Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace " na fahimci komai amman ai abinda suhaima tayi ba laifi bane ? muryarta a cike da tashin hankali "nace maka laifi  ne duk abinda zakuyi kuyi ina ruwana  amman kar a sake min makirci a bangarena  I can't take it..

"na furta mahimanciki gareni a gabanta na faɗa mata duk abinda zata soma miki ta gama dani kafin tai miki   alhalin nasan  hakan kuskure ne kuma abu mafi ciwo ga zuciyar  duk wanda  aka yiwa haka   ,ta danne zuciyarta  ta  biyoni tare da yayarta ta bani hakuri har ke  ,dan tayi kissing dina   shine zaki d'aga hankalinki akai ?

"Nace dole Sai ka soni ? "Ko nace dole sai ka faɗa mata mahimacina a gurinka ? well ni duk ba damuwata bane wannan , karka sake cewa kana sona dan na ƙaryata wannan kalmar na godewa Allah da zuciyata bata kamu da soyayyarka ba  ta karasa fada tana hura  masa hanci  haɗe da mikewa  zata wuce ya mike jikinsa na rawa ya fixgota ya rungume ajikinsa tsam  yana sauke numfashi  a tsanake ya  d'ago kanta yana girgiza mata kai sannan ya jingin bayanta da bango yana huci kamar wani zaki "Ke kadai ce  a cikin  zuciyar mah'ruf , da zan kasance tare dake muddin rai kin isheni  karasa rayuwata, ki tsaya kiyi tunani da kyau ta ya zaki ƙaryata soyayyar da nake miki nasan kina da zurfin  tunanina a koda yaushe ki tsaya kiyi tunani da kyau  zuciyarki na makale da tarin qaunata zaki iya yin komai akaina  amman baki isa ki nisanta gangar jikinki  dani ba understand .

"kwayar  idanunki da hawayen dake cikin idanunki da zuciyarki nasan duk nawa ne idanunki suna shiga cikin wani yanayi a duk sanda suka sauka akaina  ,murmushinki shima nawa ne ya busa mata hucin numfashinsa yana shafa fuskarta zuwa lip's dinta da wannan  gashin naki ya kai hannunsa ya shafa sumar kanta shima wannan nawa ne hatta kamshin jikinki nawa ne komai naki nawa ne muddin rai kalli cikin kwayar idanuna kice karya ne  bakya sona ...?"Faɗa min qauna ta yaya zaki kasa  fahimtata dan wannan karamar matsalar ?

'bayan ba  yau ne karo na farko da suhaima ta taɓa  kissing dina a matsayinta  na matata ba , kema kinsan  dole hakan yana faru a tsakaninmu  "yana faruwa amman ba akan idanuna ba  kuma kazantar da  mutun bai  gani ba tsaftace  ta karasa  maganar tana rushewa da wani sabon  kuka ...

Ya sausauta rungumar da yayi mata "kinga idan zaki yi fushinki kiyi mai ma'ana karki daura min laifi bisa wani ra'ayinki , dukkaninku matana ne meye laifi dan tayi kissing dina a gabanki ?   ya sake matsowa ya matseta  kamar zai raba jikinta gida biyu ya daura bakinsa saman nata yana hura mata iskar bakinsa  yana dubanta , idanunta cike da kwalla ta  kawar da fuskarta gefe   taki kallonsa sannan taki yin magana  ya sake matsota  yana zagaye hannuwansa da kugunta  "kin yi shiru kiyi magana mana  ko kina son  na kasance mara adalci ne agurin Allah  ya  karasa maganar a fusace yana sake  matseta a faffad'an qirjinshi "kiyi magana me yasa zaki min haka har da  ƙaryata soyayyar da nake miki  ...

Hannunta  ta  kai  ta tokare qirjinshi dashi "ya mah'ruf  dan girman Allah ka barni   bana bukatar komai daga gareka , dan  Allah ka barni bana son damuwa  da tashin   tsura mata  kyawawan idanunshi yayi yana Kallonta cikin zallar bacin rai "me nayi wanda ba daidai ba ki faɗa min ina son sani  ?  ban taba expecting haka daga gareki ba qauna  sai dai hakan yasa na fahimci makaryaciya zuciyarki dake nuna tana sona alhalin ba haka bane  , na ƙaryata kulawarki gareni   ya karasa maganar qirjinsa na dokawa da karfi idanunshi na kanta  ya juya a fusace zai  bar dakin  har ya daura hannunsa kan handle din kofar ya tsaya batare da juyo ba "bakya son tashin hankali bakyason damuwa ki bar issue din  ya wuce shine zaman lafiyarki dani ya bude kofa ya karasa fita kai tsaye gidan ya bari zuwa massalaci dan lokacin sallar magariba tayi ..yana fita ta durkushe a kasa ta  tasa fuskarta a tsakankanin cinyoyinta tana wani irin kuka "bazan yarda da cin fuska ba "duk lokacin da kake tare daita bana shiga rayuwarku saboda bana son damuwar da zata damu zuciyata  ,bazan ɗauki wannan salon ba  kuma  wallahi sai na  fadawa   ummah ta fadi haka a ranta  tana cigaba  da kukanta ...

Wata  irin mahaukaciyar dariya hajiya  rahma ta kwashe dashi tana juyi a tsakiyar  parlou'n suhaima kamar wata mahaukaciya  "kinga yadda  ake biyowa yan iska irin su mah'ruf ko ? "a kullum bazan gaji da fada miki kalmar ki dinga daga musu  kafa da kawar da idanunki akansu ba ,wallahi da makirci kadai zamu iya raba tsakaninsu ,kar na sake jin kinyi tari akansu  ,suhaima ta daga mata kai "ki kwantar da hankalinki gobe zanzo da mus'ab yayi mana abinda boka ya bukata karki manta ki tabbatar da kim samu spam d'insa ko boxer d'insa  ,"suhaima tace " duk wannan mai sauki  ne  aiki yayi "yama yi ya gama Bashir musali ne akanki kalli yadda ya dawo  ni har tausayi yake ba shima wannan dan iskan mijin naki bayan ana tsaye akanshi da sai yadda kika yi dashi  tana  magana  fadar haka ta fito   suhaima na  biye daita a baya  suna magana kasa kasa ...

Da  misalin  karfe  tara na dare  ya shigo bangaren ummita  bai isketa a parlou'n   ba daman zuciyarsa ta faɗa masa bazata zauna zaman jiransa ba ya kulle ko'ina sannan   ya nufi  d'akinta ya murd'a handle ji kofar a buɗe numfashi da ajiyar zuciya ya sauke a tare sannan ya  shiga dakin duhu  dan haka ya soma laluben makunin wuta  ya kunna haske ya haskaka dakin  kwance ya ganta akan gado ta  juyawa kofa baya.

karasowa yayi cikin dakin sosai ya kulle kofar ya soma ƙoƙarin cire  agogon hannunsa  ya ajiye a gaban  mirrow dinta ya ciro wayoyinsa ya ajiye ya shiga bayi yayi wanka ya fito yana goge jikinsa ganin suna fuskantar juna yasa ta juya dayan bangaren, ya sanye vest da boxer ya  gama shirin bacci ya fashe ilahirin jikinsa da turare  mai sanyi kanshi  ya hau  kan  gadon ya canza hasken daki zuwa dum light   ya kwanta a bayanta  yana  janyota jikinsa , tayi saurin matsawa  cikin  zafin nama ya birkitota gabadaya ta zube jikinsa hancinta ya sauka a daidai inda yafi jin kamshin turarensa  ta lumshe idanunta qirjinta na matsanancin dokawa ,ya zagaye hannunwansa duka a kugunta ya  soma wasa da sansar  jikinta kememe taki yarda dashi  ta dinga  mutsu mutsun sauka a jikinsa  ya zare hannuwansa ya d'agota ya zaunar daita shima ya  zauna ya kunna wutan dakin yana  tsareta da manya idanunshi masu bugar mata da zuciya shiru yayi  yana kallonta "lallai yayi saken da ummita ta rainashi dayawa   kenan bataji abinda  ya faɗa mata d'azu zai fita  ba  ? "Me ye haka ya faɗa yana tsareta da ido cikin bacin rai mara misaltuwa "me nayi ta bashi amsa tana  hura masa hanci tare da kafeshi da nata idon  "me nace miki d'azu ?  Kinsa idan tsiya kike ji nafiki iya wa ko ? "Kayi mana ina ruwana.

  ya  langwa'bar da kai yana dubanta haɗe da cizan lip's d'insa na kasan  "kinsan halina sai dai  ki bawa wani labarina bana daukar irin waɗan abubuwan kema yanzu ina binki a hankali dan nasan  bake kadai bace , "kayi duk abinda zakayi I don't care dan halinka ya zame min man shafawata   tana gama fadar haka ta sauko daga kan gadon ta nufi kofar fita ,saukowa yayi a zuciye ya cafkota ya juyo daita ya sauke mata yatsun biyar  "kina hauka ne  zaki fita ki barni  ko wasa nake dake ? ta dafe inda ya mareta a gigice "ka mareni ?

"an mareki ko zaki rama ne ,ke  ba mari zan iya  miki abinda yafi shi matukar bazaki kwantar da hankalinki ba  "me kike son nayi miki ki fahimceni  ? kuka ta  rushe masa  dashi "kasan Allah tun daka mareni ka mari aurenka ta wuceshi  a fusace ya murd'a key ya fito parlou'n  zuciyarsa na kuna  yana  kallon hannunsa  daya mareta dashi..

ta karasa gurin akwatin kayanta ta dauko daidai wanda tasan  zata iya dauka  ta k'araso gaban wordrob dinta ta bude ta dinga daukar kayanta tana zubawa ciki sai data cika akwatin ta rufe ta ɗauki zumbulelen hijab d'inta ta zira a saman rigarta  ta soma  jan akwati tana buɗe kofa suka ci karo dashi zai dawo dakin a gigice yake kallonta "oh my god subaia "wai meye haka ne ? me kike shirin yi  taji kome ?

"kasan Allah bazan zauna ba   yau a gidan ubana zan kwana sai kayi abinda yafi mari ta bi gefensa zata wuce ya fixge akwatin yayi jefa dashi  ya rungumeta  ajikinsa  "you are mine subaia  babu inda zaki "a ina kika koyi wannan dabiar  yin yaji ?  tunda kike da mama kin taba ganin tayi yaji ?"duk hargitsen da akayi a gidan mu wuya da dadi mama bata taba yin yaji ba me yasa zakiyi qauna  ? ka rabu dani bazan zauna ba yau ka mareni gobe dukana zakayi "I have every right on you ban yarda ki taka ko nan da can ba " haka ne sai dai kasani komai yana canzawa , ya shiga girgiza fuskarta ki natsu ki fahimceni wallahi zuciyata bazata iya daukar wannan tashin hankalin ba ...

Ta zare jikinta ta faɗa saman gadonta tana kuka wayarsa ya dauko ya kira number mama Kira daya ta ɗauka da sallama "Assalamu alaikum "wa'alaikum Salam mamana  barka da dare "barkanmu dana lafiya dai  naji muryarka haka " kina bangarenki ne ko na abba "ina bangarena ta faɗa muryarta na rawa "okay gamu nan zuwa "Allah kawoka lafiya amman dai lafiya dai ko ?"lafiyar nan da sauki mama sai dai munzo ta katse kiran ya ya dauki jallabiya ya saka ya  kamo ummita  ya sauko daita ya rike tsintsiyar hannunta  ya kulle ko'ina ya zare key  ,ya nufi inda  motarsa yake  ya shiga ya yi wa  matar  key   "ki shigo  muje nan take tsoro ya kamata "ina ta faɗa a tsoroce "ban sani ba ki shigo muje jikinta na rawa ta shiga minti goma sha biyar kacal ya kaisu family house dinsu ..

A parlou'n suka iske  mama zaune tana  jiransu , tana ganinsu zuciyarta ta soma bugawa , guri ya samu ya zauna itama ummita ta zauna gabanta na fad'uwa dan tasan halin mama  muddin taji abinda ya faru ita zata bawa rashin  gaskiya "mama ga subai'a nan na kawo miki ki tayani  bata hakuri  nasan muddin kika bata hakuri da kanki  zata hakura ? "Subai'a zan bawa hakuri akan  wani   laifin ? "me ka mata da  har   ka iya bata hakuri taki hakura ? " ita wacece ita mama tayi maganar jikinta na rawa tana kallon ummita dake zaune kamar wacce tayiwa sarki karya, ya furzar da iska mai zafi "wai akan.... ummita tayi saurin take masa kafa jikinta na rawa ya waigo ya tsura mata ido kanta ta shiga girgiza masa  , mama ta cigaba da Kallonsu  ranta a matukar bace, a fusace tace "ke har kin kai  matsayin da mijinki zai  baki hakuri kiki  hakura sannan  har ki hanashi fadar abinda ya hadaku ? "kai kuma kamar wani shasha shine ka wani  tasota gaba yarinyar da zaka gaugarawa mari  ta shiga hankalinta "no mama nifa ba faɗa na kawota  kiyi mata ba hakuri zaki bata ni ne da laifi ai"mama tayi shiru tana dubansa cike da mamaki "lallai duniya mai juyi juyi mah'ruf ne ya dawo haka ? tayiwa kanta  tambayar    sannan ta girgiza  kai "shikenna zan dai mata magana  ba dai hakuri ba bani minti biyar kacal ya mike "dan Allah mama hakuri zaki bata ban da fada "inna lillahi wannan shirmen kake mata shiyasa ta rainaka "ya girgiza kanshi  yana bar parlou'n mama bazai ki fahimci tasirin subai'a a arayuwata ba ..

Bayan fitar mahruf mama ta soma magana cikin fushi "ke yanzu irin wannan rayuwar kika zaba wa kanki mijinki yayi miki laifi har ya baki hakuri ki kasa  hakura saboda gaki yar mai ? "ke kinsan halinsa wallahi ya fiki jin duk  abinda kike ji dashi ya dai  daga miki kafa ne saboda cikin jikinki bancin haka da kin gane baki da wayo sakariyar kawai  ,daga yau sai yau  karki sake irin wannan kuskuren , da zarar yayi miki laifi kika nuna fushinki ya baki hakuri shikenna  sai ki hakura  komai ya wuce idan kika saba masa da taurin kai, duk sanda  yayi miki laifi bazai wahalar da kanshi gurin baki hakuri ba, zai barki da halinki haka kika ga suhaima nayi masa ? matar da ko shine da laifi ita ke durkusawa ta bashi hakuri "duk na makirci ne mama "koma dai na menene tayi kar na sake jin wani abu ya hadaku kina masa taurin kai shi namiji lalla'bashi ake tamkar jinjiri ki koyi hakuri da duk abinda zai miki ki saki ranki komai ya wuce Allah yayi muku albarka ta faɗa a daidai lokacin da mahruf ya dawo parlou'n yana sosa keyarsa "ɗauki matarka ku wuce dare yayi "na gode mamana babu kunya ya kamo hannun ummita suka wuce ..
A mota ya dinga janta da hira har suka kawo gida ya rungume tsam ajikinsa yana kissing din wuyanta zuwa qirjinta "Allah na gode maka da ka sanya mama cikin rayuwata Ina son mama  fiyye da kowa "fiyye da kowa har ni ya daga mata kai alamun eh "a cikin soyayyarta na tsammaki ,ya kai hannusa mararta yana shafa "wayyo baby ko a wani hali yake ? Yayi maganar yana cigaba  shafa marta  a hankali ya soma tafiya daita ya kwantar daita akan gado ya zare hijab din jikinta ya tsura mata ido yana Kallonta "kina da rigima qauna Allah ya taimakeni kar yayana su dauko rigimarki gara su dauko komai na mama "tunda itace ta daukar min wahalar  ciki ba? tayi magana a shagwa'be tana turo masa karamin bakinta ya matso da fuskarsa yana busa mata numfashinsa ya daura bakinsa saman nata ya tsotsa "sai na cije bakin rashin kunya ta mike zaune shima ya mike ta janyota jikinsa "Ina son komai naki "ba dai komai yanzu kagama cewa baka son yayanka su dauko rigimata bayan ni babu wata rigima da nake yayi murmushin gefe baki yana kissing din kunneta   ....

"Menene abinda kafi so da tsana  tare dani  ?  Ya sake yin  murmushi  yana Kallonta  da kyawawan idanunshi  "Abinda nafi tsana a tare dake   taurin kanki  , abinda nafi so  sauƙin  kanki  dan bakya shiga lamuran mutane muddin basu suka shiga naki ba ,  tayi murmushi " ni da kai kadai muka fahimci halin da zukatanu suke ciki zan so sace zuciyarka gabad'aya mallakin  subai'a ce " idan dai ba kasheni zakiyi ba ai....
tayi saurin kai hannunta bakinsa tana girgiza masa kai  idanunta na ciccikowa da ruwan hawaye "kasan yadda naji kuwa ?

ya riko hannunta yana murzawa yayi mata kyawawan masauki  a cinyarsa "faɗa min abinda kikaji "karka sake min batun mutuwa  yayi murmushi  "mu fa muslimai ne mutuwa kuma  dole  kowane muslim da yayi imani dole  zai  kawo wa rayuwarsa mutuwa....

Wasu tsiraran  hawayen suka gangaro mata  a hankali tace "plz yaya  ya kai  hannunsa  yana shafa sumar kanta   "shikenna   na amince duk duniya babu wanda ke sona kamarki  ya faɗa idanuwansa na kanta , murmushi tayi dake kara mata kyau ya kai bakinsa cikin kunneta yana hura mata iska "faɗa min  abinda   kika so atare dani da abinda na taɓa miki wanda ya tsaya miki arai  har kika kasa mantawa  ya matsota sosai  yana goge mata hawaye "uhmmmmmmm bana son kuka  ina sauraronki numfashi ta sauke da kyar  sannan ta soma magana a natse  "zaka  tuna ranar da mama  ta aikoni d'akinka har ka tsareni a bayan kofar  parlou'nka  kace duk  namijin daya aureni ya cuci  kanshi  ya aurar wa  kansa matsala da tashin  hankali har ma  .......
yayi saurin rufe mata baki yana  zaro ido haɗe da  Kallonta cike da mamaki yadda bata manta  komai daya faru ba a wancan ranar ,   ta cire  hannunsa daga bakinta ta daura bakinta akan lip's d'insa tana tsotsa wani irin abu yaji yana yawo a gabad'aya ilahirin jikinsa wanda ya haddasawa qirjinsa bugawa ta tsaida idanunta cikin nashi  "ban taba jin bakinciki irin na wannan  lokacin ba kuma shine abinda yafi komai taba zuciyata da tsaya min a rai  ...

"Na yarda  kuma na amince da hukuncin Allah shine daidai ga bawansa duk abinda kaga Allah yayi akanka shine daidai a lokacin idan  wani yace min  zamu kasance ma'aurata zan ƙaryata sai gashi yau mun wayi gari tare cikin tsananin kulawa da juna ,nasan a lokacin kayi furucin ne ba daga kasan   zuciyarka ba ,you just say it ,ajiyar zuciya ya ɗan sauke yana zuba mata idanu batare daya cire idanunshi cikin nata ba ya  kwanta flat akan katifa ya kwanto daita jikinsa,lafewa  tayi ajikinsa saboda abinda take ji ,lip's dinsa na kasa ya ciza da karfi yana jin haushin abinda yayi mata a baya wanda shima tsintar kanshi yake da aikatawa ba dan ransa na so ba .

a hankali ya soma yawo da hannunsa a  jikinta ya dinga shafawa yana  mammatsa mata jiki , kissing d'inta yake sosai tun daga wuyanta har zuwa boobs d'inta  ya zare yar rigar bacci dake jikinta ,baki yasa yana tsotsan kan  nipples d'inta  a hankali ya cigaba da romancing d'inta cikin mawuyacin hali ta kai bakinta kunnenshi "ban gama  magana ba kake neman canza hira "abar wannan hirar wannan yafi shi mahimmanci ya cigaba da saukowa bai tsaya ko'ina ba sai gonarsa she's wet  dan haka kai tsaye bata lokaci ba ya ɗauki hanyarsa  kusan raba dare suka yi suna morar juna .....

Washegari suhaima da sassafe ta tashi tayi duk abinda zata yi tana  ganin mah'ruf ya fita , ta kira number  hajiya rahma ta ɗauka "yaakayi suhaima "lafiya yayarmu daman nace na faɗa miki ya fita "kina jina ? "Ina jinki yayarmu "zuwanmu yau bazai yiwu ba, yanzu dady ya bugo min hajiyarmu babu lafiya yanzu haka ina kan hanya gida "mun shiga uku me kuma ya sameta? " ina ganin  ciwonta ne idan na karasa zan kiraki ,ta katse kiran ,ta cigaba da  tuki ,tana shiga gidansu hankalinta ya tashi saboda canzawar da kamanin mahaifiyarsu yayi a kwana ɗaya tal daman duk ta kare ta rame gashin kanta duk sun fara kakkabewa ta isa inda take kwance tana ta tambayar mahaifinsu" gata nan wai  babban yatsan kafarta ke mata ciwo daga susawa ya kumbura  babu abinda ba'a sa mata ba sai kara kunburi gurin yake duka last week ne  abuya faru ,jiya   bamu  runtsa ba saboda ihunta  "sannu hajiyarmu yauwa rahma ta faɗa da kyar  numfashinta na fita basu bata lokaci ba suka nufi asibiti ita ..

Bayan sati jikin mahaifiyar suhaima yaki dadi dan har surutai ta soma ga babban dan yatsan  kafarta ya soma fitar da wani ruwa mai wari dole likitoci suka ce za'a yanke , suna kuka suna komai aka yanke babban dan yatsun mahaifiyarsu ,mutane arzikinsu sunata zuwa dubata sai dai basa bari an ganta saboda surutan da take dan da zarar kace mata ya jiki zata fara zubo zance kamar wata zarrariya    mutanen gidansu mah'ruf sunje dubata suma basu damar ganinta ba ..

Karfe  tara  na dare ranar  ummita  ta shigo  d'akinsa    a daidai lokacin daya fito daga bayi  ,ya matso kusa daita zai rungumeta, tayi saurin ja da baya ai kuwa ya yarfa mata  ruwan jikinsa haɗe da cewa zaki gane baki da wayo  ne ba dai guduna kike ba ?
Cikin shagwa'ba tace  " daman nazo na maka sallama ne  ka shirya kayi baccinka  kai kadai dan a yau a dakina zan kwanna , yayi murmushi "kamar da gaske idan kin koma d'akinki naki  zaki iya bacci ?
"zan iya mana menene aciki dan na kwanta ni kadai  ? "Nothing ya faɗa tare da tsayawa gaban mirrow ya fara shirya kanshi ta tsura masa ido kawai tana kallonsa , kallonta yayi bayan ya saka rigar bacci me budadden gaba har ana iya hango gashin dake kwance a qirjinshi a hankali yace "ya kika tsaya kina kallona baki wuce ba   ko da magana ne ?

Ta rausayar  da kwayar idanunta cikin nashi  tana juyawa "to bari na wuce , yayi saurin riko hannunta ya juyo daita  ta fadawa qirjinshi ya soma yawo da hannunsa a sansar jikinta yana tafiya daita har ya isa gaban wordrob dinsa ya zare rigar  jikinta" bana son wadan nan  kaya sun yiwa matata nauyi , tayi saurin rufe idanunta zuciyarta na harbawa , koda yaga tayi haka sai  ya girgiza kanshi  ,yana  zira mata riga daya dauko  mai shegen kyau wanda  ya bayyana sansar jiki ,iya gwiwa rigar  ta tsaya mata ,  tasbihi  ya shiga yi a zuciyarsa saboda ganin irin kyawun da tayi  yajata zuwa bakin gado  ya  kwantar daita yayi  addu'ar ya rufe kofar part  haɗe da kashe kwayakon lantarki na ko'ina sannan ya dawo ya kwanata a gefenta ya musu addu'a ya rungumeta ajikinshi daga shi har ita sai da suka  sauke ajiyar zuciya ta lafe  a qirjinshi  tana shaƙar kamshinsa son shi na sake huda zuciyarta  "qauna  ya kira  sunanta  muryarsa a raunane ,tayi shiru taki amsawa  illa  zuciyarta data shiga   dokawa da sauri "zuciyata ta kasa hakuri,   ina son jin wata  kalma mai mahimmanci   daga bakinki sai careles  kike dani  kina batsawar .

"wace  kalma kake son ki ? ta tambayeshi tana sake shigewa jikinsa take ta  tsokano masa sha'awarsa  jijiyarsa tayi wata irin haniniya ,
Ya  kai  bakinsa cikin kunneta "love .....ya faɗa yana sake rungumeta ajikinshi "i  want hear from you "wannan ai kauyanci ne ban da abunka ,   zuwa  yanzu  kasan matsayinka dan haka  ka daina damun kanka, yayi shiru yana sauke numfashi "wato duk abinda  yayi sai ta tunatar dashi , ya tuna lokacin da rayhan yake furta mata kalmar  yana sonta , shine da kanshi yace kauyanci ne furtawa mace kalmar  so , ka nuna mata a aikace kawai shine wayewar , kallonta yayi yaga har ta soma bacci ya kai hannusa daidai kasan  mararta yana shafawa a hankali  daga nan shima bacci yayi gaba dashi...
Bayan sunyi sallar asuba ya soma lalubarta duk yadda taki haka ta hakura ta barshi yayi shagalinsa .

******
Shad'aya daidai  hajiya rahma ta shigo gidan bata tsaya a ko'ina ba sai bakin part din suhaima ta  fito tana bawa mus'ab umarni shima ya fito yana karewa gidan kallo har suka shiga  parloun gidan "ka zauna ina zuwa ta shige ciki  dakin suhaima ,kasa zama yayi saboda idanunsa daya hasko masa hoton mah'ruf  makale a bango yayi shiru yana tunanin in daya sanshi," tabbas yasan fuskar amman ya manta inda yasanshi  ganin ya kasa tunowa ya samu guri ya zauna yana jiran yaga fitowar matar da zai yiwa aiki ...

TWO FRIENDS BSBS

💗💗💗💗💗💗
     WANNAN CE
   QADDARARMU
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL
            
      
AL'QALUMAN

*AYSHA  A BAGUDO*           
*FAIZA  HAMMADU*

~DEDICATED TO~
*AUNTY RAHMATUN CAPTAIN*

SUBSCRIBE TO MY YOUTUBE CHANNEL
*HAUSA BAKWAI*
WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

PAGE 63

"yayarmu  zuciyata  na  cike da matsanamcin  tsoro da fargaba   kina  ganin   yaron nan   bashi da matsala ? " ba zai kawowa rayuwarmu  tashin hankali  da barazana ba ?

"Suhaima ya kamata ki natsu  ki  karfafa zuciyarki  daga yau bazaku sake had'uwa dashi  ba, an tabbatar min da  bashi da wata matsala ta wannan  fanni ,muddin bashi  yayi  ra'ayi  mace dan kanshi  ba , idan  kin daina   kishin mijinki ,sannan  zaki hakura  matarsa  ta cigaba da ɗaukar cikinsa tana haihuwa  kina  zaune bai da matsala  sai ki  hakura yanzu  naje na sallemeshi ya kama gabansa tana gama fadar haka ta juya zata bar d'akin.

cikin  matsanancin tashin hankalin  jin abinda hajiya rahma   ta faɗa ta k'araso gareta    tayi huging dinta gabanta na fad'uwa, sai data sanyawa  jikinta jarumta sannan tace "shikenna yayarmu kiyi hakuri karki yi fushi dani  duk abinda kika shirya  haka zan bi "danku  nake wannan tashi  fadin  a kullum hajiyarmu  burinta ku mallaki  mazajenku ke da zulaihat  kamar yadda na mallaki  Umar da taimakonta , murmushi suhaima tayi tana cewa "thank you my lovely sister  Allah ya barki da ya Umar .

Hajiya   rahma ta dade a dakin    tana  shirya mata yadda zata  biyowa  

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment