Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

asiri baki da abinda ake miki sai asiri me kike dashi me kike sawa ajikinki da za'a gani har ayi miki hassada akanshi bare ya kai ga anyi miki asiri ? Gaskiya kinyi hassara ki tuba ki daina zuwa gurin malamai ta karasa maganar tana rausaya jikinta tayi gaba ta barta tsaya rungume da hannuwanta ....

Daga inda yake zaune yana jiyo sautin maganarsu kasa cikin zafin rai suke maidawa junansu martani ya d'ago kwayar idanunshi a tsanake yana kallonsu ,a kallonsu da yake ya sake fahimtar lallai cacar baki sukayi , tayiwa badar halin nata kenan ya faɗa a kasan ranshi yana jan tsaki "ko'ina sai kin nuna halinki bai san sai yaushe zatayi hankali ba, duk yadda yake jin ana fadar zafin ransa bai kai nata ba, sannan a haka mutane suke cewa halinsu daya , shi da kafin kaga abokin fadansa da wuya .
Ɗauke kanshi yayi ya cigaba da abinda yake qirjinsa na bugawa kamar zai fasa qirjinsa ya fito .
Jikinsa ya bashi kallonsa take dan haka ya sake d'ago kanshi tana ganin zai d'ago tayi saurin kawar da idanunta akanshi .
Ya tsura mata sexy eyes har sanda ta sake d'agowa da niyyar kallonsa idanunsu ya tsarke cikin juna da hannunsa ya tafitota alamun tazo .
da kamar bazata ba sai dai tayi wani tunanin tasoma takowa cike da sanyi jiki har ta k'araso inda yake idanunshi na kanta ya kasa ɗauke idanunshi a bangaren ummita kuwa dadi ne ya kamata ko babu komai zata kasance dashi har ma taji amon muryarsa mai sakata jin kasala , da hannunsa ya nuna mata kujera dake fuskantar shi batare da yayi mata magana ba , kana ya maida hankalinsa kan wayarsa ,ta zauna har kafafunsu na gugar juna tayi saurin janye kafafunta saboda shock din daya ziyarci sansar jikinta ya ɗan kyalleta ta kasan idanunshi yana yatsina fuska "me ya had'aki da badar ?
Taji tambayar kamar saukar aradu a tsakiyar zuciyarta ,da sauri ta girgiza masa kanta tana wasa da yatsun hannunta , bata jin zata iya fada masa .
a sukwane ya sake d'agowa sosai tare da tsura mata idanunshi masu tsuma zuciyarta "tambayarki nayi ba cewa nayi ki zuba min waɗan idanun naki ba.
ta langwa'bar da kanta gefe fuskarta a shagwa'be kamar wata abar tausayi tana sake damke yatsun hannunta.
"ke me yasa kike da rashin hakuri ?
" kwananki daya a gidan amman har kin fara nuna halinki ko ?
Tayi saurin haɗe rai "dan bakaji abinda tayi bane shiyasa ,cikin sarkewar murya yace "okay na yarda ta miki wani abu , shiyasa nace ki faɗa dan nasan kina da faɗa da bala'i kamar hajiya inna ce ta haifeki amman ke naki sai an
taboki kike naki haukan, so ina jinki me ya hadaku ?
tayi shiru cike da takaici da bakinciki had'ata da hajiya inna da yayi ,wani irin tuttukin bakincikin ne ya dinga taso mata, gabadaya yanayinta ya sauya ta dinga jan tsaki a kasan ranta tana zaginsa..
Cikin second daya ya fahimci bataji dadin maganarsa ba , ya lumshe idanunshi ya bude yana sake kallon yadda yanayinta ya sauya , yayi tsadadden murmushinsa mai bayyanar da tsantsar kyawunsa yana miko mata hannusa "let's shake for that naji dadin yadda nayi nasarar 'bata miki rai kamar yadda kika batawa badar mutuniyar arziki ,Kinga Kenan na ramawa badar Kema kiji yadda taji dan haka bana bukatar sake jin abinda ya had'aku daita ....
"Saboda ka tsane ni ko ?
Tayi magana kamar zatayi kuka, ya d'age mata girarsa ɗaya sannan yace "sosai ma kuwa ai duk duniya nine mutun na farko dana tsaneki daman baki sani ba sai yau ? Yayi magana yana kafeta da idanunshi ..
jin haka yasa ranta sake ɓaci , alamar ta kama gabanta yayi mata da idonsa daya , babu mutsu ta mike a fusace tana jan tsaki "Allah ya isa da ka had'ani da wannan matar mai bakar zuciya tana tafiya tana zaginsa ,a kallon bayanta da yake ya fahimci zaginsa take .
ya girgiza kai "fatlion rayhan na da aiki sosai , idan bai yi hattara ba sai kin had'ashi da ciwon hawan jinin yana nan zaune har sanda usman ya karaso da abokinsa suka cigaba da hira Abdul atare suka ja kujera suka zauna ....
Bayan kamar minti goma Abdul yace "usman wai ina bakuwar gidanku ne ?
Nifa tun jiya dana daura idanuna akanta naji nayi mata ka shige min gaba zuwa Nigeria "wannan yarinyar da kake gani matar aure ce fatiha kawai ya a shafa inji cewar Usman "kai amman kowaye yayi min shigar sauri tunda ya soma magana mah'ruf ya shiru ya kasa cigaba da abinda yake ko dawo yana masa magana sharesa yayi cikin takaicinsa sai dai hakan bai sa Abdul daina yi masa maganar ummita ba ..

Wani bangare ummita ta nufa cikin lambu qirjinta na bugawa , ta shiga kai kawo agurin tana cinzan yatsa ,mikewa mahruf yayi a hankali saboda maganar Abdul ta soma damun kwakwalwarsa da tunaninsa ya tsani ayita magana ɗaya akan abu .
A hankali yake d'aga kafafunsa cikin takun isa yana shawagi acikin lambun , yayinda iska gurin ke ratsa sansar jikinshi yana jin dadin sahirtaccen iskar da dake shiga jikinsa takawa ya cigaba yi yana zagaye ko'ina har sanda ya tsinci kanshi a bangaren da take wanda zuwa lokacin ta zauna rungumeta da hannunwanta .
bayanta da kayan dake sanye ajikinta kawai ya fahimci itace zaune, karasawa yayi ya zauna gefenta har kafafunsu na gugan juna da saukar numfashinsa a gefen wuyanta , duk yadda take jin saukar numfashinsa da kafarshi dake manne da nata hakan bai sa ta dubi inda yake saboda haushinsa dake d'awainiyya daita.
a tsanake ya kai laulausan hannunsa gefen wuyanta da niyyar sake kular daita , take yaji wani abu ya tsarga masa tun daga tsintsiyar kafafunsa har zuwa tsakiyar kanshi sai da yayi nadamar abinda yayi .

Waigowa tayi a hankali inda yake ,ya tsareta da idanunsa dake cike da shaukin da bai san ko na meye ba, hakan yasa tayi saurin kawar da kanta gefe kamar zatayi kuka "bana son abinda kake min ta faɗa kamar zatayi kuka "me nayi miki ?
ya faɗa yana bin jinta da kallo "kasani ai ta bashi amsa atakaice, dan bata son maganar tayi tsawo atsakaninsu , idan ta wuce haka a karshe bakar magana zai guma mata ya barta da bakin rai.
Ya sake matsota sosai kamar zai shige jikinta "Ni kuma kinga ina son abinda nake miki saboda inyita ganin 'bacin ranki , Ina son na dinga ganinki cikin da... "dakata dan Allah ya mah'ruf banaso banaso stop what you are doing I don't like ta k'arasa maganar tana jan numfashi alamun zatayi kuka ,yayi murmushin gefen baki yana sake shafo gefen wuyanta "tam sarkin kuka menene abun kuka ya faɗa yana kafeta da sexy eye's d'insa "Ina ruwanka da kukana ni dai ka rabu da bakinciki had'ani da Hajiya inna da kikayi wannan muguwar matar mara imani , cikin kai daita bansan wanda nafi tsana ba ta karasa maganar tana turo masa ƙaramin bakinta , bata yi tsamanin ba taji yatsan hannunsa akan lip's dinta ya ɓalle mata baki ta saki ƙara mara sauti tare da kai hannuwanta duka gurin "baki da kunya fatlion .
"meye damuwarka da rashin kunyata ni dai karka sake had'ani daita wallahi da had'ani daita gara kullun kayita marina na yarda ..
Shiru yayi yana karewa karamin bakinta kallo wayarsa ce ta katse shirun daya wanzu a tsakaninsu, ciro wayar yayi yana dubawa sunan wacce ya gani yasa sakin murmushi sannan ya d'auka "hello ya faɗa a kasalance a bangaren suhaima dadi ya kamata a sanyaye tace "habibi an yini lafiya "lafiya ya amsa atakaice "tun safe nake kiran layinka yaki zuwa na tura maka sako ta what's app "uhmmmmm zan duba tana iya jiyo abinda take faɗa da amsar da yake bata, saboda ta bangaren kunneta ya manna wayar ta mike tsam zata wuce ya riko yatsunta biyu tare da kafeta da kwayar idanunshi suhaima taji yayi shiru bai sake cewa komai ba a tunaninta ko wayar ta katse ne dan haka ta soma faɗin "hello habibi kana kan layi kuwa numfashi da ajiyar zuciya ya sauke a tare sannan yace "kinga ina wani abu ne yanzu zuwa anjima zamuyi magana, bai tsaya jiran abinda zatace ba ya katse kiran .
Yayi shiru yana kallonta sannan yace "kina jina ta lumshe ido " nifa yunwa nake ji tunda nazo banci abincin daya kwanta min ba ,ki shiga yanzu ki min irin dahuwar indomin da mama take min ta watsa masa harara sannan tace "bazan iya ba ka kira badar mutuniyar arziki tayi maka ko ita wannan da kuka gama waya tana gama fad'ar haka ta fixge hannunta tayi gaba "haba shi yasa zakewar tayi yawa ashe wahala aikin yake son sata "ina jiranki idan kin isa karki yi stupid kawai mai fuskar zaki tayi masa banza ..
Kusan awa daya yana jiran dawowarta bata dawo ba haka yasa ya hakura amman ya lashi takobin sai yaci kaniyarta ko nan ko idan sunje gida ..

Kwanansu uku suka dauki hanyar dawowa gida a safiyar monday nan ma costom kamar bala'i , wannan karon basu sha wata wahala sosai ba , dan duk inda aka je kafin costom suyi magana ya fizgota saman fad'ad'd'en qirjinshi tare da yi musu bayanin matarsa .
kafin su kawo badagir gabadaya yanayinsa ya sauya saboda yawon haduwar da jikinsu ke yi, barin tudun dukiyar fulaninta dayafi komai dagula masa lissafi da sakashi jin kasala a sansar jikinshi, daga karshe dai manneta yayi ajikinshi yana fidda numfashi har bacci yayi nasarar d'aukarta .
tunin itama aunty aysha bacci ya ɗauketa ,yayi shiru tare da tsura mata manya idanunshi , feeling d'inta yaji yana d'awainiyya da ruhinsa da gangar jikinsa ,wani irin sanyi ya dinga ji ajikinsa a dalilin narke masa da tayi ajikinsa tana fidda numfashi da sauke ajiyar zuciya, yayinda shi numfashnsa ya dinga tsarkewa .
ahankali ya matso da fuskarshi daidai nata yana shaƙar numfashinta tare da busa mata iskar bakinsa wani abu na fizgarsa gareta wanda ya rasa gane ko menene har suka kawo gida tana lafe a qirjinshi tana sharar bacci , ya ɗan motsa qirjinsa yana jan tsaki tare da cewa "malama sai ki tashi ,kin wani narkewa mutane kamar kin samu bawa .
taja numfashi ta sauke tana buɗe idanunta da kyar aranta tace "maseefaffe kawai Allah yasa ba da son raina bane ,shine ya soma fita sannan ta fito ,lokacin tuni yaran gidan sun cika makil suna yiwa mama sannu da zuwa suka nufi cikin gida .
tunda suka dawo tunanin ummita ya ninku a zuciyar mahruf fiyye da sauran lokuta haka ya dinga d'aurewa yana son yakiceta acikin zuciyarsa amman ya kasa har gidansu jafar yaje da niyyar tambayarsa ko yasan dalilin haka "kace kana son gani zamuyi magana shiru yayi ya kasa cewa komai "ka faɗa min damuwarka mana ..?
"Barshi kawai zanyi ƙoƙarin solving din matsalar idan naga abun ya tura zan sake nemanka ..

haka yayita fama har tsawon wata daya wanda yayi daidai da sauran wata biyu ayi bikinsu gaba-dayansu sun shiga matsanancin tashin hankali barin mahruf da tunanin ummita ya addabi zuciyarsa ,duk inda ya motsa zuciyarsa dokawa take da matsanancin karfi akanta .

