Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne suka sashi daka mata tsawa yace "Ke!"

Harira da tuni tasan da fitowarshi shiru kawai tayi a tsora ce ta juyo juyo tana saki wata k'ara duk da muryar ba siririya bace da zatayi dad'in sauraro, ba kwalliyar fuskarta ce ta sake shiga madubin idonshi ba sai k'irjinta da rigar ta matseshi sosai yayi sama kamar zasu fito, tabbas mata bala'i ne, dan k'arfin da yaji lokacin daya mata tsawar nan tana juyowa sai yaji ya rasa kuzarin, wani bala'in sanyi ne yaji hannunshi sun mishi ya kasa d'aga su, da k'yar ya iya tattaro jarumtarshi yace "Lafiya? Meya kawo ki part d'ina?"

Sunkuyawa tayi tace "Ina kwana? Kayi hak'uri yallab'ai, na zo gyara..." Bai bari ta k'arasa ba yace "Kije bana so, kuma daga yau kar na sake ganinki sashi na."

Sunkuyawa tayi alamar to kafin ta nufo shi, hakan yasa ya bud'e ido yana kallonta ya ga me zatayi, kan k'aramin teburin ne ta aje k'aramar wayarta da man goge madubi, duk'awa tayi zata d'auka ta d'ago kai taga ko yana kallonta, ganin ya kawar da kanshi yasa tace "Yallab'ai na kawo maka abincin ka nan ne?"

Kallonta yayi zaiyi magana kuma sai yayi shiru saboda abinda ya gani, haka dai ta k'arasa kwarkwasarta ta fita ta barshi, tsaki yayi a ranshi yana fad'in "Dole ma ta kori yarinyar nan wallahi, ba zan iya ba haka kawai."

Falon Sameera ya shiga kai tsaye d'akin ta ya nufa da niyyar sauke mata bala'in da yarinyar can ke son d'ora masa, amma abun takaici saida ya kai daf da d'akin ya tuna rigimammiyar bata gari, a ranshi yace "Bata kira ni ba, nima kuma ban kirata ba, hmmm."

Juyawa yayi yana fad'in Allah ya sota da rahamar da sai ya tara mata uwar gajiya, daf da d'akin da Ma'arufa take ya tsaya saboda tuna akwai bak'uwa a gidan, tunani yake ko tana nan? Ko kuma tana wajen cin abinci? K'wank'wasa k'ofar yayi hakan yasa Ma'arufa dake shirin saka kaya tace "Ina zuwa."

A hankali ta lallab'o ta lek'o ta hudar dake jikin k'ofar kamar yanda sauran k'ofofin suke, saida ta dafe k'irji ta zaro ido ta fara tunanin abinyi, gamsuwa da shawarar da zuciyarta ta yanke mata yasa ta wangale k'ofar d'akin tana fad'in "Lil sis ke..."

Shiru tayi da mamaki na k'arya a fuskarta na ganinshi tsaye, da sauri ya kawar da kanshi gabanshi na dukan uku uku, bai tab'a ganin matar da ba halalinshi ba daga ita sai d'aurin k'irji na towel, yau gashi ya gani da idonshi, kana gani kasan hasken mai ne dan har k'arnin mai take, amma santala santalan cinyoyin masu d'aukar hankali ne, k'arin gashin da tayi wanda ya saje kamar gashinta ya kwanta bayanta, bai sake kallonta ba illa fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un da yake yi."

Ita kuma babu d'ar ko kunya a tare da ita sai sunkuyar da kai da tayi tace "Good morning sir, na yi tunanin lil sis ce, dan tun jiya ita ke kawo min ziyar."

Ba tare daya kalli wajen da take ba yace "Ya k'afar taki? Ki fito ki ci abinci."

Yana fad'a kuma bai tsaya jin me za tace ba ya fice da sauri, farfajiyar gidan ya fita kamar zai shiga motarshi kuma saiya tsaya, tambaya yake wa kansa me yake faruwa dashi haka yau? Sai ganin matan da babu komai tsakaninshi da su yake, Allah ya sani yanzu ya zama mai yawan buk'ata, gashi duk sun saka shi ya d'auki caji kuma maganin warakar bata nan, wayarshi ya fito da ita ya danna mata kira, a daidai lokacin daya kira Sameera kuma tana daf da shiga gidan waziri, tana ganin kiran ta tsaya ta d'auka, muryarshi babu alamar wasa taji yace "Ki bar duk abinda kike ki dawo yau d'in nan."

Take ya kashe wayar dan kar ma ta samu damar yi masa gardama, ita kuma da farko ta d'auka rarrashinta zaiyi yace ta dawo, amma sai taji yace wai ta dawo yau d'in nan, mayar da wayar tayi a jaka ta shiga gidan da sallama, ba mutane a gidan sai matar kawai a tsakar gida, amsawa tayi tare da d'agowa, tana ganinta gabanta ya fad'i dan tasan ba alkairi ya kawota ba, mik'ewa tayi daga zaman da take cikin sanyin jiki tace "Hajia ke ce? Sannu da zuwa, shigo ciki."

K'arasowa Sameera tayi cikin wata shegiyar tafiya, d'an takawa matar tayi tana fad'in "Bari na kawo miki..."

Bata fad'a ba taji Sameera ta jawo hannunta ta dawo da ita baya, kallon juna sukayi inda Sameera tace "Da alama ba sai na fad'a miki wacece ni ba? Rabuwar mu ta jiya ba tayi dad'i ba, a dalilinki mahaifina ya tafi gida da b'acin rai, a sanadiyarki mahaifina ya kasa aiwatar da abinda yayi niyya, a dalilinki jiya na kwana da ciwon kai, a dai dalilinki ne na kwana nesa da yara na ba kuma tare da mahaifinsu ba, shin kina ganin idan ban kawo miki ziyara ba nayi daidai?"

Cikin rashin gaskiya ta kalleta tace "Eh...to. Hajia duk me..ya kawo wannan..maganar kuma?"

Tassssss, saukar mari kawai matar taji, take ta dafe kuncinta ta durk'ushe a wurin kanta k'asa, Sameera kuma nuna ta tayi da yatsa dan matar ba wani finta shekaru tayi ba tace " Ki rubuta ki aje, bana sakin rigima cikin sauk'i, wannan marin tun jiya na so na miki shi, amma mijina bai bani dama ba, idan waziri ya zo kya gaishe min dashi, idan kuma kin shirya d'aukar fansa sai ki sanar dashi ya shirya miki bataliya guda wacce zata d'aukar miki fansar."

Tana gama fad'a ta juya ta fita a gidan hankali kwance, mik'ewa matar tayi tana mamakin k'arfin halin Sameera, amma kuma kamar yanda tace ba shakka zata d'auki fansa ko da ba a kanta bane, tasan shirin da suke da shi a k'asa dole zai gigita duk wani makusancin sarki da ma iyalinshi, dan haka tayi k'wafa ta shiga harkar gabanta ba tare da tunanin fad'awa ko da wazirin ba bare wani, ita kuma tana fita daga nan masarauta ta shiga, a cikin fada aka basu wuri ita da Imran suka tattauna akan maganar aurenshi, ta jima suna hira tana bashi shawarwari kafin ta mishi sallama ta fito, tana dawowa tamasal ta fara had'a nata kayan dana Abbas dan shi ma bai d'auki komai ba, amma kuma sai kawu Bakura ya dinga nemanta da shawara kan bikin Husna, a k'arshe dai saida suka tafi da *Jebu* da kuma Husna ta zab'i kayan da take so kafin suka dawo, sai bayan sallah la'asar ta shirya ta zo airport inda ta samu tunda sukayi waya da Abbas ya turo da jirgin da zai d'auke ta, tana shiga suna kimtsa suka lula sai Abuja kuma.

Tun lokacin da sukayi waya ya tura a d'aukotaya zuba ido yana jiran isowarta, yara ma da zasu tafi islamiyya sai nan suka shigo suka gaishe shi, haka yake zaune yana duban agogo, daya ga hakan ba zai gyara shi ba saiya kira captain Ali ya tambaye shi, a cewar shi har yanzu madame bata k'araso ba, nan ya kashe wayar yayi cilli da ita ya kuma niyyar ba zai kirata ba sai ta zo kawai, yana zaune ya jingina sosai a kujerar kamar mai bacci ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya yaji an turo k'ofar an shigo, in dai ba Sameera ba Ammie ce kawai keyi masa haka, dan haka bai damu ba sai bud'a idon da yayi kawai, Ma'arufa ce wacce ta ga motar shi alamar bai fita ba kuma basu ci abinci tare da shi ba, d'auke take da babban faranti da chips a ciki da soyayyar plentain, sai fresh milk kamar yanda Razeena ta fad'a mata, saida ta rufe k'ofar d'akin sannan tayi sallama cikin murya mai ja hankali, da sauri ya sauko kanshi izuwa k'asa dan jin ba muryar Ammie bace, saida gabanshi ya fad'i lokacin da suka had'a ido, yana mamakin dalilin da yasa yake jin mummunan fad'uwar gaba idan ya ganta, bai iya d'auke kanshi daga kallonta ba har saida ta sunkuya ta aje farantin akan k'aramin teburin ta d'ago tace "Barka da hutawa yallab'ai, munga shiru har yanzu baka fito bane yasa na kawo maka wannan."

Jawo mishi teburin tayi gabanshi yana kallonta ta zuba komai kuma yanda ya dace kafin ta kalleshi tace "Aci lafiya."

Da kallo ya bita harta fita ta na d'an d'yangasa k'afar ta a hankali, saida ta fita yake mamakin rashin kunyar yarinyar, anya kuwa idan yar mutumci ce zata iya yarda su had'a ido bayan ganin daya mata d'azu? Abune mai kamar wuya gaskiya ga mace mai kunya, tab'e baki kawai yayi ya k'ara janyo table d'in ya soma cin abincin.

*Yanayin* mai matuk'ar dad'i, mai kula da gidan yayi aikinshi ta hanyar share furen flawer's d'in dake zuba, ya gyara wasu flawer's d'in ta hanyar rage musu girma da basu ruwa, a hankali iska ke kad'awa yana fito da wani daddad'an k'amshi da sanyi mai ni'ima, Saleem ne zaune a cikin mota ya gama rabawa duk yaran chocolat, saida zasu shiga ciki ya kalli Khalifa da shi yanzun yake ganin ya girmi chocolat yace "Idan ka shiga ciki kace Raihan ta zo ina son ganinta."

"To." Ya fad'a yana bashi hannu ya shiga ciki, tunda ya shiga ya samu Raihan a kicthen tana had'a cake wanda ta gani anyi a tv, dayake yarinya ce mai k'ok'ari kuma uwarta ta d'ora ta tun tana k'arama yasa yanzu haka dai bata da matsalar girki, yana zuwa yace "Aunty Raihan uncle Saleem ne a waje wai yana jiranki."

Kallonshi tayi ta d'an yi shiru kafin tace "Ka fad'a masa ina aiki, i'm busy."

Wani kallo ya mata yace "Wai ke me kike nufi ne? Haka ma ranar nan yace ki zo kika ce wai kina aiki."

Cikin taushin murya da sanyin hali tace "To ba aikin nake ba? Dallah malam kaje ka fad'a masa ina aiki."

Juyawa yayi zai fita yana fad'in "Ni yaronki ne to da zaki aike ni? Ke kije ki fad'a masa."

Kallonshi tayi tace "Haba yaro ba laifinka bane da ka raina ni, Dady ne yake nuna maka kaine namiji dan haka har ni zaka iya mulka, amma ba komai its not ur fault."

Khalifa kam da son girma fa bai zo fad'awa Saleem sak'on Raihan ba, sai Raudat dake zaune falo yace ta je ta fad'a masa, tashi tayi tana turo baki dan ita kuma a nata b'angaren gani take mugun raini ne ace Khalifa ke gaba da ita, kasancewar jikin Abbas Abbas ne da ita na girman k'asusuwa yasa har gabanta ya fara tara nonuwa, tana fad'a masa ita ma ta dawo falon ta zauna, Saleem kuma k'wafa yayi yace "Ba zan tab'a barinki ba, dole sai plan d'ina ya kammala a kanki, stupid girl kawai idiot."

Harya zura k'afafunshi zai rufe motar yaji ance "Idan har kana so ka samu shiga kar ka zama lazy man, confidence kake buk'ata kafin samun zuciyar Raihan."

Juyowa yayi yana kallon Fadila dake tunkaroshi, ba laifi ita ma kyakyawa ce, bai daina kallonta ba har saida ta k'araso ta tsaya kusa da shi, kafin yace wani abu tace "Tun ranar can na hangi zunzurutun k'aunar da kake mata, amma ita d'in yarinya ce da ba komai ke zama a kanta ba bare tayi tunani a kanshi, amma idan zaka kama k'afa dani burinka zai cika akan Raihan."

Wani shu'umin kallo ya mata da murmushi a gefen lallab'anshi irin na tarkona ya kama kurciya, ita ma kallonshi take tana ganin nata burin zai cika idan tayi k'ok'ari ta had'a soyayyarsu, cikin kwanciyar hankali yace "Are u sure zaki taimaka min har nayi winnen heart d'in ta?"

Cike da k'warin gwiwa tace "Ina baka tabbacin haka."

K'aramar yatsarshi ya mik'o mata tare da fad'in "Mun kulla daga yanzu kenan? Mun zama friends."

Bata bashi yatsanta ba sai kai data jinjina masa alamar eh, fitowar Abdul a sukwane daga part d'in yasa hankalinta komawa can, bata jira ya nemeta ba ta taka da sauri ta tarbeshi tana fad'in "Yah Abdul ina zuwa haka da yammar nan?"

Cikin sakin fuska yace "K'anwata zanje wani wuri ne, ko kina zuwa ne?"

Cikin salo kamar babbar mace tace "Yah Abdul tafiya indai tare da kaine zan yarda na shekara dubu ina yinta ba zan gajiya ba ai."

Murmushi ya mata yace "To nagode k'anwata, yanzu dai zan tafi saina dawo, ko da wani geft kike so na siya miki?"

Saida ta kashe masa ido tace "Kawai ni ka kular mana da kanka."

Nan ma murmushi yayi yace "I wil insha Allah, bye bye."

Yana fad'a ya shiga motarshi ya tayar, da kallo ta bishi harya fita daga gidan kafin ya kula da Saleem wanda shima kallonta yake ya hango soyayyar Abdul a idonta, k'arasowa tayi hakan yasa ya mata dariya yace "Kina ta so ki b'oye, amma kuma zuciyarki da idonki sun k'i lamuntar hakan, meyasa zaki cutar da kanki ta hanyar hana zuciyarki abinda take so?"

Kallonshi tayi sosai tana nazari, ko ba komai yau ta samu wanda ya gano abinda ke zuciyarta, dan haka babu fargaba cikin rufewar ido tace "Saboda ba ni ce na dace da shi ba."

Da mamaki yace "To wa kenan ta dace da shi?"

Kai tsaye tace "Raihan mana."

Yanda ta fad'i sunan a take saiya hangi kamar zuciyarta ta fara tafasa, dan ya samu biyan buk'ata sai yace " Amma ke ma mace ce mai class , kina da kyau ilimi da wayewa, sannan iyayenki babu na yarwa, so meye wata 'ya mace zata nuna miki har ta hanaki cikar burinki?"

Shaid'an ne ya dinga hura wutar dake zuciyarta harta saki baki tace "Ban sani ba nima, amma ko Ummata sau da dama zaka ga tana nuna banbanci tsakani na da ita, haka ma Abbana yana fifitasu a kanmu, gaba d'aya mun zama kamar wasu bayinsu, mahaifinsu ne ke juya namu iyayen, mahaifiyarsu ma ta mulki iyayenmu, hatta makaranta wannan sai a motarsu ake kaimu alhalin iyayenmu nada halin siyan motan da tafi tasu."

Harira ce ta fito farfajiyar gidan tana waya da Adamu yayanta, hakan yasa Fadila yamutsa fuska tace "Ina ga zamuyi magana da kai, yan sa ido sun fara fitowa."

Wayarshi ya mik'o mata yace "Give me ur phone number, i wil call u."

Karb'a tayi ta saka mishi ta mik'a mishi tayi gaba, shima fita yayi daga gidan, zata shiga part d'in Sameera ta hangi Abbas da fitowarshi kenan daga wanka ya haura sama dan ya ga ko motar da zata kawo mishi matar shi ta si, ganin babu motar yasa shi ciro wayarshi ya dannawa dr Kabir kira, a lokacin kuma Fadila ta zagaya ta haura ta saman dan ta gaishe shi su kuma yi hira kamar yanda suka saba, duk da yanzun tana jin ba zata tsaya yi hirar ba dan Saleem ya tsokano mata wani abu shaid'an kuma ya sake zugata, sam baisan da zuwan mutum ba hasalima baya tsammanin zuwan kowa wurin, tambayar dr Kabir yake yaushe result d'in Abdul zai fito yaje ya karb'a, bayan ya fad'a masa ne Abbas d'in ke cewa "Ina fatan kar a samu kowace cuta a jikinshi, dan in aka samu tofa babu maganar aure tsakaninshi da Raihan, dan su Abba ba zasu bari ba, sanan dan Allah ka k'ara rik'e mana sirrin nan ko Abdul kar yaji an mishi gwajin nan bare kuma wani nashi."

Alk'awari ya mishi yace ya kwantar da hankalinshi, Fadila na jin haka tayi saurin komawa ta sauka k'asa, ranta ne ya sake b'aci sosai tana ganin kenan shi kanshi Abdul d'in ma basu raga ma ba, ai kuwa shiryawa tayi zata bayyana mishi soyayarta in ya so duk abinda zai faru ya faru.

Ta sauke kenan aka bud'e gate d'in gidan motar Abdul ta shigo tare da Sameera, dama saurin da yake zaije d'aukar ta ne, Abbas na hangensu har Abdul ya shiga da jakarta ita ma ta bi bayanshi, fita yayi daga nan yasa makullinshi ya bud'e d'akin ta ya sake rufe k'ofar da makullin ya zage shi, ya kusan minti talatin a d'akin ko hasken fitila bai kunna ba kafin yaji Sameera ta taho cikin d'aga murya tana fad'in "Ku wa Allah ku wa ubanku ku barni nayi wanka zan fito yanzu."

Yana jin ta saka makulli ya taso daga kan gadon ya lab'e jikin k'ofar, tana bud'ewa ta mayar ta rufe da niyyar shiga wanka, ta juyo kenan da nufin kunna hasken d'akin taji an cakumeta ta baya tare da rufe mata baki da hanci da tafin hannu lallausa wanda hakan yasa k'arar da tayi bata fito ba, tabbas tasan Abbas ne amma me yake nufi da haka bata sani ba? Take a wurin gyalenta da d'an kwali ya fita ta saki jakar data shigo da ita, ta bayanta ya d'ora hab'arshi a kafad'arta yace "Wato a gabana kike zagar min yara ko? Saboda kina tunanin bana gidan, ashe dama haka kike tsine min bayan ido na? To bari kiga yanda zanyi dake."

Cillata yayi akan gadon ya kuma bita ya taushe yana fad'in "Jiya nace ki zo, amma ki ka k'i zuwa dan kin raina ni, sannan kika cije ni nace zan rama kika ce na rama d'in, to bari kiga ikon Allah Sameera, ba dai dan kinga ina jin tausayinki ina d'aga miki k'afa ne yasa kika raina ni ba."

K'wafa yayi yasa k'arfi ya cire zip d'in rigarta da k'arfi, bata fara jin tsoro ba har saida taji ya rabata da komai na jikinta, da k'arfi ta k'walla kiran "Ammieeeee!"

D'aga hannu yayi kamar zai mareta yace "Wallahi kika k'ara d'aga min murya saina zabgeki da mari, fitsararriya kawai."

Yana fad'a ya fizgi k'afar ta da k'arfi babu alamar tausayi ya wareta, sake fashewa tayi da kukan shagwab'a tare da rufe kumatunta karya mareta, ai da iya k'arfin da Allah ya hore masa ya zage ya saisaita kansa zuwa hanya madaidaiciya ya durmiya cikin jikinta, rad'ad'in azabar da bata tab'a ji bane ya ziyarce ta lokaci d'aya, rikid'ewa idonta sukayi ta bud'a gaba d'aya bakinta zata saki k'ara yasa hannu ya rufe mata bakin...


*Takwara maganinki kenan ai😡*
12/06/2020 à 11:17 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*SANIN MASOYI*
_(sai Allah)_
*BAYA DA K'URA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

💞 _*MASOYA NA*_💕


_Bismillahir rahamanir rahim_

🇳🇪 *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_7_

Da sauri Abbas ya rik'o ta dan yasan me zatayi, juyowa tayi ta kalleshi ganin ya had'e rai sosai yasa ta fincike daga rik'on daya mata ta fice a falon da sauri tana hawaye, girgiza kai yayi yana sake jadadda kai kukanshi ga ubangiji akan Allah ya sanyaya mata zuciyarta, cikin sanyin jiki ya zauna inda Abba ya kalli uwar d'aki data fara magana kamar haka "Amma yallab'ai sai naga kamar gaskiya matar waziri ta fad'a, dan ko ni dake uwar gidan takawa kuma uwa ga sarkin yanzu bansan da wannan magana ba, amma abun mamaki wai har kuna cewa ma burinshi kenan."

Kallonta Abba yayi, shin nesan da sukayi da juna na tsawon lokaci ne yasa *Hafsatu* mantawa da waye shi? Ko kuma sanyin da yayi ya rage tijara ne yasa har zata iya kallonshi ta fad'a masa wannan maganar? Wane irin raini ne wannan suka d'ora mishi haka harda matar da bai ma gama saninta ba ko a fuska? Me zaiyi musu ne ma wai? Ya jima yana mata wannan kallon mai tattare da nazarin abinda zan fad'a miki kafin ya nisa yana kallonta ido cikin ido yace "Hafsatu kinsan dai da nine a gaba da mijinki ko? Sannan kinsan da mijinki ma kallo na yake kamar mahaifi tun bayan rasuwar iyayenmu? Sannan nasan kinsan cewa kaf yaranshi ina da hakk'in da zan iya yanke hukunci a kansu ba tare da sanin shi kanshi margayi ba? Dan haka ki saurara min tare da d'aga min k'afa, kar kisa nayi abinda za'a buga sunana a mujalla shafi na farko da zata fito safiyar gobe."

K'wafa yayi tare da juyawa ya kalli liman yace "Liman, kana da wata matsala idan aka d'aura auren nan a yau?"

Girgiza kai yayi yace "Babu ko d'aya ranka shi dad'e."

Imran ya kalla yace "Kai fa Imran? Kana da matsala da hakan?"

Shi ma girgiza kai yayi cikin ladabi yace " Babu Abba."

Mik'ewa yayi tsaye tare da fad'in "Duk mai farin ciki da auren nan ya fara shiri yanzun nan, dan ana idar da sallah la'asar zan d'aura auren Imran da 'yar wajen liman Safiyya."

A wannan karan kam uwar d'aki ba wai tsananin son da take sai Imran ya auri 'yar waziri bane yasa ta shiga rud"u da firgici illa yanda take ganin za'a nuna mata iko da d'an data haifa, kuma wai ba ma uban daya haife shi ba, wannan ne yasa ta mik'ewa ita ma kamar zararra tace "Me? Aure? Zaka wa d'an nawa ba tare da amincewata ba? Wallahi baka isa ba, *Mus'ab*, karfa kaga muna d'aga maka k'afa, can ma kawaici ne a matsayinka na yayan mijinmu, amma ka sani shi kanshi yanzu baya raye, dan haka wallahi ba zan tab'a yarda ka had'a auren Imran da wannan yarinyar ba yar matsiyata, indai ni na haifi Imran kuma ta hanyar aure."

K'arama a cikin matan takawa ce ta kalleta a nutse tace "Haba uwar d'aki, sai naga kuma ko takawa baya raye ai akwai alak'ar data had'a ki zumunci da danginshi ko da kuwa ba kya so, wannan alak'ar kuma ita ce 'ya'ya, ki nutsu dan Allah sai a bi komai..."

Da hannu ta dakatar da ita da cewa "Dakata min malama, 'yan bak'in ciki kawai, ai dama nasan ba son yaya na kuke ba shiyasa hakan ba zai dameku ba, to ke ki bada d'an ki mana sai a had'a shi da wannan bak'in irin, amma ba ni ba."

Imran da tunda ta fara magana yake kallon yanayin Baffan nashi, sai jimk'e hannunshi na hagu yake yana ji kamar zai kai duka, inda yake d'an lumshe idon shi yana bud'ewa duk da haka saida sukayi ja, yasan zaman nan ba zai k'are musu da kyau ba, dan haka ya kalli uwar d'aki a sanyaye yace "Umma, dan Allah ki zauna muyi magana."

Cikin b'acin rai tace "Wane zama kuma zanyi, Imran a gabanka za'a tozarta mahaifata a nuna min ban isa da kai ba, aure? Ka manta aurenka na farko ma haka aka d'aura maka shi ba tare da ina so ba, shine yanzu ma zaka sake wani auren saboda mahaifinka, me kake so da ni? Kana so dole saika nuna min ka fi son mahaifinka a kaina? Imran uwa fa ba wasa bace, karka manta da haka, amma idan kace zakayi to ba zan hanaka ba, kaje kayi ga wurin nan."

Cikin tsananin rashin jin dad'i ya d'an girgiza kai, har zuciyarshi yana son auren yarinyar baisan me yasa ba, ga kuma abinda mahaifiyarshi take fad'a, d'agowa yayi ya kalleta a nutse cikin taushin murya yace "Umma, wallahi ba wai na fifita Abba a kanki bane, ba kuma zan bi umarninsa bane dan na b'ata miki rai, wallahi ni da kaina na shawarci takawa akan maganar auren da nake so na k'ara, kuma shi ya bani shawara ga 'yar liman nan, nasan ba zai min zab'in da zai cutar da ni ba shiyasa ma na amince da gaggawa, amma ina neman afuwarki idan ranki bai miki dad'i ba, kuma duk da haka ina rok'on alfarmarki da ki barni nayi auren nan Umma, shine cikar burin takawa, Umma idan kina so ma zaki iya bani wani umarni kema na miki alk'awarin zanyi duk abinda kika saka ni indai bai sab'awa shari'a ba."

Duk maganganunshi babu wanda ya shigeta bare har yayi tasiri a zuciyarta, amma kam maganarshi ta k'arshe tayi armashi, dan haka ma ta d'an saci kallon liman da shima ya kalleta a fakaice sukayi murmushi, saida ta gyara tsayuwa tace "Ka tabbatar zakayi duk abinda zan saka ka?"

Da ladabi yace "Eh Umma, insha Allahu zanyi indai baifi k'arfi na ba."

Kallon Abba

Please Login or Register in order to submit comment