Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take?"

Shiru sukayi na dak'ik'u kafin Jibril yace "Gidanta na gaskiya."

Lumshe ido yayi, muguwar yunwar da yake ji ce ta had'u da wani zafin zuciya da yaji ya taso mishi, dafe k'irji yayi da d'aya hannu kua yana matsar cikinshi, ba tare daya bud'e ido ba yace "Me yasa baku bari na mata kallon k'arshe ba? Ina son ganin kyakyawar fuskarta."

Dafa kafad'arshi Amar yayi yace "Kayi hak'uri Ammar, ka mata addu'a shine soyayyar da zaka nuna mata."

Jinjina kai ya shiga yi kamar k'adangare yana fad'in "To, to naji, zan mata."

Bud'a ido yayi ya zura k'afafunshi ya sauka daga kan gadon, jiri ne ya d'ebe shi yayi gefen da Junaid ke tsaye kamar zai fad'a masa, da sauri ya rik'e shi yace "Sannu, Ammar jiri ke damunka ka kwanta ka huta mana."

Amar ne ya kalleshi yace "Ina ga fa kamar harda yunwa, mu kaishi gida sai a samar masa wani abu ya ci."

Zamewa yayi daga rik'on da Junaid ya masa ya nufi k'ofa, layi yayi tare da neman fad'uwa a wurin Amar yayi saurin rik'eshi ta baya, saida ya gyara shi da kyau ya matseshi a hannunshi suka fita a d'akin.

Gashi dai zaune yana kallon mutane amma tunaninshi da hankalinshi na wani wurin daban, rayuwa bata da tabbas, ya gamsu ya rasa wani b'angare na jikinshi, ta tafi ta barsa da yaran da kullum ya kallesu zai tuna da ita, ta zauna dashi cikin aminci, tayi zama dashi zaman daya zama a tarihi a cikin rayuwarsu, ta mishi alkairin da shi dai bai ga abinda zai iya saka mata dashi ba, addu'a, addu'a ce kawai abu mai mahimmancin daya rage tsakaninshi da ita. Tun yana zama a wajen makokin har zazzab'i ya ci galaba kan shi ya kai kanshi d'akin maganinshi ya burmawa kanshi allura, anan ya kwanta kan gadon dake d'akin yana tuna ranar da Hajia ta yanke hukucin aurensu, ranar auren ta su da irin zamantakewarsu har ranar data yi nak'uda kan gadon nan da yake kwance yanzu.

_Lumshe ido yayi hawaye suka shiga sintiri kan fuskarshi, ba tare daya bud'a ido ba ya hasko ranar da yace mata "Duniya ta yanzu idan nace zan k'ara aure dan Allah ya zakiyi?"_

_Dariya ta masa tace "Ya zanyi kuwa daya wuce na tayaka k'wato zuciyar ko ma wacece har kayi nasara."_

_Had'e fuska yayi yace "Kenan ba zakiyi kishi na ba?"_

_Sajenshi ta shafa tace "Zan yi mana, amma ba irin wanda kake tunanin zan yi ba."_

_Hannu ya d'aga kamar zai mareta yana fad'in "Dallah can malama, ni da nake so kiyi tashin hankali ki hana ni ko da shan iska."_

_Da k'arfi ta cakume shi ta kamkame jikinshi tana fad'in "Yi hak'uri yah Ammar, karka dake ni dan Allah, zanyi kishinka wallahi."_

_Dariya ya mata ya rumgumeta sosai a jikinshi, cikin muryar shagwab'a tace "Yah Ammar zani kishinka sosai, amma ba zan yarda na tayar maka da hankali ba saboda kishi, ni dai kawai so nake ka min alk'awarin ko da ka sake aure ba zaka wulak'anta ni ba."_

_Cikin laushin murya yace "Me yasa kike tunanin zan wulak'anta ki Amna?"_

_"Saboda ba ni ce zab'inka ba, kawai Hajia ce ta had'a mu."_

_Rumgume ta ya sake yi yace "Karki damu duniyata, ina sonki har zuciyata ba zan wulak'anta ki ba."_

Bud'a ido yayi ya tashi zaune duk k'ok'arinshi na son tare kanshi saida ya kasa ya fashe da kuka, wallahi a lokacin da za'a bashi zab'in rayuwa ko mutuwa daya bita shima su rayu acan, bansan taya zaiyi rayuwa bane yanzu babu ita, ita ke saukar dashi k'asa idan yayi samada k'arfin tsiya, an kai an kawo lokacin da Amna ko fita zaiyi waje saita gargad'e shi ya kiyaye abinda zai sa ranshi b'acewa, baiwar Allahn nan ta zab'i ya daketa ko da zai ji mata ciwo akan ya fita ranshi a b'ace yaja rigima, duk da ta kare shi ta kare mutumcin shi, to yanzu wa zai mishi wannan gatan? Wa zai bashi wannan kulawar? Ya rasa kenan har *abada*.


_*Allah ya jik'an duka mamatanmu ya gafarta musu, Allah ka kai rahama k'abarin iyayenmu mata har da ma mazan, mutuwa irin ta Amna Allah ka basu ladar shahada, Allah ka kyautata namu k'arshen.*_

*A gurguje*

Sanyi sosai kamar agogon da batirinsa ya k'are haka al'amarin ya zama a wajen Ammar da Hamna, shiru da zuba ido shi yafi yawa a cikin rayuwarsu ta yanzu, idon Hamna har sunyi fari fat tsabar yawan kuka da rashin saka kwalli, in dai har yaran zasu kewaye ta saita zubar da hawaye ta kuma aika mata da addu'a, kular da take basu kamar daga cikinta suka fito, a dalilinsu ta aje zuwa salon, tace bata da abinda ya kaisu bare ya kai daidai da su, idan ta tashi tun asuba tayi sallah, haka zata musu wanka ta shirya su cikin kayan makaranta, da kanta ta ke kaisu a motarta kuma taje ta d'aukosu, abinda suke son ci shi zata girka musu da kanta, idan na siyowa ne ta siyo musu da kud'inta, a tak'aice dai ta zama uwar yaran wacce ta haife su. *Ahmad* dama tanti Hadiza aka yanke shawara aka barwa ta tafi dashi, amma duk sati biyu sai Hamna ta tafi da yaran sun gano shi, wani lokacin har kwana suke a can kafin su dawo.

Girmanta ya k'aru a idonshi da kuma soyayyarta, yanda take d'awainiya da duka yaran yana birge shi sosai, ko Shureim bata da lokacinshi kamar su, hankalinshi kwance yake akan yaran, ko kud'in makarantarsu shi dai bata tambayarshi sai in anyi katarin ya ga takaradar a aljihun rigar Ameer sannan yaje ya kai da kanshi, sai dare idan ya dawo suke zuwa inda yake su sha hirarsu shi dasu su mishi kwaramniya, inda kowane giftawa nasu yana tuna mahaifiyarsu ne, hak'urinta akan yaran ya wuce misali, duk yaanda yaro zaiyi k'ololuwar rashin ji bakinta dashi sai dai tace "Wallahi zaneka zanyi."

Kuma ba.zata zanesu d'in ba, Allah sarki, yau gashi ta barsu zasu tashi da maraicin uwa, shi a ganinshi ma har da uban, dan uwar ita ce tasa ya zama uban, uban ma kamili da zai iya amsa sunan uban a gaban ko waye, to yau bata nan sai su kad'ai.

*Sanda* rayuwar ke tafiya a haka a lokacin kuma Hajia da Ummy da Husseina suka zaunar da Abba suka sanar dashi fa Shureim d'an Ammar ne, tunda yake a rayuwa bai tab'a jin an ci mutumcin shi an muzanta shi an wulak'anta shi irin na yau ba, wannan yafi k'arfin k'arya har da yaudara da cin amana, ta ruguza zumuncin dake tsakaninshi da d'an uwanshi, rainin wayon da rainin hammatar ma yayi yawa, haka a wannan rana ya ci fad'a ya gode Allah, yayi kamar zai dake ta abinda bai tab'a yi ba, a k'arshe kuma ya juya mata baya inda yace Ammar baida laifi sai ita.

*Kwana tashi* yau kimanin wata shida kenan da rasuwar Amna, inda kowa ya darrafe yayi hak'uri ya barwa Allah, yara sun tafi Γ©cole (school) sun dawo ba ayi, suna d'aki tare da Hamna tana canza musu kaya, cikin farin ciki Ameera tace "Ummy."

"Na'am yar Ummy." Hamna ta amsa dashi, cike da yarinta tace "Yau tunda bamu Γ©cole zaki kaimu wajen Abban mu?"

Da mamaki ta kalli fuskarta tace "Abbanku kuma? To ba yana gidan ba? Kuma jiya ba kunje wajensa da dare ba?"

Turo baki tayi "Ai Abba ne yace idan bamu karatu zai tafi damu yawo."

Shafa kanta tayi tace "To yanzu ai yana wajen aiki ko baby."

Mak'ale kafad'a tayi tace "To mu dai ki kaimu wajenshi ko ki kira shi ya zo ya d'auke mu."

Kallon fuskar yarinyar tayi sosai, d'an matse bakinta tayi a hankali saboda tunawa da tayi da mahaifiyarta, sauke numfashi tayi ta mata murmushi tace "Shikenan baby Ameera, a gama saka kayan sai mu tafi ko."

Cikin jin dad'i tayi dariya, ita ma murmushi ta sake mata ta k'arasa shiryata, su Ameer ma k'arasa shiryasu tayi cikin shiga mai kyau, a tare suka fita ta nemi izinin Hajia sannan suka fita, tana shiga mota wayarta dake hannun Ameer yana game ta shiga ruri, mik'o mata yayi ta karb'a ta ga Hadiza ce, tana d'auka suka gaisa tace mata "Kina gida ne?"

"Eh Mama, lafiya?"

Daga b'angarenta tace "Lafiya lau, dama ina hanyar zuwa ne zan kawowa su Hajia Ahmad su ganshi, kullum sai sun kira ni sun tambaye shi."

Cikin farin ciki tace "Ummy Ahmad? Yanzu zaku taso ne? Nima ina son ganinshi wallahi."

"Wace tasowa kuma Hamna, yanzu haka fa ina cikin adaidaita har mun shigo layin gidan."

Fitowa tayi daga mota tana fad'in "Lah Mama, kinga kuwa da fita ne zamuyi, ku k'araso to."

K'ofar gidan ta fita inda yaran suka bita, ko da adaidaita ta aje ta yaran sukayi caa a kanta, tana kawo musu kayan motsa baki shiyasa ta gama siye zuk'atansu (yaron kenan), Hamna karb'ar Ahmad tayi tana ta sumbatar yaron tana kallonshi, masha Allah ya mulmuje sosai fuskarshi ta fito sak ta mahaifinshi, an shirya shi cikin riga da jeans na yara masu kyau ga takalmi gwanin sha'awa, kallon Mama tayi ta marairaice tace "Mama, yanzu haka wajen Abbansu ne suka matsa na kaisu, dan Allah ki barmu mu tafi dashi, nasan zaiji dad'i idan ya ganshi shima."

Zaro ido tayi tace "Hamna kina lafiya, daga zuwanmu ko ciki ban shiga dashi ba ki ce zaki tafi dashi?"

Cikin muryar rarrashi tace "Mama, wallahi ba jimawa zanyi ba, ina kaisu zan juyo na dawo, zai fita dasu ne kinga idan ya ga Ahmad ni sai na dawo tare dashi, dan Allah Mama."

Cike da gamsuwa ta kalleta cikin kashedi tace "To Hamna kamar yanda kika ce dan Allah karki jima, nasan zan sha k'orafi wajen Hajia da Sa'ada, amma zan yi yak'i indai akan wannan d'an gudaliyar ne."

Da farin ciki tace "Wallahi ba zan jima ba, mun gode Mama."

Tare suka shigo ita ta shiga mota tare da yaran, zaunar dashi tayi kan kujerar gaba tare da Ameera ta manna musu d'amarar jikin kujerar sannan suka bar gidan.

Ya gama ganin majinyatanshi yana zaune da wasu takardu yana dubawa aka k'wank'wasa k'ofar, yaran basu jira izini ba Abba ya tura duk suka shiga, saida suka gama shiga ya taso da farin cikin ganin yaran ya duk'a duk suka rumgume shi, cikin murna yace "Waya kawo ku ne?"

Kafin su bashi amsa ta zuro k'afarta d'auke da Ahmad, cikin sanyayar muryar tace "Assalama alaika."

D'ago kai yayi ya sauke tanfatsa tanfatsan idonshi akanta, tsayar dasu yayi ko su suka tsaya da kansu sani sai Allah, amma ta mugun tafiya dashi da imaninshi baki d'aya, mik'ewa yayi a hankali ba tare daya d'auke idon ba, saida ya gyara murya sannan yace "...



*Alhamdulillah* _Wallahi yau na gaji_
04/11/2020 Γ  14:38 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*BADAK'ALA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ _*AHALI NA*_πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦

πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_65_


"Ke ma haka." Shine abinda ya fad'a yana k'are mata kallo, da sauri ya tako ya zo ya karb'i Ahmad a hannunta, rumgume shi yayi a jikinshi yana satar kallonta, da d'an mamaki yace "Mama ta zo kenan? Amma ya bata sanar dani ba? Kuma daga ina kuke?"

Ba tare data kalleshi ba tace "Daga gida, sun ce na kawo su ne kace musu zaku fita."

Girgiza kai yayi yace "Halan Amna ce?"

Sak'e tayi ko da taji ya ambaci sunan, ita ta ma rasa dalilin da yasa shi sanya ma yarinyar sunanta, ba tace komai ba sai shi da yace "Ita ce bata da mantuwa ko kad'an."

Ita dai idonta na kan yaran dake ta k'iriniyarsu, shi ma damar sake kallonta ya samu, tayi kyau sosai cikin doguwar rigar atamfarta mai kalar maroon da ratsin orange da bak'i, mayafin d'an babba ne ta rufe duka k'afad'unta da shi, babu jaka ko waya a hannunta kamar yanda babu powder bare kwalli a idonta. Kallon idonta yayi yace "Zauna ko."

Ba tare data kae shi ba tace "Zan koma gida ne yanzu, Mama na jira na."

"Yau zasu koma ne?"

"Eh." Ta fad'a kanta a k'asa, d'aga gira yayi yace "To ki jira ni kad'an sai mu tafi tare, nima yanzu gidan zan tafi."

Da sauri tace "A'a, Mama ta yarda na taho da Ahmad ne saboda na ce ba zan jima ba, ko ciki bata shiga dashi ba na karb'o shi."

"Me yasa?" Ya fad'a yana kafeta da ido, sai lokacin ne kawai ta d'an d'aga idonta ta kalle shi, ya d'anyi rama sai gemunshi daya k'ara cika fuskarshi, saurin kawar da idonta tayi saboda kwarjininshi tace "Na d'auka kana son ganinshi ne."

Murmushi yayi yana kallon labb'enta masu duhu, mamakin yanda ta canza yake sai wani sunne kai take bata so su had'a ido, juyawa yayi ya zauna kan kujerar shi yaran duk suka zagaye shi kowa da abinda yake tab'awa, kallonta yayi yace "Nagode fa."

Wutsil wutsil tayi da ido kamar mai son tuna abinda ya faru yanzun har yake mata godiya, cikin nutsuwa ta d'aga duka idonta ta sauke kanshi tace "Godiya akan me?"

Kallonta yayi yace "Akan kulawar da kike da yaran nan."

Cikin sunkuyar da kai tace "Dan na kula da yara na har ina buk'atar a gode mun ne?"

Cike da jin dad'i yace "Yaba kyauta tukuici mana."

D'an tab'e baki tayi kawai ko kallonshi ba tayi ba, murmushi yayi ya mayar da hankalinshi kan yaran, ganin sun fara hira zai manta da ita a tsaye yasa ta d'anyi gyaran murya, a hankali ya juya ya kalleta da alamar tambaya, kamar marar gaskiya ta kalle shi tace "A..h.mad, zamu koma ne."

Ajiyar zuciya ya sauke ya taso daga kan kujerar, saida ya zo daf da ita ya mik'a mata shi, tana karb'arshi ta kalli yaran tace "Sai kun dawo gida."

Juyawa tayi sai kuma yace "Kin manta."

Juyowa tayi sai kawai ya karb'o wayarta a hannun Ameer ya mik'a mata, kallon fuskar Ameer tayi sai taga duk bai ji dad'i ba, kallonshi tayi tace "Ka bashi ya ci gaba da wasanshi, idan kun dawo gida saina amsa."

Ba alamar wasa yace "Ita d'in ai ba abar wasa bace, ya kamata kuma ki fara nuna musu cewa rayuwa ba komai kake so kake samu ba." Yana fad'a ya danna mata ita a hannunta.

Kallon fuskarshi tayi amma ba cikin idonshi ba tace "Hakane, amma ai abinda ya shigo hannunka da wanda ke hannunka bai kamata ka bari ya kubce maka ba, shi ta riga data shiga hannunshi, ka bar masa kawai zan karb'a ba ta yanda ranshi zai sosu ba."

Wani shu'umin kallo ya mata had'e da murmushi yana motsa labb'enshi a hankali yace "Wannan soyayyar da kike nuna wa *Ammar* fa tana yawa."

Kallonshi tayi sai ta fahimci iskanci ne ya soka mata, ita ma d'an murmushi tayi tace "Ina son k'aramin Ammar sosai, ba shi kad'ai ba duka yaran da suka fito daga cikin babbar Amna ma."

Murmushi yayi sosai ya k'ura mata ido, kallonshi tayi tace "Sai anjima."

Bai ce komai ba har ta juya zata fita yace "Me yasa? Yana ina?"

Tsayawa tayi ta juyo ta kalleshi tace "Waye?"

Ba tare daya rusuna idonshi ba yace "D'ana Shureim."

Tab'e baki tayi tace "Yana gida mana."

"Me yasa baki taho dashi ba? Ina so naga duka iyalina a tare dani, shi kad'ai ne babu a wurin nan."

"Idan ka cire ni ba." Ta fad'a kai tsaye, murmushi ya mata mai ban mamaki yace "Har da ke mana, fuskarki fuskarta ce."

Kallonshi tayi fuskarta babu walwala, juyawa tayi zata fice taji muryarshi cikin isa da zarra da k'asaita yace "Kiyi sauri ki kawo min shi shima ina buk'atarshi anan."

Juyowa tayi tace "Kayi hak'uri, gaskiya idan na shiga gida yanzu ba zan fito ba."

Kallonta yayi cikin rikid'ewar lokaci d'aya yace "Ki kawo min shi nan da minti ashirin ina jiranki, inba haka ba saina daddala miki mari wallahi."

"Mari fa? A wannan k'arnin?" Ta fad'a cike da rashin tsoro, cikin tabbatarwa yace "Ki jaraba ki gani to, ba zan tab'a yin kaffara akan abinda nake da yarda akaina a kan shi ba."

Girgiza kai tayi tace "Ba zaka tab'a canzawa ba har abada."

Ba tare daya kalleta ba yace "Zan canza ranar da kika so hakan."

"Kamar ya?"

Saida ya zauna kan kujerarshi ya kalleta yace "Kamar yanda kika ji na fad'a."

Juyawa kawai tayi suka fice ta barsu, da kallo ya bita shima har ta fita, bai kammala abinda yake ba ya fita da yaran dan yana so ya dawo kafin rana ta sake takewa sosai.

Shigar Hadiza ciki ko gaisawa basu gama yi ba gwamna ya zo gida, cikin rakiyar masu tsaron lafiyarsa har ya shiga falon kafin suka barshi, nan aka shiga gaisawa har da Hadiza saida suka gaisa cikin mutuntawa ba tare da idonsu sun had'u ba, sun gaisa da kowa amma banda lieutenant da Sa'ada.

*Ummy* kuma ta riga Hamna fita a gidan, dan a lokacin da taje dan suyi magana da lieutenan akan banzan da yake yi da ita, tana so ya fad'a mata matsayinta, tunda abun ya faru baya ko kallonta, ya daina zuwa d'akinta ranar kwananta sai dai ita taje, idan ta je kuma ko magana baya mata hasalima wani lokacin sai yace ta bashi wuri yana son zama shi kad'ai ko zaiyi wani abu, abun ya dameta sosai ta yanda yanzu ko gaishe shi tayi gaban mutane sai dai ya amsa da lafiya ko yawwa, har ta lura da mutane sun ankara da rayuwar da suke yi yanzu, dan haka safiyar ta yau taje har d'akinshi dan ayi ta ta k'are, wata shida ba kwana shida bane ai.

Sanda ta je ta same shi yana shirin fita dan yau baida fita da wuri, sallama tayi ya amsa da k'yar ba tare daya kalleta ba, saida ta tsaya d'an nesa dashi tace "Ina kwana."

Shiru yayi yana ci gaba da saka rigarsa ta kakinshi, ko da ta ga zai b'alla botira tayi saurin matsawa zata taimaka masa, baya yaja tare da k'ara had'e fuska a cikin mak'oshi yace "Um um."

Kallonshi tayi tare da sauke hannayenta k'asa tace "Magana na zo muyi idan kana da lokaci?"

Shiru ya mata ya ci gaba da shirinshi kamar baisan da zamanta a d'akin ba, zaune yayi kan kujera yana d'aura d'amarar takalminshi, hakan ne ya bata damar matsowa tace "Magana nake."

K'asan mak'oshi sosai yace "Aiki ya min yawa yanzu bana da lokaci kaina ma, ki gaggauta fad'in abinda ya kawo ki."

Saida ta gyara tsayuwarta sosai sannan tace "Tunda abun nan ya faru ka canza min, na baka hak'uri har na gaji, Hajia da su Hajiar Jibril ma duk sun tayani baka hak'uri, amma abinda na fahita shine baka hak'ura ba har yanzu, a gaskiya na fara gajiya da irin halin ko in kular da kake nuna min, shine nake so ka fad'a min a me kake kallo na ne? Sannan me ye matsayi na a wurinka yanzun?"

Cike da nuna rashin damuwa kan maganar ya d'auki hularshi ya saita zamanta yana fad'in "Duk irin zaman da kike tunanin kina yi shi kike yi."

Jakarshi ya d'auka zai fita tayi saurin tare da gabanshi tace "Wannan wace irin magana ce? Abban Ammar ka tsaya muyi magana."

Kallon fuskarta yayi cikin yanayin firgitarwa yace "Na gama magana ni ba zan b'ata lokaci na anan ba."

Zai fita ta rik'e hannunshi tace "Nima ina so na kawo k'arshen abun ne, dama zamanka na ke a gidan nan, idan ka juya min baya banga anfanin zaman nawa ba."

Shiru tayi ta ja numfashi sosai sannan ta ci gaba da cewa "Ina so ka min magana d'aya kuma tsayayya, idan ka gaji da zama dani ne to na san inda dare ya min? Tunda kafi kowa sanin inda ka d'auko ni ai."

Ba tare daya kalleta ba yayi murmushi mai ciwo yace "Ni kuwa nasan inda na d'auko ki, da kai tsaye kika fito kika fad'a min abinda kike so, amma..."

K'ofa ya nuna mata yace "Hanya a bud'e take ban rik'e miki k'afa ba, zaki iya tafiya ko yanzu ma."

Zai wuce ta sake rik'oshi da k'arfin da Allah ya hore mata tace "Ba zan tafi ba tare da shaidar komai ba, tunda haka ka ce to ka ban takardar da zan nuna ta zama hujjar tafiyata kenan, dan in na tafi ma bana son dawowa."

Kallonta yayi yace "Kije zan aika miki da ita, yanzu bana da lokacin tsayawa rubutu."

πŸ˜‚ *Maza mutanen mu, mu ke shayar daku amma in kuka labta mana wata tsiyar...hummm*

Da sauri tace "Zan tafi yanzu, amma ka sani ina jiran takardata gobe goben nan."

Wucewa yayi yana fad'in "Anfanin me ma zata miki yanzu ko an baki? Ina ce zaki koma gidan nan da ki ci gaba da kulawa da yan uwanki."

Da kallo ta bishi tace "Ita ce lasisin fara zawarci na."

Duk da bai tsaya ba saida ya juyo ya kalleta ya kuma ci gaba da tafiya, zawarci? Matarshi ta shekara arba'in ba kad'an? Tayi zawarci har ta auri wani? Maganar fa ta soke shi sosai, ba dan baya son kulata ba da saiya buge bakinta, tunda dai har yanzu yana son abarsa kawai kuskurenta ne zai nuna mata, dan har ranshi yayi rantsuwa daya san abinda ya faru a lokacin *wallahi da sai Ammar yaje gidan maza* kan abinda ya aikata, yanzun ma wuri bai k'ure ba sai dai wacce zata zama tsayayyar shaidar ita ce Hamna, kuma yana tsoron shak'uwa ta yan uwantaka da jinin shi dake yawo a jinin jikin d'anta yasa ta basu kunya, shiyasa yayi fatali da maganar Ammar kawai.

Ai kuwa Ummy da gaske take, ko da ta shiga d'aki kayanta ta had'a a jaka ta fita a gidan ko Hajia bata san da fitarta ba.

Lieutenant kuma ya d'an jima d'akin Zeituna hakan ne yasa ko da ya fito ya samu d'an uwanshi ya zo da kuma Hadiza zaune suna gaisawa, Hadiza ce ta kalleshi cikin girmamawa tace "Ban ga Sa'ada ba ni ko har ta tafi aiki ne?"

Juya akalar zancen yayi da cewa "Ina mutumen ne (Ahmad)?"

Da murmushi tace "Ai ina zuwa uwarshi ta karb'eshi, tace ta tafi ta kaisu wajen Abbansu amma yanzu zata dawo."

Jinjna kai yayi sai Hajia data sake cewa "Babba ina Sa'ada? Yau kamar ba ranar aikinta ba ai?"

"Ta tafi." Yanda ya fad'a fuska a gimtse yasa Gambo kallonshi yace "Asibiti?"

Shirin daya musu ya tabbatarwa da Hajia ba lafiya ba, dan haka tace "Ina? Tana ina Babba?"

Cikin sanyin murya yace "Hajia ta tafi, nima ban sani ba."

"Kamar ya baka sani? Babba zauna."

Zaune yayi ya aje jakarshi gefe ya kalleta, cikin rashin son wasa tace "Fad'a min ina taje da safiyar nan? Ni dai banga sanda ta fita ba."

Ba tare daya had'a ido da ita ba yace "Hajia ta tafi, akan abinda ya faru ne, ita ce mai laifi ma amma har ta tsaya gabana tana fad'in idan na gaji da ita ta tafiyarta."

"Sai ka ce mata me?" Cewar Hajia, saida ya waina kanshi yace "Shine ta tafiyarta, tace na aika mata da takardarta."

Da k'arfi Hajia tace "Babba, kana da hankali kuwa? Yanzu kai baka ji kunyar fad'ar maganar nan ba? Matar ta ka?"

Gambo dake kallonshi da mamaki ne yace "Wai me ya faru ne haka da zafi? d'an uwa a sani na daku baku tab'a samun sab'anin da yasa tayi ko da yaji ba, me yayi zafi haka da girmanku da komai kuna fad'an yara."

Kallon Hajia yayi ranshi a b'ace yace "Hajia ni zan tafi."

Mik'ewa yayi zai fita Hajia tace "Ban gama magana da kai ba zaka mik'e min a kai Hassan, zauna min kaji malam."

Muryar da tayi magana da ita ta waccen Hajiar ce, dole ya dawo ya zauna yana sunkuyar da kai, Hadiza kam mik'ewa tayi ta kalli Hajia tace "Hajia zan jira a waje, akwai buk'atar ku tattauna."

Cikin mutumtawa Hajia tace "Zauna Hadiza, ai ke ma har yanzu iyalin gidan nan ce."

Murmushi tayi tace "Ban k'i ta taki ba Hajia, amma duk da haka akwai buk'atar kuyi magana tsakaninku."

"Hadiza karki manta fa

Please Login or Register in order to submit comment