Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cilla mishi wayar, rashin sanin zai cillo mishi yasa bai rik'e ba wayar ta sake fad'uwa k'asa, rai b'ace saurayin yace "Ammar meye haka? Ya zaka fasa min waya?"

Gwa da gwa ya kalleshi yace " Ita data saki ta fashe murmushi ka mata ka ce ba komai da yake mace ce ita, amma tunda ni gardi ne shine zaka nuna min karuwanci ko, to na fasa *Abdu* ci min uwa."

D'aga hannu Abdu yayi yace "Allah ya baka hak'uri, wuce." Ya fad'a dan yasan shi fa k'aramin aikin shine a wurin su zubar da kwadon rashin kirki, gashi dai mutum mai ilimi da aji amma wani lokaci kamar jahili.

Wucewar ko yayi ya ratsa mutanen suma, duk k'ok'arion shi na son ganota ya gagara, dan haka ya dafe k'ugu yana tunanin abinyi, duk da akwai maza wurin amma mata da iyaye sunfi yawa sai tarin yara, murmushi yayi ya nufi wajen mc dake sako baitoci, yana zuwa ya d'an mishi magana a kunne kamar abun arzik'i, hakan yasa mc d'in mik'a mishi amsakuwar (micro) d'in hannunshi ya tsayar da wak'ar dake tashi a wurin, Ammar kuma wayarshi ya ciro ya d'anyi danne danne kafin ya saita wajen sautin wayar ya jona a micro d'in, yana danna play sai ji kake

*Tatatatatatatatatatatata!!!* πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚k'arar bindiga, ba mata ba da suka fashe da k'ara da ihu har maza wanda ke tsaye zaune yayi, wanda ke zaune kuma ya fad'o daga kan kujerar, yara ma ihu suka saka inda wasu kuma yaran ke ganin kawai nishad'i ne sai kuwa suke da tafi, lokacin da wasu suka rage tsayi ta hanyar durk'ushewa da yin kwance lokacin ne ya hango kankana da ita kuma tsoronta na ganinta da boss zaiyi, kallon mc yayi ya mik'a mishi micro ya kashe satin wayar tashi ya wuce wajenta, ta juya dan son ganin ina yake sai kuwa sukayi tozali.

Tsoron daya gani a idonta a lokacin ya sani da zai auna jininta zaiga ya hau, matsawa yayi daga gabanta fuska ba annuri yace "Wuce muje gida."

Ita kam da a gida ne tasan zata samu masu ceto, amma anan? Kuma yace su tafi gida? Tab'idjam! Hayaniya ce ta kaure a wurin na son sanin abinda ya faru, ganin babu mai kulasu hakan ne ya bata damar saka kuka tace "Dan Allah yah Ammar kayi hak'uri ka bari har muje gida, a kan motona na zo fa."

Wani murmushin mugunta ya sakar mata tare da jerawa kusa da ita ya kama hannunta, a tare suka ji wani shocking ya baibaiye su, sororo take kallonshi tana zubo da hawaye tana ci gaba da bashi hak'uri, hankalin mutane ma baya kansu Hamna kuma har juyowa take taga ko da wanda zai iya rabata dashi, amma wak'ar da aka saka yasa hankalin kowa ya koma kan yaran dake rawar, suna fitowa ta kan matantakalar dake k'ofar shiga da ba tafi uku zuwa hud'u ba, yana saukowa daga na d'aya dana biyu ita kuma ta cije ta k'i gusawa, juyawa yayi ya kalleta, haushi ne ya sake kama shi wai akan me zata dinga fita haka tana tallar kanta a waje, k'wafa yayi tare da zagaya hannunshi ta bayanta kan cinyoyinta, d'aya hannunshi kuma ya kamo nata hannun ya wurgashi kan wuyanshi, cak ya d'auke ta ya d'ora kan wuyanshi ya nufi mota da ita, ihu take tana wutsil wutsil da k'afafu tana so ya sauke ta, boot taga ya bud'e ya nufi nan da ita, ai kuwa yana zuwa ciki ya watsata kamar buhun shinkafa, k'ara ta saki tare zunbura ta taso zaune zata mishi magana d'if ya rufe ta ya koma mazauninshi ya tayar, bubbuga k'ofar ta fara yi tana k'walla kiran yayi hak'uri dan Allah amma ina, dan ita tunaninta wani wurin zai kaita, shi kuma takaicin yanda ya sameta a wurin har tana bawa wani lambarta ne yake k'ara tunzura shi.

Bai kula da tsiyarta ba har suka iso gida ya paka motar, fitowa yayi ya bud'e mata yana hararanta, tayi sharkaf da zufa ga hawaye ga majina, da k'yar ta durko ta fito takalmi d'aya a hannu da wayarta dan ky d'in moto dama yana hannun Nafi, rufe boot d'in yayi yana kallonta sai wani tank'warewa take kamar tsohuwar data gaji da duniya yace "Maza yarinya tattare min wannan shegen siket d'in zakiyi ki min tsallon kwad'i a wurin nan."

Zaro ido tayi tace "Kwa me?"

Dak'uwa ya mata yace "Kwad'i." Belt d'in shi ya k'ok'arin zarewa yana fad'in "Ko ba zakiyi ba?"

Da sauri tace "A'a ni na isa? Zanyi wallahi."

Cire takalmanta tayi d'aya ta aje gefe ta fara tattare siket d'in da k'yar saboda ya kamata, cikin jin haushi yace "Yanzu wannan da zaki saka shi uban wa ya kama miki? Duk kibi ki d'aure jikinki haka ki hana komai numfasawa, mtsssss."

Ita dai ta gefen ido take kallonshi harta tattare, d'an matsawa tayi daga kusanshi ta duk'a kamar gaske zata fara, tana d'aukar takalminta sai kuwa tayi wuf da iya gudunta, kallonta yake yanda take gudun abisa gaskiyarta mazaunanta su ma na neman tsira, abun mamaki wanda ni kaina banyi zatonshi ba shine dariyar da Ammar yayi, domin kuwa duk dariya ko murmushi da yake na iya shege da da iskanci, amma wannan dariyar ta abune ya baka dariya ainin, gyara belt d'in shi kawai yayi ya sake shiga mota ya bar gidan.

➑️➑️➑️➑️➑️➑️➑️


An idar da sallahr isha'i kenan Alhaji ya fito daga d'akin shi zuwa falon cikin wata dakakkiyar farar shadda da taji kud'i, hula agogo da takalma duka farare ne, Hajia na zaune a kujerarta yara na ta yar hayaniyarsu amma cikin nutsuwa, inda matan kuma ke falon sama da yan mata, lieutenant ne ya shigo da alama yanzu ya dawo daga masallaci, kallonshi Alhaji yayi yace " *Babba* kaje ka shirya ka fito yanzu zamu je wani wuri."

Da ladabi lieutenant ya amsa da "To."

Ciki ya shiga Hajia kuma ta kalli Alhaji tace "Ina kuma zuwa da wannan shirin?"

Cikin sigar zolaya yace "Neman aure zan je, ki tayani da addu'a wannan karan na samu."

Wani murmushi ta saki tace "Allah na tuba ka yafe ni, macen da zata iya zama da kai a hakan nan ai sai ni."

Juyawa yayi dan bar mata falon yana fad'in "Dama kuma ke kika mayar da ni hakan."

Had'e fuska tayi a ranta tana fad'in "Wallahi duk da mun tsufa ko yanzu ka ce zakayi aure saina maka tijara, dan kuwa ina k'aunar ka kuma dan ni kad'ai aka halliceka."

Bai jima sosai ba ya fito cikin shirin dogayen kaya shadda kalar maroon da hula da takalmi, k'aninsu Ammar mai shekara sha hud'u wato *Kamal* lieutenant ya kalla yace "Ka fad'awa Ummynku na fita tare da Alhaji."

Shi fa yayi hakane tunda sun rabu da cewa zai tafi masallaci, tunda baisan ina zasu je ba da tsawon lokacin da zai d'auke su shiyasa yace a fad'a mata, amma Hajajju sai tayi mamakin abun da ganin kamar Sa'ada na son shiga hancinta da duk'unk'une ne, da kallo ta bishi har yace mata sun fita amma ko tanke, yana zuwa ya samu Alhaji na jiranshi jikin mota, shiga sukayi suka fita daga gidan sannan Alhaji yace "Gidansu yarinyar nan Zeituna zaka kaini."

Da mamaki ya kalleshi dan shi dai bai ma san gidan ba, Alhaji ne yace "Muje zan nuna maka, na tambayi Iya ta kwatanta min."

Ba tare daya daina mamaki ba yace "Alhaji me zamu je yi a gidansu? Wani abu ya faru ne?"

Murmushi ya masa yace "Alkairi ne zai kaimu, kuma ina fatan ba zaka watsa min k'asa a ido ba."

D'aurewar da kanshi yayi yasa bai iya cewa komai ba sai kwatancen da Alhaji ke mishi yake bi kawai, da haka suka iso dama kuma ba nesa bane da su, sunyi sa'ar samun kawu Mamu a k'ofar gidan zaune ya gama cin abinci, shi ya d'auka ma Jano ne ya dawo har ya mik'e dan gaishe shi cikin girmamawa, amma duk da haka ganin manyan mutane ne saida ya gaisa dasu cikin mutumci da basu girmansu, har zai shiga dan d'auko musu kujeru suka ce ya isa nan ma, zaune sukayi suka sake gaisawa kafin Alhaji yace "...


πŸ‘πŸ‘πŸ‘
16/06/2020 Γ  13:21 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*SANIN MASOYI*
_(sai Allah)_
*BAYA DA K'URA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ’ž _*MASOYA NA*_πŸ’•


_Bismillahir rahamanir rahim_

πŸ‡³πŸ‡ͺ *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_10_


A cikin kwana biyu su Raihan sun gama shirye shiryen tafiyarsu tare da su Ma'awa, Abbas da kanshi ya kaisu airport saida ya ga tashinsu kad'ai ya juyo ya dawo, a kwana biyun nan kuma Ma'arufa na nan ta rasa yanda zatayi hak'arta ta cimma ruwa, bata samun wata dama ta keb'ewa dashi, da safe ma sai dai su had'u a kan dinning da dare ma haka, kuma tun anan suke saida safe sannan kowa yaje ya kwanta, hakan yasa take jin haushin Sameera sosai saboda a kwana biyun nan kuma wata irin soyayya da kulawa suke kulawa junansu, wanda hakan ya samo asali ne saboda Abbas na cewa Meerah yi kaza za tace to, a wajen Harira ma hakane sam babu fuska daga gurinshi amma duk da haka bata karaya ba kwalliyarta take cab'awa, haka kuma ya karb'o sakamakon gwajin da akawa Abdul wanda ya nuna baya d'auke da wata cutar.

Yau dai Ma'arufa tayi waya da Salma kuma ta fad'a mata abinda zatayi, dan haka yau a shirye take kuma ta saka ido sosai, amma sai sauk'i ya samu saboda yamma lik'is Sameera ta fita zuwa compagninta yin wani business, kafin ta fita kuma saida ta tura yaran wajen Bilkisu dan karsu damu Ammie kafin ta fita, sam babu wanda ya tsammaci dawowarshi wannan lokacin, daga yanda yake sauri zaka san abu na gaggawa ne ya dawo dashi gidan, tunda Ma'arufa taga shigowarshi ta tafi d'akin ta da sauri dan gani tayi ba ma zata bari daren yayi ba kamar yanda Salma tace mata, tana shiga kayanta ta cire ta d'aura towel ta shafa turare sosai, wayar da suka killace domin aikin nan ta fito da ita, k'arama ce sai dai akwai d'aukar hoto rad'am ya fito ko da daga nesa ne, saisaita mata zama tayi ta yanda zata iya d'aukar komai dake kan gadon kafin ta fara sakin k'ara.

Harira ma na ganin shigarshi part d'in Sameera ta bi bayanshi da niyyar tambayrshi da wani abinda yake so saboda ya ga kayan jikkinta, yana cikin bud'e d'akin Sameera dan d'aukar takardun da suka dawo dashi kawai yaji ihun Ma'arufa daga cikin d'akin ta, da sauri ya juya ya kalli d'akin da tunanin lafiya? Jin wata sabuwar k'arar yasa shi sakin makullin a jikin k'ofar ya tunkari d'akin, da zuwanshi ya bubbuga amma shiru sai ihun dake sake tashi, Harira ma dake bayanshi ta iso da sauri ta tako dan ta tambayi lafiya? Amma tana ganin ya zunduma kai cikin d'akin saita tsaya, tab'e baki tayi kafin ta fara takowa cikin sanyin jiki da niyyar shiga taga ko meye.

Yana shiga ya ganta can gaban gado zaune rik'e da k'afa, k'arasawa yayi yana fad'in "Lafiya? Meya same ki ne haka?"

Saboda tana so ya matso yasa ta sake fashewa da wani kukan tana fad'in "K'afa ta ce, gurd'ewa nayi zan shiga bayi."

Yana zuwa gabanta yaga daga ita sai towel, kawar da kanshi yayi ya d'an kalli gadon, bai ga alamun hijabi ba dan haka ya d'auki rigar data cire yanzun ya jefa mata a jiki yace "Ki saka wannan saiki fito muje asibiti a duba k'afar nan."

Wata yar banzar shagwab'a ta saki wacce ta sa shi juyowa kallonta saboda mamakin ta lokacin da take fad'in "Please Abban Khalifa ka taimaka min to na mik'e, ba zan iya da kaina ba ni kad'ai."

Kallon k'ofa yayi kafin ya zuro mata hannu a ranshi babu tunanin komai sai kallonta kamar 'yar daya isa haihuwarta, tana jin ta kama hannunshi ta mik'e tsaye sai kawai ta zage towel d'in jikinta, dama kuma babu komai a jikin dan haka ta bayyana tsirara a gabanshi, shi kam yana cikin kallon k'ofa yaji alamar ta tashi, ya fara zame hannunshi daga nata yaji ta fad'o masa a jiki cikin salon k'warewa a harkar barikanci ta kai hannunta kan...Tsoro al'amarin ya bashi ta yanda ya zaburo ya kalleta, yana juyowa tayi nasarar had'a bakinta da nashi, duk da ba wani k'arfi bane ya saka mata amma yanda ya tureta yasa ta fad'a kan gadon, nunata kawai yake da hannu ya rasa me zai ce mata tsabar mamaki, da sauri ta taso ta sake kanainayeshi ta zagaya bayanshi ta zura harshenta a kunnenshi hannunta kuma cikin rigarshi, da k'arfi ya juyo gabanta ya kasheta da mari, ya nunata da yatsa yace "Ke!"

Duk da marin ya shiga jikinta amma nasararta take hangowa, sake danna mishi k'irjin ta tayi ta sake sauke hannunta wannan wurin, jin harta tashe shi yasa ta kalleshi tana son had'e bakinsu tana fad'in "Karka cutar da kanka mana, kai fa ba yaro bane, kawai kaji dad'in rayuwarka."

Duk tana maganar ne tana lasar fuskarshi shi kuma yana son yakicewa daga gareta cikin ruwan sanyi, dan sosai ta kama lagwonshi hakan yasa ya rasa kuzarinshi, jin ya fara mata sanyi yasa ta kamo hannayenshi ta d'ora kan mazaunanta, wai! A gaskiya duk da shi d'in ba mai sha'awar ganin mace da mazaunai bane manya amma jinsu yana shafawa yasa shi sake jin wani irin chock, tahowa ta dinga da hannayenshi sama ta sake saukewa kan boobs d'in ta, tana jin komai ya fara tafiya daidai ta zura harshenta bakinshi ta kamo na shi harshen ta fara mishi wata irin tsutsa, a d'aya b'angaren kuma kayanshi ta fara rabashi da su har ta mishi tsirara shima, Abbas dai idonshi rufe suke ruf tunaninshi ya tsaya, wacece wannan? Me nake shirin aikatawa? Matata fa? Zina ce fa? Meyasa? Bakayi haka ba ko lokacin k'uruciya, meyasa sai yanzu? Kana da 'ya'ya mata fa? Abbas farka mana.

Zunbur ya zabura ya tureta daga jikinshi ya bud'e idonshi, amma dake Ma'arufa tayi niyya sai tayi saurin zubewa ta durk'ushe tayi wuf da k'asan shi sai cikin bakinta, rintse ido yayi yar labb'anshi na kakkarwa tsabar jarabar data taso mishi da ita, dafa kanta yayi da niyyar fizgota amma ina, wata irin tsotsa data masa tare da kamo waccen biyun baisan lokacin daya sake danna kanta ba, a hankali saiga Ma'arufa ta kwantar da shi kan gadon tana sarrafa shi inda shi kuma ya manta da komai ya dinga biye mata, sun jima haka jin ya kasa samun nutsuwa sai kawai ya birkitota da k'arfin shi ya mata rumfa, sabo da kuma rashin sanin takamaimai inda zai shiga yasa shi karanta addua'r saduwa da iyali, k'arfin daya zo mishi yasa mata gaba d'aya ya shiga, duk da tana yar duniya saida tasan ya ratsata, dan haka ma ta gama yarda Abbas namiji har yanzu da k'arfin shi...

*Allah ka kare mana mazajenmu daga fad'awa tarkon kowace kucaka.*πŸ‘

Duk bura-ubar nan da ake Harira na tsaye har da kuka take wanda ta ma rasa dalilinsa, ita dai kawai taji hawaye na zubo mata kuma tana jin haushin abinda suke aikatawa, bata bar k'ofar ba saida taga aikin gama ya gama sannan ta bar k'ofar tana tunanin ko ta kira Sameera, wata zuciyar ta haneta da yin haka dan kuwa yau saidai su kwana a bola, dan babu abinda zai hana Sameera k'ona gidan nan sannan tayi ajalin yarinyar can wacce ita kanta take mata kallon kama da wata data sani.

Kiran sallah magrib da akayi ne ya dawo dashi tunaninshi, wata firgita yayi ya sauka daga kanta ya zauna bakin gadon ya dafe kanshi, "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, la'ilaha illallah, muhammadur-rasulullahi sallalahu alaihi wasallam, hasbunallahu wa ni'imalwakil, Allahumma ajirni fi musibati, waklufli khairan minha." Addu'o'in da yake maimaitawa kenan, meya aikata? *Zina*? Meya jani haka? Bai gama tunanin da yake ba yaji Ma'arufa ta kwantar da kanta kan bayanshi tana shafa shi, da k'arfi ya tashi tare da juyowa ya kasheta da wani sabon marin daya d'auke jinta da ganinta, kasa fad'ar komai yayi sai saka kayanshi da yayi ya bar d'akin a wani mummunan yanayin da shi kanshi ba zai iya misaltashi ba, kai tsaye d'akin shi ya shiga ya wuce bed d'in shi ya cire kayanshi, toilet ya fad'a ya sakarwa kansa ruwa wanda yake jinsu kamar tafasashin ruwa.

Yafi minti talatin a ciki yana kuka da dana sanin haihuwarshi da akayi a wannan rana, ya k'yamaci kanshi da tir da halinshi da bai zama namijin da zai iya kare kanshi daga aikata babban zunubi ba, kunyar iyayenshi data 'ya'yanshi ba zata bari ya sake had'a ido da su ba, bare kuma *Sameera*, wacce ba kunyarta kad'ai ba har tijararta da bala'in ta ba zai yarda tasan meya aikata ba, da wannan yanayin ne har zazzab'i ya sauko masa mai k'arfin gaske tare da ciwon kai, yana fitowa da k'yar ya iya saka dogon wando da doguwar riga fara ya kwanta ko sallah baiyi ba.

A wajen Ma'arufa yana fita ta d'auke hannunta daga kuncinta ta sauko daga kan gadon ta d'auko wayar data aje tana d'auka, zaune tayi ta dubawa taga komai yayi rigimarsu ta farko ce kawai wayar bata d'auka ba kuma taji dad'in haka, save d'in shi tayi ta aje wayar ta shiga wanka zuciyarta fari tas, tana fitowa ta kira Ma'aruf tace ya zo ya d'auketa ta gama abinda zatayi, tana gama shiryawa ta had'a kayanta ta fito, a lokacin kam babu kowa data had'u da shi a falon harta fita babu wanda ya sani, tana fita k'ofar gidan kuma taga motar Sameera ta danno kai zata shiga, da sauri ta b'uya bayan gate d'in gidan, tana shiga ta fito ta nufi inda sukayi da Ma'aruf zai d'auke ta, ko da taje bata wani jira shi ba sai gashi ya zo, shiga tayi yana tambayarta ta gama komai, wayar ta bashi ya kunna ya fara kallon abinda ta d'auka, dariya yayi ya kalleta yace "Komai yayi daidai, zuwa gobe kuma wannan vidΓ©o recoding d'in zai zama silar arzik'inmu a doron duniyar nan."

Ma'arufa kuma shiru tayi dan tunanin halin da mutumin kirkin zai shiga ya d'an fara damunta, gashi basuyi anfani da kororon robar da take anfani dashi ba idan za'a kusanceta, duk yanayin saiya mata babu dad'i da haka suka isa masaukinsu.

Har Sameera tayi sallah amma ba taji motsinshi ba, dan haka ta fito cikin rantsatsen less d'inta ta shiga d'akinshi, tana ganinshi kwance ruf da ciki dafe da bayan kanshi ta k'arasa da sauri ta zaune kan gadon ta tallabo shi cike da damuwa tana fad'in "Subhanallah, Abban Ameer lafiya? Meya sameka? Zazzab'i ne ma jikinka."

Abbas da tunda ta shigo yaji tahowarta tana haurawa kan gadon ya ji wata tsanarshi ta k'ara zuwa mishi, k'in yarda su had'a ido yayi bai kuma bata amsa ba, shafa fuskarshi take cike da tausayi tana fad'in " *Rabin raina* dan Allah ka min magana, meya sameka haka? Mun rabu da kai lafiya fa."

Tureta yayi daga jikinshi ya sake mayar da kanshi kan pillow, ba tare da damuwa ba ta sake d'auko kanshi ta rumgume tsakanin k'irjin ta tana fad'in "Na kira maka dr Kabir ne ya duba ka?"

D'an k'aramin tsaki yayi ya sake d'auke kanshi yana fad'in "Mtsss, leave me alone."

Gyara mishi kwanciya tayi tace "Ina zuwa, bara na d'auko wayata saina kira shi."

Ta juya kenan taji muryarshi yace "Bana so, karki kira min kowa, kema dan Allah ki barni ni kad'ai, please and please."

Mamaki ne ya sakata dawowa kan gadon ta juyo dashi tace "Abban Ameer, lafiya? What it's problèm?"

Ba tare daya bud'a idonshi ba cikin wata irin muryar data kasa fahimta yace "Na ce ki fita kema, bana so kowa ya dame ni dan Allah."

Cikin d'an daga murya tace "Ban gane baka san kowa ya dameka ba? Meya faru ne? Me akayi maka a gidan ko a waje? Matsalarka har ta kai k'adamin da ba zaka iya fad'a min ba? Ni fa mata...."

A hassale ya mik'e ya sauka daga kan gadon ya fizgi hannunta yayin da hawaye ke zubo mishi a idonshi na k'una zuci ya nufi k'ofa da ita, kallon fuskarshi take da mamaki tana ganin hawayen dake zuba, tabbas tasan yana kuka kuma yana son zama shi kad'ai idan ya tuna da yanda mahaifinshi ya rasu, amma ganin wannan zunzurutun damuwar kam ita dai bata tab'a gani ba, yana shirin fitar da ita daga d'akin ta cije ta fincike hannunta tace "Wai meye matsalar, dan Allah Abban Ameer ka fad'a min, kasan hankalina ba zai kwanta ba idan har baka fad'a min ba? Ni dai a sani na ban aikata maka wani laifin ba, amma..."

Zafin zuciya da halin da yake ciki na tashin hankali da jin zai iya dukan koma waye ya d'auke ta da mari, bai bari ta gama fahimtar meya faru ba ya jata zuwa waje yana fad'in "Ke har abada ba kya fahimar halin da mutum ke ciki."

Yana jefata waje ya mayar da k'ofar ya rufe da makulli, Sameera dake dafe da kunci tsananin mamaki take, toh! Me yayi zafi haka? Laifin waye ya shafeta da har Abbas zai iya marinta? Meye damuwarshi? Rashin sanin wannan amsoshin yasa taja k'afa jiki a sanyaye ta bar wurin ta koma d'akin ta, ita ma bata sake fitowa ba saboda tunanin damuwar dake damun mijinta, Ammie ma da taga shiru ta d'an damu, kuma ga duka motocin gidan bare ta d'auka sun fita, amma haka ta daure saboda tunanin kusanci na mata da miji.

*A kwana biyun nan* sosai Fadila ke sakewa suna hira ta waya da Saleem, inda yake rubtata ita kuma tana fad'a mishi komai daya shafesu, a haka ya zurmata har ya fahimci tana kishi da Raihan wacce ita bata ma damu da abinda ita Fadilar ta damu da shi ba, nan fa ya nuna mata zai mata maganin matsalarta ta yanda shi zai samu Raihan, dan shi yana nuna mata yana son Raihan ne har zuciyarshi, ita kuma zata samu Abdul ita kad'ai, abinda yace tayi ne ya d'an sata jin wani iri haka, amma daya k'arfafa mata gwiwa ya nuna mata ta haka kawai zata samu soyayyar Abdul, sai kawai tace zata k'ok'arta ta gani, amma fa dan Allah karya cutar da Raihan d'in, murmushin jin dad'in samun nasara yayi yace karta damu, shi fa sonta yake kuma zai iya komai danya sameta.

To fa a hakane yanzu Fadila take sakawa Raihan d'in ido duk wani motsinta, yau ma dawowarsu kenan tare da amarya daga wurin gyaren jiki, d'akin uwar amarya *Kubra* suka shiga kowace ta fara k'ok'arin wanka, dayake babban gida ne kuma da ban d'aki dayawa sai kowa bai tsaya jiran d'an uwansa saiya fito ba, Raihan ce tayi nasarar shiga toilet d'in aunty Kubra, babu kowa a d'akin dan haka tana shiga Fadila ta dawo d'akin, tana ganin ta shiga tayi sauri ta fita ta zagaya bayan d'akin, doguwar kujera ta samu ta taka ta lek'a ta window, ai kuwa saiga Raihan ta bayyana tana cire kayanta, sabuwar wayarsu ta d'auka ta danna camera ta fara d'aukar ta hoto, Raihan dake wanka tana jin dad'in saukar ruwan daga sama idonta rufe, saida ta d'auki tsiraicinta kad'ai ta sauko ta dawo d'akin ta aje wayar ta shiga wanka ita ma.

Saida suka ci abinci suna zaune ta shiga WhatsApp ta tura ma Saleem wannan hotunan, yana ganin hotunan saida yaji wata sha'awar yarinyar, amma haka ya daure yana ta kallo har saida ya samu nutsuwa.

*Washe gari* abun alajabi suka tashi da shi, bak'uwar gidansu babu ita babu labarinta, kuma babu wani abu data bari da zai nuna taji dad'in zaman gidan ko tayi godiya kan abubuwan da aka mata, haka Ammie ta dinga mita akan tafiyar ta ta tunda babu kayanta, da safe ma haka Abbas ya tashi babu k'warin jiki,

Please Login or Register in order to submit comment