Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ta d'ago idanunta da sauri hawaye na zubowa daga cikinsu "Allah yasa ......tayi maganar wani kuka na kufce mata "na tuba Allah , Allah kayi femin, ka sada Aminu da rahmaka ,kasa aljana madaukakiya ce makomasarsa "Ameen ya Allah injiniya ya amsa yana mai tausayawa mata ..

I really share tears on this page Allah ya jikanka rayhan..




TWO FRIEND'S ( BSBS)


💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL


AL'QALUMAN



*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*


~DEDICATED TO~
*MARYAM SANI KALGO*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim


PAGE 34

.... Damuwa ta ninku a zuciyar ummita, bata samun yin ishashen bacci saboda tsananin fargaba da tunanin wasihar rayhan ,bata
san me aurenta da Mah'ruf zai haifar ba , farinciki ko akasin haka ,da iyayensu zasu yarda da an barta ta auri mutumin da bata sani ba ,kuma wanda bata da wata halaka dashi .

tashi tayi daga kan gadonta ta zauna abakin gado kafafunta na kasa gaba-daya ta rasa meke mata dadi a yanzu da take rayuwa a cikin duniya , zuciyarta baguwa take sosai akan lamarin , idan ta hasko aurenta da Mahruf kuwa ji take kamar ta 'bace ta bar duniyar ba dan tana tsananta kiyayyarsa ba, dan tuni ta shafe wannan babin a cikin zuciyarta ,ita dai bata kinsa haka zalika bata tsananin sonshi sai dai duk saukar numfashinta da tunaninsa yake gudana ..

Mikewa tsaye tayi jikinta a matukar sanyaye ta shiga bayin dake makale da d'akinta ta d'auro alwala ta fito ta soma jero nafiloli koda ta idar bata tashi ba zama tayi ta dinga wa rayhan addu'a da neman zabin Allah tana wani irin kuka mai tattare da jin d'acin mutuwarsa a she rayuwar aurensu bazai je ko'ina ba ?
Tasan tana matukar kin aurenta da shi amman da ya rayu zata iya jure rayuwa dashi a duk yadda ta samu rayuwa a gidanshi sai gashi mutuwa tayi musu mai kankat ta É—auke mutumin daya É—auki tsawon shekaru yana fama da soyayarta ... "wayyo Allah ya rayha dina ta furta cikin wani irin kuka "me yasa ban kaunaceka tun kana raye ba a lokacin da kake bani kulawa kake rokona na sonka ?
"Kai ma baka rasa komai ba ,baka da aibun da mace zata kika ,baka da makusa yayana mai sona da kaunata nayi kewarka subai'arka na cike da kewarka .... "Ya Allah ka jikan masoyina kuma mijina aminu ka kai rahma kabarinsa kasa aljanna madaukakiya ce makomasarka ta karasa addu'ar tana fashewa da wani sabon kuka ta jima zaune akan sallaya tana masa addu'a sannan ta mike ta koma kan gado kusa da meenal dake kwance ta zuba mata ido tana kallonta .
"ina ma nice ke meenal sam baki da wata damuwa sai damuwarta data daurawa kanta dan yanzu da zata farka ta ganta zaune dole ne ta tashi ta tayata jimamin tabbas ita din yar'uwa ce ta hakika mai zumunci ....
"Allah ka dangwamar da wannan baiwa taka cikin farinciki daf da sallar asuba ta sum'baci goshinta "ina tsananin sonki menal duk duniya bani da tamkarki Allah ya azurtaki da miji na gari mai kaunarki kiyi rayuwar jin dadi sannan ta mike a kusa daita tana tashinta dan gabatar da Sallah asuba .

A hankali ta mike tana murza idanunta lokacin da ummita ta sake shiga bathorrom cigaba da zama meenal tayi a gefen gado tana jiran fitowar ummita ..
bayan data idar da sallar ma ta dade zaune tana lazimi sannan ta samu bacci ya É—an d'auketa kwata kwata baccin data samu bai fi na awa É—aya ba ta tashi ta shiga wanka ...
Suna zaune akan dining ita da menal suna cin abinci ,yayinda mama ke zaune tana kallon islamic chennel ya shigo ya zauna kusa da mama sanye da bakaken kaya masu matukar kyau sai dai fuskar nan tashi a d'aure take tamau babu alamun fara'a , ya rame sosai amman ya ƙara yin kyau sosai kamshin mayataccen turarensa ne dimauce parloun'n .

a hankali mama ke janshi da hira can ta maida hankalinta gurinsu ummita taga menal ce kadai ke cin abinci ban da ummita "ki maida hankali mamana ki cire damuwar nan kici abinci ,a hankali ta motsa labbanta tace "to mama abincin ne bana jin dadinsa wallahi "haka nan zaki d'aure dukkaninmu daga Allah muka zo kuma gareshi zamu koma ,duk ita zaman jira take muke , Allah yafi mu son wanda ya amsa sosai ta dinga yi musu nasiha har mah'ruf tana basu kwarin gwiwa lokaci daya wani natsuwa ya mamaye zukatansu ...

*****"

hajiya saudat an saduda domin kuwa ta mikawa Allah lamarinta ba dan ranta yaso ba sai dan ayar da Allah ya saukar akanta , adduarta kullun Allah yasa rayhan dinta yayi ajiya a cikin ummita , shi yasa yanzu ta kasa ta tsare kullun tana bangaren mama har ma daga karshe ta faÉ—awa inna akan a dawo da ummita bangarenta dan ta haka ne kaÉ—ai zasu samu damar saka mata ido kada aje tana da ciki su salwantar mata da jika , take inna ta amince da maganarta dan taje bangaren mama da kanta bata tura dan sako ba tana bawa ummita umarni ,ko kallonta ummita batayi ba ta cigaba dan Jan carbinta da taga abun na Inna na son zama rainin wayo sai ma mike ta shigewarta d'akinta.

"kina jina da wannan yar taki ba wai ita muke yi ba ,cikin jikinta muke da bukata , idan kuma baki saka baki ta dawo bangarena ba duk abinda ya samu cikin bazamu yarda ba kotu ce zata rabamu mama tayi ,sororo tana kallon inna gabanta na matsanancin fad'uwa "daman ciki ne ga ummita bata sani ba ko me ?
"Ni zaki tambaya dan kin rainani ai sai Kije ki tambayi yarki zaki fi samu gamsashiyar amsa agurinta , jin amsar inna yasa mama ta fahimci a filli tayi maganar "shikenan inna ai wannan abun faricikine garemu gabadaya Allah ya inganta .

"ameen idan har da gaske kike ,ki tashi ki kirawo min ita mama ta mike jiki a sanyaye ta nufi d'akin inda ta iske ummita zaune tana kuka, tana jin motsin shigowar mama tayi saurin goge hawayenta "maza tashi kibi inna , ai wannan abun farinciki ne ,kuma ina da tabbacin wannan cikin zai iya kawo karshen komai garemu ,wallahi ni kaina farinciki nake z
zamu samu madadin rayhan a duniya ,ummita ta dinga kallon mama hawaye nabin kuncinta gabadaya ta rasa fahimtar inda maganarta data Inna suka dosa ,kuka take sosai har da shesheka mama ta k'arasa inda karamin fridge dinta yake ta tsiyayo mata ruwan sanyi ta mika mata , ta kasa amsa tana wani irin kuka " ta kai ruwan bakinta bude bakinki ki sha ruwa kiji sanyi a yau ina sake alfahari dake mamana yadda kike min biyayya Kema Allah yayi miki ,a hankali ta bude bakinta ta kurbi ruwan data jishi kamar ruwan Kasafi .
Mama ta zauna kusa daita sannan ta daura kanta a saman cinyarta hannun tasa a saman kanta tana shafa sumar kanta mai tsananin yawa duk cikin zuri'a hajiya inna babu kamarta a komai, bangaren kyau da gashi ilimi da shiga ran jama'a , "kukan ya isa haka mamana kinsan bake kad'ai bace dan Allah ki daina yawon kukan nan , su hajiya inna zasu iya É—aukar abun wani iri har ma su fassarashi a matsayin ko kina bakincikin da samun cikin jikinki ne ..
Magana take son yi akan zantuttukan mama amman bakinta ya kasa furta komai sai idanunta dake tsitayan ruwan hawaye "ina ma zatonsu mama da Inna zai tabbata gaskiya ne ai kuwa da ita kanta sai tafi kowa farinciki a yanzu da ya rayhan dinta ya barta take tsananin jinsa a zuciyarta ...
"Ina ma ina ma ina ma zai dawo gareta data nuna masa soyayya fiyye da yadda yake ikirarin yana mata .
"Muje hajiya inna na jiranki "
"Me zan mata mama ki barta da wahalarta idan tagaji da jira zata wuce?
"a'a dole fa zaki bita meye a ciki duk fa a gida daya muke karki damu kanki tashi kuje , meenal zata kawo miki abun bukararki da kayan sakawarki zama kifi jin dadin zama agurinta kasancewar bangarenta na jama'a ne wannan ya shiga wannan ya fita .

" tashi Allah yayi miki albarka "ameen mama , babu musu ta mike jikinta a sanyaye,itama ta mama ta mike tayi gaba ummita na biye daita a baya "fatan dai ba wasu abubuwa kika kitsimamata ba ?
"Ko É—aya inna ga tan Allah ya inganta "muje dan gaba zan sakaki karkije kiyi mana hasarar ....
Maganar taso bawa ummita dariya sai taki yin dariya ta ta'be bakinta tana zabga mata ƙatuwar harara .....

*****
Babu laifi zaman ummita a bangaren inna ta É—an samu natsuwa dan Inna tana kula daita sosai bama zakace bata sonta ba, komai tace tana so yanzu ne tana rawar jiki zata bada kudi a tsiyo mata, haka ma bangaren hajiya saudat duk abinda tayi sai ta aiko mata dashi, sannan duk abinda tasan na masu ciki ne duk inda yake sai tsiyo an kawo mata , wanda ita ummita sam bata ci saboda ,ba komai llikita ya yarda taci ba saboda rashin lafiyar da take fama dashi data da can baya da kuma ta yanzu a dalilin mutuwar mijinta .

komai ya tsananta gareta domin likita ya sake hanata cin nama ,da abu mai gas , hatta ruwan sanyi an hanata sha , sannan ya umarceta ta yawaita shiga cikin mutane tana mu'amula dasu , ta haka ne zata rage tarin damuwar dake damun zuciyarta ..

Bangaren inna kuwa bangaren jama'a ne idan wannan bai shigo ba wannan zai shigo ayita hira su Jiddar da Malik ma kusan kullun suna gidan .
amar da sadam Jiddar da malik da Sa'ada Maryam da aslamiyya suna tsakiyar porloun inna kan daddumar mai taushi suna hira , Sai meenal dake ta zirga zirgan a uwar d'akan inna zuwa parloun domin duba ummita dake kwance , wannan zuwan nata shine na uku ta iske ta tashi, ummita ta mike ta zauna daga nad'ewar da tayi cikin borgo .
"Yauwa kin tashi gasu aunty jiddah can sunzo dubaki ,ta yatsina fuska alamun wanda ya tashi daga bacci sannan
ta sauko daga gado tana yatsina fuska "sannu inji cewar meenal ta amsa tare da soma d'aga kakafunta da kyar ,ko cikakken minti goma batayi da fitowarta ba hancinta ya soma jiyo mata kamshi turarensa mai ratsa zuciyar duk wanda ya shaka ,nan take parloun'n ya É—auki sauyin kamshin turarensa mai dadin shaqa, gaba daya ta maida hankalinta akan qofar data fi zaton tanan qamshinsa ke shigowa har sanda ya k'arasa shigowa gabadaya cikin natsuwa yake takowa cike da kamala fuskarshi ta sake yin haske komai na jikinshi casss cass daidai da jikinshi sannan mai kyau babu yadda za'a yi ya shigo waje bakaji ya burgeka ba ...
A hankali zuciyarta ta amsa ta shiga tsalle da dokawar data saba na babu gaira babu dalili kai tsaye gurin malik yayi ya mika masa hannu suka gaisa.

"babana ni yakamata ka soma gaishewa dan iyayi ka wani gaishe da wannan katon tulelen banza ta karashe maganar tana dariya .
ya É—an kalleta yana hararata alamun karta dameshi da surutu , amar dake zaune da kusa da sadam suka haÉ—a baki gurin gaisheshi a hankali ya motsa bakinshi ya amsa , sauran ma sukayi kokarin gaisheshi duk ya daga musu hannu shi bai san dalili ba yawon gaisuwa na damunsa asalima yana cikin abinda ke kona masa rai ayita gaisuwa shiyasa lokacin da suke yara ya kan ji haushin rayhan da usman saboda son gaisuwarsu tayi yawa ,kowa suka gani sai sun gaisar barin ma usman ,lokacin da suka girma kuwa raba hanya yake dasu dan idan suka dinga gaishe da mutane sai ya ji kwalkwaluwarsa na ciwo.

ya kance "wai ku bakwa gajiya da gaisuwa ne ?
Usman ne ke bashi amsa mutane rahma ne fa mah'ruf ,mutane na kallonmu sai mu wuce bamu gaishesu ba gaskiya ni bazan iya ba , kuma dai ni idan ana gadon gaisuwa nayi a gurin dangina dan ko aljani zamu iya gaisawa dashi ..

inna dake zaune ta bushe da dariya saboda ganin yadda ya amsa musu " bai dai kun iya zakewa gurin gaishe shi ba ai gashi nan , har da wani kayar da murya maganinku kenan gashi nan ya gwaleku ,ni da nake son gaisuwa ai bakwa gaishe dani ...
Suka zumburo baki , suna tashi daya bayan daya har meenal ummita kuwa tunda ta juyar da kanta gefe bata sake duban inda yake ba a ranta tace "bazan yi hasarar bakina ba ko na gaisheshi ba amsawa zai yi ba ....
shi kuwa magana yake son yi mata yaji ko tana da bukatar wani abu amman ya kasa bud'e bakinsa sai dai sosai zuciyarsa ke dokawa kamar zata fasa kirjinshi akanta , kudi masu yawa ya ciro acikin ajihunsa ya bawa inna yana mikewa tare da É—aukar wayoyinsa "me za'a yi dasu ?
inna ta tambayarshi tana dubansa "ki ajiye agurinki idan kuna bukatar wani abu .....

Sarai ta fahimci manufarsa amman sai tace "suwa kenan fa ?
Ya tsareta da manya idanunshi yana kallonta batare da yace mata komai ba "ka tsare ni da waÉ—an nan idanuwan naka , dole na tambaya kudin meye dan ban gane abinda za'a yi dasu ba.

"ya ja tsarki yana d'aga mata hannu "hajiya inna matsala gareki wallahi kin san abinda nake nufi amman dan neman magana sai kin 'batawa mutane rai .."
"Kai kuma sarkin zuciya ba ,daga tambaya zaka haiyayyako min ba kamar zaka cinyeni ai bani na kar zamon ba .. ....
"Shikenan ya isa kiyi hakuri " kai nifa da wasa nake maka ta yaya uba zai bawa yarsa hakuri, duk na fahimceka sarai kamar yadda ka faÉ—a Allah ya amfana ,a ranta tace da yanzu gurin uwarta za'a yita kai waÉ—an makudan kudin lallai bayan cikin jikinta har da alkhairi zasu dinga samu ....

Ya É—an saci kallon ummita , jin taki gaisheshi sannan taki yarda ta kalli inda yake a tun kallon farkon da tayi masa bata sake yi ba, har sanda ya mike zai fita hakan kuwa yayiwa inna dadi ,dan a gaskiya ita bata son wannan haÉ—in na mah'ruf da ummita gara dai idan Allah ya sauketa lafiya tayi aurenta wani guri daban , shima yayi nashi daban dan idan akayi auren anan za'a dinga jin muryarta dan bazata yarda a bautar mata dashi ba kai bama zata yarda ba a dinga mata dauki day day .....

*******

Wayarsa ce ta É—auki kara a lokacin da yake zaune a office sanye cikin blak suit da farar riga aciki yana zuba wani irin kamshi mai rasa zuciya gabansa system ne akan makeken table yana tura sakonin , sharewa yayi yaki É—auka ya tattara gaba-daya hankalinsa gurin abinda yake har sai da wani kiran ya sake yashigowa ya lalu'bo wayar ya danna ya manna a kunnenshi batare da yayi magana ba " hello habibi good morning ...?

Lumshe idanunshi yayi yana sauke naunayen ajiyar zuciya sannan yace ", morning dear ya kike ya jikin hajiya fatan tana samun sauki ?
"Alhamdullahi tana samun sauki sosai ya karin hakurin Allah yayi masa rahma " ameen ya Allah na gode sosai da kulawa a yanzu babu furuncin da yake jin dadinsa kamar yaji an yiwa rayhan dinsa addu'a .
Shiru sukayi su duka yana cigaba da aikinsa batare daya sake ce mata komai ba ,can taji shirin yayi yawa ta duba taga still yana kan layi, maida wayar kunneta tayi tana tunanin maganar data bugo tayi masa ,kwalkwarta ce tashiga shawagin tayi masa maganar ko ta fasa dan tasan halinsa abu kaÉ—an ke hassalashi har ya nemi burkice mata ,daga karshe ta rasa yadda zata shawo kanshi .
Lumshe idanunta tayi tana jin wani irin fargaba addu'ar da addu'ar Allah yasa zance da taji ya zamo karya ne , gyaran muryar data ji yayi ne yasa tace "habib ina son magana ne da kai amman zuciyata na cike da jin tsoro da fargaba tayi maganar tana yin shiru domin jin abinda zaice .

"uhmmmm ina jinki meke sakaki jin fargaba wannan maganar da yayi ne ya bata kwarin gwiwa ",uhmmmm amm daman nace na tambayeka da gaske zaka auri ummita bayan ta haihu ?
Yayi shiru na second biyu sannan ya ture system din gabanshi ya mike ya zira hannunsa É—aya cikin wandonsa yana cizan lip's d'insa na kasa yana jin wani dadin da bai san ko na meye ba yana ratsa sansar jikinshi ...
"Da farko dai wanda ya faÉ—a miki haka bai faÉ—a miki karya ba "
"Kenan gaskiya ne zaka hadamu tare ?
Ta faÉ—a hankalinta a matukar tashe tana dafe kirjinta "amman mai yasa za'a yi min haka saboda Allah bayan daga ni sai kai kawai na tsara rayuwata .
"sai ki canza ki maida shi a mu uku .
*WANNAN CE QADDARARMU* suhaima.

"Ni kaina ban tsamaci faruwar hakan ba lokacin da rayhan yake furta hakan gareni zuciyata bata amince da hakan ba ....
"Hakan ne ma zai faru, zuciyarka ta cigaba da kin rashin amincewa da hakan , dan bazan iya sharing dinka da kowa ba , dan ni kaÉ—ai aka hallicceka bazan iya rayuwa da kai kana rayuwa da wata ba ,tsaki yaja yana sauke numfashi "wannan tsarinki kenan ba tsarin mah'ruf ba ,tsarin Mah'ruf shine yayiwa iyayensa biyayya kina tunanin koda babu wasihan rayhan iyayenmu bazu isa suce nayi abu ba na tsallakewa umarninsu.

" bari kiji na faÉ—a miki ,ko a halin yanzu suka ce na barki na auri fatlion ita kadai duk yadda nake sonki suhaima zan barki bari kuma na har abada na zauna da fatlion Koda kuwa zan rayu cikin tsananin .
..."ni din zaka bari ,bari na har abada habibi ?
"Wace ke ?
"Ke din ba komai bace gareni akan umarnin iyayena ina son su fiyye da komai a rayuwata, bazan iya haÉ—asu da kowa da komai ba ,dan haka ki kama kanki karki É—auka sonki yayi min kamun da zan iya bujirewa umarnin iyayena .

"dan ma Allah ya taikaita miki wahala da ku uku zakuyi rayuwa dani kuma kuyi shering dina , tun a inda kike yanzu ki sauya tunanin zama ke kadai ,idan ma kika yi jinkiri dawowa zan iya hakura dake ..

"wayyohlly Allah nah zuciyata ta dafe daidai saitin zuciyarta da taji tana dokawa da wani irin sauri muryata a sanyaye tace "yanzu dai dole sai ka aureta ?
"Idan na aureta zaki fasa aurena ne ?
Shima ya tambayeta zuciyarsa a dake ,"bazan fasa aurenka ba saboda ina sonka "na É—auka zaki hakura ....."
"Ka daina cewa kana Sona habibi dan son da kake min baya hanaka faÉ—a min abinda kaga dama ,masoya suna kiyayye 'bacin ran junansu ne amman kai kullun cikin 'bata min rai kake , baka shaka ko fargaban faÉ—a min abinda ya fito daga bakinka koda kuwa ruhina zai baki ,na daina yarda da kalmar ta soyayya ta karashe maganar
DOWNLOAD
DOWNLOAD

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

11 months ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

11 months ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment