Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rufe masa ido  dan  koda ya shigo idonshi sun gama     rufewa akan matarsa     burinshi  bai  wuce ya kawar  dashi ba, mama  ta  riko hannun amad batare da ta  sake cewa komai  suka shiga  cikin gida...

Cike  da  taikaici da masifa dake cinsa  ya maida idanunshi kan ummita yana  sake  tambayar cikin  zafi  kamar zai mareta      "Ki faɗa min abinda  ya faru kinsa a rashin sani  nayiwa d'an uwana  rashin mutunci ,me yasa kina kallon abinda ke faruwa kika boye min  ,baki san haka cutawar bane?

sai lokacin  ummita ta dawo  hayyacinta sosai  ganin  wulgawar amad babu abinda ya sameshi, ta  yunkura ta mika daga jikinsa  tana kakkabe   jikinta, ya mike tsaye  zai kamota ta bige masa hannu, cikin tsiwa ta dakatar dashi da hannunta "Karka sake ka taɓani, ji irin  haukan da kayi  yanzu, idan anyi mgn  kace baka so na kishin  auranka kake haka ake  kishi?
Yanzu  wannan  kishi ne saboda Allah "?
ta  kai  hannunta daidai  saitin  zuciyarsa dake bugawa  da matsanancin   karfi  "shima wannan  kishi ne ba so ba? kana yaudarar  kanka ya mah'ruf  na tabbatar da kana so na idan ma baka sona a wannan abun daka aikata yanzu  na sake  tabbartawa kaina da  kana mahaukacin so.......

katseta yayi  ta hanyar d'aga mata hannu 
"Don't   deceiving your self  fatlion ,  ko  kina hauka   ne?  ko kuma kwakwalwarki ta dusashe ne  ?  " kwakwalwarki  da tunaninki  basu  faɗa miki  gsky ba saboda wannan  ba so ne?

"Uban wa   ya faɗa miki haka ake so  ?
" to bari  kiji wannan  ba so bane , da aurena akanki dole  nayi  kishin  aurena,  dole kiga hankalina  ya  tashi nayi hauka fiyye da haka   na sha  faɗa miki ni ba addayus   bane mutumin da  baya  kishin iyalinsa dole  nayi  kishinki  idan ba haka ba wutar Allah ta cini  dan haka ki dawo cikin  hankalinki  "  ya karasa maganar cikin masifa  yana huci, ya  dunkule  hannunsa da iyakacin  karfinsa ya sake kaiwa bango naushi yana huci   ,  runtse idanunshi  yayi gam saboda yasan  karya zuciyarsa  ta faɗa  sam ba abinda  yake zuciyarsa  ba  kenan yana jin fiyye da yadda yake kishinta  ......

Idanunta  ta  zaro  Sbd  jini  data  gani a hannunsa ta matso jikinsa  tana rike hannunsa  ya waigo a hankali fuskarshi a haɗe sai  da gabanta ya fad'i , ya tsura mata ido "jini a hannunka ya mahruf!"   dakatar  da ita yayi ta hanyar cewa   "Stop touching  me  ki barni kije kawai   amman  kinsan Allah  sai naci uban menal  yau    " ummita  tace "Dan Allah kayi hakuri ka yafe wa menal  bata da laifi Ina son ƴar uwata , bana son wani abu ya sameta ni ka hukuntani  idan bazaka hakura ba  amman  ka barta tana gama maganar   sai hawaye shar-shar suka gangaro saman  kyakyawar fuskarta.   

Sauke  naunayen  ajiyar zuciya  yayi batare daya furta komai ba ,  tasa hannu ta share hawaye   tace  "Muje ciki  ta riko hannunsa  suka nufi bangaren  mama still bai mata mutsu ba   Suna shiga ta nufi sama dashi ya  turje  yaki motsi ta juyo  tana kallonsa da lulu  eye's dinta "plz now muje  nayi maka  treament  din hannunka  yayi mata banza yana cika yana batsewa "  mama  dake tsaye a bakin kitchen  tana  kallonsu tace " kabita ku  shiga ciki mana ko ba treament zata maka ba .?
Yayi shiru zuciyarsa na dokawa da zafi idan yayi bai ji ciwon abinda suka yi masa yayi karya har shi zasu haɗawa plan ?

"Dan Allah muje yaya na  yi  maka treatment din hannunka   ummita  cike da rauni da tsantsar jin zafin jinin da ke fita daga hannunsa ta furta haka  ,"mama dan allah  kiyi  masa magana ...

Tun kafin mama ta sake cewa wani abu  , ya  fixge  hannunsa dake cikin  nata  ya soma motsawa yana daga  kafarshi da kyar , jiki babu kwari ummita ta biyo bayansa bugun  zuciyarta na tsananta, duk ta firgici  a dalilin haɗe fuskarshi da yayi dan  har yasa  miyon bakinta ya kafe  daga tsittarwa da  take ..

Juyawa mama  tayi tana murmushi ",  kuna  wahalar da zuciyoyinku" ta  faɗa a  zuci ta karaso  gurin amad tana tambayarsa  da jiki "Sannu amad ya kake jin wuyanka?" amsawa yayi "Da sauƙi mama amman na shaku gaskiya ni wucewa ma zanyi  yanzu daman  sautsayi ne ya biyo  dani  ,mama tayi murmushi "ai duk laifinsu ne ,sun san halinsa me yasa zasu yi masa irin wannan wasan" koma dai menene wallahi tafiya zanyi dan ko awa daya bazan qara ba, bansa dakiyar  zuciyar  mah'ruf ya kai haka ba.
"ya wuce duk yadda kake tunani  idan ransa ya ɓaci  gara yayi shiru akan  yayi zuciya amman dai
ka  bari zuwa  gobe da safe  ka wuce ,ya girgiza kanshi "tafiya zanyi  ya ɗauki jakar school bag ya rataye a bayansa yayi mata sallama yana ƙoƙarin cewa ta tsaida shi "jirani nazo ta wuce d'akinta .

Suna shiga ɗakin ummita ta  kama  hannun mah'ruf sai  wani  fizgewa yake yana cin magani a dole an bata masa rai , haka ta  zaunar dashi saman  gadonta  ta ɗauko kayan  dressing  ɗin tazo ta  zauna dab  dashi har suna iya  jiyo hucin junansu, ahankali  ta  ɗora idanunta  kan kyakyawar fuskarshi,  tana kallonsa cike da  mayen soyayyarsa  ji take daman ciwon ya dawo kanta,  ƙin kallonta yayi ya sake haɗe rai , idanunta  ta runtse na second biyar sannan  ta  buɗe   ta  tattaro jarumta ta sanyawa jikinta  ta buɗe  ƙwalbar hydrogen ta  k'ara  shigewa jikinsa, ta kamo  hannunsa mai ciwo  cike da  wani  irin mugun shauƙin ƙaunarsa,  ta shiga  goga masa hydrogen  ɗin  cikin wani irin yanayi tana manne masa  ta yanda ba zaiji zafi sosai  ba .

  da farko yaji zafin hydrogen  ɗin, amman yanayin yanda ummita take  masa dressing ɗin cikin  wani  irin  shauki ta haɗe jikinsu waje ɗaya, tana masa sannun cikin wata irin muryata mai rikitarwa   sai yaji zafin babu  sai  wani irin zirrrrr yrrrrrr  yammmm  ya dinga ji a sansar jikinsa sai dai   ya dake  ya basar yaki nunawa  ko motsin kirki  bai ba dan karta fahimta .

Yayinda hankalin ummita  ya sake  tashi sosai da ganin yadda yanayin   fuskarshi tayi alamun yana jin zafi ,ta runtse idanunta   dan kusan  tafi shi jin zafin ciwon daya ji ,  taci gaba da masa  dressing  ɗin hannunsa, Cikin tsantsar kulawa da tausayinsa.
wani irin  fitinanniyar soyayya da take ji yana ratsa sansar jikinta a lokacin da take  masa  dressing ,  duk ta shige masa cikin jikinsa, koda ta gama masa luf tayi a saman ƙirjinsa, tana riƙe da hannunsa tana ƙara hura masa iskar  bakinta ,  mah'ruf  ya lumshe  idanunsa yana jin wani irin mugun  yanayi  mara musaltuwa, gaba-daya komai  ya soma  kwance masa "

Bayan ta gama yi masa treament ta koma kan kujera ta tsura masa idanunta   tana zance zuci tana son ta saisaita natsuwarta ta kawar da abinda take ji akansa amman sai take jin abun na ninkuwa acikin zuciyarta  ,sama da minti 30 suna zaune a haka  tana kallonsa ,shi kuma yana kwance rigingine yana furzar da iska .

a hankali mama tayi sallama   ummita ta sake daidaita kanta tare da amsa sallamar, mama ta turo kofar ta shigo , ummita ta mike domin bata gurin zama ta zauna idanunta na kan mah'ruf ,"har yaushe zaku daina wannan fad'an ?"ya kamata zuwa yanzu ku fahimci junanku ,ku tsaida wannan tashin hankalin haka banaso ta k'arasa maganar tana sauke numfashi  "ai mama shine yake ɗaukar komai da zafi , ki faɗa masa duk abinda zai faru ya dinga saisaita zuciyarsa , kalli yadda yajiwa kanshi ciwo ta fadi tana gyara zaman  gashinta da yake kokarin rufe  mata fuska  "ni fa wasa nake masa shi.......
"ni abokin wasanki da zaki dinga wasa da rayuwata ?
"Ko ina irin wannan wasan  dake ?

Tayi shiru tana kallonsa zuciyarta na harba tsabar haushin jin abinda ya faɗa bata san sanda tace " nayi kayi abinda zakayi ,wallahi  ka ma bala'in rai min hankali, kai baka sakeni ba ,kai baka maidani matarka ba, sannan baka barni na huta  ba gaskiya  na gaji enough mahruf zan baka lokaci kasan abu yi if not "if not sai  .....
"Ya rabbi baba a gabana saboda Allah mai yasa bazaka dinga hakuri ba ?  ta karasa maganar kamar zata zubar da hawaye, yayi saurin riko hannun mama cikin nashi " shikenan mama  kiyi  hakuri na daina inshaallahu,duk  laifi na ne  "no kaima ba laifinka bane  ,duk baku da laifi Allah yayi muku albarka ke  kuma kar na sake jin yana magana kina maida mishi martani zan ci mutuncinki idan na sake ji "to ni yanzu mama haka zanyita zama da .. "shiru nace banason jin komai  ta mike ta fice ta barsu  "wallahi zan d'aga hankalin kowa a gidan  yau  amad ne daga gobe  ....
"Daga gobe me zakiyi wallahi fatlion ki kiyayeni  zan canza  miki  kamani ,kina cin daraja daya ne agurina if not da tuni na gyara miki zama  ta  turo masa karamin bakinta  tana juya masa keya ya ja tsaki ya fita  ..

Bata  juyo ba har sai da taji  fitarsa  daga d'akin  gabadaya  sannan ta mike  ta tattara  kayan  da tayi masa treament din hannunsa  ta maida,
tayi kwanciyarta  zuciyarta na bugawa  .

kai tsaye part din hajiya umma  mah'ruf  ya nufa  yayi sallama     ya shigo  ya  isketa zaune ita da   menal  tana  ganinsa    ta mike  a firgice   wani  irin kallo ya watsa mata ya samu  guri ya zauna kusa da hajiya umma  "hajiya barka da yamma ?
"Barkanmu   baba ya  gida   da aikin ?"alhamdullahi  jikinta menal  na  rawa tayi saurin durkushewa
a gabansa  tana yarfa  da hannu "kayi hakuri  yaya wallahi bazan sake ba  hajiya umma ta dubeta  "ke  kuma lafiyarki  daga shigowarsa kika wani durkushe agabansa  kina rokonsa  "barta  kawai hajiya tasan abinda tayi shiyasa , cike da tashin hankali menal tace "umma dan girman  Allah ki bashi hakuri kar ys dakeni duk  da san  laifina ne, bana   laifin umminta "shiiiiiiiiiii You very stupid ita tace laifinta ne ke kince laifinki ne  "to ayi musu hakuri ba zasu sake ba .
yayi shiru batare da yayi  magana
ba,  ba shi  ya bar gidan ba sai da yaji an soma  kiran  sallar magariba sannan  ya  fita   yayi  sallar,  mai makon  ya  kama hanyar wucewa gida sai  ya dawo bangaren  mama da niyyar sake ganin ummita kafin ya wuce  gida , ya zauna parloun shiru bai ga fitowarta ba har mama ta zubo masa  abinci  yaci  bata sauko ba ,yana ganin mama ta fita zuwa part din Abba ya mike tsam ya haye sama a kwance ya ganta da alamun bacci take ya tsura mata idanunshi yana kallonta kafin daga bisani a hankali ya kwanta ajikinta  yana sakin wani irin naunayen ajiyar zuciya,  juyowa tayi a rashin sani ta shige jikinsa yasa hannunsa mara ciwo ya matseta ajikinsa , wani irin  zazzafar soyayyarta ke fixgarshi sai dai duk yadda yake jinta a ranshi bazai iya furtawa ba, kissing din goshinta yayi a zuciyarsa yace "Allah ka ga halin da bawanka mahruf yake ciki  ,allah  ka sausata min nasan  ita din ta daban ce tun daga kan ni'imar daka  mata .

Ya runtse idanunshi tsigar jikinsa na tashi "tun daga lokacin  dana kusanceki   zuciyata ta dana tunanin  kowa  sai ke ,komai nake is  perfect   ....
"I don't know how to explain  amman Ina  jinki sosai ajikina ya sake motsowa jikinta yana kissing din wuyanta " a yanzu Yake  sake jin zazzafar soyayyarta  kusan minti goma ya ɗauka yana kallonta yana sambatu da zuciyarsa  sannan ya yunkura ya mike ya zuro kafafunsa kasa  yaji ta rike masa hannu tare da fixgoshi jikinta, ya ware idanunshi  yana mai tokare hannunwansa da katifa dan kar ya fado saman cikinta  tasa hannuwanta duka ta zagayeshi dashi tana sanya kwayar idanunta cikin nashi "meye haka kina son na illataki  ne ?
Ta kashe masa idonta daya alamun
eh "
"Bazan iya ba saboda darajan abu daya "meye shi darajan ?
Ya  runtse  idanunshi " bazaki fahimta ba amman idan lokacin  da zaki fahimta yayi zaki sani ne "idan ma sona ne  ai tuni na fahimta ..

ya bala'in haɗe rai "har yaushe zaki daina wannan tunani ?ta sauke ajiyar zuciya da karfi "sakar min jiki zan wuce gida "babu inda zaka yau ma  ka shirya kwana anan "what ?
"Uhmm anan zaka kwana ko bazaka kwana bane ?"ba zan iya ba ya ja dogon hancinta yana waskewa .
"dole  ka fadi haka saboda   matartaka  tafi karfinka sai abinda ta faɗa kake yi wallahi har kunya nake ji idan naga kana rawar jiki akanta  "uban yace miki tafi karfina ?
"Ubana ta bashi amsa da haka tana zare hannuwanta daga jikinsa ta sauko daga kan gadon zata shige bathorrom  ya sauko da sauri ya  fixgota ta fado jikinsa ya manne da qirjinsa,yasa  hannuwansa duka ya  zagaye  cikinta ya soma shafawa a hankali yana kunshe ido "me yasa zaki zagi Abba ?
"Ba zagi bane amsarka na baka ,shikenan bazan sake cewa haka ba  ,amman karki sake cewa ina jin tsoron suhaima ko nayi miki kama da matsoraci ne ?
Ta juyo tana fuskantar shi  tana watsa masa harara tare da turo masa karamin  bakinta  bakinsa ya kai kan lip's dinta "zan tabbatar miki da bana shakka ko jin tsoron suhaima  tana ajikinsa ya karasa ya sanyawa kofar key ......



TWO FRIENDS BSBS

💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL NOT FOR SELL


AL'QALUMAN



*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*


~DEDICATED TO~



WATTPAD @HAUESH

Page 49

.... A hankali ya juyo daita tana manne ajikinsa , ha'barsa na kan kafad'arta yana shinshina kwantaccen sumar kanta mai fitar da kamshn dake tsuma zuciya zuwa wuyanta ,
tsaye yayi a tsakiyar d'akin yana kare mata kallonta ta cikin mirrow yayinda kowani part na jikinsa ke sake bud'ewa da kar'barta a cikin zuciyarsa ..

jin shirun yayi yawa yasa ta d'ago Idanunta ta kalli cikin madubi domin ganin abinda yake , take idanuwansu suka sarke cikin juna , cigaba da kallon kwayar idanun juna suka yi qirjinsu na dokawa da matsanancin karfi ,ta kasa ɗauke Idanunta acikin nashi haka shima ya saka daina kallonta "a duk lokacin da zan kasance dake ina tsintar kaina cikin natsuwa mara misaltuwa ,ko fushi nake da zarar na kalli kyakkyawar fuskarki sai naji fushina ya kau , gabad'aya ji nake bana tattare da wata damuwar da zata dakushe farincikina muddin ina tare dake , sosai ya shagala yana zance zuci yana shafa cikinta zuwa kasan mararta , ta lumshe kyawawan idanunta tare da motsa ɗan ƙaramin bakinta "kana magana ne ? yayi saurin saisaita natsuwarsa ya kashe mata idonsa ɗaya yana cigaba da shafa cikinta da bashi da alamun tasawa "abinda faru d'azu sam banji dadinsa ba ya dakata yana nazarinta tayi shiru taki cewa komai tana cigaba da sauraransa "kinyi kuskure gurin wasa da abinda yake da mutunci da daraja arayuwarki karki sake irin wannan kuskuren da gangancin dan bazan dauki kalmar sorry ko rarrashi ba ...
"Zuciyata bazata jurar ana tangaliliya da aurena kiyi respecting d'insa zan ji dadi tsaki taja acikin zuciyarta ..

a hankali ya k'araso bakin gado ya kwantar daita ya soma ƙoƙarin cire agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunsa da wayoyinsa ya ajiye saman mirrow dinta kamar ya cire kayan jikinsa sai kuma fasa ya kwanta ajikinta yana sakin numfashi da ajiyar zuciya wanda kusan a tare suka yi , matsowa yayi kusa daita sosai batare da yayi magana ba ya manneta a jikinsa , ya d'aura hannunta saman fad'ad'd'en qirjinshi ,
yayinda hannunsa mai ciwo ke kan sumar kanta yana shafawa yana lumshe ido , sun kusan minti talatin suna kwance haka kowanensu da abinda zuciyarsa ke sakawa .
wayarsa ce tayi ƙara sharewa yayi ya cigaba da shafa sumar kanta zuwa wuyanta da gadon bayanta yana jin wani irin qaunarta na fizgarsa wanda yake jin zai iya komai akanta .

tayi shiru tana sauke numfashi yanayinta na sake ɗaukar sauyi na daban kiran ya katse, wani ya sake shigowa amman still yaki ɗauka ganin yaki ɗauka ta buɗe idanunta ,ta tashi daga jikinsa ta kai hannunta kan mirrow ta ɗauki wayar tana dubawa sunan suhaima ta gani yana yawo akan screen din wayar ,ta janyo numfashi da kyar ta sauke haɗe da cewa "matarka ce ka ɗauka mana "i cant ...
"I can't ta maimaita fadar haka a zuciyarta a zahiri kuwa cewa tayi " ya dai tabbata kana jin tsoronta kenan ?
ya ja dogon tsaki tare da ɗan mirgina gefe ya zuba mata manya idanunshi masu narkar mata da zuciya "me yasa kike min haka yau kika sanni da zaki dinga dangantani da kalmar tsoro? "suhaima fa matata ce......"

" naji amman kai me yasa bazaka ɗauka ka tabbatar mata da inda kake ba ?
"Babu dalili kuma karki sake min .......
"Ko kaki ko kaso ya dai tabbata kana jin tsoronta ta karashe faɗa tana matsowa gareshi ta dora lip's dinta akan nashi haɗe da busa masa numfashi yayi saurin lumshe idanunsa "idan har ka tabbatar da baka jin tsoronta ka ɗauka .......

ya sake lumshe idanunshi jikinsa a
mace ya kamota jikinsa, ta shige masa sosai tana lumshe lulu eye's dinta da son dagula masa lissafi "pick up the call ....
wani irin hot kiss ya soma bata a fuskarta yana jin soyayyarta da sha'awarta na kawowa zuciyarsa farmaki "ya mahruf ...ta kira sunansa cikin wata irin kasalalliyar murya "kasan me ake kira da soyayya ?

Ya furzar da iska yana kallon kwayar idanunta "da alamun baka sani ba ,yayi shiru yana jin wani irin sauyi a gabobin jikinsa "a soyayya akwai sadaukarwa,kyautatawa ,
tattali kaffa kaffa , yiwa zuciya abinda take so, ita zuciya ba'a takura a soyayya sannan ba'a hanata ta hanu saboda shi kanshi so idan ya bukasa da kanshi yake bayyana kanshi ...
Tun da ta soma magana yake sauraren yadda zuciyarsa ke tsalle da jin wani dadi na ratsa sansar jikinshi da zuciyarsa , ya sake matsowa jikinta yana jin kamar ya soma lasheta daga tsakiyar kanta zuwa yatsun kafafunta. "duk abinda na lissafa babu wanda baka wa subai'a ba ,ban taɓa maka irin taimakon da ka min ba ,ka yantoni daga makiya kashi da kashi sai dai .........
Ta tsinci kanta da kasa fadar abinda take son fada ta tsuke bakinta tana kallon cikin idanunshi " you still have time ya mah'ruf life is beautiful tana gama fad'ar haka ta mirgina ta sauko , yayi saurin riko yatsunta biyu ta tsaya batare data juyo ba .

yana rike da hannunta ya sauko ya mikar daita tsaye ya tsaya a gabanta yana kallonta "ban fahimci maganarki ba ki fito kiyi min bayani abinda kike nufi dani "nothing kana iya tafiyarka sai da safe daman nice na tsaida kai yanzu kuma na sallameka sai dai daga rana mai kamar ta yau karka sake zuwa inda nake ko magana ban yarda ba matsawar bakasan yadda zaka yi da aurenka dake kaina ba ,ba na matsu da kasancewa da kai bane"no no kamar yadda kace shi aure ba abun wasa bane abun mutuntawa ne , kana da ilimi daidai gargado an very proud of you yaya ta wannan bangaren amman ilimin naka ya zama na ......

Yayi saurin toshe mata baki ta hanyar d'aura nashi yana zaro mata ido kafin daga baya yace "okay dan Kinga na biye miki shine zaki nemi raina min hankali har da zagin aurena ? ya karasa fadar haka yana sake kai bakinsa kan lip's dinta bata ce masa komai ba ta cire bakin daga cikin bakinta sannan ta zare hannunta ta zagayeshi ta shige bayi haɗe da murda key ta jingina bayanta da kofa tana shafa fuskarta " na hakura bazan sake yarda na kusanci inda kake ba har sai na tabbatar da soyayyata ta gama bunkasa acikin zuciyarka , nayi wa kaina alkwarin nan kusa zaka furta da bakinka ...

Jikinsa na rawa ya matso jikin kofar bayi "fatlion ki buɗe min kofa "kayi min idan na bude ka tafi gurin firgitacciyar matarka da kake jin tsoronta "nace ki bude min yayi maganar a tsawace "bazan buɗe ba ya ja tsaki yana juya ya kai hannunsa ya dafe goshinsa tare da rike kugunsa ya soma zagaye d'akin can ya sake komawa jikin kofar "ki bude dan babu inda zani ana zan kwana tayi masa banza har minti talatin ta wuce bata fito ba , wata minti talatin ta sake wuce amman tana ciki bayi taki fitowa ganin idan har bai fita daga dakin ba zata iya kwana acikin bayi yasa ya kwashi wayoyinsa ya buɗe kofar d'akin da karfi ya fita.

Tana jin motsin buga kofarsa ta fito tana sauke numfashi ,ta kwanta

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment