Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zame masa qaddara ne  babu yadda zai iya , da ana iya bude zuciyar mutun tabbas da zan bude miki zuciyarsa ki gani babu kowa acikin sai subai'a , kina tunani duk tsubace tsubace da kike zai rage soyayyata acikin zuciyarsa ne no soyayyata baza ragu  ba ,shi asirin naki ma tasiri ya karawa soyayyata dashi , ai kin rigada kinyi kuskuren dana shigo rayuwarku me kikace asirinki bazai tono ba zakiyi abinda kika ga dama a kuma lokacin da kika so sannan zaki kashe mahaifiyata bari kije lokaci yayi suhaima ki rubuta ki ajiye lokacin tonon sililinki yayi aron lokaci Allah ya baki domin ki sake shagala da duniya amman ina tabbatar miki rayuwa ta kusan miki muni ke da yan'uwanki , kin kusan zubda hawaye mara amfani Allah zai tona duk wani shirinku dake da yan'uwan naki ....

Wani mahaukaciyar dariya ta sake kwashe dashi tana nunata da dan yatsanta "wannan wasa kike faɗa wasa wasa wasan yara  ina jin dadin yadda  kika kasa yarda da fahimtata , idan Allah bai tona min asiri ba ke me yasa bazaki fada musu su sani ba ?    Bama zaki iya ba ta ya ma zaki iya tona min asiri ki fadawa mutane asalin boyayyen halina ko kin faɗa musu zai kasance zargi ne babu wata sheida da zasu tabbatar da nice amman kafin ki fadawa mutune asalin boyayyen halina na rigada na gama lalata rayuwarki da mahaifarki "Ki natsu ki fahimceni da kyau kamar yadda na faɗa miki zan iya daukar ran kowaye akan mijina wallahi da gaske zan iya kuma  mahaifiyarki ce mutun ta farko sai ke  idan kika yi kokarin cigaba da rayuwa da mah'ruf, ki furta bakya son shi ya rabu dake shine zaman lafiyarki a duniya  ta karasa maganar tana dauketa da marin dayasa tayi mutuwar tsaye "ta juya  bata tsaya jin me zatace ba ta fice daga gidan gaba-daya zuwa gidan hajiya rahma  tun daga haraban gidan ta cire mayafinta sannan ta karaso parlou'n Hajiya rahma ta zauna tana kiran sunanta "yayarmu na dawo ta faɗa tana  sauke numfashi  ,ta fito daga kitchen sanye cikin doguwar riga tana murmushi "ya kuka kare da shegiya ? nan suhaima ta koro mata komai "yauwa  autar hajiya kin min dade haka nake so gara da kika firgita idan tana da hankali zata bukaci rayuwarta akan mah'ruf..

******

Hajiya rahma  na zaune ita da suhaima  idanunsu  na kan tv hannun kowanensu  rike da plet tana cin soyayyen cray fish , zulaihat ta shigo parlounta  da kuka kamar wacce aka zane ya'yanta duka na biye daita , da sauri  hajiya rahma da suhaima ta ajiye plet din hannunsu suka   mike a tare  jikinsu  na rawa suka  isa gareta "zulaihat lafiyarki kike wannan uban kuka waye ya mutu?  zulaihat bata samu damar yi mata bayani sai babbar diyarta ce  ta shigo korowa hajiya rahma bayani  "shekaranjiya nida mama muka je kasuwa siyan kayan  abinci  da kayan redymedy    gurin  costomer dinmu ,daman duk sanda  mama taje sai sunyi faɗa da matar  dake siyar da kayan abinci daga karshe ta siya mu wuce  haka ce takasance a shekaranjiya mama taya wa mai saida redymedy kaya  matar tace bazata siyar akan yadda mama ta taya ba mama ta juya zata wuce sai matar ta zageta da yoroba dan batayi tunanin mama naji ba , shikenna sai mama ta dawo ta rama daga nan sai  faɗa ya kaure a tsakanunsu ,daga kallon dan matar mama tayi tace sai ta binne  d'anta shine ɗan ya mutu yau da safe  ita kuma matar tace Allah ya kasheta mama ce ta kashe mata da , yanzu haka an cika unguwarmu da police ta kofar baya abbanmu ya bude mana muka fito zaro ido hajiya rahma da suhaima  suka yi  "me ya kai ki wannan furucin zulaihat ?

"wallahi yayyarmu ban kashe mata d'anta ba bani da hannu cikin mutuwarsa gabad'aya ilahirin jikin hajiya rahma  rawa yake take cikinta ya kada ta nufi bayinta na parlou'n ta soma zuba zawo ta dade a cikin bayi sannan ta fito "zulaihat kin cuci kanki me ya kaiki wannan danyen aikin ? "Nima ban sani ba ta faɗa tana rushewa da kuka "yanzu meye abun yi  ? Inji cewar suhaima "kira bashir naji halin da'ake ciki  wayarta ta mikawa mumynah   nan  ta kira abbansu ta mikawa hajiya rahma yana ɗauka yace "Kinga maseefar da kika jawo ko ?  ban san wace irin mace bace ke  tunda na aureki daidai da rana daya ban taba samun kwanciyar hankali  "bashir hajiya rahma ce ba zulaihat bace "yanzu ya ake ciki ?numfashi ya sauke "police sunce duk inda take na tabbatar da karfe ɗaya  daidai na ranar yau na damkata a hannunsu tunda tana gidanki bari muzo yanzu   .......

TWO FRIENDS BSBS

💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL

AL'QALUMAN

*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*

DOMIN SAURARON LITTAFAINA SABABBI DA TSOFAFFI KUYI SEARCHING DIN *HAUSA BAKWAI*

~DEDICATED TO~
*UMMIN KADUNA KAWAR AMANA*
*MARYAM OBAM KAWAR HIRA KAWAR AMANAR*
*DARLING MIMI'S QUEEN KAWAR HIRA KAWAR SIRRI*
*JIKAR KULU KAWAR AMANA KAWAR KWANTAR DA HANKALI*
*HASSANA DAN LARABAWA KAWAR SIRRI KAWAR FADAR GASKIYA*
*MRS ADAM KAWAR AMANA KAWAR HIRA *😃😃😃😃😃😃😃😃😃😃😃

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

PAGE 70

"Haba bashir karka zo da police ka nuna musu baka san inda take ba, "na nuna musu bansan inda take ba su kamani? yayi saurin katseta ta hanyar fadar haka a kausashe "wannan ne kuma bazai yiwu ba gaskiya , ai mugun bakinta ne ya janyo mata wannan masefar , idan ma kika bari ta gudu wallahi ke zance su rike a madadinta yana gama fadar haka ya katse kiran, cikin hajiya rahma ya sake murd'awa da karfi , ta tashi da gudu ta shiga toilet jikinta na rawa ta shiga zuba zawo bayan kamar minti uku tayi tsarki ta mike ta tsaya jikinta na wani irin rawa ta kusan minti biyar tsaye a bayi tana wanke hannunta da fuskarta sannan ta fito tana d'aga kafafu da kyar ta zauna gefen suhaima tana sauke numfashi "sannu yayarmu suhaima ta furta jikinta a mace ta gyada kai kawa , ita kanta suhaima cikinta kadawa yake da kugi gabadaya sun firgice sun fita haiyacunsu "muna cikin tashin hankali inji cewar suhaima "babba ma kuwa hajiya rahma ta faɗa zulaihat najin haka ta fashe musu da kuka "wallahi nayi danasani abinda ya faru me yasa naje kasuwa a ranar da na hakura ban je ba ? ta karasa maganar tana wani irin kuka nabil da mumynah suka rungumeta suna goge mata hawaye .

shiru suka yi na wani lokaci sannan hajiya rahma ta d'ago idanunta ta zubawa zulaihat " kiyi shiru zulaihat ba zaki dangwama a hannun hukuma ba zanyi duk abinda zanyi matukar kudi da bokaye na doron duniya zan fitar dake mu jira zuwansu ,bayan mintuna talatin suka fara jin jiniyar motar yansanda a kofar gida a tare suka mike tsaye suka yi cirko cirko suna kallon juna , jikin zulaihat na rawa da wani irin kuka ta rungume hajiya rahma ajikinta , bashir ne ya fara shigowa ya zuba musu ido yana Kallonsu gaba-daya a tsure suke ganinsa yasa suka saki juna , a tsanake ya fara magana cikin fushi da bacin rai "ba dai baki da tunani ba , sannan bakya tunanin abinda harshenki zai faɗa ba , abinda kika saba faɗa min gashi nan ya janyo miki bala'in da masefar da babu wanda ya isa ya fitar dake ,kowa kina iya fadawa maganar da kika gadama batare da tsoro ko fargaba ba yanzu ga karshen mugun bakinki nan ga maseefar da bakinki ya jefaki ciki kina tunanin akwai mai fiddake daga cikin wannan bala'in ...?

"wannan ai ba wani abun damuwa bane bashir da kake tada jijiyoyin wuya hajiya rahma ta faɗa zuciyarta na bugawa da matsanancin karfi , wannan qaddara ce, kuma tana kan kowa kai ma baka fi karfin haka ta faru da kai ba ,abu ya rigada ya zo da karen kwana dole zai faru bashir , batun wanda zai taimakawa zulaihat kuwa nice idan kai mijinta uban ya'yanta bazaka taimaka mata ba ni zan taimaka mata tunda ta zame min dole bazan taba barinta cikin wahala ba muddin ina raye , duk runtsi duk wuya zan fito daita kuma a cikin kankanin lokaci do you understand ta k'arasa maganar cikin matsanancin fushi tana watsa masa harara da kallon banza .....

"ka bani mamaki bashir kana fadar magana kamar wani karamin yaro kamar ma kaji dadin abinda ya faru daita sam banyi expecting zaka yi haka ba ,ya tsaya yana Kallonta "to ni me na faɗa bayan gaskiya abinda take yi ne na fada ko zan danne gaskiya ne saboda tana matsayin matata ? hajiya rahma tayi shiru tana dubansa tana mamakin yadda yake faɗa mata magana kan shi tsaye yau, mutumin dake zullumin haduwa daita shine yake faɗa mata magana ? tayi maganar a kasan ranta a matukar fusace ta bude bakinta tace "karewar fadar gaskiya kace a gabanka tayi kissan ...

" me ya kamata muyi yanzu yayarmu bamu da isheshen lokacin dogon magana fa ? inji cewar suhaima data fi kowa shiga tashin hankali "yayyarmu dan Allah ki taimaka min nasan zaki iya yin komai tunda kika furta , kuma daga yanzu zan kwantar da hankalina nasan kina sona kuma zakiyi komai dan ki fitar dani daga wannan bala'in, hajiya rahma ta matso kusa daita ta dafa kafad'arta "zulaihat karki damu zan taimaka miki bazan barki ki ɗauki wani lokaci ba zan yi komai muje ta karasa maganar tana riko hannun zulaihat suka nufi haraban gidan inda police Ke tsaye rike da bindigogi ,matar da danta ya mutu na ganin zulaihat tayi saurin nunata da yatsa "itace wannan nan itace ta kashe min d'ana take police sukayi kanta da bindiga , nabel da mumynah suka fashe da kuka sukayi gurinta bashir ya kamosu jikinsa ya rungumesu bai taba nadama da danasanin auren zulaihat a rayuwarsa ba sai a wannan karon ,ya cuci kanshi ya cuci ya'yansa tun da bai za'ba musu uwa ta gari ba, suna ji suna gani police suka tasa keyarta a bayan mota suka wuce daita bashir ya tasa yaransa gaba yana ƙoƙarin shiga motarsa ..

"Ina zaka tafi dasu ? " ka bar su anan har sanda komai zai daidaita"girgiza mata kai yayi yana riko hannun yaransa "bazan iya barinsu ba gara suna tare dani "kana nufin bazakaje police station din bane ko me? inji cewar suhaima "me zanje nayi ? ya juyo yana kallon suhaima zuciyarsa na tafarfasa " kun ɗauki case din nan karamin case ko ? "Kusani uban ɗan yana da baki idan ma kuna tunanin za'a shawo kan matsalar ne cikin sauki Ku daina , yana gama fadar haka ya nufi mota ya shiga yaransa suka shiga ya bar gidan ransa a matukar bace "kuyi hakuri ya'yana laifi na ne ya furta haka yana share hawayen idanunsa "abbanmu ka daina kuka ka dawo mana da mumy kaji karka bari police su harbeta inji cewar karamin dan zulaihat nabel, shiru yayi ya kasa magana dan bai san me zai faɗa masa ba gara mumynah tasan komai dan akan idanunta komai ya faru ..

Kai tsaye *area g* aka nufa da zulaihat aka nufi d'akin bincike daita take dakin ya hargitse da hayaniyar yansanda dake zaune ciki ,kowa kallonta yake cike da mamaki wata police ta mike ta dauketa da gigitaccen marin da tasa zulaihat tuntsurawa bayan kujera tana zaro ido rike da kuncinta "kika iya kashe karamin yaro kamar wannan kamar ba uwa ba ? Espector runke ta faɗa tana kallon hoton yaron dake kan table " gaskiya baki da imani wasu hawaye suka sake zubowa zulaihat saboda azabar rad'ad'in , kuka take sosai kamar karamar yarinya "wallahi ban yi masa komai ba , bani na kasheshi ba , nan sauran police sukayi caaa akanta ana rubuta statement kafin kace me kamanin zulaihat ya canza saboda mari da duka gabad'aya duniya ta soma jujjuyawa daita..

Bangaren ummita kuwa tunda suhaima ta bar gidan ta shiga damuwa da matsanancin tashin hankali hawaye ne ke zubowa daga cikin idanunta a hankalin take tunanin irin rayuwar kuncin da sukayi a baya da mahaifiyarta gashi itama tana d'and'anar kwatankwacin wuyar da mahaifiyarta ta sha, maganganun suhaima sun samu kyakkyawan mazauni acikin zuciyarta, hawayen idanunta ya cigaba da zuba a hankali take rera kukanta tana tunanin anya kuwa bazata hakura da mah'ruf domin tsiratar da rayuwarta data mahaifiyarta ba ? "Idan kika yi haka ya tabbata tayi nasara akanta ki tsaya tsayin daka tunda kin rike Allah kyayyawar zuciyarta ta nusar daita, tana cikin wannan jimamin mama ta shigo dakin ta tsaya tana kallonta da tsantsar mamaki tana ganin mama tayi saurin goge hawayenta "kukan me kike yi ?"babu komai ta faɗa dan tasan ko ta faɗa mata zantuttukan suhaima ba yarda zatayi ba har gara ta fadawa Hajiya umma ko aunty.

mama ta tsura Mata ido "babu komai kike kuka ko kina bukatar komawa gidan mijinki ne ?ummita tayi saurin girgiza mata kai alamun a'a ta karaso gurinta ta rike mata hannu ta zauna sannan ta zaunar daita kusa daita ta tsaya tana kallonta tana nazarinta, ta ɗauke kanta tana tunanin wanda zata fadawa maganar ko zuciyarta zata rage rad'ad'i da take mata "ki kwantar da hankalinki mamana ki mika lamarinki ga Allah ki rike addu'a hasbiyallahu lailaailahuwa alaihi tawakaltul wa huwa rabul arshil azim ,azubikalmatillahi tamat min sharri ma khalaq ki ya waita yinsa safe da yamma duk wani sharrin mutun zai gaji ya barki ,nasan akwai abinda ke damunki kina dai boye min koma menene ina fatan ya zamo alkhairi atare damu gaba-daya, tana gama fadar haka ta mike tsaye "kowa yaje ya duba jikin hajiya inna har yanzu baki je kin dubata ba ,ki daure ki shiga ki dubata ,ta turo baki tana kallon mama "nima fa bani da lafiya idan naji sauki na shiga ,mama ta girgiza kai tana murmushi " sam baki gaji mai sunanki ba , bata da riko bare gaba Allah ya baki lafiya ki daure ki shiga , ta juya ta bar dakin tana fita ummita ta rasa wanda zata fadawa kai tsaye zuciyarta ta umarceta data fadawa mah'ruf koda bazai yarda ba ta ɗauki wayarta ta kira mah'ruf kira ɗaya ya dauka "ya'akayi qauna kina lafiya .... ? Muryarta a matukar sanyaye tace
"lafiya ya aiki ? Idanunsa ya ɗan lumshe yana busa mata iskar bakinsa ta cikin waya , "alhamdullahi ya karfin jikin naki ? "Lafiya kana ina son ganinka yanzu ? "lafiya ya faɗa yana sauke numfashi "akwai abinda nake son faɗa maka ne "uhmm ina jinki"ai maganar bazata yiwu a waya ba dole sai gani gaka "nayi tafiya yau din nan , shiru tayi zuciyarta na rawa kafin daga baya tace "yaushe zaka dawo to ? tayi maganar a shagwa'be .

"Not yet ki fad'i abinda zaki faɗa ko kinyi missing dina ne ? ta girgiza kai kamar yana kallonta sannan tayi shiru "haka ne ko ? tayi saurin cewa "no ya sauke numfashi murmushi na bayyana akan labbansa cikin natsuwa yace " kinga ni kuwa nayi missing dinkin sosai na kasa jurewa rashinki tare dani jiya nazo na tayaki kwana kika min wulakanci yanzu kin kyauta min kenan bayan kinsan bazan iya kwana ɗaya batare da naji dumin jikinki ba ? "ka bar wannan maganar plz maganar da na kiraka akai tafi wannan mahimmanci ,nan ta shiga koro masa komai da suhaima ta faɗa mata tun daga farko har karshe yayi shiru sai data gama ya sauke numfashi gabadaya atsorace take kar yaki amincewa daita sautin muryarsa ce ta doki dodon kunnenta "karki sake bari tazo inda kike ,zan kira mai gadi yanzu kar ya sake barinta ta shiga gidan wenesday zan dawo but dole na dawo gobe sun ɗan dade yana janta da hira yana rarrashinta haɗe da kashe mata zuciya sannan sukayi sallama ya kira mai gadin gidansu ya bashi umarni ..

Lokacin da hajiya rahma da suhaima suka zo basu samu damar ganin zulaihat ba , suka tambayi gurin wa case dinta yake ? akace musu yana gurin dpo, take suka nemi ganin dpo bayan dogon bayani hajiya rahma ta nuna zata iya bada ko nawa ne akan a rufe case din amman fur dpo yaki "wannan case din ba kamar sauran case bane uban yaron mahaukaci ne akan dansa idan kuga yadda yake hauka akanshi zaku sha mamaki Kinga bukatarku bazai yiwu ba , shi a son samunsa ne ma a wuce kotu zuwa monday hankalin hajiya rahma ya tashi zulaihat zata zauna har monday a tare dasu ,Kai bazai yiwu ba ta furta a kasan ranta tana riko hannu suhaima ta soma tafiya tana janta bata tsaya ko'ina ba sai gurin motarta tayi shiru tana tunanin abun yi kafin daga baya tace "suhaima muje na ajiyeki a gida ki zauna min da yara ,zani ishari gurin malamin nan muga yadda za'a yi dan bazan iya barin zulaihat agurin nan ba ta karasa maganar tana buɗe murfin mota ta shiga suhaima ta zagaya ta shiga da sauri suka bar haraban station ta sauke suhaima a kofar gidanta ta ɗauki hanyar isheri tana isa ta zube a gaban bokanta tana koro masa bayani bayan ya gama saurarenta yace "za'a yi aiki da zai fito daita sai dai yana da matukar wahala "ka fadi ko menene zanyi muddin zulaihat zata fito "aikin zai ci rai sai an kashe wani acikin dakinku sannan aiki zai ci ya karasa maganar yana Kallonta ....

Tayi shiru qirjinta na bugawa haɗe da zaro ido "mu nawa ne da zan bada ran mutun daya duka mu uku ne fa wa zan bada na fanshi ran zulaihat ka dai duba ko akwai abinda za'a yi bayan wannan ya sake dubawa ya d'ago ya dubeta zaki iya kasancewa dani na tsawon wata guda muna tarayya ? shiru ta sake yi tana kallonsa sannan tace" dama wannan ,ya mike tsaye "kina iya tafiya idan kin shirya kizo zuwa jibi itama ta mike "har jibi gaskiya yayi nisa zulaihat tayi ta zama a hannun police ni da nake son zuwa gobe ta fito "bazai yiwu ba akwai aiki da zanyi kafin na kusanceki ki kwantar da hankalinki ki barta har zuwa lokacin da na gama ina mai tabbatar miki zata fito ..

Haka ta baro gurin bokan bata dawo gida ba ta zarce wani gurin bokayenta taje guri ya kai biyar aka bata aiki iri dabam dabam ta dawo gida tana nunawa suhaima da yadda akace tayi amfani dashi "kinga wannan dashi zan gobe tsirara akace zanyi haihuwar uwata na fita tun daga gida har zuwa pencilima bazan dawo ba sai goshin asuba, sannan wannan ance lallai zulaihat taci gobe haka dai ta dinga lissafo mata su,daga karshe tace dole ki kwana a gidan nan suhaima Allah ma ya taimaka mijinki baya gari nima gashi abbansu bilal baya gida , ranar basu runtsa ba kwana suka yi suna tattaunawa akan lamarin ..

Washegari suhaima ta kira mah'ruf domin sanar masa abinda ya faru yaki ɗaukar wayarta dan haka ta tura masa text yaga text d'inta yaki reply sannan yaki kiranta ....
hajiya rahma ta shirya taje area g saboda maganin da zata bawa zulaihat sai dai fur police suka hanata ganinta haka ta gaji da magiya
ta dawo gida jiki a sanyaye hankalinsu yayi matukar tashi hatta mahaifinsu tunda yaji bala'in daya samu zulaihat qirjinsa ya buga bai sake sanin me ake ciki ba , bashir ya kasa hakuri yazo gidan hajiya rahma domin jin halin da'ake ciki kallon banza tayi masa a lokacin da yake tambayarta bayan ya gama magana "tace baka san hanyar area g bane ? ya kalleta a kaikaice batare da yayi magana ba "nasan kasani ko iskanci ne yasa kazo min gida saboda kai dakiki ne mahaukacin banza kawai maza tashi kabar min gida dan iska hada iri da kai ko bala'i dan....

"Dakata dan Allah daga abun arziki zai zama na tsiya ni ba dakiki bane haka ba mahaukaci bane ba kuma banza bane maganar hada iri ni ne zan ce hada iri daku ko bala'i ,ina ganin jiya da yau baki zauna da kin zauna da kunnuwanki zasu jiye miki abinda ke faruwa kowa Allah wadai yake daku ni kaina nadama nake nasan na auri zulaihat har zuwa rabuwarmu amman bansan lokacin dana dawo daita gidana a matsayin matata ba alhalin nasan saki uku nayi mata ya ɗan numfasa yana kallonsu "daga wannan lokacin bani ba zulaihat babu sakin bare nace na saketa yaya kuma Allah ya raya min yasa karsu yi mugun gado yana gama magana ya juya fuuuuuu ya bar gidan suhaima tace "yayarmu kinji abinda yace ?"bar shege da kanshi zai dawo yanzu bata shi nake ba bari zulaihat ta fito ..

Karfe hudu daidai mah'ruf ya sauka kai tsaye inda ya ajiye motarsa ya nufa ya ɗauki hanyar gida yana shiga gidan bangarenta ya nufa sai dai bai ganta ba da alamun bata gidan ya isa inda mai gadi yake mai gadi na ganinsa ya karaso da sauri yana masa sannu da dawowa ya amsa yana cewa "tun yaushe matar gidan ta fita ? "ai tun bayan daka bar gidan nan ta fita bata sake dawowa ba, yana jin haka ya juya yana kiran layin suhaima ta ɗauka tana rawar jiki "kina ina ? Ina ina gida ina yini ?"kina gida ya maimaita tace "eh bai sake cewa komai ba ya katse kiran ya nufi part din ummita ko cikakken minti goma bai yi ba ya fito ya iske mahaifin hafiz da wasu mutane da bai sansu ba ya karaso inda suke cike da girmamawa ya gaishesu nan suka shiga rokonsa, mahaifin hafiz har kasa ya durkusa yana kuka " karka bari na rasa rayuka biyu masu mahimmanci a rayuwata matata da dana kayiwa Allah da darajan iyayenka yaci darajar Annabi Sallallahu s.a.w sauran mutane suka saka baki ya numfasa yace "shikenna muje police station duk suka shiga mota suka nufi police station ya sanya hannu aka saki hafiz saboda shi kansa yasan anyi amfani dashi ne kamar yadda kanin mahaifinsa ya faɗa godiya sosai suka yi masa da saka albarka ..

A tsanake mah'ruf yake saukowa daga saman dpo kawai idanunsa yakai kanwani Matashin da ake hukuntashi adakin bincike,yana lekawa sai yaga fuskar mus'ab ne yaron daya taba kaiwa ummita hari ya ganeshi ne saboda hotonsa da yan'uwansa suka bada a lokacin da ake nemansa ,hakanan tsinci kanshi da zuwa ya tsaya a wajan, yana sauraron irin tambayoyin da ake mishi, acikin tmyr yaji cewa Ashe Neman matan aure yake da yammata,sai Dan sandan yake tambayarshi sunayan wynda yanema,to cikin sunayanne yaji ya ambaci sunan suhaima aciki, mah'ruf bai sanda ya shiga ckn office din ya nema yagana dashi, ya ciro wayarshi a aljihu yanemo hoton suhaima yanuna mishi yace "wannan ce suhaiman daka ambata ynz,? Ya gyada kai nan ya koro mishi duk abinda yafaru tundaga lokacin da Hajiya rahama takawo shi gidan jikinsa a mace ya fito daga da kyar yake daga kafafunsa idanunsa ya kada yayi jazir dan bakinciki ..

Misalin ƙarfe takwas na dare ya shigo bangaren mama ya iske ummita zaune cikin doguwar riga mama tsaye tana shirin zuwa gurin hajiya inna tana ganinsa ta saki fuska "saukar yaushe kai da kace wenesday zaka dawo ? wani abu mai mahimmanci ne ya dawo dani ummita ta kalleshi ta gaishe dashi ya amsa yana binta da wani mauyen kallo idanunta ta lumshe tare da mikewa shi kuma ya bawa mama hanya ummita ta haye sama cikin sanyi jiki ita kuma mama ta fita ..

tana shiga dakin ya shigo ya tsaya a gabanta yana Kallonta jikinta a sanyaye ta ta raba gefensa har jikinsu na gugan juna kamshin turarenta ya doki hancinsa ya kai hannunsa ya damko damtsen hannunta ya dawo daita gabansa ya matseta gam ajikinsa "ya kamata fushin nan ya kare na baki hakuri me kike son nayi miki qauna ? "Ki tausaya wa zuciyata sun dade a haka rungume tsam da juna yana shafata "a taimaka a yafewa mah'ruf nasan nayi kuskuren rashin yin bincike nasan tarbiyar mama bazata taɓa aikata haka ba "daga baya kenan ta faɗa tana zare jikinta tsaye yayi yana binta da kallo jikinsa na rawa ,ya matso kusa daita zai kamota ta goce tana turo masa baki kwalla na ciko mata a ido ta nufi kofa zata bar

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment