Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

Ammar Hassan Gaga."

Zaro ido yayi ya bashi hannu yace "Abokina kace yan biyun lieutenant ne? Ah masha Allah, zaku iya tafiya kawai, Allah ya tsare Allah ya raba lafiya."

Hannu ya bashi suka gaisa kafin ya kalli waccen yana hararenshi suka wuce, suna tafiya ya kalleta ya mata rank'washin tsiya a kai yana fad'in "Shegiya yanzu baga anfanin saka babban mayafi ba, da wannan shegen siririn ne a jikinki da yanzu tayaya zan iya kallonki na ce matat..." Sai kuma yayi shiru, turo baki tayi gaba ba tace komai ba har suka isa gida, saida suka tsaya sun fito a tare suka nufi hanyar b'angaren su, tana daf da shiga falon ta juyo ta kalleshi tace "Allah ya isa rank'washi na da kayi."

Juyowa yayi hakan yasa ta arta a guje tayi falon, girgiza kai yayi a ranshi yace "Ai zamu had'u ne, zan miki horon da har ki mutu ba zaki manta dani ba."

Tana shiga falon ta tsaya das saboda Hajia data samu zaune kan kujerarta fuskarta a had'e sai kuma Ummy da Zeinabu gefenta da alama fad'a ta musu ke take musu, ko kuma dai tuhumarsu take, cikin tsananin fad'uwar gaba da sanyin jikin ta tako zuwa tsakiyar falon, murya k'asa k'asa tace "Assalama alaikum."

Kallonta kawai sukayi amma babu wanda ya amsa, nufa hanyar da zata sada su da d'akin su tayi, a hankali Hajia tace "Zo nan."

Kamar wacce k'waiya fashe ma a ciki haka ta taho ta durk'usa gabanta kanta k'asa, tsaye Hajia ta mik'e hakan kuma baisa Hamna yunk'urin kare kanta ba dan bata san Hajia da saurin hannu ba inba abu ya kai mak'ura ba, bata ankara ba taji saukar yatsu biyar, tana dafe kunci ta d'ago ta kalleta yayin da Hajia kuma tace "Ke har ni zaki mayar wata mahaukaciya a gidan nan, ina cikin gidan nan amma kike nema kiyi rayuwar da kika ga dama, me kike so ki zama Hamna? Yar iska? So kike ki zama kamar uwarki kenan? To baki isa ba wallahi, yanzu fad'a min a cikinsu wacece tasan da fitarki a gidan nan?"

Ta fad'a tana nuna su Ummy, Hamna kuma babu abinda ya mata zafi kamar cewa wai tana so ta zama yar iska kamar uwarta, kenan mahaifiyar tasu ce yar iska? Lallai ni na jawa mahaifiyarmu wannan wulak'ancin, tsawa Hajia ta mata tace "Dake nake magana kina jina."

Kallonsu Ummy tayi ta girgiza kai tace "Basu san fita ta ba."

Cikin masifa tace "To gidan ubanwa kika je? Me kika je yi da baki dawo ba sai yanzu? Hamna kina 'ya mace ace ba kya cikin gidanku kina waje, to me kikeyi? Kuma ba a motonku kika fita ba, kenan wani ne ya zo ya d'auke ki kuma ya dawo dake."

Kallonta Hamna tayi tace "Wallahi Hajia adaidaita na shiga, kuma wurin kan amarya ne muka tafi, nasan idan na tambaya ba za'a barni ba shiyasa, kuma ki tambayi yah Ammar kiji tare ma muka dawo yanzun."


Kallonsu Ummy tayi tace "Ku b'ace min da gani ku Allah ya taimake ku." Tashi sukayi inda ita kuma ta koma ta zauna tana kallonta tace "Tare da Ammar?"

Kai ta gyad'a alamar eh, amma me Hajia za tace sai cewa tayi "To na sani ko tare dashi kuke yawon iskancin na ku, dan ni ban yarda dake ba, shi kuma dama idonshi tsakar kai suke ba kunya ne dashi ba, yanzu idan na kira shi zai iya fad'a min abinda ya faru tsakanin ke da shi."

Mamaki ne yasa Hamna kallon Hajia kawai ta kasa cewa komai, hakan yasa Hajia cewa "Je kirawo min shi, dan wallahi ko iskanci kuke yau saina kawo k'arshen shi a gidan nan, watak'ila dama wannan dalilin ne yasa kika k'i amince da auren nan."

Mik'ewa tayi ta fita jiki a sanyaye da tunanin halin kakarsu, tana zuwa k'ofar d'akin ta tsaya dan tana jin hayaniyarsu, sallama tayi Amar ya amsa, ba tare data shiga ba tace "Yah Amar Hajia ke son ganin yah Ammar yanzu."

Amar ne ya amsa da "Yana d'aki bari na fad'a masa." Juyawa tayi ta fita shi kuma ya shiga ya fad'awa Ammar, fitowa yayi babu ko riga zai fita Junaid yace "Haka kuma za'a tafi wurin Hajiar?"

Ko kallonshi baiyi ba yace "To ko nine Hassan meye a ciki? Ba haihuwarmu tayi ba? Tunda ita ko dare da Allah yasa mana mu samu nutsuwa a cikinshi bata bari mu nutsun ai sai mu fara zuwa mata tsirara inta neme mu."

Jibril dai da abun duniya ya isheshi da kallo kawai ya bishi, ai kuwa yana shiga Hajia ta kalleshi da wani mamaki, zaune yayi kujerar dake kallonta ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya wanda hakan yasa suke iya ganin kwantaccen gashin k'afar shi mai silb'i, ido cikin ido ya kalli Hajiar yace "Mutan makka gani, ance kina kira na yanzu a daren nan, shine nace bara na zo da gaggawa kar azo ko zuciyar ce ta fara bugawa ba daidai ba."

A murtuke ta kalleshi tace "Duk maitarka wallahi zuciyata tafi k'arfin ka nuna k'warewarka a kanta, shege kenan burinka kenan a kai na."

Murmushi ya mata na shegantaka yace "To in kuwa hakane baki shawara mana? Ki rage b'acin rai da sakawa mutane idanu, ki dinga samun isashen bacci hakan zaisa ki dinga samun nutsuwa, sannan ki rage yawon surutu da hayaniya, inba haka ba Allah in kika bari zuciyarki ta kamu da ciwo da hannu na zan parkaki na fito da zuciyar na 'yar da ita."

Murmushi Hamna tayi harda rufe baki inda Hajia ta gama cika, cikin fad'a tace "To yanzu wace rashin d'a'ar ceta saka shigo min falo babu riga?"

Murmushi ya mata yasa hannu ya shafi k'irjin shi har zuwa kan nonon shi yace "To dan kin kalli wannan meye? Ko jariri dai ba zai iya tsotsar wannan ba, kuma ma Hajajju me kike tsammani dama ga marar mata wanda yayi shirin kwanciya."

Tsaki tayi yayin da Hamna ta sunkuyar da kai kamar tace k'asa bud'e na shiga, tana mamakin wannan rashin kunya tashi ita kam, a nutse ta kalleshi tace "Wannan take fad'a min wai tare kuka shigo yanzu daga wajen kan amarya, shine nake so naji daga bakinka?"

Kallon Hamna yayi wacce ita ma ta kalleshi, murmushi yayi mata wanda ta tabbatar na mugunta ne, sai yanzu ta tuna Allah ya isar data masa, take tace "Na shiga uku."

Kallon Hajia yayi yana murmushi yace "...

*Addu'arku*๐Ÿ‘
23/06/2020 ร  13:57 - Ummulkhairi: ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
*BADAK'ALA*
๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ _*AHALI NA*_๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_22_


Murmushi yayi yace "Ni kuma? A ina muka had'u? Ni ina zuwa wannan shirmen banzan ne da har zamu had'u dake? Hajajju ki matseta ta fad'a miki inda ta tafi, amma ni karki tambaye ni, saida safenku."

Mik'ewa yayi kam ya nufi k'ofa zai fita, juyowa yayi ya kalli Hamna wacce ta juyo ita ma tana kallonshi kamar ta d'ura mishi ashar, wata 'yar iskar shoki ya kwaso daga k'asa yayi sama da hannu ya rufe rabin fuskarshi yana dariya, haushi ne ya k'ara kashe Hamna wato irin yanda take yi masa ne yayi, kashe mata ido d'aya yayi ya fice daga falon, Hajia kuma kallon Hamna tayi tace "Wallahi idan kika sake fita daga gidan nan ba da izini na ba wallahi dake za'a d'aura auren nan, tashi ki bani wuri."

Mik'ewa tayi jiki a sanyaye ta nufi d'akin su ita ma Hajia nata d'akin ta shiga, tana shiga ta samu Amna kwance kan gado da rabin fuskarta harya kumbura ga jini daya kwanta a idonta d'aya, kaya ta fara cirewa inda Amna ta mik'e tace "Yawwa kin dawo, Hamna gaskiya daga yau ba zan sake taimakonki ba idan kina son fita a gidan nan, ki nemi izini idan an barki ki fita amma ni ba zan sake amsa sunanki ba idan ba kya nan."

Juyowa tayi da niyyar sauke mata kwadon bala'i sai kuma taga fuskarta a kumbure, da sauri ta matso ta zauna kusanta tace "Amna meya sameki a fuska haka? Ba dai dukanki sukayi ba?"

Cikin b'acin rai tace "Eh mana duka na yayi, ki duba kiga yanda ya rugurguza min fuska kamar wata jaka."

Da mamaki tace "Waya dake ki haka?"

A k'ufule tace " Wa fa idan ba boss ba."

Kwance tayi saboda tafasar da zuciyarta keyi ita kuma shiru tayi ta mik'e ta ci gaba da cire kayanta, ban d'aki ta nufa tana fad'in "Wallahi saina d'aukar miki fansa, ba dai ya dake ki ba, bak'in mugu kawai azzalumi."

Tab'e baki tayi a ranta tace "Ga ki gashi ai idan ke ma kina son ganin fuskarki kamar ni d'in ne."

*Washe gari* da safe Hajia na zaune a falo sai Husseina gefenta amma babu mai kallon wani, Hajia ce cikin yamutsar fuska tace "Ki fad'awa jikanki daga yau zuwa gobe ina son fara had'a kayan auren jikokina, dan haka ina so naga yayi bajinta ta hanyar kashe kud'i sosai, dan Jamila yar dangi ce mai nasaba da asali na k'warai."

Murmushi Husseina tayi tace "Gashi kuma anyi sa'a mahaifin Jibril ya tara masa dukiya, kuma shi kanshi ma zai iya d'aukar nauyin duk wani caji da zaki mishi akan auren jikarki, dan haka karki damu kanki indai akan matsalar kud'i, akwaisu kuma za'a kashe ko nawa ne."

Tab'e baki tayi ta harareta ta ci gaba da danna wayarta, Ummy ta fito a shirye zata tafi wurin aiki, sunkuyawa tayi wurin Hajia ta gaisheta, amsa mata tayi ta juya zata fita tace "Auren mijinki za ayi gobe, bai kamata ace kin d'auki hutun aiki ba?"

Tsayawa tayi ta kalleta sai dai kuma bata da abun fad'a, idan ma tace ta bayar da uzuri zata ce ai asibitin tasu ce, dan haka Ummy ta girgiza kai alamar to ta juya jiki a sanyaye zata koma d'aki kuma ta sake cewa "Yau zuwa gobe yaranku su had'a min akwatinansu, sannan babu maganar dangantaka ko alak'a, komai ina so naga anyi na bajinta yanda zai nuna harkar manya."

