Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ajikinka?
" yawon bin mata ka fara bansani ba ?
"me na rasa ajikina ?
"Ko kuma me na rageka dashi da zaka soma bin mata "ki natsu dan Allah ba wani guri na kwana ba a gida na kwana ...
"karya kakeyi wallahi da a gidan ka kwana kai tsaye zaka faɗa min gaskiya saboda baka karya na sanka nasan halinka ...
Wani irin bakinciki ne mai hade da zallar bacin rai ya tokare masa makoshi "idan baki yarda da maganata ba ,sai ki yarda da hukuncin zuciyarki ya zagayeta ya zai shige d'akinshi ta sha gabansa tana huci ....
"kina hauka ne ko kin soma shaye shaye ne da zaki sha gabana ?
"Duka nayi , ba laifinka bane dan kaga ina mutuwar sonka ne ,amman kasani soyayyarka bazata rufe min ido na kasa kwatar yancina ba ,gefenta yabi ya shige d'akinsa
aiko cikin sauri ta biyo shi tana zuba masa bala'i iri iri "wannan zalunci ne da rashin daukata da daraja da kayi , idan ma a gidan naku ka kwana ai an san kana da mata da za'a daure maka gindin ka kwana a can , Allah dai yana gani kuma sai ya saka min ,soyayya ba hauka bane ban ga laifinka ba laifina ne ,wallahi duk wanda yake da saka hannu akwananka wani guri Allah ya tsine masa albarka .......
ta karasa maganar tana shako wuyan rigarsa tare da shigewa jikinshi tana kuka " duk maganunta suna shiga kunnuwanshi amman yayi mata banza yaki tanka mata saboda yasan bai kyauta mata ba ,amman ba zai dauki tsinuwa daga gareta ba ta bude bakinta da niyyar sake furta wani abu kawai taji ya zareta ajikinsa ya ɗauketa da wani gigitaccen mari Wanda yasa ta saki kara ....
ta d'ago tana dubansa tare da kankace idanu "ka mareni ?
"Yes ko zaki rama ne ?
"Bafa tsoronki nake ji ba da kike fadar duk abinda yazo bakinki ya karasa maganar yana shakota ya makata da bango "to be your last warning da zaki tsaya gabana kina faɗa min magana ko na miki kama da dan iska ko me neman mata ?
"Ko ki yarda ko karki yarda a gidanmu na kwanta a rikice ta soma kokarin kwatar wuyanta tana nishi da kyar "ban iya duka ba shi yasa bana son yi ya d'ago kanta yana jinjigata "idan bakya control din bakinki zakiji jiki a hannunsa saboda ni ba irin waɗan mazan bane bazan kyaleki ba , zan ɗauki mataki akanki ya karasa Maganar yana wurgi daita ya take wuyanta da kafarshi ..

Manage

TWO FRIENDS BSBD


💗💗💗💗💗💗
     WANNAN CE
   QADDARARMU
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL
            
      
AL'QALUMAN


*AYSHA  A BAGUDO*           
*FAIZA  HAMMADU*

~DEDICATED TO~
MUHAMMAD AUWAL KANINA NA KAINA NAYI MISSING DINKA SOSAI  SAURAN KACE NICE KANWARKA ..

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

PAGE 42

..... bai ɗauke  kafarshi ba sai  daya   fahimci numfashinta  na  ƙoƙarin barin  jikinta  sannan ya ɗauke   kafarsa  yana shureta   ya  nufi bayi "kafin  na  fito  ki  san inda  dare  yayi miki stupid  kawai  yaja  tsaki yana  furzar  da  iska mai zafi daga bakinsa  sannan  ya  shige toilet   ..

  Kuka  take  sosai  rike da  wuyanta  tabi bayansa  da kallo  tana sake fashewa da wani sabon  kuka   tare da d'aura  hannuwanta duka a  saman  kanta "na shiga  uku  ta furta a fili  sannan    tayi  kokarin mikewa  ta  bar d'akin cikin  sauri  tun kafin ya fito  ya  iske  ya ninka  mata   wanda  yafi  na yanzu ..

Tana  shiga  d'akinta  ta ɗauki  waya  ta  kira hajiya  rahma  kira daya ta  ɗauka  tana jin ta ɗauka  ta sake rushewa da  wani  kuka "yayyarmu na  shiga  uku ina cikin wani  hali mah'ruf  bai kwana  gida  ba jiya  sai yanzu  da safe  ya shigo nayi hasarar nagani nan .....
"Nayi  missing  last hope dina  tunda  aiki   ba wani tasiri   yake  ajikinsa ba, ko ma  yayi  zuwa wani lokaci  zai karye  ki taimakeni  yayyarmu karki  barni  haka "

Naunauyen ajiyar zuciya hajiya rahma  ta sauke "shikenan   ki natsu ki kwantar da hankalinki  yanzu  aka  kirani zulaihat  sun  samu matsala  da mijinta  idan na  dawo  zamuyi waya "
Da  sauri ta tsaida kukanta  tace " matsala yayarmu to ko  nima na taho ne  ?
"A'a  kiyi  zamanki duk abinda  ake ciki zakiji, idan  kuma  kinji zaki iya zuwa  shikenan  ki taho din mu  haɗu a gidanta  "ok  gani  nan  zuwa yanzu   ta  katse kiran tare  da faɗawa bayi  tana tunanin  irin kamun da zata sake wa mah'ruf , dan  dole ta mallakeshi completely   , sannan dan dole  ya sawwakewa wacan tsinanniyar  yarinyar  tana bakinciki aurensa dake kanta ..

a lokacin   ɗaya suka fito da mah'ruf  ya  tsaya  jikin   motarsa   yana kallonta a  tunaninsa yaji zatayi  har  zai shiga mota  ya  dakata  ya soke hannunsa  ɗaya  cikin aljihun  wandonsa  yana nunata  da  keyn mota   "wallahi !  wallahi !!  idan kika yi  kuskuren   fita ko bakin  get  din gidan nan ne   ki tabbatar da  kin saku   agurina ,  ba zaki sake   dawowa rayuwa   mah'ruf  ba har abada   yana  gama  faɗar  haka ya  bude  mota  ya shige  ya  bar  gidan..
Dole  ta  juya  ta koma ciki  tana hura hanci "dani  kake  wallahi zaka san  baka da mutunci ..

sai  gurin  goma ummita  ta  farka    duk  wata d'awainiyya  ta  gidan mahruf ne  yayi   da kyar ta  iya  yunkurawa ta sauko  saboda   gabobin  jikinta da  taji sunyi mata nauyi ga wani ciwo da suke mata uwa uba kasanta  da  take  jin wani  rad'ad'i tamkar ana tsagata , jikinta  duk   babu  dadi  ta dinga jin tamkar  ba  a gangar jikinta yake  ba  ,
kasa  tafiya  tayi , ta durkushe  a  kasa tana ciza  lip's  dinta.

a  hankalin  ta soma rarrafawa  a daidai lokacin  ya  shigo d'akin  jin   motsin  shigowarsa  yasa  ta  koma  ta zauna  tana  dubansa  sanye cikin  riga  yellow da bakin  wando   ,saurin runtse  idanunta tayi tana yatsina  fuska,
da  sauri  ya  k'araso  ya tsuguna  a gabanta  ya kamo  hannuwanta  duka cikin nashi  yana massaging  ahankali "ya dai  meke  damunki?
yayi  mata tambayar yana  d'ago  habarta   tare  da  zuba mata manya idanunshi masu bugar mata da zuciya   ....
     Kawar  da  kanta  tayi gefe  tana matse  hannuwansa  cikin nata  "wallahi  gaba-daya ilahirin  jikina  ke min ciwo  tayi maganar a shagwa'be  hawaye  na zubo mata bisa kuncinta ..
tausayinta  ne ya kamashi   kamar ya zubar  da kwalla ya kamota  ta  kasa mikewa tsaye  "na  taimaka miki ?
Tayi  shiru  tana  kuka hancky ya cire a aljihunsa  ya kai goshinta ya fara  goge goshinta zuwa kuncinta  yana kallonta  itama shi din take kallo tana cigaba da kuka ,  bai  sake  sauraratar ba ya maida hancky  aljihunsa ya  ciccibeta  yayi  bayi  daita  ya zaunar daita a bathtube ya  tara  mata ruwa  mai  zafi   "ki  gasa jikinki  da  ruwan zafi.

   sosai ya   matsota  kamar zai  shige jikinta ya  kai bakinsa dai-dai kunnenta  ya  hura mata iska  bakinsa sannan ya soma magana cikin rada   "wannan  yanayin naki kamar  kinyi  kokuwa da wani  ciki  bacci ......?
ya karasa maganar yana tsotsar cikin kunnenta 
Tayi  saurin  kawar da kunnenta  dake cikin bakinsa  ta tsura masa fararen idanunta "haka ne ko ?
ta girgiza masa kai  " ki  dai   kiyi  tunani saboda gabadaya  yanayinki ya nuna  haka  dan  haka kiyi  hado  da  wankan tsarki   yana   gama faɗar haka    ya  juya ya fita  ta bishi  da  kallon mamaki  zuciyarta  cike da tambayoyi iri iri  "mamaki maganarsa  da kuma  sauyawarsa  take, gabadaya   a cikin  tamkar ba Mah'ruf din data  sani ba ...

A hankali  ta samo zubawa  jikinta  ruwan zafi ,  kwakwaluwarta  na tsanata  tunani   tana  watsawa  jikinta ruwa  da  kasanta  da take jin wani azaɓaɓɓen zafi "lallai tayi kokuwa  cikin  baccinta ko  mafarki zata ce , to amman ya'akayi  shi ya sani ?
Ta yiwa kanta  tambayar  cike   d'acin  rai  haɗe da bakinciki   "baza'a yi wanka tsarkin   ba ,ta furta  tana furzar da numfashin tana tsotsa tsakiyar kanta    "uhmmmm   ummita tunda  kina da tabbacin kinyi  mafarkin  mafi alkhairi  kiyi  wanka kawai  da wannan shawarar  tayi  wankan tsarki , ta cigaba da zubawa  jikinta  ruwan zafi  cikin ikon Allah yadda ta dinga   ruwan jikinta ruwan zafi  ta som a  jin dadin  da sanyi na ratsata  daga karshe  ma  tashige  cikin ruwan zafi gbdy  ta dade sannan ta fito tana dingisa kafarta  ...

  ta shirya cikin  wani  had'ad'd'en  atamfa  riga  da  siket  tana d'aura d'ankwali  ya shigo kamar  ya zame dankwalin  yayita kallon gashinta  yaji ,amman bazai  iya ba "muje kiyi breakfast wani sabon mamaki  ya kamata, tayi sororo tana kallonsa dan zuwa  lokacin lamarinsa  ya soma bata tsoro, bata gama mamakinsa ba ya k'araso  inda take yana fuskantartata   har numafashinsu  na tsarkewa guri ɗaya ,
  taji ya kamo hannuta "tunanin  me  kike yi,  kin wani  tsare mutane  da waɗan idanun naki  ?
Tayi  shiru taki cewa komai , ya lumshe mata  idanunshi  muryarsa a kasalance  yace "ki daina min  irin wannan kallon mai cike da abubuwa ,
"dole   nayi   dan  ka soma  bani tsoro ta fadi a  kasan ranta ..

"Ok  mamaki kike yi dan na tausaya miki?
Ta hura masa hanci kawai batare data yi magana ba
" Bai  kamata ki tsaya mamaki  ba  tunda haka  ba wani sabon abu bane ba kuma shine karo na farko  da zan taimaka miki ba  " ke din tsoka ɗaya  ce  agurin  mamana tun  tana raye ta damka amanarki a hannuna  duk da babu soyayya tsakaninmu   bazan   iya tsallakeki  cikin  hali  na rashin lafiya ba  , ya k'arasa magana  yana sake matsota  sosai yana shishina jikinta , tayi saurin ja  da baya taji kamar numfashinta zai  dauke  , gabadaya  ta rikice  tare  da yin kasa da kanta , bai san yadda akayi  ba shi dai  kawai  ya  ganshi   a gabanta suna fuskantar juna  kaɗan  ya  rage   qirjinshi bai  haɗe da nata ba , cikin tashin hankali ta kai hannunta ta  tokare qirjinshi  batare da tayi magana  ba  hakan yasa qirjinshi  ya tsananta  dokawa , ya  tsaya shiru haɗe da   kafeta  da idanunshi, kallonta yake kamar  wata sabuwar halitta  a gabanshi kafin daga  baya ya shafa sumar kanshi yana   lumshe  idanunshi  haɗe da  furzar da iska mai zafi  kana ya ɗan  ja  baya kaɗan   yana shafa goshinsa  "menene haka kake  yi mah'ruf you have to   control  your self  , ya  kake  ƙoƙarin  fito da felling dinka   alhalin ba sonta kake yi ba  ? Mikewa yayi tsaye yana
Yarfa  da hannunshi  sannan ya  tura hannuwansa duka cikin aljihun  wandonsa "muje kiyi  break  sai na kai ki hospital  ,  cike da karfin hali ta soma  daga kafafunta  tana dingisawa    ya biyo bayanta  yana  kare mata kallo  komai nata irin wanda yake so ne ina ma   yana  sonta ?
Ganin yadda take takawa da kyar ya matsota  ya ɗauketa ya rungumeta a jikinsa ta ware idanunta da mamaki tana cewa "no  karka d'aukeni  Ina da kafa .
Idanunshi na kanta yace "yau kafafunki basu da wani amfani dole na taimaka miki    ta bude idanunta tace "no  ..
Maimakon ya sake yin wata magana kawai ya cigaba da tafiya daita ajikinsa suka    sauko  parlour'n kasa ya ja kujera da kafarshi ya zaunar daita  ya duko ya daura habarsa akafadarta tana jin yadda yake sauke naunayen ajiyar zuciya wanda tasa zuciyarta curewa guri daya  kusan minti goma suna haka babu wanda yayi magana sannan ya zauna kusa daita ,da  kanshi ya zuba mata  abinci ya turo gabanta   "eat "
zuciyarta  ta sake  cika da wani  sabon  mamaki abu kamar a farki ko dai har yanzu  cikin dreaming take ?
"shi  yayi  girkin  ko kuwa amso  mata  yayi  agurin ummah ?
"Ke yanzu ina ruwanki ko shi  ya  girka ko amsowa yayi , ke dai kici kawai ?

duk  motsin da tayi idanunshi na kanta daidai  da cin abinci  abun  sha'awa ne ,sai juya karamin bakinta take a hankali   ya ɗauki cup  din ruwan zafi ya kai bakinshi  ya kur'ba yana kallonta  ta mike da kyar  bai ce mata komai ba ta koma kan kujera ta kwanta , bayan kamar minti  goma ya mike "tashi  muje asibiti a dubaki   ta  yatsina fuska "na  warke fa  bana jin komai "ke banson iskanci  ki tashi muje ko dan  Kinga ina lalla'bakin kin  ma  yi wankan tsarki  da nace miki ?
Jikinta a sanyaye tace "nayi  ta yi mgn tana mai tsananin  jin kunya   " to ki tashi  ki ɗauko  mayafinki  muje "
Mikewa tayi tana tafiya a hankali  "ke  tsaya ..
Cak  ta tsaya  a inda take, tana  kallonsa  ya haura sama cikin mintunan da basu  wuce  biyu ba ya sauko  ya  cilla mata hijab ya ɗauki  jakarsa yayi  gaba kulawa yake son bata  amman yasan halinta  batsare masa zata yi  daga karshe suyi faɗa  batare da ya kaita taga likita ba .

   wani asibitin kudi  ya kaita  ya  kebe da wata nurse  yayi mata bayanin komai  "dan Allah kisan yadda  zakiyi   aiki  batare da  gane komai ba,  sannan ya had'ata da ummita ,  kallo ɗaya likita tayi  mata ta fahimci bata  samu wata  matsala  ba tunda tana iya takawa , amman duk da  haka sai daya tayi mata  yan tambayoyi yadda take jin jikinta  tana bata amsa "ina ganin effetion  ne yasa kika  ji kasanki yana miki zafi  ,kwanta na dubaki cike  da jin kunya ta kwanta ta dubata babu wata matsala  tayi mata allura  tare  da bata magani  sannan  ta sallamesu  a kofar gida ya sauketa "ki tabbatar kin  sha magani
Ta  'daga masa kai  ta fita ,  ya ja motarsa  ya kara gaba .

  tana  shiga bangarensu   ta sake sulalewa ta kwanta  tana  mamakinsa , ta rasa a wani muhalli zata ajiye wannan sabuwar kulawar data  samu daga gareshi zuciyarta ce ta soma mata  magana cike da gargadi "ki daina mamaki  kamar yadda ya faɗa miki  ai ba yau ya fara taimaka miki ba, kuma duk abinda zai yi saboda mama yake yi ba saboda ke  ko  aurensa dake kanki ba.
"to ai ni ina son wannan kulawar  daga garesa  me yasa bazai min komai dan karan kanshi ba sai dan darajar mama  ....?
Tayi maganar a fili  hawaye na zubo mata " shikenan ni  haka zan kare rayuwata babu farinciki ?
"Ke kika so yin rayuwarki haka ai mijikn ne me yasa bazaki saki jikinki dashi ba ta yadda zai damu da lamarinki?
"Oh my goodness   I need happiness from him ta fada cikin zuciyarta ta jima kwance tana tunaninsa hawaye na cigaba da bin kumatunta cike da sanyin jiki ta mike  da kyar ta fita daga part  dinsu zuwa nasu meenal  ..

zubewa tayi a gadon meenal , ta kalleta  "yar'uwa  ya jiya  kika kulle  kofa nazo nayita bugawa  har na gaji  na dawo "wallahi wani irin mahaukacin bacci ne ya daukeni  ban ma san ya'akayi  ba sai farkawa nayi  na ganni  a dakina  yanzu  haka ma bacci nake  ji  ,ta juyar da  kanta tare da daura akan pillow  ,"bari na runtsa kad'an   "okay inji cewar meenal " a hankali bacci ya d'auketa  tare da tunanin mahruf  .

yadda tunansa ya addabi ruhinta  ,haka shima tunanita   ya addabishi  a office duk motsi sai ya jita acikin zuciyarsa,
barin aikin yayi ya tsurawa  celling dakin  ido take  ya soma gani tana  yi masa gizo wai gashi    tana tahowa  gareshi  har ta shige  jikinshi aiko bai san sanda  ya rungume iska  ,yayi  mata riko mai  karfi kamar za'a kwace masa ita  sai bude idanunshi tayi yaga wayam rungume da jikinshi  "meke damuka ne ?
You have to stop all this nonsense  mah'ruf ,me yasa kake zurfafa tunanin yarinyar da bata damu da kai ba  ?
" ka natsu mana duk kana neman saka kanka cikin damuwa  plz control your self ya faɗa a bayyane yana mai dawo wa cikin haiyacinsa ..

wunin ranar gabadaya ya rasa sukuni ,  ummita ta sake  tsaya masa  arai  wani lokaci yayi murmushi wani lokacin yaja  tsaki, kowa ya ganshi yasan akwai wani farinciki dake tattare dashi daga gurin aiki  kai tsaye gidan  ya nufa yana taɓa  kofar yajita a kulle dan  haka    ya nufi part din ummah  dan yasan bazata wuce nan  ba ,yana shiga daita ya soma cin karo suna kallo ita da meenal suna dariya suna ganinshi kowace ta shiga hankalinta ya k'araso  ciki  sosai ya zauna opposite din ummita  , meenal ta gaishe  "sannu da zuwa yaya ,
Ya amsa  a ciki kamar koda yaushe .
itama batayi kwaron baki ba  ta gaisheshi "ina yini ? ta  ɗauke  kanta
"Lafiya  ya jikinki ya faɗa tare da  d'ago kanshi a hankali ya tsura mata ido  ,ta sake dawo da fuskarta    taga  ita yake kallo  har lokacin yana cizan lip's d'insa dukkaninsu suka tsaya shiru  suna kallon lumtsamsun idanun juna a hankali ta motsa bakinta "na..naji sauki tayi maganar muryarta na shaking .
Ya ɗauke  kanshi adaidai lokacin da hajiya ummah ta  fito daga d'akinta "waye bashi da lafiya kuma ?
Da hannu ya nuna mata ummita  "shine baki faɗa ba kika zauna   kallo  da ciwo tun  safe  "naji sauki fa  ummah, wallahi babu inda ke min ciwo yanzu   "to  shikenan  Allah ya sauwake "ina yini hajiya?
"lafiya  lau ya aiki ..?
"alhamdullahi atare ummita da meenal suka mike sukayi ciki  ,nan   suka soma  hira da hajiya umma"wai har yanzu ba zaka yunkura akan tarewar ummita ba  yau wajen wata  uku zamu shiga na hudu kenan abun fa ya  fara damuna gsky  taja numfashi  ta sauke " gaskiya kayi wani abu akai  kowa ya kawo ido  ya saka , mamanka fa ba zataji dadin hakan ba "hajia ku nake gujewa shiga damuwar hajiya inna " haka ne  amman dan  Allah kayi wani baba bana jin dadi ganinta zaune haka ita ba bazawara ba ita ba gidan mijinta ba "kamin alkawarin zakayi wani abu ..
"Karki damu inshaallahu zanyi komai dan  faranta ranku , ki bani lokaci  "shikenan  Allah yayi maka albarka Allah ya tsareka da tsarewarsa "ammen ya rabbil alameen.

Bai  koma  gidan ba sai bayan  sallar isha'i yayi wanka  ya fito sanye da farar riga  da boxer can iya cinyarsa  ,ya zauna akan  dining babu komai akai , sai gwangwanin milo da madara   flaks da cups da  bread da  wasu abubuwa  amfani , tsawon  minti goma yana zaune sai gata ta fito tana cika tana batsewa, idanu  ya  zuba mata yana  kallonta ta wuce shi  ta zauna kan daya daga  cikin kujerun parlourn  ta canza tasha zuwa  zeeworld ,bai taɓa especting zata iya  sharesa    ba ,da kamar bazai yi mata  magana ba  sai dai yayi karfin halin  cewa " ina abinci ?
Ya tambayeta yana sake tsareta  da manya idanunshi "banyi  ba ta bashi  amsa atakaice tana yatsina fuska .

"akan wani dalili  kenan bayan ga kayan abinci birjik a gida ko akwai abinda babu ne ?
Ya sake tambayarta yana kallonta ,
"ko ɗaya akwai komai  ta mike tana jijjiga jiki  tana tahowa inda yake  "kaje inda ka kwana jiya kaci dan ni ba baiwarka bace , auroni  kayi  bazai yiwu na wuni  ina kokarin ganin nayi maka  abinda zai  faranta  maka ba  amman kai kullun cikin bakanta min kake ,"  kunnenki da jikinki  bai ji  abinda da na  faɗa miki  da safe kafin na fita office ba  kenan   ?
" Bansani ba abinci ne dai bazan sake girkawa acikin gidan ba, idan kace kaine nima nice wallahi nafika tashanci kawai makewa nake dan a zauna lafiya, amman tunda iskanci ne abun  mu zuba ..
"gidan kika zo dan nafiki iyashi suhaima idan kin sake girki a gidana baki haifu ba  cikin uwarki da ubanki ba ,ya mike ni za'a kawo iskanci acikin gidana ?
" idan kin hanani  banzan abincinka inda wata matar da zata bani naci na  koshi ...
,"oho kace dama   can kake lalla'bawa gurin wannan laananiyyar yarinyar mai siffan aljanu  yar  ...
  Saukar yatsunsa  ya sa ta katse maganarta ta   da kuncinta "kika sake zaginta sai na miki dukan mutuwa ,  mara mutunci kawai ....
  "Ni ba sakaran namiji bane dole kiyi abinda nake so ,wallahi ki kuka da kanki tunda kika bari na fahimceki ,a fusace yake magana "girki kuma dole kiyi tunda ina da halin da za'a girka koda ba zanci ba sai kin girka..
a matukar zafafe ya nufi d'akinsa yana huci tabi bayansa da kallo tana rike da kuncinta ..
Ya faɗa saman gadonshi tare da runtse idanunshi maganar mahaifiyarsa ya shiga dawo masa ya tuna damuwar daya gani  akan fuskarta lokacinbda take masa maganar ummita dan dole ya nemo mafuta domin ya faranta zukatan iyayensa  ...

Da  sauri tashiga dakinta number  hajiya sadiya  ta kira,  kiran bai kareta da komai ba illa bakinciki dan mugun labari taci karo da shi mijin yayarta zulaihat yayi mata saki uku bayan ya mata dukan mutuwa sakamakon tukunyar tsafin daya ci karo dashi acikin kwa'barta  tukunyar ta fadi ne tare da fidda hayaki wanda yasa take ya dawo haiyacinsa "ki bari miji da abinda ya sanyo kai kisan yadda zaki lalla'bashi kafin mu san abun yi ,  akwai matsafi da hajiyarmu zata kwatanta min inda yake a ijesha cikin satin nan zamu ki lalla'bashi yanzu kije ki kwantar da kai ki bashi hakuri ki nuna masa kinyi nadama  "shikenan yayarmu  zanyi yadda kikace ta katse kiran bata tsaya bata lokaci ba ta nufi hanyar d'akinsa .

Zumbur   ya mike  i yana kallonta fuskarta Shabe Shabe da hawaye idanushi sun rikide sunyi jawur tsabar bakinciki "maza ki barni daki kafin na taso ta soma buga kanki da bango uban me ya dawo dake ?
Saurin durkushewa tayi kasa ta hade duka hannuwanta guri ɗaya tana kuka "kayi Allah da Manzonsa kayi hakuri nayi realize din mistake Dina nasan ba halinka bane amman Dan Allah kayi min uzuri na tuba bazan sake ba duk abinda nayi na yi ne dan tsananinn kaunar da nake ma ka yafe min saukowa yayi daga kan gadon "You have fall ya faɗa sannan ya nufi fridge ya bude ya dauko ruwan roba ya kafa abakinsa ya sha sosai sannan ya rike ragowar a hannunsa "kin fadi warwasss suhaima ni kika kalla kika dinga  fadawa son ranki ,wallahi kin sa zuciyata tashiga kwankwanto akanki naji gabadaya nayi danasani aurenki na ɗauka mai tarbiya na aura ashe tantiriya yar tasha na kawo gidana  ban sani ba  ..
"Nayi dana sanin aurenki dana yi  amman nasan abinda zan yi zan datse au......
cikin hawaye ta matso gareshi ta rike kafafunsa "na shiga uku karka sakeni gara ka kasheni akan ka furta wannan kalmar wallahi nayi nadama idan ka sakeni ban san yadda zanyi ba ,na tuba bazan sake ba wallahi bazan kara ba sharrin sheidan ne"bazaki canza ba koda na yafe miki saboda asalin boyayyen halinki kika fito dashi wannan shine halinki  na asali  ,halin da kike nunawa yanzu na munafurci ne dan haka gara kawai na ...
Da sauri  ta mike tsaye ta dauki alqur'anisa dake ajiye akan Dre's mirrow ta daura akanta "wallahi na daina bazan sake ba take jikinsa yayi sanyi ya tsura mata ido yana kallonta cike da tausayawa  "ka yarda dani  bazan sake ba idan na sake na yarda kayi komai lumshe idanunshi yayi ta zube ta kife kanta bisa kafafunsa tana wani irin kuka a hankali ya kai hannunshi ya d'agota ya rungumeta  ",is okay  na yafe miki komai  wuce ya shiga  shafa bayanta ta kamkameshi ajikinta....

Tun daga wannan lokacin bata  sake shiga lamarinsa ba ko me zai yi ido ne nata , yayinda  ummita ta kauracewa part dinsu ta dawo part din hajiya Umma  saboda tsoron  daya soma bata , dan kusan rana day  day ne  bata  felling  ana yi wani  abu daita  ,duk da  tafi tunanin  mafarki ne ,hakan da tayi ya kawowa  mah'ruf cikass dole ya hakura daita  sai dai kullun zai zo safe dare da ,da  safe ne kawai yake samunta a a part din amman da zarar  dare  yayi  zata gudu part din hajiya umma   ...

******
A wata  safiyar asabar ummita  ta tashi da zazzaɓi  mai  zafi sai dai bata , faɗawa  kowa ba har abbanta bata bari ya sani ba sannan ko bangaren hajiya umma bata shiga ba , ko daya shigo bai kalli inda take ba  ya kwana tare da ciro system dinsa ya da'ura akan Centre  table ya soma  aiki ko yar gaisuwar da take masa batayi ba  ,kanta  ke matsanancin  sarawa da cikinta , jiri ya dinga   dibarta duk da kasancewar a kwance take tana felling  ,a hankali  ta dinga jin aman
DOWNLOAD
DOWNLOAD

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

11 months ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

11 months ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment