Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har zuwa haraban gidan sai data ga fitarsu sannan  ta dawo tana saisaita natsuwarta ,cike da natsuwa ta shiga dakinsa kai kace ba itace tantiriyar dake daukar darasin makirci ba , tana shiga ta hangosa zaune yana tunani  alamar yana cikin damuwa, ta samu guri ta zauna  kusa dashi tana dafa kafad'arsa yaki dagowa ya kalleta "dan Allah kayi hakuri komai zai wuce   ,amman kana ganin idan aka tsananta bincike baza'a sake binciko abinda zai d'aga maka hankali ba ? ya d'ago ya kalleta  da idanunshi da suka kada suka yi ja zuwa lokacin ,kwata kwata ya rasa abinda zai ce mata ,  ya mike tsaye yana kallon kanshi a madubin mirrow  "komai zai faru sai dai ya faru amman sai an  nemo wanda ke da saka hannu acikin lamarin nan, bai juyo ya kalleta ba duk da tana tsaye a bayansa gabad'aya tsoronta ya sake fito filli tasan halinsa maye ne akan abinda yasa gaba  tunda ya nace akan sai an binciko wanda ke da saka hannu tabbas tasan za'a nemo ya ja tsaki yana barin gurin ya karasa wordrobe  dinsa yana sauke wani wahalallen numfashi, jallabiya ya dauko baki  ya saka  ya dawo ya raba ta gefenta ya hau kan gado ya   kwanta  ya runtse idanunsa gam haɗe da  yin  pillow da hannunwansa  .

jikinta a matukar sanyaye ta matso kusa dashi tana kai hannunta kanshi  ",bacci bayan la'asar   ...? bana  son damuwa  ,Kwakwaluwata na bukatar hutu   ya kawar da kansa gefe yana furzar da iska mai zafi   ta mike tsam  idanunta na kanshi  kallon  second biyu tayi masa  sannan ta nufi kofar  fita daga dakin, ya bude idanunshi yana binta da kallo  tun daya shiga daki bai  fito ba sai goshin magariba yayi alwala ya fita zuwa matsalaci bashi ya dawo gidan  ba sai gurin tara  ..

Da daddare suna zaune a daning  table    suhaima ta  sha jini jikinta sosai   saboda  tsura mata  idon da mah'ruf  yayi  yana Kallonta  ta  d'ago kai ta kalleshi  gabanta na fad'uwa  , daga  ita har mah'ruf kallon juna suke   bai yi kokarin  sanyawa cikinsa komai ba ita kawai yake kallo ,itama babu wani  abincin  kirki da taci  sai  tsakura da take yi ,tana kallonsa   ya dauki cup  ya haɗa coffe  take ta narke fuska  " haba habibi   gani zaune  zaka hada coffe da kanka ni meye amfanina ? " karki  damu    ki cin abincinki kawai    ,yana gama sha ya mike ya  shige d'akinsa,   ta biyosa  duk jikinta a sanyaye hankalinta  a matukar tashe kwanciya tayi a bayansa zuciyar cike da matsanamcin tsoro ,shima baya ya juya mata yayi  shiru yana tunani gabad'aya bacci ya kauracewa idanunsu, tunaninta duk ya kare akan  son sanin abinda  ya sauya  shi  , tasan dai  yana cikin damuwar abinda ya faru amman ko da safe ai lafiya suka rabu kuma tasan daya ji tautaunawarsu da y'an'uwanta  ba zai  boye ba, dole  zai yi magana washegari  ya tashi da wuri ya shirya ya bar gidan ya bar   zuciyarta   da wasiwasi  .

Qarfe goma da minti goma sha biyar ummita ta farka  bakinta ɗauke da salati  ta tashi zaune tana  kallon dakin  motsinta  ya  tadda shi ya tashi  yana  gyara mata sumar kanta daya baje kallonsa tayi da mamaki a saman fuskarta  shima kallonta yayi haɗe da sakar mata kasalalliyar murmushi ya shafa gefen fuskarta zuwa wuyanta sannan ya matsota sosai yana busa mata iskan bakinsa "ya karfin jikin   ?

Lumshe idanunta tayi cikin sanyayyiyar muryarta tace "Better  tana ƙoƙarin ja da baya, lumshe idanuwansa yayi tare da jinjina kai ya sake  matsowa zuwa inda take  ya daura kanshi a saman cinyoyinta  mamakinsa yasa ta kasa magana
"lokaci zuwa lokaci yake rikidewa yana  canzawa   ,ta rasa dalilin canzawarsa ko dai ya gano  gaskiya   bata aikata laifin da yake zarginta  bane ?

  "Allah kasa gaskiya ta bayyana bata gama dogon tunaninta ba taji   ya riko  hannunta cikin nashi  yana kallon zara zaran  yatsun hannunta  kafin daga baya ya  fara  shafawa a hankali take tsigar  jikinta  suka mike yrrrrrrrrr , ta  tsura  masa idanunta tana kallonsa ya buɗe bakinsa ya zira fingers dinta  cikin bakinsa  ya hau tsotsa yana shafo  gashinta, kusan minti goma ya ɗauka  yana tsotsar fingers dinta sannan ya maida hannunsa yana shafo cikinta dake lafe yana kallonta cikin wani irin yanayi na galabaita ya bude bakinsa da kyar "nayi kuskure *QAUNA*  daga yanzu ba zaki sake fuskantar wata matsala a tare dani ba ,kimin uzuri ,ba kowani mutun   zai ga abinda na gani ya iya kawar da zuciyarsa ba, dole ne a matsayina na mijinki  naji   babu dadi araina  wallahi ina da tsananin kishi akanki ke kanki da zan yi shiru akan matsalar batare da na nuna fushina ba zaki ji babu dadi ,zaki ɗauka baki da matsayi a zuciyata ne  zama ki iya tunanin ko bana sonki  ....

"Ina sonki Ina son abinda zaki haifa min i love you with all my heart 
Zare hannunsa  tayi cikin nata  tana fesar da iska ta d'ago kanta a hankali  suka  hada ido  ya kashe mata idonsa daya ya tashi ya kai hannusa kan kafafunta  yana mammatsa  mata
yana faɗa mata kalamai masu sanyi  ...

"Ya sallama baba ba dai har yanzu kana  gidan nan ba  , maza ka tashi ka wuce aiki  ,"babu inda zani mama ki barni haka zuciyata na cike da matsanamcin tsoro da firgici  ya fadi haka yana ɗauke hannunsa  daga kan  kafafunta  sai lokacin  ta sauke wadataccen numfashi "ni dai  ka tashi ka wuce gida, ka wani zauna kamar  wani bawanta "barni kawai mama ai  sai mace ta cika mace sannan namiji zai zama bawanta ko karya ne qauna ?tayi shiru tana dan ciza lip's dinta ya kamo hannuta cikin nashi ya tsarke yana shafawa  "ni dai kaji abinda nace maka ka tashi ka tafi  aiki  ta faɗa a daidai lokacin da ummita ta zare hannunta ta   sauko daga kan gado ta shiga bayi mama ta biyo bayanta, ya zauna shiru yana tunanin  .

Ruwan zafi mama ta haɗa mata ta zaunar daita  runtse idanunta tayi saboda zafin daya ratsata sai data tabbatar  ruwan zafin ya shigeta sosai sannan ta bata umarnin tashi ta sake hada mata wani ruwan zafi tayi wanka  "mama ......
Ummita  ta kira sunanta "ya'akayi mamana ?" jini  ya tsaya  fa tun jiya  ,mama tayi shiru taki cewa komai  dan kusan tafi su jin zafin fitar cikin  ,ummita  ta fito daure  da towel a tunaninta mah'ruf ya tafi  sai ganinshi tayi zaune ya mike ya  tarota ya rungumota  jikinsa yana mata sannu  ta matsa baya  da  sauri  saboda jin motsin fitowar mama  ,mama ta wucesu tana cewa  "sai ka haɗa mata tea tunda bazaka wuce  ba , tana  fita ya d'auketa ya maidata  kan gado   bayan ya dauko mata kaya ta canza ya fita  ya  hado mata  tea mai kauri  da zafi   ya  dawo dakin yana shigowa ya k'araso inda take kwance ya dagota da kyar ta yarda ya bata ta sha tana hararasa  "karki  damu duk zan wanke laifina ta hanyar dawowa bawanki , rabin cup ta sha ta kawar da bakinta , ya janyo  laidar magungunanta ya bude ya ciro ya balla ya bata  ta sha kwanciya tayi shima ya kwanta  ya janyota  jikinshi ta tashi da sauri  ta zauna tana dubansa  tana yatsina fuska "ka tashi ka tafi aiki mana  tayi maganar cike da shagwa'ba .

ya kai hannusa ya janyota ya mannata a qirjinshi  yana kyakwayon maganarta "karki damu kasancewata dake   yafi zuwana   aikin mahimmanci ,ya soma ƙoƙarin lullu'besu "muyi bacci  qauna "nifa ba bacci  zanyi ba na gaji da bacci  "to mu kwanta muji dumin  juna "gaskiya a'a ban yarda ba ka tashi ka wuce kawai  "ba zani ba  ko dole sai  na tafi aiki ?jikin ummita a sanyaye ta sauko zuciyarta na bugawa da karfi ya   fizgota ya matseta gam  ajikinsa ya kai bakinsa cikin kunneta  "banason abinda kike min  ,ya  buɗe bakinsa da niyyar sake magana aka bude kofar  dakin atare suka kallo kofar d'akin aunty ce tsaye "inna lillahi baba meye haka ?ya lumshe mata idanunshi ke kuma shine kika wani manne masa yar dadi son miji shi yasa nan da nan kin ɗauki ciki  maza  tashi ka fita "haba aunty kinsan fa bama haka dake "mu fara daga yau amman wallahi sai ka tashi ka fita , dole ya sauko ba dan ya so ba sai dan  aunty ta rantae , tasa keyarsa tayi  gaba har sai daya  ya fita ya bar gidan

Daren ranar daga mama har Hajiya umma  babu wacce ta runtsa  suna zaune suna kaiwa Allah kukansu , hatta Abba shima   ba'a barshi a baya ba yana tsaye  akan daddumar sallah bayan ya idar ya d'aga hannunwansa sama "ya Allah ka karemin yarana ka tsare minsu   ,ya Allah  kada kasa wani mugun ya cutar min dasu Allah kaga halin da diyata subai'a take ciki Allah kafimu sanin komai ,  Allah  ka gaugauta bayyana gaskiya Allah ka bawa mahaifiyata lafiya da sauran marasa lafiya waɗan da suka rigamu gidan gaskiya Allah ka jikansu ya shafa ya cigaba da lazimi .....

******
Bincike ake sosai sai dai har lokacin babu wani cigaba da'aka samu ta  bangaren wanda yake da sa hannu , mah'ruf da mahaifin  hafiz da kanin mahaifinsa  zaune a office din  dpo  ,shiru suna  kallon hafiz wanda zuwa lokacin kumburin idanunshi ya sabe  yana iya gane kowa ,hakuri kanin  mahaifin hafiz  yake bawa mah'ruf "yaro kayi hakuri mun san d'anmu yayi ganganci da kuskure shiga gidanka , ina tabbatar maka  a halin yanzu daya yasan inda  matar data sashi wannan danyen aiki   daya dade da  bayyanata   shi kansa ya huta ,ta bangaremu  muma muna    kokarin muga an kama ko wacece  dan tayi amfani da girman son da yakewa yarinyar ne tayi amfani dashi ,dan Allah kayi hakuri   bama  son maganar ta je kotu  ka taimaka  shi kadai Allah ya bamu  ....

mahruf ya sauke numfashi yana furzar da iska mai zafi sannan ya ciro wayarsa daga gaban aljihunsa  ya shiga gallary dinsa ya dubo wani  hoto  ya mikawa hafiz wayar  hannun hafiz na rawa ya amsa yana dubawa "wannan matar ce  tasaka aiki ?shiru  hafiz yayi yana kallon hoton kwakwaluwarsa  na caji gurin tunani "ba ita bace amman tabbas suna matukar kama da matar data sakashi aiki  yayi magana a zuciyarsa "kayi shiru mahruf yayi magana a tsanake  "itace wacce ta sakaki aikin ya sake tambayarsa a karo na biyu ? girgiza kansa yayi  ,cike da matsanancin faduwar gaba ya shiga motsa bakinsa yana son yin magana akan cewar suna kama da matar amman ya kasa lankwasa  harshensa, kawai sai  hawaye sharrrrrrr  suka shiga gangaro masa ,wanda take mahaifinsa ya shiga goge nashi hawaye idanunshi na kan  tilon dansa , tausayin mahaifin hafiz ya kama mahruf  sai dai duk da haka bazai daga kafa ba .
ya dubi hafiz sosai  sannan ya kalli dpo  "a  cigaba da rike shi har sanda zai  dawo hankalinsa ya gane waɗan da suka sakashi aikin yana gama fadar haka ya mike ya kama gabansa   yana mamakin abinda yasa  hafiz ya kasa fadar gaskiya , mahaifin hafiz ya shiga tashin hankali matuka ya dinga turowa mah'ruf manya mutane dabam dabam  domin bashi hakuri a kashe case din   ,shi kuwa mah'ruf ya rantse sai hafiz yayi magana da bakinsa ,yayinda  harshen hafiz  ya rikice duk sanda za'a zo akan maganar sai kuka da karyar da  kai gabadaya an rasa gane kansa har police suka fara tunanin ko  ya samu tabin hankali ne   batare da bata lokaci ba aka nufi asibiti dashi  iya bincike anyi sai dai  likitoci sun tabbatar da lafiyar kwakwaluwarsa lau , cikin kwanaki sam mah'ruf bai samu zama ba gida da office ,kullum yana gurin ma'aikata  gabadaya suhaima ta rasa gane  kanshi yana tsaye a dakinsa yana duba wasu mahiman bayanai ta shigo sad'af sad'af bai ji motsin shigowarta ba sai tsayuwarta a bayansa yaji da hucin numfashinta , ya ɗan juyo ya kalleta ya ɗauke kanshi  ya cigaba da duba file din hannunsa "habibi ta kira sunansa a raunane , ya juyo gabad'aya yana  fuskantartata  batare daya amsa ba ,sai dai ta fahimci ita yake sauraro ",gaba-daya ka canza habibi tunda ummita ta bar gidan na rasa fahimtarka ka kaurace min a shimfida ka daina cin abincina ka daina duk wata muamula dani ka  taimakawa zuciyar dake  tsananin sonka , ina tsananin sonka  da bukatar kulawarka ..

"nasan kina sona kuma zaki iya yin komai akaina  ko ba haka ba ? yayi maganar yana  ajiye file din hannunsa ya dauki wani "haka ne  zan iya yin komai akanka kamar yadda  nasan  kai ma zaka iya komai akaina jin abinda ta faɗa yasa ya zauna yana ci-gaba da aikinsa , ta zauna kusa dashi  "ina ji ajikina kamar nayi maka laifi    ya juyo  inda take zaune  tare da  tsura mata idanunshi  sai da yayi  second biyu sannan yace "idan kin min laifi zan fada miki idan kuma har jikinki na baki kin min laifi   a tafi haka  ya karasa maganar yana furzar da iska mai zafi a  fuskarta haɗe da mikewa tsaye  ,itama ta mike da sauri ta tsaya gabansa  "ya tabbata dai nayi maka laifi  dan Allah ka faɗa min  abinda nayi  maka dan gaba na kiyaye ?  "matsa na wuce ina da abubuwan  yi .......

idanunta ta lumshe batare da ta sake furta masa  komai ba ta  matsa gefe guda tana kallonsa zuciyarta cike da  mamaki a natse  ya wuce ta gefenta  yana rabe   jikinsa dan baya son abinda zai sake  haɗa gangar jikinsu,  shiru tayi kafin daga baya ta fito cikin sauri ta nufi d'akinta ta kira number hajiya rahma tana ɗauka ta fashe mata da kuka tana koro mata yadda sukayi da mah'ruf "kina da matsala wallahi mutun bai fito ya nuna miki komai ba  ke meye naki na damuwa? "ina da tabbacin da yasan shirinmu da tuni ya fahimtar damu ki kwantar da hankalinki yanzu haka  ana  aikin ne akan  hafiz dan na samu labarin an kama shi yana hannu ma'aikata  sai dai  ina tabbatar miki babu abinda zai faru  karshe akai  maganar kotu, rashin kwararan   hujoji da sheidu  zai sa case din ya mutu murus kinga munyi win gobe ya sake biyewa soyayya,  ke  kuma yadda bai faɗa  miki komai ba ki rabu da dan iska   ki share shege ki cigaba da rayuwarki ko zaki kashe kanki akansa ne kiyi mana hasara  ?   bari na faɗa da hauka ake maganin hauka  sharesa tunda shi asiri bai aiki ajikinsa kissa ma ko anyi masa bai san ayi ba move up ur life joooo  nan Hajiya rahma  tashiga  kwantar  mata da hankali  har ta dawo daidai suka cigaba da  tautaubawa ..

tun daga nesa  mah'ruf ya hango daya daga cikin police din dake  case din hafiz   gurin mai gadin gidansa a hankali yake takowa    inda suke zaune  daga  yake  yana iya jiyo  sautin police  yana magana da mai gadi   "malam kamilu oga Umar  ya kira sunansa   "naam ranka ya dade barka da  yamma ?  "ya kake malam  kamilu ya aiki? " lafiya  ranka ya dade "sunana  s p  Umar kamar yadda kagani a rubuce  nazo domin tautauna  wani  abu mai mahimmanci ne da kai "inshallahu baka da matsala dani muddin nasani zan fadi gaskiya ," ko zan iya sani dalilin da yasa kake barin mutane dabam dabam suke shigo  gidan nan  ? tambayar ta daure masa kai cike da mamaki yace "mutane dabam dabam ranka ya dade gaskiya babu mutanen dake shigo wala mace wala namiji idan har kuma suna shigowa  sai dai idan  shigo dasu ake "wa kake tunani yake shigo dasu ?"eh to akwai wata mota dake zuwa gidan nan yayyar matar mai gidan ce
amman asanina babu masu shigowa barin ma wancan bangaren babu masu zuwa gurinta  ya nuna part din ummita "kuma  babu mai  aikenka  siyan wani abu acikin matan gidan  ?  "gaskiya babu  wacce ta  taɓa aikena tunda tazo gidan nan aikina iya get ne kuma bana wuce haka "shinkena na gode ya mike a daidai lokacin da mah'ruf ya karaso ya mikawa oga umar hannu suka fita zuwa wajen gidan suna magana kasa kasa har suka isa gaban motarsa oga umar suka  shiga tare suka bar unguwar daga station Kai tsaye massalaci  ya nufa bayan sallar isha'i ya shiga part din mama domin ganin abar kaunarsa ya murd'a kofar d'akinta yajita a kulle gam  ya kwankwasa , daga cikin daki tace waye ..?"ki bude Ni ne "me zan maka dan Allah bana son damuwa  ta faɗa tana gyara kwancinyarta shiru yayi  yana kallon kofar ya lura duk zuwan da yake bata wani sakewa dashi , shima ya saki ranshi   me yasa bazata sauko ba su cigaba da rayuwarsu  ?

Mama na zaune a gefen abba yana cin abinci a parlou'nsa  yayinda bangare guda yana sauraronta cikin gamsuwa da irin binciken da'ake yi "bazan yarda ummita ta koma gidan baba ba  sai an gama bincike an gano gaskiya shine nake bukatar ka bani goyon baya duk da shi kansa baba bai nuna damuwarsa akan ta koma  ba "wannan shawara ce mai kyau dan nima abinda yake raina kenan sallamar da yayi ta dakatar dasu a tare suka maida idanunsu akanshi cike da girmamawa ya karaso ya zauna agabansu ya lankwashe kafafunsa Abba yace ",ya akayi babana da magana ne ? "Abba ina tunani  jibi zanyi tafiya zuwa Cross river Ina da meeting   zuwa wenesday zan dawo  nasan  lokacin  yansanda sun gama bincike  zan so ayi komai ina nan  "Masha Allah Allah yayi rayuwa albarka kular gabansa ya tura masa "kaci abinci  duk ka rame da alamun baka cin abinci " kar ya  soma ci  idan yaci yayi yaya dana matarsa? mah'ruf  bai d'ago ya kalli mama ba ya soma cin abinci "ban fa yarda kaci ba  sai lokacin ya d'ago ya kalleta yana karyar da kai  "rabu daita  kaji yarona kaci daga abincin da abbanka yaci ya rage "ni dai babu ruwana idan yaci kasan yadda zai dana matarsa "dan Allah mama ki daina fadar haka sai naga kamar kina fushi dani ne ..  ....

  sai gurin goma ya koma gida a kwance ya tarar daita tana kallo sallamarsa tasanyata mikewa da sauri ta mike ya wuceta  ya shige daki yana shiga ya soma haɗa kayansa a karamar jakar matafiya  ta shigo tana kallonsa  ",me kake yi haka habibi?" ina zaka kake shirya kaya  ?"tafiya zanyi ko akwai damuwa ne ?"tafiya zakayi shine bazaka faɗa min ba sai kawai naga kana hada kaya ?" haka abun yazo , ta kai hannu zata tayashi ya dakarta daita yana cigaba da shirinsa ya gama ya zuge  zip  yayi kwancinyarsa "na kawo maka abinci ?"no ya faɗa atakaice ta juya jikin a sanyaye ta shiga jan kafa tana tunanin abinda tayi masa washegari jirgin karfe  shida yabi zuwa Cross rive yayinda suhaima  ta tashi tun bakwai ta haɗa masa break duk da tasan ba zai ci ba sai dai tana murda handle din kofarsa taji gam a kulle ta juyo zuwa d'akinta  can tayi tunanin zuwa gurin Hajiya rahma ta faɗa wanka ta Sharya  cikin riga da siket ta nufi gidan Hajiya rahma hankalinta ya tashe da gani suhaima  a daidai lokacin ta karaso gurinta "lafiya nagaki adaidai wannan lokacin ..?

"Lafiyar nan dai  da sauki gabadaya komai ya kwa'be min mah'ruf ya canza min gashi na rasa dalili  yanzu ma tafiya yayi kika gani ", wannan miji naki akwai dan tusa gashi aiki baya cin irinsu bare ace asan abun yi "mu ajiye maganarsa mai sauki ne , ya ake ciki da wacan matar tasa ya sake ko kuwa suna tare har yanzu  ? "Suna tare wallahi ni abun ma ya fara damuna  ya isheni "matsalarki  Kenan  ke komai sai an koya miki kamar ba mace ba , zaman me kike yi  kije gidansu  ki daga mata hankali  ta yadda da  kanta zata bukaci saki daga hannunsa,  kina nan zaune sake da baki  yana zuwa yana rage zafi daita "uhm  maganarki gsky yayarmu  matsalata kenan   ummita  muddin tana duniya bani ba farinciki ,"  bari naje gidan yanzu  ta mike   ta nufi gidansu taci Sa'ar mama bana  part din  tana bangaren Hajiya inna bata abinci da magani ,kai tsaye ta nufi dakin ummita tana zaune  ganin suhaima  akanta yasa tayi wata irin zabura ta mike,"meye haka zaki shigowa mutane daki babu sallama kamar  wata arniya ?
wata  mahaukaciya dariya ta tayi  tana nuna ta " ki ajiyeni  a ko'ina kike so  zan zauna muddin zan ga rayuwarki cikin kunci ,zaman gidan dole  ina tabbatar miki sai dai ki tabbata a wannan daki ba dai a gidan mahruf ba  "sannu mayya  diyar mayu mai mugun hali ta Allah ba taki ba kina tunanin duk abinda kike ban sani ba ? "nasani  na san komai da kike yi akan cikina sai da sannu Allah zai min magani   ..

"Abinda kika sani ne zan sake tuna miki yanzu  ni suhaima nice nan na turoki daga sama bene  kika gangaro kika kifa  saman cikin na farko kikayi nagudar dole   saboda tsananin kiyayyar da nake miki "nasani sai dai meye ribaki a yanzu  ? baki ma ji kunya ba  har kina iya faɗa da bakinki saboda jahilci  wallahi  kina cikin bala'i da fushin Ubangiji   ina tausayawa rayuwarki saboda karshenki bazai kyau ba ,ina guje miki tsincetsince a bola kafin mutuwarki ........

"Enough   kice zaki yi tsince tsince a bola bani ba kuma nice  nan da kaina  zan tabbatar da haka tabbas zan baki mamaki ina tsaye akanki da kuma taimakon yan'uwana, ummita tayi shiru tana  dubanta cike da mamaki "oh kina mamaki ne ? "Ki daina mamaki saboda yanzu aka soma wasan dan  banyi komai ba tukun  tunda har yanzu ban haukataki ba ban rabaki da gidan mah'ruf ba , ina faɗa miki ne saboda babu abinda zaki iya yi, kuma muddin baki fita rayuwar mijina ba rayuwarki zata dawo abar tausayi na dade ina faɗa miki ki bar rayuwar mahruf na baki dama kin kasa fahimta, ki saurareni da kyau idan zaki yi dauki cikinsa sau dari ni nan suhaima zan zubar dashi sau dari kuma na zauna lafiya  idan kin gwamaci karasa rayuwarki cikin kunci da bala'in rayuwa ki cigaba da rayuwa da abinda nafi so a duniya , Ina boye miki ko wacece ni sai naga boyewar bashi da wani amfani gara kisan ko ni din wacece ki san cewa gaba da gabanta ba'a kishi da irinmu kishi da zuriyarmu tashin hankali ne  maseefa ce duk abinda zan miki babu wani mahaluki a duniya da zai sani ko zai yarda  ,gani damana ne na bari mutane su sani sannan ganin damana ne na rufe musu baki ruf  su gagara sanin ta karasa maganar tana  rufe hannuta guri daya...

" wani irin kallo ummita ke mata mai tattare da tsananin  tsoro da firgici mutun kamar aljana "kina son cigaba da sanin abubuwa akaina  ? Tayi mata tambayar tana zagayeta hatta ciwon hajiya inna nice nan silar komai duk da mahaifiyarki na so ta dawo abar tausayi  ba wannan rikitacciyar tsohuwar mai bala'in tsiya  ba ,kina son sani wani abu bayan shi ?tayi mata tambayar tana  dariyar mugunta "ina da abubuwa da zanyi na ruguza rayuwarki da rayuwar mahaifiyarki take jikin ummita ya kama rawa jin ta ambaci mahaifiyarta, zan iya komai kuma a lokacin dana so dan haka kiyi hanzarin fita rayuwata da mijina duniyata , kema sautsayi ne  aurenki, dan dani mah'ruf ya fara aure da duk runtsi da maseefa da jaraba ta iyayenku basu isa su aura masa ke ba , akan mah'ruf  zan iya dauka ran kowa ina da kwakwaluwar shirya komai koda babu wata a kasa ki gaugauta fita rayuwarsa idan ba haka ba zan kashe mahaifiyarki a banza  kuma akan idanunki .......

Tass kake ji ummita ta dauketa da wani gigitaccen mari,"kika mareni ta faɗa a gigice ? "an mareki  ta d'aga hannu zata rama ummita tayi saurin rike mata tana kallon tsakiyar idanunta kafin daga ba ta saki hannun da karfi ta soma magana a fusace   "suhaima ki tsaya iya kaina dan mahaifiyata tafi karfinki , dan da adduarta kika kasa cin galaba akanmu  idan kika sake wani furuci akan mahaifiyata zan kasheki kafin ki kasheni  ke ko ciwon kai tayi wallahi zaki sha mamakin yadda zanyi da rayuwarki zan so ki sausautawa zuciyarki ki daina wannan haukan banza dan zuciyar mah'ruf tawace mah'ruf baya sonki kin dai

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment