You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
,kallon kallon suka shiga yiwa juna kafin daga baya yace "daman inna ce bata da gaskiya shine da cin zali ka mari yar mutane ?
Mah'ruf ya sunkuyar da kanshi yana tsosa keyarsa alamun jin kunya "oya shige muje har part dinsu ka bata hakuri, babu musu yayi hanyar part dinsu ummita suna shiga mama na saukowa , tana ganinsu ta saki fuskarta duk da ranta a matukar 'bace yake "yau injiniya ne da kanshi ?
"Dole ki gani ,ga wanda na taso gaba nan ya bada hakuri "hakuri kuma me ya faru ?
Injiniya ya nuna ummita dake sheshekar kuka da yatsansa "murmushi mama tayi "kai injiniya dan yayi mata hukunci bisa ga laifinta shine har da wani ban hakuri ai ni bai kyauta min ba mari uku ya kamata yayi mata ba daya ba ..
take mah'ruf ya sake yin kasa da kanshi yana mai tsanani jin kunyar mama "ka k'arasa gurinta mana ka bata hakuri ka wani tsaya kana kallona ko sai kaima na gaugaura maka marin kaji yadda taji ,injiniya yayi maganar a fusace. Mah'ruf yasan halin injiniya zai iya aikatawa ya maresa agaban ummita dan shi babu ruwansa da wani girman mutun matsawar kayi laifi zai hukuntaka bisa abinda ka aikata ,jikinsa a sanyaye ya soma d'aga kafafunsa meenal na ganin haka tayi saurin mikewa ya zauna a mazauninta data tashi muryarsa can kasa tamkar mai koyon magana yace "kiyi ......
Sai kuma yayi shiru ya kasa karasawa baya jin zai iya bata hakuri , injiniya yayo kansa a fusace zai d'aukeshi da wasu mahaukanta maruka mama tayi saurin shiga tsakani "kayiwa darajar Manzon Allah kada kayi haka ,wallahi idan ka mari yarona bazan
yafe maka ba sauke hannunshi yayi yana dubansa Sannan ya juya yana huci kamar zaki "ke kuma maza ki tashi ki bar nan mara kunya kawai ummita ta mike simi simi tayi sama,
sai dai bataji dadin abinda mama tayi ba taso injiniya ya rama mata marin da yayi mata, Allah ya isa kuwa tayi masa yafi cikin kwando
Mah'ruf ya riko hannun mama cikin nashi a daidai lokacin data juya zata shiga kitchen "kiyi hakuri mamana ki yafe min nasan ban...
"Karka damu babu komai har ga Allah ban ji komai ba da kai da ummita ya'yana ne dan ina jinka kamar nice na kawoka duniya , ya saki wani bayyanane ajiyar zuciya ta koma ta zauna kusa dashi "mah'ruf kayi hakuri da halin ummita dan Allah ka cigaba da kular min daita duk runtsi duk wuya kada ka dubi idanuna ka hukuntata daidai da laifinta kai din tamkar uba ne a gareta kasancewarka babban yaya , ina alfahari da kai kanshi a sunkuye akasa yace "na gode mama duk duniya babu mama kamarki ina sonki mamana "nima haka mah'ruf ban haɗaka da komai ba ni dai ka rike min ummita amana ko ina raye ko bayan bana nan ka zame mata bango majinginta, ka kular min da lamarinta na baka amanar rayuwarta...
"inshallahu mama Allah yaja da nisan kwana "ameen Mah'ruf Allah yayiwa rayuwarku albarka ya nuna min ranar aurenka ....
nan suka shiga wata hirar mama kenan mamar da samun irinta sai an sha wuya ..... Allah ya bamu irinta mama
Ummita kuwa tun daga ranar take jin haushin mah'ruf a zuciyarta daga karshe ma tattara ta bar gidan zuwa gidan aunty Aysha dan idan ta cigaba da zama zasu koma gidan jiya ....
Kusan kwana biyu bai sanyata acikin kwayar idanunshi ,duk ya damu amman ya kasa tambayar yaji inda taje mama na hankalce dashi amman tayi masa shiru ,shi kuwa rayhan tuni yasan inda take dan haka kullun yana can suna shan hirarsu kwasam ma'hruf yaje gidan idanunshi ya gane masa ita suna sallama da rayhan "good bye ya rayhan, yayi murmushi yana ƙoƙarin riko hannunta "bakiji daidai ba yarinya anjima zan dawo wani guri zani yanzu ..
A hankali ya dauke idanunshi akansu ya sanya kai ciki yana jin faduwar gaba ,ta gabanshi tazo ta wuce tana rausaya ko kallonsa batayi ba dan har lokacin tana tattare da jin haushinsa shiru yayi yana satar kallonta daga karshe yaja tsaki
*****
Ranar wata alhamis mah'ruf ya dawo daga aiki , sai mama take faɗa masa ranar asabar zasu je kwatono saka ranar auren Usman ,take ma'hruf yace shima zashi dan yana son yaje gurin Usman bayan kwana biyu ummita ta dawo gida ta samu labarin zuwa kwatono ,take tace itama zata , mama tace "a'a ban shirya tafiyar dake ba , dan haka bazani dake ba da baba babba zamu kiyi hakuri idan zan sake zuwa sai muje tare ,ta fadi haka ne saboda tasan muddin mah'ruf yaji daita za'a zai ce ya fasa zuwa , ita kuwa daya fasa gara ita tayi zamanta ,ummta ta 'bata rai zuciyarta na faɗa mata kila saboda Mah'ruf ne yasa mama bazata daita ba , tama san shine ya zigata kartaje daita , ana cikin maganar mah'ruf din ya shigo yana jin abinda suke tautaunawa, kai tsaye yace ya fasa zuwa aje daita kawai shi yaje wani lokaci ,itama tace ta fasa zuwa su tafi kawai sukayi dragging da mama datafi bukatar tafiya da mah'ruf akan ummita , take aunty aysha matar yayan Mah'ruf kuma diyar aunty salma tace "me zai hana mama mutafi gabadaya ...
Shiru mah'ruf yayi bai sake cewa komai ba saboda mama ,dan ya lura bata ji dadi da yace ya fasa zuwa ba ..
Suna barin parlour'n ya dawo kusa da mama ya zauna yana kiran sunanta ta amsa masa a ciki batare da ta kalli inda yake ba "fushi kikayi dani mama?
"dole baba babba ,dole nayi fushi na rasa meke damun kai da ummita duk duniya nafi sonku da kowa, baka ji yadda nake jin zuciyata ba a duk sanda naga kuna sa'insa da junanku ..
"To kiyi hakuri mun daina zani kinji mamana ,ta sake yi masa banza "dan Allah mama Karki yi fushi dani "naji ai dan kasan bana iya fushi da kai ne yasa "to kiyi hakuri na daina yayi maganar yana langwa'bar mata da kai kamar wani ƙaramin yaro , tayi murmushi "kai ko Allah sai nayi fama gurin bawa matarka hakuri "hakurin me kuma ?
"Hakuri da halin miskilancinka idan aka kawota gidanka musamman zan ce akawo min ita na zaunar daita "nayita bata hakuri nace kiyi hakuri suhaima ! kiyi hakuri suhaima !! nasan bazata fahimci irin hakurin ba, amman daga baya zata fahimta ,yayi murmushin gefen baki tare da mikewa akan doguwar kujera ya kwanta yana lumshe sexy eye's dinsa , "babu wani hakuri da zaki bata ai ita taji ta gani ta nace "kai baba babba bana sharri ka dai nacewa yarinyar mutane inji cewar aunty Aysha data dawo parlour'n bayan ta gama yiwa ummita faɗa a d'aki .
ranar juma'a suka shirya tun da asubar fari suka d'auki hanyar kwatono , suna cikin tafiya costom din farko suka taresu sukace mama ba yar kasa Nigeria bace ina zata?
Tace aure zasu nan zango basu yarda ba , da kyar dai aka samu aka shawo kansu suka barsu suka wuce ,kafin su kawo costom na biyar dake tsaye tsayen yayi yawa sai mama tace "kai nifa na gaji da wannan tsayuwar da costom suke mana ,zaku ga yadda zan shigar daku kasata lafiya babu costom din daya isa ya tuhumeku har mu shige, amman kalli yadda na kasarku suke min ,tayi maganar kamar zatayi kuka , ni dai yanzu abinda za'a yi kawai ke ummita koma kusa da mah'ruf ki zauna daman ita mama tana gaba kusa da direba mah'ruf da ummita suna sit din baya shi yana gefe ummita na gefe matar yaya a tsakiyarsu , mama tace " matar yaya ta koma d'ayan gefe ummita ta dawo kusa da ma'hruf ta zauna duk costom din daya sake taremu kuce amarya da ango ne ku ,an d'auro muku aure za'a kai ku nan zango idan suka ce ina a zango " kuce zango gidan ashiru .
take ummita ta bata rai tana yatsina fuska da zunzuburo baki ,mama tace "ke zanci ubanki wallahi maza ki matsa kusa dashi nace ,shima ma'hruf ranshi bai so haka ba amman babu yadda zai yi da mama ,gashi ya matso yaga sun isa , dan hk ya kawar da kai , suna cikin magana direba yana tuki maganar mama na bashi dariya ,matar yaya kuwa har da rike ciki saboda dariyar mama, cikin haka sai costom suka ƙara tsaida motarsu, yace "ku kuma fa daga ina ?
"ina zaku haka ? Ke kamar ma ba yar kasar Nigeria ba suka tambayi mama" ina zaku take mama tace waɗan mata da miji ne jiya aka d'aura musu aure ko ba matarka bace mama ta juyo tana kallon ma'hruf zuciyarsa na dokawa da matsanancin karfi yace "ma..matatace "to ka nuna musu mana cewar matarka ce nan zango zamu "ke ummita ba zaki nuna musu mijinki bane kike kallon mutane tare da haɗa mata da zagi ,tana cika tana batsewa ta kwanto saman qirjinsa shima ya kai hannunsa gadon bayanta yana shafa kanta zuwa bayanta tare da rufe mata fuska da qirjinshi yana kirkiro murmushin dole "aunty Aysha tace "kasan mu a gurinmu ba'a ganin fuskar amarya tayi maganar tana zolayar mah'ruf ..
take dariya ta subucewa costom sai da yayi mai isarshi sannan ya basu hannu suka wuce a haka har suka isa kasar kwatono tana manne a qirjinshi gabad'aya sun manta da sun gama wuce costom da imgration sun mannewa juna suna shaƙar numfashin juna da kamshin turaren juna .
Mota na tsayawa a harabar gidan su mama, suka fita ya kai hannunsa ya shafa gefen fuskarta yana magana kasa wanda ita kadai taji abinda yace da sauri ta tashi a gigice ta fito da sauri daga motar tana hada hanya sai dai tana jin gangar jikinta ce ta fito, ta bar zuciyarta a cikin motar , tayi kokarin sanyawa jikinta natsuwa kafin ta isa inda aunty Aysha ke tsaye tana jiran karasowarta ..
Gidan ne ya hargitse da hayaniyar yan sannu da zuwa , Kai tsaye Usman ya zo ya dauki mahruf zuwa gidan mahaifinsa , ranar da suka sauka a ranar su mama suka tafi kai kayan saka ranar auren Usman ..
TWO FRIENDS (BSBS)
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
https://youtu.be/-Xy64PJiHiQ
domin sauraron abinda muka daura a YouTube danna blue rubutun dake sama. 👆🏻
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
*MAMAN AYMAN*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 28
.... Daren ranar kasa bacci ummita tayi sai faman juyi take akan makeken gadon kakarta , gabadaya ta rasa abinda ke damun zuciyarta gashi dai bacci take ji kamar tayi hauka amman da zarar ta runtse idanunta sai kwakwalwarta ta shiga harhaɗo mata hoton mah'ruf da yanayin character's d'insa, jin kanshi , yanayin miskilincisa , tausayinsa akan mutane , hakurinsa da rashin ɗaukar raini , rashin jin tsoro akan komai ,wayewa ta kowani bangare uwa uba kyau da kamewa tare da nagartaccen ilimin addinin dana boko .
wani irin yaji idanunta ke mata da zugi yayinda zuciyarta ke tsalle akanshi duk tunaninsa sai qirjinta ya buga ,
A hankali ta zuro kafafunta kasa ta sanya silifas ta sauko ta shiga zagaye d'akin , kafin ta soma zance zuci " ya mah'ruf ........
ta kira sunanshi a fili qirjinta na tsananta bugawa da matsanancin karfi " dan girman Allah ka bar zuciyata ta huta haka ,ka daina zuwa kana damun tunanina , me ma yasa kake yawon zuwa cikin tunanina ba kai yakamata na dinga tunawa ba adaidai wannan lokacin ya rayhan yafi cancanci da haka,to me yasa sai kai ne zaka zo kayi kanekane a ruhina ?
" dan Allah ka fita rayuwata ta k'arasa maganar tana sauke
naunayen ajiyar zuciya tare da yin shiru ta koma ta kwanta akan katifa tana juyi .
numfashi ta dinga saukewa a hankali kamar wacce tayi gudu ceton rai ,hannu ta kai cikin suman kanta ta dinga yamutsawa kafin daga bisani ta dinga sakin murmushin da ita kadai ta bawar kanta sanin ma'anarsa, lokaci ɗaya kuma ta sake sauke ajiyar tana cikin tunaninsa bacci barawo ya d'auketa .
bangaren mah'ruf shima raba dare yayi zaune yana tunaninta abinda yafi tsana kenan ya zauna yana tunaninta a karon banza alhalin yasan hakan bai da faida agurinsa , ganin tunanin banza da iska ya saka shi a tsakiya yana kawowa zuciyarsa farmaki ya janyo system dinsa ya shiga aiki kafin daga baya bacci ya fara fixgarshi ya janyo bargo ya lullu'be jikinsa yana fidda numfashi mai gyaraye da jin dumin jikinta a nashi ,yana son sanin abinda yasa yake yawon tunaninta , amman zai bari har sanda zasu koma nigeria ya tambayi jafar amininsa dan sosai yake son sani dalili wannan banzan tunanin , daren rana haka ya kwana yana tunaninta da bukatar son Jin dumin jikinta a nashi ..
Tun bayan da suka sauka a kasar cotonou bata sake saka mah'ruf a cikin kwayar idanunta ba , tun tana basarwa har ta tsinci kanta cikin tsananin damuwa dashi tana son tambayar auty Aysha ammn jin kai da miskilanci ya hanata ...
a hankali ta lumshe fararen idanunta sakamakon tuno abinda ya faru a tsakaninsu a sanda zasu zo , babu abinda yasa zuciyarta sake makance akan tunaninsa bai wuce yadda ya dinga cusa fuskarta a tsakankanin fad'ad'd'en kirjinshi daya waddatu da sihirtaccen kamshi turarensa mai tsuma zuciya .
sosai zuciyata ta tsinci kanta da jin matsanancin kewarsa , ta dinga jin zuciyarta na harbawa akanshi tana bukatar d'aura kwayar idanunta akanshi wanda ta rasa dalilin faruwar haka "bai dace ki dinga tunaninsa ba ummita zuciyarta ta fahimtar daita haka "i really has to do that meye ciki dan nayi tunaninsa a matsayinsa na d'an'uwana ?
kuma ya damu da lamarina dana mahaifiyata kyakkyawar zuciyarta ta faɗa mata haka ,yayin da wani bangaren na zuciyarta tace "ya dai kamata ki daina zurfafa tunaninsa haka idan ma yin tunani ya zame miki dole to kiyi tunanin mijin da zaki aura ba wannan mugun ba ...
abinda bata sani ba zuwan ma'hruf biyu gidan ita din ce baya bukatar gani saboda ganinta na haifar masa da kasala da jin sanyi a sansar jikinsa ,
haka zuciyarta ta dinga tunaninsa duk hirar da Badar cousin dinta ke mata baya shiga kunnuwanta saboda hankalinta yana wani bagire , ganin tunaninsa yaki barin zuciyarta da gangar jikinta yasa ta yunkura a hankali ta mike sanye da doguwar rigar abaya baka wanda akayiwa adon orenge stone tun daga samansa har kasa ta d'auki mayafin abayar ta rufe kanta dashi wanda ya fidda shape din fuskarta da sirrin kyawunta tare da zurawa kafafunta bakin silipas na roba a wannan zuwan da sukayi ne kakarta ta bata , ta soma ƙoƙarin bin kofar baya wacce zata sadata da harabar gidan ..
badar ta kalleta tana nazarinta "ina kuma zaki ko kina bukatar wani abu ne ?
A hankali ta girgiza mata kai "na gaji da wayon kwanciyar nan ne zan dan fita harabar gidan nan da lambu na sha iska "to ko bakin ruwa za'a rakaki ?
"No kinsa bana son kallon ruwa bari dai na tsaya iya nan din tayi maganar tana sanya kai, Badar ta biyo bayanta suna tafiya tana yi mata hira har suka wuce kofa biyu ta bangaren kakarta inda suka iske yan aiki kusan guda goma kowa na aikin dake gabansa .
"Ummita tunda kika zo nake especting naji kince wani abu akaina amman naji kinyi min shiru alhalin duk wanda ya gani tsawon wata biyar zuwa yanzu zai fahimci na canza sosai .
ummita ta juyo a hankali ta tsaya a gabanta tana kare mata kallo da nazarinta domin son gano abinda take son ta tofa albarkacin bakinta akai
, jiki a sanyaye ummita ta dafa kafad'arta haɗe da kiran sunanta "badar .....
Badar ta tsura mata ido tana sauraronta "a gaskiya banga abinda kike son nayi magana akai ba, gaki nan kin kara kyau kinyi fresh .
"baki dai kalleni da kyau ba amman babu wanda zai ganin da ba zai fahimci yadda na dawo ba "to ke meke damunki gara kawai ki faɗa min dan ban fahimci komai ba ?
Badar ta sauke naunayen ajiyar zuciya "wallahi asiri , anata min asiri ta nan data nan bakiga yadda duk na lalace ba na rame, baki ga idanuna duk sun kunbura ba ..?
Ummita tayi saurin dafe goshinta "kai badar me yasa maganarki kullum bata wuce wannan dan girman Allah ki daina ire iren wadan nan magangun bashi da amfani wallahi babu abinda wani ya isa yayiwa bawa sai abinda Allah ya kaddarowa bawansa tana gama fadan haka tayi gaba bunta.
da sauri Badar ta biyo bayanta
bai fi taku biyu su k'arasa lambun gidan ba ummita ta tsaya cak sakamakon kamshin turaren mah'ruf data soma jiyowa , a hankali qirjinta ya shiga luguden bugu , ta cigaba da tafiya qirjinta na dokawa da sauri badar na biye daita a baya tana cigaba da magana akan abu ɗaya da Ummita ta kasa fahimta .
a tsakiyar lambun suka iskeshi zaune shi kaɗai akan daya daga cikin fararen kujerun dake ajiye agurin domin shakatawa hannunsa rike da waya sanye cikin kananan kaya farar riga da blue jean gabansa farin table ne dake dauke da ruwa da lemu da snaks naunayen ajiyar zuciya ta sauke tana jin wani irin yanayi mai wuyar misaltuwa a jikinta , yayinda kyakkyawan murmushi ya bayyana akan fuskan badar gabadaya ta maida hankalinta akan mah'ruf cikin rawar jiki badar ta dafa kafadun Ummita da karfi "Ummita wannan yayan naki ya haɗu matuka kalleshi saboda Allah ina son yanayin kamewarsa , bana son nayi aure a wata kasa amman da yayan nan naki zai soni ya aureta wallahi da babu abinda zai hana na aureshi , amman wannan asirce asirce da ake bina dashi bazai bari wani namiji yaga haskena bare har yace yana sona ....
a matukar fusace ummita ta zabga mata ƙatuwar harara kana tace "wai ke wake miki asiri da kika damu mutane da asiri ake miki "wallahi zuwa nake ana duba min .
"amman dai kinyi hasara rayuwa wallahi kina ta zuwa gurin malamai da bokaye suna amshe miki kudi suna faɗa miki karya kou ?
"to wallahi ana min asiri gashi an hanani cigaba ba'a son cigabana ,abarni jiya iyau a shekaruna ya kamata ace ina da aure har da yara biyu shekarata ashirin fa yanzu amman kalli yadda aka barni duk na susuce na lalace "kinga malama ni dai gaskiya kin dameni gaskiya da maganar asiri asiri nan ni dai babu ruwana idan ma ana miki can ki karata ,ni dai karki kara min maganar asiri "
",okay dan na faɗa miki matsalata shine zaki dinga min haka ba laifinki bane ni da tattaro nazo gidan saboda ke ,bazan ƙara zuwa ba har kubar kasar nan ,"dan girman Allah karki ƙara zuwa "ai daman bazan ƙara zuwa ba.
"oya kama gabanki tun yanzu "bazan wuce ba sai lokacin dana ga dama tafiya zan tafi tunda gidan ba naki ba hasalima nafiki karfi da gidan "koma dai menene ni dai karki kara min maganar asiri ko yaushe ko yaushe
Book Chapters
Chapter 26
Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76