yanzu haka kwance yake a d'akinsa zuciyarsa cunkushe da tunani daban daban ga lokaci bikinsa da matansa biyu na karatowa ga tunanin sarkin naci sunan daya lakaba mata kenan "baya son auren sakina sai dai babu halin zai fito ya fada, haka tun da lokacin bikinsa ya karato zuciyarsa ke sake dilmiya cikin matsanancin tashin hankali kashi da kashi matsalar sakina da kuma yanayin da yake ji akan ummita yarinyar daya tsana a tun tasowarsa sai gashi tunaninta ya addabi zuciyarsa saɓanin wacce yake ikirari zai aura .

juyi kawai yake akan kafitirsa tare da janyo pillow dake gefenshi ya rungume a faffad'an qirjinshi gam yana jin tamkar ita ya rungume ajikinshi , duk ta inda ya juya ita ce makale da zuciyarsa tana shawagi , duk yadda yaso
ya yakiceta tunaninta abun ya faskara ,shi dai yasan a tunaninsa baya sonta to me ye dalilin na yawon tunaninta da zuciyarsa keyi ?
tunaninta ya addabi zuciyarsa da ruhinsa hawaye ne ya cicciko acikin kwarnin idanunsa yana takaicin kansa da wannan hali daya tsinci kanshi "why zuciyata me yasa kike tunanin ummita ?
"Ki taimakeni ki barni na huta da wannan banzar tunanin bana bukatarsa plz plz yayi magana jikinsa na ɗaukar zafi adalilin yanayin daya tsinci kanshi ,zuciyarsa ce ta dinga harbawa hatta numfashi da kyar yake iya fitarwa ,yayi shiru yana kallon celling d'akin kamkame da pillow, yana ciza lip's d'insa yana bleming kanshi dan me zai dinga tunaninta?
Rayhan ya shigo dakin ya gashi cikin wannan halin, yayi masa tambayar duniya yaki kulashi saboda gaba-daya rayuwar duniya tayi masa zafi ,tuninta yayi masa yawa gashi ya rasa mafuta ya rasa da wa zairautauna , rahyan ya fita hankalinsa a tashe ya faɗa a cikin gida saboda shima dauriya yake da yadda yake jin kanshi da zuciyarsa kowa ya shigo ya tambayi mah'ruf abinda ke damunsa yaki magana ,sai mama tazo da kanta saboda tana ganin idan itace tazo da kanta zai iya mata bayani ,a rud'e take shafa sumar kanshi tana tambayarsa "me ya faru baba babba ?
" meke damunka?nan ma shiru yayi mata yaki magana sai numfashi yake janyo da kyar "ko an maka wani abu ne ? Ta sake tambayarsa still
Yaki yin magana ,
mikewa tayi ta koma d'aki ,ganin cewar acikin kwanakin da sukayi a kwatono yana ɗan damuwa da al'amuran ummita , yasa mama ta turota a tunaninta idan idan tazo ta tambayeshi zai iya faɗa mata abinda ke damunsa tunda kowa yaje yaki cewa komai .
Itama ummita tazo a lokacin da hawayen idanunshi sun gama kafewa sai da idanunshi sunyi jazir tamkar garwashin wuta , tayi tayi ya gaya mata me ya faru ,meke damunsa yayi mata banza yaki kulata ,ta kyaleshi tana jin zuciyarta babu dadi kowa ya fitar harkarsa can bayan wani lokaci damuwar ta ragu ya mike ya shiga bathorrom yayi wanka ya shirya ya bar gidan ba shi ya dawo gidan ba sai daya saura ...

Washegari da safe kafin ya tashi ummita ta riga shi tashi yana fito zai shi masallaci ya soma shiga bangaren mama domin haka al'adarsa take kullun da asuba sai ya shiga bangarenta, a parlourn kasa ya hadu da ita ha hasko tochlight din wayarta kasancewar babu wuta ta tabbatar shi ne ,karasowa tayi gurinsa zuciyarta na wani irin mahaukanci buguwa ,muryarta a raunane tace " ya mah'ruf me ya faru da kai ne jiya ne ?
Kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kanshi "babu komai ya furta a can kasan makoshi"karka ce haka ai komai idan zai faru sai da dalili tayi maganar a daidai lokacin da haske ya haske parlourn gabadaya, ido cikin ido suke kallon junansu "ka faɗa min mana ya Mah'ruf, jiya mama bata runtsa ba har kuka tayi fa ta k'arasa maganar cike da shagwa'ba tana karyar da wuya ",ke ban son iskanci dan Allah ki kama gabanki rayuwa duniya ce kawai....
Ta tsura masa idanunta na second biyu sannan tace "Allah ya saukewa Allah ya baka hakuri ...
Banza yayi mata ya haye saman mama yana furzar da numfashi mai zafi daga bakinsa...



TWO FRIENDS (BSBS)



💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

https://youtu.be/-Xy64PJiHiQ

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL


AL'QALUMAN



*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*


~DEDICATED TO~ *BASEERA MUSA MAI KAJI , QANWATA TA KAINA ,INA JIKANA SULAIMAN? KI SHAFA MIN KANSHI*😄

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim


PAGE 29


....Ya shigo d'akin mama a daidai lokacin data fito daga bayi fuskarta da danshin ruwan alwala ,tsaye tayi tana binshi da kallo idanunta na ciccikowa da ruwan hawayen tausayinsa , take jikinsa ya kama rawa ya k'araso inda take tsaye ya riko hannunta "me yasa zaki zubda hawayenki mamana ?
"Dan Allah mama karki min haka, karki zubda hawayenki akaina nasan ban kyauta miki jiya ba .
Ta zare hannunta cikin nashi tare da zagayeshi ta wuce tana cewa "karka damu kanka da hawayena baba saboda baka damu da halin da zan shiga akan damuwarka ba , tun jiya kana cikin damuwa mai tsanani amman kaki sanar min da abinda ke damunka da har ya sakaka zubda hawayenka .

Ya sake takowa zuwa inda take "kiyi hakuri mama "me ye damuwarka tukunna ?
" me kake so ka faɗa min matukar ina da halinshi zan maka idan kuma bani da zan yi kokarin nemo maka shi ta k'arasa maganar ta tsura masa idanunta domin jin abinda zai faɗa ,girgiza mata kanshi yayi tare da yin shiru yana kallon yatsun kafafunsa ganin bazai faɗa mata ba yasa ta wuce ta ɗauki hijab dinta ta zira ta soma ƙoƙarin tada sallah ..
Mikewa yayi jikinsa a sanyaye tare da zura takalminsa ya fito ya nufi masallaci ..


sakina durkushe a gaban hjy umma bayan ta gaisheta sannan ta shiga koro bayanin abinda ke tafe da ita, "umma na zone kamar yadda nazo a farko da da ki amince kisanya baki mah'ruf ya aureni, na zauna nayi dogon nazari ko na aureshi ba abinda zan tsinta a aurenshi face bakin ciki da bacin rai, shiyasa na ɗawo akaro na biyu daki lamunce afasa auren nan saboda tsiratar da rayuwarmu da kwanciyar hankalinku da zumunci, dan matukar aka ce za'ayi auren nan komai zai iya faruwa madadin karfafa zumunci sai zumunci ya lalace , ni kuma bazan so faruwar hakan ba ta k'arasa mgnr hawaye na gangaro mata "me yasa zaki zo min da wannan maganar bayan komai yazo sauran kiris ?
"Ki duba kigani ta kowani bangare shirye shiryen aurenku ake yi me kike so mutane su faɗa ?
"Ummah na gode sosai da kulawarki da kaunarki gareni ni kaina a yanzu na fahimci ban dace da ma'aruf ba saboda na biyewa son zuciyata ne batare da na nemi zabin Allah ba yanzu kuma dana tsananta addu'a akan lamarin tare da ya kice soyayyarsa a zuciyats sai naji ko na hakura da aurensa babu abinda zai faru kuma zan cigaba da rayuwata har lokacin da Allah nima zai kawo min nawa mijin ...

Naunauyen ajiyar zuciya ummah ta sauke tana kallonta tare da yin nazarinta "bil hakki da gaskiya take magana " dan Allah ummah kada kiyi wani tunani daban ki ɗauka daman ni din ba matarsa bace "me kike tunanin baba sarki zai dauki al'amarin ?
"Bazai dauki komai ba saboda na rigada na sheida masa kafin nazo gareki nayi masa bayanin komai kuma ya fahimceni kema dan Allah ina son ki fahimceni numfashi ta sauke "shikenan Allah yasa hakan yazamanto alkhairi Allah ya albarkaci rayuwarki Allah ya baki wanda zai soki ya kaunaceki
"ameen ummah na gode sosai Allah ya bar girma "ummah ta shafa kanta kamar zatayi kuka sun ɗan dade suna hira sai wajen la'asar tayiwa umma sallama ta wuce .

A daren ranar ummah ta sanarwa Abba ya jima yana mamaki sannan yace " gobe
DOWNLOAD
DOWNLOAD

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

11 months ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

11 months ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment