Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ita jikinsa a sanyaye  " fat lion ya Kira sunanta muryarsa a kasalance  tayi masa banza ya sake matsota sosai  kamar zai shige jikinta dan har tana  jin  hucin numfashnsa a gefen wuyanta.
" nasan za ki ji babu dadi  game da abinda  ya faru  da kuma  abinda hajiya  inna ta yi miki , tabbas kina dauke da  ciki kuma wallahi cikina ne, nasan  ban kyauta miki  ba  na aikata kuskure mafi  muni agareki  wanda sanadiyyar haka inna tayi maiki tonon silili da aibantawa , wallahi  ban yi miki haka  dan  na kuntata miki ba ko nayi silar da za'a tozartaki ba , nayi ne saboda wani dalili nawa ,naki nasar miki ne saboda  ban san yadda zaki ɗauki abun ba   amma kiyi ha.......
Tun  ka fin ya k'arasa abinda yake son fad'i   ta juyu  da  sauri  ta rufe masa bakinsa  da hannunta ɗaya  tana kallon cikin kwayar idanunshi  dake cike da damuwa da ruwan kwalla ya cire hannunta  "am really sorry  ya faɗa yana  kallon cikin idanunta dake zubar da ruwan hawaye ....
"ka daina bani hakuri sannan ka daina  fadar  ina dauke da  ciki ,nasan ka fada  ne dan ka kareni agurin hajiya inna ba wai da gaske cikin gareni ba ...

Ya matso jikinta  sosai har  suna iya jiyo numfashin junansu "it's true fatlion  kina d'auke da cikin mah'ruf shuaib , nayi auratayya dake batare da saninki ba ,idan baki manta ba akwai   ranar dana na iskeki a dakin kina daga kafa da kyar har na kaiki gurin wata nurse ta dubaki lokacin mama ta tafi cotonue ,  lokacin na kaiki gurin likita  ta duba min ke saboda abinda na aikata miki , sannan ina lokacin da  kika  yita amai  har doctor Husain ya zo ya dubaki ,shi kuma a ranar yake faɗa min ciki gareki shiyasa naki yarda yayi magana a gabanki ,na dade ina son fada miki amman zuciyata ta dinga kwabata saboda sanin halinki  ..
Tayi sororo tana kallonsa kafin daga bisani ta soma girgiza masa kai "ko ka rasa tunaninka ne ya ma'hruf  ta yaya kake cewa ina da  ciki  ?
Ya  rungumeta tsam ajikinshi yana shafa bayanta bakinsa na kan sumar kanta daya gama wargajewa a bayanta "ta yadda nayi miki bayani  .

a hankali take  zubar da hawaye da sheshekar kuka  "ki kwantar da hankalinki  ,ki daina kukan nan haka,  ba fa mugun abu mukayi ba ni burina yanzu bai wuce  kiyi hakuri ki yafe min  saboda nayi tarraya dake batare  da saninki ba ta soma ƙoƙarin zare jikinta daga nashi "karka sake ƙara min damuwa akan wanda nake ciki  ni bani da komai tayi maganar tana ja da baya tana ƙoƙarin juyawa ya riko damtsen hannunta ya manneta da bangon d'akin zuciyarsa na dokawa da sauri , ya kai hannusa daya jikin bango ya tokare ya matsota sosai  yana ƙoƙarin   shigewa  jikinta  ya haɗe goshinta da nashi hancinsa na gugan nata   zuciyoyinsu   ya  dinga harbawa  a  tare  ,a hankali  suka sauke numfashi , ma’aruf ya lumshe idanunsa  sannan yasa hannun shi daya ya talla'bo fuskarta yasa kwayar idanunshi cikin  nata kana  ya kira sunanta  "fat lion ina me neman afuwarki  please sannan ki yarda da cikina dake jikinki  ummita ta marairaice fuskar  tana dubansa "kice kin yafe min ko hankalina zai kwanta , jikinsa a sanyaye ya haɗe fuskarsu waje ɗaya "talk to me fatlion  zuciyata na son jin wani abu  daga bakinki ya k'arasa maganar yana goga hancinsa akan nata  yana busa mata iskar bakinsa  da numfashinsa kafin daga baya ya hade bakin su guri daya ya shiga   tsotsa lip's dinta   batare da ta shiryawa hakan ba.
  kokarin hanashi take amman ta kasa aiwatar da komai  dan tuni  har ya zarce da  romance dinta   sun dade a haka rungume da juna gam gam yana tsotsan bakinta ...

Buga  kofar d'akin  da a kayi  ne yasa mah'ruf    janye jikinsa  daga nata ya nufo bakin kofar ya bude    ganin mama yayi tsaye   rike da akwatin kayanta , mika masa tayi" muje ka rakani inda zan shiga mota zuwa kasar haihuwata ..
"What mama Ummita ta furta da karfin gaske tana karasa fitowa daga dakin   da sauri "karki min haka mama yaya kike son rayuwarta ta kasance kina gidan nan  ma yaya na kare bare baki cikinsa  "akwai Allah sannan ga  mijinki  nan zai kula dake  fiyye dani.

"wani miji mama ni bani da wani miji, wallahi ba zaki bar gidan nan  ki barni ba kafarki kafata duk inda zaki  ummita da hankalinta yayi kololuwar tashi ta fadi haka fuskarta  tayi ja saboda kuka , jikin mama babu kwari ta soma jan akwatinta tana tafiya "haba mamana  karki min   haka idan kika barni yaya kike son nayi ta shiga binta tana rike da  akwatin "ba tun yanzu ake bukatar na bar gidan nan ba , lokaci bai yi ba sai yanzu ,ni kaina na gaji da zama a cikin gidan nan  tayi maganar a daidai lokacin da suka k'araso tsakiyar parlour'n inda mutane  suke tsaye, jin abinda mama  ta faɗa yayi mugun taga hankalin Abba take jikinsa ya kama karkarwa  gumi na sake  tsatsafo masa injiniya ne yayi karfin halin fita ya kira hajiya umma da baba sarki  .

Hajiya umma ta shigo hankalinta a tashe, mama ta isa gaban Abba ta durkusa har kasa kanta a sunkuye "to Ibrahim lokaci yayi da zan bar  maka gidanka da ahlinka zan tafi sai naji  daga  gareka Allah ya sadamu da alkhairi, idan nayi  maka laifi a zamantakewar da muka gudanar ka yafemin ni dai baka min komai ba tana gama fad'ar haka ta yunkura ta mike ta isa gaban  hajiya inna "inna kiyi hakuri dan girman Allah yau zan bar gidan Ibarahim dinki nasan kina kinsa  da kuntata masa ne  saboda  ya aureni, a yau ki cigaba da son d'anki kamar yadda kike ada saboda zan barshi bari na har abada ..

Abba ya ja dogon ajiyar zuciya  da karfi yana mai  runtse idanunsa jikinsa na wani irin rawa, bai taba tunanin mama zata iya furta abinda ta faɗa a yanzu ba  ,bai san ciwo da rad'ad'in barinsa zai daga masa hankali irin haka ba ,parlour'n ya kara  rikicewa   da kuka  da rud'ani jin furucin mama  mah'ruf kuka ummita kuka mama da sauran mutane kuka  abun ya citura  wata razananniyar
kara ummita ta saki mai karfi tace "nashiga uku Allah karka jarabi iyayena da wannan maseefar Allah idan hukunci ne ka hukatani  amman ka  bar iyayena su rayu kamar yadda suka d'auko rayuwarsu, "hajiya inna yau burinki ya cika amman da ikon Allah sai kinga ......
mama tayi saurin toshe mata baki tana girgiza mata kai "kul naji kince mata  wani abu saɓanin alkhairi "haba mama me yasa zaki hanani magana  "inna mahaifiyar mahaifinki ce , duk nan babu wanda ya isa ya faɗawa  inna maganar daya gadama ban taka masa burki ba bare ke diyar cikina ta k'arasa maganar  tana ƙoƙarin  barin  parlour'n Mah'ruf ya amshi  akwatinta   tare da rike hannunta "muje mama ai kinyi hakuri na tsawon shekaru tunda kin gaji babu mai takura miki ana aure dan ibada ne ,Allah daya halicci aure shi hassalata saki  dan  haka....
yayi kasa da kanshi yaki duban inda abba yake  sannan ya cigaba da magana  "Abba ka sawwakewa  mama aurenka dake kanta  kawai ta huta da wannan bala'in  na hajiya inna ya karasa maganar yana sharce kwallar idanunsa tare da kallon hajiya inna  yaji mai za tace  , zata saduda ko kuwa tafi bukatar tafiyar mama   ...

Wani irin ihu ummita ta  zunduma "wayyo Allah  na shiga uku karku bari mamana ta rabu da babana ,wallahi ina son su  tare banason na rabu dasu ,  ta isa gaban mama  tana hawaye wallahi  idan kika tafi zan kashe kaina duk ku huta ..... .
a matukar tsorace mama tace "karki aikata sabo mana , rabuwa kaddara ce babu abinda zai sameki you will be fine ummita adduata tana tare dake dan Allah ki kwantar min da hankalinki kinji mamana kinga bake kad'ai bace  ki zauna gidan ubanki tare da mijinki .

"mijin banza mijin wofi me zanyi dashi wallahi babu abinda zanyi dashi nafi bukatar ke da mahaifina tare  ,yadda ta dinga wasu  abubuwa kamar zararriya ya d'aga hankalin mama matuka .

Mama na kallon Ummita ta  k'arasa kusa da ma'hruf ta fixge akwatin kayanta   dake rike a hannunsa "dan me zaka goyin bayan tafiyarta? " kana   bakinciki ganinsu tare ne ?
Girgiza mata kai yayi yana cewa "wallahl azim nafi son ganinsu  tare "
"karya ne  kai ga mahaifiyarka   tare da Abba shine ni kake son raba tawa mahaifiyar da mahaifina ,wannan itace  kalar taka soyayyar  ga mama ?
"daman duk soyayyar da kake nuna mata shekara da shekaru karya ce ?
"Are you out  of your sence  ki  natsu kiyiwa mutane shiru anan sannan ki shiga hankalinki  kasancewarki  diyar  mama kawai kike  amman soyayya dake tsakanimu ta wuce misali ,mama tayi niyyar tafiya da kanta I can't stop her  wallahi bazan hanata tafiya ba dan nafi son rayuwarta akan komai , tsawon shekaru bata taɓa tunanin tafiya ta barmu ba  ,ta ɗauki tsawon shekaru tana addu'a dan  yau ta furta zata barmu sai nace a'a "bazan hanata ba sai dai na goya mata baya dan na  samu kwanciyar hankalinta .

"to ni ban yarda ba ban kuma amince  da wannan tsarin ba banason rabuwarsu nafi son na  gansu tare  "na rantse da wanda ya busa min numfashi matukar  mama ta bar gidan  nan sai dai ku farka kuga gawata tana gama fadar haka ta kwasa da gudu tayi  hanyar step  tana wani  irin kuka da sauri ya saki hannu  mama ya biyota aguje itama mama bata san sanda ta biyo bayansu   tare da sauran jama'a ba.

Ummita na shiga dakin ta shiga bubbude dorowar  bedside dinta ta dauko  magani ciwonta , gabadaya ta zazzaga a tafin hannunta tana ƙoƙarin  zubawa a bakinta ya banko kofar dakin da karfi  ya shigo bai tsaya wata wata ba ya buge hannunta yana fuskantarta "kina hauka ne ko kin fara shaye shaye ne ?
"  zan miki rashin mutuncin da baki taɓa especting daga gareni ba  .. "dakata malam babu ruwanka da rayuwata waye ma kai meye hadinka dani  ,mama ta k'araso gurin da suke   ta d'aga hannu sama zata sauke mata mari , yayi saurin rike mata hannu "dan Allah mama   karki mareta   ki barta taji da halin  da take  ciki  ,mama ta fashe da kuka tare da zama a gefen katifa, hajiya umma da injiniya da abba  har ma da aunty  suka  shiga  bata hakuri da bata baki .

"ku daina bata bakinku  bafa zan zauna ana wulakantani ba meye aibuna ? "Meye laifina
"Me mahaifiyarku take son nayi mata?" iya biyyaya ina mata ko ita ta kawoni  duniya iyakacin  abinda zan iya mata kenan ,gara na kama gabana wallahi bazan zauna ba ......
jin furucin mama dake shiga kunnuwanta yasa ta soma yin kasa mah'ruf yayi saurin tarota jikinshi  yana taɓa  mararta jin  numfashinta ya  dauke yasa     gabadaya  a gigice ya soma kiran sunan mama "mama ta suma ....
  gabadaya sukayo kanta, suna kiran sunanta "ummita ummita  shi kuwa mah'ruf sai fatlion yake  kira yana rungumeta daita tsam a faffad'an  qirjinshi  "dan Allah mama kiyi hakuri kice kin fasa tafiya  wallahi  idan wani abu ya sameta nima zaki rasani  ,kiyi hakuri  mama karki rasa yayanki alokacin ɗaya ...
     Hannun ummita  mama ta riko cikin nata  tana kuka "ummita karki min haka ki tausaya min ganin yadda duk suka rud'e babu wanda yayi tunanin a yayfafa mata ruwa yasa aunty  fad'awa bathroom ta dibo ruwa da sauri mah'ruf ya karbi roban ruwa, ya shiga shafa mata a fuska ,amman  shiru bata motsa  ba ,a matukar haukace mama ke girgiza ummita tana kuka tana kiran sunanta "ki tashi dan girman Allah wallahi na fasa tafiyar karki mutu ki barni idan kika mutu bazan taɓa yafewa kaina ba, saboda nice sanadi shima Abba a zabure yake girgizata wani ruwan ya sake tsiyaya mata amman shiru taki motsowa  .

hankalin kowa yayi bala'in tashi fiyye da tunanin mai karatu sunanta kawai suke kira "shikenan ta mutu ta mutu "bata mutu ba mama mah'ruf  ya faɗa a gigice  yana   sake janyota jikinshi  ya zauna akan tayis  ya rungumeta yana girgizata "fatlion karki mutu ki barni ki rayu saboda ni  dan Allah .   gabad'aya ya rud'e  ya gigice ya d'ago fuskarta Yana busa mata numfashinsa  a cikin bakinta da hancinta  tare da zira  yatsun hannuwansa  duka  cikin kunnuwanta a hankali ya haɗe bakinsu  guri daya gabadaya ilahirin jikinsa rawa yake gumi na tsatsafo masa   ..

Tsura masa ido sukayi suna dubansa kafin daga baya suka soma barin d'akin daya bayan daya saboda ganin abinda yake mata ,  waje sukayi gabadayansu suka tsaya  cirko cirko suna addu'ar kowa hankalinsa a tashe yake ban da hajiya inna , wacce bata cewa kowa komai ba dan tasan ko tayi magana babu mai kulata ta nufi dakin inda ta iske Mah'ruf zaune rashe rashe  rungume da ummita  a jikinsa yana tsotsan bakinta da iyakacin numfashinsa mutuwar tsaye tayi  tana kallonsu cike da mamaki   idan ya tsotse bakinta sai zare ya sake maidawa haka ya dinga yi daga karshe ya zarce da romacing dinta yana tsotsan bakinta yana zuba mata sambatu, babu shiri ta juya da sauri ta bar dakin sai lokacin ta fahimci abinda ya fidda mutane   daga dakin,  tana fita ya sake damkar bakinta yana hura masa iska ta hancinta da karfi ..
Wani irin atishawa ta saki da karfi haɗe da sakin numfashi  tare da kiran sunan mama "karki barni mamana karki tafi ki barni ina bukatarki ya mike  tsaye rungume daita ajikinshi ya kwantar daita a saman katifa  ya riko  laulausan tafin hannunta ya rankwafo jikinta yana gyara mata kwanciya sannan ya zauna gefenta yana  rike da hannu daya ,dayan hannunsa ya kai gefen fuskarta yana  shafawa a  hankali  yana sauke numfashi, yafi karfi minti talatin  a gabanta  yana kallonta  ya  kai hannunta dake  rike cikin nashi yayi kissing yana d'aura dayan  hannunsa  ya haɗe guri daya "ta matso ruwan hawaye "ina mamana  ta wuce ko ?
Ya girgiza mata kai "ta fasa tafiya  ki kwantar da hankalinki ki sanyawa zuciyarki natsuwa kinsan mama bazata iya barinmu ba.

"zata  iya  ya  ma'hruf naga  hakan a cikin kwayar idanunta ni dai ka dakatar daita duk lalacewar gidan nan  nafi son ganita cikinsa, idan bata ciki rayuwata zata tagyyara "babu inda zata muna tare ya fadi haka yana kai hannunsa kan cikinta jin yana motsi har lokacin ya sauke naunayen ajiyar zuciya kana ya kai bakinsa cikin kunneta "am so happy cikina yana nan lafiya.
cikin kuka tace "ni ina ruwana da wani ciki ta zabura zata mike yayi saurin  matseta gam a faffad'an qirjinshi "dole kuwa kiyi  ruwa dashi wannan cikin rayuwata kenan  ,akan cikin nan  babu abinda bazan iya yi ba, babu wanda zan iya d'agawa kafa "To ni wallah  ka rabani da cikin nan idan ma gaske ne   dan  banason shi ,me zanyi da cikin wanda bai sona bai kaunata . "okya kiyi  hakuri sannan ki taimakeni  ki  bari ki haifa min cikina  sai mu  rabu  tunda kinfi bukatar haka  ...?
Tayi shiru zuciyarta na wani irin  zugi "ai nasan zaki fi buƙatar rabuwar mu ko ba haka ba ?   "ban sani ba matukar na tabbatar da cikin babu abinda zai hanani zubar dashi ,"karki soma  wannan gangancin ,ayi ɗaya kacal na sameshi kinsa walahar da ake sha kafin a samar d'a  ... ?
Taja tsaki tana kawar da fuskarta gefe "dan girman Allah ka rabu dani ka rabani da wani zance ciki  "Bazan iya rabuwa dake ba fatlion  saboda aurenmu auren zobe ne, bazan iya barinki ba duk runtsi duk wuya muna tare dan haka ki daina kawowa  zuciyarki  rabuwa  a tsakaninmu ,
da kyar ta samu ta raba jikinta da nashi ta soma ƙoƙarin saukowa "ki kwanta ki huta babu inda mama zata,
  ta girgiza masa kai "ina son ganin mamana bai ce mata komai ba ya riko hannunta suka fito yana rike da hannuta ..

Suna gama saukowa ummah ta nufo gurinsu" sannu ummita     ta rungumeta ajikinta tare da manna mata kisss a goshi tana shafa    gadon  bayanta "kin  kwantar da hankalinki mamanki ta fasa tafiya  ta barki ,kuna tare muddin rai kinji diyata.
"inji uban wa   ai  tafiyar uwarta  dan ada  huta roro, dole ta wuce kuma tare da diyarta idan mutuwa zakuyi idan sun tafi  sai  ku mutu mu gani  amma dole  sai  ta bar gidan nan  kuma a yau daman nafi son barinta gidan  sai gashi  kuma    ta bukata huta roro ta tafi na huta da jaraba   ..
Abba ya motsa bakinsa zai yi magana hajiya inna  tayi saurin dakatar dashi "karka sake naji bakinka ka rubuta mata takardar sakinta yanzu yanzu da zafi zafinsa  ka bata dan ....
"  Ba zai rubuta  ba  mah'ruf ya katse mata hanzarin ta hanyar faɗar hk  " ko kin raba auren nan  bazaki raba zukatan mutanen gidan nan da kaunar mama ba ..
" Da yarda Allah sai kin mutu ki bar wannan auren hajiya inna ,baki isa kisa Abba ya saki mama ba, ko da kika ga dazu na goyi da  bayan ya sawwake mata  bawai har cikin zuciyata nake son Abba ya  saki mama ba ,na fadi haka ne saboda   rabata da bala'in da maseefarki sannan na gani idan nace ya saketa  zaki hana a she kema abinda ke ranki kenan ,to  ko mutuwa zakiyi  sai dai ki mutu amman abba da mama mutu ka raba suna nan tare  daram .

"oho to bari kaga yadda karfin ikona ya kai yau  idan bani da iko akanka ai ina dashi akan ya'yana Ibrahim sagiru ta kira sunan Abba da injiniya a tare suka d'ago suka zuba mata ido suna kallonta jikinsu na rawa   "me ye matsayina agurinku ?
"Mahaifiya suka fadi haka jikinsu na sake rawa "to ina umartaku a yanzu
da ku sa ma'hruf  ya saki ummita saki uku rasss  .......kuma a yanzu idan ba haka ba  duk sai na tsine muku  albarka duniya tayi muku dumi  sannan aljannarku dake tafin kafafuna zan danne bazan taɓa daga muku kafa ba,  jin haka yasa hantar cikin mah'ruf  kad'awa a hankali  jikinsa ya soma rawa tamkar mazari  yana kallon inna cike da mamaki.

Abba da injiniya kamar zasuyi kuka  "ya mah'ruf kaji abinda Hajiya inna  take buƙata  ka aiwatar aikaina   ka sakeni  kamar yadda ta bukata  kowa ya huta dan ni kaina  bana bukatar zama da kai ,ya  watsa mata kallon banza mai haɗe da harara  hankalinsa bai tashi ba sai daya ji saukar Muryar abba cikin kunnenshi "ka sawwake mata baba Allah yasa hakan shine mafi alkhairi ...
kallon Abba ya dinga yi shesheke kamar wani mahaukaci tare  da kallon sauran  mutane dake gurin ,gabadayansu  sukayo kanshi suna umartashi  bai san sanda ya isa gurin Hajiya inna ya rike hannunta   "haba inna karki min haka kiyi hakuri dan girman Allah karki sa  Abba cikin wannan lamarin, ni ne fa  babanki ma'hruf  da kike so fiyye da komai .
"Ina sane da hakan ,sai dai tuni  na soke maka  wannan matsayin ba dai akan wannan matar ka rufe idanunka kana   min tozarci ba ?
"na tuba Inna ki yafe ni , "baka isa ba sai ka rabu daita ya mike ya isa gurin ummita ya riko hannuwanta muje ki bawa inna hakuri ina bukatar rayuwa dake bazan iya rabuwa dake ba  ..
"taja ta tsaya tana kallonsa sannan ta soma magana a tsanake "zaka min wata alfarma ?
Ya d'aga mata kansa da sauri  yana sanya kwayar idanunshi cikin nata "ka sake ni  kamar yadda ta bukata sannan ka fita cikin rayuwata bana bukatarka .....
"Idan kina bukatar na sadaukar miki da rayuwata zanyi fatlion  amman bazan iya   sakinki ba ya k'arasa maganar yana ƙoƙarin zubda hawayen dake   idanunshi , cike da sanyi jiki take kallonsa  ta kai hannunta fuskarshi tana shafawa batare da tasan ta aikata hakan ba   tana kallon cikin kwayar idanunshi da suka canza kala tsabar tashin hankalin da yake ciki .
" dole ka sawwake min aurenka  inna bata son zamana da kai ni kuma bazan iya rayuwar kunci ba ,bazan iya  irin rayuwar da mahaifiyata tayi ba "Ki yarda ki amince  ki kasance  tare dani bazan bari wani abu ya sameki ba sannan bazan iya sakinki ba, ki kasance tare dani  fatlion dan wallahi  bazan iya barinki ba ,Allah ne kaɗai yasan abinda zai same ni idan kika bar rayuwata haushin furucinsa take ji ,a da taso tayi rayuwa dashi amman a yanzu bata bukatar haka cike da jin haushi ta  fixge jikinta ta juya cikin sautsayi kafafunta suka gurd'e tayi kasa  zata  kifa kan cikinta yayi saurin  tarota  ya mannata da qirjinsa , wani irin bugawa qirjin inna yayi da wannan abu, ta zaro idanunta tana kallonsu zuciyarta cike da bakinciki a fusace yake kallonta numfashinsa kamar zai bar jikinsa  "me  yasa  kike  sakaci da kanki  da  rayuwarki ? "Me  yasa  bakya  tunanin halin  da  zan shiga akanki ?  ta hura masa hanci hawaye na zubo mata " hannun sa ya kai ya rike kafad'unta dashi  yana sake  kallon kwayar idanunta da tsare gira "  I love you fatlion ! I love you  fatlion !! 

Yan wattapad Sai hakuri yan what's app zasu rigaku samu saboda matsalar network

TWO FRIEND'S BSBS

💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL


AL'QALUMAN



*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*


~DEDICATED TO~
*MUHAMMAD AUWAL*


WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim


PAGE 54

Tsaye ummita tayi tana bin mah'ruf da idanunta waɗan da suka koma jajaye tsabar hawayen dake zubowa daga cikinsu tana jin kalmar daya furta kamar almara tare da yin nazarin furucinsa mai kama da sake kusancinsu tare , wani sanyi ne ya dinga taso mata yana ratsa sansar jikinta ,jinin jikinta ya ninka gudun da yake fiyye da farko, hatta ɗan cikinta sai da yayi tsalle ya cure guri guda , gabad'aya ta kasa motsi dan kalmar i love you fatlion ba iya zuciyarta kaɗai ya tsaya ba har cikin jininta take jin tafiyarsu ..

"yau ita mah'ruf ya furtawa wannan tsadadden kalmar mai dadi da sanyaya zuciya ?"anya kuwa wannan drama ba'a mafarki yake faruwa ba ?
" tasan mahruf fiyye da kowa mutumin daya girma da kiyayyarta shine yanzu tsaye a gabanta yake furta wannan kalmar gareta anya kuwa ba yayi hakan dan hajiya inna taji haushi bane ?


Hannuwansa dake kan kafad'unta ya cire ya zuba cikin aljihun wandonsa haɗe da tsura mata idanunshi yana kallonta , da sauri ta share hawayenta dake sake turereniyar gangarowa haɗe da girgiza masa kanta yayinda soyayyarsa ke sake fixgarta da karfi ,tabbas tasan ita kanta ta kamu da mahaukacin qaunarsa sai dai duk runtsi baza yarda ta amince masa a karon farko ba ,zata adana nata soyayyar ba zata ta fito da nata fili ba ....

Shima zuba mata idanunshi yayi yana jin zallar farinciki da fargaba na ratsashi a lokaci daya qirjinsa ke wani irin mahaukacin dokawa kamar zai fito waje jikinsa a kasanlance ya buɗe bakinsa " babu ta yadda zan iya rayuwa babu ke ya furta yana sake kusanto jikinshi da nata qirjinsa na dokawa da matsanancin karfi ,still shiru tayi taki cewa komai tare da tsura masa idanunta dake cigaba da zubar da hawaye , " there's no way to survive without you fatlion I love you with all my heart banason na rasaki , banason rasaki a rayuwata saboda
DOWNLOAD
DOWNLOAD

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

11 months ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

11 months ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment