Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maka son da  babu mahalukin da  zan  iya  yiwa kamarsa  ,bazan  iya cigaba  da  rayuwa babu kai    ,ka  tausaya  min mijina .......

A matukar  fusace ya buge  hannuta  dake  bakinsa  tare  da tsareta da  manya idanunshi yana sake  jin  matsanancin sabon  'bacin rai mara  iyaka    kafin daga  bisani  ya katseta ciki fushi da  tsawa   " you are very stupid   dake da  shegiyar  soyayyar   da  kike  min , "a duniya  babu tozartacciyar   masoyiya kamarki  suhaima ...
"da na san haka   kike   Wallahi  da  tun  farko  ban  takura kaina  gurin  aurenki  ba ,nayi nadama wallahi   amman    babu  komai , Allah daya haɗa  ya raba  sai kibi  wani  jirgin .......
  yana  gama  fadar haka ya juya ya  buɗe  motarsa  a fusace yana huci ya shiga ya  murd'a key  ya  bar  unguwar  a guje  zuciyarsa kamar zata tarwatse ...
 
Juyawa tayi da  kuka ta shiga   gidansu  tana  zunduma  ihu  tamkar wata mahaukaciya sabuwar kamu  "wayyohlly   Allah na shiga  uku  na lalace ,  karo  suka  ci  da zulaihat  dake ƙoƙarin fitowa  sakamakon  sautin muryarta  data jiyo,  da  sauri zulaihat taja  baya tana dafe  goshinta  ,  cike da  matsanancin  tashin hankali  tace " suhaima lafiyarki  kuwa kike wannan  zunduma ihun waye ya mutu ?
"Wayyo Allah nah zulaihat  na mutu  na lalacewa  ta faɗa jikin  zulaihat tana sake fashewa  da   kuka ..

Zulaihat  ta  d'ago kanta  daga   jikinta   tana sake  tambayarta  a rud'e kirjinta  na  bugawa  da matsanancin  karfi  "ki faɗa min abinda ke faruwa   mana kin tasani  gaba  kina  risgar kuka, sai data ja majina  tace "wayyo Allah  ni  suhaima na mutu  karshena  yazo tunda  mah'ruf  ya sake ni .....

"What ?"when ?
Tayi mata tambayar  ajere  tana  girgiza kai    jikinta  na sake ɗaukar  rawa  " me kika ce   suhaimai ?
" Mah'ruf ne ya  sakeni, ya sakeni ,ni yanzu yaya zanyi da rayuwata ? "bazan iya rayuwa babu shi ba ku  taimakeni yan'uwana  kar na rasashi  idan na rasa shi mutuwa zan yi  nima zaku  rasani har aba .....
zulaihat tayi saurin  kamo  hannunta tana toshe mata baki   hakan  yasa ta kasa k'arasa maganar suka k'arasa   bangarenta dake zaman jiran gawar shanu    dan kar  mahaifiyarsu  taji
hankalinta ya tashi ..

  Ta zaunar daita  a bakin gado tana cewa "garin yaya haka  ta faru  ?
"Akan   wannan  muguwar  tsinanniyar yarinyar  nan ce ummita shine ya ... ....
ta kasa k'arasa maganar saboda kukan daya ci karfinta    "wallahi   bazan iya rayuwa babu shi ba aunty   tayi maganar tana fixge dankwalin  kanta tayi cilli dashi  a tsakiyar d'akin   tana wani  irin kuka .

jikin  zulaihat na rawa ta janyo wayarta ta shiga neman  layin  hajiya rahma  bayan ta ɗauka ta koro mata halin da ake ciki , ko cikakken minti ashirin ba'ayi ba ta bayyana  a gidan , nan suka kulle kansu a d'akin zulaihat  suka  yita rarrashin  suhaima daga karshe suka yanke shawarar  zuwa gurin baba   na  isheri  domin karkato da hankalin mah'ruf .
suhaima  tayi shiru tare da rafka uban tagumi tana kuka cikin zullumi da rashin sanin abun yi, dan gabadaya maganganu  y'an'uwanta basa  shigarta  duk da bata  cire tsamammanin akan  shawararsu na taimaka mata ba, tasan matukar suna da hali zasu taimaka mata  ta koma gidan  mijinta  "yayarmu  dan girman  Allah  kar a ɗauki dogon  lokaci  ,aiki nake so mai  zafi cikin gaugauwa  bana son na rasashi a rayuwata ."bazaki rasashi ba  suhaima ki bani nan da kwanaki  biyar zuwa sati da  kanshi  zai zo har inda kike  nayi miki wannan  alkawarin.

ta rungumeta a jikinta tana janyo  numfashi da kyar "na gode yayarmu Allah ya bar mana ke ina alfahari da ke nasan zaki iya komai  ,hajiya rahma  ta  shafa  bayanta tana cigaba da rarrashinta  sai gurin  sha daya    saura hajiya  rahma  ta bar gidan shima ɗan mijinta ya azalzala mata ne if not Sai ta kai shabiyu .

Mah'ruf    zaune   shiru  akan  kujera  mai  zaman mutun  d'aya  ya  da'ura  hannunsa ɗaya a saman goshinsa yayinda d'ayan  hannun ke bayan keyarsa yayi pillow dashi, yana furzar  da iska mai zafi  daga  bakinsa .
  a hankali  ya  daura   kafafunsa duka  a  kan Centre  table   din dake gabansa  ya mike su yana girgizasu  ,sosai   ƙwaƙwaluwarsa  tayi  zurfi cikin   tunanin  sakin da yayiwa  suhaima , gabadaya   zuciyarsa babu  dadi , sai dai bai yi nadamar  sakin da yayi  mata ba   , cikin   haka mama  ta  sauko  daga samanta   ta  ganshi  zaune   cikin  yanayi  na damuwa  da tashin hankali ,   kallo ɗaya tayi  masa ta fahimci  yana cikin  zallar damuwa   ,  take yar  farar data  sauko dashi akan  fuskatar  ta  ɗauke ,ta  karasa  kitchen  ta d'auko masa  hollodian  milk   mai  sanyi    ta d'aura akan  tire  da  glass cup  ta fito ta  d'aura  tiren  akan ƙaramin   table  ta tsiyayya hollodian   a   glass  cup .
har  sanda ta gama tsiyayawa   bai  san da zuwanta  gurin  ba ,  sai daya  yaji  tafin hannunta cikin  sumar  kanshi  sannan  ya   motsa  fuskar  a murtike  tamkar wanda   aka yiwa  mutuwa  ,ya haɗe hannuwansa duka ya  shafa fuskarshi  batare daya  yi  magana ba ,
  itama bata ce masa uffan   ba  ta mika masa cup din dake cike da  hollodian   data  tsiyaya masa  "ungo ka sha kaji sanyi .

jikinsa a matukar sanyaye  ya  kai hannunsa ya   amsa  yana sauke  naunayen ajiyar zuciya  sannan  ya  kai bakinsa ya  kur'bi kaɗan  ya ajiye cup akan table  muryarsa a kasalance yace  "na gode mamana "

  "Me ke  damunka baba babba ?  Tayi masa tambayar  tana tsareshi da idanunta  ,da kyar ya buɗe  bakinsa yace "
Babu   komai  mamana "
" babu komai shine duk jikinka  ya sake  haka?  "ka faɗa  min  gsky karka min karya  mana   " hannuwanta duka  ya  kamo cikin nashi ya  rike gam   yana  kirkiro  murmushin  dole "karki damu mamana zan  sanar  miki  abinda ke damuna  zuwa  gobe inshaallahu , ya  faɗa  mata   haka  saboda  yasan halinta matukar  taji  abinda ya faru tsakaninsa da suhaima   tabbas zata takura  ya dawo  daita a daren,  shi kuma abinda ba zai so faruwarsa kenan ba  dan  bai  shirya dawo  daita gidansa a halin  yanzu ba, yafi  son  ko zai dawo daita  sai ta taga rayuwa ta shiga  hankalinta   ta yadda  zata san matsayinsa da darajarsa, bare baya tunanin sake rayuwa daita  ,duk macen da zata iya  kallon  idanun  mijin aurenta ta kirasa da kalmar  bunsuru  rayuwar aure  daita  bashi  da faida  ....

   Murmushi mama  tayi "fatan dai ba wata  damuwar  bace kou  ?
Ya d'age  mata girarsa d'aya   alamun "eh .." to allah ya kai mu  goben  yasa muna  da rai da lafiya   ,  a hankali ya motsa  bakinsa ya amsa da  "ameen ..

Da  sauri  ummita take saukowa  daga  step  har lokacin bata  cire kayan dake   sanye   a jikinta ba , turus  tayi  sakamakon ganinsa  zaune  shiru tayi   dan a tunaninta  tuni ya dade a gidansa shi da matarsa  .
mama  na  ganin saukowarta  ta yunkura ta  mike   ta ɗauki abinda ya  sauko  daita  tayi hanyar  sama tana mata  magana  a hankali cikin muryar rada ta yadda mahruf ba zai ji ba  "kije ki  kwantar  masa hankali da alamun yana cikin damuwa " tsuke ƙaramin bakinta tayi tana bin mama da kallo a ranta tace "haka  kawai ya kwaso  damuwarsa  naje ni ya sauke akaina ....

Bayan  barin mama parlour'n  ya  tsura  mata idanunshi  yana  kallonta batare  da yayi  mata magana ba har sanda ta shige  kitchen  ta dibo abinci a plet  ta  fito  ta wuce shi  tana taka step da  sauri  sauri "fat lion .......
Ya kira sunanta da kasalalliyar   muryarsa dake  cike da  tashin hankali , tsayawa  tayi cak batare  data juyo ba  "ki  daina   irin wannan tafiyar  da karfi plz ....."
Har lokacin  bata ce masa  qala ba ta cigaba da tafiyarta  da  karfi  kamar yadda  tayi niyya  har  ta  sauka akan step tare  da zancen zuci  "ji min  mutun da iyayi  tsiya  ko meye  ruwanshi da tafiyata oho ?
"wayyohlly  Allah  ya faɗa  da  sauri  yana  dafe daidai  saitin zuciyarsa  a dalilin  yadda  ta k'arasa tafiyar da karfi  .

ahankali ya tura hannunsa ɗaya  cikin sumar  kanshi  yana chakud'awa tare  da ciza lip's d'insa na kasa  "i love you more than you know  ya  furta  kalmarta  ta karshe  garesa  a wanin  da suka gabata daman yasan karya  ne  ba  gaskiya ta faɗa masa ba  ,kissa  ne kawai irin nata  ya san  ba zata taba son shi ba   gashi kai  kuma  ka kamu da matsanancin  soyayyarta ba  inji  cewar kyakkyawar  zuciyarsa..

A hankali ya shiga girgiza kanshi yana karyata zuciyarsa  yana cigaba da   jin abinda yake ji akanta ,yayinda  ko wani part na jikinsa ke  sake bud'ewa suna  kar'bata acikin zuciyarsa da bata matsayi mai mahimmanci a rayuwarsa .... ..

Yana  nan zaune har sanda kowa  na gidan ya shigo  , su  meenal  kuwa tuni an zarce daita gidan mijinta dake labak estate  dake abulegba  , ya mike akan  kujerar  ya kwanta yana  tunanin ummita, yana  son ya kice tunaninta a zuciyarsa amman ya  rasa  dalilin da yasa  tunanita  yaki barinsa hasalima sai   sake  kawo masa farmaki yake .... .
"to  kod'an cikinsa dake jikinta ne ?
Yayi wa kanshi tambayar  yana dafe  goshinsa , take zuciyarsa ta amince da  hakan ,yana  son faɗa mata tana dauke da cikinsa ko dan tasan yadda zata dinga movement dinta amman yana fargaba  bai san me zai faru   ba  idan tasan da  zaman  cikin , da karfi  qirjinshi ke dokawa kamar zai fito waje saboda tsananin tunaninta daya addabi zuciyarsa, ya takure jikinsa  guri daya tare da lumshe idanunsa  yana shaƙar sanyayyen Kashim turarenta dake makale da kayansa ,
kusan karfe dayan  dare yayi   agurin yana kwance  tana  tunani  batare da   bacci yayi nasarar  daukarshi  ba.

bangaren    suhaima kuwa  itama     kasa runtsawa tayi  ko abinci daren kin ci tayi duk irin  fama da zulaihat ta  dinga  yi  daita taci abinci kin tayi  har ta gaji  ta kyaleta, ta barta da tunanin neman mafuta, gabadaya tunaninta  kaf ya tafi ne akan  yadda zata koma gidan mijinta da kuma yadda zata raba auren ummita da  mijinta  .. ....

ummita  ta  sake  saukowa   cin abincin dare   tayi mamakin ganinsa  kwance  bai wuce ba  ta k'arasa har inda  yake  kwance  ta tsugunna  gabansa tana kallon  kyakkyawar fuskarsa mai tattare da haiba    zuciyarta  na sake  samun  natsuwa dashi   , a hankali  ta  kai hannunta  fuskarshi  ta  shafo  kasumbarshi  tana lumshe kyawawan  idanunta  , duk yana  jinta  ya sake lafewa yana  sauke numfashi  a hankali tayi kasa da hannunta  zuwa faffad'an  qirjinsa  mai  cike da yalwan  gashi kwance luf ta soma shafawa tana cigaba da kallonsa .

   a qalla ta ɗauki sama  da minti goma tsugunne a gabansa  tana shafa  sumar  fuskarshi zuwa qirjinsa  tana kallonsa  sannan  ta yunkura ta  mike  tsaye da niyyar barin  gurin  on-expecting taji  ya  riko hannunta tare da  fizgota   ta fado  saman  fad'ad'd'en  qirjinshi  tana sauke numfashi haɗe da furta "wayyo  cikina ..... 
ta soma ƙoƙarin mikewa daga  jikinshi tana yatsina  fuska  da jin haushin  abinda tayi  gashi ya ka mata tana  kallonsa  da shafa jikinsa ,sake matseta  yayi ajikinshi sosai   yana fidda numfashi mai haɗe da shaukinta bai san sanda yace "sorry nayi kuskure bansan zaki ji ciwo  a cikinki  ba ya kike ji yanzu ko zamu hos.........
saurin datse harshensa yayi kafin ya k'arasa abinda  yake son fadi ,
ta watsa masa wata ƙatuwar harara tana  yatsina   fuska  wani irin kallo ta  dinga  masa    kafin daga  baya tace "plz ka  sakar min jiki  ta yunkura  zata sake  mikewa  da karfi yayi saurin kai bakinsa cikin kunneta yana hura mata iskar bakinsa   "plz ki taimakeni ki daina abubuwa da karfi irin haka ,da fa ba haka kike abubuwanki ba   me yasa yanzu kike yin haka  ne ?
"Ra'ayi  ne ko dole sai na cigaba a yadda ka sani ?

"Yes ya  faɗa tare da zarce wa da shafa jikinta , "kiyi  hakuri ki daina  zan  ji dadi idan kika daina  ,ba tayi ƙoƙarin dakatar dashi  daga  abinda  yake mata  ba,dan haka nan ta dinga jin wani irin dadi na ziyarar  jikinta , kamshin turarensa da take  shaka  a halin yanzu yana  sake haddasawa jikinta  jin wani  iri .....
yayinda feeling d'insa  ke kawowa sansar jikinta farmaki ,fuskantar ya hade da nashi idanunsa na kallon cikin nata " "kallon me kike min har da shafani  ko soyayyata ce ta hanaki runtsawa  ?
tayi shiru haɗe da  shigewa  jikinsa tana sake shaƙar kamshin turarensa  me kashe mata  sansar jiki ....

" Fatlion  ina  matukar kishin aurena dake kanki fiyye da  tunaninki  haushinsa ya kamata ta tsani  taji yace  yana kishin aurensa dake kanta , kenan ita  ba zai  yi kishinta ba sai dai na aurensa  ?tsaki taja a kasan ranta batare da tace masa komai ba
kusan minti goma suna haka yana yawo da hannunsa a sansar  jikinta ita kuma  tana faman   lumlumshe idanunta alamun bacci, d'agata yayi suka bar  parlour'n  zuwa d'akinta  ya kwantar daita shima ya kwanta ya zagaye cikinta da  duka hannuwansa      suna  fuskantar  juna yayinda hancinsa ke gugan nata, bakinsa daf da nata yana busa mata hucin numfashnsa me tafiyar da ruhi .

A tsanake   ya dinga rabata da kayan jikinta yana ajiyesu a gefe haɗe da  tabo  wasu wurare ajikinta daya san dole idan ya ta'ba  zata ji  feeling d'insa ,taja numfashi da kyar ta sauke tana kokarin shigewa jikinshi, shi kuwa a tsanake  ya dinga  yawo da harshensa akan  lip's d'inta kafin daga baya ya haɗe bakinsu guri daya ya shiga tsotsan  bakinta  tamkar wani mayunwacin zaki dan a matukar bukace yake daita sai dai  ba zai iya kallon idanunta ya  amfana da  jikinta ba, yasan muddin wani abu ya shiga tsakaninsu tana sane kashinsa ya bushe agurinta  .

kusan awa daya ya ɗauka yana juya harshensa cikin bakinta batare daya cire ba  gabadaya ya manta da wata suhaima a rayuwarsa , itama ummita ya mantar da ita komai  bata gane komai da kowa sai shi da sakoninsa  a haka har  bacci 'barawo yayi awon gaba dasu cike da shaukin juna  sai goshin asuba ya farka ya maida mata  kayanta  ya shiga bayin  dake cikin dakinta  yayi  wankan sarki dan a wasanin da yayi daita  yayi realizing   ya fito
ya qarasa inda take kwance  ,kissing din goshinta  yayi  cikin zuciyarsa  yace "mayya yarinya  tayi nasarar dasa soyayyarta  cikin zuciyarsa  sannan ya fita zuwa masallaci ...

Yana  fita ta sauke naunayen  ajiyar zuciya dan ba wani  bacci take  ba  ,  mikewa tayi  a hankali ta shiga bayi  tayi tsarki  saboda yanayin jikinta  daya ɓaci sakamakon  hannunsa ɗaya kwana yawo a sansar jikinta sannan ta dauro alwala ta fito ta sauya kaya  tana jin tafiyar tafukan hannunsa  a fatar jikinta, tayi sallah zuciyar  na makale da tunaninsa  tana jin wani dadi na ratsa sansar jikinta  da zuciyarta ," ina ma zasu kasance tare kamar  yadda suka kasance a daren jiya ? duk da  basu jiyar da junansu  komai ba illa romacing dinta  daya  kwana  yi .

Mikewa tayi  ta faɗa saman katifa   duk juyi sai  ta tsinci kanta cikin yanayi na daban da bata taba tsintar kanta ciki ba sai akanshi ,ta san  mijinta na daban ne acikin maza  kuma na kece raini,sannan  mijin  yayi ne  da kowace mace zata so mallaka har ma tayi alfahari dashi , "ki mika wuya  kawai ummita ki rungume mijinki ,ki janyoshi jikinki ki bashi kulawar da zai soki ,ki manta komai kuyi rayuwarku  ....

lamo tayi  tana runtse idanunta da tunanin hanyoyi da zata bi domin mallake  zuciyarsa  da komai nashi ...
wuni  ranar a kwance tayi shi cike da kewarsa sai dai har yammacin ranar bataji duriyarsa acikin bangarensu  ba, shi kuwa yaki dawowa gidan ne saboda mama  dan karta rutsashi  da tambaya ..

Bashi ya shigo gidan ba sai gurin goma na dare kai tsaye part din mama ya shiga ya ganta kwance alamun ta soma bacci bai yi kokarin tashinta ba ya juya ya nufi dakin ummita, kwance  ya isketa ta takure jikinta guri daya  tana bacci cikin rigar bacci mai sharara kallo ɗaya yayi mata ya k'arasa shigowa da sauri  ya haye saman katifa yana had'iye abinda ya tsaya masa a makoshi, ya kwanto jikinta   ya kai bakinsa cikin kunneta ya soma hura mata iskar bakinsa kamshin turarensa ne ya kaiwa hancinta ziyara a hankali ta soma jin wani sanyayyiye dadi na shigarta ta sauke naunayen ajiyar zuciya sai dai ta kasa bude idanunta har sanda  ya kamo ya  kwantar  daita ajikinsa  suna fuskantar juna  a hankali suke shaƙar numfashin juna  kafin daga baya ya kai bakinsa dai-dai  bakinta yana tsotsar pinky  lips  dinta har  yayi nasarar  cafko laulausan  harshenta  nan ta bud6e idanunta tarrrrr akan shi wata irin kunya yaji ta mamaye ilahirin jikinsa  amman jin ta kai hannuwanta duka ta kamo fuskarshi tana busa masa numfashinta  yasa ya sake rungumeta  a jikinsa  yana cigaba da sarrafa harshenta  cikin bakinta  cikin wani irin yanayi na shaukin juna suke exchanging numfashin , take  yanayin fitar  numfashinsu ya sauya   suka  rud'e   tare da  fita  haiyacinsu  , ya kai hannunshi  kasanta  yana shafa  mararta zuwa pent dinta    yana jin wani irin farinciki mara misaltuwa saboda jiyo tudun  cikinta  , cike da shaukinsa   ta  tura hannunta  cikin sumar kanshi   ta soma wasa da gashinsa  tana sauke numfashi  , wani irin numfashi yake  fizgowa  da karfi yana fitarwa,  bai ankare ba  ya ji ta cafke  harshensa dake cikin nata  ,ta soma  sarrafashi  tana tsotsar bakinsa  kmr yadda taga yana  mata , sai daya gama yamutsata sosai, da ragewa  kanshi zafi  sannan ya barta ya soma ƙoƙarin  mikewa ta riko tafin  hannunsa gam cikin nata   tana narke masa ajiki tana fidda  numfashi sama sama
da rausayar masa  da fararen  idanunta ,ya lura kwarai da zai dara daga abinda yayi  zata bashi haɗin kai ,kokarin cire hannunsa yayi  acikin nata amman taki sakar masa tana sake narke masa dole ya rankwafo jikinsa ya kai bakinsa cikin kunneta "menene fatlion ?
"Me kike bukata  ?
Yayi  mata tambayar yana hura mata iskar bakinsa cikin kunneta take tsigar jikinta suka mike  gabadaya kamshin turarensa ya addabi hancinta da sake    tunzira zuciyarta akanshi da  matsanancin sha'awarsa ,yayinda iskar bakinsa da yake hura mata ya sake kashe mata jiki "kin yi shiru ki faɗa min  idan akwai abinda kike bukata daga gareni  saboda  Ina son wucewa  gida yayi maganar yana manneta da qirjinshi da tsura mata ido ,sai numfashi take fitarwa tana sake narke masa ajiki "baza kiyi magana ba ?
nan ma  shiru  tayi taki cewa komai duk da  so take tace  kar ya tafi  ya barta ya kasance tare daita amman bazata iya furta masa haka ba ,
ta shige jikinsa sosai  tana shaƙar kamshin turarensa ya daura hannunsa akan sumar kanta yana shafawa ahankalin  zuwa gadon  bayanta , ya zare hannunshi ya janyo blanket ya lullu'be mata  jiki  sannan ya sauko ya durkusa daidai fuskarta "zan wuce gida ki kular min da kanki ban da tsalle tsalle plz  yayi maganar tamkar wani maraya "idan kina bukatar wani abu ki kirani tayi shiru tana mamakinsa "lallai namiji fa bai da kunya tsab ta gama karanceshi so yake ya mallaki jikinta cikin sauki  sai dai ina bazata bari ba zata cigaba da rud'ashi kamar yadda yake  rud'a mata jiki  ..

*******
Hajiya rahma  ke  tafiya  da baya da baya tana kokarin   shigowa bukkan boka na isheri  har ta karasa  shigowa  bukkansa sannan  ta juyo da gangar jikinta tana kallo cikin bukkan  inda ta iske bokan zaune babu komai  ajikinsa daga  shi sai wani dan kanfai da  iya gabansa kawai ya rufe gabansa wani kasani acikin bakin dutse  .
ya  kalleta  yana washe wakeken  bakinsa tare da bushewa da mahaukaciyar dariya  " shadiya  yau kece a gari ?
"Nice    aiki  yanzu magani  yanzu ta samu guri ta zauna can nesa kaɗan dashi tana kunshe miyon bakinta saboda warin da bukkan keyi  "ya jikin alaja ? ya tambayeta  cikin yaren yaroba  yana jan layi biyu akan  kasa da yatsun hannunsa .

" tana  kan samun sauki dai  "ai na faɗa mata abinda zatayi taki, daga karshe ma  ta   ɗauke kafafunta  a gurina ,na faɗa mata zata samu lafiya amman lallai sai ta bada   rayuwar mahaifinku  domin nata rayuwar , hajiya rahma ta jinjina  kai  da girman al'amarin dan tasan wannan ba abu ne mai sauki ba ,  a yadda hajiyarsu ke son mahaifinsu ko farcensa ba zata iya bayarwa ba bare rayuwarsa ...

  Boka  ya soma buga kasa domin son sanin abinda ke tafe daita kusan minti goma yana aiki zana kasa sannan  yaja wata ƙatuwar numfashi da ajiyar zuciya atare  sannan ya soma magana cikin harshen yaroba "wannan yaron zai yi wahala ku iya mallakarsa kamar yadda kuke bukata  saboda ta kowani bangare zagaye yake da tsari, iyayensa suna tsaye akanshi  shima kuma haka babu yadda zaku iya dashi..
"yanzu  babu abinda za'a yi  yanzu ?
"Babu kuma duk inda kika je kudinki kawai za'a ci sannan ko anyi masa aiki daga karshe abun zai iya taba duka zuriaku saboda karfin addu'ar dake zagaye dashi ,dama baya tsaye gurin ibada ne   akwai aikin da zanyi da kanshi zai dawo wanda
dawowarsa  kuwa zai yi daidai da mallakarsa gaba-daya amman yanzu kije gida tukunna idan an kwana biyu ki dawo mu duba mugani  "bama bukatar 'bata lokaci aiki mune bukata boka dan yar'uwata tana cikin wani hali taki ci taki sha ka sake dubawa idan akwai yadda za'a yi "babu shadiya idan akwai zan miki  duk inda zaki akanshi kudinki za'a ci a banza irinsu asiri baya cinsu idan ma yayi tasiri na wani lokaci ne    ..

Babu  shiri hajiya rahma ta baro gidan boka tana surutai "yanzu me zata cewa suhaima bayan tayi mata alkwarin mah'ruf da kanshi zai dawo gareta  ...
Jugun jugun sukayi a daki hankalinsu a tashe suna tunani mafuta dan kuka ma kasawa suhaima tayi sai dai idanunta sun kankace sun koma tamkar garwashin wuta naunayen ajiyar zuciya hajiya rahma  ta sauke "ina gani mu dan dakata tukunan kamar yadda bokan yace "ni dai yayarmu kisan yadda za'a yi mah'ruf ya  maida  ni gidansa ta kowani hali ne ,ko  kisa dady  ya nemi abbansa ya bashi hakuri nasan muddin suka sa baki zai maidani.

"shikenan ki kwantar da hankalinki zan sanar masa idan Allah ya taimakemu ya maidake sai ki shiga hankalinki ,ki iya bakinki , kiyi taka tsantsa kiyi masa biyayyar karya na sha faɗa muku shi sihiri baya tasiri sai da biyyaya bawai da kun kama maza a hannunku shikenan ba ,ki kawar da idanunki akan duk abinda zai yi da yarinyar akwai makirci kala daban daban da zan koya miki ina tabbatar miki muddin kika rike biyyaya da waɗan makirci wallahi kina zaune zai dankarawa shegiya saki uku rasss ku matso kuji atare suka matso daga zulaihat har suhaima tayi musu rad'a  kunne ,wani irin ihun dadi suhaima ta saki "dan Allah yayyarmu ki san yadda zaki yi na koma wallahi zanyi duk abinda kika ce nan suka cigaba da tautaunawa a tsakaninsu har yamma  hajiya rahma na gidan, har sai data gana da mahaifinsu sannan ta bar gidan , faɗa dady yayiwa suhaima sosai sannan yace zai nemi Alhaji Ibrahim , bai yi sanya a gwiwa ba ya nemi Abba saboda shi kanshi baya jin dadin zaman ya'yansa gida gara sakin suhaima za'a iya gyarawa tunda saki daya ne , zulaihat ce dai sai hakuri .....
Abba yayi matukar mamaki  jin bayanin dady daga karshe yace karya damu da izinin Allah kamar mah'ruf ya mayar da suhaima d'akinta ya gama ..

Karfe tara daidai Abba ya kira mah'ruf lokacin daya shigo parlour'n Abba , sai da gabansa yayi mummunar faduwa saboda ganin mahaifiyarsa da mama da injiniya  har ma da Hajiya inna, guri ya samu ya zauna cike da biyyaya yana ƙoƙarin gaishesu inna tayi saurin katse shi "amman babana bansan tsami bane kai sai yau ta yaya dan rashin tunani , da rashin  hankali zaka saki matar arzikinka, yarinyar mai biyyaya da sanin ya kamata da son yan'uwanka , shine dan ka iya wulakanci ka rasa wacce zaka saka sai ita   sannan kayi mukut da bakinka  da rashin hankali ...
tsaki yaja saboda takaicin maganar  Hajiya inna ransa a matukar 'bace ya soma magana "kin san abinda tayi min da zaki zo kina damun mutane , wallahi idan kika hassalani zan mata mai gabadaya na huta .

" wanda ya fasa ya raina uwarsa da ubansa dan me shegen girman kan  tsiya wa ka cuta kanka dan bazaka ta'ba samun kamarta ba ehee ..
"Hajiya dan Allah kiyi hakuri ki bari muyi abinda ya taramu anan kai kuma kar na sake jin bakinka idan bani  na nace kayi

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

2 years ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment