Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Kinga idan kin d'aga kice gamu nan kan hanyar zuwa gida, dan na tabbata Hajia ce zata saka shi ya kira mu, kuma nasan ni zata d'orawa laifin ta min tijara, gwara idan mun koma ayi duk wacce za ayi."

Hadiza dai dariya tayi inda Amna ta d'aga ta kuma fad'a mishi duk abinda ta fad'a mata, kasancewarshi ba mai son jan magana ba yasa ya kashe wayar ya kalli Hajia yace " Suna zuwa yanzu, sun tsaya bitar jarabawarsu ne ta gobe kasancewar lissafi zasuyi."

Yana fad'a ya juya zai fita tace "Shalele ka jira yanzu za'a kawo muku abinci."

Uhum bai ce mata ba ya fice, Hadiza data saka su Hamna gaba suna tattaunawa irin na mahaifiya da 'ya'ya, umartarsu tayi da su shirya tunda anyi sallah, haka kuwa akayi suna gama shiryawa Ammar ya shigo tare da Shu'aibu, sallama sukayi cike da kewar juna suka d'auki hanyar komawa gida, yanzun ma Amna ce gaba sai Hamna a baya, yanzu ma cikin mintin da bai gaza ashirin da wani abu ba suka iso saboda yana gudu sosai.

D'akinsu suka wuce ba tare da kowa ya lura da su ba suka shiga shiryawa suma, yamma tayi sosai suka gama suka fito, lokacin ne akasan da zuwansu gidan, Ummy har d'aki ta shiga da Hamna ta k'ara duba lafiyar jikinta, ana sallah magrib Hajia ta hangesu farfajiyar gida suna d'aukar hotuna tare dasu Umaimah da Jamila, k'anwar Jamila mai bi mata *Nazeefa* ta turo ta kira su inda ta e su sameta a d'akin ta, dukansu babu wanda jikinshi baiyi sanyi ba tare da tsoron abinda zai faru suka nufi d'akin nata.

A tak'aice dai fad'a da masifa da bala'i babu wanda basu gani ba, saida tayi ikrarin idan haka ta sake faruwa to su kuka da kansu, suna fitowa suka ci gaba da harkokinsu kamar kowa tunda dama sun saba da irin wannan tijarar, anyi sallah isha'i ana ta shirin tarban amarya Ammar ya shigo falon Hajia, duk da kowa na hada hadar gabanshi amma ganin Ammar da wasu manyan kwalaye har biyu yasa kowa ya tsaya dan kashe k'wark'watar idonshi, gaban Hajia wacce ke zaune cikin manyan tsofaffin mata k'awayenta ya diresu, juyawa yayi ya fita bayan wani lokaci kuma sai gashi da manyan salkar goro ha guda biyu ita ma, ajewa yayi gabanta kafin ya kalli idonta yasa hannu aljihun wando ya fito da babbar enveloppe, mik'a mata yayi tare da fad'in "Hajiar mu ga lefena na kawo, ga kud'i na tambaya da gaishe da iyaye da duk wata bidi'a, sadakin kuma sai ranar d'aurin aure Alhaji Hassan zai biya."

Hajia data saki baki tana kallonshi d'ora k'afad'aya kan d'aya tayi ta kalli Sa'ada dake zaune gefe ko kallonshi ba tayi tace "D'an ki ya rasa yan uwan da zasu kawo mishi kayan ne? Ko kuma dai rashin kunyar tashi ce ta motsa? Shiyasa ya kawo kayan da kanshi saboda ya nuna mana shi kangararre ne."

Kallonta Sa'ada tayi cikin taushin murya tace "Hajia kema kinsan halinshi ai, yana so ya nuna rashin kunyarshi a fili ne, sannan ya nuna babu wanda ya isa dashi."

Shi ma bai juya ya kalli Ummy ba yace "Banga abun rashin kunya ba anan, k'anwata ce zan aura da muke gida d'aya, saboda kawai na ragewa mutane wahala sai ya zama fitsara?"

Enveloppe d'in daya mik'a mata ta karb'a ta jinjinata tana kallonshi tace "Da alama kud'in dayawa, ai banyi tsammanin zakayi k'ok'ari haka ba."

Murmushin nan dai ya mata wanda yake mata idan zai b'arkota yace "Hajiata kenan, Amna fa kika bani, tunda kika ga nayi wannan k'ok'arin kisan da cewa ni kad'ai naga abinda na gani."

Ita kanta Hajiar wani wawan murmushi ta masa tace "Allah ko marar kunya? Kenan dai jikar tawa tayi ko?"

Wannan karan har saida sautin murmushin ya fito kafin yace "Sosai ma, ai ko baki bita da gyara ba nasan zan huta da kayana."

Wata dattijuwa ce gefe Hajia tace "Kai fice mana a wurin nan bama son surutun nan na kwankwatsar kwalabe."

Dariya suka saka mata inda shi kuma yace "Tsohe ikon Allah, to ku da kun riga kunci naku zamanin, kuma fa kinsan ance kamar *kumbo* kamar *katanta*."

Tshohuwar a zuciyarta ta amsa masa da "Tabbas, yanda kayi gadonta wajen kyau da zubin hallita, haka kayi gadon rashin kunyarta da sako zance."

Kallonshi Hajia tayi tace "Ina fatan dai uwarka ta fad'a muku irin hidimar dake gabanku? Dan kamar yanda na fad'a ne dole za ayi aure irin auren buzuwa."

Hannayenshi ya zuba aljihu yana mamakin yanda ko gaban idon mahaifiyarshi ko bayan idonta ba zata iya cewa mahaifiyarka ko mamanka ba sai dai uwaka, juyawa yayi zai fita yana fad'in "Zanyi komai akan zab'inki ai a shirye nake."

Cikin d'an d'aga murya tace "Kace ubanka ne zai biya sadakin? A wane dalili ne kai ba zaka biya ba?"

Ba tare daya tsaya ba bare ya juyo yace "Saboda shi za'a haifawa jikan."

Ummy ce ta d'aga kai ta bi k'eyar shi da kallo tana jinjina wannan al'amari na d'an nata, kamar ba shine jiya yayi wa yarinya fyad'e a cikin gidan nan ba, kai dole ma su b'oye wannan sirri ita da Hamna, dan ko sun fito dashi shi dai babu ruwa a idonshi bare yaji kunya ko nadama, zai ma iya fassarawa mutane yanda al'amarin ya kasance kad'an ne daga cikin aikinshi, Hajia kuma ko a jikinta sai jawo akwatinan da tayi aka bud'e, sam babu wanda yayi tsammanin da kaya a cikinsu duba da yanda shi kanshi ya d'auko su ya shigo da su, amma abun al'ajabi dukansu guda goma sha hud'u cike suke da kaya masu yawa da kyau, ga kuma goro da kud'i har million biyu rigis, Hajia kam ya birgeta a karon farko na rayuwarta, nan aka manta da jiran amarya ake anata duba kayan nan wasu na d'auka hoto, isowar motocin da suka tafi d'aukar amarya ne yasa Hajia kallon Sa'ada tace "Ki shiga da kayan d'akinki ki ajiye."

"To." Ta fad'a tana mik'ewa ta d'auki kayan tare da taimakon k'awayen ta ita ma da suka zo tausar k'irji.



*Alhamdulillah*
09/09/2020 Γ  17:58 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*BADAK'ALA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ _*AHALI NA*_πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦

πŸ‡³πŸ‡ͺ *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_*Alhamdulillah Ala ni'imatil islam, Allah nagode maka daka sawak'e min komai, ba yin kaina bane, ba dubarata bace, ba wayona bane, Allah nagode maka, yan uwa kuma nagode sosai da gudummuwarku, Addu'arku ta riskeni a sanda nake da buk'atar ta, haihuwa ta zo min da sauk'i fiye da zatonku, Allah kaine Allah kuma abun godiya, Allah ka raya min yarana ka bani ikon yi musu tarbiya irin ta addinin musulunci.*_πŸ‘

*Aci gaba da gashi guy's.*πŸ’ƒ

_27_


Ana cikin wannan hidima aka kawo amarya, motoci dai gasu jingim wanda suka paka k'ofar gidan, amma Zeituna bata da dangin da har zasu iya d'aukar motocin, gaba d'aya wanda suka zo rakiyarta basu fi mata ashirin Ba. Kuma a haka wai dangi sun zo ne k'wansu da k'wark'watarsu saboda ta auri mai kud'i, tarba ta musamman suka samu daga gidan girma, inda aka wuce da amarya d'akin ta aka zaunar da ita, saida suka ci suka sha suka k'oshi kafin suka bar gidan tare da yi wa amarya jan kunne cewa karta manta da danginta wajen cin arzik'in, wasu daga cikin motoci aka saka suka mayar dasu gida suka bar amarya da halinta.

Kafatanin yaran gidan ne suka baibaye Zeituna suna kallo, wacce ita kuma ta sanda kanta k'asa ta kasa had'a ido da kowa saboda tunaninta duk kallon rashin mutumci suke mata, Hamna da Amna da Jamila ne suka shigo tare sai Umaimah dake bayansu, zaune sukayi inda Umaimah ke fad'in "Ku kuma ku tashi ku fita ku ba mutane wuri duk kun zo kun sata gaba kuna kallo."

Nazeefa ce ta kalleta tace "Ai dai ganin amarya muka zo."

Cikin tsawa Umaimah tace "Ke dallah tashi ku fita, ba gidan zata zauna ba sai kiyi ta kallonta ai."

Kamal ne ya kalli Umaimah ya mik'e tsaye yana zuba hannayenshi aljihu yace "Kaji mace dan Allah zaki kore mu, amaryar ubana ce fa."

Kallon juna suka shiga yi dan abun ya basu mamaki, a sanin da suka ma Kamal baya da surutu irin haka, Hamna murmushi suka bishi da kallo har suka fita, sai Jamila da tace "Allah yasa kar mu samu yah Ammar na biyu a gidan nan."

"Ameen." Cewar Amna da saurinta, Umaimah ce ta kalli Zeituna wacce k'irjin ta ke dukan uku uku saboda zatonta zasu mata rashin kunya ne shiyasa suka kori yaran, cewa tayi "Aunty Zeituna ki bud'a fuskar ko, yaran sun fita sai mu kawai."

K'ara sanda kanta tayi taja gyalenta ta sake rufe fuska ruf, Hamna ce tabi hannayenta da kallo wanda suka sha lalle ba laifi mai kyau, amma da ganin gyalenta da kayan jikinta kasan ba shirin k'warai tayi ba ko aka mata, duk da bata yanayin farin ciki hannu tasa ta janyo mayafin tana fad'in "Haba aunty Zeituna mu ga kwalliyar mana, mu fa ba bak'in ki bane."

Kallon juna sukayi yayin da Umaimah har saida tayi dariya saboda ganin kwalliyar dake fuskarta, da sauri ta rufe bakinta tana kallon jagirar da ke fuskar Zeituna wacce ta mik'e zat babu lank'wasa,cike da mamaki Amna tace "Aunty Zeituna, waya miki wannan kwalliyar haka?"

Da sauri Zeituna ta d'ago kai ta kalleta sai kuma ta sauke kanta tana mamakin yanda duk suke kiranta da aunty, Umaimah ce tace "Aunty Zeituna, gaskiya tashi ki sake wanka ki zo ki sake shiri, dan kawuna ba zai so ganinki haka ba a darenku na farko."

Tintsirewa sukayi da dariya sai Hamna kawai data girgiza kai tana murmushi, ganin bata da niyyar tashi yasa Amna mik'ewa ta kamata suka nufi ban d'aki tana fad'in "Mik'e mana auntynmu, wannan kwalliya taki ai ta asalin 'yan k'auye ce aka miki."

Turata tayi ban d'akin tace tayi wanka ta fito dan ta goge wannan kwalliyar marar kan gado, Jamila ce ta mik'e tace ma Hamna "Sis ki duba mata kayan daya dace ta saka yanzu, dan ke ce ke shirin zama gwanar kwalliya da iya tsara kaya."

Hararanta tayi tace "Wai ku ina ruwanku da shirinta? Haka kawai ku mata katsalandan, kunsan tana so ko bata so da zaku mata shishigi? Watak'ila fa haka ta iya kwalliyarta, kenan zamu zauna kullum muna yi mata ne?"

Amna ce tace "Ke dai babu ruwanki kawai ki mata, in kuma ba zaki mata ba ki fad'a ni saina mata."

Hararan Amna tayi tace "Bansan iskanci Amna, ina wasa dake ne? To ba zanyi ba ki mata ke."

Mik'ewa tayi zata bar d'akin Amna ta tab'e baki tace "Kar Allah yasa kiyi d'in kiga idan za'a kasa yi mata ne."

Duk da Hamna taji zafin maganar amma banza ta mata dan bata son hayaniya, saida ta kai k'ofa zata fita Amna ta sake cewa "Dama tun jiya kike bak'in rai kamar wacce aka aikowa sak'on mutuwa."

Juyowa tayi ta kalleta cikin hassala tace "Amna bana son iya shege fa, wallahi karki sake min magana, inba haka ba kuma..."

K'wafa tayi ta sake juyawa zata fita Amna tace "Inba haka ba sai me? Me zakayi?"

Juyowa tayi ta dawo cikin harzuk'a tana fad'in "Dan Allah in kin cika 'yar halak ki sake tanka min, Amna ki min magana kiga yanda zan kifar dake a wurin nan."

*'Yan biyu akwai rigimaπŸ€”, ko kuma dai na familyn Gaga ne haka.*

Ba tare da wata shakka ba ta matsa kusa da ita tsabar jin masifa tace "Anyi d'in naga me zaki..."

Marin da Hamna ta sauke mata a kumatu yasa ta yin shiru bata shirya ba, dafe kunci tayi ta d'ago daga sunkuyawar da tayi bata shirya ba, da tsantsar mamaki ta kalleta tace "Hamna ni kika mara?"

"An mareki Amna me zakiyi?" Cewar Hamna a hassale, d'orawa tayi da "Ko zaki rama ne marar kunya?"

Ai kuwa Hamna na gama fad'a Amna ta d'auke ta da mari ita ma kamar wasa, jin zafin marin yasa Hamna idonta kad'awa sukayi ja sosai, takaici ne ya lullub'e ta wai k'anwar ta ce ta mareta a fuska, lallai akwai raini tsakaninsu kuma babba, tana shirin kai mata duka Jamila tayi saurin shiga tsakaninsu ta ture Amna gefe guda tana fad'in "Dan Allah kuyi hak'uri ya isa haka, ku bari."

Umaimah ma tasowa tayi ta rik'e Hamna ta fara bata hak'uri, wannan hayaniyar ce ta fito da Zeituna daga ban d'aki da kuma Ummy da su Zeinabu dake d'akin Ummyn wanda yafi kusa dana Zeituna, suna zuwa suma rabasu suka fara yi suna bawa Hamna hak'uri wacce ta d'auki zafi sosai, tabbas kowa yasan ranta ya b'ace saboda yanda ta rikid'e ta zama kamar Amna idan tayi zuciya, kuka Hamna keyi tana fad'in "Wallahi Ummy saina tozarta yarinyar nan, dan na sakar mata fuska shiyasa har zata iya d'aga hannu ta mareni, Allah saina ci uwarta a gidan nan dan ta gane da banbanci ni da ita."

Ummy ce ke fad'in "Kiyi hak'uri nace ko Hamna ta, ki k'yaleta tunda ke ce babba, muje d'akina ki huta kinji ko."

Cikin wani irin kuka kamar wacce aka wa mutuwa tace "Babu inda zanje, Allah saina tattaka ta Ummy, idan ba haka ba kuma kowa zai shiga matsala a gidan nan."

Murmushi Ummy tayi saboda ita dai tasan yan biyunta basu da k'ohi yanzu, dan haka ta jata tana fad'in "Naji to muje dai."

Tirjewa tayi sosai tace babu inda zata je saidai a barta da Amna, ita ma kuma Amna da su Zeinabu ke rik'e da ita cewa take "Dan Allah Ummy ki saketa ta zo ta kashe ni in zata iya, an fad'a miki tsoronki nake ne."

Ganin abun ya k'i kwantawa yasa Ummy daka tsawa tace "Ke Jamila, tunda ba zasu hak'ura ba ku kira Hajia ta zo ta rabasu, ni kam na gaji da wannan jininin kamar kukan tsohuwa."

Juyawa Jamila tayi da sauri ta fita daga d'akin, amma zuciyar kowa a wuya take babu wacce tayi yunk'urin dakatawa sai aikawa juna ashar suke da son a sakesu. Jamila na zuwa a falo ta samu Hajia da sauran aminanta da suka rage, saida taje kusa da ita sosai ta sunkuya ta dafa kujerar da take zaune akai cikin k'asa da murya tace "Hajia, wai Ummy tace na fad'a miki ki zo ki ma su Hamna magana fad'a suke, kuma sun rabasu sun k'i su rabu."

Wani mugun kallo ta watso mata kamar ta kashe ta da mari tare da d'aga murya tace "Dallah malama b'ace min da gani daga nan, ku mahaukatan ina ne da baku san ta kamata ba? Ina cikin mutane ne zaki zo min da wata maganar banza, to kije ki fad'a musu nace su barsu su kashe kawunansu, tunda su 'yan iska ne ba za'a fad'a musu suji ba."

Jiki a sanyaye ciki da haushi Jamila ta juya zata koma, muryar Hajia ce ta tsinta tace "Tunda sun k'i rabuwa cikin lalama kije ki kira min Ammar, shi zai ci uwar kowace sai su zauna lafiya ai."

Juyowa Jamila tayi ta kalleta, Ammar kuma? Shine abinda ta maimaita, tasan in dai ya zo to fa sai sunji jiki dukansu, to amma ya zatayi? Wucewa tayi sumi sumi ta nufi b'angaren samarin, tana daf da kaiwa ta had'u da shi ya fito da alama fita zaiyi, saida gabanta ya fad'i ita kam dan sam bata san shiga shirginshi, saida ta d'auke kallonta daga kanshi kafin tace "Yah Ammar dama Hajia ce tace wai ka zo?"

Wani farrr yayi da idonshi ya kalli wata bishiyar mai kyau ya dafe k'ugu yace "Ebola, me kuma ya faru yanzun?"

Shiru Jamila tayi bata ko kalleshi ba hakan yasa ya daka mata tsawa yace "Da wani bakinki kamar na jab'a, ba dake nake ba kika min shiru? Da gulma ce da kin fad'a ko?"

D'agowa tayi kamar zatayi kuka tace "Nima ban sani ba yah Ammar, su Hamna ne ke fad'a a ciki, kuma su Ummy sun rabasu sun k'i su rabu, shine Hajia tace na kiraka ka rabasu."

"Wato ni d'an iska ko? Ni ne zan iya rabasu kenan? Ai dama ance kowane kare ma da ranarshi."

Jamila dai satar kallonshi tayi ta juya ta barshi, take ya canza tafiyarshi zuwa ta k'akk'arfan soja mai ji da izza ya tunkari b'angaren, fuskarshi kad'ai zaka kalla ta baka tsoro ta saka fargaba da fitsari a wando, dan alamu ne na babu wasa a tare da shi, da haka ya shiga ko kallon Hajia baiyi ba ya nufi d'akin Zeituna da yake jin hayaniyar kuma ya ga Jamila ta shiga can.


*Nagode da addua'r ku mutane na, na haihu lafiya haka ma ina cikin k'oshin lafiya ni da beby Khalid, Allah ya bar k'auna masoyana.*
09/09/2020 Γ  17:58 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*BADAK'ALA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ _*AHALI NA*_πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦

πŸ‡³πŸ‡ͺ *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_28_


Yana shiga d'akin babu sallama fuska a had'e ya soma kallon Hamna da Amna, Ummy na ganinshi had'e rai tayi ita ma ta kama hannun Hamna da nufin su fita, durk'ushewa tayi cikin wani irin kuka tana fad'in "Wallahi Ummy saina daki yarinyar nan, kawai ki tafi ki barni da ita."

Sake sunkuyawa tayi zata kama hannunta tana hararan Ammar dake tsaye yana kallonta tace "Tashi muje nace Hamna, bana son taurin kai fa."

Kamar ba da ita ake magana ba saboda yanda tayi bata ji ba, a hankali ya fara zago belt d'in shi daga jikin wandonshi cikin motsa labb'a a hankali yace "Ku fita ku barni dasu kamar yanda suke buk'ata, tunda 'yan daba ne su."

Kallonshi Ummy tayi tace "Kaga malam babu ruwanka, karka kuskura ka tab'a min yara wallahi, inba haka ba kuma ranka zai mugun b'aci."

Kallon Jamila tayi tace "Ke wa yace ki kira shi? Ba Hajia nace ki kira min ba?"

Cikin turo baki tace "Wallahi aunty na fad'awa..." Shiru tayi saboda kallon da Ammar ya mata, mayar da kallonshi yayi kan Amna wacce ke tsakiyar Zeituna da Zeinabu, cikin dakakkiyar murya yace "Meya had'a ki da ita?"

Duk bala'in zuciyarta da masifar dake ciciyarta saita samu kanta da jin fad'uwar gaba, hawaye taji suna neman cika mata ido yayin da jikinta ya fara d'aukar rawa, tafin hannunta tasa ta share 'yar kwallar ba tare da tace komai ba, zaro manyan idonshi yayi masu surkin launin ja ya daka mata tsawa yana fad'in "Tambayarki nake meya had'a ki da ita?"

Rintse ido tayi sosai dan mummunar fad'uwar da gabanta yayi, dunk'ule hannunta na hagu tayi ta bud'e idonta, hawayen da take so rik'ewa ne suka zubo, cikin rawar murya tace "Kawai daga zamu sakewa aunty Zeituna kwalliya ne fa, shine tace ita ba zatayi ba nace mu zamuyi, kawai shine tace idan ban daina shiga harkarta ba zata kifar dani, daga 'yar k'aramar magana kawai saita mareni, shine ni kuma..."

Shiru tayi ta kasa k'arasawa dan tasan babu abinda zai hanashi gaura mata mari, cikin yanayin muryarshi mai firgita tunani yace "Shine ke kuma me? Kina nufin kice kika rama?"

A hankali ta d'an ja baya tana k'yak'yabta ido da turo baki irin eh nima ramawa nayi, ba tare daya kula dasu Zeinabu ba yasa hannu ya jawo hannunta ya direta gabanshi, kallon Ummy take tana so ta bashi hak'uri kar ya daketa, cikin tsawa yace "Kalleni nan."

Matsakaitan idonta ta zuba cikin nashi, amma ina tsabar kwarjininshi da tsoronshi yasa tayi saurin sunkuyar da kanta k'asa hawaye na zubowa, sake daka mata tsawa yayi yace "Kalleni ido cikin ido, inba haka ba zan gurguntar dake a wurin nan wallahi, kin dai ji na rantse miki."

Kallonshi tayi cikin idon amma hawayen dake ambaliya sun kasa barinta ta fahimci asalin mugun kallon da yake mata, cikin saisaita murya yaja kunnenta sosai yace "Amna wannan sa'arki ce? Tsararki ce ita? Shin ba tana gaba dake ba?"

Bayan hannu tasa tana shan majinar wahala ba tace komai ba, sake murd'e kunnenta yayi yana fad'in "Bani amsa mana ina jinki."

Rintse ido ta sake yi saboda yanda taji har fitsari na k'ok'arin taho mata bata shirya ba, girgiza kai tayi hakan yasa yace mata "K'adangaruwa ce ta haifeki da zaki dinga juya min kai?"

Cikin masifar jin zafin murd'e mata kunne ta sake girgizawa da k'arfin ta tana fad'in "A'a, a'a nace, dan Allah kayi hak'uri yah Ammar."

Turata yayi gaban Hamna yana fad'in "Maza to bata hak'uri kafin ranki ya b'ace."

Juyowa tayi ta kalleshi alamar bata gane ba, belt d'in hannunshi ya gyara yana fad'in "Ko ba zaki bata hak'urin ba ne kike kallona haka?"

Zeinabu ce tace "Ke Amna bansan taurin kai, ki ba yar uwarki hak'uri komai ya wuce."

Ummy ce tayi saurin cewa "Bata hak'uri kinji, shiyasa tun farko na so ku sulhunta kanku kafin kuji ba dad'i."

Yanda ta had'e fuskarta zai nuna maka tabbas zata bayar da hak'urin ne dan anfi k'arfin ta, amma ba dan haka ba ba zata bayar ba, wata harara ta gallawa Hamna da har yanzu ke durk'ushe tace "Kiyi hak'uri."

Tana fad'a ta juya da gudu ta bar d'akin ranta b'ace, cikin takon izza ya dawo gaban Hamna yana kallonta yace "Ke kuma malama kada ki sake saurin d'aga hannunki kika dakar min amarya dan ba jaka bace, bare har ki mareta a fuska wajen da yafi komai daraja, ko ni dole zan koyawa kaina yanda zan dinga tausar kaina ba tare dana mareta a fuska ba saboda tsaro, sannan 'yer uwarki ce ita kamata yayi ku zama kamar aminan juna."

Tunda yace amaryarshi Hamna ta d'ago kai da sauri, haka kawai taji kalmar ta daki zuciyarta sosai, sam bata ji dad'in maganar daya fad'a ba, mik'ewa tayi da niyyar zazzaga masa masifa, dan dama saurin hushin nata ya samo asali ne daga abinda ya mata, shiyasa har ta biyewa yar uwarta sukayi cacar baki, sai dai yana ganin ta mik'e ya juya ya bar d'akin da sauri yana mayar da belt d'in shi, ita ma bayanshi ta bi ta fita daga d'akin haka ma su Jamila da Umaimah, Zeituna kad'ai aka bari tsaye jikinta yayi sanyi ta rasa akan me zatayi tunani, a hankali taja k'afa ta koma ban d'akin ta cire katan jikinta ta shiga wanka, sosai ta jima tana goga sabulu mai dad'in k'amshi wanda taga har wata madara-madara ke fita tsabar kyawun sabulun (Dove kenan), tana idawa sabon maclean da brush data gani ta d'auka ta tsabtace hak'oranta kafin ta fito, mai ta shafa ta shafe jikinta da humra data gani a gaban madubinta sannan ta samu turare ta feshe jikinta, babu abinda ta shafa bayan wannan sai nufa da tayi wajen kaya ta fara dubawa, dama dai lefen da aka mata gaba d'aya guda bakwai ne aka d'inka mata wanda zata fara sakawa, kuma kaf d'inki babu mai kyawun wanda su Umaimah suka dare, dan haka kawai ka d'auki doguwar bak'ar riga ta saka wacce ke cikin lefenta mai kyau ta saka, ita kanta data tsaya gaban madubi sai taga ta canza, duk da babu kwalliya a fuskarta, amma ta haska tayi kyau komai nata ya fito, hatta hasken fatarta ya k'ara fitowa, kallabin kayan ta d'ora ta k'ara fesa turare sannan ta zauna kan gadon tana k'arewa d'akin kallo.

*Bayan wasu awanni* gidan yayi shiru sosai alamar kowa ya kwanta huta gajiya, lieutenant ne da kanshi ya shigo gidan, Alhaji na zaune a farfajiyar gidan, ledar dake hannunshi ya d'an b'oye bayanshi ya durk'usa yace "Alhaji barka da hutawa."

Cike da

Please Login or Register in order to submit comment