Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dai kun cigaba da hirarku zai fi "ai kunji mugun halin nata ba ..mutun da ɗan uwansa amman ya dinga nuna masa kabilanci..

A fusace ummita tace "an nuna abinda yafi kabilanci aikin banza aikin wofi ,saboda bani da aikin yi sai na zauna na biye muku ana hirar mutumin da a duniya idan akwai wacce ya tsana to nice ,Ke ni ko muna gud time dashi bani da lokacin da zan zauna ina maganar namiji ɗaya kullun kamar na rasa mashin shini ,ba baku da aikin yi ne dake da masu maganarsa , shiyasa kullun kuke bani haushi da bakwa gajiya da maganar mutun daya ,mutumin da arayuwarsa ma bai san daku ba sunan dai yana dan'uwanku ne ..
"Wallahi ni duk macen dake son shi kallon
hasararriya nake mata wacce ta rako mata duniya ,kuma wallahi tayi hasarar rayuwa maganar duk da zakuyi sai kun sako wani katun banza mai tsiffar samudawa a ciki "

"karki sake zaginmu ina ruwanki ko had'iye shi mukayi ,ko fadar sunan shi ?inji cewar aslamiyya
"An zaga sai kiyi duk abinda zakiyi banza kawai "ai kice banza ,mutun sai mugun halin tsiya "to kun fara ko ba dama ku haɗu sai kun nuna hali" hajiya kowa a nan yaji abinda take cewa akan yaya Ma'aruf ko shi ba d'an'uwana bane bai kamata ta dinga fadar munanan kalamai akanshi ba " to shikenan ya isa kar na sake jin kunyi faɗa akanshi ra'ayi mutun yayi hirar d'an'uwansa ra'ayi ne mutun yace bai so ,babu ruwanku ku da kukaji zaku iya ku cigaba,

Dukkanninsu sukayi shiru babu wace ta sake yin magana ,tunda ummita da aslamiyya ke tanka in taka aunty sakina Ke kallon ummita ta kasa ɗauke idanunta akanta idan ta fahimci maganarta daidai ,itace tayi hararrriya wacce tayi hassarar rayuwa tunda itace tafi zakiwa akan maganarsa kuma itace ke sonshi .... "
"Bama hirarsa muke ba Hajiya maganace ta kawo magana har...."nace ya isa banason jin sharhi , Allah ya kara haɗa kanku, gaba-daya ...suka haɗa baki suka amsa da "ameen Hajiya ..."

Hajiya ta maida hankalinta kan ummita "ummita ki dinga hakuri da yan'uwanki, baki da kamarsu suma haka ku zama tsintsiya madaurinku daya kinji,
ki dinga hakuri sosai Hajiya tayi musu nasiha sosai tare da cewa karta sake jin sunyi faɗa akan ma'aruf ,dan haka kafin ta baro parlour'n hajiya kulu tayi ƙoƙarin shirya su ,sai dai kowace a cikinsu taki sakin ranta sai fixge fixge suke barin ma aslamiyya dan tafi kowa daukar zafi ,yayinda aunty sakina Itama ta dauki zafi duk inda ummita tayi da ido take binta tana harararta tare da jin haushinta hatta aunty jiddah bata ji dadin abinda tayi ba ..
Bayan hajiya kulu ta koma d'akinta aunty sakina da aunty jiddah suka shige d'akin aunty sakina "kiyi hakuri sakina naga ranki ya baci kwarai ,haka halinta yake ni kaina bana jin dadin abinda take wa ya Ma'aruf , gaskiya ban taɓa tunani ummita zata iya faɗar abinda ta faɗa ba hasarariya mai hasarar rayuwa fa ?"kiyi hakuri ,sai dai zuwa yanzu ya kamata mu ɗauki tamaki akanta "kamar ya kenan wani irin mataki zamu dauka ? Inji cewar aunty sakina.
"Mu ware ta acikin mu mu nuna mata mu fi son ya Ma'aruf akanta Wallahi ban taɓa jin na tsaneta ba sai yau ,wannan shine karo na farko da naji na tsaneta , tsana fiyye da irinta ya Ma'aruf "Gaskiya ni dai bana cikin wannan tsarin naku ko kun juya mata baya ni dai ta zame min dole , dole nayi mu'amala daita inji cewar meenal atare suka juyo suka fuskanceta tsaye abakin kofar d'akin "aunty jiddah komai ummita zatayi bai kamata ba ,bai kamata kice haka ba "ki yi min shiru anan daman ba tun yau na fuskanci kinfi sonta akanmu ba wannan shine abinda zamu yi mata kuma babu fashi sai munyi ......
"ba haka bane aunty jiddah , matsayinku daya ke da ummita ,matsayi daya kuke dashi duka acikin zuciyata , dukanku nawa ne, idan ku ummita bata zame muku dole ba ni dole nace saboda ubanmu daya daita ke kuma uwarmu daya dake babu wanda zanki acikinki duk duniya a halin yanzu kune mafi kusanci da rayuwata "Please aunty jiddah karku yi haka wallahi mama bazataji dadi ba ,ni kaina dana sani ban janyota dole ba ,sai data ce bazata zo ba na takura mata ," aunty sakina kuyi hakuri ku yafe mata dan Allah zan mata magana nasan kuma za taji ta karasa maganar tana haɗe hannuwanta duka guri daya "tsaki aunty jiddah taja" ke a matsayin ki na wa kenan da zaki faɗa mata taji?
" yarinyar da uwar data haifeta ma bata isa ta faɗa mata ba taji
ba sai ke uwar kankanba tana gama faɗar haka ta nufi kofar fita ta tsaya a bakin kofar ta kira Maryam da Khadeeja da aslamiyya da Sa'ada har da kannen sakina amman ban da ummita..... parlour'n ya rage daga ummita sai Ammar su kuwa sun kulle kansu a daki ...
Wannan abu yayi mugun batawa ummita rai taji haushi acikin ranta take gefen kanta ya soma sarawa ta runtse idanunta kawai tana fidda numfashi sama sama tamkar mai cutar asma ...

a qalla sun ɗauki sama da awa ɗaya suna tautaunawa, acikinsu Maryam da meenal ne kawai basu bada goyon baya ba amman sauran duk sun amince da hukunci da aka zartar .. ..


Sai yamma lesss suka dawo gida kai tsaye kowace ta kama gabanta tana cika tana batsewa , meenal da da Maryam suka wuce bangaren su ummita, kowace tayiwa kanta mazauni "sannu da gida mama suka hada baki gurin faɗan haka "sannuku yan albarka kun dawo lafiya yasu hajiya kulu ?" Duk sunce agaisheki ",ina amsawa "akawo muku abinci ne ?
"Sai dai ummita dan naga itace kaɗai ce bata ci abinci ba amman mu a koshe muke" sosai mama ta maida hankalinta kan ummita dake zaune ranta a matukar bace kallo ɗaya tayi mata ta fahimci tana cikin damuwa "ummita ...... mama ta kira sunanta a tsanake
Ta d'ago kanta a hankali tana kallon mama tare da ƙoƙarin boye damuwarta , cikin kwayar idanunta mama take kallo tana karantan yanayinta "tashi kije ki rage kayan jikinki kizo kici abinci muryarta a sanyaye kamar zatayi kuka tace "to sannan ta soma balbale mabalin abayar jikinta ta cire ta ajiye agefenta tun kafin ta mike mama ta rigata tashi ta isa gaban dining tablet ta zubo Mata abinci jollof din kuskus ne wanda yaji kayan hadi kabeje da hanta da nama , ta dawo inda take zaune ta mika mata "maza kin ye ki bani plet mama ta fadi haka sanin da tayi ba wani abinci kirki take ci ba ..
A hankali ta soma tsakurar abincin tana kaiwa bakinta idanunta ya cicciko da ruwan hawayen tausayin kanta da mahaifiyarta da kuma bakinciki abinda su anty jiddah sukayi mata ne yake cin zuciyarta "ita kaɗai tasan yadda take ji ...
Ita kaɗai suka ware suka kulle kansu a daki ..
abun yaki barin ƙwaƙwalwarta tana son sanin abinda suka tautauna acikin daki kafin ta ɗauki mataki akansu ta sani idan kowa bai faɗa ba dole meenal zata faɗa mata ,da wannan tunanin ta karasa cin abinci , mama ta miko mata ruwa cike da kulawa ..
ko cikakken minti talatin da gama cin abinci bayi ba ,sai ga
fauziyya ta shigo da gudu ,bata kula kowa ba ta kalli ummita "aunty Ummita wai kizo inji abokin ya Ma'aruf " take ta haɗe rai dan sai lokacin ta tuno da muhd Sa'id "jeki ce banana haka kawai azo a damu mutun daga dawowarsa ni babu inda za.. "ke bana son shashanci kije mana kiji abinda yake tafe dashi ,ai ko baka son mutun baka nuna masa a filli ba ,sannu a hankali idan shi mai hankali ne zai fuskanta, karki kuskura ki furta kalmar kiyayya ga mutun cin zarafi ne babba in har ba'ayi dace da mai kyawun hali ba zai iya qullatarki har ma ya cutar dake tashi maza kije yana jiranki .....

Tun daga nesa da muhd Sa'id ya hangota ya fara aiko mata da kyakkyawar murmushi ya diro daga kan motarsa da yake zaune a lokacin data karaso "barka da fitowa tauraruwan taurari,tauraruwan matan duniya .. gimbiya a zuciyar said , tayi saurin ɗauke kanta daga garesa tana jan tsaki "ina wuni " ta faɗa atakaice lafiya lau yammtana ya mutanen gida ?
"Lafiya ta amsa a ciki ya sake yin murmushi "gani na dawo hajiya subai'a na cika alkawari ,ina fatan nima za'a cika min nawa alkwarin a sanar dani matsayin dana samu ko da yake tuni zuciyata ta gama amincewa na samu babban matsayi ina fatan hasashena ya zama gaskiya idanunshi akan ta ya karasa magana ....

Gaba-daya sai taji ta diririce tamkar ya daureta da irin mayataccen kallon da yake mata "kar ki kuskura ki furta kalmar kiyayya a gareshi cin fuska ne babba kalaman mahaifiyarta suka fado mata a hankali ta d'ago ido ta kalleshi har zuwa lokacin ita yake kallo qirjinshi na dokawa da matsanancin karfin gaske "uhm ke nake sauraro subai'a"tamkar kai ne ka rada min sunan muhd Sa'id..........
Ta faɗa tana tsareshi da fararen idanunta masu narkar da zuciya .

"kama yayi ka sake yanka min ragon suna da irin sababbin sunayen da kake kirana dasu ,Hajiya ,gimbiya tauraruwa ....."
Dariya muhd Sa'id ce ta katseta "au gimbiya subai'a kowane suna matukar yana da kyau gani nake ya fi dace dake ,karki ga laifina soyayayarki ce ta min yawa ,ganina da jina da komai nawa duk soyayayarki ta mallakesu bana iya yin komai sai da amincewar qaunarki .. amman dai mu koma baya kan abinda ya kawoni dan shi nafi bukata, nafi son na fara jin matsayina agurinki ..
Shiru tayi tare da tsurawa zanin atamfa dake d'aure ajikinta ido dogon lokaci shi kuma ya kasa ɗauke idanunshi akanta zuciyarsu cike da zullumi da tsoron jin abinda zata ce ,gyaran muryar da yayi ya sa ta dawo daga duniyar tunani ..
"So take ta faɗa masa gaskiyar abinda ke zuciyarta amman kalaman mama na tauyeta da kanainayeta , dan haka ta bude baki da kyar tace "Allah ya zaba mana mafi alkhairi mutun ai bazai ki mu.....ta datse harshenta wannan shine karo na farko data dade da nmj har ta furta wannan kalmar garessa sauran da ko kallon arziki Basu isheta ba Shima wannan adalilin samun damar shigowarsa gidansu if not bazata sairaresa ba ..." ina fatan ka gamsu "ko kadan kalamanta basu gamsar dashi ba domin ma'abota soyayya sun jima da fassara kalmar mutun bazai ki mutun ba da rashin samun karɓuwa a wajen yarinya ,sai dai wayo irin na muhd Sa'id bai bari hakan ya kayar masa da zuciya ba, ina ma laifi da yasamu kamar wannan kalmar agurinta ...duk da kalmar batayi masa ba amman zai yi mata kyakkyawan maajiye acikin zuciyarsa da ƙwaƙwalwarsa , a hankali ya kudirce a ransa matukar zata cigaba da fitowa ta sauraresa shi kuwa sai yayi kwance kwance ya warware duk kullin soyayayar kowa daga zuciyarta ya cusa nashi dan tunda Allah ya haliccesa bai taba jin ya so wani abu so mai tsanani irin soyayyarta ba ..

Cikin hikima ya cigaba da yi mata hira mai dadi har zuwa karfe bakwai ko kadan baya don rabuwa daita ,lokacin data bukaci suyi sallama bai Musa ba bayan ta tafi ya samu wani yaro ya damkawa masa ƙatuwar ledar daya ciro a bayan motarsa ya nuna masa ummita yace ya kai mata ,bai jira dawowar yaron ba yaja motarsa zuciyarsa cike da kaunar ummita.. ....





.... Two friend's (bsbs)
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL NOT FOR SELL


AL'QALUMAN



*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*


~DEDICATED TO~
*FATIMA ABUJE BAGUDO*




WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim


PAGE 13



.......a daidai bakin kofar part din su ummita ya rayhan ya ci karo da saifullahi rike da ledodi niki niki sai faman nishi yake .
ya kalleshi cike da mamaki kafin daga baya yace "kai kuma daga ina haka da kaya ?
" um amm ... abokin .ya ma'aruf ne yace na kawo wa aunty ummita" "abokin ma'aruf rayhan ya faɗa yana mamaki zuciyarsa na dokawa da matsanancin karfin gaske .
"wanne kenan daga cikinsu yayi maganar jikinsa na d'an rawa ?
"Ya Sa'id"
a hankali ya cigaba da bin fararen lododin dake rike a hannun saifullahi da kallo.
"ai yaya Sa'id yana da kirki sosai ko shekaranjiya yazo gurin aunty ummira har nima sai daya bani kudi kuma yace zai kawo min glass daidai size dina, bai kowa min glas din ba amman ya bani kudin yace na.. ......
"Yi min shiru magananne kawai , fadi ban tambayeka ,
tambayarka nayi da zaka hau zuba kamar ruwa ?
"Bani lododin ka ƙara gaba , saifullahi ya mika masa ledodin kama hanya ya wuce yana wagensa .
Rayhan ya bude ledar ta farko idanunshi suka karo da kaya na garari da kece raini a ciki, paper less kwaya uku kala daban daban baki mai adon ja da shudi, sai mai ruwan lemon da ruwan zuma , sai atamfa top wax kwaya hud'u , dakakkiyar shadda galila guda biyu purple da ash colour , baki daya su ukun ,ya dade yana bin kayan da kallo bakinsa bude zuciyarsa na cigaba da dokawa ,dayar ledar ya bude kayan kwaliya ne kala daban daban da takalma , hakan nan yaji zuciyarsa na tsinkewa haɗe da rawa rawa tamkar wanda ake bugawa guduma ..

a zafafa yasanya kai ya shiga parlour'n hannunsa rike da ledodin , daita ya soma cin karo zaune , meenal da maryam sun zagayeta suna tambayarta ita kuma tayi musu shiru tare da zabga tagumi dan ta rasa abinda zata ce musu ,meenal da maryam suna ganin shigowarsa suka mike tare da gaishe shi basu tsaya jin amsar shi ba, suka shige ɗaya daga cikin daku nan dake Parlour'n ..

Shiru yayi kawai yana kallonta zuciyarsa cike da jin haushi da bakinciki ,kallo ɗaya zaka masa ka fahimci yana cikin damuwa da tashin hankali ..
kusan minti biyu bata d'ago ta kalleshi ba , da alamun ma bata san ya shigo parlour'n ba, sosai tayi zurfi cikin tunani, gaba-daya ta rasa meke mata dadi ,kalmar data yiwa muhd Sa'id amfani dashi ta tsaya mata arai ,"mutun ai bazai ki mutun ba ,ita kanta ba tasan lokacin da kalmar ta fito daga cikin bakinta ba , ba abinda taso faɗa masa kenan ba ,maganar mama ce tayi tasiri a cikin zuciyarta ......

"anya kuwa bata yi kuskuren ba .....?
"Anya muhd Sa'id ba zai ɗauka ko tana son shi bane ?" kai ta ya ma zai ɗauka tana son shi ne,alhali gabad'aya kalmar bata yi kama da kalmar soyayya ba..

kusan minti goma yana tsaye yana dubanta zuciyarsa na harbawa batare da yace mata komai ba , jikinta ne ya bata cewar ana kallonta dan haka ta d'ago kanta a hankali karaf idanunta ya sauka akanshi tsaye ga wasu fararen ledodi masu matukar kyau a gefenshi ..

Wani irin kallo yake binta dashi mai cike da tsantsar 'bacin rai yayinda hankalinsa ke sake tashi ... muryarsa a kausashe ya kira sunanta "ummita daman kina sauraron wasu samari bayan ni ?
gabanta yayi wata irin muguwar faduwa ,take jikinta ya ɗauki rawa ta zuba masa fararen idanunta batare da ta ce komai ba shima idanunshi ya zuba mata "daman zaki iya kula wani bayan ni?
"Na ɗauka ni kaɗai kike bawa lokacinki a she kina sauraron wasu a bayan idona ?"na ɗauka rashin kula soyayyata da bakya yi wani al'amari ne daban da tare son cikar burinki ashe ni ne baki so...?
"Amman babu komai na gode ,Allah saka da alkhairi daman nasan hauka kawai nake akanki , ni kadai ke haukan sonki da damuwa da lamarinki, shikennan babu komai tunda kinfi .son muhd sa'id a kaina ga kayan daya aiko miki dashi nan yana gama faɗar haka ya juya.
da sauri ta mike ta riko hannunsa "ya rayhan tsaya kaji "
"me zanji me zaki faɗa min? ya katseta da sauri yana tsareta da idanunshi .
"yanzu na amshi kayan a hannun saifullahi har yana tabbatar min wannan ba shine karo na farko da muhd Sa'id yazo gurinki ba , runtse idanunta tayi tana jin wani irin kuna cikin ranta da zallar bacin rai , duk da tasan bata son ya rayhan daidai da kwayar zarra a cikin zuciyarta amman bata jin zata juri ganinsa cikin damuwa a dalilin muhd Sa'id ba ..
Shi din wani jigo gareta dama rayuwarta gabad'aya .

Muryarta cike da in.. ina tace "ni...ni..ban san wani muhd Sa'id ba da kake magana akan shi ba ka dai .....
"Yi min shiru karki min karya mana ko last week an fada min yazo gurinki ...
Sunkuyar da kanta kasa tayi tana jin fad'uwar gaba mara misaltuwa, ahankali ya soma ƙoƙarin zare hannunsa cikin nata , ta sake riko hannunsa sosai "kayi hakuri yaya hakan ba zai sake faruwa , ka faɗa min abinda kake son nayi ?
Naunauyen ajiyar zuciya ya sauke da karfi har tana iya jiyo yadda zuciyarsa ke dokawa da sauri "dan Allah yaya karka yi fushi dani wallahi ba son muhd sa'id nake ba , yanzu ma ba'a son raina na fita ba ,wallahi ka tambaya kaji , da umarnin mama na fita ba dan ina ra'ayin hakan ba.
yaya in dai zan so wani d'a namiji arayuwata kai ne ...
" kai ne fa yaya rayhan dina ,da ka soma sona tun bansan ni wacece ba , ka soni tun ban san kaina ba ,ka nuna min so da kulawa ,ka nuna min gata a cikin duka sauran yan'uwa kallonka nake a amatsayin wanda ya rage min a fadin duniya .... ta k'arasa maganar muryarta na rawa alamun tana son yin kuka dan har ta fara lumshe idanunta ..
take ya daburce ya riko duka hannayen cikin nashi ya isa gurin kujera ya zaunar daita shima ya samu guri ya zauna yana lakace mata hanci " naji bance ki min hasarar hawayenki ba ,sai dai hankalina yayi mugun tashi "me kake so nayi yaya ka fadi min duk abinda kake so ummita zata maka ?
"duk abinda kake so shi zanyi ka faɗa min sosai ta kashe masa jiki ya tsura mata ido ya kasa ɗauke idanunshi akanta ..
Wani sanyayyen dadi ne ya dinga zirayar tsokar dake makale da kirjinsa, fuskarsa kunshe da farinciki yace "bana son ki sake kula wancan muhd Sa'id din , ke bama shi ba , bana son ki ƙara kula kowani namiji bayan ni ..
Yayi maganar kamar zai shige mata jiki "duk duniya idan aka cire mama da Abba nafi sonki akan kowa burina bai wuce na cigaba da sonki tare da mallakeki a matsayin matar aurena sannan ki kasance uwar ya'yana , ummita idan na rasaki mutuwa zanyi ..ina sonki! ina sonki !!
ina miki son da ni kaina ban san adadin son da nake miki ba harufan baki sun yi kaɗan da kwatata mizanin kaunarki gareni , taɓa zuciyata kiji yadda take dokawa akanki kullun cikin irin wannan dokawar take ,nasan da zarar ta rasaki zata tsaya cak ta daina bugawa dan Allah ummita kada ki barni, kada ki auri wani da namiji ki barni , karki bari wani da namiji ya rugaza min zuciya a sanadiyyarki ya K'arasa Maganar cikin killer voice dinshi ..
Tuni jikin

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment