Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yau zan fara addu'a Allah ya cire min sonka, tunda dai dan kaga ina sonka ne kake wahalar dani, me ye gare ni da ba zaka iya rayuwa dani ni kad'ai ba? Kullum tunani na shine yanda zan faranta maka amma kai ba haka ba."

Da sauro ya zauna kusanta ya rumgumota a jikinshi yana fad'in "Kai kai kai Hamna, karki fara wannan addua'r dan Allah, kinsan kuwa yanda nake ji idan kina wannan sababin akan kishina? Wallahi karki tona raina kiji farin cikin da nake, kamar yanda nake kishinki nake jin zan iya komai haka nake so ke ma kiji a kaina, kiyi hak'uri kinji."

Kaallonshi tayi tace "To wacece ta kiraka yanzu?"

Wayar ya fito da ita ya mik'a mata yace "Duba ki gani."

Dubawa tayi kam ta ga sunan Sayyada, kallonshi tayi tace "Sayyada ce ta kiraka ba zaka iya magana da ita a gabana saika fita, wani abu ne tsakaninku?"

Da sauri ya dafe k'irji yace "Ni? Wallahi babu komai, ki yarda dani."

Kallonshi tayi da kyau tace "Allah yasa haka, amma ka sani Ammar duk ranar dana ji wani abu ya fito tsakaninku mai kama da soyayya ko aure saina maka sabon yanka."

😂😎

Zaro ido yayi yasa tafukan hannayenshi ya rufe baki yana fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, Hamna gaba d'aya fa anan mazan suke."

Ba alamar wasa tace "Saboda nasan anan suke d'in ai shiyasa suke alamta maka daka kalli matar da ba taka ba ai."

Tab'e baki yayi yace "Gwara ki kashe ni ai da ki tab'a min kayan aiki na."

Murmushi tayi tace "Ai saboda su d'in ne zakayi sha'awar k'ara aure."

Kallonta yayi yace "Ke ma ba zaki iya zama dani ba ai idan da bana tsoratarwar nan."

Cike da tabbaci tace "Zan iya mana, kuma ita Sayyada ai zata iya tunda yar uwarka ce."

Mik'ewa yayi yace "Ke babu aure tsakani na da ita fa."

Ita ma tsayen ta mik'e tana fad'in "Inji wa yace? Ai ko su Abba akwai aure tsakaninsu da ita bare kuma kai."

Ba tare daya kalleta ba yace "Ni ai Sayyada ma bata cikin tsarin irin matan da nake so, ni nafi son masu manyan cinya da mazaunai yanda idan na shiga zaiyi luf abuna."

Kallon sama da k'asa ta mishi tana fad'in "Kace haka mana, kafi son irina yanda zaka ji dad'in b'arka mu kana d'inkemu."

Dariya yayi yace "Ai da kinga na miki d'inki to kin b'ata min rai ne."

"To me yasa ba zaka hukunta ni ta wata hanyar ba sai wannan? Kana so ka lalata ni ne?"

Saida ya jawota jikinshi yace "Babu abinda zai faru, kayana mallakina da ni kad'ai ke da hurumin shigarsu, nasan yanda zan ci gaba da tafiyar dake."

A daren bayan ya fita Sayyada ta zo tare da masu cake d'in da aka bawa suyi, shi kad'ai ma abun birgewa ne kamar kayi ta kallo, ga kyaututtuka daya mata na bazata da gigita tunani, tayi farin ciki sosai tare da mishi godiya.


*Rayuwa dama haka*, duk son kwalliya da k'walisar Hajia tsufa ya kasa barinta ta ci gaba, inda yanzu ta fara rud'ewa wani abun idan tayi sai an kalli juna, ita da Husseina zamu iya kiransu da tsofi masu taurin rai, dan har yanzu suna nan a cikin gidan ana ta damawa dasu ana kuma fama dasu, yanzu Ummy ce kawai mai fad'a a ji a gidan a cikin mata dai, komai sai ace Ummy Ummy, sai dai kuma yanzu gidan babu hayaniya kamar da, dan tunda Ammar ya tashi kowa ya k'wallafa rai yana so ya tashi, a hankali duk sukayi nesa dasu sai dai su kawo musu ziyara.

Har yanzu Amar na fama da Umaimah wacce ta kasa fahimtar inda duniya tasa gaba, sai dai farin cikinshi d'aya Farisa, babban sake da tayi shine barin Farisa ta fahimci irin zaman da suke, daga sanda ta gane saita d'auri niyyar faranta masa, kuma akan haka take yanzu, in dai ba larura ta yau da kullum ba bata yarda ya sameta da k'azanta ba ko da ba ranar aikinta bane, kullum cikin gyaran gidanta da jikinta take, shima kuma yanzu yayi wuri ya aje Umaimah idan ta fara bala'i saiya bar mata wurin, haka ya zage damtse kamar yaro shima yana ta kwasar soyayyarshi da ita, baya jin nauyi ko k'yashin yi mata abu ko million nawa yake, haka zaman nasu ke tafiya farin ciki a hannun dama bak'in ciki a hannu hagu.

Su Junaid ma da Salma da kuma Jibril da Jamila da Zeinab da Jamil duk dai rayuwa ce irin ta yau da kullum, yau farin ciki gobe bak'in ciki sai dai farin cikin shi yafi yawa, sab'ani ne da dama dole a same shi tsakanin mutane bare kuma ma'aurata.

B'angaren Amarya Huda ma tana farin cikin zamanta, kullum suka d'an samu sab'ani ko k'arami ne sai yace karta fad'awa tonton Ammar, dan ya samu labarinshi shi har ga Allah tsoronshi yake, da haka Huda ke tak'ama tana murza rayuwarta ita ma. Matsalar mahaifiyarta dai ce ke d'an mata cikas wani lokacin, duk da har yanzu a dangin mijinta babu wanda ya kalleta yace yar karuwa, amma tana jin kunyar kasancewarta yar Mari dan babu shiriya a gabanta, ta zo gidanta sau d'aya amma saida ta fito fili ta fad'a mata ta dinga canza shiga indai har zata zo gidanta, irin bala'in data gani a ranar kamar zata cinyeta d'anya, ita dai bata biye mata ba tayi ta gama sannan tace ta bata kud'in mota, ko da ta bata ta tafiyarta ko sallamar arzik'i basuyi ba.

Gambo duk da baya kan muk'aminshi amma har yanzu ana damawa dasu a siyaya, Hajia tace ya dawo amma ya kasa dawowa saboda ya saba zaman can, saidai ya zo yayi kwanaki har satittika ma sannan ya koma, Aissata ma na nan banda buga mulkinta babu abinda take yi, shiyasa aka ce *wata shari'ar sai a lahira*.

A k'arshe dai ta samu mijin aure bayan ta kwashe shekara *talatin* cir a duniya, kasancewarta mai k'aramin jiki yasa ba zaka ga shekarun a jikinta ba sai a fuska, Sayyada kenan (my besty na), Hamna sun shiga hidima sosai ba kama hannun yaro inda ta d'auki nauyin gyaran amarya da kanta.

Yau ake kamun amarya, kuma ta rok'i Ammar ya kaita yace babu inda zata je da tsohon ciki, saida ya fita ya bar gidan ganin a gidansu Hajia ne sunfi kusa da plaza kawai ta shirya tare da Ameera ta tuk'a motar Ummy suka tafi.

Bata tab'a tsammanin yasan mijin da zata aura ba dan bai tab'a fad'a mata ba, bata kula da motarsa ba a filin wurin saida ta shiga can ciki, hangoshi tayi cikin abokansu suna ta hira, rik'e Ameera tayi a hankali ta shiga juyawa da nufin su koma, saida ta sauka kan matakala ta tsaya tana sauke ajiyar zuciya, kallon Ameera tayi tace "Beby Allah ya taimakemu bai ganmu, yau da cire mana wando ta kai."

Dariya Ameera tayi tace "Ummy mu tafi to, ni ke nake tsoro ma yaje gida yayi ta miki masifa."

Dariya tayi ta kama hannunta suka sauka, saida ta kama murfin k'ofa zata bud'e ta shiga taji message ya shigo wayarta, ko da ta bud'a message ne kamar haka.

_"Mrs Ammar Gaga, tun kafin ki shigo numfashina ya canza salon bugawarsa, hakan ya tabbatar min kina kusantowa gareni, taya kike tunanin na barki sakaka da har zaki iya min satar hanya, kuje gida sai na zo zamu had'u, ki kula da kanki."_

Lahaula, shikenan ta *faru* ta *k'are*, kallon Ameera tayi tace "Baby ya ganmu fa."

Zaro ido tayi tace "Lah Ummy mun shiga uku, yau zamu sha bulala a gida."


*_Washhhhhh Allah, na tsaya iya nan, dramarsu kullum aukuwa take, kunsan waye Ammar nasan kunsan me zai faru idan ya koma, baya barin ta kwana kamar yanda baya mantuwa da yafiya, baya bawa mak'iyinsa baya sai dai ya tareshi duk a rugumtsuma, see u Ammar, yan matanka na nan lodi lodi birjik suna jiran amsar amincewa buk'atar aurensu daga bakinka, ni ban tab'a jarumi mai farin jini irinka ba ma, ga kuma santaleliyar k'anwa daka samu uwar yarinyata wacce ke shirye da take bayanka bata son b'acin ranka, ni kuma uwar d'akinka duk muna bada gaisuwa shugaba. Auntynmu Hamna gaisuwa gareki ta musamman, masoyanki na nan tare dake, Allah k'ara had'a kanku tare da baki hak'uri da juriya na zama da yayan uwar jaririyata, kishiyoyinki ma suna gaisheki tare da rok'on alfarmar ki barsu su shigo suma su samu nasu rabon d'inkin.🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️*😂


*Alhamdulillah*

*Alhamdulillah*

*Alhamdulillah*


*Yan uwa mun kawo k'arshen BADAK'ALA, sai mun had'e a SALAHADEEN da SARAH*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment