Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

file dinta kenan.....
"Me ya kamata yayi yanzu ?"ya hakura daita tayi rayuwarta har sanda ta samu wanda take so ne ko kuma ya jajirce ya aureta suyi rayuwarsu a haka ?
Yana kallonta ta zare yatsun hannunta cikin nashi ta zame ta kwanta akan kujera idanunta sun kad'a , ta fara runtse idanunta a hankali har ta rufesu ruf tana fitar da numfashi sama sama tamkar mai cutar asma ...
hawaye yaga suna bin gefen idanunta ahankali yaji tana rera kuka mai taɓa zuciya , ya sake riko yatsun hannunta yana kiran sunanta "subai'a kiyi hakuri ! Kiyi hakuri !! zan.........
sai kuma yayi shiru ya dakata ya mike da wani irin sauri ya fita daga parlourn yana ƙoƙarin goge hawayensa ,kai tsaye ya nufi d'akinsa kawai domin yana son ya samu damar da zubar da hawayensa ko zai daina jin rad'ad'in da zuciyarsa ke yi ,ya rasa dalilin daya kasa furta mata abinda ke ransa tabbas ya so ya furta mata zai hakura ne daita amman ya kasa furta hakan sosai yake zubda hawaye ....

Bayan fitarsa daga parlour'n rushewa tayi da wani matsananci kuka, sosai take jin tausanyinsa a halin yanzu ko babu komai bai cancanci taki shi ba wanda ke sonka yafi wanda ke kinka , dan haka daga yanzu zata sanyawa zuciyarta hakurin aurensa zata rayu dashi tunda ko bata auresa bata da wanda take so a yanzu, zuciyarta wankakkace bata san komai akan soyayya ba,tasan matsawar suna tare da sannu komai zai shude ya zama labari "kayi hakuri ya rayhan zan daina sakawa zuciyata damuwa sai dai bazan iya sonka ba muddin rai ,zan rayu da kai ba dan ina sonka ba ta K'arasa maganar tana sake rushewa da matsanancin kuka ...
Ta dade agurin tana kuka sannan ta yunkura da kyar ta nufi d'akinta ..

zaune ma'aruf da jafar da abbati suke a Parlour mama suna kallo , sai ga Ummita ta sauko daga sama da niyyar kwanciya , kawai ta gansu zaune , bata ce musu komai ba ta soma gyara inda zata kwanta taji alamun ana kwankwasa kofa ,cike da sanyin jiki taje ta buɗe a yangance saifullahi ne hannunsa rike da pack din ruwan roba wanda ya siyo wa mama a super market a hankali ta bashi hanya ya shigo bayan ya shigo ta amsa tayi hanyar kitchen ta ajiye pack din ruwan sannsn ta k'araso ta zauna batare da kalli inda suke zaune ba duk da tana son tace musu zata kwanta , amman girman kai da miskilanci ya hanata magana , Ma'aruf kuwa kallo ɗaya yayi mata ya fahimci tana son ta kwanta ne, dan yanzu anan take kwana tunda akayi baki, amma daya lura baza tayi magana ba, a ranshi yace "bai da lokacinta idan ta matsu ta magantu ,dan haka ya sake ware kafafunsa suka ci gaba da kallo da jafar , jifa jifa suna hira akan kallon da suke .....

tafi awa daya zaune a gurin tana tunani yadda zata kwanta suna gurin ita dai komai za'a yi bazata ce musu komai ba , duk abinda take Maaruf na ankare da ita ,har sanda suka gama tukunna suka mike shi da jafar suka fice zuwa side d'insa suna fita jafar ya kwashe da wata mahaukaciyar dariya yace" kai Maaruf baka da kyau ka cika yarinyar nan fa , naga hankalinka ba'a kan kallon yake ba amma saboda ka kunata ka zaunar damu"
" ai kaɗan ta gani tunda takamarta miskilanci da girman kai "
"Ai idan miskilanci da girman kai ne kai ta gado ta wannan bangaren bai kamata kaji haushinta ba , daman kuma hausawa sunce mabiyinka mafiyinka , ita bata tsaya a girman kai da miskilanci ba har rashin kunya ,uwa uba nuna kowa ba kowa bane agurinta , well koma dai menene rayuwarta na burgeni dan bata shiga shirgin mutane ...
" ai yau ba dan bakin dake bangaren ba , wallahi a wurin zan kwana naga karshen iskancin miskilanci sai dai ta kwana a kitchen ..
" jafar ya sake dariya gaskiya Maaruf kana kunna yarinyar nan fa da yawa , ba abinda yafi bani dariya sai lokacin da tace wa abbati ya rage sautin ƙaran tv cikin sanyayyiyar muryarta kamar tayi kuka Ina lura da ita wayarta ma dake rike a hannuta a dole take dan nawa..
"Kai rabani da maganar yarinyar nan please "
"ni kuma kaga ina son maganarta ba ko ya suka kare da abokina ..?
Ma'aruf bai sake cewa komai ba ya juya ya koma ciki ya nufi part d'insa inda ya iske abbati yana shirin kwanciya . ..

Washegari suna zaune tare da abbati suna hira yana shan fruit ,yana son yaron sosai saboda yana girmama na gaba dashi abbati ya dauki kankana ya saka abakinsa yana cewa
"ai ba kasan wani abu ba d'azun mun sha hira da mutuniyarka ...
nan da nan Maaruf ya chanja fuska tare da haɗe rai "kar ka kar6a cewa mutuniyata Abbati idan ba haka ba zan canza maka .....
"to yi hakuri na daina" in jinka ma'aruf ya fad'a yana cigaba da shan fruit ," kasan me tace wai tana son tayi aure amma ita a ra'ayinta bata son ta auri mai kudi ko wanda yake bala'i sonta dayawa ,a'a ita tafi son ta auri mara kudi wanda take so, shi kuma yake sonta kaɗan saboda idan ta auri wanda yake bala'i sonta baza tayi masa biyayya ba amman idan ta auri wanda take so zata yiwa masa biyayya ..
" ni kuma nace mata data auri mara kudi talaka gara ta auri mai kudi dan ita kalar masu arziki babu ma talakan da zai zo yace yana sonta dan ko gidan mutun ya kalla ya isa mutun ya fahimci tafi karfinsa amman yarinyar nan tace Ina ita bata san haka ba sai mara kudi take so wanda zai kula daita ya bata farinciki da. ......
"Shiiiiiiiiiii plz abbati maganar ta isheni kwalkwaluwata ta soma birkicewa babu ruwana da maganarta fatan dai Bata zageni ba ?
Abbati yace " a'a "
Maaruf ya mike ya nufi kofar gida ya bar Abbati a gurin sake da baki yana zancen zuci " anya.. sai ya katse tunanin shima ya mike ya bi bayansa ..
washe gari Ma'aruf yana zaune a kofar shiga part din mama, ummita na zaune daga ciki sanye da hijabi akan dudduma shi kuma Maaruf yana chat da budurwansa suhaima , kana ganinsa kasan yana cikin farin ciki da annashuwa ,kamar ance ya juyo ya hango ummita a bayansa tana zaune ta zuba masa ido, sai da zuciyarsa ta buga da matsanancin karfin gaske a yadda take kallonsa yaji kamar ya tashi yaje ya yaryarfa mata maruka tare da kashedi zuciyarsa ta cigaba da dokawa da sauri ya ɗauke kanshi, a madadin ya cigaba da chart sai kawai ya zarce da kira layin suhaima suna gaisawa tare da furta mata kalamai masu sanyi ,yayi haka ne dan kawai Ummita taji haushi , yayinda ita kuma tayi kamar bata san da wani halitta agurin ba , sai ma tayi kamar wacce take lazimi Yana gun bai tashi ba daga karshe ma ya dinga bugawa friend's d'insa mata waya a ƙalla sai da yayi waya da mata sama da biyar kuma duk a handsfree yasa wayar dan taji ta samu damar kai gulma....

********
..Kamar kullun Abba zaune a tangamemen parlour'nsa bayan ya kammala da duk wani abinda ya zama al'adarsa , sannan ya bawa yaran dake ɗan taya sa hira umarnin shigowa , ya dade yana hirar da su cikin nishadi da farinciki , ya aika saifullahi yayi masa kiran ma'aruf , cikin haka ya rayhan da sadam suka shigo domin kawo gaisuwa ,can bayan kamar minti a shirin sai ga maaruf ya shigo parlour'n bakinsa ɗauke da sallama lokacin Abba na zaune yana shan caffe , ya amsa masa sallamar ,a hankali ya karaso har gaban Abba ya durkusa har kasa ya gaishe da Abba cike da girmamawa , "ma'aruf kana lafiya ?
"Lafiya lau Abba ya fama da jama'a ?
"Alhamdullahi ,nan suka shiga muhawara atsakaninsu har kusan karfe goma suna tare suna hira , sannan ɗaya bayan suka fara kokarin barin parlour'n , duk suka watse, kowa ya nufi bangarensa sai mutun ɗaya ne ya rage zaune kansa a kasa wanda ko dan hirar da'aka yi bai wani saka baki ba saboda ya fuskanci tun shigowarsa Abba yake binsa da kallo , hakan yasa yayi saurin fahimtar akwai wata damuwar, duk da yasan lokuta da dama Abba na kiransa idan yaga lokacin shigowarsa kawo gaisuwa yayi har ya wuce bai shigo ba, sai dai yau yanayinsa ya bambamnta da sauran lokuta, shiyasa ya kasa tafiya parlour'n ya ɗauki shiru na kusan minti goma yayinda a hankali abba yake nazarinsa sannan ya d'ago ya dube ma'aruf sannan yayi gyaran murya kana ya kira sunansa "ma'aruf ........
hakan yasa ma'aruf ya tattara dukkan natsuwarsa garesa ya amsa da "Na'am Abba yana gyara zamansa ya d'ago kanshi kaɗan batare daya dubi fuskar Abba ba.
"a halin yanzu muna shirin zuwa ga mahaifin ita yarinyar da kake so da aure, sai dai wani hanzari ba gudu ba , mahaifiyarka ta nemi wata alfarma wanda tun kafin na nemeka na fahimtar daita cewar sai na tuntubeka.
take gaban ma'aruf ya shiga dukan tara tara , "wannan maganar ya tsaya min a rai tun ranar da ta fara faɗa min shi , hankalina ya ɗan tashi kwarai sai dai a jiya data sake min maganar naji idan nayi shiru ban mata adalci ba a matsayinta na mahaifiya , sannan a yadda ta daukekeni da karanci matukar dai naga abinda zai amfanimu dani daita dole ne na nasanar , ma'aruf ya sake gyara zama qirjishi na harbawa da sauri tun bai ji maganar ba walwala ta ɗauke akan fuskarsa ," wannan maganar ba wata magana bace illa akan sakina .........
A matukar firgici ya d'ago kanshi gaba-daya yanayin buguwar da zuciyarsa tayi bata saisaita ba, yanayin yadda ya tsorota sai yaba mutun mamaki,yayinda Abba ke kallon ma'aruf yana sake nazarinsa , jikinsa ke wani irin rawa tamkar wanda aka jona masa wutar lantarki , take idanunshi suka Kada suka yi ja, buɗe idanunshi yayi sosai yace "wace sakina kenan Abba ?
"Ta gidan baba sarki Abba ya bashi amsa atakaice yana dubansa ," hakika mahaifiyarka ta nuna tana bukatar ka haɗasu da ita yarinyar da kake so , ka aurensu gabadaya domin gudun maganar da zataje tazo, atakaice dai mahaifiyarka tana umartaka ka auri sakina amman nace mata lallai sai naji ta bakinka jikinsa ne ya kama rawa har Abba na iya ganin yadda hankalinsa ya tashi dan haka yayi ƙoƙarin kwantar masa da hankali " ka kwantar da hankalinka itama sakina yarinya ce mai nagarta da tarin ilimi zakaji dadin rayuwa daita karka duba girman da tayi maka ,domin hakan bawani sabon abu bane, fiyayyen halitta Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama ya auri matar data girmeshi da shekara shabiya bare sakina da kwanaki arba'in kacal ta baka ya K'arasa maganar yana sauke numfashi still idanunshi na kanshi ....
Tun da Abba ya soma magana zufa ke tsatsafo masa ta ko'ina a sansar jikinsa , yana son katse maganganun Abba amman bazai iya ba .
wannan shirun da abba yayi ya san jira yake yaji daga garesa , gashi shi gaba-daya bashi da lakar iya furta wani abu ko ma ya bud'e bakinsa bai san me zai ce ba, gara kawai yayi shiru ya cigaba da jiran tsammanin ..
Tsawon minti goma suna zaune parlour'n ya sake ɗaukar shiru yayinda idanun Abba ke kansa "kayi shiru ma'aruf baka ce komai ba ko akwai damuwa ne ? Abba ya dafa kan ma'aruf
"Kaje kayi tunani akan lamarin mahaifiyarka sosai ,duk da zanso kayi aurenka kamar yadda ka dauko niyya, amman ka daure kayi mata biyayya ta hanyar amincewa da auren sakina .....
Da kyar ma'aruf ya bude bakinsa yace "shikenan Abba ba sai nayi wani tunani ba tunda har kai ma kaga tana da nagartar da zan iya aurenta ,Allah ya tabbatar da alkhairi ka fadawa umma na amince tayi min addu'a saboda zuciyata na buqatar haka daga gareta , tausayinsa ne ya kama Abba saboda yasan ya dai amince ne kawai dan ya faranta ransu ba dan yana so ba "Masha Allah , Allah yayiwa rayuwarka albarka , yadda kayi mana biyayya kai ma Allah ya baka ya'ya masu albarka da zasuyi maka biyayya , Allah ya tsare mana kai ,naji dadi kwarai da wannan labarin ...
sai magana ta gaba akan abokinka muhd Sa'id ina son ka fahimtar dashi anyiwa ummita miji kar ya sake takowa gidan nan da sunan yazo gurinta , sai dai gurinka wannan kuma bazan masa iyaka ba " sai daya tsaida zuciyarsa sannan yace "Inshaallahu Abba zanyi masa magana tun farko ma na fahimtar dashi "to shikenan kana iya tafiya ka soma shirin auran mata biyu a rana daya ai d'ana jarumi ne .. Abba ya fadi haka cikin tsigar wasa ,da kyar ma'aruf ya mike tsaye bisa kafafunsa ya baro parlour'n Abba zuciyarsa na wani dogawa ,yana layi ya nufi bangarensa dafe da kanshi daya ji yana sarawa tamkar zai cire yana shiga ya faɗa saman katifarsa , ransa duk babu dadi tunani kawai yake "shikenan shima ya zama ummita... auren dole za'a yi musu shi daita , Allah sarki haka ya ɗan ji tausayinta ya tsarga masa, wani irin yanayi ya tsinci kanshi ciki na zallar bacin rai "sakina kin cuci rayuwata bazan taba yafe miki ba kuma da ikon Allah bazaki samu yadda kike so ba, ko kin aureni gangar jikina kika aura ,farinciki kuwa sai dai kiga ana yinsa a wani muhalli amman ke kam kinyi bankwana da farinciki, ajiyar zuciya kawai yake saukewa yana tunanin mafuta yana jin kamar yayi kuka ,ƙwaƙwalwarsa ce tashiga shawagin da cajin neman abinda ya kamata yayi , dan dole yasan abin yi , gaskiya sakin kin cuceni kin yiwa rayuwata shishigi sam bani da Budget din auren mata biyu a rayuwata yayi maganar fili yana cizan lip's d'insa na kasa , mikewa yayi ya soma zagaye d'akin ....
Ranar shima yadda yaga rana haka yaga dare yana tunani yadda zai kaucewa auren amman duk yayi tunaninsa ya gama bai gano hanyar bi ba , daga karshe dai bayin dake makale da d'akinsa ya nufi yayi alwala domin kaiwa Allah kukansa nafila yayi tayi tare da neman zabin Allah....

Ummita ce rike da hannun nusaiba diyar aunty Asiya ,tafiya take a natse kanta sunkuye a kasa ta nufi gidan mama rukkaya aminiyar mama kamar ance mata ta d'aga kanta motar muhd Sa'id tagani tana kokarin shigowa layinsu, wani irin zafin nama da bata san tana dashi ba ta damki hannun nusaiba taku biyar ya shigar dasu harabar gidan, har lokacin qirjinta sai bugawa yake da sauri bata kaunar ganin muhd Sa'id arayuwarta , asalima tsoro yake bata, da sallama ta shiga cikin gidan, mama rukkaya dake zaune ta fad'ad'a fuskarta da murmushi" "ummita talaka yana ganin ku yau satina daya da dawo wa daga ilori amman ko sannu da zuwa ina Amina ?
Ummita ta ɗan saki fuskarta kadan ita kanta tasan basu kyauta ba tuni suka cinye soyayyiyar awarar garinsu amman suka kasa lekowa suyi mata sannu da zuwa ,ta zauna kusa da nadiya diyarta . "ai shiyasa nima naki shiga gidansu inji nadiya diyar mama rukkaya "tam kuyi hakuri gaskiya bamu kyauta ba, kullun muna cewa zamu zo ni da meenal to jikin nawa ni sai a hankali yau lafiya gobe babu, ya kuka baro mutane ilori ?
"Suna nan lafiya har nayo meenal tsarabar samari Fulani kyawawa sai ta kawo tukuici dan ke nasan cewa zakiyi baki da lokaci "gaskiya kam samari me ana zaman qalau ni neman kai ma nake yi dasu , sai dai meenal din kamar yadda kikace.
"neman kai sai kace wasu ciwo, ke dai baki ga samarin garinmu bane shiyasa da tuni kin mika wuya har da rawar jiki yarinya suka bushe da dariya mama rukkaya tace "kunga ni nayi nan da wannan shirmen naku ummita na son mama rukkaya saboda mace ce mai kirki da natsuwa da sakin fuska akwai ta da son mutane kuma tana son mama sosai ..

Muhd Sa'id yayi parking daidai kofar gidan da ummita ta shiga bai yaudari kanshi da tunanin in ya aika ta fito zata fito ba ,babban burina kawai idan ta fito zata shiga gidansu ya sake ganinta dan yasan ko yayi mata magana ba zata kula shi ba tunda sakon mahaifinta ya iso garesa ..
"Ya buɗe murfin motarsa ya ziro kafafunsa waje ya danna CD inda take wakar naramali ta fara tashi, a hankali yake bin su ,a haka awa ɗaya yazo ya wuce, ya canza wani waka, a haka wata awar ta sake shudewa ,jikinsa ya gaji matuka da wannan zama sai dai zuciyarsa bata gaji ba ,ya sawa ranshi
Sai ya ga abinda ya turewa buzu nadi ,kamar yadda ma'aruf ya sanar dashi ya hakura daita rayhan zasu bawa, amman shi ina ba zai iya wannan hakurin ba ,dan zuciyarsa ta kasa fahimtar haka ,zuciyarsa ta makance ta kurmance baya ji baya gani komai sai tarin kaunarta ,idan a lokutansa na baya za'a sanar dashi akwai ranar da zai tsinci kanshi cikin zazzafar so irin na wannan lokaci hakika daya ƙaryata mai magana ,a halin yanzu soyayya ummita ta canza masa rayuwar bakiɗaya , ya kuma yarda ya amince da gaske ummita bata son shi ,kuma bazata sake sauraronsa ba , idan haka ne menene abin yi a gareshi?
Ya shafa sumar kanshi "abin yi kawai ya zauna daga lokacin har zuwa kwanciyar bacci yasan dai dole ta fito ta tafi gidansu ...
Wani tunani yayi ina zai samu yaron da zai kira masa saifullahi yaron da yake kauna har cikin ranshi duk da jin kanin abokin takararsa ne bai sa ya tsani yaron ba saboda shima yayi imani yaron yana kaunarsa ,da wannan shawarar ya fito daga motarsa ya soma takawa da alamun a gajiye yake , cikin haka wata mota kiran bmw ta faka abayan motarsa , matukin motar ya fito zai shiga gidan da ummita ta shiga, da sauri Muhd Sa'id ya K'arasa garesa "dan Allah abokina idan ka shiga ka turo min ummita , Umar ya kalleshi da tunanin inda ya sanshi ,kamar daga sama ya tuno yana ganinsa

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment