Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rayuwar ummita  adalici,  ya kamata  hankalinka ya dawo jikinka kayiwa ummita duban hankali da kyakkyawar fahimtar da tsananta bincike kafin ka yanke hukunci ,amman ka zauna ka cigaba da ɗaukar hakinta akan abinda ni nasan ba zata taɓa aikatawa ba ..

" A yanzu baka da sauran kalmar da zakayi amfani dashi a wajena"  dan girman Allah mama kiyi  hakuri  ki yafe min wallahi wallahi bazan iya rabuwa  daita ba koda kuwa duk duniya ne zasu taru akaina I can't I can't wallahi bazan iya ba yanzu haka na kai maganar gurin ma'aikata har an samu nasarar kama  hafiz ...

zuba masa idanunta tayi na second biyu sannan tace "babu ruwana da wannan matsalar abinda ya kamata kayi a farko shine ya dawo karshe    "ka bar min ita  ta huta  kawai idan ta mutu ni nayi hasara .......
nice zan yi hasarar  ba kai  ba  zaka cigaba da rayuwa da matarka ni kuma fa ?" shiyasa na rokeka ka bar zuciyarta ta huta    .

kwallar idanunsa ya sharce yana girgiza mata kai , flat  ya  kwanta a gabanta tare da haɗe hannuwansa   "am sorry my mumy ,my everything  , my happiness  am sorry for huting you I apologise on my behalf  naunauyen ajiyar zuciya ta sauke sannan ta samu guri ta zauna hade yin tagumi da hannunta ɗaya  tana kallonsa ya matso da sauri zuwa gabanta "ki yafe min mama muddin na  rabu da subai'a  duniya ce zata fara  tsine min albarka ..

"Ki tausayawa halin da zan shiga idan bata tare dani , kiyi hakuri ki yafewa mah'ruf bazai sake aikata kwatankwacin haka ba , nayi kuskure wallahi mama nasan nayi kuskuren yarda  da hakan ,zan canza mama ,zan zame mata yadda take so wallahi bazan sake yarda da maganar kowa ba ki taimaka mamana wallahi tun yanzu na soma zazzabin mutuwa idan kika masa zan mutu na bar mata duniyar ...

hannunta na rawa   ta d'aura bisa  kanshi  tana mai runtse idanunta "bazata iya jura rasashi ba   ita kanta ba wai tana son raba tsakaninsu  bane  amman wahalar tayi yawa, tayi haka ne dan yasan mahimmancinta ,
soyayya gaskiya da gaskiya take masa uwa uba uwar data kawo shi duniya, mace mai karamci da mutuntaka tattare da kawaici, macen da samun irinta ke da tsananin wuya  a wannan lokacin kusan minti goma hannunta na saman kanshi shi kuma yana mata magiya   "kinyi shiru mamana dan Allah  kice kin  hakura   karki yi fushi da mah'ruf ɗinkin duk  duniya   bani da  kamarki     " ki kara min lokaci    just a litttle time zan canza gabad'aya ba hoton wani ba ko ganinsu nayi tare zan hakura .

"Allah ma bazai sa ba komai ya wuce   tayi saurin dakatar dashi  ta hanyar fadar haka ya d'ago da sauri kuma a gigice  ya zuba mata idanunshi   alamun da gaske take ? " ta gyada masa kai "na gode  mamana  cikin   hikima  take   masa nasiha  mai shiga jiki  , daga  nan   sai hira ta barke  atsakaninsu kamar basu ke kuka a wanin da suka gabata ba, lallai tsakanin mahruf da mama sai Allah  ya riko hannunta cike da farinciki "wai mama  da gaske kinyi  niyyar rabani da qauna ..?

"In har  zaka iya nunawa duniya ita din ba kowa bace a gareka me zai hana baza'a rabaku ba shi fa aure ibada ne matukar   akwai cutarwa gara rabuwa "ai kuwa wallahi da kin iskeni cikin mahaukatan dake yawo a cotonue dan haukacewa zanyi  na koma can da zama "Allah bazai sa naga wannan mugun abu  ba ...

Tashi sukayi  suka nufi d'akin  mama , ummita na zaune  tare da aunty  tana shan tea mai zafi    ganinsa yasa   ta haɗe fuska  tare  da kawar da fuskarta gefe  tana cizan lip's  dinta,  ya tsaya a bakin kofa  rugume  da hannuwansa a qirji  yana  cigaba  da  kallonta da tsantsar mamakin abinda yaga  tayi ,a hankali  ya  karaso   ya zauna  akan gadon   ya kai  hannuwansa duka bisa  kafafunta yana mammatsa   mata    batare da yace  mata  uffan ba  , ganin yadda   yake mata     yasa  mama ta juya  ta  fita  ta bar musu d'akin  , aunty ta dube shi tace  "meye haka daga shigowarka babu kunya babu tsoron Allah ka wani farwa yar mutane ?

"me nayi aunty ?"Ban sani ba dan rainin hankali kawai ka  tashi hankalin mutane shine yanzu zaka wani lalla'bo wa yarinyar mutane da ko lafiya bata dashi ,oya tashi  maza ka kama gabanka bama bukatarka anan  "ya zubawa ummita kyawawan idanunshi da suke kara narkar mata da zuciya "ko zan iya sanin abinda  ke damunki ? tayi masa banza rike da cup din tea da tunda yashigo ta gagara sha ,ya mugun tsareta da idanunshi yana jan yatsun kafafunta ta ɗan kalleshi qirjinta na dokawa "meke damunki ? ya sake tambayarta yana shafa tafin kafafunta "Babu komai  ta faɗa cike da sanyi jiki  .

aunty ta amshe maganar "babu komai fa kikace ? ki bude baki kiyi masa bayanani  yasan mugun abinda ake miki   "plz aunty ki barta tayi magana mana ki daina saka mata magana a baki yayi magana yana cigaba da mammatsa kafafunta ,cike   da  mamaki  ummita  take  satar   kallonsa  zuciyarta na bugawa da matsanancin  karfi ,  amman ta kudurce aranta komai zai mata sai dai ya gaji zata jure bazata nuna a jikinta ba .

tsaki aunty taja ta nufi hanyar fita  "karka bari na dawo dakin nan na  tarar da kai tana fita ya tashi yayiwa kofar key ya dawo   ya  cigaba da matsa mata  kafafu har ya yaye doguwar  rigar dake sanye ajikinta  fatar kwarinta   suka   bayyana mai matukar kyau da sheki  ya lumshe idanunsa kana ya fara yi mata tafiyar tsutsa  da  farcensa  gaba-daya   ta kasa motsin kirki dan abinda yake mata  ba a iya sansar jikinta kadai   take ji ba, har cikin  zuciyarta take jin saukar  yatsun hannunsa, a tsanake  ta  tsura  masa  idanunta tana  kallonsa batare da ta kifta  ba .

tsadadden murmushinsa  ya sakar mata  ya matsota sosai ya hura mata iskar bakinsa da sauri tayi kasa da kanta ta ja baya zata sauka , ya riko hannunta cikin nashi yana murzawa  kasa juyo tayi  ta kalleshi saboda abinda  take ji ajikinta ,cikin wani irin salo ya  kira sunan  daya rad'a mata "qauna .......
wani irin zirrrrrrrr taji a gabad'aya ilahirin jikinta mai kama da shocking a yadda ya kira sunan ba karamin rudar daita yayi ba "Yau kuma guduna kike yi ?cikin Sa'a ta sanyawa jikinta  jarumta ta janye hannunta  dake  cikin nashi  ta sauko tana haɗe fuska tare da  cewa "ka je can ka nemi qaunarka amman ni ba qaunarka bace  , ta tsaya a tsakiyar dakin  tana rungume  duka hannuwanta a qirji  ,wani kalar numfashi yaja ya sauke  da karfi ya yunkura  ya sauko  ya tsaya a tsakiyar d'akin tare  da zira hannunsa ɗaya cikin aljihun wandonsa , yayinda hannunsa ɗaya ke kan habarsa yana kallonta yana takowa gareta yana  shafa  sajen fuskarsa , baya  taja  tana sauke numfashi  da kyar ,shima ya  biyota yana cigaba da kallonta batare da yayi magana ba , har ta kai karshen bango ta jingina bayanta tana sauke   ajiyar zuciya  "meye haka  ? ta faɗa tana haɗe rai kamar bata taɓa dariya ba .

"I don't know  ya bata amsa yana  shafa dukiyar fulaninta da qirjinsa , ta sake kurewa bango ya matsota har suna musayar numfashi ya kai hannunsa wuyanta yana shafa zuwa kirkira  tayi  saurin buge hannun tana sunkuyar da kanta  kasa "plz banason damuwa dan Allah  abar zuciyata haka, bata son ganinka yanzu a kusa dani , ya Kai hannunsa jikin bango ya tokare  yana kallon sansar  jikinta  "say it  again  ?

"Banason ganinka banason  kusancina  da kai  ya sake motsota sosai  ya matseta da qirjinsa  batare daya kai hannunsa jikinta ba " sosai jikinsu ya haɗe suna shaƙar numfashin juna da kanshin turaren da sukayi amfani dashi ," kina  fadar  son ranki ne kawai  amman  duk duniya babu abinda zuciyarki tafi so da bukatar  kasancewa tare kamar  mah'ruf  ya kare maganar yana yawo da hannunsa a fuskarta "ka daina  banaso idan  ma kana yi dan naji wani abu ne kasani bana jin komai wallahi  sai zallar bakinciki .

"uhmmmmmmm okay bari na tabbatar da hakan da kaina  ya d'ago habarta ya  haɗe hancinsu  guri daya bakinsa dai-dai bakinta, kwayar  idanunsu cikin   juna  ,suka zubawa juna idanu    suna jin  qaunar junansu na sake shigarsu , matso da bakinsa  yayi  yana kakarin  haɗe bakinsu ta kawar  da fuskarta tana sauke wani wahalallen numfashi "no ta furta a fusace  .....

Cikin zafin nama  ya  juyo  da  fuskarta "bai  kamata ki juyar da fuskarki  ba tunda bakya  jin  komai  "ni ...ni ka barni  dan Allah tayi maganar  cike da in Ina, " baki isa ba sai kinji abinda  baki son ji , bakinsa  ya sake daidaitawa  da  nata  ya cafki lip's dinta   wani   irin  tsotsa  yake musu na fitar hankali ,tun tana iya  kaucewa har ta hakura ta barshi , ganin tsayuwa  na neman gagararsu    ya jata zuwa  kan gado dan itama a lokacin babu abinda zata iya tabuka wa  dan ba karamin mutuwa jikinta yayi  ba ,ya  kwantar daita a gadon  ya haye bisa  kanta ya cigaba da sarrafa  a hankali  muryarsa ta fito "yanzu fa  ko har yanzu bakya jin  komai  ?tayi masa banza da alamun da gaske bakya jin  komai  rigar jikinta ya zame kasa kadan dukiyar  fulaninta  suka bayyana yayi saurin had'iye wani miyo daya tsaya masa a makoshi, tun daga wuyanta ya fara shafata  yana lasar skin dinta  bai  tsaya   a ko'ina ba sai saman dukiyar fulaninta ya shiga kissing dinsu  ido rufe  , lokaci daya  jikinta ya  fara kyarma tsabar  tashin  hankali .

A tsanake ya dinga  aika mata da manya sakoninsa   wannan karon ƙoƙarin  dakatar dashi tayi ta hanyar fashe  masa da kuka "dan Allah ka barni  misscarriage    fa nayi  yau  ka barni naji da damuwata  take jikinsa ya dauki rawa gaba-daya ya rikice ya mike a matukar  gigice yana dubanta  fuskarsa da alamun tambaya "'bari......
ya maimaita yana Kallonta   ta gyada masa kai tare da yunkurawa  taja baya kaɗan tana sauke ajiyar zuciya matsota yayi da sauri  "wayyohlly Allah da gaske karki faɗa min karya mana ?

Bata ce masa uffan ba ta sauko tana duba jikinta saboda dumin zubowar jini da taji ,ya  tsura mata ido yana yafitota da hannunsa alamun tazo garesa , taki zuwa  babu shiri ya sauko  ya kamota  ya  zaunar daita ya matso kusa daita  yana cigaba da kallonta "kayi hakuri nasan  zakayi wani tunani daban akaina  amman wallahi cikinka ne ban taɓa aikata wani abu da wani namiji ba bayan kai ...

"On expecting taji ya   rungumeta a jikinsa yana  sauke numfashi yana shafa  bayanta ya kasa furta komai duk da maganar yake son yi kusan minti  ashirin tana rugume ajikinsa  canzawar numfashinta  yasa  shi  zareta ajikinsa ya  kafeta da idanunshi  ahankali   take  fitar da numfashi  ,alamun ta soma bacci, ya kwantar daita ba dan ya yarda baccin take ba , "ko bakiyi baccin karya ba zan barki dan nasan  kina bukatar hutu ya  lullu'beta ya gyara zaman rigar jikinsa, ya fito  daga d'akin  zuwa   parloun kasa inda  ya iske mama , ya tsaya kusa  daita "mama a she qauna  bata da lafiya ?
"Eh kawai  mama ta faɗa  ta mike ta shige kitchen , ya biyo bayanta "shine kuma aka barta a gida ba'a kaita hospital ba ?"Kai  za'a fadawa ,kai din kuma  baka cikin  hankalinka , me zaka iya yi alokacin  ko an faɗa maka ?

"koma dai menene mama ai bai kamata abarta a gida ba , bari na kira doctor husain ya ciro wayarsa ya soma dilling number doctor husain, cikin wasu yan mintiuna ya k'araso tare suka shiga dakin  idanunta biyu suka tarar daita tana ganinsu ta runtse  idanunta  doctor husain ya dubata yace" suje asibiti ayi mata wankin mahaifa .

"doctor kayi min allura kawai ta wadatar banason wankin cikin nan akwai wahala ina  ji kamar na mutu a duk sanda ake min , jin haka yasa mahruf yace "kayi mata allurar kawai idan babu matsala "okay , allura yayi mata a hannu suka fito tare da mah'ruf cikin lokaci kankani bacci yayi awon gaba daita kai tsaye police station mah'ruf  ya nufa dpo ya bada umarnin a kawo masa  hafiz wanda ya sha mugun duka a dalilin kin fadar gaskiya da yayi da farko ,shi kansa mah'ruf bancin yayi masa mugun sani da bazai ganesa ba , shiru yayi yana kallonsa yana sauraron bayanin dpo akan gaskiyar lamari bayan dpo  ya gama magana yace hafiz ya fadi yadda komai ya faru  ..

"Ina zaune a kofar gidanmu a wani yammacin ranar laraba wata mata   tazo min da wannan aiki tace kasan ummita subai'a ?ina jin haka nayi saurin  tattara hankalina gareta dan  jin sunan subai'a   "nasan kaso subai'a a can baya  kuma har yanzu kana kan sonta ? nayi saurin girgiza mata kai "sosai ina sonta fiyye da komai dake cikin duniyar nan amman ke din wacece ? Babu ruwanka da koni wacece   aiki nazo maka dashi wanda zai kawo maka farinciki arayuwarka   nayi shiru ina saurarenta domin jin wani irin aiki ne "nasan a yadda kake haukan sonta zaka iya yin komai akanta dan ka sameta "nayi saurin daga mata kai ,tayi murmushi sannan tace "  zaka zo gidana vekly estate da dopemu express  a matsayin kwarto  ni  kuma zan qarasa sauran aiki  muddin kayi  haka ina tabbatar maka zaka sameta cikin sauki  , nayi matukar mamaki sai dai nayi faricikin cewar hakan zai zamo silar da zan samu auren subai'a a rayuwata  wanda ban sani ba a she matsala zan jefa kaina  ,  cike da farinciki na amince mata  ,da fari taso na kasance tare da ummita har mijinta  ya dawo sai dai naji  tsoron haka dan ba san me haka zai jawo ba ,na gwamaci Gara idan mijin baya gida   yana nan kawo wa nan  yayi shiru yana duban mah'ruf da kuburarun idanunta da bai iya gane kowa mahruf ya numfasa yace " Allah sarki shiyasa ake son bincike idan matsala irin haka ya faru yanzu da zuciya ta debeshi ya kusan sakin matarsa dawa gari ya waya ?  "Wacece wannan matar dan sam zuciyarsa bata kawo masa suhaimar nace "ban santa ba hasalima ranar na soma ganinta amman idan na ganta zan ganeta mah'ruf ya haɗe hannuwansa ya rufe fuskarshi dashi dpo ya bada umarni a mai dashi "zamu cigaba da bincike inshallahu za'a gano kowacece take da sanya hannu mahruf ya mike tare da mikawa dpo hannu "na gode sosai kuma na yaba da kokarinku dan Allah a gaugauta binciko min ko wacece , sannan nima ta bangarena zan cigaba da bincike sukayi sallama ya wuce  ..

Lokacin da labarin  abinda  ya faru ya  iske hajiya rahma kamar su zuba ruwa a kasa dan dadi rawa  ta kama yi ita kuma zulaihat har da birgima a kasa  ,  suka fara  cashewa domin nuna murnarsu  suka yiwa gidan diran makiya bayan sun gama waya da suhaima  har  yamma  suna tare suna taya juna murna  barin  suhaima  da  burinta ya cika  makiyayarta  ta bar mata gida kallon juna  suke suna sheka dariya suna maimata abinda ya faru..

Suhaima ta tashi haɗe da shekewa da  wata mahaukaciyar dariya "yayyarmu Allah yayi miki albarka  ,Allah ya barki da ya  Umar   daga ke babu kari a gidansa  ke dashi muddin rai mutu ka raba  ,haka kema aunty zulai ,  yanzu bancin ina daku bansan yadda rayuwata zata kasance dani  a gidan nan ba  ,kune gatana maganin kukana,  kun taimaka ta kowani hanya na tarwatsa rayuwar wannan annamimiyar yarinyar  , na rabata da mah'ruf bari na har abada  ,ta sake matsowa kusa da hajiya rahma yayarmu dan  Allah  sauran ayi masa  aikin da zai manta da ita arayuwarsa dan da alamun fa yana sonta dayawa  ,kinga mutumin nan daya bamu  sirrin zubar da cikin nan dole mu sake riƙe shi hannu biyu biyu zan  koma masa yayi min aikin da zan mallake mah'ruf  gabadaya na rabashi da kowa nashi muyi rayuwa daga ni sai shi .

"karki damu ko bai miki aikin da kika mallakeshi ba, shi din naki ne  har abada saboda babu wata mace da zataji dadin rayuwar aure dashi  bayan ke,  kinfi karfin ki  zauna da kishiya,  dole ne kowace iri kishiya ce ta fita ta bar miki gidanki  ko babu asiri akwai sharri iri iri   da makircin  da zamu gama da rayuwar kishiya   .....

Suka sa dariya "ni babu abinda ya bani dariya ya wanke min zuciya kamar yadda ya haukace saboda ganin hafiz a video ke Kinga hauka kamar ya kamasu tare wannan da kamasu tare yayi sai ya haukace shi kuma hafiz wawa kai dan giya bai yi ba wallahi "ai tunanin iska garesu shi a tunaninsa taimaka masa akayi ba sai amfani mukayi dashi ba wawa huhulahu kawai inji cewar zulaihat "bar shege mu ina ruwanmu tunda kwaliya ta biya kudin sabulo komai mah'ruf din zai masa can ta matsesu idan ma yayi kuskuren dawo daita gidan nan wallahi da kato zai iskesu tare a saman ruwancinki "aiko da mutuwa zai yi wannan mai shegen kishin tsiya bare ma bazata dawo ba Kinga yadda na dinga masa rarrashin munafurci ina bashi hakuri yana nuna sam ya gama zama daita suhaima ta karasa maganar ta kamo hannun hajiya rahma .

"Yayyarmu kinsan wani abu ?
Hajiya rahma ta girgiza mata kai "sai kin faɗa ," dangin mah'ruf fa sun fara tsarguwa dani dan dazu da naje gidan ita wacan yar iskan aunty magangagu ta dinga zuba min  kamar wata sabon shigar hauka "gud barta a mahaukaciyar dan babu abinda zata iya  mun rigada mun sha gaban  kowa dan ma shi dan iskan mijin   naki aiki baya shigarsa da sun ga kudi sunce kashi ne ...

Daga zulaihat har Hajiya rahma surawa suhaima ido  sukayi  saboda  ganin yadda  ta ɗauke wuta  lokaci daya jikinta ya kama  rawa a tare sukayi saurin juyowa bayansu  mah'ruf suka gani tsaye yana duban suhaima fuskarsa babu yabo babu fallasa , Gabadaya  jikinsu  ya kama rawa  ..

" TWO FRIENDS BSBS
💗💗💗💗💗💗
     WANNAN CE
   QADDARARMU
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL
            
      
AL'QALUMAN

*AYSHA  A BAGUDO*           
*FAIZA  HAMMADU*

~DEDICATED TO~
*MAR'ADAM  UWAR GIDAN  ABDUL , ALLAH YA  KARA DAMKON QAUNA  YA RAYA MANA UMAR FAROK, KHADEEJA,  MUHAMMAD DA ABUBU SARKIN RIGIMA*

SUBSCRIBE TO  MY YOUTUBE CHANNEL
*HAUSA BAKWAI*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

PAGE 69

.. Gabad'aya  jikinsu  ya kama   rawa  da ganinsa kallo ɗaya zaka musu ka tabbatar da tsantsar rashin gaskiyar dake tare dasu , a  natse    ya k'araso tsakiyar  parloun  ya tsaya kikam kamar wani jami'in tsaro   yana  binsu    da  wani  mugun kallo, take hantar cikinsu ya soma  kad'awa,
wani irin bugawa zuciyarsu ke yi da matsanancin karfi , lokaci daya hankalinsu yayi masefar tashi,  jikinsu ne ya cigaba da rawa, gabadaya sun rigada sun sadaukarwa kansu ya gama jin maganganunsu, cikin zuciyarsu babu abinda suke sai Allah wadai da kaifin harshensu ,"me yasa basu shiga dakin suhaima sun kulle kansu a ciki  dan  gujewa ɓacin rana   ?

  Ganin   yadda yanayinsu ya sauya  da  ganinsa yasa ya ɗan saki murmushin karfin hali akan  fuskarsa   tare da gyara tsayuwarsa  still  idanunshi na kansu ya kasa ɗaukesu daga  kallonsu , muryarsa a raunane yace   "sannu ku a she kune a gidan? ya faɗa yana tsaresu da manya idanunshi masu matukar firgitawa .

"Uhmmmmmmm ammmmm mu  ne     yanzu ma muke shirin  wucewa  "ok  ya  jikin hajiyar ?   "naunauyen  ajiyar  zuciya suka  sauke da karfi , a tare  suka hada baki   "ai ..ai taji sauki  sosai  ,Cikin yanayi na jarumta hajiya rahma ta cigaba da magana "a she Kuma abinda ya faru kenan ?  "Na   me kenan? yayi mata tambayar ido cikin ido yana Kallonta , wani irin buguwa zuciyarta  tayi da matsanancin karfi hankalinta yayi bala'in tashi  da jin irin amsar da ya bata ,  da kyar ta sake bude bakinta cike da tsoro da fargaba   "na yarinyar nan ummita  mana ,wallahi na tausaya  mata matuka, ka ƙara  hakuri  dan Allah, kasan  zama damu  sai ana hakuri  sannan kayi  bincike akai  ko dan darajar dangantar dake tsakaninku kar azo zumunci yayi rauni ....

" ai an wuce wannan gurin  ,bincike kuma ana kanyi  dan sai naga karshen wanda yake da sa hannu a cikin lamarin gidana  ya karasa maganar yana dan lumshe ido tare da kallon suhaima   "  ya akayi  ne naga  duk  kinyi  wani rikice kamar mara gaskiya   ko akwai damuwa  ne ?ta mike da sauri tana waskewa   jikinta na  rawa ta isa  gurinsa ta tsaya  kusa dashi zuciyarta na harbawa da sauri sauri  " babu komai habibi  da ciwon kai na shigo  gidan shiyasa ka ganni wani iri   sannu da zuwa  ai na ɗauka sai zuwa dare  zaka dawo ? tayi maganar tana amsar  jakar  hannunsa bai ce daita uffan ba ya sakar mata   ya  raba ta gefenta ya nufi hanyar d'akinsa zuciyarsa na kuna da tuttukin bakincikin , ta biyo bayansa  da sauri tana addu'ar Allah yasa bai ji tautaunawarsu ba .

ta ajiye jakar  a inda ya saba   ajiyewa sannan  ta  shiga bayi ta haɗa masa ruwan wanka  ta fito a  lokacin daya soma cire kayan jikinsa , ta tsaya  a bayansa ta soma ƙoƙarin   tayasa  cire kaya  bai hanata ba haka zalika bai ce mata uffan ba har ta gama   ya saura daga shi sai  boxer  da singlet  ta  miko masa farin  towel   "ka shiga   wankan  bari naje na sallami su yayarmu  na dawo  Kai kawai ya  gyada mata ya shige bayi  ita kuma  ta dawo inda suke  ...

Tsaye yayi a cikin baya yana kallon tafkeken madubin dake makale a jikin bango yana kallon   kyawawar surar jikinsa tunani ya shiga yi sosai akan abinda ke faruwa , wani irin zafi tsakiyar kanshi ke masa da  zuciyarsa , ya dauki cup ya tara ruwa yana tsiyayawa akashi ko zai dawo daidai , yayinda  kwakwaluwarsa ke  sake budewa  yana adana wasu  mahimman abubuwa a cikinsu, Kanshi ya dafe da hannunsa daya  saboda tsananin tashin hankali  ....

da sauri ta karaso inda suke zaune "yayyarmu me kika fahimta game da mah'ruf   kamar  ya jimu fa ?girgiza  kai Hajiya rahma tayi tana sauke wani wahalallen numfashi  kana taja hannuta" zo  mu shiga  dakinki  ban son irin haka suhaima  , suka nufi d'akinta suna shiga suhaima ta rufo kofar   dakin tana sakin labule ta fuskancesu" kina da gigicewa suhaima  bana tunanin  yaji maganarmu  wannan  mai shegen zuciyar tsiyar ai  da yaji  da dole   zamu  ga alama , ki saki jikinki karki bari ya fahimci   bamu  da gaskiya  " suhaimai ta sauke numfashi da kyar tace   bakiji yadda  qirjina   ke luguden  buguwa   ba  , Allah   ya  rufa min asiri  ,ya  dai rufa mana   daya  ji maganarmu  bansan abinda zai yi ba ta ina zamu fara ? ban san inda zamu boye acikin gidan nan ba inji cewar zulaihat   " bai ji  ba kuma bana addu'ar  ranar da zai ji da kunnuwansa ........

Gabadayansu suka yi shiru , hankalin hajiya rahma  a matukar tashe tace  "kusan wani abu ? suka girgiza mata kansu a tare da zuba mata idanunsu  "dole musan yadda zamuyi da hafiz  akan wannan matsalar kafin binciken mahruf ya hau kansa   "wannan  gaskiya ne yayarmu tsabar gigicewa ma   na manta maganar da yayi  a parlou'n  kamar cewa yayi ana bincike ko ? Inji cewar suhaima  "haka ya faɗa, wani irin abu suhaima taji ya caki zuciyarta tayi saurin dafe gurin gabanta na faduwa "yanzu ya zamuyi  yayyarmu tsoronsa ya sake  shigata   ? "Karki damu  babu abinda zai faru babu matsalar da zan bari ta kuno kai muddin ina numfashi a duniya zan yi komai  dan na kubutar damu gaba-daya , shiru sukayi gabadaya  suna Kallonta "ki kwantar da hankalinki hajiya rahma ta sake furtawa suhaima ....

"yayyarmu wallahi tsoro nake ji nasan halin mah'ruf bashi da kyau gurin rashin mutunci "oh my God  , suhaima ki fahimce  irin zafi da rad'ad'in da zamu ji idan wani abu  ya faru dake bana tunani mah'ruf yaji tautaunawarmu  ki natsu   zanji da komai zan sa a d'aukewa hafiz komai nashi ayi nisa dashi  na  tsawon shekaru   ta yadda idan a samu nasarar ganinsa bazai musu amfanin komai ba tana gama fadar haka ta kalli zulaihat  "Kinga tashi mu kama gabanmu sai wani jikon    .

A tare suka  fito  suna wa kansu dariyar rud'ewar da sukayi ,  tayi musu rakiya

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment