ya ke so, cikin yardar ubangiji sai ga k'afafun su sun taka k'asa bayan kwashe musu su da akayi, nan ma airport d'in wata motar ce ta d'auke shi zuwa wata babbar hotel ta manyan mutane.


♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

Ko da su Ma'arufa suka sauka gidan masu zaman kansu kai tsaye d'akinta ta bud'a ta shiga, inda Ma'aruf ya shiga nashi d'akin shi ma, kaya ta cire ta fito ta d'ibi ruwa ta shiga wanka babu wanda ta kula duk da habaicin da wasu daga cikin mutanen gidan ke mata, Ma'aruf kuma fitowa yayi ya tsaya akan wasu dake buga karta a kan tabarma yana kallonsu, tana fitowa Ma'aruf shi ma ya shiga ba jimawa ya fito, amma kai tsaye d'akin Ma'arufa ya shiga hakan kuma ya haifar da k'ananan maganganu a wurin, dama dai tun zuwansu gidan basu fad'i alak'ar dake tsakaninsu ba cewa su yan uwane, sai dai wasu sunfi zargin dadiro kawai suke kuma suna rainawa wasu hankali suna karb'ar kud'in wasu mazan, yana shiga ya sameta tana saka bras, bayanta ya tsaya tare da kama hannayenta kamar zai saka mata sai kuma ya b'alle mata, a hankali yake shafa harya zura hannayenshi ya cabko nonuwanta ya masu wata matsa, cike da barikance tace "Ahhhhhh, huhhhhh."

Juyowa tayi ido a lumshe tasa hannu ta kamo gabanshi tana lasar leb'e tace "Dama ina da haushinka, tsohuwar gurguwar nan ce ta kawo mana cikas."

Zata had'e bakinsu ya juyar da kanshi ya kai bakinshi a kunnenta yace "Yau kuma zan huce wannan haushin nawa, dama wannan na jima da haushinsu."

Cikin rashin sanin ciwon kai da rashin kunya da fitsara da rashin albarka suka dinga iskancinsu kai kace mata da miji ne, daga ita har shi ihu kawai suke sun mata a cikin mutane suke, suna cikin wannan bad'alar tasu wayar Ma'arufa ta fara ringing, amma saita zura hannu ta kashe wayar tana ci gaba da ihu, cike da bushewar zuciya take fad'in "Ahhhhh, washhhhh, D'an uwa na, huhhhhhh, wallahi duk kafi min kolayan banzan nan, ashe haka kake dama hhhhhhh, ahhhhhhhh, wayyo, harder."

*Allah ka shirya mana zuri'a*

Sallamar wani daga cikin masu neman Marfu'a ne wanda yake kira ta k'i d'agawa ta katse musu hanzari, tsaye yayi yana muzurai ya kalli wanda ke karta yace "Marfu'a ta zo ne?"

Wani d'an daudu ne ya kalleshi ya yatsina fuska cikin harshenshi na mata yace "Kaga wani sabon salo kuma shafa kwalli da tab'arya, to yanzu duk nan cikin mu wa ka aje ya maka gdinta da zaka mana tsaye haka saman ka kana tambayarmu ita."

Wani jan kallo ya masa zaiyi magana wata mace tace "Ka wuce mana tana ciki, mu ka tsaremu ka tambayemu ita kamar ajiyarta ka bamu."

Su Marfu'a dake d'aki suna jin ance ya wuce ta zabura ta mik'e dan ita tasan masifar *Labo*, da sauri ta kalli Ma'aruf tace "Labo ne fa, yi sauri shiga nan." Ta nuna mishi bayan wasu tarin kaya, ba musu kuwa ya tattara rigarshi da wando ya kutsa ciki yayi shiru, saida ya kalli takalmin dake k'ofar d'akin na Ma'aruf kafin ya wuce ciki ko sallama babu, shigarshi kuma yayi daidai da Ma'arufa dake kwance kan gado tana gyara d'aurin k'irjin ta, wani kallon tuhuma ya dinga bin d'akin dashi harda ma ita kanta, da k'yar ya tsaya gabanta ya yaye zanin jikinta, ganin babu komai jikinta yasa yace " Me hakan ke nufi? Ke da wani d'an iskan ne a d'akin?"

Kamar zatayi kuka tace "Wai me yasa kake hakane Labo, ni da wa ka gani a d'akin nan? Zuwa na fa kenan daga k'auye wanka kad'ai nayi."

"To amma takalmin uban waye na gani a k'ofar d'akin, tunda dai ba naki bane."

Kamar wacce ta tashi daga bacci tace "Uhum! Ina jin takalmin Big (Ma'aruf suke kira da haka a gidan)ne, ina jin ma harya fita ai."

Jin ta fad'i haka yasa ya kalleta ya sunkuyo tare da kwantawa gefenta, hararan gefen ido ta masa tana yak'e, shi kuma nan ya fara shafarta yana fad'in yayi kewarta, na d'aya idan ta hanashi samun abinda yake so bala'i zai fara yanzu watak'ila ya had'a da dukanta ma , na biyu kuma tana buk'atar kud'i shi kuma tasan a wannan fannin indararo ne baisan ciwon kud'i ba, dan haka tana ji tana gani ya sake mata wawiyar caccaka.

Ma'aruf na cikin kaya yana jin duk tsiyar dake faruwa yayi luf abin shi, sun jima kafin ya saka kayanshi ya fito da kud'i ya jefo mata ya fice, d'aukar kud'in tayi ta kalli k'ofar daya fita tace "K'aramin d'an iska kawai, kaji da bak'in halinka."

Juyawa tayi inda Ma'aruf ke k'umshe ta bushe da dariya tace " Big sai a fito ko tunda dodon ya tafi."

Fitowa kam yayi daga cikin kayan yayi sharkaf da zufa yana kallonta yace "Yarinyar nan ba ki da mutumci wallahi, ina cikin d'akin kuma shine zaki yarda ki biyewa waccen bunsurun."

Tsaki yayi ya juya zai fita tace "To kuma aikin daka fara fa?"

Juyowa yayi ya kalleta yace "Allah ya kiyaye na jefa gugata bayan Labo ya cire tashi gugar, sai kuma wani lokacin yarinya."

Juyawa yayi yaji tayi tsaki ta kuma cewa "D'an iska kawai, kawai ka ce ba zaka iya ba."

Saida yasa takalminshi ya kalleta yace "Ke wai jakar ina ce d ba kya gajiya? Yanzu duk abinda ya faru kice baki gaji ba."

Mik'ewa tayi tsaye ta rarumo zani ta d'aura a k'irji tace "Haihuwar Salma ce fa, ko ka manta ne, gadon juriya nayi."

Wucewa yayi zai shiga d'akin da yake kwantawa mutan gidan suka saka shewa da habaici wai suna nuna ba komai amma kuma da wani abu a k'asa, d'an daudun nan kad'ai ya kalla ya malmala mishi wata ashar ya wuce ya barshi.


♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

Bayan tafiyar Abbas Sameera ta samu Ammie lokacin Abba shima ya fita, nan ta fad'a mata abinda ke faruwa yar aikin data d'auka, Ammie ce ta kalleta da mamaki tace "Takwarata, kuma ke yanzu kin yarda ki taimaka mata? A gaskiya ni dai hankali na bai kwanta ba."

Cikin rarrashi tace "Ammie, wallahi babu abinda zai faru da yardar Allah, kuma ma Ammie ai ba su suka aikata laifin ba, kinga ba zamu hukuntasu da laifin da iyayensu ne suka aikata ba."

Ajiyar zuciya ta sauke ta kalleta tace "Shi ya amince ne?"

Da fara'a tace "Ammie munyi magana da shi kuma ya amince, kawai yace dai bai yarda taje ko kusa da d'akin shi bane bare kuma ciki."

"To shikenan, Allah ya taimaka mana." Saida ta kwanta kan k'afafun ta tace "Ameen Ammie na."

Shafa bayanta ta fara yi tana fad'in "Ya kamata fa kisan girma kikeyi takwarata, shiyasa kullum mijinki ke k'orafin ni na lalataki kika raina shi."

Sake gyara kwanciya tayi tace "To Ammie idan banyi ba wa zan ma, shekaru na d'auka babu soyayyar uwa a tare dani saita uba, shiyasa ma ban damu da Abba ba kamar yanda na damu dake, Ammie nayi rayuwar kad'aici da maraici wanda har yanzu idan na tuno na kanji ba dad'i, soyayyar uba goma d'aya take data mahaifiya k'waya d'aya tak."

Hannu Ammie tasa ta juyo da fuskarta tuni hawaye sun fara mata zuba, goge mata yake tana fad'in "Nasan da haka takwarata, shiyasa ma har yanzu bana kallonki a matsayin wata babba, nasan kinyi kewar mahaifiya a kusa dake, kin rayu cikin mutanen da baki da wata alak'a ta jini dasu, amma yanzu ba gashi komai ya wuce ba kina tare da ni."

Rumgume Ammie tayi sosai kamar tana bata nono, tana jin soyayyarta na sake shiga zuciyarta, sai dai har yanzu tana ji ina ma zata ga mahaifiyarta ido da ido ko na awa d'aya, da zata k'arar da lokacin wajen nuna mata irin yanda take son rayuwa da ita.

Sallamar su Raihan ce tasa ta tashi zaije tana kallonsu cikin kayan makarantarsu, Ameer ne ya taho da gudu ya fad'a da jikinta yana kuka wai shi ba zai je makaranta, kallonshi tayi tace "Haba dai Babana, da girmanka da komai ka ce ba zaka je makaranta ba, dubi fa kowa ya shirya kuma tafiya zasuyi , kamata yayi ace kaine ma shugaban tafiyar nan, ko ba kaso ka zama kamar Abba ne?"

Cikin kukan ya amsa da "Ina so." Murmushi ta masa tace "Good man kenan, dan haka ka wuce gaba ka rigasu shiga gaban mota, kaji ko."

Aida gudu ya juya ya bar d'akin, sai lokacin ta kalli Abdul da suke gaisawa da Ammie, suna had'a ido yayi k'asa tana gaisheta, amsawa tayi tare da cewa "Har kun gama shirin kenan?"

Da alkunya ya amsa da "Mun gama Ammie, amma kuma bamu ga Dady ba."

Murmushi tayi tace "Sai dai kuyi hak'uri kam, amma yanzu haka dadynku na sararin samaniya akan hanyarshi ta zuwa Belgium."

Raihan ce tace "Ammie Belgium fa, amma shine ko ya mana sallama."

Raudat ce tace "Ai zai dawo gidan ya samemu, Allah ba zan mishi magana ba."

Sameera ce tace "To sarauniyar masu wayon duk duniya, kuna bacci ya tafi, amma bai fita daga gidan ba saida yace na tabbatar na sumbaci dukanku a madadin shi."

Khalifa sarkin surutu da sauri ya fad'o jikinta yace "Ni ne farkon da za'a farawa, dama ko a haihuwa nine farin cikinshi na farko."

Tab'e baki Raihan tayi tace "Dallah malam matsa min daga nan, taya zaka zama farin cikinshi na farko bayan an haifeni kafin kai."

Matsowa tayi kusan Sameera ta sunkuya tace "Ammie ni ce farko."

Hararansu Sameera tayi tace "Ga Abdul babban amma saiku da kuka fi kowa son girma."

Hannun Abdul ta kamo ta matso dashi kusanta, kunya ce ta rufe shi dan shi yanzu kallon suruka yake mata ba uwa kad'ai ba, haka ko ta dafe kumatunshi ta sumbata tare da shafa kanshi tace "Allah ya albarkace ku yarana."

Cike da jin dad'in addu'ar ta yace "Ameen Ammie, mun gode da addu'ar ki gare mu."

Jabeer ta kamo shima ta masa kafin Raihan da Khalifa da kuma sauran yaran, bye bye suka musu suka tafi har Khalifa na juyowa ya kalli Ammie yace "Yar tsohuwa naga sai kallona kikr yau ban kulaki ba ko, to zan siyo miki goro idan zan dawo."

Tab'e baki tayi tace "Ka ci k'aniyarka ko da kai da goron."


🤴🏻 *Masautar Basraba*🤴🏻

Sarki Imran Musayyib ne zaune akan sofa wacce tasha kwalliya mai d'aukar ido da birgewa, sanye yake cikin kaya na alfarma kuma na sarauta, sai dai babu nad'i a kanshi sai hula kawai, hatta takalmin k'afar shi irin na sarauta ne masu kwalliya daga sama kuma rufaffe, sai gefenshi liman ne tare waziri suna kallonshi da girmamawa yace " Liman kunce zakuyi magana dani mai mahimmanci, shiyasa ma na ce mu zo nan ciki saimu tattauna."

Duk da yana sarkinsu amma suna jin dad'in yanda yake girmamasu saboda shekarunsu da kuma dad'ewarsu a fada, dan tun mahaifin Sameera na kan mulki suke tare da su har mahaifinshi ya karb'a kuma shi yanzu gashi a kai, liman ne ya kalli waziri yace "Waziri sai kayi bayani ko."

Kallonshi waziri yayi ya kuma kalli sarki yace "Ranka shi dad'e Allah yaja zamaninka, dama magana ce data shafeka ta kuma shafi cikin gida, to mun jima muna sonyin maganar amma duba da yanda zaka d'auki maganar yasa mukayi shiru, yanzun ma mu fara jin jita-jita ne a gari da kuma labari daya zo mana daga wasu masarautun na magaganu da ake ta yad'awa akan ka, shiyasa muka ga hakk'inmu ne mu sanar da kai abinda ke faruwa."

Wata lallausar ajiyar zuciya yayi ya kallesu a tsanake cikin fitar da kowace kalma a bakinshi yace "Liman, waziri, kar kuji komai ku fad'i abinda ke ranku, ina kallonku ne kamar iyaye na, kuna da damar sakani nayi abu ko bana so."

Cike da jin dad'i waziri yayi murmushin gefen labb'a ya k'ara gyara zama yace "Mai martaba dama magana ce akan aure, kamar yanda kasan dokar garin basraba ta bawa mace damar yin mulki in har tana da aure, to haka ma dokar basraba ta bawa sarki damar auren mace biyu, uku, hud'u, amma mata d'aya bata dace da sarkin wannan gari mai
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment