Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yasa ta kuma samu matsayi mai girma acikin zuciyarsa ya sake daita sosai ...

Watan suhaima daya hajiya rahma tazo gidan ko cikakken minti goma batayi ba jiddah ta shigo suka gaisa tana fita ta banka mata harara ta bata kule kulen data kawo mata , tace kawo kunnenki kiji da sauri suhaima ta mika mata kunnenta ta faɗa mata yadda zatayi amfani dashi suhaima tayi murmushin gaskiya yayarmu ina alfahari dake , kamar kuwa kinsa zan bukaci magani nan kinsa randa ya kusanceni sai danayi da gaske tukunan na shawo kanshi karki damu wannan magani zai taimaka sannan akwai aikin da babalawo wanda zai miki a gabanki sai dai yayi tafiya an kirashi aiki kasar ghana da zarar ya dawo shine next budget dinmu sai kin sha mamaki "wayyohlly Allah yayarmu akwai tunani mai kyau ta dade suna hira sannan ta tafi ..

A wata safiya bayan Mah'ruf ya fito daga masallaci ya zarce gidansu kai tsaye part din mama ya shiga ko'ina shiru baka jin motsin komai ya shiga dakin mama bata nan dan haka yayi tunanin ko tana dakin ummita ne dan haka ya hayewarsa gadonta yaja bargo ya lullube jikinshi har kanshi tare da lumshe idanunshi ya rasa me ke masa dadi,kullun zuciyarsa a cunkushe take da bakinciki da bai san ko na meye ba , tsaki yaja yana sake takure kanshi guri ɗaya a hankali bacci ya soma ƙoƙarin daukar shi,bai jima da runtse idanunshi ba bacci ya daukeshi gabadaya , kunsan yadda bacci safe yake da dadi da natsar da zuciya cikin bacci ya juyo da fuskarshi a daidai lokacin da ummita dake lullu'be cikin bargo ta juyo itama suka fuskanci juna suna shaƙar numfashin juna batare da sun sani ba, haka nan wani bacci mai dadi ya sake kawo musu ziyara, ya sake matsota sosai itama cikin bacci taji dumin jikin mutun ajikinta ta shige jikinsa sosai tana shaƙar kamshin turarensa ahankali ta kara shigewa jikinshi tare da yi masa riko mai karfi kamar za'a kwace mata shi ,fuskarsu na kallon juna hancinsa na kan nata bakinsu kadan ya rage basu manne da juna ba ,a hankali ya soma jin wani irin yanayi ajikinsa cikin bacci ya kamo fuskarta sosai ya haɗe bakinsu guri ɗaya ya soma kissing dinta har ya sauko saman dukiyar fulaninta, take yanayinta ya sauya a hankali take sauke numfashi yayinda mah'ruf ke cigaba da wasa da jikinta yana rabata da kayan jikinta har ya cire mata kaya tsaf ya sake matsota sosai ya soma sarrafa albarkatun kirjinta dake tsaye cak
a kirjita ga taushi ga ciko bai san lokacin daya soma sarrafa su ba tare da sake haɗe bakinsu waje daya ya shiga tsotsa kamar mayunwacin zaki yana shafa kirjinta yana sauke ajiyar zuciya ,yana tashan budurinsa cikin bacci, yayinda amarya suhaima take kitchen dan had'awa mai gidanta abinci bata kammala ba sai kusan tara tashiga wanka ta fito ta zauna gaban mirrow tana neman layinsa shi kuwa yana can
kamkame ajikin ummita ta manne masa batare da tasan ta aikata hakan ba ,hannuwansa duka biyu bisa dukiyar fulaninta ,manne masa tayi tana cigaba da amsar sakoninsa, gadon bayanta yake shafawa zuwa sansar jikinta ya sake zartar da hannunsa kan dukiyar fulaninta bakinsa ya cire cikin bakinta ya daura kan nipples dinta wani irin abu taji yana ratsa gabadaya ilahirin jikinta har tafukan kafafunta take jin komai ,mutsu mutsun kwace bakinta take daga cikin bakinsa saboda azabar zafin da taji yana ratsata ,hakan yasa shi soma kokarin bude idanunshi a hankali yayinda ita kuma ke makale da jikinshi bakinsa na kan nipple dinta a matukar zabure .......


TWO FRIENDS (BSBS)


💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL


AL'QALUMAN



*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*


~DEDICATED TO~
*MRS SULAMAN*


WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim


PAGE 39

............ Ya bud'e idanunshi yana akan kyawawar fuskarta yana kallonta zuciyarsa na wani irin dokawar da matsanancin karfin gaske , take jikinsa ya ɗauki kyarma, a hankali ta sake matsowa ta shige jikinsa tana shaƙar kamshin turarensa ,cikin wani yanayi mai wuyar misaltuwa ya lumshe idanunshi na second biyu ,sannan ya bud'esu yana ciza gefen lip's d'insa na kasa da karfi dan tabbatarwa kanshi gaskiyar lamari ,"shin mafarki yake ko kuwa a gaske shine tare daita manne da juna a cikin wani yanayi ?

zafin jikinta daya ji ya ratsashi ne ya fahimci lallai gaskiya ne ba mafarki yake ba ji yayi tamkar numfashinsa zai ɗauke a hankali ya soma ja da baya tamkar wani barawo , hannunshi dake saman kirjinta yayi saurin d'aukewa yana sake ja da baya tare da ƙoƙarin saukowa daga saman gadon zuciyarsa na wani irin tsalle, har cikin hanjinshi yake jin rawar da jikinshi ke yi , cak ya tsaya sakamakon gefen rigarshi da yaji an rike ta baya , ya waigo da matsanancin fargaba , naunauyen ajiyar zuciya ya sauke ganin still idanunta a lumshe suke, gabadayan ji yayi kamar numfashinsa zai bar gangar jikinsa ,ya kai hannunshi ɗaya ya zare hannunta , ya k'arasa saukowa sannan ya tsaya a gabanta yana gyara kwalar blue shirt din dake sanye ajikinshi , yayi mugun tsurawa kirjinta ido .

cikakken 5 mint ya ɗauka yana kallonta zuciyarsa da tsantsar fargaba "ya Salam Allah yayi halitta agurin nan bai taba matsamanin cikar halittar jikinta ya kai haka ba , kirjinta cike bammmmm da dukiyar fulanin babu alamun zasu zube ,sai sheki suke ga wani haske na musamman da suke dashi ,ahankali yake kallonsu har zuwa kan nipple's dinta dake tsuke jajir dasu abun sha'awa sake ji yayi tamkar ana zarar ranshi ya kai hannu ya soma shafa sumar kanshi "wayyo Allah wani abu yaji yana harbin jijiyarsa da wayo cikin jikinsa ....

ci-gaba kallonta yayi da tsantsar mamaki a saman fuskarshi ganin zata iya farkawa at any time yasa ya janyo bargo a hankali ya lullu'be mata jiki dashi dan bazai iya tsayawa saka mata kaya ba ,ya juya da sauri kamar wanda aka koro ya bar d'akin yana dafe daidai saitin zuciyarsa a parlour'n kasa yaga mama zaune ita da wasu mutane guda biyu suna ganin saukowarsa suka gaisheshi kana suka mike sukayi mata sallama ..

" yaushe ka shigo gidan baba ? tayi masa tambayar tana tsareshi da idanunta ,
"Ban dade ba daga massalaci na biyo na shiga d'akin banga kowa ba "daga massalaci mah'ruf me yasa kake irin haka?
" duk kwanakin nan na lura da kai haka ke yi zuwan sassafe , haka fa babu dadi ,suhaima ba zata ji dadi ba.
"yanzu mama dan nazo gurinki shine zataji haushi aiko tana da aiki dan zuwa ya zama dole safe dare dole ne nazo naga mamana ya k'arasa maganar yana shafa sumar kanshi .....

Murmushin jin dadi mama tayi "kai dai kabi a hankali ka dan ɗauke kafa ,da da yanzu ba ɗaya bane duk wata biyu ne fa da auren "no mama Karki sa na soma jin haushinta wallahi har an yi macen da zata qalubalanceni akan zuwa gurinki bare matar dake zamana ?
"to shikenan amman dai ka rage zuwan safen nan har gara na dare nan suka bar zance suka shiga wata hira har ta d'auko masa batun tana son zuwa cotonue duba jikin mahaifinta ....

A matukar firgice ummita ta farka "oh no .....
Sannan ta buɗe idanunta,
da mamaki take kallon jikinta babu komai an cire mata rigar dake sanye a jikinta, tayi shiru tana tunani ita dai tasan da kaya ajikinta ta kwanta bayan ta idar da Sallah hannunta ta kai kan rigar baccinta data gani a saman gadon yashe tana kallo, tabbas tana jikinta koda asuba datayi sallah to garin yaya ta fita ajikinta ?

Ta dade zaune tana kallon jikinta da nazarin sauyin da jikinta ya samu , sosai kwalkwaluwarta tashiga tunani kafin daga baya ta fahimci mafarki data saba yi tayi, rigar baccin ta mayar ta sauko ta nufi bayi .....
Mama da Mah'ruf kuwa suna tare har lokacin suna hirarsu Ummita ta sauko daga sama cikin wata had'add'iyar doguwar riga pinky colour har kasa abunka ga fara mace , rigar tayi mugun kar'bar jikinta ga wani sihirtaccen kamshi da jikinta ke fitarwa kallo ɗaya tayi musu ta ɗauke kanta tana hura hanci .
mama ta kirata adaidai lokacin da take ƙoƙarin shiga kitchen ta dawo da baya jikinta na wani kad'awa mai ban sha'awa , ta tsaya can nesa kaɗan da inda suke zaune akan kujera .
" Ya kina kallon mutane zaki wani wuce kamar baki san da zaman mu ba ,kin gaishe da baba da zaki wani ɗauke kanki ?
Muryarta a raunane tace "mama na gaishe fa tayi maganar tana rausayar da idanunta cikin nashi wani irin zirrrrrrrr yaji a gabadaya ilahirin jikinsa saboda yanayin yadda tayi magana babu sauki .
Mama ta kallin inda yake zaune tamkar mara lafiya tace " ummita ta gaisheka ne a sama ?
shiru yayi yana dan murmushin gefen baki wanda da gani kasan na takaicin karyar data yi ne .
hakan yasa mama ta fahimci batayin ba "kika ce kin gaishe shi?
fuskantar babu yabo babu fallasa ta sake cewa "eh .
"wallahi karya kike saboda da kin gaishe shi ina tambayar shi zai fara cewa "eh turo ƙaramin bakinta tayi cike da shagwa'ba tana shan kamshi "to mama kona gaishe shi baya amsawa shi yasa na daina.
"ina ruwanki da rashin amsawarsa ke dai ki gaisheshi .
"ina kwana...... ? Ta gaisheshi tana tsare shi da fararen idanunta waɗan da suka wadatu da gashin ido masu matukar kyau da bugar da zuciya , yadda ta tsareshi da idanunta bai isa yaki amasa gaisuwar da tayi masa ba dole tasa muryarsa a kasalance ya amsa da kyar" lafiya......
sannan ya mike yayiwa mama sallama ya wuce dan bazai iya jurar cigaba da zama yana kallonta ba hakan zai iya fallasa abinda yake ji akanta ..

Yana fita meenal ta shigo ta durkusa har kasa ta gaisheta da mama "ina kwana mama ?"an tashi lafiya ameena ?
"Lafiya lau mama ta k'arasa ta kamo hannu ummita cikin hannunta, "yar'uwa yana ganki haka kamar an 'bata miki rai "dole ki ganta haka saboda anyi mata magana agaban makiyinta ,ummita ta kwace hannunta daga hannun meenal ta juya cikin fushi mama ta kirata .
"ke zo nan"
ta dawo jikinta a sanyaye" zauna ta nuna mata kusa daita ta zauna tana cika tana batsewa
" ke wace irin yarinya ce ace mijinki ba zaki iya buɗe baki ki gaisheshi ba saboda baki da tunani da hankali ,koma meye ai yanzu matsayin mijinki yake ,ko shi kike jira ya gaisheki ?
Ta girgizawa mama kai alamun a'a ,"mutumin daya zamo sanadiyyar farincikina acikin gidan nan ,babu yadda ba'a so aci zarafina ba, babu yadda ba'a so arabani dashi ba amman ya tsaya tsayin daka yace lallai ni din wata ce agurinsa shine abun wulakantawa agurinki ,ke yanzu bancin sanadiyyarsa da tuni waɗan can yan iskan yan daba basu lalata miki rayuwa ba ?
yaro mai kirki da son zumuncin irinsa babu kamarshi ,kinsan adadin dadin da na ji araina daya kasance miji a gareki ?
"Kinsa adadin matan dake can suna neman irinsa basu samu ba ?
amman saboda ke baki da hankali kin samu a sadaka shine har kika maida shi abokin gabanki .
murya meenal a matukar sanyaye tace "ai suna magana fa ....
"Karya kike yi ameena ina lura daita gurin wata uku kenan banji tace masa wani abu ba tun kafin a d'aura musu aure ," me yayi miki ki fada min laifin da yayi miki ?
" ina dalilin wannan tsana haka ?
Hawaye ya cicciko a idanunta "tambayarki nake me yayi miki kika tsaneshi haka ? "Ko so kike ya rusuna miki saboda gaki yar mai da ba'a son bacin ranta ?
"Babu komai tayi maganar hawaye na gangarowa bisa kuncinta sannan muryarta na rawa tace "kiyi hakuri mama wallahi laifin shi ne fa ko nayi masa magana baya kulani ,ko na gaisheshi baya amsawa.
"ko ba zai amsa ba ki dinga gaisheshi matsayinsa na da daban na yanzu daban, ko baki ga yanzu ku biyu ne agurinsa ba wace tafi kyautata masa ita zai fi so ,ki duba kiga Kullun sai munyi waya da yarinyar nan suhaima nan a gidan me yasa take kirana ?
"Tana yi ne dan tasan matsayina agurinsa, kuma tasan duk kyautatawar da tayi min zai ji dadi , ke me yasa bazaki dinga yi masa abinda zaiji dadi ba ?
"Da wannan mugun halin nasa ai komai zan masa bazai farinciki ba ta fadi haka aranta .

"ki daina yin banza da lamarinsa ki dinga shige masa ,da haka zai sake dake ,yanzu da ace kin tare a gidansa haka zakije ki dinga banza da lamarinsa ki dawo koma baya a zuciyarsa ?
"To wallahi maza ki canza salo dan kina ji kina gani za'a fara gefe da wannan bakin halin naki "

"kiyi hakuri mama inshaallahu zata canza kuma gaskiya kika faɗa mata , dan baki ga yadda matarsa take masa biyayya bashi ba , hatta mu bata barmu ba , randa mukaje gurin aunty jidda ta matsa mana lallai sai mun shiga part dinta wallahi dukkanmu babu wacce ta kira sunan mu, wai aunty meenal aunty Maryam dukkanmu muka bita da kallo cike da mamaki ....

"To kinji ko ,ku da yakamata ku kirata da aunty bakuyi ba, ita ta sauke nata girman ta baku , kin dai ji ki canza idan zaki canza idan kuma bazaki canza ba ruwanki , duk abinda kike takama dashi baba yafi jinshi , babu yadda zakiyi dashi baki isa ki zageshi ba ,ko bai aureki ba jininshi ke , haka kema jinisa ce ke , dole kiyi hakuri dashi komai lokaci ne wata rana sai labari duk abinda yake miki idan kin jashi ajiki kuma kin canza hali shima zai daina kuma zai canza ..
" Zata canza mama inshaallahu , "Allah yasa " meenal tace Ameen .

Goge hawayenta tayi da bayan hannunta tace " dan Allah mama kiyi hakuri nayi miki alkawarin zan canza amman dan Allah ki tambayar min shi batun rubuta jam dina sabon wata za'a soma .
"nice ma zan tambayarki Miki shi ?
"ke baki da baki sai nice na iya magana ko?

"Kin jita ko ameena ?
" kin ji yarinyar da tace zata canza yanzu , ana maganar ta canza tana maganar jam kada Allah yasa ki tamabayeshi da kanki kiyita zama har sanda mahdi zai bayyana babu ruwana .

"to ni mama wallahi tsoro nake ji kinsan halinsa "ke dai ki tamabayeshi idan kina bukata , idan kin tashi ki tambayesa har da batun zuwanmu cotonue idan ya barki sai muje tare idan shima kin ki ,ga gurin nan kiyi sha zamanki tana gama fadar haka ta mike ta haye sama ....

Ummita tayi shiru haɗe da zuba tagumi hawaye na zubo mata ita yaya mama take son tayi da rayuwarta ?
"Ita ba maganar ce ba zata iya masa ba wulakancinsa take gudu ..
"Ki cire komai ki tamabayeshi karki ji tsoronsa ina ma jarumtarki taje?
" kiyi facing dinsa eye's to eye's ki fada masa me zai yi ?
" karkari yace ya yarda ko akasin haka ....
"Shikenan meenal zan yi kokarin "kin dai zama matsoraciya karfi da yaji yanzu " Allah ba tsoronsa nake ji ba wulakancinsa nake gudu kuma ko nace zan rama babu riba , "haka zaki d'aure ,ummita ta mike ta shiga kitchen ta debo musu abinci ta dawo suka cigaba da hirarsu suna cin abinci ..


Juya sitiyarin mota kawai yake zuciyarsa na wani irin tsalle haɗe da tuno masa yanayin tsarin jikinta da abubuwa da suka faru tsakaninsu dan babu abinda ya 'bace masa, komai daya faru a baccisu tar yake kallonsa yana jin kamar ya juya ya koma ya cigaba da playing boob's dinta .
har kawo gida yana jin fellling din abun aransa babu abinda yafi tsaya masa arai kamar dukiyar fulaninta ko cikin gida suhaima tasan yana cikin wani yanayi dan kai tsaye d'akinsa ya shiga ya zube kan katifa yana fidda numfashi zuciyarsa na sake hasko masa ita , tana ganin ya saman d'akinsa ta bar abinda take ta mike tsaye ta shigo d'akin, ganin yanayinsa yasa ta kasa isa inda yake, tasan tunda ya shigo bai kalli inda take ba akwai matsala , idan tayi kuskuren nufarshi zai iya 'bata mata rai tare da bata hutun sattittuka dan haka sad'af sad'af ta juya ta bar d'akin har kusan awa ɗaya din daya dawo gidan bai nemeta ba yana d'akinsa yana shirya kanshi dan zuwa office ..
Tun daga ranar bai sake samun sukuni da natsuwar zuciya ba ,duk sanda ya runtsa idanunshi ita yake gani tayi masa gizo da aika masa sakonin masu tsayawa a rai.

*****

Ana washegari ranar da mama zasu wuce cotonu Mah'ruf ya shigo jikinshi sanye da riga deep blue da jeans baki ya d'aura jaket a saman riga ,kafafunshi sanye cikin blue canvers da ratsin baki , kafadarsa rataye da bakar jaka gashin kan nan nashi kwance luf luf suna zuba sheki sai dai ya rufe da facing cap ,amman duk da haka ana iya hango kwanciyarsu ta bayan keyarsa , yayi kyau sosai sai kamshi yake zubawa .
ya zauna kusa da mama yana furta "washhhhh Allah mamana na gaji ina wuni lafiya lau ya gajiyar office dan nasan daga can kake ?
suka gaisa da mama sosai batare da ya kalli inda ummita ke zaune zuciyarta na dokawa ba ,wani abu daya tsaya mata a makoshi tun shigowarsa tayi kokarin had'iyewa sannan tayi karfin halin sanyawa jikinta jarumta tace "ina wuni ?
"Lafiya ya fada atakaice yana gyara zamansa "ka ganmu muna ta shirin tafiya kou?
"Ai nima banci zuwa office da tare zamu na dubo tsoho ..
Mama tayi murmushin jin dadi ,ummita ta mike mama ta dubeta "ki fa kwanta cikin shiri dan karfe huɗu zamu wuce, yayi saurin bude idanunshi ya kalli mama sai dai bai yi magana ba illa maida idanunshi kanta da yayi yana kare mata kallon tsab sai data wuce sannan yace "ai gara ki tafi daita mama zaki fi samun natsuwa yayi maganar yana lasar lip's d'insa na kasa "ta dai faɗa maka dan nasan halinta ?
lumshe idanunshi kawai yayi ya amsa da "uhmmmm dan baya son aja maganar ..
Anan yaci abinci dare sannan mama ta mike tace " bari naje muyi sallama da hajiya inna "zaka tafi ne ko kana nan tukun har na dawo ko kuma zaka taso muje tare ?
"bazan shiga ba mama ina shiga zata kashe ni da matsalolinta ni Kuma yanxu zuciyata bata son damuwa , ba tace masa komai ba ta fice .

Tana fita ya mike tsam ya haura sama ,kai tsaye d'akinta ya nufa ya tura kofar ya shiga ya maida Kofar ya rufe ya jingina bayanshi da jikin kofar ya tsura mata manya idanunshi tana ganinsa gabanta ya shiga dukan uku uku , ta juya da sauri tare da kwanciya akan gado ta runtse idanunta ganin haka yasa ranshi ya ɓaci

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment