Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta shigo, kallon juna sukayi inda yaji zuciyarshi na raya mishi kamar ya mata dukan mutuwa, tana shirin zama yace "Fad'a min nawa kike so na baki da zaisa ki goge wannan d'aukar ba'a iya wayarki kad'ai ba har da k'wak'walwarki ma?"

Tsayawa tayi daga shirin zaman ta kalleshi tace "Ko gaisawa ma ba zaka bari muyi ba?"

A fusace yace "Bana ciki da shirme, karki b'ata min lokaci ke nake sauraro."

Tsaye tayi da kyau tana kallonshi tace "Ina buk'atar naira million arba'in, yau ba sai gobe ba."

Da k'arfi yace "What!"

Matsowa yayi daf da ita ya galleta da wani mari saida ta fad'a kan kujerar da tayi niyyar zama ya nuna kanshi yace "Yanzu dama akan naira million arba'in ne kika sa na aikata zina? Akan wannan banzan kud'in kika saka na aikata abinda ban tab'a aikatawa ba tsawon rayuwa ta? Naira million arba'in kike so kika kasa fitowa ki fad'a min na baki? Nasmat kin cutar dani da rayuwata, ba zan tab'a yafe miki ba har abada."

Mik'ewa tayi tana share hawayen wahalar da suka zubo mata tayi murmushin mugunta tace "Naji, ka tura min kud'in a wannan account d'in yanzu, ba zaka sake gani ba."

Fizgar takardar data mik'o mishi yayi ya nuna mata k'ofa yace "Get out."

Murmushi ta sake mishi ta nufi k'ofa, saida ta bud'e k'ofar zata fita ta juyo da murmushi tace "Mahaifiyata, tana gaisheka, baka canza a yanda muka sanka ba, saidai ka k'ara zafi sosai, kayi sukuwa akan mahaifiyata kamar doki tun zamanin k'uruciya, yau gashi 'yar daka raina kamar 'yar daka haifa a cikinka ita ma kayi sukuwa akanta, a gaskiya da zan samu namiji kamarka da zanji dad'in rayuwa dashi, dan ka zo min a yanda nake son namiji ya kasance min, see u *Dady*."

Tunda ta fara maganar nan kanshi ya fara wani bala'in nauyi, mahaifiyarta, yar daya raina kamar yarsa, wa kenan? Yar daya raina har ya mata aure ita ce *Husna* yayarsu Abdul, to amma ai ba komai tsakaninshi da mahaifiyarsu Safeena, sai dai ko...

Cak yaji tunaninshi ya tsaya kanshi ya kulle, sunan da zuciyarshi ta ambata ne yayi barazanar tafiya da numfashinshi, da k'yar ya iya had'a sunan Sss... al..m...a, k'ara waro ido yayi yace "Kenan Ma'arufa ce? Na shiga uku ni Abbas mena aikata haka?"

Ya d'an jima a wannan halin yana tunanin da sam babu mafita, yana cikin haka yaji wani sak'on ya shigo wayarshi, da sauri ya duba dan a tsorace yake, yana dubawa kuma me zai gani? Sabuwar lamba ce ta turo mishi hotunan Raihan tsirara, zunbur ya tashi tsaye ya rufe ido ya dafe kanshi yana so ya samu kowace irin addu'a a baki amma ya kasa, a karo na biyu sake sakin wayarshi yayi ya fad'i kan lallausan carpet d'in, voice not d'in da aka turo ne yayi saurin d'auka ya bud'e, tattausar muryar Saleem ce yace "Shin da kake nan zaune gida ka tura 'yarka can kasan me take aikatawa ne? To wannan ma sanfuri ne, nan gaba zan turo maka da video yanda nake mu'amulantar ta."

Cikin matsanancin sauri ya nemi lambar Raihan, tana d'auka daga can b'angaren cikin muryar dake son yin kuka yace "Kiyi gaggawa ki shirya kije airport, ki hau duk jirgin da kika samu ki dawo gida *Raihan*."

Tabbas Raihan ta tsorata dan kuwa bata tab'a jin ya kama sunanta ba, cikin sauri kamar yanda yace ta tattaro kayanta ta nufi airport d'in, tayi sa'ar samun jirgin da zai tashi zuwa Abuja, dan haka ta hau aka juyo da ita babu shiri.

Suna gama yawa ya sake yin zaune yana matsa k'irjin shi da yaji ya mishi bala'in zafi, tunanin abinyi yake nema har saida yaji lambar nan ta sake turo mishi da sak'o kamar haka _"Kayi gaggawar aurar da ita, idan ba haka ba zan kafa mata tarihi kuma mummuna, idan bakayi abinda nace ba wannan hotunan zasuje inda baka tsammani ne, domin kuwa zan d'ora su a kafafen yanar gizo ta yanda kowa zaiga tsiraicin 'yarka, a haka ma zata rasa mijin da kuka zab'a mata."_

Had'a kanshi yayi da gwiwa ba tare daya shirya amsar da zai bawa mai turo sak'on ba, shi dai kawai yasan alhaki ne ya fara biyarshi tun yanzu, dama ance idan kayi da 'yar wani za ayi da taka kaima, a hakan kuma yana ganin ko da ace Raihan bata tab'a sanin d'a namiji ba to angama dashi tunda har akaga tsiraicinta, kai shi sam bai ma yarda da babu abinda ya faru ba, tayaya namiji zai samu hotonta haka babu kaya a jiki inhar ba wani abu ne ya shiga tsakaninsu ba? Yana tsaka da wannan tunanin wani sak'on ya sake shigowa cewa _"Tunda baka da lokaci na zanyi abinda ya dace, da fari zan fara tura hotan a wayar mahaifiyarta, daga nan kuma zan sake shi duniya ta gani, ni ba kud'i nake nema a wurinka ba, ka aurar da 'yarka kawai ga wanda ka zab'a mata."_

Sai lokacin ya kira lambar Saleem na d'auka ya canza murya Abbas kuma yace "Bansan ko waye kai ba, amma dai nasan baka nufi na da alkairi, dan Allah karka saki hotunan nan domin kar mutumcin 'yata ya zube, nasan gabarka ba zata wuce dani ba dan haka ka d'auki fansarka a kaina, dan Allah karta shafi iyalina."

Cike da izza yace "Ka fad'i gaskiya, amma ka sani ba zan huce ba har sai naga ka tara taron jama'a zasu shaida d'aurin auren 'yarka."

A tak'aice yace "Zanyi, zan d'aura mata aure da safiyar gobe da Abdul, ban buk'atar had'uwa da kai, amma dan Allah ka goge hotunan nan daga wayarka, ba mutumcin 'yata bace harda ni kaina."

Cike da dariyar iskanci ya amsa da "Saina gani idan kayi abinda nace."

Makullin mota ya zara tare da takardar da Ma'arufa ta bashi yayi gaba ya bar gidan, a hanya tunani kawai yake wanene kuma wannan? Shin tarbiyar daya bawa Raihan kenan? Meyasa haka ta fara faruwa dashi? Wayarshi ya d'auka ya duba takardar nan ya turawa Ma'arufa wannan kud'in, bayan kud'in sunje yana ganin tana kiranshi amma ya k'i dagawa harya isa gidan, falon Sameera ya zarce ya sameta zaune ta gama waya da Bashir tana tambayarshi ko yasan abinda ke faruwa, amma yace mata bai sani ba tun jiya ma da rana rabon da su had'u, tana ganinshi ta mik'e da sauri tana fad'in "Abban Ameer sannu da zuwa, lafiya ka fita daga gida cikin sauri haka?"

Saida ya kalli falon da kyau kafin ya kalleta yace "Idan Raihan ta zo kice ta same ni a falo na."

K'ofar da zata sada shi da falonshi ya nufa ita kuma tace "Raihan kuma? Amma ai bata nan, ko ka manta ne?"

K'ala baice mata ba harya shige, ita kam mamaki da damuwa ne suka hanata zama sai kai da kawowa, haka yara suka dawo daga islamiyya suka sameta, kiran Harira tayi ta had'a ta dasu ita kuma ta ci gaba da tunani, tana haka taji sallamar Raihan, tana juyowa ta ganta da jaka ta kinkimo cikin doguwar riga sai d'an siririn d'an kwalin data d'ora, da sauri ta k'araso ta rumgumeta tace "Ammie na, ya kike?"

D'agota tayi daga jikinta fuskarta cike da damuwa tace "Mamana lafiya? Meyake faruwa ne? Ya kika dawo haka kwatsam? Meyasa Dadynki ke nemanki?"

Cikin sanyi tace "Ammie i don't know, nima kawai Dady ya kirani a waya yace nayi gaggawa na zo, i hope komai lafiya?"

Girgiza kai tayi tace "Ba nace ba Mamana, amma kije yana son ganinki a falon shi."

Ba tare da tunani ko damuwar komai ba ta aje jakarta ta nufi k'ofar tana fad'in "Ok Ammie."

Da sallama ta shiga falon, ganinshi zaune ya d'ora gwiwar hannunshi kan k'afafun shi kanshi k'asa ya had'e hannaye, sai kuma k'afafun shi da yake d'an bunbugasu, sallama uku tayi amma bai iya amsa mata ko d'aya ba, tsoro ne ya fara ziyartar ta amma a haka ta k'arasa kusa dashi ta zauna k'asa cikin taushin murya da sanyi tace "Dady?"

D'ago kai yayi ya sauke kanta, gabanta ne yayi muguwar fad'uwa saboda ganin idonshi jawur kamar yayi kuka, mik'ewa yayi ya shiga bed ya dawo hannunshi rik'e da wata sharb'eb'iyar waya data sanya gudun gabanta tsananta, yana zuwa zaune ya sake yi ya kalleta ya d'auki wayar shi ya mik'o mata cikin rawar murya yace "Raihan waya d'aukeki hotonan?"

Hannu tasa ta karb'a danta gani, da sauri ta dafe k'irji ta d'aga kai ta kalleshi sai taji wata kunyarshi ta rufe ta, sake kallon hoton tayi ta k'ura musu ido, ita ce ke wanka kuma ba'a ban d'akin gidan nan ba na basraba, to kenan waya d'auke ta? Waya bibiyeta haka? Tana cikin kallon taji tsawa daga Abbas tare da kashe ta da mari yana fad'in "Nace waya d'auke ki wannan hoton? Gaban wani d'an iskan kika tub'e?"

Sakin wayar tayi ta dafe kunci hawaye wani na bin wani ta kalleshi a firgice, d'an siririn hannunta ya fizgo ta matso daf dashi cikin k'arajinmurya yace "Ba dake nake magana ba Raihan? Ke yanzu har ni zaki zubarwa da mutumci? Ina ganinki luf-luf yanzu nan ke har kinsan namiji? Raihan meyasa baki fad'a mana kina son aure ba? Amma shine zaki fita waje kina iskanci har ana d'aukar ki ana turo min da hotunan."

Tsaye ya mik'e ya fara zabga mata bulalar nan baji ba k'akk'autawa, Raihan da zafi ya ratsata ta ko ina kuka take tana fad'in "Wallahi Dady ban san waya d'auki hoton nan, ka yarda dani ban tab'a iskanci ba a rayuwata, dan Allah Dady kayi hak'uri karka kashe ni."

Sameera da taji kukan Raihan da gudu ta shigo falon, ta taho a sukwane zata tunkarosu ya d'ago ya d'aga mata hannu da cewa "Wallahi kika k'araso nan dake zan had'a."

Tsayawa tayi tana kallo ya sake cin gaba da dukanta yana fad'in saita fad'a mishi ubanwa ya koya mata iskanci, da gudu Sameera ta sake fita sai part d'in su Ammie, ta sameta tana shirin kabbara sallah azahar, ai tana fad'a mata suka rankayo tare suka shigo, da k'yar Ammie ta dakatar dashi kafin ya tsaya cikin b'acin rai ya kallesu yace "Ko ku shirya ko karku shirya gobe zan aurar da ita kafin ta ja min abin kunya."

Bed d'in shi ya shiga Sameera tayi kan Raihan dake kwance tana kuka, kamata tayi cike da tausayi tana kallon jikinta da duk ya canza ya fita hayyacinshi, tashinta tayi suka tafi d'akin ta ta kwantar da ita, zage mata zuf d'in rigarta tayi ta cire mata ya rage sai bras d'in ta da pant kawai, kallonta Sameera tayi da kyau tace "Raihan ki fad'a min gaskiya, shin kin watsar da tarbiyyar da muka baki ne?"

Zaune tayi ta janyo blanket d'in kan gadon ta rufe jikinta tana kuka tace "Wallahi ban zubar ba, Ammie bansan ya akayi hoton tsiraici na ya fito ba, Ammie ki yarda dani dan Allah."

Sunkuyar da kai tayi tace "Ba zan iya yarda dake ba Raihan, domin kuwa yaran yanzu ka haifesu ne baka haifi halinsu ba."

Ammie dake tsaye ne cike da jimami tace "Ki had'a mata ruwa tayi wanka."

Mik'ewa Sameera tayi inda Ammie ta kalli Raihan da duk jikinta ya sauya tace "Kinsan da gobe yace zai d'aura aurenki da Abdul?"

Da sauri ta kalleta kamar zatayi magana sai kuma tasa kuka tace "Ammie ba damuwa na amince, ni kuma zan tabbatarwa da iyayena a budurwa naje gidan mijina."

♡♡♡♡♡♡♡♡♡

Tun daren jiya Ma'aruf daya fad'awa Meena aikinsu ya kammala ta dinga saka mishi wani tunani tana nuna mishi dukiyar nan fa kamata yayi ace tashi ce shi kad'ai, farko baisa abun akai ba dan ba zai iya cutar da yar uwarsa akan dukiya ba, amma da dare suna zaune d'aki shi da Ma'arufa ya kalleta yace "...


👏👏👏
22/06/2020 à 17:26 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*BADAK'ALA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

👨‍👩‍👧‍👦 _*AHALI NA*_👨‍👩‍👧‍👦

💞 _Kyautarku ce_💕

*Momyn Dady*
*Lubabatu Shehu Shayi*
*Umman Modee*
*Sis Chappa*
*Zeinab*
*Hafsat Yahaya Ali*
*Choukra*
*A~A~S~*
*Maman Abulkhairi*
*Voisine Ruky*
*Maman Tasleem*
*Aisha Gimba*
*Rafi'a*
*Wahabijubaina*
*Hafsat Uba*
*Soumayya mahaman kaka*
*Ummu Khairat*
*Maman Chapa'atu*
*Fasma*

🇳🇪 *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_20_

"Gaskiya nayi farin ciki sosai da kuka amsa kira na, dama kuma nace su turo iyayensu ne domin a samu fahimtar juna sosai, yanzu Alhamdulillah zamu iya tsayar da magana."

Lieutenant ne yace "Hakane Alhaji, kuma dama ai mu ya kamata mu fara zuwa Allah bai nufa ba sai yaran, amma yanzu mun zo muji da kanmu daga bakinku."

Wani hukuncin ubanjigi sosai Labaran ke kallon tsohon saboda zamansu iri d'aya ne irin zaman rak'uman nan, kawai kamar had'in baki sai suka sa hannu suka d'an tura hularsu baya suka shafi goshi, tsam colonel yayi da ido ya kallesu ganin sunyi abun a tare kamar sun tsarashi dama, shi kanshi Labaran satar kallonshi yayi amma malam Rabi'u bai kula da hakan ba, nan suka ci gaba da tattaunawa suka tsayar da magana inda lieutenant ne yace "Idan har zaku lamunce mana zamu so ayi bikin nan da wata d'aya, da yake akwai sauran yan uwanshi da suma duk za'a aurar dasu nan da wata d'ayan, shiyasa muke so ayi lokaci d'aya a gama."

Malam Rabi'u ne ya kalli yan uwan mahaifin Maryama da kuma yayan mahaifiyarta kafin yasa hannu ya maido da hularshi inda take wanda yayi daidai da Labaran ma ya dawo da tashi hular, cikin fara'a yace "Wannan ai ba wani abu bane, dama dalilin da yasa muka nemi ku zo kenan, dan haka ba wani abu kawai."

Farin ciki sukayi inda lieutenant yace "To dama a shirye muka zo, dan haka."

Colonel ya kalla da Labaran suka d'anyi k'usk'us kafin su kalli Junaid dake can gefensu, mik'ewa yayi ya fita jim kad'an saiga yara matasa suna shigo da akwatina masu kyau guda bakwai da kuma goro, nan suka tsayar da ranar daidai da sauran bikin tare da bayar da duk abinda ya dace, girkin da akayi dominsu aka fito musu da shi, har zasu fara ci sunawa juna bismillah muryar Labaran da malam a tare suka ce "A'a Alhamdulillah, ai ni bana cin naman tsintsaye."

"A'a Alhamdulillah, ai ni bana cin naman tsintsaye."

Wannan lokacin kallon juna sukayi a tare, murmushin da sukayi ne ya bayyanar da wani tabo dake fitowa a duka fuskokinsu a duk sanda sukayi dariya a gefen kumatunsu na dama, gaban Labaran ne yaji ya sake fad'uwa, amma banda malam da shi ko a jikinshi ma, haka dai suka gama cikin mutumta juna da girmamawa suka sake dawowa.

*Tun* daren jiya Alhaji ya d'aure wa Hajia yace fa babu fashi auren lieutenant, a k'arshe ma cewa yayi ta mishi lissafin abinda za'a buk'ata ya bayar, kamar wasa kuwa da safe haka ya sake sakata gaba saida tace kawai ya bada duk abinda yaga dama, aifa nan ya bata mamaki ta hanyar bata babbar enveloppe da kud'i har million uku ciki yace tayi idan ma basu isa ba tayi magana ya k'ara mata, sai ga Hajajju na kira a waya harda fita ita da drebanta wajen siyo kayan lefe da saurensu, amma ji take kamar ta mutu dan sam Zeituna bata mata ba, tana ganin bata dace da ajin d'an ta ba duk da yanzu d'an nata ya zama tsoho.
😛

Da yamma Alhaji ya had'a kan yan uwa da abokan arzik'i suka kai akwati guda goma sha shida wanda kowace saida aka mata k'at da kaya a ciki gidansu Zeituna da goro salka biyu da kuma 1 million kud'in d'inkin kaya, kad'an ya rage Zeituna ta mutu tsabar bugawar da zuciyarta tayi, ita fa har yau a mafarki take ji da kuma ganin abun, ba zata tab'a yarda wai lieutenant ne zata aura ba, nan fa unguwa ta d'auki tsegumi k'asa k'asa anayi, wasu na fad'in ya siyar da ita saboda kud'i, wasu na fad'in kawai akwai surkullen da akayi har babban mutum kamar wannan ya kalli Zeituna yace yana sonta, to haka dai akayi aka gama Hajia ita ma kamar ta mutu.

*Ammar* na gama cin abinci ya kalli aunty yace "Aunty zan d'an fita, watak'ila ma na wuce ta wajen mutumin (mijinta) dan nasan akwai hira a bakinshi."

Dariya tayi tace "Ai kam kamar ka sani, kasan shi baka raba shi da zance, amma kafin nan muyi hira mana."

A tsanake ya kalleta ya sauke ajiyar zuciya, d'orawa tayi da "Ammar meke faruwa a gida? Tun shigowarka na hango damuwa tare da kai, sannan ga hannunka da bandeji, bugu da k'ari baka tab'a zuwan safe irin haka ba."

Wata ajiyar zuciya ya sake saukewa amma baice komai ba, hakan yasa tayi murmushi tace "Hajia ce ko? Ammar ou dinga hak'uri da ita wata rana sai labari, ka duba ni ka gani mana, yanzu haka fa su Hamna sunfi shekara d'aya rabonsu da nan, kuma sun fad'a min suna son zuwa Hajia dai ce bata amince musu ba, amma kaga nayi hak'uri duk da cewar bayan rabuwata da mahaifinsu dana auri *Shu'aib* bamu samu haihuwa ba har yanzu, amma hakan baya damu na tunda ina tare da wanda zuciyata ke so, kaga dai ba cikin birni nake ba, sannan ba cikin daula ba kamar gidanku, amma wallahi hakan yafi min komai, kaima da wannan nake shawartarka da akayi hak'uri, idan ka samu wacce kake so sai kaga komai ya wuce."

Cike da gamsuwa da bayaninta ya kalleta yace "Aunty wannan karan ma ba Hajia bace Alhaji ne, wai aunty jiya Alhaji yake cewa wai ya nemawa Abba auren yarinyar nan yar aiki, Zubaina take ko uwar wa ma? Kuma wai za'a d'aura auren ranar juma'a ta gobe, kiji fa?"

Ita kanta wani banbarak'wai taji abun, amma sanin halin yaron nata yasa tayi murmushi tace "To yarona meye na tashin hankali a ciki? Shi aure ai lokaci ne, nasan kuma kasan da haka, sanin kanka ne duk iyayen nan naku matansu d'aya d'aya ne, tunda har yanzu Alhaji ya yanke wannan hukuncin to ku rumgumi k'addara mana, watak'ila fa tsananin rabo ne, kuma inhar ya kasance rabo ne to ka sani wallahi ba kai ba ko Hajia ce tayi yunk'urin hanawa wannan rabon zai iya halakata, ko da kuwa zata gitta masa tsinuwarta ce, dan rabon 'ya'ya idan ya koka wallahi sai sun zo duniya ko duka mutanen duniya basa so, dan haka ni dai abinda zan shawarce ka dashi shine kuyi hak'uri dan Allah, kar ka d'agawa iyayenka hankali Ammar, kuyi fatan yarinyar ta zama alkairi ga mahaifinka kawai da kuma mahaifiyarka."

Kallonta yayi a nutse yace "Shikenan Aunty, ni zan fita saina dawo."

Mik'ewa yayi ya saka takalminshi ta kalleshi tace "Baka fad'a min cewa Hajia ta zab'a muku yan uwanku ba?"

Murmushi yayi kawai ya shafa sumar kanshi ya fice, girgiza kai tayi dan tasan bai gamsu da abinda ta fad'a mishi ba, yana fita kuwa shawagi ya dinga yi ya jima bakin ruwa yana kallon gudanarsu, daga nan kuma ya zarce bakin kasuwa wajen mijin auntyn suka sha hira, a tak'aice tare suka wuni har yamma suka dawo gida, nan ma wani shafi hira suka bud'e kamar d'a da uba kafin daga bisani zuwa *05:56* ya d'auko hanya, saida yayi sallah ya wuce gida kai tsaye da tunanin wacce zai samu kuma yau.

*Bayan* dawowarsu da yamma Labaran na d'akin mahaifiyarshi da abinci gabanshi amma tunani ne fal a ranshi, lura da hakan yasa Husseina kallonshi cike da kulawa tace "Ga damuwa ina gani a fuskarka, sai dai bansan dalilin da yasa kake son b'oye min ba?"

Da d'an murmushi ya kalleta yace "Ba komai Hajiata, kawai dai gajiya ce sai kuma yau da gobe."

Murmushi itama tayi kawai ta share maganar, d'ibar wata loma yayi zai kai baki sai kuma ya tsaya ya kalleta saboda tsikararsa da zuciyarshi tayi yace "Hajiata, zan iya tambayarki wani abu?"

Kallonshi tayi tace "Zaka iya mana, ina jinka."

Kallonta yayi yace "Hajia kiyi alk'awarin ranki ba zai b'ace ba da tambayar da zan miki?"

Annurin fuskarta ne ya b'ace ta kalleshi da kyau tace "Ka fad'a ina jinka."

Cike da fargaba ya d'anyi k'asa da kanshi yace "Hajia dama...dama in..ina son...sanin..cika...kken bayani...ne akan..." Shiru yayi ya kalleta hakan yasa ta kalleshi tace "Akan me kake son sani?"

Sauke kanshi yayi yace "A...kan mahaifi na." Saida ya sauke wata ajiyar zuciya mai nauyi saboda abune da shi dai rabon daya fad'a tun yana shekara ashirin da biyar a duniya, k'ura mishi ido tayi tana kallo wanda hakan ya haifar da zubar hawayenta, hijabinta ta saka tana share hawaye, a tsorace ya matsa kuma da ita yasa hannu yana share mata hawayen yana fad'in "Dan Allah Hajiata kiyi hak'uri ki gafarce ni, Hajiata ki daina zubar da hawayenki dan Allah indai akan abinda na fad'a ne, na hak'uri da son sanin abinda nake son sani."

Cikin kuka da son bayyanar da abinda ke ranta tace "Alhaji mahaifinka ya cuceni, ya cutar da rayuwata, ya lalata min k'uruciya ta, sanadiyar abinda ya aikata min har yanzu nake zaune a matsayin bazawara, mahaifina har ya mutu yana hushi dani saboda abinda ya faru dani, Alhaji meyasa zaka min maganar shi? Wannan tsinann..."

Da sauri ya rufe mata baki saboda jin hakan ba zai mishi dad'i ba, duk da ta hanyar da bata dace aka same shi ba kuma bai ma san waye mahaifin nashi ba, amma dai ba zai so jin tsinuwarta akan shi ba, hak'uri ya dinga bata yace ba zai sake maganar ba ta hak'ura kawai, saida tayi shiru ta kalleshi tace "To ka ci abincin naka."

Da sauri ya koma kan kujerar yace "To Hajiata zan ci, kiyi hak'uri dan Allah." Nan ya fara aika abincin ba dan yana masa dad'i ba sai dan faranta mata rai kawai.

Ana idar da sallah magrib Hamna ta shirya zuwa kan amarya ba tare da kowa yasan fitarta ba a gidan, Husseina ce a falo zaune ta k'walla mata kira saboda sunyi magana da Alhaji akan hidimar bikin lieutenant, yanzu haka ta kirata ne dan taje ta siyo mata pliwa dasu sukari da sauran kayan had'in biscuit da cincin na tarban bak'i, Amna dake kwance kan gado da doguwar riga bak'a da kallabinta, rigar ta mata kyau sosai ta fito mata da gwagwab'an mazaunanta da k'irarta, tashi tayi ta fito tana amsawa a matsayin Hamna (baki daddara ba kenan)?, tana zuwa ta zauna kusa da ita tace "Hajia gani."

Kallonta Husseina tayi ita dai bata ga wani banbanci ba, domin kuwa akwai kwalliya a fuskarta wacce ta b'oye duhun da take dashi, sai dai bata ga dogon gashi kwance a baya ba, k'aramar jakar hannunta ta d'auka ta fito da kud'i ta mik'o mata tace "Hamna wajen *Ilu* zakije ki siyo mana wannan kayan." Ta fad'a da mik'a mata takardar da tasa aka rubuta mata kayan dan karta manta ita ma.

Amsa tayi tace "To Hajia." Mik'ewa tayi ta shiga d'akin su ta d'auko makullin moto ta fito, har ta wuce Husseina tace "Hamna." Cak ta tsaya da tunanin ko ta ganeta, a hankali ta juyo ta kalleta ita kuma tace "Yau wace rana Hamna na aike ki baki ce a kawo kud'in mai ba."

Wurga yan matsakaitan idonta tayi ta sauke b'oyayyar ajiyar zuciya tace "Hajia ai akwai mai."

Girgiza kai Husseina tayi tace "Dama can ai iskanci ne kesa kike cewa babu mai."

Yanda tasan idan Hamna ce za tayi haka kuwa tayi sumbatar hannunta tayi ta jefa ma Husseina tace "Saina dawo sai ki biya kud'in aiki."

Da murmushi kawai ta bita har ta fice, motonta ta hau ta tsaya bakin k'ofa tayi oda wanda yasa mai gadi bud'e mata k'ofa, ta murd'a zata fita kenan motar Ammar ta kutso ciki shima, yanda hasken fitilun motar ya d'auke mata ido yasa tasa bayan hannunta ta rufe ido, ganin haka yasa ya k'i kashe hasken sai k'urawa bakinta ido da yayi wanda shi kad'ai ya fito fili, a hankali ya lumshe ido saboda wani tunani da yayi yanzun nan, ina ma ace matarshi ce shi kam da ya samu nutsuwa a tare da ita a halin da yake ciki na rashin

Please Login or Register in order to submit comment