Ummy da Zeinabu ne suka jinjina kai daga inda suke tsaye kafin Ummy ta koma d'aki, Hamna ce ta fito tare da Amna cikin shirinsu na makaranta, gaishe da Hajia sukayi suka nufi k'ofa, suna fita Hamna ta fito da powder ta ruwa daga jakarta ta matsa a hannunta sosai, kallon Amna tayi tace "Ki fitar da moton ina zuwa."

"Ina zaki je?" Cewar Amna, komai ba tace mata ba tana kallo ta nufi b'angaren su Ammar, ita ma bayanta tabi dan nemo izini wajen boss, suna kusan kaiwa Amar ya fito daga d'akin shigarshi sam bata bambamta data Ammar ba, sai dai kuma fuskarshi babu annuri a tare da ita, gashi ya saka farin gilashi a ido wanda yasa ya k'ara fitowa sak Ammar, Hamna na ganin haka tayi murmushin mugunta ta tunkareshi da sauri ta sanda kanta k'asa ta fara lalube lalube a jakarta kamar mai neman wani abu, da gangan ta kaiwa Amar karo tare da saka hannayenta bibbiyu ta damk'o rigarshi tana sakin yar k'ara alamar bata lura ba, kallon juna sukayi ta kalli rigarshi da powder ta fito a rigar mai hasken sararin samaniya, ido ta zaro alamar tsorata tasa hannayen ta matsa kusa dashi ta fara kakkab'e mishi amma a zahiri k'ara damuk'a rigar take tana fad'in "Wayyo Allah na boss kayi hak'uri, kayi hak'uri dan Allah ban kula ba ko kad'an, wai ni a ina ma na samu dattin nan?"

Ta tambayi kanta tana kallon hannayen nata, Amar da ido kawai ya zuba mata kasa magana yayi sai karantar fuskarta da yake, ganin kallon da yake mata yasa ta ja baya ta fara tattare siket d'inta, yana lura da haka yayi saurin cewa "Karki bawa kanki wahala, ga boss d'in can."

Ya fad'a yana nuna mata Ammar dake bayansu jikin motarshi tsaye duk yana kallon abinda ke faruwa ya rumgume hannayen shi a k'irji, a hankali ya taso ya fara takowa ya zuba hannayenshi cikin aljihun wandonshi yana tunkarosu, tana ganin haka da gudun tsiya hijabin daya tilasta mata sakawa yana tashi sama shima ta fita a gidan har tana bangaje mai gadi, da kallo ya bita inda Amar ya bita da dariya, kallon Ammar yayi yace "Allah ya isa wallahi, akwai muguntar daka mata wacce tasa ta rama a kaina."

Tab'e baki yayi ya mayar da kallonshi kan Amna yana fad'in "Kai ka siya da kud'in ka, ni nace kayi shiga irin tawa?"

K'wafa Amar yayi ya juya ya koma ciki dan sake shiri, Ammar kuma matsowa yayi kusan Amna wacce tayi saurin cewa "Ina kwana yah Ammar."

Ba tare daya d'auke idonshi daga kan fuskarta ba yace "Izinin fita ne kika zo nema?"

Da tsoro fal a idonta ta jinjina masa kai alamar eh, matsowa ya sake yi daf da ita ya zuro hannayenshi ya shafi gefen fuskarta inda ya kumbura, bud'a ijiyarta yayi yaga yanda tayi ja sosai, kallon fuskarta yayi yace "Kan ki yana ciwo ne?"

Girgiza mishi kai tayi kafin ya d'ora da "Ki daina b'ata min rai kinji ko, ba son raina bane na daki mace, amma kinga wannan banzan ko yanzu da zan ganshi saina kikkifar dashi."

Jinjina kai kawai tayi hakan yasa shi kama hannunta yace "Muje yau da kaina zan kaiki makaranta, ki rabu da waccen kankanar."

Tsoro ne ya bayyana a fuskarta dan ita a yanzu kam bata fatan sake fita tare da shi, juyowa yayi ya kalleta yana ganin yanayinta ya had'e girar sama da k'asa yace " Meye? Ba kya so na kaiki ne? Ko mamaki kike? To ki saba ma dan in akayi aurenmu da kin samu ciki ba zan bari kiyi tuk'i da kanki ba, dan ni ba sakarai bane nasha wahala na d'auki tsawon awanni na zuk'urk'ula miki ciki amma cikin minti d'aya ki zubar, ba zai yiwu ba."

Hannu tasa ta rufe baki ita dai tana kallonshi har ya bud'e motar ya zaunar da ita, rufewa yayi ya juya ta bishi da kallo, ga mamakinta sai gani tayi kuma ya nufi falon Hajia, gyara zama tayi dan tasan sai wanda ya ga fitowarshi, da shigarshi kamar yanda ya saba babu sallama, d'akin Ummy ya nufa yana kallon Hajia ya d'aga mata hannu yace "Hajajju barka da zama."

Kallonshi tayi da harara tace "Wai kai wane irin kunnen k'ashi ne da kai? Na fad'a maka indai wannan yar iskar gaisuwar ce bana so ka daina."

Murmushi ya mata yace " Me yasa kika k'i fahimtar ina son fara jin muryarki ne a kowace safiya kafin ta kowa?"

Da mamaki ta kalleshi tace "Ina masifa ko?"

Murmushin ashe kin fahimta ya mata yace " To ai ita ma d'in kyau take miki ko?"

"Ita masifar?" Ta fad'a tana zaro ido, shiru kawai ya mata nufi d'akin Ummy, da sauri Hajia tace "Kai."

Tsaye yayi amma bai juyo ba dan ya k'osa da maganar fa shi, ganin bai ko kalleta ba yasa tace "Uban waye zai siya min tv ta daka fasa jiya?"

Juyowa yayi ya saka hannu d'aya a aljihu yace "Ki ce kawai na siyo miki tvnki amma ba ki tambayeni wa zai siya ba, idan fa nace lieutenant ne zai siyo miki sai kuma kice nayi rashin kunya?"

Yana fad'a ya juya cikin takon k'arfi ya bud'a d'akin Ummy ya shiga ba tare da sallama ba, Ummy dake tsaye gaban madubi tana gyara dogon gashinta juyowa tayi cikin tsoro, tana ganinshi ta sauke ajiyar zuciya ta juya tana fad'in "Dama waye inba kai ba, ko Kamal kafin ya shigo d'akin nan sai yayi sallama ya nemi izinin shigowa an lamunce mishi, amma banda kai."

Kujerun dake farkon shigowa d'akin na roba mai gautsi masu kyau ya zauna a tsakiyar yana kallonta, kafin yayi magana tace "Bai kamata ba ma na b'ata yawun baki na, dan haka kamar a addininka ne aka koya maka shi, ko kuma dai matsalar da kake da ne a k'wak'walwarka tayi tasiri har a sallamarka."

Wani d'an iska ya furzar yana sake had'e fuskarshi ya kalleta yace "Ummy zamu iya yin magana?"

Juyowa tayi tana murmushi ta zauna kan kujerar gaban madubin tace "Ina kwana Baba Ammar, fatan dai ka tashi lafiya?"

Ba tare daya kalleta ba ya d'an k'ikk'ifta idonshi alamar fa ya gaji da zancen nan, shirun da yayi yasa Ummy sanin ba fa zai iya gaisheta ba kenan, girgiza kai tayi tace "Kafin nan muyi magana akan kayan lefenku, ya kamata ku fito da kud'i dan had'a lefenku, Hajia na buk'atar shi yau zuwa gobe."

Had'e hannayenshi yayi yana mammatsawa yace "Ba damuwa, zanyi."

A kauce ta kalleshi jin yace wani wai zanyi, ko me zaiyi? Oho! Banza tayi dashi kawai dan babu anfanin b'ata yawun bakinta a kanshi a yanda take gani, kallon fuskarta yayi yace "Ummy, dan Allah meye tsakaninki da Abba da har zai miki kishiya? Kishiyar ma kuma wai wannan yarinyar wanda ba komai had'a ki da ita zai ja miki ba sai zubar da aji."

Kallonshi ita ma tayi tace "Na d'auka angama maganar nan, meye kuma na taso da ita? Kaga bana son tashin hankalin, aure ne za'a d'aura shi gobe, banda matsala da hakan, mahaifinka ya auri ko mace uku ce ma ya kawosu duk a goben, ni dai ina son zaman k'ark'ashin kulawarshi, dan haka wannan ba matsalarka bace."

A tsanake ya kalleta yace "Ummy, ki fad'a min idan akwai laifin da kika masa? Ni zan masa magana ya fahimta, amma bai kamata ya miki kishiya ba a yanzu."

Nuna shi tayi da hannu a zafafe tace "Kaga, ni dai a sani na ban masa wani laifi ba, ka daina maganar nan kawai idan ba so kake a fitar da uwarka ba a lokacin da za'a shigowa da mahaifinku amaryarsa ba."

Mik'ewa yayi yana mayar da hannayenshi aljihu ya kalleta yace "Ummy tambaya nayi kawai ko akwai wani laifin da kika masa ne, dan ni a gani na a shekarun da kuka d'auka tare bai kamata ace kishiya ta biyo bayan haka ba."

Tsaye ta mik'e ta nuna mishi k'ofa tace "Fitar min a d'aki na, kaje kayi duk abinda zakayi, amma ka sani wallahi idan ka ja min magana ba zan yafe maka ba, mutumin banza kawai, ni ce marainiyarka kenan zaka zo ka tsareni da maganar ko na masa laifi, idan ma na masa laifin saina zauna na fad'a maka? Ni kenan bansan ta yanda zan iya ji da matsalarmu ba har sai sakarai irinka ne zai mana magani, shi kaje ka tambayeshi mana idan kai marar kunya ne."

D'aya hannunshi ya fito da shi ya kama yalwatattar k'asumbarshi yana shafawa, takowa yayi kusanta yana kallon idonta babu wani d'ar ko tsoro cikin taushin murya yace "Ummy, ko zaki iya tuna abinda ya faru muna da shekara goma sha shida a duniya ni da Amar? Mun samu matsala dashi akan riga, a lokacin Amar nada rigima sosai, ko abu nawa ne saiya nuna nashi ne ko yana son shi saboda yasan kowa zai goya masa baya, asalin rigar tawa ce, kuma ke ma kinsan haka saboda kinga alamar da nama tawa, amma sai kika rufe ido dake da duk sauran mutanen gidan kuka ce dole sai dai ni na hak'ura tunda nine babba, hakan ne yasa nima raina ya b'ace a cikin dare na yaga duka rigunan da reza, amma me zai faru? Washe gari Hajia ta mareni a fuskata ta zageni zagin da ko kare tayi wa saiya zubar da hawaye, ta kira ni d'an iska har ba adadi, ta kira ni shege munafiki mai bak'ar zuciya..."

Sunkuyar da kai yayi yasa yatsa d'aya yana share hawayenshi, ba tare daya d'ago ba yace "Zagin da yafi tsaya min a rai shine data kalle ni a gabanki a gaban idon mahaifina ta kira ni da *d'an Allah bani*, wai da tasan haka zan zama da ko da aka haifeni tasa an min allurar mutuwa, a wannan ranar ta fad'a ni, ni Ammar nine *annobar ahalinta*, zuciya nayi na fita farfajiyar gidan ina kuka, na wuni a wuri d'aya zaune da tunanin ko zan samu wanda zai zo ya rarrashe ni ya kwantar min da hankali, amma babu wanda ya zo kusa da ni, a lokacin mahaifiyata ce kawai nake ganin zata iya zuwa kusa dani kuma ta rarrasheni, ganin ke baki zo ba yasa ni naje har d'akin ki, Ummy me kikayi a lokacin?"

"Ina shiga kika rufe ni da wani fad'an wai na fita na baki wuri, haka kema kika sake kirana d'an iska mai ja miki magana, a k'arshe bud'a baki ki kayi kika ce wai na fice miki daga nan ba kya son gani na ko kad'an, Ummy kinsan meya hana ni barin gidan nan a wannan ranar?"

Ummy dake kallon yanda hawaye ke zuba a idonshi kasa amsa mishi tayi, dafe k'irjin shi yayi saitin zuciyarshi ya ci gaba yayi da cewa "Ummy *saboda soyayyarki ne*, ina ji a jikina kamar idan na tafi na barki a gidan Hajia zata ci gaba da k'untata miki, hakan yasa na hak'ura na zauna duk da zafin da nake ji a zuciyata, bayan faruwar hakan kwana shida na d'auka ina zuwa d'akin ki da nufin gaishe ki, amma sai kika ce ko amincin da nake nema miki ba kya so bare kuma gaisuwa ta, daga ranar ne ya zamana duk d'akin da zan shiga a gidan nan bana iya sallama, Ummy zan fara gaishe ki ranar da kika fara kallona kamar d'an da kika haifa, zanje wajen Abba."

Yana fad'a ya juya ya fita da sauri sosai, fad'awa tayi kan gado dab'as kamar an turata, sai dai ta nemi hawaye ta rasa, maganganunshi ke dawo mata, kenan babu abinda yake mantawa? Zai fara gashe ni ranar dana fara kallonshi *kamar d'a*, kamar d'a? Ba ma d'ana ba? Tunawa da tayi yace zaije wajen lieutenant kuma tasan ba lallai su kwashe lafiya ba, dan haka ta mik'e ta d'auki wayarta ta fara kiran lieutenant, amma bai d'aga ba saboda wayar na silence yana ganawa da wasu manyan mutane, aje wayar tayi ta fito falo sam bata wani saka wani al'amarin a kai ba bare tayi tunanin halin da d'an nata ke ciki.

Yana fitowa ya samu Amna ta gaji da jiranshi, Hamna kuma ta d'auki moton ta tafiyarta, yana shiga taga ya had'a kanshi da sitiyarin motar yana sauke wata k'akk'arfar ajiyar zuciya, ya kusan minti biyar kafin ya d'ago ya jawo lotus d'in dake cikin motar ya goge fuskarshi da kyau, tayar da motar yayi suka fita daga gidan, saida suka fara tafiya ya kalleta wacce ita ma take kallonshi ganin sabon yanayi a tare dashi yace "Kinyi latti ko?"

Ganin idonshi jawur alamar kuka ba wai b'acin rai ba yasa saida gabanta ya fad'i, duk sai taji jikinta yayi sanyi tana son sanin meye damuwar, cikin taushin murya tace "Yah Ammar lafiya? Me yake faruwa?"

Kallonta yayi yana doka wani uban murmushi ya kuma kalli gabanshi ya ci gaba da tuk'i, har ta fidda ran zai mata magana sai kuma ta ji cikin wani yanayi dake nuna damuwar dake zuciyar mutum yana sakin murmushi yace "Amna meyasa zaki tambayeni me yake faruwa? Shin baki tab'a lura da abinda ke faruwa bane?"

Girgiza mishi kai tayi hakan yasa ya kalleta yace "Tunda kike a gidan nan kin tab'a jin wani Ammar Allah yayi maka albarka? Ko kuma zan fita kiji wani yace Allah ya tsare ko a dawo lafiya? Ko kuma kiji ance Allah ya taimake ka ko makamantan haka?"

Shiru tayi alamar zurfafa tunani da sauri yace "Karki ba kanki wahala, ba zaki tuna ba dan babu ranar."

Ci gaba yayi da tuk'i harya sauketa, har zata shiga cikin makarantar yace "Ko na zo na rakaki ne? Kin makara fa sosai."

Cikin sanyin jiki tace "A'a yah Ammar, kaje kawai, kai ma nasan ka makara a asibiti."

Jinjina kai yayi alamar to ya fara k'ok'arin tayar da motar, kamar daga sama ko saukar ruwa ya tsinci muryar Amna cikin wani mugun yanayin da har k'asan zuciyarshi ta birgeshi tana fad'in "Allah ya
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment