Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zata aikata laifin da yake tuhumarta dashi ?bata rasa komai daga gareshi ba  duk wani abinda cikakken namiji mai lafiya zai wa matarsa   yana mata  ,  yana gamsar daita dari bisa dari ita kuwa me zai kai ta aikata haka gareshi ?

a hankali ya sake  matsowa  gabanta   yana  kallon  yadda  hawayen  idanunta  ke cigaba da zuba ...
Ya kai hannuwansa duka ya talla'bo  fuskarta "me na rageki  dashi  da kika zabi  aikata min haka ?
"Me wani namiji zai miji da ni mijinki bazan iya yi miki shi  ba ?
"Me yasa kika min haka subai'a  ?
"Yanzu na sake tabbatarwa kaina    bazaki taba qaunata ba arayuwarki  ya karasa maganar yana kai hannunta daidai saitin zuciyarsa  "ki saurara kiji yadda zuciyata take jin zafin abinda kika aikata mata alhalin bata rageki da komai ba   ...

a natse ta sake zuba masa  idanunta dake tsiyayar  hawaye  shima idanunsa ya zuba cikin  nata  hannunta  na karkarwa ta kai gefe da gefen  fuskarshi ta kamo tana kallonsa tana girgiza masa kai cikin kaduwa da matsanancin tashin hankali " kada kaki yarda dani mijina ,dan girman  ka yarda dani   yaya ,   babu    wannan a  tsakaninmu, a tunanina ko da idanunka ka ganni da wani zaka natsu ka min uziri  kayi bincike , ka yarda dani sannan ka ƙaryata duk wanda ya faɗa maka cewar ina cin amanarka 8dan ba haka  zaka  kasa zuciyata ta  fashe ,ba gaskiya bane yaya  wallahi ban aikata abinda kake tunhumata  dashi ba ,   ka taimakeni ban san komai ba ka natsu kayi bincike domin gano gaskiya " kai mutun ne mai  tunani da natsuwa da hangen nesa   ,ban kasance mayaudariya makaryaciya ba ,ban kasance mazinaciya ba ka sani yaya ban taba wannan tunani ba , wallahi ban taba sanin wani mutum bayan kai mijina , zuciyata da kwakwaluwata bazu taba hasko min wannan kazantar ba ka yarda ka amince da  ban aika ba sharri kawai ake son kulla min dan a hadamu ,na rokeka ka natsu ka binciko gaskiya ya fixge hannuwanta daga fuskarsa yana watsa mata wani kazamin kallo  .

"wata gaskiyar zan  binciko  bayan wanda na gani da idanuna  ?
ya furta yana  damke kafad'unta "ki faɗa min gaskiyar da zan bincika ?
Ya zarce da shafa jikinta a rud'e jikinsa na rawa gaba-daya ya gama fita haiyacinsa  "me yasa ba zaki faɗa min cewar bana gamsar dake ba  na kara akan kulawar danake  baki, kika buge da biyewa wancan shashan tantirin dan giya?
" me dan giya zai miki kiji dadi ...? Yayi maganar a tsawace jikinsa na rawa ..

"Abba  dady ku tambayeta menene bana mata da yasa ta aikata min haka  ? Dan giya fa har cikin gidana
Ya karasa  gaban Abba "nasan  idan kowa ya karyatani  abba bazaka karyayata abinda na gani ba ..
Abba ya rungumeshi ajikinsa yana shafa bayansa "ka natsu babana , kulli musibati qalu Inna Lillahi  wa Inna  ilaihi rajiun  a duk sanda wata maseefa ta samu mutun wannan itace kalmar data dacewa ka furta domin samun natsuwa   "Abba bazan iya cigaba da zaman aure da subai'a ba na hakura daita !na hakura daita  !!!  kamin lamanince  na    sawwake mata aurena dake kan subai'a .....
"Abba nasan zaka fahimceni  dan Allah ka yafe min saboda  nasan zakuji babu dadi kai da mama amman ka fahimceni bazan iya cigaba da rayuwar daita ba ...

  da sauri ummita ta zagayo tana  fuskantarshi tana sake jin kalamr  dake fitowa daga bakinsa "me kake faɗa haka yaya mai kama da almara  sakina kake ƙoƙarin  furtawa  batare da kayi bincike  ba? ahankali ya d'ago daga jikin  Abba   suka zubawa junansu  kyawawan idanunsu  suna kallon juna  qirjinsu na dokawa da karfin gaske "wani bincike zanyi subai'a zan sa.....

"Sakarta dan ubanka  ba dai sakinta zakayi ba to saketa  ta huta da jarabarka , rubuta min takarda  sakinta ka kawo min  , wallahi wallahi ina tabbatar maka muddin ka saki subai'a  ta gama aurenka har abada ko daga  baya gaskiya ta bayyana bazata koma gareka ba muddin ina raye   ,ina jiranka da takardar sakinta  ai miji goma ba uba goma bane , abinda wani ya  gaji dashi  shi wani zai yi  hauka da muradi akan sa ,
"kai kasan banda qaddarar aure   kayi kaɗan  ka samu  auren subai'a a rayuwarka , "hajiya umma Abba ya kira  sunanta "kayi hakuri Abba banason jin komai daga bakinka  injiniya ya bude baki shima zai yi magana , tayi saurin dakatar dashi "ka adana kalamanka dan bazan saurareka ba a yanzu , mama ta karaso ta rungumeta ajikinta  tana kuka "kiyi hakuri dan girman Allah karki yi haka ."baki ji abinda yake faɗa ba agabanki agaban mahaifinta ko mutuwa tana jin kunyar idon  iyaye  amman shi da yake  tantiri ne shi har  ikirarin furta wannan kalmar ga subai'a aganku  ..

Ta sake juyawa ta fuskanci shi "ina jiranka  ka rubuta min takardar shaidar  sakinta  , ummita ta soma yin kasa zuciyarta na bugawa da matsanancin karfi  ta durkushe  bisa gwiwowinta  ta  kife kanta a kan kafafunta tana  wani irin kuka "wannan wace irin rayuwa ce mai muni gareni ?"Har sai yaushe zan fita cikin tashin hankali da iftilin rayuwa ?"wayyo  Allah  ina son mijina  da d'aukacin numfashina  !
"I love you  more than my self !! "It's Tru love I have for you  karka sakeni  kuka take sosai har sanda Hajiya umma ta kamota  ta mikar daita tsaye  bata sani ba ,tana gama mikewa tsaye  ta soma ganin  juwa  saboda jin furucin Hajiya umma "idan mah'ruf ya saketa yaya take son tayi da rayuwata ?"Tana  son mijinta bazata iya rabuwa  dashi ba, duk runtsi duk wuya tana tare dashi , idan ma ta yarda aka  raba aurensu ina zata samu jajitaccen miji kamar sa  ?
A hankali bakinta ke furta  sunan umma ! ummah !! .......

"na'am subai'a kiyi hakuri zan tsaya tsayin daka naga kin rabu da baba kiyi rayuwarki cikin salama  da kwanciyar hankali kai ta soma girgiza mata idanunta a lumshe "karki  rabani da mijina  umma ina son shi son da ban ta'bawa yiwa wani mahaluki a duniya ba  ,gidan mahruf gidana ne  umma  ba zan iya barin gidansa ba ko ya sake bazan saku ba muddin rai ina tare dashi, ki rokaman shi yayi hakuri yayi min uzuri karya sakeni wallahi zan  kasance  dashi  a duk yadda rayuwa tayi  tsananin  ,nasan  bashi da laifi  umma,an rigada an  gurbata    zuciyarsa da   tunaninsa umma karki ji haunshinsa ni ba  matsoraciya bace  akan tashin  hankali , zuciyata  na zafin abu biyu a halin yanzu  rasa yarda mijina da kuma sakina da kike son yayi ,ina son ya mah'ruf , ku barni nayi rayuwa dashi idan kuka rabani dashi zaku iya rasani  "duk da wannan mummunar furucin da yayi akanki kina son shi  subai'a ? Inji cewar hajiya umma...

"Ina son shi  umma  karki rabamu dan girman Allah "idan  ya mallake miki zuciya    bakya     ganin  aibun abinda ya aikata miki , ni ba shashar uwa bace dole na amsar miki yancinki dole ne ya sakeki jin wannan furucin na umma yasa ummita yin  luuuuuuuu ta  karasa zubewa   ajikin Hajiya  umma  sumammiya .

a matukar haukace hajiya umma ta dinga jijjigata   tana kuka mama kuka hatta hajiya saudat sai data zubar da hawaye Abba  da injiniya suka yo kanta "ummita ki tashi dan girman Allah karki mana haka wallahi idan wani abu ya sameta bazan taba yafe maka ba saboda kai ne kajawo wannan maseefar ..

Shima mah'ruf jikinsa na rawa ya k'araso kanta a haukace zai ta 'bata Hajiya umma tayi saurin dakatar dashi" karka taɓa ta  idan ka tabata  ban yafe maka   duniya da lahira   duk yadda suke kiran sunanta bata motsa ba hankalinsa yayi mugun tashi  fiyye da tunanin me karatu  ,sunanta kawai suke kira suna  kuka  ,Abba   da kashi ya cicibeta ya nufi hanyar dakin mahaifiyarta daita hajiya  umma da Hajiya saudat da mama da injiniya suna biye dashi a baya suna kuka....


Abba na gama shiga dakin mama ya kwantar daita yana kiran sunanta Hajiya umma ta miko masa ruwa ya amsa ya shafa mata a fuska shiru ..

Jikin mah'ruf  na rawa ya soma neman layin doctor  husain yana ɗauka  yace "doctor husain kazo yanzu yanzu subai'a ce ta suma bai jira jin abinda  doctor zai faɗa ba ya katse kiran ya haura sama a gigice  ..

Bayan kamar minti goma sai  ga doctor husain ya k'araso da hanzari mah'ruf ya sauko ya shigar dashi inda ummita take kwance tamkar matacciya  iyayenta zagaye daita hankalinsu a tashe batare da bata lokaci ba ya soma aikinsa cikin iyawa da kwarewa Hajiya umma da mama suka kasa zaune suka kasa tsaye addu'a suke gabad'aya Allah ya dawo da numfashinta da kyar doctor husain ya dawo da numfashinta  ya mike tsaye  yana kallonsu daya bayan daya "na mata allurar  zata farfaɗo zuwa wani lokaci  zuciyarta tayi  shock, amman da zaran ta farfaɗo zata samu sauki sai dai a kiyaye abinda zai sake barin zuciyarta  shiga irin wannan yanayin saboda  zuciyarta  bata da isasshen lafiya ....
"Mun gode doctor "ku dan ragu a dakin zuwa wani lokaci , gaba-daya suka juya suka bar dakin ban da mahruf da hajiya umma da mama "tsayuwa uban me kakewa mutane ?
" Ka bacewa idanuna  da gani bana son kallon wannan bakar  fuskartaka ,   kallon umma yake wasu hawaye Masu azabar zafi suka taru acikin kwarnin idanunshi  ya matso kusa daita" Hajiya  kiyi hakuri dan girman Allah ki yafe min kin kasa fahimtata ne amman ba sharri na...
Babu abinda zaka faɗa min baba kawai fita ka bar dakin nan tun baka gama bata min rai na tsine maka ba  ..

Ya kalli inda ummita ke kwance numfashinta na fita da kyar ya k'araso zai shafa fuskarta "nace karka taɓa min ita ka wuce ka kama gabanka Abba ya riko hannun hajiya umma ya bude kofa ya fita ya soma tafiya  daita yana magana  "banason abinda kike  uwar marayu mah'ruf dan mu abun ikon mu ne ,danmu wanda idan muka ce yayi zai yi idan muka hanashi zai hanu meye sa zaki damu kanki, auren ummita da mah'ruf alkwarin Allah ne aure ne na soyayya koda mu iyayensa bamu hada  ba zasu hada kansu tunda suna tsananin son juna wallahi nasan mah'ruf bashi da burin cutar da ummita ko cin amanarta dan haka nima a matsayina na mijinki ban yarda ki sake furta kalmar zaki tsine masa ba ko dole sai ya saki Ummi ki duba ki gani yadda take kokarin rasa numfashinta akan shi  , adduarmu a yanzu Allah ya bayyana gaskiya, Abba bai zarce ko'ina da Hajiya umma ba sai a bangarenta ya zaunar daita kana ya bude fridge dinta ya dauko ruwa mai sanyi ya tsiyaya mata a cup ya Kai bakinta "ki sha dan Allah ki samu natsuwa ...

A hankali ta kurba hawaye na gangaro mata   fashewa tayi da wani kuka "Kinga abinda banaso ko  "banason ganin Maryam cikin damuwa bare wannan da baba ne silar damuwar "nasani mah'ruf dan Maryam ne matsayin bazai taba canzawa acikin zuciyarta ba da yarda Allah babu abinda zai faru kinji sosai Abba ya dinga rarrashinta duk wani kalma da'ake rarrashi mutun daita Abba yayi amfani daita ..

Can dakin mama kuwa mahruf ne ya rarrafo ya zube a gabanta mama "mama kiyi hakuri ina tsananin sonki ,ina tsananin son subai'a wallahi ina sonta hasalima kishin abinda nagani ne ya haukatani ki yafe min mama karki yi fushi dani "ya isa baba na fahimceka amnan idan rai ya ɓaci hankali ke dawo dashi idan na faɗa maka wani abu zaka yarda  bazakayi zargi  wani abu ba acikin zuciyarka ba ?

Yayi saurin girgiza mata kai "zan yarda mama  ,da yardar Allah da taki yarda   na girma "ta tsura masa ido sannan tace " subai'a bazata taɓa aikata abinda kake zarginta dashi ba  ,kamar yaddaa nake da tabbacin akanka haka itama nake da tabbacin sai dai bance dole sai ka cigaba da rayuwa  daita a matsayin matar aurenka ba ,ra'ayinka ne ka cigaba da zama daita ko akasin haka ni dai farincikina ka yarda bazata aikata wannan mummunar kazantar ba ...
Tana gama fadar haka bata jira abinda zai ce ba ta mike ta bar dakin ..

Mikewa yayi ya samu guri nesa kaɗan da inda ummita  take kwance ya dafe goshinsa yana  jin yadda zuciyarsa ke kuguden bugu ....

Awa daya  tazo ta wuce bata farfaɗo ba haka wata awa dayan ta cika tana daf da wucewa bata farfaɗo ba wanda zuwa  lokacin  gidan ya cika makil da yan'uwa  har da suhaima, kowa yayi jugun jugun yana addu'a a cikin zuciyarsa shi kuwa mah'ruf sallah kawai ke tada shi da yaje yayi yake dawowa ya zauna a mazauninsa  sai gurin tara na dare ta farka ta bude idanunta a hankali tana kallon celling d'akin kafin daga baya tashiga kallon dakin har idanunta ya sauka akanshi a daidai lokacin daya waigo yaga yanayin da take ciki, da sauri ya mike ya k'araso gareta ya janyo kujera ya zauna yana fuskantartata .

"How are  feeling  tayi saurin kawar da kanta gefe tana sauke numfashi ," ok you don't want to talk to me ?
"Karki min magana Amman .......
menal ce ta shigo  tana jin abinda ya faɗa tayi saurin  katse shi "yaya dan Allah ko ka manta abinda doctor yace ne "zuciyarta na bukatar hutu ka barta karka dameta plz ..
shiru yayi haɗe da mikewa tsaye yana bin menal da wani irin kallo...






TWO FRIENDS BSBS
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL

AL'QALUMAN

*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*

~DEDICATED TO~
*AUNTY GAMBO UWA TA GARI ABAR TUNKAHO ALLAH YA KARA MIKI LAFIYA*

MY YOUTUBE CHANNEL
*HAUSA BAKWAI*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

PAGE 67

Ya kusan minti biyar a tsaye idanunshi na kan menal yana kallonta , magana yake son mata dan ta fahimcesa sai dai ganin yanayin fuskarta ya fahimci itama fushi take dashi mai tsanani, yasan ko me zai faɗa mata bazata sauraresa ba a bayan ummita zata tsaya ,ya runtse idanunshi zuciyarsa na wani irin dokawa da karfi " me yasa bazasu fahimceni ba ?

"kai me yasa ka kasa fahimtarsu ? kyakkyawar zuciyarsa ta aiko masa da wannan tambayar , ya bude idanunshi zuciyarsa na kuna ,menal kuwa kallonsa ta cigaba da yi cike da tsantsar tsana da jin haushinsa da bakinciki kasancewarsa dan'uwa gareta , bancin duba ga daraja iyaye da yau ita kadai tasan abinda zata masa tayi masa ,da bata samu wannan damar faɗa masa magana ba ta dinga masa Allah ya isa yafi sau dari a zuciyarta ,dan ya gama cutar mata da yar'uwa kullum tashin hankali daga wannan matsalar sai wannan ina dalili ,wallahi ko ita ta sanya hannu araba auren kowa ya huta ..

jiki a sanyaye ya ɗauke idanunshi akan menal ya maida kan fuskar ummita dake kwance idanunta na fitar da ruwan hawaye , ya tsura mata ido ,ganin irin kallon da yake mata yasa ta runtse idanunta hankalinta ya sake tashi ,bata son ganin wani abu daya dangancesa dan ta rigada ta gama sadaukarwa kanta rabuwa zai yi daita, sai dai runtse idanunta bai kareta da komai ba face tashin hankali dan idanunta babu abinda suke hangowa sai kyakkyawar fuskarsa da miskilanci fuskarsa tattare da kyawawan halaiyensa , a hankali ya soma tafiya da baya da baya yana kallonta tana zubar da hawaye , ji yayi zuciyarsa na wani irin zafi kamar zata tarwatse , shi kadai yasan yadda yake ji akanta .

yana fita idanunshi ya sauka akan suhaima bai tsaya bi ta kanta ba , ya cigaba da tafiya ya shiga bangaren hajiya umma ta biyo bayansa da sauri , kai tsaye d'akin umma ya shiga ya kwanta a kan gadonta kansa ke wani irin sarawa tamkar zai rabe gida biyu, ta k'araso ta hawo kan gado, gabad'aya hankalinta a tashe yake da ganin yanayinsa , ta riko laulausan tafin hannunsa cikin nata ta matse tana sake jin tsana da haushin ummita acikin ranta, sai data kwantar da murya sannan ta soma magana cikin rarrashi "dan girman Allah habibi ka kwantar da hankalinka kada abinda ya faru ya nemi tarwatsa zuciyarka ,nasan akwai ciwo mutumin da ka yarda dashi ka bashi yarda da amana ya cutar da kai abun akwai ciwo , kada kace zaka rabu daita akan wannan abun....

ya d'ago ya zauna yana watsa mata jajjayen idanunshi waɗan suka canza kala tsabar tashin hankali da yake ciki , muryarsa a ƙausashe yace "babu ta yadda za'a yi na cigaba da zama da matar dake ha'intata, na gama amincewa da subai'a bata kaunata kuma bazata taɓa kaunata ba , fuska hudu gareta ba biyu ba kuma da wannan fuskar take min komai , ta shayar dani mamaki a yau zuciyata na cike da bakincikinta, bancin kin nusar dani abinda ake ciki da haka zamuyita rayuwa daita tana cutar dani ya karasa maganar qirjinsa na wani irin dokawa kamar zai fito waje....

a fili suhaima ta nuna masa damuwarta tare da jimamin maganarsa "bakinka ya daina fadar waɗan nan kalaman habibi ka natsu ka dawo hankalinka , kai daita yan'uwan juna ne , ko baka son cigaba da zama daita bisa ra'ayin kanka iyayenka fa ?"zasu iya tursasaka akan ka maidaita kuma dole ka hakura ka cigaba da rayuwa daita , ni ba komai nafi tunani ba kar a manna maka fasa gurbi ace naka .. .

Ya sauke wani zazzafan huci har sai daya daki fuskarta sannan ya girgiza kai cike da tafasar zuciya "ai kuwa da ta cuceni cuta irin wacce ba'a taba min irinta ba , ki tafi kawai ki kyaleni ina bukatar zurfafa tunanin akan wannan lamarin , naunayen ajiyar zuciya na munafurci ta sauke ta saki hannunsa ta janyo bargon mahaifiyarsa ta lullu'beshi dashi saboda rawar sanyi data ga jikinsa yake , gabadaya ya rasa abinda ya kamata yayi banda kukan zuci babu abinda yake .

Ta mike haɗe da rankwafowa ta kai bakinta daidai saitin kunnenshi "mijina ka rufa min asiri ka sausautawa rayuwata da zuciyarka , ina matukar bukatarka da bukatar lafiyarka da farincikinka ,da wani mummunar abu ya sameka akan cigaba da rayuwa da ummita gara ka gaugauta rabuwa daita ka zareta acikin rayuwarmu mu hutu ......
yayi saurin bude idanunshi a gigice ya zuba mata "yes haka nake nufi banason ganinka cikin damuwa da tashin hankali , bana son na rasaka a dalilinta nafi bukatarka arayuwarka daita ....

"ni kuma nafi bukatarta arayuwata akanki ba, yayi maganar a cikin zuciyarsa qirjinsa na dokawa da matsanancin karfi "ka kwanta ka huta idan ka tashi zaka ji sauƙin rad'ad'in bakincikin da'aka kunsa maka tana gama fad'ar haka ta juya tayi bangarensu ummita ..

Can d'akin kuwa bayan fitar mah'ruf menal ta k'araso gurin ummita da sauri tana cewa "subuhanallahi ummita "why ?
"Me yasa zaki dinga hasarar hawayenki akan abinda baki aikata ba ,ummita bata amsa mata ba illa kukan data cigaba da yi kukanta take ji har cikin ranta .

Yunkura ummita tayi zata tashi , menal ta taimaka ta d'agota tana cewa "sannu me kike so?
"fitsari zanyi ,da kyar ta sauko suka shiga toilet ta tsugunna ta soma fitsari idanunta na sake zubowa da ruwan hawaye , menal ta zuba mata ruwa tayi tsarki ta wanke fuskarta , suka dawo dakin , kan gado ta zaunar daita ta jingina mata pillow har biyu a bayanta wani sabon kuka ya kufce mata "na shiga uku ni subai'a wace irin maseefa ce take ƙoƙarin fadowa rayuwata ?.

"Wani irin al'amari ne wannan ?
" Nayi hasarar ya'yana har biyu ,nayi hasarar cikina kashi da kashi mijina yaki yarda dani wallahi menal ban aikata abinda yake zargina akai ba ,bansan Wanda ya qulla min wannan makircin ba, na shiga uku ya Allah ka kawo min ɗauki cikin gaugauwa "ka gaugauta bayyana gaskiya mijina ya fahimceni ya san ban aikata komai ba dan bazan iya rayuwa babu shi ba ..

"Na sani ummita ko rantsuwa zan iya yi akan baki aikata ba, kowa ya sani wallahi, ki kwantar da hankalinki dan girman Allah ,baki ga yadda hankalin kowa ya tashi akan lamarin nan ba " shi kanshi yaya yana cikin rud'ani hatta ...

Sallamar suhaima ce ta katse mata hanzari "ina ummitan take?
suka yi mata banza haka ta cigaba da shigowa d'akin tana rafka sallama ,"ina ta sallama kuna jina , still shiru suka mata sukayi tamkar basu ga tsayuwar wata halitta agurin ba , ta iske ummita tana ƙoƙarin hadiye kukanta , tana daura idanunta akanta gabanta yayi mugun faduwa saboda abinda ta gani ajikinta tayi shiru tana kallonta gabanta na cigaba da faduwa aranta tace "pregnant again ?
Kallon da menal tayi mata yasa ta dawo haiyacinta haɗe da saka sallati ta karaso jikin gadon sosai tana cewa "inna lillahi "wai meke faruwa ne yau ?"Wa ya fasa miki baki haka ?" d'azu naga fitarku keda habibi ko kafin na fito kun fice daga gidan.

"dakata dan Allah malama wannan ba huruminki bane idan ma da hali ki koma daga waje dan Allah banason zakewa da makirci ,ran suhaima yayi bala'in ɓaci amman take taji zuciyarta tayi fari kal tamkar ammata bushara da gidan aljanna saboda tasan zaman ummita da mah'ruf na wani lokaci ne yanzu, sannan shima wannan cikin sunanta zubabbe dan baza tabar wata halaka a tsakaninsu ba tafi son suyi rabuwa ta har abada batare da suna tsatso a tsakanin ba , duk abinda menal zata faɗa mata bazata damu ba burinta a yanzu ummita ta bar rayuwar mijinta , cike da nuna damuwa tace " haba aunty menal me yayi zafi daga tambaya ?" dan Allah kiyi min bayani abinda ke faruwa tunda shi habibi yaki sanar min komai ?
"Baza'ayi ba sannan ba'a bukatar tambayarki ,ki tashi ki kama gabanki ba'a ma a son ganin fuskarkaki ...

"karku zargeni bani da masaniyar faruwar komai , lokacin daya shigo bangarena nayita tambayarsa bai yi min bayani komai ba hasalima hucewa yayi akaina , kalli fuskata ki ga yadda yayi min da fuska?
" yaki min bayani sai surutai yake marasa kan gado ..

banza suka mata babu wanda ya tanka mata daga ummita har menal har ta gaji ta mike ta ɗauki jakarta ta fice tana dariyar farinciki a ranta tace " daga haka shikenan kun rabu ,rabuwa ta har abada ....

Menal ta rakata da harara , zuciyarta cike da zarginta iri iri babu shakka ta dade tana zargin suhaima cikin faruwar wannan al'amari tunda bayan ita babu mai shigowa part din ummita , sai kuwa su y'an'uwanta ,
y'an'uwanta kuwa tana da tabbacin babu wanda zai ajiye mata maganin zubar da ciki .....

A hankali ta lalubo tafin hannun ummita cikin nata " dan Allah ki rage damuwar nan , ki cire yaya arayuwarki idan da hali ma ina son kiji haushinsa , " bazan iya ba menal har abada bazan ji haushinsa ba saboda nasan bashi da laifin komai idan ma yana da laifi ɗaya ne da yaki fahimtata sannan yaki tsayawa yayi bincike akan lamarin ,
Sun jima tare suna tautaunawa ,a hankali ummita ta fara rawan sanyi zazzafan zazzaɓi ya rufeta haka nan gabanta ya dinga faduwa sam bata son ganin suhaima arayuwarta , ta zame ta kwanta hawaye na cigaba zubowa akan fuskarta "lullubeni minal sanyi nake ji ,tayi mgnr bakinta da jikinta na rawa kamar wacce aka jonawa wutar lantarki ,jikin minal na kyarma ta janyo bargo ta lullubeta tana jero mata sannu ..

Hajiya umma ce ta shigo tana bin ummita da ido ,yadda take hawaye da rawar sanyi yasa jikinta ya kama rawa tana jin wani tausayinta , ta matso kusa daita ta d'aga kanta ta zauna ta maida kanta bisa cinyoyinta tare da d'aura hannunta saman sumar kanta dake hargitse ta fara shafawa a hankali taji wani irin zafi na ratsa tafin hannunta "menal maza tashi ki shiga bayi ki dibo min ruwa a cikin karamin roba ki kawo min da towel , ta mike da sauri ta nufi toilet ta kunna fanfo ta tari ruwa acikin wani madaidaicin roba ta dauko towel ta jefa ciki ta fito ta ajiye a gefen hajiya umma "yauwa menal ki ramin abbanku ko kuma kice masa a sake kiran doctor har yanzu jikin nata da zafi , menal ta juya da sauri tana cewa "to " ummita tayi saurin riko yatsun hannunta tana girgiza mata kai alamun karta je ,ta juyo ta zuba mata idanu "me yasa ummita kina son wani abu ya sameki ko ?
"Kina son mu rasaki ko ?
"Bazan iya juran rashinki atare dani ba" kiyi hakuri ki taimakeni ki sausautawa

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment