Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaba da zan faɗa ka sani ba wai zuwan kaina nayi d'akinka ba aikoni mama tayi kuma ga sheida nan idanunka sun gane maka , ka daina tunanin ummita zata nemi kusanci da kai dan har abada ummita bazata yi zuwan kanta ba ,nasan zuwa yanzu kasan dalilin zuwana ,tun taso wata ni nan ban san me ake kira la'be ba ,sai dai naji labari abakin mutane bare na rasa wanda zan wa sai kai ,ni nan nafi karfin nayi maka la'be .....

"Yi min shiru stupid fat lion..... ni zaki haɗa da bakin jaki ?

"An haɗaka da bakin jaki me zaka yi ?"ai sanin haka ne kawai baka yi ba amman kafi kama dashi kamarku ɗaya tamkar an tsaga ƙara..

Shiru yayi kawai yana facing dinta yana kallon yadda take motsa bakinta cike da bakin ciki mara misaltuwa yayinda tsanarta ke sake qaruwa a cikin zuciyarsa tare da bin kowane part na jikinsa tsawon minti biyu yana kallonta ya rasa takamaimain abinda zai ce mata ....

Murmushin yake tayi wanda yafi kuka ciwo ," ashe dai babu dadi ?
"A she haɗa mutun da dabba babu dadi ,a she hakan na saka zuciya jin wani irin har ta nemi tarwatsewa ,amman kai kake takarkarewa ka dinga kiran mutane da fat lion ,tare da muna nan kalamai iri iri.........
"Kasani daga yau na kashe wannan sunan daga bakinka , karka qara kirana dashi idan kuma baka daina ba zan .......

Wata muguwar tsawa ya buga mata take tayi shiru da bakinta ta ƙasa qarasa maganarta zuciyarta na harbawa da sauri, cike da ɓacin rai yace "dan ubanki me zaki iya yi idan ban daina ba?
Ta zumburo masa baki tana tunanin abinda zata faɗa masa mai zafi ,da zai 'bata masa rai ,shi kuwa tsareta yayi da sexy eye's din shi kafin daga baya yace "ba zaki wuce bane ko kuwa sai naci ubanki a yanzu , idan kuma kika sake furta wata magana mara daɗi anan sai na miki azaba mai rad'ad'i ....
sai na miki jina jina wawiya kawai mai fuskar samudawa ...

Wani murmushin takaicin ta sake yi sannan tace "uhnmmm sannu mama da Abba ,kana bani umarni kamar ka haifeni ,okey kayi sauri kayi min jina jina ina jiranka ?
"Allah yaya ma'aruf ka kama kanka dani dan abubuwan ka sun fara damuna ,ka mutunta sauran girmanka ,kafin na maka abinda ba kayi tunani ba, koda yake ai ba girma a tare da kai bare....
cikin zafin rai yace "dan ubanki ni kike fad'awa wannan magana ?

laulausar tafin hannunsa ya kai daidai gefen wuyanta zai fixgota da karfi da niyyar ingizata waje ya huta da kallon fuskarta .....
hankalinta ta soma ƙoƙarin kwatar wuyanta daga garesa saboda wani azaɓaɓɓen zafin da taji ya ratsata ,ta fizge wuyanta da kyar ta juya da sauri.. ya sake riko hannuta cikin nashi , ta juyo a matukar firgice ai ko ta faɗa saman qirjishi batare data shiryawa hakan ba ,yayi baya zai fad'i cike da tsoro tasa hannuwanta duka ta riko shi sosai a jikinta , suka haɗe guri ɗaya sannan suka yi luuuuuuuu suka faɗa kan kujera mai zaman mutun uku dake parlour'n, hancinta ya sauka a daidai inda yafi jin kamshi turare a qirjinsa, shi kuma fuskarsa ta haɗe da qirjinta a matukar firgice suka d'ago idanunsu ya kalleta itama ta kalleshi atare suka zaro idanuwansu....
take kuma zuciyoyinsu ya dokawa da matsanancin karfin gaske ,Kusan sumewa ta so yi agurin yayinda shi kuma ya bita da wani wahalallen kallo aranta tace " wayyohlly Allah yau na shiga uku ... gaba-daya ta kasa motsi ajikinsa duk ta rikice sakamakon sansar jikinta dake budewa, wani irin yanayi ta tsinci kanta wanda bata taɓa jin makamancin sa ba ...
so take ta mike daga jikinsa amman hannuwansa duka dake zagaye da qugunta yasa ta ƙasa mikewa ta ɗan motsa dan ya sakar mata jiki amman yaki ,illa wani kallo daya dinga binta dashi wanda bata san ko na menene ba.. aiko take idanunta suka cicciko da ruwan hawaye ganinta kwance ajikinsa sun tsurawa juna ido,'bangaresa kuwa wani irin takaici ke tattare dashi na ganin yanayin da suka kasance wanda yafi komai ciwo a rayuwarsa, ransa idan yayi dubu to a matukar 'bace yake......
Ahankalin ya ci gaba da Kallonta da mamaki a saman fuskarsa ummita kuwa kallon yanayinta kawai zaka ka gane kalar tashin da take ciki, Kallonta yake yana jin zafi acikin zuciyarsa da gangar jikinsa Ahankali suka dinga fidda ajiyar zuciya ..


Mama taji shiru har goma ta kusan bugawa bata ga ummita ta dawo ba dan haka ta kira number ma'aruf wayar tana ringing amman ba'a ɗauka ba ,duk ta damu saboda tasan ƙarshenta tayi masa halin nata ne ,shi kuma babu hakuri ya tsareta a d'akinsa .....

kusan minti goma suka ɗauka a haka sannan ta kai hannuta daidai saitin qirjinshi da niyyar mikewa ya buga mata tsawa "if you touch me I will finish you ,zan miki dukan mutuwa idan hannunki ya taɓa qirjina ...
tsawar daya buga mata ne yasa gaba-daya ta sake daburcewa ta rud'e ganin yadda yake Kallonta a kaskance, muryarta na rawa tace" ka... ka sakar min jiki to....
sai lokacin ya lura da hannunsa dake daidai kugunta , runtse idanunsa yayi ,zuciyar na wani irin harbawa da zafi, ahankali ya ware duka hannuwansa alamun ta tashi, jikinsa har rawa yake saboda bakin ciki kasancewarsu tare , ai ko yana gama ware hannuwansa ta mike da sauri ta bar d'akin tana haki .


Cikin sauri ta shiga Bangarensu tayi hanyar dakinta ta faɗa saman gadonta tana runtse idanunta tare da kudundine jikinta gurin ɗaya dake wani irin kyarma....
tsigar jikinta kuwa ban da mikewa babu abinda yake, duk inda ta motsa tsigar jikinta yrrrrrrrrrrrrr take jinta ta makure sosai tana fidda numfashi sama sama "Allah kayi min tsare da yaya ma'aruf , duk sharrin da yake bina dashi Allah ka mayarsa ,wata zuciyar tace "dan'uwanki ne fa ....,?
"Kai wannan baya daga cikin ahlinmu ,ni ina ganin shi ba ma d'an umma bane ,an canza mata shi a asibiti dan gaba-daya halinsu ya bambamta da nata mama ga kirki sanin Yakamata da mutumtaka .

Bata ji motsin shigowar mama ba sai jin sautin muryarta tayi akanta " ke me ya zaunar dake daga kai abinci ?
Ummita ta bude idanunta da kyar batare da tace mata komai "kina jin mutane suna magana amman kinyi shiru?
" me ke mun ki naganki haka ?
Ummita dake kwance tana fidda numfashi sama sama sakamako tafin hannun ma'aruf dake kai kawo ajikinta , muryarta a sanyaye tace " babu komai mama .
"Babu komai shine zaki zo ki takure kanki ? Ummita ta kad'a wa mama kai "to ai shikenan Allah ya yaye miki idan ma wani abu ne ke damunki .."


Shi kuwa ma'aruf kasa zama yayi a d'aki saboda wani bakon al'amari daya tsinci kanshi ciki mai wuyar misaltuwa ,shi bama zai ce ga abinda ke damun zuciyarsa da ga gangar jikisa ba ,haka nan ya dinga ji zafi acikin ranshi , zuciyarsa na quna tamkar ana tsomata cikin wuta , zumbur ya mike ya fito wajen gidan yana shawagi da tunani iri iri , dafa kafadarshi yaji anyi ta baya, ya juyo idanunsa a fusace da niyyar yiwa wanda ya dafa shi maseefa,karaf idanunsa ya sauka akan Yusuf makwafcinsu kuma abokinsa dan tare suka taso, sukayi karatu, jami'a ce kawai ta raba tsakaninsu, kowa ya tafi jami'ar da yake so ..

hannu Yusuf ya miko masa suka gaisa "dama ashe Kai ne tsaye a nan na ɗauka rayhan ne ?
Yusuf yayi magana fuskarsa cike da fara'a " "eh wallahi ..
ma'aruf ya faɗa yana furzar da iska ta bakinsa mai zafi " ya kake ka dawo lafiya?

" alhamdu lillah ya faɗa atakaice ,"me ke faruwa da kai ne haka duk sai naga kayi wani sukusuku kamar wani mara lafiya ?
Yusuf ya faɗa tare da gyara tsayuwarsa yana fuskantar shi sosai , ma'aruf ya dubi kanshi sama da kasa sannan ya sauke ajiyar naunauyen zuciya ya maida idanunshi ga Yusuf dake tsaye a gabansa ya ɗan ciza lip's d'insa " babu abinda ke damuna ya faɗa atakaice dan ya soma gajiya da Yusuf har sai da ya sanin fitowar da yayi , dan Yusuf ba dai surutu ba ko aku ta shafa masa lafiya .

Yusuf yayi murmushi yana shafa kanshi yace " dama fa Ina cewa zan kira ka a waya sai kuma gashi mun hadu.

" Ya rabbi ya furta a kasan zuciyarsa sai dai babu yadda ya iya dan haka azahirance yace" toh Allah yasa lafiya ?
"a'a lafiya dama magana ne akan Ummita a firgice ma'aruf yace "wace ummita?
" ummita naku mana don Allah ina son in tambayeka ne ko an tsaida Mata miji ?

Wani irin banzar kallo ma'aruf yayi masa sannan ya amsa a ciki "uhnmmm ?

"Kenan kana nufin ba'a
mata miji ba ?
",Eh ya bashi amsa a qaugauce .....

"Amman na tambayi meenal tace min am mata miji " maganata zaka yarda dashi ko ta meenal ?
" Ta ka "to ba'a mata miji ba, idan kana sonta ne ka shigo sahun masu nema aurenta yana gama faɗar haka ya juya ya barshi tsaye yana zance zuci "mahaukaci banza kawai ,ai daman sai irin mahauka ne zasu zo nemanta har kuce kuna son wannan wawiyar yarinyar ,wani me cikakken hankali ne zai zo ...?
"Ai gara ka kwashe mana ita mu huta akan rayhan dina ya aureta .. ..


"Kai tsaye part dinsu ya nufa inda ya iske meenal da jidda suna kallo a zeeyworld a fusace yace "Sannnku manufukai banza wato shine har kuke fadawa mutane a muku miji kou ?
' toh wallahi idan kukayi wasa sai na kai hotunku masallaci ko za'a samu wanda taimaka muku ... .

"wai meya faru ne ma'aruf ? Inji cewar umma .
"Barni dasu Hajiya ai sun san abunda suka yi," toh ai shikenan kun fi kusa Hajiya tayi wucewarta ta barsu "ke jidda me kika gayawa Yusuf ? Nan da nan idanunta ya cika da hawaye tace" wallahi ya'ya bani bace meenal ce..

"okay dama ita naga alamar ta fiye rawan kan tsiya daita da wacan fat lion din mai tsiffar namun daji "toh ku shirya dan zan ci ubanku daya bayan daya a gidan nan ,duk ga saninku can anyi musu aure ko kunya bakwa ji , za'a taimakawa ɗaya daga cikinku amman dan iyayi da bakin ciki kice an mata miji "to uban wa kika tsayar mata dashi ?

"yaya ma'aruf dan me Yusuf zai rasa wacce zai ce yana so a gidan nan sai ummita wannan ai dis great ne wallahi ..

"Eyeeeeee wace ce ita da ba zai ce yana sonta ba ,ko kina nufin tafi karfinsa ne ko me ?

"Ai ya ma'aruf ba sai an fada ba,kai kanka kasan da bambancin tsakanin ummita da Yusuf sam ba'ajinta bane , bambancin ma bayyane yake, yaje gaba ya nemi matarsa amman ina ummita tafi karfinsa wallahi , ba zato ba tsammani taji saukar mari a kuncinta "ubanki da wannan maganar da kike faɗa .
Tayi saurin dafe fuskarta tana dubansa "idan baki sani ba ai Yusuf ne dai-dai ita," wa kika taɓa ganin yazo gidan nan da sunan yazo gurinta zance ?
"Wallahi idan na sake jin kin cewa wani am mata miji sai na balbaleki a gidan nan "
"Tana kuka tace "ai ita ce bata son kula samari .. asalima abakinta naji tana cewa duk wanda ya tsaida ita anyi mata miji , ya kai hannu ya shafa goshinsa na second biyu sannan yace "duk sanda tace haka ki ƙaryatata agabansu yana gama faɗar haka ya juya fuuuuuu...
"ai kin gani ba....?
" sai dana kwa'beki saboda gudun haka kika ki , gashi kin jawo kanki shan mari da tsakar dare nan kina zaman zamanki "to ni yanzu meye laifina anan aunty jiddah ?
"Oho miki ke dai kika sani ,ni dai Kinga shigewata babu ruwana wallahi .....

Zuciyarsa na matuƙar zafi ya dawo cikin d'akinsa goran ruwan ya ɗauka tare da kafa shi a baki sai da ya shanye tas sannan yayi wurgi da robar ,bedroom d'insa ya shiga ya d'auko hoton suhaima ya rungume ajikinsa yana jin wata irin soyayyarta na ratsa kowani sashi na jikinsa ,shi dai yana sonta sosai sai dai sha'awarta biyo bayan soyayyar da yake mata tunda yasan duk inda so yake dole sha'awa tana biye ....




Two friend's (bsbs)
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL NOT FOR SELL


AL'QALUMAN



*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*


~DEDICATED TO~
MARYAM ALHASAN D'AN IYA
(MARYAM OBAM)

BEST FRIEND FOREVER AND EVER, AKWAI AMANA 'KAWARMU ALLAH YA BARMU TAREN TARE SON SO FI SABILILLAH 🥰🥰

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim


PAGE 5


.......meenal d'akinsu ta nufa ,ta iske jiddah har ta soma bacci , ta samu guri daga nesa can daita ta faɗa kan katifa ta kwanta tana sauke numfashi, tana kwance har kusan minti goma bacci bai samu nasarar d'aukarta ba tana shafa inda ya ma'aruf ya mareta haɗe da tunanin maganganunsa akan Ummita , hannu tasa tana tashin jiddah. "aunty jiddah ! aunty jiddah !!

"Wai me ye ne kin zo da wahalarki kenan kou ?
"no ba wani wahala bane aunty jiddah ki tashi magana zamuyi ?
"Gaskiya ni bacci nake ji amman kiyi ina sauraronki .

" daman akan abinda ya faru d'azu ne , na fad'awa ummita abinda ya ma'aruf yace gobe ko kuwa ?
Jiddah ta gyara kwanciyarta sannan tace "wannan kuma damuwarki ce ki faɗa mata ko karki faɗa mata babu ruwan, may be marin da kika sha d'azu ne bai isheki ba ,kiyi harama ki sake janyowa kanki ,ni dai Kinga bacci zanyi na gaji da matsalarki...
meenal ta ta'be baki batare da ta sake cewa komai ba sai dai
ta kudiri aniyar sai ta sanarwa ummita abinda ya ma'aruf yayi ..

******
Ɓangare ummita kuwa kwance lamo ta rasa abinda ke mata dadi ,sai faman juyi take akan katifa , ranar bata yi isasshen bacci ba, gaba-daya abubuwan da ya ma'aruf ke mata ne yake dawo mata daki daki suna samun muhalli a cikin zuciyarta tana auna su 'kwa'kwaluwarta tare da yi musu kyawawan ma'aji a in da baza su goge ba , sosai ta dinga tunani har tsakiyar dare tana sak'e sak'e a ranta, sannan bacci barawo ya saceta.

Washegari

Ummita tsaye a d'akinta sanye cikin wando da riga na makarantar islamiyya, wando blue ruwan sararin samaniya, da rigar fara sol har kasa mai ratsin blue ajiki ,rigar ta sha guga sosai sai kyalli take, ta ɗan murzawa fuskarta farar hoda kana ta tsurawa fuskarta ido na second biyu sannan ta ɗauki agogonta a saman Dress morrow ta d'aura a tsintsiyar hannunta ta sanya farin hijab ta dan turare mai sanyi kamshi a kayanta , ta ɗauki jakarta ta rataya a kafadarta ,duk yadda ummita take tamke fuskarta amman sai da tayi looking attractive , kasa ta sauko a hankali fuskarta a d'aure ta tarar da mama ta gama shirya dining table , kai tsaye ta wuce dining taci abinci sama sama tana duba agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunta karfe 9 na safe ne yanzu.

mikewa tayi ahankali ta isa gurin mama tace "zan wuce makaranta daga nan zan biya gidansu himaya na dubo jikinta wai bata jin dadi.

"uhnmmm karki biya daga makaranta ,ki bari idan kin dawo gida sai nasa sale ya kai ki ai zai fi ko ?
zumburo baki tayi " kai mama ai da y'an ajimu zamu gaba-daya fa "to na hana, ki wuce ki tafi sai kin dawo Allah ya tsare "ameen ta faɗa a cikin ranta sannan ta fice daga part dinsu tana rausaya .....


Adaidai bakin kofar part d'insu meenal ta ganshi tsaye sanye cikin kananan kaya da jaket mai hula a saman rigar , hannunsa ɗaya rike da waya yana daddanawa yayinda ɗayan hannun ke cikin aljihun jaket din ya yi crossing legs d'insa ..

taji kamar ta koma da baya ta kaucewa maseefarsa ,amman ta d'aure ta sanyawa jikinta jarumta kamar koda yaushe idan sun haɗu ,ko ba dan haka ba ma ko saboda su meenal ta d'aure ,dan kullun sune ke biyo mata su wuce , yau da alamun sunyi makara ne yasa taji su shiru .
shi kuwa tun
ta howarta yasan itace ke tafe amman yaki d'agowa dan baya son kallon lion face dinta d ..

Qirjinta na dokawa ta dinga daga kafafunta har ta qaraso daidai inda yake tsaye batare da ta kalleshi ba ta taɓa ta gefensa har kafad'unsu na gogar juna , saurin goce kafadarsa yayi cikin izza da dakiya ya sake kawar da fuskarsa da hankalinsa kan abinda yake batare da ya yarda ya kalli ko ɗan yatsanta ba ..


Naunauyen ajiyar zuciya ta sauke lokacin data sanya gangar jikinta ciki parlour'nsu meenal cike da natsuwa , bakinta ɗauke da siririyar sallama ,har kasa ta durkusa a gaban hajiya umma ta gaishe da ita sannan ta k'arasa d'akinsu meenal , ko cikakken minti biyu ba tayi ba suka ta fito gaba-dayansu ,tun a lokacin meenal taso ta sanar mata amman ganin sunyi latti yasa ta bar maganar har idan sun taso ...

Tafiya suke a hankali duk da lokaci ya tafi amman hakan bai sa ummita d'aga kafafunta ba ,"muyi sauri mana kin san fa lokaci ya tafi ,"idan zaki iya jerawa dani haka mu cigaba da tafiya ,idan bazaki iya ba ki qara mai kawai ,dan daga haka bazan qara sauri ba.
"dole ki fad'i haka mana tun da kinsa duk rabbin malaman makaranta sonki suke yi ,babu wanda zai yarda a cikinsu ya taɓa lafiyar jikinki ni kuwa fa ...?

Murmushin gefen baki kawai tayi tana sake lankwasa kafafunta "karki damu kema kinsan matsawar muna tare babu mai ta min lafiyar jiki ...
duk inda suka wuce idanun jama'a na kansu ko in ce yana kan ummita .
Har suka qaraso gurin wasu maza kusan su biyar zaune kowane a cikinsu hannunsa rike da sigari suna zuka a hankali tana fitar da hayaki ,ganin ummita yasa gaba-daya hankalinsu ya karkata akanta ,tun daga sama har kasa suke binta da wani mayataccen kallo, daya daga cikinsu ne ya soma magana ahankali "kai friend's yarinyar ce haɗuwarta na kasheni kullun na ganta zata wuce sai naji kamar na fizgota gareni ,wallahi ina maseefar jinta araina.
"ai yarinya ce gsky ta haɗu babu karya dan bata da makusa, nima da zan samu zan d'ana, dan irinsu wuyar sha'ani garesu ,basa kula 'yan zaman banza irinmu ,kai ba ma haka ba ko aurensu kaje nema ba'a baka ba .
mus'ab yayi murmushi yana kada sexy eye's dinsa kamar mai jin bacci irin nasu na yan shaye shaye "tunda raina ya biya sai na d'and'ani zumarta ta kowani hali....
Wanda ke zaune a gefensa ya kwashe da dariya "kai mus'ab ban da saka rai a irinsu fa "kai ka share tunda na kwadaitu dole na lasa " shikenan idan ka lasa ni ne second ..
"Ni Kuma third suka sake kwashewa da dariya har sanda suka ga bacewarsu ummita ..
Haɗe rai sosai mus'ab yayi "wannan zumar tawa ce ni kaɗai ku dai yan tayani farauta ne ,take suka shiga tsara yadda zasu samu nasara akan ummita ..

*****

Akan hanyar dawowarsu daga islamiyya tafiya ummita take yi , cike da natsuwa take ta kawa ahankalin kamar mai tausayin kasa ,
yayinda gefenta meenal ce take bata labarin abinda ya faru daren jiya, har ma da marin data sha a hannun ya ma'aruf "amman ke ummita me yasa baki son kula samari alhalin kina samun masu tsananin sonkin da aure ?
" ni an ji babu me zuwa gurina koma nace babu wanda ya taɓa cewa yana sona as age of 17 ....amman ke meye dalilinki nakin kulasu ?
"Babu wanda ya isa ya hana faruwar haka ,dole kiyi aure ,ai duk ɗan sunah baya gudun aure ,ko ya ma'aruf ma da alamun ya soma gajiya damu, faɗa fa yayi sosai jiya har da gori ...

Shiru kawai ummita tayi mata amman gaba-daya ranta idan yayi dubu to a ɓaci yake. ..
har suka qaraso kofar gidansu bata furta komai ba,sai hancinta kawai take hurawa tana cizan lip's dinta na kasa , hawaye ne yake ƙoƙarin zubo mata tayi saurin danne zuciyarta.

cike da sarewa meenal ta dubeta ummita "shirun nan naki fa yana bani tsoro, ba wai na faɗa miki bane dan kije ki sameshi ,abinda yasa ma na gaya miki, ji nayi idan ban faɗa miki ba tamkar na munafurceki ne ,kuma na boye miki abu mafi muhimmanci ga rayuwarki ,ko babu komai ummita ya ma'aruf me kaunarki ne tunda yaji zafi akan kina korar samarinki ,a daidai harbar gidansu ummita taja ta tsaya tana fuskantar meenal tare da d'aura hannunta bisa kafad'arta "wannan ba qauna bace meenal duk

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment