Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na  neman taso mata hakan  yasa ta mike da sauri ,d'ago kanshi yayi yana dubanta sannan ya mike da sauri  ya nufota
kafin tayi wani yunkuri gabadaya  aman ya  taho sai ajikinsa a lokacin da yake kokarin tahowa gurinta saboda ganin halin datake ciki , ta dinga kwara amai kamar zata amayar da kayan cikinta hankalinsa yayi matukar tashi sai data gama , ya kwantar daita ya shiga bayin dake manne da parlourn ya cire kayan  jikinsa  ya saura daga shi sai dogon wando ya dawo da ruwa rike a hannunsa runtse idanunta tayi ganinshi babu komai ga fad'ad'd'en kirjinshi sai sheki yake sakamakon kwantaccen sumar dake kwance luf ....
kamota yayi ya wanke mata baki da fuska inda ta taɓa ya goge ko'ina ya janyota jikinshi sai yaji jikinta zafi rau
"subuhanallahi fat lion daman baki da lafiya ne  ?
Ahankali ta d'aga masa saboda yadda kanta ke sarawa sosai kamar zai cire, ya dafe goshinsa "shine dan iskanci kikayi shiru  tashi muje asibiti ta narke fuska  taki tashi  ya dauki waya ya kira doctor husain dake dubata, yace "gashin nan  zuwa ya daukeshi  ummita  bata da lafiya ,mikewa yayi ya dauki White singlet d'insa da bai ɓaci ba sai  danshi amai  ya sanya dole dan babu yadda zai yi ,gida ya wuce ya sauya kaya sannan ya d'auko Dr husain cikin minti talatin suka   k'araso cikin parlourn  tare da  mah'ruf.

ya nuna masa inda take kwance akan doguwar kujera ta lullube jikinta  da bargo saboda sanyi da take ji ,Dr Husain ya zauna ya tsira mata ido "ummita sarkin ciwo ke ba sikila ba amman kinfi mai ciwon laulayi yanzu ya kike ji ? Ta  waigo   tana yatsina fuska a shagwa'be da niyyar magana  sukai  ido biyu  dashi ya watsa mata harara  " Malama  ki amsa  masa  tambayarsa yadda dace ya fadi haka yana kawar da fuskarshi ..
Dr husain yayi  mata tambayoyi tana bashi amsa a tsanake ,  ya ga bama bangaren da yake tunani bane ya dubi Mahruf dake aiki a system dinsa "ina ganin yakamata ayi mata awon fitsari  saboda babu duk abinda nake zato  ..

Mah'ruf yayi shiru tare daina abinda yake ya d'ago  kirjinshi na wani irin  matsanamcin dokawa  da karfin gaske sai daya ɗauki second biyar yana kallon Dr husain sannan ya mike tsaye ya kamata suka shiga bayi gabansa na dokawa da karfi  ,yayinda ita kuwa ko ajikinta  bata damu ba ,a bakin bayi ya tsaya tashiga tayi fitsarin suka dawo ya mika  masa, ya mike tsaye  yace ",zan  je asibiti na dawo duk abinda sakamako ya nuna zan  dawo dashi da magunguna .

  Yana fita Mah'ruf ya dawo ya zauna gabanta yana kallonta saboda ganin tana kuka dan  jikinta gabadaya babu dadi ga sanyi  mugun  ciwon kai ,  bai ce mata komai ba  ya mike ya dawo kan aikinsa yana yi hankalinsa na kanta yana sauraron kukanta mai bala'in kona masa rai ya tsani wannan kukan nata, idan ta fara shi bata ji bata gani banda abunta  meye abun kuka a zazzabi  .

Awa daya tsakani Dr husain ya dawo da sakamako, hannu ya mika masa da niyyar soma magana ya dakatar dashi "muje daga waje kou.
Yayi gaba Dr husain na binshi a baya ya jashi bangaren  baya ta inda babu me jin abinda zai faɗa , haka nan  zuciyarsa ke cike da tsoro  jin   furucin da Dr husain zaiyi a gabanta hannu ya sake mika masa  ....

Zaku dan jini  shiru  sai yadda ta yiwu ..

TWO FRIENDS BSBD


💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL


AL'QALUMAN



*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*


~DEDICATED TO~
*MARYAM TIJJANI ADAM*


WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim


PAGE 43

......"Bismillah ina sauraronka dr husain ?
Sai da dr husain yayi gyaran murya sannan yace "congratulations matarka na d'auke da juna biyu na wata ɗaya da yan kwanaki .
mah'ruf yayi mutuwar tsaye cike da matsanancin tashin hankali tare da zaro idanu waje "ciki doctor?
doctor husain ya gyada masa kai "kwara kuwa sai ka saka rai nan da wata bakwai da wasu kwanaki zaka samu d'a ko 'ya koma ya'ya ..

Ya lumshe idanunshi yana shafa keyarsa qirjinsa na cigaba da dokawa , ba kowa yake ji ba kamar fatlion dinsa , bai san yaya zata yi react idan cikin ya fito ba , saurin kawar da wannan tsoron yayi acikin zuciyarsa ya maye gurbin wajen da addu'a cike da murna, dan Allah yayi shi da son yara bare wannan da zai kasance nashi na kanshi bai san irin kulawar da zai bawa baby'n ba ,sosai cikin ya shiga ranshi murmushi ne ya subuce masa yana cigaba da shafa sumar kanshi .

"doctor husain yace " bari na faɗa maka magunguna da zata dinga sha ,kuma a kula daita sosai ba'a son tayi ayyuka masu wahala dan gudun samun matsala , a tsanake ya sake lumshe idanunshi "karka damu Dr duk za'a kiyayye inshaallahu na gode .

"Allah ya inganta ya kuma sauketa lafiya idan ya kai wani watani zata soma zuwa awo domin a dinga sanin halin da yarinyar ko yaron yake ciki, mah'ruf yayi shiru sai dai har lokacin fuskarshi ɗauke take da murmushi da shi kaɗai ya barwa kanshi sani irin farincikin daya tsinci kanshi , doctor husain yace " su ummita za'a yi ɗan kai ko yaya zataji ?
"ka faɗa mata daga yau kuka da shagwa'ba ya kare sai tabarwa babynta ,ga kuma batun karatu ko yaya zata yi da jam dinta ?
"duk shirme take babu wani karatu wanda tayi ma Allah yasa albarka" "kenan baka da ra'ayin karatun mace ?

"Ko ina da ra'ayi ita din ce bazata yi ba ,doctor ya soma tafiya yana murmushi mah'ruf na biye dashi domin yi masa rakiya suna tautaunawa har inda yayi parking din motarsa sukayi sallama .

Da hanzari ya koma part din mama ya zauna kusa daita yana kallonta yana jin kamar ya sunkuceta ya d'agata sama yayita juyi daita ko kuma ya rungumeta a jikinsa amman bazai iya ba ,ba zai iya nuna mata halin da ake ciki ba , zai barwa zuciyarsa komai har zuwa sanda cikin zai bayyana kanshi , cikin wani irin farinciki mara misaltuwa yake kallonta gabad'aya ya manta da matsayin da take dashi a zuciyarsa .

Ta zuba masa fararen idanunta haka nan ta tsinci kanta cikin zallar farinciki duk da zuciyarta na cike da fargaba , mikewa tayi zaune suna fuskarta juna sosai , yayinda gwiwowinta ke haɗe da nashi tafukan hannuwanta duka ta d'aura saman cinyoyinsa wani irin abu taji yana fizgarta akanshi da ba zata iya cewa ko menene ba , zuwa yanzu zuciyarta tayi sanyi sosai akanshi har take jin zata iya cigaba da rayuwa dashi ko ma a yaya makomarta zata kasance agurinsa, koda kuwa bazasu so juna ba zata daure ,idan ma bata d'aure ba yaya zatayi da rayuwarta ?
Zuciyarta ta yiwa kanta tambayar ...........
zuciyarta cike da
zullumi ta cigaba da kallon cikin idanunshi, sannan a hankali ta soma motsa labbenta "yaya .... ....ta kira sunanshi jikinka a sanyaye ya tsura mata idanunshi kawai "ya naga jikinka a sanyaye sannan fuskarka kunshe da faricikin me doctor yace yake damuna ?

Cikin sanin madafar abinda zai faɗa mata ya
d'aura tafin hanunshi a saman nata "ba wani abu me tsanani yace ba illa zazzaɓin maleria dake damunki .

"Shine fuskarka ke kunshe da annuri da farinciki irin haka ?
Tayi masa tambayar tana tsareshi da narkakkun idanunta qirjinta na dokawa , ya lumshe idanunshi na second biyu sannan ya buɗe yana busa mata iskar bakinsa "ko ɗaya saboda me zanyi faricikin dan baki da lafiya ?
"Kawai dai wani abu ne daban ya sani farinciki "me ye shi ? ta sake tambayarsa shiru yayi yana kallonta itama
ta tsura masa idanunta tayi cikin zullumi ,tana sauraronsa tana jin wani iri a sansar jikinta tana aiyana ina ma ita dashi suna son juna da bakaramin dacewa sukayi ba , yadda take aiyanawa ranta , haka shima yake ji a zuciyarsa , tafukan hannunshi dake saman nata ya dinga yawo dashi a saman hannunta .

a qalla sun ɗauki tsawon lokaci suna kallon kwayar idanun juna zuciyoyinsu na dakowa da sake nikaya acikin tafkin qaunar juna ya had'iye abinda ya tsaya matsa a makoshi "ya kika yi shiru ko baki yarda bane ?
Ta kakkalo murmushin yake wanda ya tsaya iya lip's dinta tace "me ka gani ?"Rashin yarda acikin kwayar idanunki " "kamar haka ne .

"ai na fahimta hannu yasa ya d'agota tare da mikar daita tsaye yana aika mata da wani mugun kallo wanda yasa take gabanta ya fadi ,tana kallonsa a ranta tace "ba dai yaji haunshin maganar danayi ba ?
"ki yarda da maganar ko karki yarda am not care ni dai ki natsu inji cewar likita yace babu wani aiki kawai " ta dinga kallonsa assessing maganarsa ," har yaushe zai nuna ita din wata abace a gareshi? sosai kirjinsu ke bugawa a tare saboda kusancin da sukayi , hannunwanta duka ta kai kirjinshi batare da tace masa komai illa kallonsa da take kamar yadda yake kallonta ahankali jikinta ya soma rawa saboda rashin kuzarin da jikinta yake dashi .

a kallon da yake mata ya karanceta tsab ganin tana kokarin yin kasa yayi saurin janyota tare da matseta ajikinshi ya d'aura kanshi a saman sumar kanta yana shaƙar Kashim gashinta tare da lumshe ido , matseta yayi sosai tasa hannu tana kokarin zamewa ajikinshi "ka daina zakewa a jikina plz .....
Ya Kai bakinsa cikin kunneta "ni ne ma nake zakewa ? ya faɗa yana sake matseta sosai a kirjinshi kamar zai rabata gida biyu " cikin ni dake waye yake zakewa ?
"Wa ya soma kai hannusa jikin wani ?tayi shiru ta kasa furta komai ,yadda ya matseta yasa numfashinta ke kokarin tsayawa saboda rashin samun isasshen numfashin , iskar bakinsa ya dinga busa mata a fuskarta wanda hakan yasa jikinta mutuwa ta dinga jin wani irin yanayi ajikinta "plz ka sakar min jiki a yadda nake jin kaina komai zai iya faruwa ...
"Bazan sakeki ba duk abinda zai faru ya faru amman sai kin faɗi wanda ya soma taɓa wani ya k'arasa maganar a daidai lokacin da numfashin yake daf da tsayawa ta soma yin kasa yayi hanzarin surata gabad'aya ya kwantar akan doguwar kujera ya rankwafo jikinta suna shaƙar numfashin juna, kamkame jikinta tayi guri ɗaya tana fitar da numfashi da kyar gabadaya kwalkwarta ta kasa ɗaukar abinda yake mata , matsota yayi sosai yana furzar da numfashi, ta runtse idanunta gam jikinta na cigaba da rawa kuka ne ya kufce mata "banason abinda kake min I don't like it if..... "shiiiiiiiiiii ya da'ura yatsansa akan lip's dinta "malama kiyiwa mutane shiru ko wani abu aka miki ?

ta girgiza kai "babu tana kokarin had'iye kukanta , janye jikinshi yayi a hankali ya koma mazauninsa yana jan tsaki yana jin haushin da takaicin kanshi tare jin wata matsanamciyar kunya ...
"ka dinga saisaita kanka mah'ruf akan yarinyar nan baka son yarinyar kake ba me yasa kake son shige mata ?
"ai ba laifina bane nima tsintar kaina nake ya bawa zuciyar data aika ma kwalkwaluwarsa tambayar amsa , ya rufe system dinsa ya mike tsaye "zanje gida daga nan zan biya na tsiyo miki magungunan da doctor ya rubuta karki fita ko'ina ko bangaren hajiya kafin tace wani abu har ya juya ta buɗe idanunta tana bi bayansa da kallo "ya rabbi ni kuma irin tawa qaddara kenan ?
" wajen matarsa fa zai fara zuwa kafin ya tsiyo mata magani ,tayi shiru tana tunani kafin daga baya tace "ni yanzu menene makomar aurena dashi ?
Ta gyara kwanciya tana jin ranta babu dadi ta ja guntun tsaki "har da wani kafawa mutun doka aikin banza kawai malam sosai tayi zurfi cikin tunaninsa babu abinda zuciyarta take sai zafi da rad'ad'i ,a halin yanzu ta soma tsanar matarsa tsana kuma mai karfi, bata son ganinsu tare ,yanzu da taji gida zai fara zuwa kuma tasan dole su hadu hankalinta yayi bala'in tashi ta dinga jan tsaki ,ta lumshe idanunta inda take zuciyarta ta soma aiko mata da tambayoyi iri iri "kin fara son mijinki subai'a ki fito ki nuna masa ko kuma ki kwantar da kai ya amsheki tamkar matarsa ta gida ...


tana kwance tana wannan tunanin meanal tashigo , da sauri ta karaso ta zauna kusa daita "sannu ummita yanzu yaya yake fad'awa ummah a she baki da lafiya yaya jikin naki ?
ta ware idanunta tare da ƙoƙarin mikewa zaune menal tayi saurin kamota ta zaunar daita ta jingina bayanta da kujera ,shiru sukayi na kusan biyar sannan ta kira sunan meenal cikin wata kasalliyar murya ..
Menal ta motso sosai kusa daita ta riko hannuwanta duka "me kike so ummita ?
"Babu komai menal but ina son na tambayeki wani abu ne "
"Uhm ina jinki ?
"Kina son abdulshakur ko?tambayar ta bawa meenal mamaki daga karshe murmushi ya subuce mata "me yasa kika min wannan tambaya ?
"Ki amsa min tambayata Yes or no ?
"Ina son shi mana har ina fatan ya zamo miji gareni ,"ta lumshe fararen idanunta qirjinta na dokawa kamar zai fito waje "plz can you tell me how do you feel about him ?

Meeanal ta tsaya shiru tare da tsura mata ido jin abinda tace , ta motsa yatsun hannunta dake cikin na menal "tell me plz bani da wanda zan tambaya sama dake . naunauyen ajiyar zuciya menal ta sauke sannan tace "I feel many things ummita , abu mafi muhimmanci akan yadda nake ji shine yawon fad'uwar gaba alokacin dana tsinci kaina cikin tafkin kaunarsa, a duk sanda zan gashi zuciyata zata cure guri ɗaya ta kasa sarrafa kanta hatta numfashi da kyar nake iya fitarwa , idan ina kallonsa kuwa har banason ɗauke kwayar idanuna akanshi ,bana kaunar abinda zai min shamaki dashi har yanzu da nake gabanki ina jin haka a sansar jikina duk sanda na tuno shi gabana na fad'uwa da matsanancin karfi sannan banason ganinsa da kowace mace matukar ba kanwarsa bace ...

idanu ummita ta runtse zuciyarta na bugawa da karfi tamkar ana buga mata guduma "duk wannan abun data lissafa babu wanda bata jin akan mah'ruf ta sha jinsu a tsawon shekarun da suka gabata idan haka ake ji a soyayya kenan itama ta dade da faɗawa cikin tarkon so?
Tayiwa zuciyarta tambayar "no impossible ta yaya zan so mutumin da bai kaunata yau bare gobe "kina jin duk abinda na lissafa miki ?
Ta gyada mata kai jikinta a sanyaye "duk inda mutun ya tsinci kanshi cikin wannan yanayi tabbas ya afka cikin shaukin so, kin kamu da soyayyar ya mah'ruf kou?

Tayi saurin bude idanunta tana dubanta gbdy ta rasa me zata ce mata "ki fada min yar'uwa , zai yi wuya ace zuwa yanzu baku kamu da so juna ba , ki fada min gsky akan shi kike wannan tambayar "no.... ...kawai dai na tambayeki ne.
"ba zai zama kawai ba ummita dole akwai wani dalili just tell me the truth ..?
Hawaye ya gangaro mata ta shiga girgiza mata kai "ki fada min gaskiya mu san hanyar da zamu bi domin karkato da hankalinsa gareki "ko sau d'aya ki bawa zuciyarki abinda take so sannan kiyi abinda kowa zai yi farinciki , kuka kawai take batare da tasan abinda zata cewa yar'uwarta ba "kai ba ta yarda ba ina baza ta amincewa zuciyarta da ta kamu da matsanancin son Mah'ruf ba Allah ya tsareta da wannan mugun abu .

ahankali ta zare duka hannuwanta cikin nata ta mike tsaye a hankali take tuna abubuwan da sukayi ta faruwa a tsakaninsu ..
"Mutumin da bai damu daita ba , me yasa zaki dinga damuwa dashi kamata yayi ki sake nisanta kanki dashi ,ki kauracewa tunaninsa ba wai ki zauna kina hasarar hawayenki akan mutumin da baki da tabbas akanshi .....

"ina son na ganku tare muddin rai cikin inuwa ɗaya zan so ace duk abinda kike ji akan shine, kina son ya mah'ruf karki boye min damuwarki juyowa tayi tare da rungumeta "bana son shi meenal ,amman ina jin duk abubuwan da kika lisafa akanshi yaya zanyi na daina jin haka kuka take sosai "plz find solution for me ...
"menal do something to save my life zuciyata na cikin wani hali bansan yadda zanyi ba ..
bayanta meenal ta shafa "stop crying ummita ki yarda ko karki yarda kina sonshi tunda kina jinshi ajikinki just sacrifice your happiness to him "what are you trying to say menal ?
"Abinda nake kokarin cewa shine cikin biyu kiyi ɗaya ko ki furta masa ko kuma ki sauke wannan girman kan naki ki janyo mijinki jikinki ki nuna masa a aikace .. .

"i cant I can't babu wanda zan iya ciki abinda kika lissafa gara na mutu akan furta masa wannan kalmar gareshi , koda kuwa da gaske ina son ne , bare ba son shi nake ba tana gama fadar haka ta zame kasa bisa gwiwowinta tana wani irin kuka ..... ..

Fridge menal ta nufa ta buɗe ta d'auko ruwa mai sanyi kaɗan ta dawo gurin da take durkushe ta mika mata ruwa "take some water , kin amsa tayi "ki amsa ki sha sannan ki natsu sosai ki saurari zuciyarki duk abinda ta fahimtar dake kiyi amfani dashi amman ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba kin kamu da matsanancin son ya mah'ruf "Allah ya tsareni domin kuwa son shi shine babban abun kunya da zan aikatawa rayuwata tana gama fadar haka ta mike jikinta na rawa ta nufi step da kyar ta kai kanta d'akinta ta rufo kofar da karfi ta sanya key tare da jingina bayanta da kofar hawaye na zubo mata .

"ya Allah me yasa abubuwa ke faruwa dani haka ? "Allah ka gani bani da kowa sai kai da mahaifiyata idan har da gaske na kamu da son mah'ruf Allah ka gaugauta ciremin saboda ban san yadda zanyi ba Allah ka taimakeni ka kubutar dani .......

Buga kofar menal take da karfi tana kiran sunanta "ummita ki buɗe ga ya mahruf nan ya dawo ,shiru tayi jikinta na cigaba da rawa , tasa duka hannuwanta ta toshe bakinta haɗe da bude kofar ta faɗa saman gadonta hankalinsa a matukar tashe ya k'araso "ke ina take ? Ya tambayi menal .

"Tana cikin d'akin ta bashi amsa tana nuna masa d'akin da yatsanta "me yasa na ganki haka kamar baki da gaskiya ? Ya tura kofar batare daya tsaya

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment