Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

inshaallahu zani gidan baban sarki muji daga garesa .
injiniya da Abba har ma da baba sarki da wasu daga cikin ya'yan baba sarki ,ciki har da mahaifin sakina , injiniya yayi dogon turanci sannan yayi shiru yana gyara zama ,"baba tawa shawarar tunda sakina ta hakura dan kanta me zai hana mu hakura da batun auren dan bamu san abinda Allah ya boye ba amman bamu da ja sai abinda ka zarta , gaba-daynmu agurinka muke neman mafuta dan yanzu al'amarin ya fi .....
Abba yayi saurin katse maganar mahaifin sakina " ina ganin kafin muyi haka ya dace mu fara miƙa al'amarin wajen Ubangiji mubi tsarin sunar maaiki a kowane al'amari daya umarcrmu, mu bawa Allah zabi kafin mu aikatashi, kada mu bi son zuciyoyunmu Kuma daman shi son zuciya yana kai mutun ga halaka ko ba haka ba ? Abba ya kallin injiniya da sauran mutanen dake zaune a dakin wanda sai lokacin injiniya yaji sanyi a zuciyarsa "haka ne zamuyi Allah kuma ya barmu akan daidai ,"ameeen suka hada baki gurin fadar haka , baba sarki ya numfashi bayan ya gama sauraronsu sannan yace "shikenan Allah yayi rayuwarku albarka suka amsa da ameeen "inshaallahu zamu dage bisa kafafun domin tsananta addu'a amman zuwa yanzu na dakatar da batun aure tsakanin Ma'hruf da sakina har sai munga yadda hali yayi saboda na fahimci yarinyar da uzurinta nan suka cigaba da tautauna cike da tsantsar kaunar juna ..

******

Hankalinsu injiniya da Abba bai tashi ba sai a wata ranar asabar inda sakon mutane biyu suka ziyarci gidansu sako na farko daga amercan ne yayi musu diran makiyya wato hafiz almustapha ,sakon hafiz almustapha ya iske ummita ne ta hannun masoyinta rayhan wanda kaɗan ya rage bai had'iye zuciya ba ,yana mika mata sakon ya juya dafe da qirjinshi daidai saitin zuciyarsa da yaji yana masa zafi bayansa tabi da kallo batare da ta bude ba tana jin babu dadi aranta ,tasan har ga Allah ya rayhan na hakuri, yana danne zuciyarsa akan masoyanta bai fiyye nuna mata damuwarsa ba .

Tana tsaye agurin sakon Muhd Sa'id ya isketa ta hanyar masoyinsa saifullahi ..
wata ƙatuwar jaka ce mai dauke da nauikan kayan kwaliya iri daban daban ciki har da ɗan kunnen da sarka na zinari tare da yin mata fadan alkhairi bata san sanda takaici yasa ta fara dukan saifullahi ba "shegen yaron nan ka likewa mutumin nan ,idan ma dan ya kan kai ne kai zai fara sacewa ,da zarar na ganka gabana ke fad'uwa saboda baka zuwar wa mutun da alkhairi , idan na sake ganin kafarka a part din nan sai nayi gunduwa gunduwa da namanka ,shege mai katon kai , dukanshi take kamar shine muhd Sa'id din .
"Daina dukansa ummita Karki karya musu yaro kisa mushiga uku "mama sau nawa ina yi masa kashedi tayi maganar kamar zatayi kuka Kamar guguwa ta nufi hanyar step ta haye sama , hannunta rike da sakon takarda hafiz almustapha da aka rubuta (only subai'a ..)
Tana zaune abakin gado. hawaye na tsiyayo mata akan kuncinta mama ta shigo ta tsaya akanta "to kuma meye abun kuka ?
"Ni mama yaya zanyi da rayuwata daga wannan sai wannan Ni Ni dama bakin jini gareni na huta da wannan jarabar "uhmmmm ummita Karki fadi kalmar da Allah zai yi fushi dake sannan ya tuhunmeki akai tunda bake kika halicci kanki ba asalima ba wayonki ko dabararki tasa Allah ya gaddaro miki haka ba iko da hikima irin tashi Ni babu abinda zancewa Allah sai godiya domin idan bakinjini kikayi a gidan me kike tunani ?
"Dan haka daga yau Karki sake furta wannan kalmar hakan yasa ta cigaba da rera kukan takaici ,kukan dake konawa mama rai ..

Tun safe take kuka har dare da take durkushe a gaban Abba "bana son kukan nan ummita ina tsoro kar yawon damuwa ya haifar miki da ciwon zuciya ,na baki hakuri mammanki ta baki ,
uwar marayu ma ta baki hakuri ,ga yar'uwarki da kullum kuke kuka tare ya isa haka inshaallahu komai ya kusan zamowa labari ki dai cigaba da hakuri da addu'a Allah ya mana zabi mafi alkhairi, da sanyi jiki ta baro parlour'n da gudu tana wani irin kuka bata son rayhan bata son muhd sa'id bata son hafiz almustapha amman su kullun cikin kusanta rayuwarsu suke daita ....

karo tayi da mutun a tsakiyar parlour'nsu a gaugauce ta d'ago fuskarta sakamakon kashin turarensa daya kawowa hancinta ziyara, take idanunsu suka tsarke cikin juna wani irin abu suka ji yana d'awainiyya da gangar jikinsu , ganin shine yasa kukanta ya tsananta batasan lokacin data zube ajikinsa ba tana fidda numfashi ,
shi kuwa Ma'hruf shiru yayi ya kasa magana sannan ya kasa bambareta ajikinsa , sai dai jikinsa rawa yake yana jin wani sanyi ratsa sansar ajikinsa, sai daya bari tayi kuka mai isarta sannan ya kai hannunsa daidai kafad'arta ya rike tare da d'ago kanta suka sake hada ido ya talla'bo fuskarta kusan minti biyar suka ɗauka suna kallon kwayar idanun juna sosai ya tsura mata manya idanunshi yana kallon hawayenta, a hankali ya shiga girgiza mata kai saboda ganin tarin hawayen dake kokuwar tsiyoyowa daga cikin idanunta ,wani abu ke fizgarshi akanta yana jin kamar ya mallaka mata farinciki , a hankali ya sauko da hannunshi ya rike tsintsiyar hannunta ya nufi d'akinta ya zaunar daita ya janyo kujera ya zauna yana facing dinta.

Muryarsa a kasalance yace "kinsan banason yawon kuka "tayi saurin had'iye wanda ke kokarin fitowa "meye damuwarki ko duk akan rashin son auren rayhan ne ?
Ta girgiza kai "ki bude baki kiyi min magana kamar yadda nayi.
"bashi bane ta bashi amsa hawaye na gangarowa bisa kuncinta yayi shiru yana kallonta bai ce mata komai ba tà ɗan d'ago tana dubansa tasan abinda shirun nasa yake nufi ,ita yake jira muryarta cike da sautin kuka tace "akan muhd sa...Sa'id ne da hafiz almustapha ,ni matsalar muhd Sa'id ne yafi damuna akan ta hafiz ..
"Saboda shi kike so ba ..?
Yayi maganar a fusace yana zaro mata ido take gabanta ya shiga dukan tara tara ta shiga jan jikinta tana kokarin ja baya saboda ganin yadda yanayinsa ya sauya alokaci daya .
haɗe kafafunwata yayi guri daya ya janyo ta matso gabansa sosai har suna iya jiyo hucin numfashnsu .
"tsabar mugunta ga wanda ke sonki can kamar zai mutu amman ke wani gato kike so ko..... ?
Ta sake girgiza masa ya kai hannunsa ya damki kafad'arta da karfi ta saki ƙara mara sauti tare gigicewa "idan kika bari bakincikinki yayi silar dana rasa rayhan zan baki mamaki ya k'arasa maganar yana zuba mata kyawawan idanunshi da suke kara narkar mata da zuciya a hankali ya furzar huci mai zafi
ta fashe masa da kuka saboda zafin rikon da yayi mata tasa hannun tana kokarin raba hannunsa da jikinta tana kuka sosai ,ya mike ya tsaya a tsakiyar dakin ya zira duka hannunwansa cikin aljihunsa wandonsa yayi taku ɗaya biyu ya tsaya yana tsareta da idanunshi da sauri ta soma share hawayenta tana shesheka tare da sunkuyar da kanta dan bazata iya jurar irin kallon da yake aiko mata dashi "kiyi addu'ar kuyi aure da rayhan yana raye if not I will del with you Idan wani abu ya same shi akanki yana gama faɗar haka ya juya ya bar dakin ..

ta zube akan gado cike da takaici "to ni meye laifina da zaka kakaba min maseefa ina zaman zamana ?
""Kama barni damuwar dake damuna bai sai ka ƙara min wani akan wanda nake fama dashi ba ,bana son ya rayhan amman bazan iya gujewa aurensa ba,yana son bana sonshi haka zamu hakura ....... *WANNAN CE QADDARARMU* dani dashi ,sosai take matso hawayen idanunta ...
*****

Bangaren rayhan kuwa tunda ya shiga d'akinsa bai sake fitowa ba ya kwanata ,sallah ne kawai ke tada shi ,dafe da saitin zuciyarsa inda yake jin zafi, yana son ummita soyayya mai tsanani ,soyayyar da bazai iya hakura daita ba gaba-daya da ita kadai zuciyarsa ta shirya rayuwa bazai iya cireta aransa ba duk runtsi duk wuya zai yi hakuri .
ya kamkame jikinsa yana jin feeling dinta tun daga ranar bai sake samun ishashiyar lafiya ba ,kullun ciwo da zuwa ganin likitan gashi yan'uwa sun rasa abinda ke damunsa sunyi tambayar duniya yaki cewa komai hatta saurauninyarsa yaki sanar mata ,yana kwance a dakin mahaifiyarsa ma'hruf ya shigo dubasa ya soma gaishe da Hajiya saudat sannan ya zuba masa ido yana kallon yadda ya rame ," ba zaka daina dogon tunanin nan ba ko ya tsaya akanshi "wa ya faɗa maka tunanin nake ? "bana tunanin komai kuma babu abinda ke damuna cikin takaici hajiya saudat tace "rabu dashi yana boyewa ne amman ni nasan tunanin ummita ne ,yana cutar da kanshi, ni daman ba son auren nake ba ,da zai hakura jarabbiyar yarinyar sai nafi kowa jin dadi da farinciki "girgiza mahruf yayi "ki daina ce mata jarabbiya domin ita din ba tace dole sai ya sota ba amman tunda Allah ya kaddaro masa babu yadda zakiyi hawaye ne suka zubowa rayhan ma'hruf yasa hannu ya share "ka daina damuwa dan Allah ya runtse idanunshi batare dayace komai ba har sanda ma'hruf ya fita "kana zauna kana kunsawa kanka bakincikin akan wannan tsinanniyar yarinyar mara amfani haka tayi ta zagin Ummita tana tsine musu ....

a wani yammaci Ummita ta shiga d'akin ya rayhan domin duba lafiyar jikinsa , bata iskeshi a dakin ba,jin motsin a bayi ta ɗan tsaya ,kusan minti goma tana tsaye can ta soma jin tarinsa haɗe da kakarin amai ,,da sauri jikinta na rawa ta isa cikin bayin , zaune ta ganshi dafe da goshinshinsa yana amai wani bakin a madadin abinci ,da sauri ta juya yayi saurin riko tafin hannunta ,"kira min Ma'hruf da sauri ta koma dakin ta shiga neman layinsa kira daya ya ɗauka "kazo inji ya rayhan gashi kwance yana amai kmr na jini tayi maganar cike da tashin hankali hawaye na zubo mata .
ko cikakken minti goma ba'a yi ba Mahruf ya shigo lokacin rayhan yana kwance akan gado yana mata magana mai kama da wasiha tsaye ma'hruf yayi yana kallonsa kafin daga bisani yayi wa ummita kallo ɗaya ya ɗauke kanshi zuwa ga rayhan dake kwance yana fidda numfashi , a hankali ta durkushe kasa bisa gwiwowinta tana wani irin kuka ,har cikin zuciyarsa yake jin kukanta dake bala'i kona masa rai ..

" Ma'hruf Bani da lafiya ina bukatar ganin likita, Mah'ruf bai ce komai ba, ya kira doctor Husain kasancewar shine likintansu na gida cikin kankanin lokaci ya iso yashiga dudduma shi ..
zaune Mah'ruf da doctor suke a gaban rayhan sun tsura masa ido suna Kallonsa .
bayan likita ya gama aune aunensa cikin damuwa ya nemi Mah'ruf ya basu guri batare da bata lokaci ba ya kalli inda ummita ke tsaye tana kuka ,take ta fahimci abinda yake nufi tun bai kai ga fita ba ta rigashi ta tsaya a waje shima kofar dakin ya tsaya yana zariya hankalinsa tashe yana tunanin abinda ke damun Rahyan haka , dan har ya fara cire rai dashi a yanayin daya ganshi "anya iya matsalarsa da Ummita ke damunsa ?
Yayiwa kansa tambayar da bashi da mai bashi amsa , sosai ya shiga damuwa yana masa addu'ar samun sauki ,ita kuwa ummita kuka take sosai kamar ranta zai fita ..
muryar doctor can kasa yace "rayhan abinda ke damunka yana dada cin jikinka cutar nan taka tasoma bani tsoro kullun idan na dubi iyayenka sai naji gabana yana faduwa sai na dinga jin kamar ina cutar iyayenka da munafurtansu ne , me yasa kake son boye musu abu mafi muhimmanci ga rayuwarka , rayhan ka duba lamarin danginka ...
Irin tarin yanuwan da Allah yayi maka me ka nema ka rasa , ka duba i soyayya irin ta iyaye ga dansu , ko dan soyayyarka garesu zasu maka addu'a idan suka san damuwarka da kuma ciwon dake damunka zasu yi maka addu'a , ka bari su sani ya qarasa magana yana riko tsintsiyar hannunsa yana duba jijiyar da zai bukata domin qara masa drip ..
"Doctor ka taimakeni karka sheida masu , ina tausaya musu ina tausayawa halin da zasu shiga na fi jin tausayinsu akaina, karka manta kai ne kayi min alkawarin bazaka sanar musu ba ......
"Ka fi son Sai lokacin da mutuwa ta riskeka sannan suji abakina ko abakin wani likita ?
ni kaina ina jin tsoron abinda zai faru gaba kusan abu daya ke damunka da ummita " karkaji komai doctor, bazan mutu yanzu ba sai kwanakina sun cika ,ciwo ai ba mutuwa ba , wallahil azim kaji rantsuwar musmulimi naji sauki sosai akan farkon lamarin , sai ɗan abinda baza'a rasa ba , ciwon kai ne da zafin zuciya shima a cikin dan kwanaki nan , doctor Kamin adduar kar na mutu har sai na haifawa iyayena abinda zasu kalla suyi farinciki bayan raina ...
Girgiza kai likita yayi "Allah yasa amman ya kamata dai su sani "don't worry doctor akwai lokaci idan lokacin yayi ni da kaina zan faɗa musu bare ina addu'ar samun lafiya , cigaba da bashi kulawa likita yayi kamar koda yaushe " har sanda ummita da mama da mahaifiyarsa suka shigo dakin ,
mahaifiyarsa ta rushe da kuka "yanzu rayhan baka lafiya sai a bakin wasu zanji ?
"Ya lumshe ido cikin azabar ciwo "guri ta samu ta zauna kusa dashi tana cigaba da yi mata sannu kowa sannu yake masa hankalin kowa a tashe yake most especial ummita ..



TWO FRIEND'S (BSBS)


💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

FREE NOVEL


AL'QALUMAN



*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*


~DEDICATED TO~
*HAJIYA UMMI, JIDDONA INA ALFAHARI DAKE SISINA ,DUK DUNIYA BANIDA TAMKAR KI ,KECE NI ,NICE KE, ALLAH YA BARMU TARE YAR'UWARTA , INA KYAWUN YINKI MY LOVE*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim


PAGE 30

.....A hankali bakinsa ke furta sunan ummita ...,
Da sauri ta matso kusa dashi sakamakon sunanta data ji ya am bata ,"sannu yaya, Allah ya baka lafiya , inshaallahu zaka warke tayi magana hawaye na zubo mata ..
wata uwar harara hajiya saudat dake zaune a kusa da kafafunsa ta banka mata haɗe da buga mata tsawa "dan Allah Malama ki matsa daga kusa dashi ,idan da hali ma kiyi nesa dashi, ban son kinibibin banza da iyayi da kankaba ......
" duk uban waye silar ciwon nasa bake ba ?
"Kun asirce min d'a bashi da iko da kansa bare lokacin kanshi, bashi da tunanin komai sai naki , ke wallahi idan na tsine miki sai tsinuwata ta biki ........

"maza maza ki tashi ki bar d'akin nan .....
"Munafuka Allah ji yadda ta marairaice kamar da gaske , wallahi da inda hali rayhan ba zai aureki ba ,kukan da rayhan ya fashe da shine yasa sukayi shiru suka yo kanshi .
"plz ma...ma .....
Tari ne ya tsarkeshi ya kasa k'arasa magana ..... kuka hajiya saude ta fashe da kuka ,ummita ma kuka ta fashe dashi had'i da durkushewa a wajen batare da tasan abinda zata yi ba tana mai bakin ciki kalar rayuwar mahaifiyar rayhan da inna .
sam rayhan bai da irin halinsu hasalima ba kalar rayuwarsu daya ba , kukan da suke yi ne ya janyo hankalin injiniya da Mah'ruf suka shigo gabad'aya sukayi kanshi, suna jera masa sannu babu wanda hankalinsa bai tashi ba ...

"Manufakar banza sai anyi magana ki sawa mutane gaba kina kuka...
"Dan Allah inna ya isa baki ga halin da muke ciki bane da me kuke so muji?
"Wannan munafukar zaka yiwa magana ta daina damumu da kukan munafurci, ta barmu muji da abu ɗaya ..

rai hannun Allah suka nufi asibitin doctor husain dashi , tun kafin su karaso tuni mah'ruf ya kirashi a waya koda suka iso harabar asibiti sun iske likitoci a ƙalla guda biyar tsaye da gadon marasa lafiya a gabansu suna jiran karasowarsu .
aka d'aura shi akan gadon marasa lafiya likitoci suka shiga turashi zuwa emargycny room lokacin har ya fara aman jini ...

Take aka shiga bashi taimakon gaugauwa, likitoci sun dauki dogon lokacin acikin d'akin suna duba shi sannan suka samu nasarar ceto rayuwarsa ,gabadaya family din kuka suke babu wanda bai zo ba har yan gidan baba sarki , tashin hankali kuwa ma'hruf ya fi kowa shiga , bai san yana tsananin son rayhan da bukatar rayuwarsa ba sai a wannan lokacin da yaga yana ƙoƙarin rasa shi.

ya tausayawa halin da yake ciki ,kowa addu'a samun lafiya yake masa , fuskar kowa kunshe da tashin hankali mara misaltuwa, yayinda ummita tafi kowa shiga tashin hankali, kuka take sosai tana jin duk runtsi zata rayu dashi koda kuwa zatayi rayuwar kuncin a gidansa amman ba zata iya rabuwa dashi ba, dan rabuwa dashi daidai yake da rasashi gbdy .

a hankali Abba ya matso inda take durkushe ta kife kanta bisa gwiwowinta tana kuka ya da'ura hannunsa bisa kanta ya soma rarrashinta "kiyi hakuri ummita ciwo ai ba mutuwa bane zai samu sauki kiyi masa addu'a kinji addu'ar ki yafi bukata , gaba-daya dangin suna cikin tashin hankali da fargaba .

hankalinsu ya kara tashi a lokacin da suka ga fitowar doctor daga d'akin, cikin sauri likita ya nufi office d'insa Yana k'ok'arin cire yar saman farar rigar daya d'aura a saman farar rigar dake sanye dashi , yana zama suka shigo gbdy suna rige rige shigowa , Abba injiniya mah'ruf da hajiya saudat cirkocirko sukayi tsaye a gaban likita suna fuskantar doctor domin jin ƙarin bayani ganin likita yayi shiru yana duba wasu takardu yasa suka shiga tambayarsa, hajiya saude na kuka tace "ya mutu ko doctor ?
"Rayhan dina ya mutu ya barni kou likita ka faɗa min idan ya mutu ne .....?
Da kyar injiniya Ya lalla'bata ta koma waje tana kuka ,likita yayi rubuce rubucensa sannan ya d'ago ya dubesu cike da tausayawa "ku zauna "
A tare suka janyo kujerar dake gaban doctor suka zauna suna Kallonsa ,"ku kwantar da hankalinku an samu an shawo matsalar dake damunsa, bayani likita ya shiga yi musu dalla dalla akan ciwon da rayhan din yake ɗauke dashi ,zuciyarsa na daf da bugawa...
shiru sukayi zuciyoyinsu na tsinkewa cike da matsanancin mamaki rayhan ɗauke da ciwon zuciya?
Suka yiwa kansu tambayar sannan suka haɗa baki gurin furtawa a fili "doctor zuciyarsa tana daf da bugawa?

Doctor ya d'aga musu kai alamun "eh ",subuhanallahi Abba ya furta ,injiniya kuwa kalmar inna lillahi wa Inna lillahi rajiun ya shiga furtawa "meye matsalar rayhan ?
"Tunanin me yake ya Allah ka kawo mana ɗauki Abba ya fad'i haka yana dafe kanshi kamar yayi kuka, yana jin ina ma zai iya, daya cire wa rayhan cutar ya maida kanshi.
"ba san meye matsalar ba amman dai yakamata asan abun yi saboda an ɗauki shekaru yana fama da ciwon naso tun farko na sanar muku amman rayhan din ne ya hana, dan haka ku tabbatar da kun bincikeshi da kyau idan akwai abinda yake so a gaugauta yi masa idan kuma babu asan yadda za'a kwantar masa da hankali domin zuciyarsa tana daf da bugawa kmr yadda na faɗa ,ganin idanunku kun ga har ya fara aman jini "inna lillahi wa Inna lillahi rajiun suka sake furtawa atare likita ya dade yana musu bayanin kafin daga baya suka mike atare suna yiwa doctor godiya ..

Sosai likitoci suke tsaye akan shi saboda irin kudin da Abba ya saki dan yaso ya fitar dashi kasar waje ne amman likintan yace abarshi zasu iya dashi ..
satinsa daya asibiti wanda zuwa lokacin ya dawo haiyacinta yana iya gane kowa har magana yana yi mah'ruf zaune a kusa dashi yana masa magana muryarsa can kasa "abba ya damu da ciwonka sosai naso na faɗa masa saboda
nasan abinda ke damunka yana da nasaba da ummita abinda yasa ban nasar masa ba naga ita din zaka aura ,dan haka dan girman Allah na rokeka kayi hakuri ka tausaya mana ka cire damuwar wannan yayi maganar qirjinsa na dokawa
"Ina sonta ma'hruf , dan Allah ka taimaka min da adduar
DOWNLOAD
DOWNLOAD

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

11 months ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

11 months ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment